Showing 60001 words to 63000 words out of 110841 words

Chapter 21 - BAKIN CIKI BOOK COMPLETE BY ESHAT.txt

12 Sep 2025

88

ya sha ba wanda xai sa
ya mance da sakeena bane. Da wannan xulumin
ya tafi yin sallah la'asar hankalinsa bai kwanta
ba, sai da ya tura yatsansa ya arce
makogwaronsa ya kirkiro wa kansa aman dole.
Bayan sallar magriba dady ya shigo ya tsare shi
yaci abinci. Sannan mami ta debo ruwan
addu'arta ta mika masa, ya shanye. Allah Allah
yake yi tashi ya koma dakinsa ya jawo aman,
amma kmar dady ya sano ya ki barinsa tashi.
Yayi ta jansa da hirarrakin duniya, wai don ya
rage tunanu. Kafin ya bar wajen ya kwashe awoyi
sama da 2 takaice ya ishe shi, don ya tabbata
ruwn nan ya gama bin jininsa. Wannan karon bai
nemi yin aman ba, gado ya fada ya fara tunanin
iska, har bacci ya samuyi, da alama an fara
samun nasara. Shi kansa yayi mamakin irin
barcin da yayi bugu da kari ya rage jin xugin
xuciyarsa ke y, hankali kwance suka yi karin
safe. Mami ta kara bulbuo ruwan addu'ar ta a
gora, ta mika masa. Ya kwankwada duk ba a son
ransa yake sha ba, a yau takardun komawarsa
Rasha xasu kammalu, haka dady ya gaya masa.
Saboda haka ya umarce shi daya kasance cikin
shiri koda yaushe xa'a iya basu tym din tashi.
Jikinsa babu kasala ya koma bangarensa ya jwo
jakar kayansa yayi ta lda kaya har da wadanda
ya dade bai anfani da su ba. Ya wuce dirowar
madubinsa ya jawo ya kashe takardun cikin kaf,
dinsu ya dauko xai xuba jaka, wata ambula ta
fado duk hotuna ciki suka watse bisa kafet
daidadi shigowar mami dakin. Ya aje takardun
gefen gadon yana amsa sallamarta, sannan ya
tsugunna ya kwashe hotunan, akasarinsa duk na
mama ne, sai kalilan wanda suke tare. Tayi tsye
tana kallon katuwar jakar da yake lodawa kaya,
ya akayi mami na? Tace kamar bada jakar nan
ka xo ba? Ya mike dauke da hotunan a hannunsa
yana amsawa, xan kara wasu kayan ne, shi yasa
na sauya jaka. Ya matsya xai cusa hotunan, tayi
wuf ta karbe ina xaka da dasu? Ai wadannan
hotunan wuta ya kamata ka cinna musu. Wuta
mami? Me ya san xan sa wa sakeena wuta?
Saboda nan gaba xata xama matar wani, ka ga
haramun ne gareka kallon hotonta. Ina fatan ka
gamsu? Yayi shiru na 'yan dakikai kafin ya
numfsa, ya dubeta idanuwan har sun kada, yace
kin fadi gaskiyya mami, amma baxan iya cinna
wa jikin sakeena wuta ba, sai dai ina rokonki
dan girman Allah ki adana min su har xuwa tym
din da xata halasta gareni. Tayi masa xuru tana
shakku cikin ranta, addu'ar Baba liman batayi
tasiri bane ko kuwa bata fara aiki bane tkunna?
Ta kada kai ta dubi hotunan ta sake dubansa,
amma shi ya riga ta magana. Mami pls ki ajeye
min su inda ba xa su salwanta ba. Ta sauke
numfashi, xan boye maka sun tunda kafi son
hakan, gwaggo ce ta xo tana daki na. Ya ware
ido sosai. Gwaggo? Da sasssafen nan? Dole tayo
sammako, hankalinta a tashe yake, ka fito tana
daki.Tayi waje da ambulan din a hannunta,
shima ya biyo bayanta. Tana xaune a shimfida
bisa kafet ya xube gabannta dauke da murmushi,
uwargida ran fida, kuma sai ki bugo min
sammako kamar ban aika da cefane ba? Duban
tausayi take masa, ta dafa kafadarsa tace dole
nai sammako, in xo in ga halin da kake ciki. Ina
fatan xaka sanya dangana cikin ranka. Ka mance
da yarinyar nan, domin dai.... Ya katse ta, ya
kamata mu gaisa gwaggo kinxo lfya? Ya tsufa?
