Showing 39001 words to 42000 words out of 110841 words

Chapter 14 - BAKIN CIKI BOOK COMPLETE BY ESHAT.txt

12 Sep 2025

62

shikenan nima
na gode, amma don girman Allah abi a hankali
asamu a sulhunta. A. Basiru yace ba komi baba
mun gode. Sukayi sallama ya shige gida. Tsho
ya kama gabansa cike da wasi-wasi cikin ransa.
Falon Uban dawaki A. Basiru ya koma ya
xayyane masa labarin da tsho yaxo da shi, da
kuma shawarwarin da ya bayar. Abba bai iya
cewa komai ba saboda tsabar bacin rai. Sun jima
suna tausar xuciyar Abba sannan suka koma
sasan su, inda matan suke xaune dirshan suna
xuba gulmace gulmace. Suna zagin mama da
iyayenta. Basu hanasu ba, hasalima zama sukayi
suka dora xancan babu dadin ji, ita kuwa baiwar
Allah mama, tana tare da Danliti cikin mota,
bayan fitowarsu asibiti, yana ta faman
rarrashinta, don ta daina kuka ta kwantar da
hankalinta, da kyar ya samu ta nutsu ta daina
xubda hawayen. Yayi fakin kofar shagon sa ya
juyo ya fuskance ta. Yanxun ya xamuyi mu
fuskanci juna abba ya gane cewar idan ba mu
auri juna ba, komai zai iya faruwa da mu? Tace,
ai ga misali nan na fara nuna masu kuma ba xan
fasa ba, ina nan akan baka na. Ya marairaice
yace wannan misalin bana son irinsa sakeena,
don bana son na rasaki. Gaba ki daya kin fita
kamanninki kin kuwa ci abinci yau? Ta kada kai,
abinci ba xai iya wuce min ba Dan liti ina cikin
wannan masifar meye illar ka? Da abba xai ce
samm baka dace dani ba? Ya lumshe ido, ya
bude kafin yace, saboda suna ganin ni bako ne,
bani da kowa agarin nan..... Ta katse shi, hakan
shine xai nuna daga sama ka fado? Wannan ba
hujja bace Danliti, son rai ne kawai irin na iyaye
ni kuwa ba xan yarda ba, sai dai muyi ta ba juna
wahala. Ya ja gwauron numfashi ya sauke, ya
lalubo yatsun ta ya runtse su cikin nasa, ya xuba
mata ido yace, nasan ki na sona sakeena, amma
ki daina damuwa ko sun hana ki xuwa wajena,
sannan ki daina wasa da rayuwarki, don tana da
muhimmanci aguna. Abu da gaba, ki daina zama
da yunwa, ita ma zata iya illata minke. Yaunxu
abinda nake so dake, ki zo muje shago in hada
miki tea ki sha, sannan kije gida ko sun zage ki,
kar ki ce dasu komai, don kar su sami damar
dukanki. Kinji bebi na? Ta amsa da ka. Tace,
yauwa mai kyau, to dan kalle ni mana, ta dube
shi suka yiwa juna xuru, jim kafin ta kauda kai,
tana dan murmushi, shima murmushin yayi yana
mata kllon kwadayi, ya ja yatsunta xuwa bakinsa
ya sumbata. (kuji dan iska). Ta kwace da sauri
ta kara sadda kai. Yace, bebi na kenan, sarkin
kunya. To muje ko? Zaki iya sauka ko in zo in
fito dake? Ta balle murfin batare da tace wani
abu ba ta fito, shima yayo waje yana kallon
yadda take dingisawa har cikon shagon sa. Ya
ba za mata tabarma ta zauna. Ayuba na mata
sannu. Akwai wani labule jikin wata kwana a
shagon, sai alokacin ta gane daki ne. Cikinsa
Dan liti ya shiga ya fito da filas da kofi da cokali
ya aje gabanta. Yace ga ruwan zafi, ki daga
idonki, ki duba duk irin madarar da kike so, ki
zaba na dauko miki. Tana murmushi tace, kai
wacce iri kake sha? Yace ai bana shan madara a
tea, ganye kawai nake sha. Kinsan buzaye ai?
