Showing 105001 words to 108000 words out of 110841 words

Chapter 36 - BAKIN CIKI BOOK COMPLETE BY ESHAT.txt

12 Sep 2025

77

no sir ai ba wani sai ogan mu
yana yar dariya yace kinyi gaskiya zainab kina
damaki ashirin tace"thank yau sir mama tasa
musu baki har wata godiya ki ke yi ki na kware
baki kar kiyi karatu yarinya ki jira bonus" ta
bude kofa suna dariya dr al-ameen ya ce ina
ruwanta zainab ta amsa nima shi na gani ke ko
tukuicin baki bani ba amma kina sawa oga ido
suna tsaye tsakar daki ya laluba aljihunsa ya
zaro dubu biyar ya mika mata karbi wannan ki
kyaleta kawai sai mun hadu gobe.............. -
Takarba mama na fadin ok mun gane dama da
mun ganki da manyan maki mun san na coge ne
yace eh ba komai zainab tayi dariya tace na gode
sir sai ka fito ta wuce tanayi wa mama dariya
yayi mika yana salati sannan ya zauna a kujera
ta ware ido tace zama naga kayi kar in zauna
tace gida ya kamata kaje yace korata ma kike yi
ta kada kai ba haka bane zai fi kyau kowanne
mu ya samu yay wanka ya huta kafin magariba
ta karasa ya munfasa yace haka ne yi hakuri don
Allah sai ina ganin kamar an daura ne unguwa
muka je muka dawo ta ware ido iye eh wallahi
kiris ya rage in fada katifar nan in kwanta fuska
yamutse tace wasa ka ke kin san Allah bada
wasa nakeyi ba a dai bar kaza cikin gashinta
miko min ruwa in sha in gudu,,Tace sai dai in
karbo maka wajen zainab ka sha na firij dina
babu sanyi yace to barshi kawai bari in tafi ya
zubo mata ido suka kalli juna yai dan murmushi
tace mene ne ya mike yana fadin nothing sai
munyi waya ko ta kada kai a ranta race dokta ke
nan ya wuce tanataka masa tana fadin ina
sauraronka tara kashi har mota suka y irin
sallamar sa suka saba yaja mota ya wuce ta
tako a hankali daki irin son da ala- ameen yake
mata shi yasa take jin kanta ita wata ce ta shige
wankanta ta fito ta sauya kaya ta kwaso
littatafanta ta baye a kasa ta fara karatu tana yi
tana zuba hamma barci ne sosai yake son
kamata gashi yamma tayi babu kyau yin barci a
wannan lokacin don haka ta aje littafinta
yunkura zata tashi da nufin fita wajen zainab
suyi hira ko barcin ya fita idonta, wani sauti mai
dadi ya fito wayarta alamun sakon ya shigo ta
dubi wayar kawai ranta ya kwao mata zakin
zuciyar tane tasa hannu ta dauko tana dan
murmushi ta bude sako amma sai taga sunan
yaya ali dake rubuce kamar haka, Assalamu
alaiki ya kanwata sai yau nayi saranda na sauke
hannayena daga rokon soyayyarki a yau na yarda
na amince kin sami gwarzo jarumin da nake da
yakinnin zai shaer miki hawaye tamkar yadda
nake zaton zan miki shine nake da tabbacin zai
rike ki babu gori balle mugun kallo ko zargin kin
taba yin wata mummunar rayuwa a. Baya amma
ina so ki aje a ranki wallahy wallahi!!! Wallahi!!!
Al-ameen bai fini sonkiba sai dai zanyi hakuri ne
saboda ke shi kika fi so a gunsa duk farin cikin
ki yake to nima ina son farin cikin ki mama shi
yasa na ke son abinda kike so ina muku fatan
alkari tare da tayaku murnar sake haduwa da
juna,,Yanyaki aliyu!! Hawaye kawai taji ya goce
mata saboda. Tausayin yaya ali to doka tagumi
tana kalubalantar kanta me yasa nake zama
butulu akan son da yaya ali ke nuna min laifi na
ne meyasa ban yarda. Na aure shi ba tun kafin
mu sake haduwa da dokta ta goge kwalla ta
kada kai abin ya dame ta kwari ta rasa inda
zata sa ranta taji sanyi sai kawai ta nemo
lambobin sa ta kira bugun farko taji muryarsa
yana mata sallama murya na rawa take fadin don
girman Allaj yaya ali kayi hakuri ka yafe min..
