Showing 9001 words to 12000 words out of 110841 words

Chapter 4 - BAKIN CIKI BOOK COMPLETE BY ESHAT.txt

12 Sep 2025

56

gida ya rakata da kallo bakinsa kamar
gonar auduga kasala ta rufe ya kasa tada motar.
Ta sake lekowa tayi masa bye-bye shima ya
daga mata hannu sannan ya sami karfin tada
motar yayi ribas yai kwana ya fada hanya ya
kara dago mata hannu ya wuce cike da begenta
tamkar yadda takeji a ranta. Tana shiga cikin
gida muryar Ya Ali kawai ke tashi yana
bambamin fada "ai dama haka rayuwa take
kiri'kiri jininka saiya wulakantaka don baka da
kudi! Muma muna kan hanya indai arzikine
abuna Allah! (Kana da gsky Baffaba!) Mama tayi
tsaye jikin kofar sassansu tana saurare haj Hajjo
tace nace dai kayi shiru haka ko? To kaci gaba
idan hakan shi zai sa a baka ita. Mama dai ba
saurana mata tafi ba ga yanmata nan bila adadin
duk wacce ka zaba sonka zatayi idan ita ma ba
kwadayi tasa wa ranta ba. Sbd haka kar in sake
jin wata magana ta fito daga bakinka akan wata
Mama! BARKA DA SALLAH
HAUSA Novels BOOK
BAKIN CIKI 1****5 H. Gaje ta cafe, "ki kyale shi
ya amayar da bacin ransa, kar ya zame masa
ciwo! Da wanne zai ji?" yace, "ai inna ba zata
gane ba mama gaje, wannan rainin arziki ne a
ckn gida. Uwa daya uba daya? Haba! Ya kamata
a duba!". H. Hajo tace, "wa zai duba? Lallai
ranka zai fita idan har zaka kwallafa wa kanka
wannan maganar!" Tana sa aya daidai da
sallamar uban dawaki, yayi tsaye yana kalln
mama na zubda kwalla, yaynda yaji muryar h.
Gaje na fadin, "babu wnda zai duba wannan
al'amari, tnda dai shi da kansa alh. Babban ya
ya yamutsa al'amarin!". Kalaman da suka fada
kunnuwan uban dawaki tare da bugun zcy, ya
zurawa mama ido tamkar ynda take kallnsa, "me
ke faruwa?". Bai gama rufe baki ba yaga Ali ya
fito a fusace, idanuwnsa na tsatso kwalla. Shi
kansa gabnsa yayi mugun faduwa, kasala ta
kama shi, ya rage sauri, "kai ali lfy?". Ya gnge
fuska, ya dan rankwafa yace, "sannu abba!"
"nace me ya faru?" "babu komai" "ina wasa da
kai ne? Kake gaya min babu komai!". Mama
tace, "abba tun jiya gidan nan a yamutse yake,
ana ta habaici tare da yada magana akan zancen
al'ameen. Umma taki gaya maka ne sbd gudun
fitina. Amma kowa gani yake yi sbd kudi ne yasa
ka amince inyi aure, bayn ka hana kowa kace
karatu zanyi. Me yasa za'ayi mana mugun
zato?" Nan da nan ransa ya baci, yayi fushi
sosai, ya kwalawa umma kira. Ta fito ta samesu
ransa bace. Ckn fushi yace, "kira min matan
gidan nan!" "lfya alh?" yace, "ban son jin wata
magana". Tace, "alh ka kwntar da hnkalnka kayi
hakuri har zuwa lokcn da mazajnsu zasu dawo.
Zai fi kyau duk abnda zaka fadi ka fada a
gabnsu. Ina rokn wannan alfarmar don girmn
Allah!". Alh. yayi jim! Shiru yana kalln umma,
kafn ya dubi mama yace, "kin shirya kayanki?"
tace, "eh" "to kwaso ki zuba a mota maza mu
tafi". Ya wuce da sauri daknsa, kowa ya kama
gabnsa, har da ali ba tare da wani ya kara cewa
komai ba. Kayn jiknsa kawai uban dawaki ya
canza, yayi rawani kamar ynda ya saba, ya fito
lokacn mama na tsakar gida da jakar kaynta tare
da tsarabar da umma ta bayar a kaiwa yara.