Tayi dariya tace, ba'a raba su da jiko. Yace shayi
dai. Ta ciga da dariya tana fadin, to shayi, wai
menene sirrin shayin nan ne? Yace xan gaya miki
amma da farko wacce madara kika zaba, in
dauko miki? Na kowa ki sawa cikinki abinci.
Tace, bani peak ta ruwa. Ya mike ya dauko hade
da katon bread ya hada mata tea mai kauri,
domin duka ya juye peak din. Tana sha, suna
hira ya gaya mata ire-iren shayin su. Bayan ta
kammala, ya matsa gareta yace, yanxun ya
kamata ki koma gida kiyi barci, ki huta kinji?
Karki damu ko an hana ki xuwa nan, wane tym
zamu hadu. Ke dai kiyi addu'ar fatan samun
nasara. Tace, Insha Allahu zanyi. Yana
murmushi ya mika baki ya sumbaci kuncinta. Ta
sunkuyar da kai tana murza yatsunta. Ya zura
mata ido, gaba daya jikinsa yai la'asar, sannan
ya dago habarta, suka dubi juna, yace I love U!
Tace me too, yace, to ki tashi kije gidan, zaki
iya ko? Tace xan iya. Ta yunkura ya taimaka
mata mikewa suka fito tare ta sallami Ayuba, ya
dan taka mata kadan ya dawo, yana zuwa ya
kwashe da dariya, ya mikawa Ayuba hannu suka
tafa. Ayuba yace, baka da kyau dan iska. Yace
raina kama gayya! Gaskiyya ta gurzu, na
tausaya mata wlh. Shegiya akwai taushin fata,
baka ji ba kamar auduga, duk ta susuta ni. Ya
zura masa ido yace, tunda kuka shiga, na
karance ka, shi ya gaba na yayi ta faduwa, kar
ka sata labulan nan. Yace, ko na sata ba zata
hani ba, nake gaya maka kuma babu abinda zai
faru dani. Kawai dai ban yi niyya bane yanxu, ni
nasan abinda nake hari. Yace a dai rika tuna
Allah Danliti, shagalinka yayi yawa kuma ina ma
kwadayin cin ubanta nakeyi, ai har uanxun
duniya bata fara zaginta ba. Kaga da sauran
mutuncinta. Ya bishi da kallo, bai ce komai ba,
yayi tsaki ya tashi ya koma shago abinsa. Tana
tafe tana dingishi, ta iso gida, kanta tsaye bata
fargabar komai ta fada zaure, kicibus suka yi da
Ya Ali sabe da jakar sa zai bar garin. Ko kallon
sa batayi ba ta wuce, ya biyota yana kiranta bata
waigo ba, balle ta amsa, ta shiga sasan su har
falo yana binta. Su abba na kallon ikon Allah,
domin dai Mama bata saurara ba, cikin dakinta
ta shige. Ya Ali na shigowa ya gansu, ya ja birki
amma ransa na son ya shiga wajen mama, yayi
magana da ita, abba ya dube shi. Yace, Ali ka
daina wahalar da kanka abanza, mama bata
bukatar komai sai addu'a. Saboda haka ka kama
hanyarka ka koma bakin aikinka. To amma, kayi
hkr Abba, don girman Allah karku daketa, kamar
yadda kace nayi mata addu'a kuma kuyi mata
addu'ar. Yace, na yarda da kai Ali, amma ban
yarda auran kowa ba, sai wanda na aminta da
shi. Zan gani idan ita zata daura wa kanta aure
ko mune? Yace, haka ne Abba don Allah ina
rokon 2mins in ishiga in dayi mata nasiha, koda
bazata saurere ni. Ya suke numfashi yace, shiga
Ali, Allah ya sa taji abinda zaka gaya mata. Ya
aje jaka ya wuce cikin dakin. Tana kwance
niyyar barci ma takeyi, kamar yadda Danliti ya
umarceta. Yana shigowa ta runtse ido ta juya
baya, ya tsya kanta yace, komai zakiyi, dole in
gaya miki gaskiyya, tunda kunnuwanki naji.....