148-yace mama kuka ki keyi me yasa tace dole
inyi kuka yaya ali don ban taba sanin ni butulu
bace sai yau komai ya faru laifina ne kamar
yaya laifinki komai bana Allah bane tace laifina
ne me yasa ban aure ka ba tun kafin mu sake
haduwa da al-ameen kuma ni nasan kana sona
fiye da tuna ni na me yasa na zama butulu akan
soyayyar da kake nuna min ya numfasa ya dan
kada kai yace saura reni da kyau mama ai yanzu
mu ba yara bane dai dai gwargwado mun yi
hankali gane komai shirin Allah ne ni nayi imani
sabo dani ba mijin ki bane shi yasa aurenmu bai
yuwuba alkawari ne sai kin auri al-ameen shi
yasa Allah ya sake hada ku wallahi bana BAKIN
CIKIN auren ki da shi illa iyaka ina ciwon rasa
abinda ni nake so.. Abinda na rubuto miki a
sakona har cikin zuciyata haka yake Allah ne
shaida na saboda haka ki manta komai ke
yar'uwata ce ta jini abar alfaharina a ko'ina kar
ki sake zubda hawayenki idan har kin yarda kin
amince da abinda nake fadi kin yarda? Ta sauke
munfashi wasu kwallar suka sauko bisa kuncinta
tace na yarda da kai yaya ali ya ce to share
hawayenki tasa bayan hannu tana sharewa kafin
tace na share ya yi dan murmushi yace zamanin
kuka ya wuce har abada da yardar Allah farin
ciki muka fuskanta babu waiwaye yanzu gaya
min ranar da kuka fara ganin juna duk a sume
kuka fadi ko yasa dariya ta kubce mata ta cw
wane irin suma yaya ali ah ya baza ku suma ba
saboda murna ai so ba karya bane kanwata,,, ,
149-tace hakane amma ina mai tabbatar maka
shi din ma Allah ne yayi dole sai na aure shi
wallahi da da gaske nake bazanyi aure ba sati
uku muna dauki. Ba dadi har na bar makaranta
saboda shi daga baya muka sasanta saboda
abokinsa ya cika min ido yace baki kyauta ba
kuma da kin zalunci kanki akan aikin banza don
nayi rantsuwa kina son al-ameen to
alhamdulilahi tunda Allah ya gyara komai
sauranmu shan biki ko? Yayi dan murmushi ta
sunkuyar da kai kin yi shiru. Tace me kake so in
ce ki gaya min ranar shan shagali mu fara shirye
shirye tace kaji yaya ali baku. Ne masu sanyawa
ba yace eh gaskiya ne dama abba ya gayawa su
baba za'a zo asa rana da zarar sun turo ni zan
bada shawara kar asa da tsawo yaci gaba da
dariya yaya ali ke nan yace ba dai kunya ki ke ji
ba na sani to shi ke nan bari in kyaleki ki huta
sai mun hadu a gida ko to shi ke nan Allah ya
kai mu lafiya.. Yace amin suka danyi shiru jim
sannan tace yaya ali ya amsa ina jinki ta
sanyaya murya tace indan na gaya maka wata
magana zaka yarda yace me zai hana tace ina
sonka yaya ali ya yi jim shiru kana ya numfasa
yayi dan murmushi yace to na gode ki gaida min
angonki tace zai ji...bata karasa amsawa ba taji
ya kashe wayar ta runtse ido tana mai da
numfashi kwalla suka tsatso mata tayi sauri ta
goge su ta jawo filo ta jin gina shiru tsawon
lokaci sannan ta kada kai tace a fili Allah sarki
yaya ali Allah ya kara maka dan gana haka
zalika yaya alin jikinsa ya yi mugun mutuwa ya
dade yana sakar zuciya sai dai kalmar da mama
ta furta. Masa tayi masa dadi kuma ya tabbata
duk lokacin daya tuna zaiji sanyi a ransa, 150-
TABBATACCEN ALKAWARI duk inda ka duba
kofar gidan uban dawaki jama'a ne kwatsam
babu masa ka tsinke motoci kuwa sun tasar ma
bakin babban titi zan so mai karatu ya tsamo
mutum daya cikin wadannan daruruwan mutanen
ku kwatanta irin FARIN CIKIN da yake ciki a
halin yanzu kuma a wannan rana mai dimbin
tarihi cikin rayuwarsu sanye yake cikin wani
farin lallausan yadi yar ciki da wando hadi da
mulun malun hula fara da farin takalmi. Fari