"Baki kai kayan motar ba?" inji abba. Tace, "ai
basu da yawa, su kenan" "wuce muje". Umma
tace, "Allah ya tsare, a sauka lfya". Ya amsa da
amin, yayi waje. Mama ta biyo baynsa. Ali na
zaune bisa dakali tmkar yayi bindiga sbd tsabar
fushi da kishi, domin sosai yake son mama.
Kuma yayi wa ransa alkawari zai ci gaba da
farautarta, sai yaga abnda ya turewa buzu nad'i.
Shi yasa ya aje wa ransa zai iya jiran ta gama
karatnta. Shi kuma zai ci gaba da gina kansa da
duk wani tanadi wnda zaizo daidai da jin dadin
rayuwr aurnsu. Ina zai sa ransa yau yaji dadi?
Yana ganin mama ta shige mota idanuwnsa suka
yo tam! da hawaye. Musamman wannan zuwan
ita yazo gani, sanin cewa sunyi hutu. Kamar ya
kwarma ihu. Ya mike ya sake fadawa ckn gida.
Alh. Ya bude mota, kalla ya matso, "ranka ya
dade tfya za kuyi?" yace, "ai tare zamu tafi da
kai, taso ka shiga mota. Minna zan kai mama
na" yace, "to shi kenan". Ya mika masa makulli,
"ka tuka motar kalla, bana jin dadin jiki na". Ya
amsa yana fadin, "assha! Allah ya sauwake"
"amin". Ya bude gidan baya inda mama take,
shima ya shiga. Jikn mama ya kara sanyi, tasan
abbanta ya kanso suyi tfya su 2 kacal! Suna tafe
yana bata labarin duniya. Ta tabbata bacin rai ne
yasa ya gayyato kalla ya tuka su, gudun afkuwar
wani abu. Sun mika tfya shi babu mai magana,
shirun sam baya mata dadi, sbd haka tace,
"Abbana kayi hakuri don girman Allah, kar
hnkalnka ya tashi akan wannan maganar". Ya
dubeta sosai yace, "dole raina ya baci, sbd an
zarge ni akan abnda ba shine a ckn zcyata ba.
'Yan uwana basu yi min adalci ba, na tabbatar
da saninsu mataynsu ke yada habaici da
kananan maganganu. Amma zanyi wa tufkar
hanci. Tnda babu wnda ya haifa min ke". "kara
kayi fada dasu abba....." yace, "ya za'ayi in
tsaya ina fada da kannina? Umarni kawai zan
bayar, kuma dole kowa yabi idan ana son zaman
lfya. A iya sanina na basu hakknsu, na zauna da
su na gaya musu uzuri na. Amma duk da haka
basu gane cewar komai na Allah bane. Ke dai
abnda nake soki dashi, ki rike yarn nan amana,
sannan ki kara kula da kanki, don tsare
martabar gidan nan" tace, "Allah ya taimaki mai
martaba. Mamanka na tare da albarkar umma da
abbanta, da yardar Allah ba zata basu kunya ba".
Yayi dan murmushi yace, "Allah ya kara yi miki
albarka". Tare da kalla suka amsa, "Amin abba
Sun iso minna la'asar sakaliya, shi yasa ruwan
alwala kawai alh. Ya fara tambaya. Yayi sallah a
babban falon gidan, yaynda jerin kayan abincnsa
ke jiransa. 'yan jikoknsa kuwa sai safa da
marwa suke yi. Ya idar da sallar, suna jiran su
tumurmushe shi. Ilai kuwa yana idarwa suka
zube a jiknsa, yana drya ya soma tsokanarsu"
"ameera tsohuwa mai majina" tace, "Allah ameer
ne mai majina" ameer yace, "karya ne abba,
kullum wa ake ba tishu in zamu skul?". Abba
yace, "kyaleta Uwair, waye bai san halima
tsohuwa bace? Mai majina kawai". Ai nan da nan
tayi fushi ta tashi fuu.... Zata fice,suna mata
drya. Sai ga sallamar anti Rabi. "momy kin
gansu ko? Wai nice mai majina". Ita ma dryar
tayi ta wuce ta zube gabn abba ta kwashi
gaisuwa, sannan ta tambayi mutan gida. Yace,
"duk lfyrsu kalau" Kuka ameera ke yi, yaynda
mama ta shigo da ita falon, "ynzu don Allah wa
ya taba min umma na?" yace, "kyale ta mai
majina ce, ni bana auranta!". Ta kara kware
baki, mama ta rungume ta, "kiyi shiru ki kyale
shi, ke ma baki auran. Me zaki yi da shi tsoho?"
