Showing 78001 words to 81000 words out of 110841 words
banxar kuiyam shi ya sa yaki yarda Mama
ta daukeshi. Aunty Rabi ta tasa ta da nasihohi,
ayoyi, hadisan Manxo SAW akan ta dage ta yaki
xuciyarta ta dawo kan kanya, sannan ta nuna
mata wannan ba shine soyayya ba, duka
saurayin da ya nemi lalacewa da yarinyar da
yake so, a hakikanin gaskiyya ba son gaskiyya
yake mata ba. Sha'awar sassan jikinta kawai
yakeyi. Haka yayanta ta tsatsagge mata
gaskiyya, har yayi mata alkawarin idan ta nutsu
ta xauna gida kamar yadda aka umarceta, to
bayan ta haohu za'ayi bikinta, duk abinda take
so, shi xai sayo mata. Mama ta wani kuka tana
ba su ameera tausayi. Anann suka kwana,
washegari lhadi karfe 12noon suka juya. Su
ameera nata tambayar antyn su yaushe xata xo?
Tace kar su damu tana nan xuwa nan bada
dadewa ba, suna isa gida, yayan ya kira 'yan
uwansa, ya labarta musu abinda ya gani game
da Mama, idan har ya dore a hakan, alhmdlh!
Ana iya cewa an fara samun nasara. Kowa yayi
farin ciki jin wannan labarin da fatan Allah ya
shige mus gaba. Allah, da ikonsa a yammacin
yau din, tun bayan sallar la'asar mama ke cike
da kewar Danliti, kafin 5pm ra mance kaf! Da
alkawuran da dauka, babu abinda take so face
gain Danliti, kewarsa ta gigita kwakwalwarta, ta
birkita ta. Kamar an tsikare, kawai ta tashi ta
suri gyale da takalmi ta fito kanta tsaye ta fice
abinta. Dan gogan ta samun cikin dakin
barcinsu, tana shigowa yana xubawa wani
kaskon rushi ruwa, ya dago ido ya dubeta, yace
ba xan miki sannu da xuwa ba. Ta xaune gefensa
tana murmushi, saboda me? Ya xubo mata
harara, yace kwanaki nawa rabon ki da nan?
Sabo da nayi miki fada ko? Ta rungomoshi tana
dariya, ayya nawan ba haka bane, kowa yasa
min ido, sai surutai sukeyi kamar ni kadai na
fara soyayya agarin nan. Amma kana cikin raina,
kaima ka sani, bani da burin da wuce in kasanxe
tare da kai, ta bae baki yace tsarani, au baka
yarda ba? T yanxun ba ni na xo ba? Dana kiraki
ba? Ka kirani? Kamar ya? Ya ture kaskon ba
xaki gane. Sai dai na yarda kina sona, tunda
kika amsa kiran. Ta xura masa ido tace ngode,
tunda kasan hakan, me kake yi da kasko? Ke
duk xamanki a dakin nan baki taba ganinsa ba?
Da shi fah muke turaren daki. Kai amma wannan
bai hadu ba, kauri gare shi, kin kuwa san
tsadarsa? Ai ku maza ba gwabe bakin ku ake
wajen siyayya? Kabari xan kawo maka mai kyau,
idan ka sanya shi sai makwabta sun tambayeka
ina ka samo. Ko? To sai kin kawo din. Yanxun
mu ake maganar turare, ina kuka kwana da su
Abba? Ta tabe baki, me ma? Wai an bashi hkr
ya kyaleni, amma idan na sake xuwa nan, dole in
tafi. To kice kin karya doka, tunda gaki kin sake
xuwa, ni kuma da har nayi cinikin wani gida can
bayan tasha, ina fasa kenan? Bakinta har kunne,
tace ka fasa kuma? Ai xai mana anfani idan
munyi aure ko? Ya shafa kai, gaskiyya ne, xan
biya kudin in sa a gyara shi, ai sau muje ma ki
ganshi ko? Ya xama dole, yaushe xamu? Duk
tym din da kika shirya. Ko yanxumn a shirye
nake, mu tafi kenan? Bismillah. Ta sumbace ta
yace, amarya ta kenan, maman bebi! Ta rausaya
da kai tana dariya. Tare suka fito yana rike da
hannunta, har gaban motarsa. Ya bude mata ta
shige, ta dawo maxauninsa yaka suka tafi. Gidan
ginin kasa ne mai dauke da dakuna 2 kicin da
bayi, tsakar gidan turbayar kasa ce, haka ginin
babu digon siminti ko kadan, zallar kasar ce
kawai, illah iyaka cikin dakunan anyi masu dabe,