Fadan hakan yasa tai sauri ta toshe kunnuwan
nata da yatsunta. Yace aikin banza kike yi
Mama, kuma rayuwar ki na cikin hatsari, muddin
baki daina jefa su abba cikin BAKIN CIKI ba.
Menene anfani abinda kika aikata yanxu? Ki
kashe kanki a banza da wofi, ba asarar Danliti
bane, don na tabbata duk tsananin son da yake
mi, ba zai hallaka kansa ya biki ba. Ki nutsu kiyi
tunani. Akwai abinda magabatan mu ke hangowa
kan wannan ra'ayin naki. Ni zan koma kuma ina
fatan zanji canji daga gareki? Ya juya ya fice
bata re da ta daga kai ta dube shi ba. Wani
dogon tsaki ta raka shi da shi, wanda ya tilasta
masa juyowa ya dubeta ji, sannan ya karasa
ficewa. Ya dauki jakarsa ya kara yiwa su Abba
sallama, ya bar gidan ciki da Al'ajabin maras
misaltuwa a zuciyarsa. Bayan tafiyarsa, su
Umma suka shigo gunta ta tana kudundune ta
dunkule wuri daya, ko 'ina jikinta ciwo. Umma ta
zauna gefen gadon shi kuma Abba n atsaye
kanta, yace Mama barazanar kashe kanki ba zai
sauya abinda ke cikin raina ba, idan ma baki
sani ba, ki sani gara ki mutu da mutunci na ya
xube a idon duniya. Saboda haka fadowar ki a
mota bata girgiza ni ba balle ta cire daidai da
kwayar zarra na alkawarin da na daukarwa Al-
ameen da iyayensa. Mu zuba ni dake, duk wani
matakin rashin kunyar da kika hau, ni na fi ki
hawa matakin karshe! Ya juya ya bar dakin.
Umma ta kura mata ido, hawaye suka cika
idanuwanta, tace Mama zaki iya tashi ki saurare
ni? Ta shiru bata motsa ba, ta sake fadin, idan
har ni na haifeki kuma na isa dake, to ki tashi
zaune ki fuskance ni. Ta jima kafin ta yunkura ta
tashi fuskar ta sharkaf da hawaye, kamanninta
sun sauya, saboda fitinar da ta daukarwa kanta
a tunanin iyayenta. Umma ta zura mata ido,
kafin tace, nasiha xan miki, idan kiji ki dauka
wahala ta kare miki, idan kuma kince ba haka ba
to rayuwa zata cigaba da yi miki kunci, domin
Allah ne ya wajabta miki yi mana biyayya,
muddin ba mu sa ba masa. Ban jin akwai wani
dalili ko hujja da xaki gayawa ubangiji da ace
kin mutu sakamon bude murfin motar da kikayi,
ki fado lasa. Wannan ya nuna muraran kin kashe
kanki ne da gan-gan. Ma'ana kin mutu kafira.
Me zai jawo miki wannan masifar da hankalinki
da komai? Ko kuwa kina so ki nuna mana kin fi
karfin mu cikin dan kankanin lokcine ne? Kina
nufin mu sanya miki ido ki zubar da mutuncin ki
da mu a garin nan? Ban taba tunanin Mama, ke
din nan zaki zama kaza kici share baki a game
da irin so da Kaunar da Al-ameen da iyayensa
syka nuna miki. Haka kuma ban taba mafarkin
ke din nan zaki iya hango wani da namiji ya rufe
miki ido har kice kin fo sonsa akan Al-ameen.
Kina nufin daman can yaudara sa kike yi ba
tsakani da Allah kike sonsa ba? Har yanxun
mafarki nakeyi Mama, don ba gaskanya abinda
yake shirin fitowa daga gareki nake ba. Ki yiwa
girman Allah kir ki bari wannan magana ta zama
gaskiyya, ba ke kadai za'a zaga ba har damu
iyayenki. Na mu ma zai fi yawa saboda mune
muka isa dake. Yanxun abinda na rokonki shine,
ki share hawayen ki ki gaya min, laifin me Al-
ameen yayi miki kike son ki katse masa rayuwa?