hakan zai tabbatar da yanayin da yake ciki koba
ka kalli fuskarsa ba,idan ka kalleta kuwa kai
kace gonar auduga ne a haske da walwaki da
annuri wajen kwatance,Ayi kurum ke nan tabbas
shirun shine zaifi domin kwatancen bazai yuwu
ba tsaye yake jikin wata makekiyar jeep yayin da
wasu rukuni na manyan lokitici daga ko ina gida
da wajr suka zazzagaye shi domin dai akwai
wasu jajjayen kunnuwa su uku gab da za'a daura
auren dr lawal ya sake ketowa da wasu tawagar
bakin likitocin a matsayinsa na mai tarbar baki
al-ameen ya tarbesu kusan dama sune kawai dr
al-ameen yake zaton basu iso ba tawagar likitoci
ne da wasu ma'aikatan jinya daga sakkwato ana
ta musabaha baki yaki rufuwa kowa ka kalla ka
san yana cike da farin ciki daga ciki kuwa
waliyyai ne ke ta shirye shiryen gabatar da
daurin auran cikin dan kankanin lokaci alhaji
basiru ya mika amanar sakeena a hannun alhaji
nuhu waliyyin dr al-ameen akan sadaki dubu
hamsin... -nan da nan masu. Shela suka hau
aikin su wasu tsofafin mata suka fara rangada
guda makada da mabusan marafan lafai suka
dirfafi ango rerawa suke yi abin sai wanda ya
gani kwarai suka birge bakin turawan da ke tare
da ango shiyasa suka zaro wayoyinsu suka fara
dauka baya ga haka ga makadan nufawa nan
birjik kowa na gwada basirarsa da kwarewar sa
duk inda ango yake takawa kuwa kudi ne kawai
yake zubdawa marokan da mawakan na
kwashewa daga nan ma'aikatan hotel din da a
ka kwaso daga minna da kaduna suka fara raba
wasu manyan fararen ledoji guda biyu ake
mikawa kawanne mahaluki dake wajan koda
almajiri ne al-ameen ya bada umarnin a basji
kamar yadda akaba kowa leda daya kayan
kwalama ne dangin abubuwan da ake yi da
fulawa watau (snacks) nama kala kala akwai na
kaza rago da shanu jus iri iri da robar ruwa,
dayar ledar kuma abinda rabonka ya tsaga
domin dai babu abinda ba 'a raba ba,, Agogon
bango da na hannu da wayoyin hannu dardumar
sallah kai harda takalma da huluna turare masu
zafi banda kana nan abubuwa irin su tawul
hankici birorin rubutu da littafan addini da
sauran abubuwa zaiyi wuya ka bude jakar ka ka
sami kyauta kasa da iri bakwai can kuma sai ga
wasu kananan yara suna raba wata yar karamar
jaka mai ban sha'awa bakin jakar a tsuke take
in ka bude ka sha dariya domin babu komai
cikinta face SACET SACET NA PARACETAMOL
nan. da nan abokai suka kaiwa ango don ya
ganewa idanuwansa lallai yau shagalin na
likitoci ne yana karba ya kwashe da dariya
turawan wajrn na taya shi su kansu. Abin ya
basu al'ajabi har daya daga cikinsu yace lallai
wanda yayi kyautar nan yana da basira hakan
yasa al-ameen ya duba sunan take nan yaga
(CUT CEE BARAKA) ya kada kai yana yar dariya
yace best friend din ta ce aka ci gaba da dariya
tare da annashuwa mai yawa...... .idan muka
shiga daga cikin gida kuwa ita uwar gayyar
kusan can ake kankat.wajen ado tayi canji sama
da talatin tun kwanaki uku dafara shagalin
bikin.dole tasa domin angonta yasa mata kaya
akwati goma sha biyu.ita kanta dataga kayan
ciki saida suka girgizata.musamman kit din na
kayan karas.mai karatu nabarka da tunanin ya
suke?kusan yanxu abubuwa sun kawo
karshe.tunda anfara neman amarya ana zagawa
da ita gun manya dan su samata albarka.inna
saude ke riqe da mayafinta.sasan gidan aka
zaga da ita.iyaye suka tofa albarkacin
bakinsu.daga qarshe akajata falon abbanta.inda
gabadaya yayunta suke zaune shi.suna shigowa
ta wuce jikinsa,yawan shekarunta bai hanata
gaucewa da kukaba.shikuwa abban farin ciki!