suna tsaye kafada da kafada, ya dubeta yace,
kinga gidan, ina fatan yayi miki? Ta yake baki
ta makalo wuyansa tace, ya fiye min kowannne
irin gida muddin da kai xan xauna cikinsa. Kar
wani abu ya dameka,a hankali na gyara shi,
kyau xaiyi fa, yayi dan murmushim ya falla ido
sannan yace, toh shikenan, tunda yayi maki, yau
din xan nemi dillalin in bashi kudin. Ta kara
kankame shi tace, ina tayaka murna. Ya xubo
mata ido yace ni xaki taya murna, ko ke xan
taya murna, gidan ki ne fa? Tayi dariya sosai. To
dukkan mu Congratulations! Ya sumbaci labbata,
tace thnk U! Sun jima cikin gidan suna
sharholiyar su, ana kiran magriba, suka fito, ya
kulle kwadaon gidan suka koma shago, maimako
ta koma gida sai ta rashe nan, tana nishadantar
da shi, kamar yadda ya bukata, ya siyo mata
abubuwan da take so, tace, tayi hani'an, kai
barci sace ta mana, ta yada kai bisa filo tai tayi
kuwa...... 11pm za su kulle hsago, ayuba yayi
juyin duniyan na Danliti ta tashe ta, ta tafi gida
amma yaki, ya kuma hana Ayuba ya tasheta. Da
ita suka kulle shago, ayuba ya kwana tsakar
shagon, shi kuwa dan gogan yana tare da
gimbiyar. Tsakar dare ta farka da ganta tare da
mutum. Ta tashi xaune ta bubbuga shi ya tashi,
menene? Tace dama ban tafi gida ba? Yace ga
shi nan kin gani, ai da ka sani ka tasheni
Danliti. Yace waya gaya miki ana tashin mai ciki
barci? Kiyi kwanciyarki kawai da safe kin koma,
Abba xai koro ni Danliti, yace akwai gida na biya
kudinsa, baki da haushin wannan. Idan kina
kwanciyarki, ki kwanta ida kuma yanxun xaki
fita 2am ga hanya nan babu ruwana. Bebi na
kawai nake ji. Ta watso masa harara ni banda ni
ko? To! Na ga kin wani hakikance ne, meye sabo
idan kin kwana anan? In banda gulma! Ta dare
ruwan cikinsa ta kai masa duka, ni ce
magulmaciya? Kai din fa? Todama mai neman
kuka ne aka jefa shi da kashi awaki, sai yaya?
Washegari, yadda bata sallaci magriba da isha
ba haka batayi asuba ba, karfe 7am ta dauko
hanya. Gata nan ga nan har gida, salalau-
salalau ta karaso ciki, ta iske duk sammakonta
Abba ya riga ta tara jama'am don haka tana
xuwa tsakar falo, tayi sanrada. Gwiuwa 2 ta xbe
ta fara kuka. Kowa ya saki baki yana kallonta,
M.kasin ya fara magana, yanxun saboda Allah
Mama duk maganganun da aka gaya miki ta
bayan kunnunwaki suka wuce? Ashe haka kike
da taurin kai? To mu babu ruwan mu, dama
rokonsa mukayi, ya ga girman mu ya hkr, tunda
ke baki gani ba. Shikenan ga hanya na, ki bi duk
wacce kika xaba. Abu yaya kamari har da
kwana? Ke Mama kiji tsoron Allah ki tausayawa
iyayenki. Ba xata suka ji tana magana, wlh Baba
bada niyyara kwana ba na fita, Danliti ne ya sayi
gida, yace muje na gani, mun dawo ina hutawa,
ban tym din da barci ya kwasheni ba, abba ya
xaburo yana fadin, kunaji Maganar Banxan da
take fadi ko? Kun tabbatar da cewa abinda nake
fadi gaskiyya ne? To ya isheni haka! Ya isheni
haka!! BAKIN CIKI ba xai akshe mu ba. Daga nan
ki juya ko koma, idan har ki na son kanki da
arxiki, wlh! Wlh!! Babu wanda ya ya sake roko
na in kyaleki cikin gidan nan! Duniya ce da fadi,
karki saurara wajen bin ta kwararo-kwararo har
ki gano iyakar ta! Tashi ki bace min da gani,
kafin in kusa kashe ki da duka. Gaba daya falon
yayi tsit, sai shasheshekar kukan Mama, jim
kadan muryar abba ta kara gauraye falon, kai
Jama'a! Ina xan kai takaici da BAKIN CIKI? Me
nxan yi wa yarinyar nan a dniya na huce, banda
in sallama ta, tamkar ban taba haihuwarta ba?