Gaya min daga ni sai ke ce a dakin nan kuma
share hwayenki, muddin shi ne baida gaskiyya.
Ta shre hawayneta wasu suka xubo mata,
kalaman ummanta masu taushi ne dashiga
xuciya, amma kash Danliti ya riga ya gama da
ruhinta. Allah ya bashi sa'a ya kamata ahannu,
idanuwanta ba sa ganin kowa sai shi,
kunnuwanta ba sa sauraron kowa face kalaman
yaudarsa da izgilanci. Dalilin da yasa kenan
kalma daya bata tasiri a hrt dinta, a duk tsahon
jawabin da Umma tayi, da ka dubi fuskarta, zaka
gane bata yarda bane kawai. Murya cunkushe
tace, ni babu abinda Al'ameen yayi min Umma,
kawai raina yafi kwanciya da Danliti kuma shi
nake so na aura. Haushi kamar ya kashe Umma
ta mike tsaye. Tace, to baki isa ba! Mu dan Liti
baiyi mana ba, idan kina da wasu iyayen da za
su dauta miki auran to bismillah! Ya ci gaba da
fadin, ai kuwa bata isa ba, ni zanje in dauko ta
kuma dole ta auri wannan yaron tunda itace tace
tana so tun farko! Yace, Yaya duk yadda kake
tunanin al'amarin nan ya wuce nan, amma ka
gwada ka gani, kilan kai tafi jin tsoronka, sai
dai kafin nan xance Al-ameen din ya kira ka,
kuyi magana, don ni gaskiyya ban san me xance
masa ba. Yace ba wani abu xan rarrasheshi, ya
kwantar da hankalinsa, kaima yaunxun nan ka
kama hanya kaje ka yiwa Hajiyansa bayani, kace
kar su damu ba wata matsala bace babba. Ya
numfasa ya amsa da to kawai. Lallai babban
yaya yana dau kara abin wasa ne. Suna aje waya
Aunty amina ta nufo shi, me ya faru ne wai? Nan
take ya labarta mata abinda ke faruwa. Tun
kafin ya kare idanunwanta ke waje, wai kana
nufin Mama ta fasa auran Dr? Yace gara da
kikace wai, don bata ida ba. Ni xan je na dauko
ta, cikin gidan nan zata zauna sai ya dawo. Ta
kada kai cikin damuwa, tace amma mama ta ban
mamaki, me Dr? Yayi mata? Babu abinda yayi
mata, wani ta hango saboda rashin hankali irin
naku na mata da butulci! Tace wlh na yadda sai
dai matsalar banyi zaton haka ba daga wajen
Mama ba ganin yadda take nunwa Dr. So mai
tsanani, duk yaudara ce, kai gani kuma a zahiri
ai ta nuna. Amma ai tayi kuskure ni zan gyara
mata zama, don bata isa ta zubda mana mutunci
ba! Tace gaskiyya ne. Allah yasa ta gane. Ya
wuce tebur don cin abinci. Shi kuwa
abdulkareem, bai sami zaman cin abincin ba
gidansu Al-ameen ya nufa ba tare daya san wane
irin bayani xai iya yi masu ba, don hankalinsu ya
kwanta. A haka ya isa gidan. Nan da nan aka
tarbe shi da girmamawa da abubuwan kusa da
baka, marafa baya gari, saboda haka mami ce ke
tare da shi, ina fatan dai kaci abinci? Yayi dan
yake yace, Alhmdlh Hajiya, nagode. Tace amma
dai ko Juice kasha ko? Haba, kamar wani bako?
Yanata murmushin rashin nayi, yana kallo ta
xuba masa ta mika masa, Ungo sha don Allah.