ameer sai drya yake mata. Da yaga kukan da
gaske take ynsa sai ya jawota jiknsa, "wanene
ya taba min madam dita? Manta da ameer, tsoho
ne shima. Ina dady bai dawo bane?" ta amsa da
kai tana murzar ido. Anti rabi tace, "bai shigo
gida ba tukuna, amma yana bisa hnya". Yace,
"To Allah ya dawo dashi lfya" suka ce amin..anti
rabi da mama suka bashi wuri yaci abinci tare da
jikoknsa. Yan minticoci bayan kammalawarsa
motar Ya Abdulkareem tayi fakin a harabar
gidan, ganin motar Abbansu yasa ya fito da
sauri kalla ya tarbe shi ya karbi jakarsa yayi
masa sannu da zuwa suka gaisa, tare suka shigo
falon ya zube gaban Alh yana fadin oyoyo
abbanmu! Yace Abdulkareem dan Abba sadauki!
Ya kara fadada dariyarsa domin yana jin dadin
kirarin da Abba yake masa tun yana yaro sbd
tsananin kokarinsa wajen neman duk abnd yake
so musamman ilimi. A yaran gidan kaf! Babu
wanda ya fara sauke Qur'ani da karancin
shekaru sai shi, yana 14yrs yayi sauka kuma
yasan littattafai dayawa. Daka dubeshi kaga
Mama illa dara daran idanuwanta ne kadai suka
banbantasu. Kazo lfy Abba? Yasu Umma? Yace
lfy lau Mamana na kawo maka hutu.....Mama?
Yanzu haka tana ciki? Sai gata ta shigo falon ta
karaso gunsa da gudu ta zube jikinsa Yayana!.
Ya kamo kunnenta ba wani yayankitashi zakiyi ki
koma inda kika fito! Tace Allah sarki yayana dan
Abba sadauki! Ya dada mata duka suna ta dariya
"maras kunya ba Abj kika fiso ba? Ai dama nace
duk randa kikazo yan kafafuwan zan karya..
Tace, "tuba nake yayana, daga yau duk hutu
anan zan yi shi" yace, "naji amma ban yarda ba,
ke da soja ai sai Allah, watakila kema sojan zaki
aura". Ta kada kai ckn shagwaba, "a'a!" Abba
yace, "ai baka ma sani ba? To karkade kunnenka
kasha labari". "ko abba? To bani insha". Abba na
bashi labari, ita kuma mama na boye a bayn
yayn nata. Tas! Ya zayyane masa abnda ke
faruwa. Abdul-kareem ya cika da mamaki, "to
menene abn tashn hnkali a nan?" yace, "nima shi
na gani, har ga Allah zcya ta bata da wani nufi
akan wannan al'amari, amma tnda haka suka
dauko zamu tafi a hakan, kuma mama zata auri
wnda take so". Ya dan kada kai yace, "kayi
hakuri abba, kasan shi mutm a kullm yakan fi
son kansa maimakn neman zabn Allah. Abu
kankani sai a ruruta shi yayi girman da zai
rarraba kan zumunci. Abba ka dauki girma
kamar ynda ka saba, ka dauke kai ga
tsegunguman mata". Ya zura masa ido yana
murmushi, "dan abba sadauki! Duk abnda ka fadi
gskiya ne, shi yasa ma bazan gaya wa yaynku
ba, don nasan halnsa, daga ali har mutn gidan
babu wnda zai kyale idan hauknsa ta tashi".
Yace, "haka ne, kuma nasan ali yana son mama,
dole yaji zafi a rnsa, amma su a matsaynsu na
manya ai bai kamata su rika tnzira shi ba.