Ki tashi fice min nace, in daina ganinki a
gabana..... Ki ta... Kawai sai ya yanke jiki ya
fadi, gaba daya suka mike da sallalami sukayi
kansa...... Toh masu karatu, wannan fa shine
wasa farin girki. Nayi iya kar kokarina ace nayi
muku sallama anan. Amma ina abin ya faskara,
kuyi min hkr karshen badakalar wannan littafi
yana cikin 3, ku biyo ni, kada ku gajiya nayi
gaba....................THE END!!!
BAKIN CIKI 3***1 Ganin haka yasa Alh Adamu ya
figi wayar rediyo ya tsulawa mama "zaki kashe
mana shi ne? Ta mike a gigice ta yanka waje a
guje shima ya bita da gudun yana fadin fita!
Shegiya! Tsinanniya! Yar iska! Idan kin sake
dawowa gidan nan sai mun taru mun kasheki!
Har suka wuce kofar gida a guje sannan yaja ya
tsaya yana haki, yar banzar yarinya gantalalliya
maras mutunci! Ya dawo yana ta zage-zage yan
kallo suka fara kawo dauki ya fada cikin gidan
ya iske umma ma ta sume anata shafa musu
ruwa tare da firfita ya kutsa cikin yan
gudummawa. Abba kam ya farfado amma umma
abin yaci tura don haka gaba 1 aka debesu sai
minna inda zasu fi samun kulawa sosai sannan
yayansu susan halin da ake ciki. Al*amrin ya
daurewa Abdlkrm kai kwarai da gaske sanda ya
sami waya a office. Yaushe suka baro fandogarin
har wann abin ya faru? Dama mama bakan
kawai tayi tana jinsu tana kallonsu a dage?
Tirkashi! Ai dole su hakura da mama!
Hankulansu bai kama tashi ba saida suka zo
asibitin suka ga halin da umma ke ciki. Tun
isowarsu take sume Dr yace heart dinta ta riga ta
buga saidai suyita addua Allah yasa ta mike.
Kowa ka kalla dole ya baka tausayi musammn
Abba da yayi wata muguwar rama sbd zullumi. 3
days anata kai kawo akan umma abun yaki dadi
abdlkdr yace a basu ita su wuce Abj a daren aka
sallamesu suna jira gari ya waye su wuce. Karfe
3 na dare Abba na zaune a gaban gadon yaga
umma ta daina jan numfashi a zatonsa ta sami
sauki ne don hk yayiwa Allah godia ya leka ya
kira nurse yace tazo ta gani ko zasu cire mata
tukunyar gas din iska ta huta. Nos ta kalleta da
kyau tace tana zuwa cikin sassarfa ta fita ta kira
dr suka dawo tare ya gwada ta da kyau ya cire
duk injin dake jikinta ya rufeta da mayafi ruf!
Gaban Abba ya fadi ya tsurawa dr ido ya juyo ya
dubeshi... Alhaji..... Ya katseshi naga ka rufe
mata fuska me hakan yake nufi? Ya dafa
kafadarsa yace sai hakuri Alh kuyi imani da abnd
Allah yayi. Yasa kai ya fice. Abba yayi mutuwar
tsaye fadi yake Innalillahi.... .....!!! Nos dinnan
ce ta kamashi ta zaunar tana kwantar masa da
hnkli saidai zaiyi wuya idan yanajin ta ya dai
zauna ya zubawa gawa ido yana tasbihi. A haka
ya riki asubahi sannan ya tashi da kyar ya fito
masallaci yai salla. Yana fitowa su abdlkdr na
fakin har sun fito tafiya ya nufesu da sauri suka
yi saurin gaidashi ya jikin ummar? Yace jiki yayi
sauki ina fatar zakuyi hakuri ku dauki maraici.
Haka Allah yaso.... Ya wuce da sauri yana goge
kwalla ya barsu suna kallon juna kamar ba. Ya
jima yana kallon gawar umma tamkar a dream
sannan suka shigo yaya soja ke kan gaba ya
zauna ya bude fuskarta nan da nan abdlkrm ya
fice daga dakin yana kwalla da salatin Manzo
SAW. Shi kuwa soja zura mata ido yayi baya ko
kiftawa ganin haka yasa Abba yaja mayafin ya
rufeta sanna ya cira kai ya dubi Abba amma bai
iya firta komai ba idanuwansa kamar garwashi.