Tace tsufa na nan kuma lfya lau na xo. Amma
me yasa ka katse min magana? Babu komai gani
nayi bamu ko gaisa ba, alhalin ya dace na fara
gaisheki. Haka ne to ina fatan duk shawarwarin
da kowa ke ba, kana ji ka kuma dauka? Ka
manta sakeena... Da sauri ya katse gwaggo tuni
na hkr da ita, hasalima yau ko geb xan koma
sch. Ban xan dalilin katseni ba Al- ameen akwai
abinda baka so na fadi. Mami ta amshe, sosai
kuwa kina so ya mance da sakeena,
kunnunwansa ba sa son ji, shi yasa yake
katseki. Tace oho, to wahalar banxa kakeyi,
domin dai labari ya tabbata tare da shashashan
saurayinta suka tafi, kaga kuwa sai abinda Allah
yayi. Gara ka kama kanka ka san inda ke maka
ciwo. 'yan mata dai ga su nan birjik duk wacce
kace kule xata ce cas. Rayuwa kawai sakeena ta
xaba, don na tabbata yaron nan baxai aureta ba,
nawa ya lalata, ya watsar tana gani kuma ta
bishi, inm banda ita ma, rayuwarka ta sha
banban da wacce sakeena ta dauka, kaga kuwa
tafiyarka ba xata xama daidai da tata ba. Ka
fahimce ni? Wasu kwalla masu xafi suka sauka
bisa kuncinsa, hakan ya jawo mamaki ga
gwaggo da Mami suka xuba masa ido baki sake.
Xugum sukayi, daga bisani mami ta numfasa
tace ikon Allah! Gwaggo ta xare tagumi tace,
akwai sauran aiki, kuma ina mai tabbatar maka
, bata tym dinka kakeyi. Ya jawo hankaci ya
share fuska, yace, ko kadan gwaggo, labarin ki
tsananin tausayin sakeena ya cusa min, sakeena
ba haka take ba, nayi rayuwa da ita sosai na
fahimci halayenta, xan iya cewa nafi kowa
saninta, na fahimci halinta. ,Zan iya cewa nafi
kowa sanin ta hakika ya zalunce ta tunda ya
sauyamata rayuwa ya bata tarbiyarta ya gurbata
mu'amalarta da iyayenta da yan uwanta ya datse
tasananin soyayyar dake tsakaninmu ka ALLAH
bazai kyale shi ba ta ko wace hanya ya bi yayi
nasa a kanta sai ya ga sakayya,"ya mike da
sauri zai bar dakin gwaggo ta kwala masa kira
ya tsaya bakin kofa yana goge kwalla tace dawo
ka zauna ai ban gama magana da kai ba yana
daga tsaye gaskiya gwaggo kunnuwa na ba za Su
iya sauraron irin wadannan labarurrukan akan
sakeena ba,tausayin ta bazai barni sukuni ba
gara a bar ni cikin bakin duhu ina laluben inda
ALLAH zai sake hada fuskokin mu har ta zama
mata a gare ni," jikin gwaggo yayi mugun sanyi
tace dawo zauna nan ya dawo ya zauna gefenta
ya hade kai da guiwa ta dafa kansa tace idan
nayi kuskure kayi min afuwa amma ba laifi na
bane ka sani ko wace uwa tana kishin danta
kuma abinda ya faru da kai dole mai kaunarka
yayi bakin ciki balle mu da muka fi kowa kusa
da kai, na san kana son sakeena sai dai ba na
son idon ka ya rufe ka kasa ganin aika aikar da
ta aikata a garemu, ya cire kai ya dube ta ni
kuwa hakan na fi so gwaggo domin na yi imanin
ba yin kanta bane sace min ita akayi hure mata
kunne akayi da kalmomin shaidan addu'a zatayi
maganin abin, da zaki taimake ni da ita ma zan
fi farin ciki akan wadannan labaran da ki ke son
