Showing 66001 words to 69000 words out of 110841 words
muka so ba. Sai dai hkr kwai. Haj. Gaje ta
tabe baki tace, ya xama dole, amma a hakikanin
gaskiyya mama ta bamu kunya. Ajin ai ba daya
bane in banda batan basira. Koda yake ance so
mako ne. Allah ya sanya alkhairi. Sukayi dan
shiru, kafin suka nufi dakin Mama, ina kike?
Kina jin mu amma ba xaki fito ki gaishemu ba?
Tana xaune gefen gado, ta fesa ado kyanta ya
kara bayanna, banda haka da ibar da ta kara
suka kalli juna sabe da haba, kafin Haj. Gaje ta
soma xuba, lallai Mama, watau hankalinki a
kwnace kika je, ki ka dawo! Wannan kiba haka?
To Allah yasa ki sami irin wannan a gidansa.
Haj. Hajjo ta amshe amin dai, kin dai riga
kinsan halinsa, komai yayi miki sai ki hadiyewa
cikinki, kar ki doshi kowa, tunda kin nace shi
kike so! Ko kuwa gaje? Tace haka yake yaya, ai
kowa ya sayi rariya yasan zata xubda ruwa.
Mayafinta dake bisa filo ta figo ta mike tsaye ta
xura takalmanta tayo waje tana yafa gyelenta, ta
barsu anan sake da baki, suna kallon juna. Ko
kinga dibar albarka? Inji Haj. Hajjo, Haj. Gaje
tace, mamaki kikeyi Yaya? Karfa ki manta
watanni 3 ta shafe a bariki, an kuwa ce xama da
madaukin kanwa, shike kawo farin kai. Mu meye
namu? Ta malam ai bata wuce amin. Can suka
sameta dakin Umma tana neman izinin zuwa
wajen Danliti, don ta shaida masa sakon abba,
suna isowa, umm ana fadin bance kije ki xauna
ba, mutunciki shine ya biyo ki nan kofar
gidanku. Saboda haka daga yau kar na sake jin
kin koma shagonsa. Tace, to Umma, insha Allah
yanxun xan dawo. Ta sa kai ta fice, ba tare da
Umma ta kara wani abu ba. Nan su Haj. Hajjo
suka xauna suka cigaba da kwasar tsegumi, ita
kuwa tana fitowa xauran farko, angwaye ta ci
karo dasu, saeed Ya maka mata harara, ya wuce
abinsa cikin gida. Ta dubi ya Ali, tace me nayi
masa? Yace kin fi kowa sani. Taja dogon tsaki,
aikin banxa, to shinme me? Don ya ki min
magana? Yace, kin baci da Rashin K mama, me
yasa? Da ba haka kike ba. Ta dan tabne baki
tace, ni ina da wurin xauwa, ba na fito magana
da Ya Saeed bane. Yace amma ba kije kinga
amare ba. Xanje ai, so nake in sauke wannan
nauyin ko ni,a na kama dahir. Yayi dan
murmushi yana kllonta, mama kenan, to a dawo
lfya, nasan sakon bai wuce na Danliti ba. Tayi
'yar dariya. Shi ysa nake sonka Yayana, bari dai
in dawo amaryarka ka xan fara xuwa na in gani.
Ta wuce tana cigaba da dariya, ganin yadda yayi
tsaye duk jikinsa ya mutu. Ya bita da kallo,
sannan ya kada kai, yace, ni ma ina mutuwar
sonki Mama. Ina ma ace hankalinki xai dawo
gareni? Ya sauke numfashi ya shige wajen
amaryarsa. Bakinta har kunne take sallama kofar
shagon, ayuba ta gani xaune ckin shagon ya
amsa mata cike da fara'a amaryarmu kenan, ya
gajiyar tfya? Tace tabi lfya, ina mutumin? Ya
amsa yana ciki tun azahar yake barci saboda
ragwanci. Ta fara dariya, lallai kuwa ragwanci,
barin inshiga dole ya tashi ya bani goron
albshiri. Ta wuce ciki, ayuba na fadin, ya dai
kamata ya tashi ko salla ya samuyi. Kan tsaye
bisa katifar ta fada, ta dada masa duka cinya,
don Allah tashi rago! Ka wani baje kana gugar
barci, ni ina can ina tunaninka. Ya bude ido
firgigi yana kallon ta jim, sannan yayi dan
gajeran tsaki. Yace kash! Wlh ba don ke bace,
marin Mutum zanyi. Kin ji dadin barcin kuwa?
Tayi far da ido, tace ko? To ka tashi, na tabbata
dadin barcin bai kai albishir din baki na ba. Ya
xuba mata ido yace fadi ina jinki. Idan kuma bai
fi ba, kinsan Allah sai na sanya ki kuka, ai kin
san gamuwar mu babu tausayi. Tayi 'yar dariya,
tace, haba duk wannan kukan wasa nakeyi,
kama daina hura hanci. Yayi murmushi, haka
kikace? To shiknen, fadi ina jinki. Ta gyara xama
albishirnka? Yamasa goro. Xaka bani Ah! Me xai
hana? Ke dai gaya min inji. Abba yace in fada
maka ka turo, ranar auren mu za a sanya. Ya
xuba mata ido, ya kasa ko motsi, kayi shiru? Ya
sa hannu 2 ya mutsutsuke idanuwansa yace, dan
Allah karki xalayeni! Ta ware ido, kana nufin
baka yarda ba? Gaskiyya ban yarda ba, yaushe
Abba xai yarda ya bani ke, bayan ya san bani da
kowa a garin nan? Sannan suna min kallon dan...