yasanya shi zubda hawaye.yau autarsa zata tafi
gidan mijinta hartakai ga bai iya cewa
komaiba.sai yayunta ke mata fada tareda sawa
auren albarka.kamar wasa sai yazama dakyar
aka banbareta daga jikin abba.takoma dakin
ummanta takifa kai ciki.kukan rashin ummanta
takeyi.jitayi anzauna kusa da ita muryar yaya ali
taji yana fadin kiyi haquri kitaso mama!kowa
yashiga mota ke kadai angonki ke jira!nanda nan
tadago ta dubeshi duk idanuwa sun kode jajir!sun
qara fitowa waje. 153.yasake fadin pls.ki kwantar
da hankalinki ki taso a fita dake,,kin san hanya
ba kyau ko?batace komaiba.ta tashi zaune ya
miqa mata hankici yace share hawayenki!ta
karba ta share ya gyara zaman mayafinta ya rufe
mata fuska.sannan yakamo bakin mayafin
yajawo ta falo.inda su anty amina ke tsaye cirko
cirko.yace gatanan na fiddo da ita.ku muje nizan
sata a mota.ya wuce anata musu dariya.wasu na
guda.makekiyar jeep din sabuwa fil!itace angon
ya tanada don amaryarsa.yaya ali yasanya ta
aciki.inna saude da baraka tare da zainab da
anty amina suka take mata baya cikin
motar.gabadaya motoci suka tashi aka jera
kamar an rako shugaban qasa.sun iso minna
karfe biyar da rabi na yamma.akwai wasu
kosassun dawakai guda goma dake jiran
isowarsu.akan mahadar dazata shiga dasu
anguwarsu..amarya da zainab suka hau
biyu.sauran takwas din kuwa ango da abokansa
cikinsu harda turawan da sukazo daga
rasha.gaba daya sun daura alkyabba da rawani
na alfarma.musamman alkyabbar amarya tafi
kowacce ado.sai wanda ya gani suka tankaya
makada da mabusan sarakunan lafai na gaba da
bayansu suna qayata sha'anin.motoci na biye
dasu ga jama'a suna tafiyar qasaita anata dauka
da kamarori kala kala.tafiyar minti talatin
takaisu get din gidansu.mami ta fito ta tarbi
amarya da turarenta mai shegen qamshi.tana
fesa mata anata rangada guda.sannan takamo
hannunta suka wuce gida sauran ayari suka take
musu baya.sashi na musamman aka warewa
amarya da yan uwanta.babu abinda babu na
nau'in abinci dasu kala kalar kayan sha.sun cika
wani dan matsakai cin sito.sai abinda kake
sha'awa zaka debo kaci.
BAKIN CIKI 3***12 bayan anci abinci sallar
la'asar aka gabatar data riskesu a hanya.bayan
magrib da isha'i motoci suka sake kwashesu sai
gidan amarya.wanda layi biyu kacal ne a
tsakaninsu.dukiya taji jiki.irin dukiyar da aka
zubawa mama agidan sai ka rantse da Allah
baza a kwanta a kabariba.shikansa tsarin gidan
abin kallo ne.bayan yan rakiya sungama bawa
idonsu abinci.motoci suka sake dibansu suka
maida wajen mami.amarya kawai aka bari dan
bawa ango damar hutawa da amaryarsa.ganin
basuda isashen lokaci suma gobe lahadi zasu
koma zariya.karfe tara ya raka bakinsa hotel
dindaya kama musu.shikuma yadawo gida cike
da zumudi maras misaltawa..ita kuwa amarya
tuni tayi wanka saboda zafin datakeji.tasake
caba ado ta qame tana ta zuba qamshi.kawai
sallamarsa taji cikin dakin gabanta yayi mugun
faduwa.ta amsa masa tanajan mayafi.yatako a
hankali yazo gaban gadon ya zuba mata
ido.tsawon lokaci sannan ya sauqe
numfashi..yazauna gefenta ya duqa sosai.yaleqo
fuskarta suka hada ido.tayi murmushi tasadda
kanta qasa yayi dariya yace amarya
kenan.yadauke mayafin ya zura mata ido.yayin
da yake juyo fuskarta gareshi.ta dubeshi tana