bani," gwaggo " mami ta karbe za a yi maka in
dai addu'a ce ka samu tashi kaje kaci gaba da
shirinka bai tofa komai ba ya yunkura ya bar
dakin,kamar daman can ya kosa ya
barshi,"gwaggo ta dubi mami hankali tashe tace
bai kamata ku kyale yaron nan ya koma haka
kawai ba tare da wani taimako ba tace tun jiya
na je lafai na samo masa wajan baba liman wai
nan yama sha ruwan addu'ar ke nan tafdijan ki
na kallo fa ko laifinta baya son a fadi wannan so
yayi yawa gara ma da auran bai yuwu ba da
muna kallo zai zama mijin ta ce,abin haushi
nama na jan kare, mami tace me ki ka gani
gwaggo?ALLAH dai ya zaba alkairi abin cewa ke
nan anan gwaggo ta wuni, Shi kuwa Alameen a
dakinsa ya wuni don baya son ana daga masa
hankali da labaran sakkena kazantar da baka
gani ba tsafta ce,kai a yadda yake jin mama
cikin ransa koda ya ga kazantar da idanuwansa
zuciyarsa ba za ta amince masa ba bai fito ba
sai da gwaggo zata koma suka yi sallama daga
nan dakin iya ya shige ya kudundune kamar
maraya sama da awa guda tana tausar zuciyar
sa da kalamai masu dadi,ya kuwa ji dadin cikin
ransa saboda kalaman iya sunfi rinjaye ga. Bashi
tabbacin idan sakeena matarsa ce duk rintsi duk
wuya sai ya aure ta karfe shidda dai dai dady ya
dawo masa da takardun tafiyarsa sun kammalu
kuma gobe da yardar ALLAH sha biyu ranan zasu
tashi don haka yana gama cin abincin dare mami
ta ba shi ruwan addu'a ya kwankwada kai tsaye
asibiti ya wuce don yin sallama dasu abba,kowa
yayi masa nasiha kuma sun jaddada masa ya
maida hankalinsa akan anibda ya kaishi kar ya
tsaya bata lokacinsa. Akan tunanin iska wanda
ba zai fisheshi ba,sai dai abin yana basu
mamaki yadda lafuzzan alameen ke nuni da
tsantsan son mama a zuciyarsa. Wanda ko alama
na bayyana har yanzu bai yarda sakeena. Taci
amanarsa ba, akwai mishkila wani wuri shiyasa
yake ta rokansu dasu taya shi addu'a ALLAH
yasa wata rana sakeena ra zama mata a gare
shi,gaba daya ya kwabe masu guiwa har suka yi
masa alkawarin yin yafiya a gareta idan har ta
dawo ta nemi gafara,kowa ya dubi alameen sai
ya ji tarin kwalla cikin iadanuwansa lokacin da
yake barin asibitin yana gugar fuska shi kansa
yaya soja a yau zuciyarsa ta karaya,tausayi ya
kwarara cikin jikinsa ya nemi haddasa masa
abin mamaki domin kwalla ya ji tam da
idanuwansa suna zubowa da saurinsa ya bar
wajan bai gama ganin wucewar alameen ba
AKIN CIKI 2*** 11 Karfe 8am suka dauki hanyar
abj tare da mami. Hankalinsu bai gama tashi ba,
sai da tym ya cika aka kira passengers. Al-
ameen ya rungume su, idanuwan sa cike da
hawaye, bakinsa na son yin magana amma kasa,
haka su ma Allah ya doro masu nauyin baki,
kallon juna sukeyi. Da sauri ya juya ya wuce,
yana goge fuska da hankici. Shi yasa suke tafe
cikin mota kowa shiru. Mami dauke da
taguminta. Tunaninta yay rayuwar dan nata xata
kasance a kasar da babu wanda ya damu da
wani balle ya sami wata kulawa ta musamman.