Abba ya dafashi yace ya kamata mu wuce gida
kuyi hakuri kaji?. Ya kada kai kwalla suka zuba
kuncinsa yasa hannu ya share nan da nan aka
fito musu da gawar aka sanya a mota suka tafi.
Anti rabi da inna saude suka gigice ta fasa kuka
ganin haka suma yaran suka hau kukan. Abba ya
rungumesu yana rarrashi yaya soja ya kira waya
abj ya shaidawa anti amina. Daga nan ya kira
abdrhmn yace su hadu a fandogari nan take suka
danko hanya shida ya saeed da matarsa suka
biya birnin gwari suka wuce da yaya Ali. Gida ya
barke da koke-koke kan kace kwabo rasuwar
tayi tambari a gari. Baraka da mahaifinta suka
garzayo gidan. Misalin 10am suka iso da gawar
kowa sai cewa yake mama ta kashe uwarta!
Hnklinta ya kwanta, babu bata lokaci aka
shiryata aka fito da ita jama'a kamar kasa suka
sallaceta suka kaita makabarta, uban dwk dai
karfin hali yake har suka sata a kabari shida
yayansa wanka zata fito lokcn danliti ya shigo
gidan a sukwane ina kike? ta karasa fitowa da
bocket a hannu gani nan wanka nayi. ya matso
ta yana fadin kina da lbr kuwa? tace name?kai
tsaye yace ummanki fa ta mutu yanzu aka wuce
da ita..... ta saki bokiti da kwandon soso ido
waje tace gane ba? yace ya hausar baki gane
ba? kije kisa riga kije gidan ki gani amma ni
tabbs haka naji ana fadin matar uban dawaki. ta
rasu ko yana da wata matar bayan ummanku? ta
fasa kuka ta ruga daki ta rarumi riga tasa ta fito
waje a guje ba takalmi ta kwasa da gudu. tana
salati hawaye na kwarara, danliti ya fito ya bita
da kallo cikin ransa yana fadin mahaukaciyar
banza ta wani kwasa da gudu kamar barinta
zasuyi zama a gidan. Shashahsa! yaja tsaki
yajawo kofar gidan yasa kwado. ita kuwa taci
gudu gidan ma nisa yayi mata tana isowa
motarsu Abba na tsayawa. Taja birki tana haki
kamar ranta zai fita ga hawaye na kwarara duk
suka fito suka zuba mata ido shi kuwa soja yana
fitowa ita ya dosa gadan-gadan idanuwansa
kawai ta hanga ta soma ja da baya kafin ya
karaso don kanta ta juya ta koma inda ta fito.
yace dakin tsaya mana in karaso! kiga yanda
zan kasheki da sauran kwananki! su M kassim
suka rikoshi suna bashi hakuri kwalla taf idonsa
yace in banda raini me zatazo nema bayan ta
kasheta? tunda wuri ku gaya mata idanta bari na
damketa saidai wata ba ita ba! akayi tabashi
haquri,yazauna cikin en uwansasunata karban
gaisuwa,inna saude da sauran matasun cika
falon umma.baraka kuwa hawayenta yaqi yatsaya
da zarar ta tuno mama sai taji kamar ta
sheqabarzamu da bakin ciki! Gidan dan liti
mama takomatana tafe tana kuka anata kallonta
tamkar mahaukaciya...tana isowa taga gidan a
rufe,tarasameke mata dadi....mutuwar umma ko
rashin makulli?tasake bin titi tadawo shago
tazauna akan benci kofarashagon dan liti na
kallonta bai tanka mata ba.ayubayace kace
tashigo ciki mana a ranafa take.......yacekasani
ko ranar tafiso?kyaleta tagama juyayin muma
haka mukayi muka bari.ayuba yace bakada
tausayidan liti,narasa inda imaninka yake,yace
to kaki filincigiya da sanarwa mana,sai su nemo
makashi.ayubayafita ya lallashi mama tadawo
shago tayi kukantaharta gaji,bacci ya
dauketa.danliti kuwa yaci gaba dacinikinsa
hankalinsa kwance..don yasan yasha gaban
kowa babu mai tinkararsa akan wani
magana.ammayamanta Allah nanan?kuma yana
kallonsa?baikulataba saida yagama cinikinsa,zai
kulle shagoyasameta zaune yace kitaso muje in
sauqeki indawoyau anan zan kwana,,,,,,tadubeshi
ido jazir tace anankuma?nikadai zan kwana
kenan?ya qara tsuke fuske yace ke!na aureki ne?