Kuma maimakon kazo min da surukartwa, yau in
riketa cikin gidan nan sai tayi min sati. Ya aje
kofin lemo ya kara gyara zama, Yace Hajiya, hkr
na zo in baki, domin ban sami dawowa da Mama
ba,... Saboda me? Kodai maganar Al-ameen
gaskiyya ce, sakeena na cikin wani hali? Bata da
lfya ko? Ya karkada kai.... Tace karka bote min
komai Baban ameer, duk tsananin da sakeena ke
ciki, nasan yadda xan rarrashi Al-ameen don
hankalinsa ya kwanta. Gaya min me ya faru da
ita? Jikinsa ya kara sanyi, cikin taushin murya,
yace Matsala ce babba Hajiya, wacce ni kaina
ban da ita ba, sai da naje daxun. Ashe tun
komawar ta gida, wani yaro ya hure mata kunne,
shi ya hana ta dawowa. Su abba na ta fama da
ita kuma suna kan kokarin su don ganin raba ta
da shi. Na yi nayi ta biyo ni, taki hajiya, shine
Abba yace in zo in baku hkr kafin yazo. Insha
Allahu za'ayi maganin abin. Gaba daya hankulan
mu atashe suke, al'amarin yana daure mana kai.
Idanuwanta xuru akansa, hannunta bisa kunci.
Tace, wyyo Allah! Wayyo Allah! Me xanji yau mai
kama da almara? Ta goce da sallalami, yanxun
baban ameera kana nufin sakeena tace amanar
Al-ameen kenan? Idanuwanta suka cika da
kwalla, yayi da yaya Abdul ya kara kasa da
kansa. Yace, kiyi hkr Hajiya, a gaskiyya ban san
yadda xan fassara wannan al'amarin ba, amma
abinda nake so ki gane Abba ba xao rungume
hannayensa ya sanya mata ido ba. Haka muma
'yan uwanta. Muddin kuwa tana son albarka dole
tabi umarnin mahaifinta. Shi yasa ya fara turo ni
kafin ya zo da kansa ya ga alhaji. Haka kuma ku
rarrashi Al-ameen ya kwnatar da hankalinsa
komai zai daidaita cikin hukuncin Allah da
yardarsa. Ta cire tagumi. Tace, a gaskiyya ba
zan iya fuskantar Al-ameen da wannan maganar
ba, in katsa masa karatu. Na san ya damu
kwarai ya san halin da sakeena ke ciki, amma
ba xan iya gaya masa wannan mummunan
labarin ba, kuma na rokr ku don Allah ku
kyaleshi kawai. Gara abar shi cikin duhun da
agaya masa sakeena ta sauke alkawarin da ta
daukara masa. Na tabbata komai nasa zai tsaya
jarabawar su gab take da xuwa. Ni da kaina xan
iya xuwa na roketa, ta tausaya wa Al-ameen
karta kashe masa zuciya. Kwalla masu zafi suka
xubo bisa kuncinta bata re da saninta ba.
Hankalin Abdul ya kara tashi, BAKIN CIKI ya
dada lulluba shi. Don girman Allah Hajia karki
xubda hawayenki akan maganar nan. Da yardar
Allah komai zai gyaru. Kamar yadda kika ce kar
agaya masa ba, ba za'a gaya masa ba. Gara ace
masa bata da lfiya ne, xuwa lokacin da xa'a
shawo kanta. Ta goge kwallah, tace ina ganin
hakan zai fi sauki iyaka dai yayi tunanin jikinta,
mu kuma nan mu rinka gaya masa tana samun
sauki. Yace, to shkienan, Allah yasa mudace.
Don girman Allah hajiya kuyi hkr, sakarci ne
kawai irin na yara. Tace, ya za muyi baban
ameer? Dole mu rungumi kaddara. Ya mike babu
isasshen laka a jikinsa, yayi mata sallama ya
fice, batare da hajiyar ta kara ko motsi ba.