Abnda ya dace shine su nuna masa komai na
Allah ne. Amma muna musu fatan Allah ya
ganas da su. Ke kuma mama ki rike amana,
domin duk garin nan babu wnda bai san familn
marafan lafai ba. Babban gida ne masu mutnci.
So u hv 2 b very carefl, ke ma ki nuna wa duniya
kin fito daga babban gida mai cike da tarbiyya,
OK?" Tace, "insha Allahu yaya zanyi iya kokari
na". Yace, "to da kyau likita matar likita. Abba
kasan wani abu? Ai mu juma munyi bye-bye da
rashn lfya". Suna ta drya, anti rabi ta shigo
itama. Sun jima suna hira, sannan uban dawaki
ya bar garin minna tare da yarnsa kalla.! Anyi
sallar magriba lokacn da suka shigo Fandogari,
don haka a guje uban dawaki ya nemi bada
farali. Bai wani ci abnci sosai ba, sbd abncn da
ya ci da yammacin dazu a minna. Umma ya aika
ta tattaro masa kaf kannensa da 'ya'yan gidan
tare da ali. Duk suka hallara a falnsa, ya dubesu
ya fara magana ckn rashn jin dadi, "abnda yasa
nace a kira min ku, a gskya abnda ya biyo baya
sakamakn maganar da muka yi da ku jiya, sam
banji dadnsa ba. Basiru da amamu kar ku manta
gaba daynmu ciki daya muka fito, babu bare.
Kar ku bari tsegunguman mata su raba kawunan
mu, domin da halima da hajo da gaje tare suka
same mu. Bai kamata in gaya muku uzuri na ba,
ku kuma ku koma kuna min yankn baya wajn
mataynku, har su sami damar yada maganganu
marasa dadi akai ba. Ko ban haifi daya daga
cknku ba, ina zatn ni uba ne a gareku, kuma
daidai gwargwado ban shiga hakkn kowa ba. Ali
da sa'eed a wancn lokaci sun yunkuro,
kowannensu yana son auren mama, a gabnku
yaran nan suka rika rigima a junansu, gaba ta
kullu, babu mai kalln dan uwnsa. Sbd Allah idan
ban ynke wancan hukunci ba me ya kamata inyi?
Shi za'a tsaga mama gida 2 ne, ali ya auri rabi
sa'eed ya auri rabi? A gani na idn aka hana
kowa zai fi mana alkhairi. Ko da bani da ra'ayn
mama tayi zurfn karatu, ballantana ina da shi.
Wlh bani da wani buri akan mama da ya wuce
tayi zurfn karatu ta zama likita gabana. Amma
da Allah ya sauya al'amarinsa, ba zan iya
jayayya ba. Sai dai a cknku laf din nan na bar
muku zabi, idn akwai mai iya yin wani abu bayn
wnda Allah ya zartar bismilla, ina saurarnsa. Ni
kam na yarda nayi gmanin al'ameen Allah ne ya
turo shi, ban isa in koreshi ba. Kuna iya kirana
kuda sbd kwadayi, ba zai sauya komai a jikina
ba, don nasan har ga Allah bana bukatar sisin
kwabo daga al'ameen ko mahaifnsa. Na kare
maganata, idan akwai mai abin cewa yana da
damar fadi". Gaba daya ka rasa mai yin koda
motsi, sbd dogn jawabn uban dawaki ya tattaro
musu kunya ckn idanuwnsu, musamman matan.
Jin sunyi shiru, uban dawaki ya kara da cewa,
"idan babu mai magana kuna iya tfya, shikenan
magana ta kare" Har matan sun mike, alh.
Basiru yace, "ku zauna. A gskya munyi kuskure,
amma ynzu mun gane bamu kyauta ba ko kadan.
Kayi hakuri alh. Da yardar Allah wata magana ba
zata sake bullowa akan mama ba. Ku kuma hajo
da gaje ku ba alh. hakuri, har ma da h. Halima"
Da ganin fuskoknsu kowacce ba akan son ranta
take magana ba. Sun dai bada hakurin, kuma
abba da umma sun yafe, sun maida komai ba
komai ba, a matsaynsu na manyan gida, sun
nada gammo sun dauki girman kamar ynda
hausawa ke fadin Babba juji ne. Aik. Adamu ma
yayi nasa dan guntun jawabin na neman afuwa.