Dadi yayi tana share hawaye ya dan dube ta,
kada kai. Amma bai iya cewa komai ba don ya
san mami tana mukatar zubda hawaye ko ta ji
dadi cikin ranta, amma da ya ga abin yaki
karewa, dole ya tanka, ina ganin bai dace ki ci
gaba da bata ranki ba, wanda kika yi ai ya isa,
ko sai ya jefa ki wani hali ni in rasa da wanda
xanji? Ta goge kwalla, tace Alh. Ba haka bane
ganin Al-ameen na da abin fadi, amma yakasa
ya wuce da damuwar cikin ransa? Wa zai gaya
mawa a can? Kai tsaye ya bata amsa, Allah zai
gaya mawa, kin kuwa san ya fini, ya fiki, yafi
duk wanda kike tunani zai ba Al-ameen wanni
taimako, saboda haka ki bar shi da buwayin
sarki, shine xai masa dukkan gudunmawa. Ta
zare tagumi ta numfasa, haka ne, Allah ya
taimake shi, to amin kuma na tabbatar zai
taimakeni shin, tunda kika furta, addu'ar uwar
yankan wuka ne, don haka ki kwantar da
hankalinki. Ina fatan kin ji ni. Tace, naji alh.
Allah ya shige mana gaba, yace amin. Daga nan
Mami ta saki jikinta suka ci gaba da hira. Suna
shigowa gari, asibiti suka wuce gano jikin
Umma. Alhmdlh, Umma na samun sauki,
watakila ma xuwa gobe a sallameta. Ba su iske
yaya abdulkadeer da Abdul- rahman ba, duk sun
koma a wannan yammacin. Sun dan jima
asibitin, sannan suka dawo gida. Mami ta dukufa
rokon Allah cikin sallolinta, Allah ya sanyaya wa
Al-ameen xuciyarsa, ya cire masa wannan
makahon so sa ya ke wa Mama. Haka ta kwana
tunaninsa har barci tayi mafarkinsa xaune yana
wasa da xobunan guda 2. Shiyasa da ta fara tayi
ta da na sanin da ta raba shi da zobunan kafin
ya tafi. Suna karin safe karfe 8:30, waya ta
dauki kuka, mami ta baro tebur ta zo duka tayi
sallama. Muryar dan lelenta taji ya amsa. Farin
ciki ya lallube ta tace, Allah sarki Dr. An sauka
lfya? Yace lfya lau Mami, ina dadina? Ga shi
nan, ya taso ya ji kaini, ina fatan ba matsala?
Babu mami, na ma iske time table din jarabawar
mu ya fito, karatu kawai xa mu fuskanta, ni da
abokan karatuna. Dadi ya tsaya wajen tana
fadin, kai naji dadi sosai, to Allah ya baku sa'a
baki daya. Ga dadinka. Ya ce, to nagode Mami.
Dadi ya amsa suka gaisa. Dady time table ya
fito a taya mu addu'a. Yace kullum a cikinta
muke, amma xa mu kara kaimi. Ubangiji Allah
ya taimako. Yace amin. To xan wuce cikin sch,
sai kun sake jina. Yace, yayi kyau, all d bst!
Cike da fara'a ya amsa. Nagode Dadina. Ya aje
waya ya dubi mami yace hankalinki ya kwanta?
Bakinta har kunne ta amsa. Kai bari Allah ya
kara masa hkr. Yace amin, muje muci abinci ko?