Wucewar awa daya da rabi tana zaune xuciyarta
cike da sake-sake iri-iri. Ji take kamar a
mafarki abdul yaxo mata da wannan mummunan
labari, wanda take ganin zai iya salwantar fa
rayuwar dant tilon danta da takeji da shi. Duk
fadin duniyar nan bata hada shi da kowa. Yaya
marafa zaiji, idan wannan labari yake kunnen
sa? Tabbas xai fita shga damuwa, domin yafi ta
sanya Al-ameen ransa, ko alama baya son yaga
ya nemi abu. Waya ta dau ruri a falon, ita ta
katse tunaninta tare da haddasa mata faduwar
gaba mai tsanani. Ta mika hannu ta dauka ba
tare da tayi hasashen mai kiran ba. Tayi sallama
cikin raunin murya. A raunane taji muryar Al-
ameen ya amsa mata kafin yaci gaba da cewa,
mami na, ashe sakeen ba ta da lfiya shine aka
boye min? Ni ban ma yarda bata da lfiya bane
Mami, kawai ku gaya min idan mutuwa tayi, xan
hana Allah ikonsa ne? Ai nasan yafi ni sonta,
kuma ta shi ce ban isa in hana shi amsat
kayansa ba.... Tace saurareni Al-ameen, kar
hankalinka ya gushe.idan baka yarda ba da
maganar yayun sakeena ba, ai ni mahaifiyar
kace, ba xan rufe maka komai ba, ka yarda ko
baka yarda ba? Murya na rawa ya amsa, Na
yarda mami, tace to sakeena bata mutu ba,
rashin lfya ce ta sameta aka maida ta gida.
Bana so ka damu da yawa, domin sosai take
samun sauki, gobe ma xan sake xuwa in dubo ta,
kaji? Ya numfasa yace, amma Mami me yasa
za'a ajiyeta gida? Akaita asibiti mana, ko can
xariya xanyi magana da abokina, na tabbata xai
kula da ita tamkar ni. Pls mamy ki basu shawara
idan kinje goben. Tace ba ciwon asibiti bane,
shedanu ne suka tabata, kuma su iyayen nata
suna tsye neman magani. Kai ma kasan xa su
xauna ba. Ni dai rokona gareka shine ka nutsu
ka kwantar da hankalinka, ka fuskanci jarabawar
ki mai xuwa. Ka zama mai imani da Allah, shi
xai sa ya karbi addu'ar ka idan kayi mata. Ka
jini? Ya goge kwalla, yace naji mami don Allah
idan kinje ki dafa kanta ki karanta mata ayatul
kursiyu, falaki da nasi. Idan har gane ki ko da
baxa ta iya miki magana ba, ki gaya mata Al-
ameen dinta na gasheta, kuma xan ciga ba da yi
mata addu'a har xuwa lokacin da xanji muryar ta
a waya. Idanunwanta suka tara kwalla. Tace,
Insha Allahu xan gaya mata, tare da dukkan
abinda kace, muddin kayi min alkawarin zaka
kwantar da hankalinka. Da sauri ya amsa, Allah
nai miki alkawari mami, kinsan bani da wani
buri daya wuce in faranta maku rai. Tace, Allah
yasa dalilin alkawarin da kayi min Ubangiji ya
yayewa sakeena abinda ya sameta! Yace, ameen
Mami na! Dadina bai dawo ba ko? Bai dawo ba
sai zuwa jibi. Yace Allah ya dawo da shi lfya. Ta
amsa da ameen. Yace ki gayawa su iya su taya
mu da addu'a, Allah ya taimake mu. Tace, xan
gaya musu. Al-ameen, karka damu kaji? Murya
raunane ya amsa, to mami sai kinsake jina. Bata
iya kara komai ba ta aje wayar, domin muryarsa
kawai ta isa jefa mutun cikin damuwa. Taci gaba
da xama dauke da tagumi tunani na cin xuciyarta
fiye da tunanin mai kallonta. Haka al-amarin
yake wajen Al-ameen, domin dai rayuwa tayi
masa tsauri kuma hasashen rashin lfiyar Mam
yafi koma zama cikin ransa. Ba don yayi wa
mamy alkawari ba, da babu makwa zai iya baro
abinda yakeyi ya dawo ya ganewa idon sa
Mama, tana cikin mummunan hali. Kafin kace
kwabo, kowa ya fahimci samun sauyin sa, domin
ya yamutse ya wayi garim duk kuzarin da
nutsuwar sa basu jikinsa. Yana zaune

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login