Kowa ya tashi aka bar Ali a zaune, ba tare da
yace wani abu ba. Abba ya dube shi yace, "akwai
magana ne ali?" ya karkada kansa da ke
sunkuye, sai hawaye shar-shar! Suka hau zuba.
Uban dawaki ya sauke numfashi, gaba daya
jiknsa ya mutu. Harga Allah bai taba tunanin
soyayyar mama tayi zurfi ckn zcyar ali haka ba,
wa ke ganin hawayn ali? Da yarntarsa ma ba
karamar azaba ke sanyashi kuka ba, shi yasa
yaci sunansa Gadanga! Domin kaf tsaransa babu
mai nuna masa yatsa. "zo nan ali!" yayi kirnsa
yana nuna masa waje bisa kujera kusa da shi,
"zauna kaji". Ya zauna yana goge kwalla. "abnda
nake sonka dashi ali kayi wa girman Allah ka
dauki imani ckn ranka. Wlh a zatona tuni kun
share maganar mama a zuktnku, ganin na jima
da soke maganar. Amma kayi hakuri, ka dauki
dangana kasa wa ranka, duk abnda Allah ya
hukunta daidai ne" Ya dan gnge kwalla ya dube
shi, "abba sa'eed ne ya hakura, amma ni burina
inyi ta jiran mama har zuwa lokacn da zata
gama karatnta. Kullum addu'a nake yi Allah yasa
a tsayn shekarun nan zcyr mama ta aminta da
ni". Ya numfasa ya kada kai, sannan ya ci gaba,
"bansan yanda zanyi ba abba". Abba ya rungumo
kafadarsa, "hakuri magani ne ali, ban son ka
tashi hnkalnka. Mama 'yar uwarka ce, ka
taimaka ka bata goyn baya tare da addu'ar fatan
alkhairi, kaji? Ka kwntar da hnkalnka, nayi
rantsuwa da mama tana da kanwa da na baka
ita. Amma tnda babu, ina son kasa natsuwa ckn
ranka, ka ji ni?" Yace, "naji abba, kuma na
gode". Umma tace, "nima dai hakurn nan shi zan
baka ali, gaba daya hawaynka sun kashe min
jiki. Amma babu abnda zamu iya yi, sai dai ince
Allah ya musnya maka da alkhairi" yace, "amin
umma". Abba yace, "to tashi kaje ka kwnta, ka ci
gaba da addu'a, komai zai wuce". Ya mike babu
kuzari ya bar falon. Shiru su umma suka yi
tsawn lokaci, kafn abba yace, "Allah ya kyauta!".
Ta cire tagumi tace, "amin. Da gaske ali yake yi"
"mtsw!" yayi dan tsaki ya tashi ya shige daknsa
dauke da tausayn ali, ya bar umma zugum! Tana
tunanin iska. Gidan yayi tsit! Ko da tasa
damuwar. Washe gari da wuri ali ya koma birnin
gwari don kara samun natsuwa. Idan bakwa
comments sai inga kamar littafin ne baiyi muku
dadi ba, na kuma sai inji bana son turowa din.

BAKIN CIKI 1***6 Karfe bakwai da rabi na safiya
wayar tebur ke ta bugawa a babban faln.
Dawowar anti rabi kenan daga rakiyar mai gidan
da yara da zai aje makrnta, kfn ya wuce wajn
aiki. Can gefn wayar ta nufa ta dauka tare da
sallama. Bai mance muryar da ya fara ji jiya
tawaya ba, don haka ya zarce da fadn, "ina
kwana anti?" tace, "lfya kalau, wa ke magana?"