Suka koma tebur. Mami tace abinci hankalinta
kwance. Ba Haka al'amarin yake wajensu Umma
ba, domin yau sun koma Fandagori sun iske da
kuara da suka bari baya. Hankulansu su kara
tashi yadda xance ke ta yamadidi a agari. Zagi
iri-iri babi irn wanda ba'ayi ba wasu suna ba
iyayen Mama laifi, amma da dama sunfi zargin
mama akan rashin hankali da ta aikata. Wani
abinda yafi daga wa Ubandawaki hankali shine,
wai gaba daya gundarin labarin daga bakin 'yan
uwansa da matayensu ya fara fitowa. Bayan
gaskiyya ga tarin karya da karairayin da suka
yiwa labarin kawanya, don haka ya tara su falon
sa bayan sallar isha'i. Wannan shine karo na 2
da na tara ku akan wasu maganganu na batanci
da suke fitowa daga gareku. A zatona ku masu
rufa min asiri ne ko bayan raina a matsayin ku
na 'yan uwana da muka fito ciki daya. Amma
bansan abinda nayi muku ba kuke min bita da
kulli, ko kuma ince kuke farinciki don wannan
abin ya sameni. To abinda nake so ku gane
shine, da frko dai bamu mukayi kanmu ba. Allah
ne yayi mu, mu kuma shi ya rubuta duk abinda
zai faru da mu. Babu wanda yasan kaddarar
mu2m bnalle ya share masa mummuna kafin
tazo. Da anayi da na gogewa Mama, don na duk
fadin duniyar babu wanda zai kaini BAKIN CIKI,
sai kuwa mahaifyar ta. Idan kuwa hakane, bai
kamata ace ku da matayenku, ku dauki wannan
al'amarin ya zamar maku abin hira a gari ba.
Kaddara na kowa, idan baku duba kusancin mu
ba, ya kamata ku duba wannan. Allah yai sani
ban zalunci kowa ba cikin ku ba, haka ban
xalunci mama ba, kamar yadda kuke yadawa
cewar mu ne muka dage sai mai kudi xata aura,
alhalin kun san komai a game da alkawarin
auran ta da Al-ameen. Kun fi kowa sanin
gaskiyya, amma kuka boye ta, saboda son rai to
na bar kowa da Allah, yayi min sakayya, Da
yardar Allah BAKIN CIKIN Mama bazai kashe mu
ba, haka zalika ina mata fatana shiriyar koda
yaushe. Mai surutu da dariya kuma Allah ya
bashi sa'ar yi. Amma kar ya mance kaddara bata
fatan shiryar kowa! Yana sa aya, ya mike ya bar
falon ba tare da wani yayi magana ba, ita ma
umma tashi tayi ta bi bayansa, yayi sauran ke
mazuran rashin gaskiya. Haj. Gaje ta buga tsaki,
ta bar falon. Daga bisani Haj. Hajjo ta lallaba ta
sulale, Alh. Basiru ya dubi Alh. Adamu. Yace
mutane munafukai ne, wai daga dawowarsa, an
sami wani kusugurmin ya feshe shi, don neman
fada. Alh. Adam yace, wai me akace? Au ya faru
ba za'a maida yadda akayi ba? Me za'a baoye
bayan ta gudun kowa kuma ya sani tare da
shegen yaron nan suka tafi! Ai ko ba 'a fada ba,
amsar a bayyane take. Tace, bata so, ba sai a
kyale ta ba, ta auri dan iskan da ake ganin ba
shi da asali ba, ba ita zata zauna da shi ba?
Wahalar tace tunda tasan halinsa. Tace sai shi.
Wai kuma mu ake ganin laifin mu, don fin karfi!
Mts.... Ya ja tsaki yayi waje abin sa. Alh. Basiru
ya mike yana kada kai, shi ma ya fice. Zaman
doya da maja yaci gaba da yaduwa cikin gidan,
duk da ba gaba daya sukeyi ba, amma babu wata
kyakkaywar fahimta atsakninsu. Shi uban dawaki
yana ganin ya kamata su ba shi hkr a
matsayinsa na babban su, sannan yana gani sun
yi masa laifi, don sun bada labarin yadda akayi
mama ta gudu, tunda ba su suka xuga ta ba,
komai ya kwana gidan sauki saboda haka basu
ga dalilin da xai sa Uban dawaki Ya dauki dalan
laifi ya dora masu ba har ya rinka jiran kalaman
tubansu. Su ma fah yanxun ba yara bane, girman
'ya'yan su ya kai, ya gane shekarun su sun cika
daidai matsayin masu 'yanci. Zuwan Ali da Ya
saed don duba jikin Umma da kuma jin labarin
Mama ko ta bayyana, Al-amarin bai yi musu
dadi ba, ganin Yadda iyayen su suka ware
ubandawaki suna masa yankar baya. Musamman
Ya ali, hankalinsa yayi mummunan tashi, babu
bata tym ya gurfana gaban abba yana bashi hkr.