murmushi kafin tace sannu da zuwa!yace
kezanyiwa sannu kin iso lafiya?tadan murmusa
lafiya lau.yace to alhamdulillahi.dukkan godiya
ta tabbata ga Allah.daya nuna mana wannan
rana dabamu taba mafarkin zatazoba.155.ya
lalubo yatsanta ya runtse cikin nasa ya nisa
sannan yaci gaba abinda nakeso dake shine ki
kwantar da hankalinki muyi zama na amana
wannan zama dazamuyi bana soyayya bane zalla
a'a harda ibada.mudauka hanyar aljanna muke
nema.ina fatan zaki zama mai bani hadin kai
har qarshen rayuwarmu.ta dubeshi ido taf
kwalla.tace insha Allahu zaka sameni mai
sadauqar da rayuwata a gareka.tareda bin
umarninka muddin bai sabawa shari'ah ba.kwalla
suka sauqa bisa kuncinta ya zura mata ido
sosai.yadan kada kai.meya kawo hawayen? yayi
sauri yajawota jikinsa.no pls bansan dalilin
wannan kukanba.murya shaqe tace farin ciki
dokta! bantaba tsammanin zansamu nutsuwa
kamar daba.azatona rayuwata tagama
rushewa.amma sai gashi kanata hidima dani
tamkar zaka auri.......yayi wuf ya rufe
bakinta.bana sonji.kawai kiyi shiru idan bazaki
fadi alheri ba.ta zuba mishi ido shima nasa sun
fara kadawa.ya share mata hawaye.kinga tashi
muje muyi alwala muyi sallah shine zaifi mana
kyau.yaja hannunta yakai bayi fara yi ki fito.tayi
ta fito.shida ya shiga sanda ya watsa ruwa tukun
yayi alwar ya fito.ya jagoranci sallar raka'a biyu
tareda miqa godiya ga Allah........ya juyo gareta
tana miqe kafafunta saboda gajiya.yace in
kwanta? tace kwanta mana waya hanaka?nazaci
za a min irin na rannan ne a koreni inaji ina
ganin abinda nakeso.tayi yar dariya.mesa baka
mantuwa?yayi lum da ido!yace sharp brain.!ya
qara bata dariya tace ai yanxu ban isaba,,,kayi
kwanciyarka mai gida... .kawai taga ya yada kai
bisa cinyoyinta kunya ta kamaata.ta kauda kai
daga kallonsa.yasa yatsansa yamaida
fuskarta.yace kalleni mana.mekike nufi da kauda
kai?ta yamutsa fuska tace ina na kai shi? yayi
dariya.wai naga har paracetamol kuka raba wai
ku doctors ko?tace babu ruwana aikin baraka
ne.tace alqawari ta dauka sama da shekaru biyar
dole ta cika.gashi nima tasaka min ajaka dazu
dazasu koma.yace kuma wlh ta birge har dr
begas yasarawa basirarta.sai dai kun mance
baku rubuta dose ba yakamata agayamana nawa
nawa zamu sha?tayi dariya ai yawuce
dokta.in,miqo maka kasha?.kawo min.tace to
dagani.ya manne ido daya yace nanfa daya.ta
watso masa harara.yayi murmushi.yace kinajin
yunwa ko?takada kai.yace aikuwa ko bakiji
yunwa dole kici tsarabata..tace dole?yace
yazama wajibi ne yau inshayar dake madara inji
manzon Allah.kinga kuwa dolene tayi shiru tana
kallonsa kamar yadda ya zubamata ido.karfe
biyar na asuba da kwata taji ana bubbugata a
hankali tabude ido taga fuskarsa dafda tata.yasa
mata ido za a iya tashi koda sauran gajiya?taja
mayafi ta rufe fuskarta yayi dariya.yasa hannu
ya yaye rufuwar.ta mulmula ta dirqa tadayan
side din tafada bayi.yanata dariya sannan yanufi
sallaya yatada kabbarar sallah.157.yayi nafila
kana yakawo farali.kafin ya kammala tafito ta
kintsa ta daura hijab.ta fara sallah.sai da ta
kammala tsaf harda azkar din safe.sannan ta
juyo ta dubi inda yake.yana kwance bisa
shimfida.yasa hannu yayi kiranta.ta miqe ta nufi
gunsa ta zauna gefe sannan tace ina kwana?