"al'ameen ne'. Take ta fara fara'a, "au Allah
sarki, ya aiki?" "Alhamdu lillahi" "madalla, bari
in kira ta" "to na gode". Ta aje kan wayar gefe ta
wuce da sauri tana kira, "mama! Mama ki aje
girkn nan kizo, mutumin naki ya bugo!". Ta fito
daga kicn da sauri, suka hade a kofa. "wannan
likita naki da naci yake" "kai anti!" ta fadi cike
da fara'a. "ke dai jeki da sauri". Ta wuce tana
drya, ta dauki wayar, daddadar muryarta a
sanyaye tace, "hello!". Ya runtse ido yace, "hello
'yan mata ya aka yi?" tace, "kalau, an kwana
lfya?" "sosai ma, har da miyan barci". Tayi 'yar
drya, "kaji dadnka" yace, "har na kai ki? Nasan
barci kike yi aka taso ki". "haba, kamar wata
raguwa?" "ita ce mana. Kowa ya ganki ai yaga
kalalatu" "kai kuma kalala ba" Yayi drya yace,
"tun asuba nake tsaye ina shirn ofis. Na rataya
neck tie, shine nace bari in kira madam ta daura
min" Ta dan rufe fuska da hannu daya tana
murmushi. Yace, "baki ce komai ba" tace, "to me
zance?" "au ba zaki daura min ba?" tace, "na
daura!" yace, "ga abu a wuyana yana lilo kice kin
daura, don Allah ki daura min" Ya fada a
shagwabe. Tace, "yau na bani! To rufe idnka". Ya
kuwa runtse yace "na rufe" "me ka gani?". Ya
danne kan wayar a gefn wuynsa ckn tunaninsa
yake magana ido ruee, hannaynsa na aikin daura
neck tie din. Yace, "ga ki nan kin fito daga dakn
barci, kin zuba kwalliya da wani farin less, kin yi
kyau bebyna. Sai murmushi kike min, kin kama
neck tie din kina daura min........ "Wash!" ya
bude ido firgigi, jin ya shake wuyansa.
"menene?" Ta tambaya ido waje, ji tayi ya
shagwabe, "Gaskiya ba haka ake yi ba, ba haka
ake yi ba sakeena. Ai dai ba'a shake wuya". Drya
sosai ta kubce mata, "ni na shake ka?". Yana
sassauta daurn wuyn yana fadin, "da kyar fa
nake numfashi, so kike in suma?" tace, "kaga
zaka makara wlh, idan suka ma bulala babu
ruwana". Yace, "ya zaki ce in tafi? Kin bani
brkfst ne? Ga kofn tea nan a gabana, yi sauri ki
ban insha in wuce". Tace, "oya, dauki kofi kayi
bismilla". Ya dauka ya rufe ido yana kurba, yana
ganinta ckn idanuwnsa, itace ke bashi. "ka
shnye?" "minti daya, na kusa saura kadan". Ya
kwalkwale ya aje kofn, "yauwa, na koshi". Tace,
"good boy. To sai ka dawo ko?" "to me zan cewa
zobenki?" "ina gaishe shi". Ya zura wa zoben
ido, sannan ya sumbace shi yace, "wai yana
amsawa". Tayi murmushi, "shikenan, tek care,
ok?". Murya sanyaye ya amsa, "i will......." yayi
dan jim, tace, "ina jinka!" ya rada mata, "I love
u!". Ta dan numfasa tace, "me too!". Tayi saurn
kife kan wayar. Da baya da baya ta tafi har ta
jingina da kujera, ta wuce a natse ta zauna
shiru, hannunta na gugar zoben yatsnta. A lokaci
guda shi kuma al'ameen ya rataye kot dinsa, ya
suri makullai da jaka ckn kuzari ya fito ya kulle
gida, ya fada motarsa. Mai gadin rukunin
gidajen ya bude masa get. Bayn sun gaisa ya
mika masa dubu daya ya wuce. Mai gadi na ta
murna tare da sa albarka. Shi kam kullm ckn
sawa Dr. Al'ameen albarka yake, domin shi kadai
yake masa alkhairi duk safiya, yace yaci abnci.
Da ka dubi fuskar al'ameen zaka tabbatar yana
tattare da farn ciki ba karami ba. Tamkar ynda
mama ta kasnce babu sukuni sbd tsabar kewar
al'ameen dnta. Bayn ta gama ayyuknta tayi
wnka ta kimtsa, sai ta kwnta bisa gado ita
kadai, bata aikn komai

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login