Daga bisani Ya saeed ya shigo falon. Ya ali Yayi
rantsuwa da ace mama zata dawo ta amince da
auransa, maimakon Danliti, a shirye yake a
daura masu aure. Ko a gaban iyayen sa haka ya
maida zancansa. Haj. Hajjo ta rufe shi da bala'i
Allah wadarn wannan so kuwa, tunda yake hana
ka kishin kanka. To idan ma mafarki kake yi, ka
wanke idon ka, ka saurareni, idan har ni na
haifeka, ba xaka auri ragowar Danliti ba. Wannan
kalma tayi masa ciwo, bai san tym daya tasshi
ya tabbatar wa su Haj. Hajo cewa kashe miciji
sukeyi basa sare kansa. Domin ko banza sun
kwana da mamakin Ya ali da yayi tafiyarsa,
daga magana, shima ya gudun kenan? Ko mene
nufinsa? Muna iya cewa matsalarsu ce, ko dama
abba ya fadi kaddara na kan kowa....... Inna
saude ke xaune gefen gadon tana mata fifita.
Kallo daya zakayi mata, ka gane cewa ta jima
tana fama da ciwon tsananin damuwa, domin dai
ta fyade ta fita kamanninta. Amma hakan bai
hana ragargazar shagalin bikin da akeyi cikin
gidan ba. Nasan xakuyi mamaki, idan na gaya
musu cewar bikin yaya Ali da Ya Sa'ed akeyi.
Iyayeyn sun hur masu wuta, tun tym din da suka
lura da take taken shi Ya alin, sam hankalinsa
ba shi akan abinda zai fishshe shi. Shi yasa
suka matsa kwarai da gaske akn ya fiddo matar
aure ko su su fidda masa, ya kuwa tabbatar da
mahaifiya sa xata ita. Gudun kar ta manna masa
alakakai ya sa ya fito da yarinyar da ta dade
tana sonsa a birnin gwari. Amina sunanta, kuma
makwabtansa ne a gidan daya ke xaune. Sa'ed
tuni yake tare da Hassana a kd. A yau ne maza
suka daura auran 11am. Daga can suka wuce kd,
inda xa'a daura na sa'ed bayan azahar. 8pm
wannan rana motocin amare ke shigowa layin
gidan angwayensu, haka daidai wannan tym
motar Danliti parkn a kofar shagon sa dauke da
tasa amaryar. Cike da mamki ayuba ya taso, ya
bude kofar yana fadin, wa nake gani kamar
amafarki? Wai dama kuna tunanin gida? Dan liti
ya fito yayi doguwar miki, yana dariya, yace ah
gamu kuma mun dawo, ya juya cikin mota ya
cigaba da fadin, ya Gimbiya anan zaki sauko ko
na karasa dae gida? Ta kada kai, tace, naji tsoro
ya kamani Danliti, bansan yadda xanyi ba? Yayi
'yar dariya. Yace tsoro kuma? To me xa suyi
miki? Ta kada kai bari dai na sauka nan, canm
ajima na karasa gidan. Ya kace da dariya. Amma
ke shirmen ki yayi yawa, to fito ki shiga ciki. Ta
ballo murfin ta fito, kai! Anya kuwa Mama ce?
Tayi wata shegiyar kiba ta kara ja, ina ganin shi
yasa Ayuba ya xura mata ido, tym din da take
mika masa gaisuwa. Danliti ya bude but suka
ciro manyan jakunkuna guda 2 da kit, sai manya
ledoji guda 3. Ayuba ya taimaka suke shige da
su cikin shago. Kai tsaye dakinta shige ta xube a
katifa. Duk suka biyo bayanta. Danliti ya xauna
kusa da ita. Yace kin gaji ko? Tace kai dai

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login