yatashi zaune yabita da kallo yace qalau na
kauna kefa?tace nima yace da kyau!kinsan wani
abu?ta girgiza kai.to rufe idonki.tayi murmushi
ta rufe.cike da annuri.ya tura hannu qasan filo
ya zaro dan mukulli.yakamo hannun damarta ya
damqa mata.bude ki gani.ta bude ta bishi da
kallo dan mukulli nagani.yace hausawa sunce
yaba kyauta tukuici.wannan shine tukwaicin
kyautar kanki daki ban jiya.wata yar mota ce
kiyi maneji.kanta yayi gingiri gin dokta
shine......ya nuna mata alamun tayi shiru banson
ji ok?ta wuce jikinsa ta qnqame.ban cancanci
wannan ba dokta!don Allah kadaina wahalar da
kanka akan......ya daka mata tsawa akanme?
nace akanme? ta gigice cikin kuka ta kasa
magana yace wallahi! wallahi!!wallahi!!!idan
kikasake aibanta kanki ayau zan barmiki
qasarnan.sai ranar da kikayi hankali
zandawo.kina jina?haba!jiya jiya fa kika min
alqawari? kina nufin abaki ne kawai?to wlh
bazan dauka ba.bazan jure jin lBAKIN CIKIN
Lafazinki susa min hawan jini ba.kin gane?
tafada jikinsa ta qanqamesa sautin kukanta na
ratsa kunnuwansa.shiyasa zuciyarsa taci gaba da
tafarfasa..don baison jin kukanta sam.haka
kuma bayaso taci gaba da aibata kanta.abinda
yafii tsana da kyama kenan.dan haka ya kyaleta
taci gaba da zubda hawayen.amma yadda ta qara
qanqamesa kamar zata shige jikinsa.shiya
tabbatar masa da lalle haquri take bashi dukda
bata furta da bakintaba. hakan yasa fushinsa
yadinga sauqa harya rabu da zuciyarsa.yabar
masa tausayin amaryarsa kawai..ya tallafo kanta
yasauqe numfashi ya sassauta murya.tun ranan
da Allah ya hada ni dake ya manna min
matsanancin sonki a zuciyata har rana mai
kamar yau. Banji sassauci ba.duk wani abu
dakikaga nayi a halin yanxu dama shiryayye
ne.tunda mafarki nane kawai yazama
gaskia.karkiyi mamakin irin tarairayar da
zanmiki cikin zaman da zamuyi.kiga kamar
shekaruna sun wuce hakan.ni a wajena dole
inyiKARA'IN Soyayyarki.duk abinda na shirya
mana a farko sai na nuna miki.tunda ubangiji ya
nufeni da mallakarki.idan kuwa shekaru basu
hanani dawowa yaroba.banga dalilin dazai
hanani aiwatar da abunda nayi niyyaba.don
faranta ran wacce ta faranta mini,,,,,ya dago
fuskarta idanuwa sunyo jajuz.yaci gaba pls
kidena kona zuciyata da zafin hawayenki.ta zura
masa ido na tuba dokta!yayo dan murmushi
amarya bata lefi. Kota kashe dan masu gida.tace
gara da kace wai.ya goge hawayenta baki yarda
ba? yanxu ki kamo waleed ki yanka ai babu
abinda zanyi.illa in miqo miki waleeda itama ki
yanka duk cikin nishadin amarci ne.159.tace
Allah ya tsareni nazaama mahaukaciya kenan!ba
amaryaba.karka sake min irin wannan misalin ya
lakucr hancinta nima karki sake min asaran
hawayenki.tace idan bakason hawayena kadaina
min hidima..ya dubeta yace uhmm....to shikenan
nadena.tamiqa masa yatsanta promise? yace
bawani promise.karkiyi mini wayau maman
waleen.ta watso masa harara.yafara dariya ai
gaskia kisan nanda watanni tara zuwa goma zaki
haifi ameer ko ameera.kinga kuwa hidima
takama babab waleed da waleeda uba awajen
ameer da ameera.ta shagwabe fuska takai masa
duka a kirji.ya kece da dariya yakwanta a filo
yana kallon shagwabar datake masa.zaka dace
da roqo tace masa wannan irin kirari?yace eh
bandeji haushiba..tayi dariya ta lallabo jikinsa
nagode dokta Allah qara budi na halas!ya
tallafota ameen bebina.abinda kawai nakeso ki
rinqa fadi kenan kinji?tayi far da ido insha
Allahu.good sai gari yawaye muje kiganta tana
motor park.ta dada shigewa jikinsa double thank
sir!sir sis!?babu sir a wannan gidan daga darling
sai cweethrt sai honey. Sai sugar da
mazarkwaila.ta fashe

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login