ina tambayarki...na aurekine?Daga taimako sai
ya zama tsiya?kuma shikenan saiin ringa kwana
dake,salon kisa mutane su zageni,acena ajiyeki
muna dadiro ko?......takada kai dasauri,tace a'a
wlh ba haka nake nufi ba,yi haquri,yacemeyasa
kikeson batamin rai?kinga nafasa kaiki tashi
mazaa ki kama kanki,ungo makulillin ki
wuce.tamarairaice tace kayi haquri katausayamin
dan litikaga dare yayi bayan tashan nan yan
shayeshayene.wulaqanci zasumin don Allah
kayihaquri.......ya zura mata ido fuska daure
yacemuminar qarya!da anyi magana ki
marairaice,ni tashi muje in ajiyeki indawo!iya
mike yayi wajeabinsa,canta sameshi cikin mota
ayuba dai bai iyakallontaba saboda tausayi
tunda tashiga baitankamataba duk lallashin
datake masa kuwa...hakata sauqa tana waigensa
yayi ribas ya figi mota yawuce tasa mukullai ta
bude kofan tashiga ta kulle da sakatagidan
bakikirin tayita laluba tashiga daki talalibo
ashana ta kyasta,,,ta hango inda fitilar kwaitake
tana kunnawa ko minti goma
baiyibayamuta,kalanzir din dake ciki ya
qare.........dole takwanta kusa da katifar da
danliti yasayo mata.takasabacci tarasa abunda
yake damunta...tsorone?fushin da danliti yakeyi
ne?ko rasuwar mahaifiyarta?saikusan asuba
tasamu bacci mai nauyi yadauketa. kwanaki uku
da rasuwar umma.a tsawonkwana ukun nan abba
baya barci,daka dubeshi zakagane yana wani
boyayyen ciwo dake
tsananindamunsa.idanuwansa sun
zurma,fuskarsa ta tsukekwarai da gaske,shisa
hankula yayansa yaketashe,abincin kirki babu
mai cinsa...sallar azahar aka kira kowa ya tashi
da nufin yin alwala,akaja sahu nanbisa tabarmi
malam qasim ke limanci tunda akafarazaman
makoki,,,,,,,,,,,,,,,a raka'an qarshe suka dagojiri
yadebi abba ya buga da qasa mutan biyu
dakegefen hagu da damansa su suka yanke
sallan,sukajanyeshi gefe suna masa firfita har
saura suka idar da sallah.yaransa suka rugo
gunsa tare da sauranmutane,,,,,masu shafasa
ruwa nayi masu firfita nayiharya farfado,sai dai
yanayin yanda yafarfado yafirgita kowa,gefen
damansa ya shanye,baki yakomagefe,gwanin ban
tausayi.labari yashiga cikin gidamata sukayi ta
fitowa suna koke koke ganin yanda akadauko
abban kaman gawa akasa a mota sukakaman
hanyan minna......har akayi bakwai abbanacikin
kaka nikayi.dole suka kasu,alh basiru da yaabdul
kareem suna tare da abba saura kuma sunawajen
karban gaisuwa..kai!sunga tashin
hankali,kukadai anyishi babu adadi,da yana
magani.daya magance matsalar data sauqa cikin
gidan uban dawaki.. Wasawasa abba ya kwashe
wata guda ana jelarasibitoci,daga minna aka
turasu k.d dagananzariya,akarshe ya abdulqadeer
ya daukeshi yadawodashi abuja,sukafara shirin
fita egypt cikin sati gudakomai ya
kammala,abdurah man da anty amina ne suka
tafi dashi saboda yanayin aikin sauran ammashi
yaya soja zai biyosu da zarar yasamu
umarnidaga ofis. andanga canji a cikin sati
biyun dayasamu yana ganin kwararren
likita,domin ansamu yanamagana kuma yana
amfani da hannunsa kadankadan,kafarce dai
bata aiki haryanxu.,...a sati nauku..akabasu
sallama tareda magunguna da zai ringaamfani
dasu.suna sauqa abuja.ya soja yawuce dashi
gida yace anan zai zauna yarinqa samun kulawan
dayadace..aka gyara masa daki,,,sannan yayi
masarijistan zuwa ganin likita lokaci lokaci,anty
aminatasha damarar kulawa dashi cikin hakuri
dagirmamawa Dan jikansa kuma malami yana
debemasa kewamusamman da yamma zaiturasa
akan kekensa sufito shan iska yana zagayawa
dashi cikingidan,wataranma harwaje dan yaga
gari,,,,kullam daresai sunyi tilawar alqur'ani mai
girma sannan sukebacc.haka kusan duk sati
yayansa ke zuwa dubashi danasu iyalan.har
safiya ta haifi ya mace,abdurahman yaso yasa
mata sunan umma,ammaabba yace tunda
akwaita yana roqon arziqin asamasasunan
mahaifiyarsa watoo sakeena tunda shi
yanxubaida mai sunan....abdurahman bai musa
masa badukda dai sunan bai kwanta masaba
yabi zabin abba,don ya faranta masa rai....komai
na abbayadawo qarqashin kulawan yaransa
hardagonakinsa,,,bayan wata biyu da haihuwar
sakeena. Bayan wata biyu da haihuwar sakeena
qarama yaaika da takardar murabus,,,aka nada
alh basiru amatsayin uban dawaki.zaman sa yayi
masa dadi agidan dansa hankalinsa kwance
dukda yana damuwada rashin umma...sai dai
imanin dayayi qokarintusawa kansa wajen maida
al'amuransa wajen ubangiji.illa iyaka yarakata
da addu'a tareda nemawamama shiriya. To
komai dai sai Allah yayi hattaasiririn dayayi
tasiri ajikin mama da izininsa ne,,,,donya jarabta
ta da iyayenta kuma yayi wa danliti
daurintalala.saboda fidda tsoron Allah a
zuciyarsa. Page 12:mama dai sharholiyanta
takeyi dukta mance abubuwan da suka
faru..domin ko alama bata ganinkowa a idonta
sai danliti.....shine mai sata shine maihanata
musamman yanxu data samu
lafiya,cikintayashiga wata 6 yana neman 7
batada watamatsala,batada abun dayake daga
mata hankali saifushin danliti.shikadai zata gani
yanxu tafita hayyacinta...tun mutan gari na
suru2 suna zaginta harabun yazama jiki bamai
kallonta......sau dayawa zakasameta cikin shago
ita ke siyar da kayan shagon saitazauna tun safe
har dare suna sakarci kalakala...gidan danliti
kuwa yanxu bata tsoronsa dukdare zatabi hanya
takoma takwanta,,,shiyasa ma inna saude
tadaina bin hanyar haka ma baraka ko saudaya
bata bari hanya ta hadasuba. A yan tsakanin ne
akasa ranar baraka da Muhd dinta 5mnths. Basu
baraka kadai ke gudun mama ba harda Ya Ali
shima idan yazo garin bai biyowa ta kofar
shagon ya gwammace yayi zagaye ta hanya mai
nisa, ya kanyi kuka shi kadai idan ya tuna halin
da mama take ciki baida abinyi face addua
kullum bata yankewa a bakinsa yakan jima bai
shigo garin badon kar ya shiga gida a rinka
bashi mummunan lbr masu jirkita masa tunani.
Kwanci tashi watan haihuwar Mama ya tsaya ta
kumbura dam! kamar ta fashe sbd hawan jini
bata sani ba, tunda ba awo take zuwa ba, amma
shegen dariya yake mata wai ta dawo alkubus.
Ita kadai a daki tsakar dare nakuda kamata ta
rasa inda zata tsoma ranta taji dadi tayi nan tayi
can tana ambaton Allah tare da tambayar kanta
wannan wane irin ciwone kuma? gab da asubah
jini ya goce mata idanuwanta suka raina fata
fadi take shikenan zan mutu! ta hau kuka tana
kiran zan mutu danliti ka taimakeni! garin Allah
ya waye 7am danliti baiga tazo shago ba alhalin
kullum 6am take zuwa wata zuciar tace yaje ya
ganota ya buga mota ya iso gidan ya iske a
kulle yayi ta bugu bata bude ba wasu samari
suka taimaka masa aka buge kofar ya shiga. a
zatonsa ma ta mutu ganin ta shame shame cikin
jini saida ya tabata ta motsa tace zan mutu ka
taimakeni. cak! ya daukota ya saka a mota sai
asibiti take sukace bazasu iya ba ya kaita
kagara, nan da nan ya buga mota