Tayi wuf ta rufe bakinsa, sau nawa xan gaya
maka ka daina dorawa kanka maraici? Ina sonka
Danliti..... su abba kuma sun amince ka turo asa
mana rana da gaske na ke gaya maka maganar
nan ba wasa ba da sauri ya figo ta jikinsa yayi
wani irin ihu wai shi murna ayuba ya kwaso a
guje ya fado dakin ya same si kankame da juna
dan haka. Bai tsaya tambayar komai ba ya juya
ya fita yana kada kai cikin ransa yana fadin
"Danliti akwai dan iska"ya jima bai kyale mama
taci gaba dayi masa bayani ba yanzu yaushe.
Zaka turo? Ya yunkura ya tashi zaune yace
bashine matsalar ba wadanda zan turar sune
matsalar ta dan bata fuska tace ai ba za ka
rasaba "Danliti ko yan dattijan daku ke gaisawa
sun isa su wakilce ka ko kuwa? Ya zura mata
ido duk sun juye, yace haka ne sai ki baru in gan
su mudaidaita tukunna sannan in gaya miki
ranar daza su zo ko" tace shi ke nan bari in
kwashe sauran kayana in koma gida ya kara
matsarta haba tun yanzu ?" Umma ta ce kar na
dade kuma tunda sun amince da kai ai zaka
rinka zuwa ne kan ka tsaye,"ya kankameta ya na
fadin haka ne amma ban so ki tafi yanzu sonki
kawai ke azabtar da ni ina kewarki da yawa jiya
da kyar nayi barci kinji yadda ki ke tashin
kamshi?gaya min dame dame ki ka shafa in karo
miki irinsu?"Bata iya bashi amsa ba don tun
tafiyar su yake koya mata irin wannan renon ya
gama da rayuwar ta gaba daya kai ALLAH ka
raba mu da sharrin masu sharri,magariba ta
wuce wadan da sukaje masallaci ma sun koma
gida yayin da mama ta fito daga shagon Danliti
jaye da katuwar jakar kayanta. -yar tafiya kadan
ya taka mata ya dawo abinsa bata sami dan
dakon da zai daukar mata kayanba ba don haka
da kanta tayi ta ja har gida abba da umma na
zaune a falo dauke da bakin ciki maras
misaltuwa mama ta turo kofa ta shigo sa
sallamar ta dauke da uwar jakar kaya babu
wanda ya amsa mata ta wuce ta gabansu ta
tsugunna tace sannu abba, wani irin kallo yayi
mata mai isar da sakon haushi da takaici kafin
yace daa ina kike?ta dan sunkuyar da kai tace
naje gaya wa Danliti sakon ka ne ai na gayawa
umma kafin na fita ko um..."Ya daka mata tsawa
rufe min baki don ALLaH shine zakije ki zauna
har bayan magariba kiji tsoran ALLAH mama ki
sani cewar mutuncinki ki ke zubarwa wannan
uwar jakar da kika shigo da ita tawace tukuna?
idanuwanta suka kawo kwalla ta fara rawar
murya na...nawa ne.. Kayan da...Danliti ya siya
min ne yace to ba a gidan nan ba idan yazo ki
maida masa kayansa ya baki can gidan sa,ai
kinji ni ko,?ta amsa da kai umma ta cire tagumi
ta kare mata kallo sannan tace Alhaji ya kamata
a tuhumi yarinyar nan idan idan tabada kanta
gareshi kasan istibira'i ya kamata, kafin a daura
auransu domin ni banyarda da mama ba a yadda
suke tare da yaron nan,ya numfasa ciki da bacin
rai yace ki na da gaskiya don ni ma wallhy ina
wasi wasi cikin raina ke mama ki gaya min
tsakaninki da ALLAH ki fi jin tsoran sa akan
komai na duniya ki gaya min gasjiyar abinda ke
tsakanin ki da Daliti kar kisa muyi kuskure da
gangan idan kin san da wani abu to ki gaya
mana mubi tsarin da ALLAH ya shimfida. -sosai
ta goce da kuka murya na rawa tace ALLAH abba
babu abinda ya shiga tsakanina da shi duk
sukayi shiru suna dubanta kamar sun gaskanta
ta kamar basu yarda ba amma dolensu yarda
tunda basu da wata hujjar kama ta don haka
abba ya daka mata tsawa ya isa don ALLAH tana
wani bare baki kamar mummuna tashi kiba mu
wuri kuma na gaya miki yana zuwa ki maida
masa jakar kayansa,ta goge hawaye ta dan
sunkuyar da kai tace yace ya gode insha ALLAH
zai turo din suka yi banza da ita shiyasa da dago
ido ta dube su uwar hararar da ta yi arba da ita
tilas tasa tayi saurin maida kanta kasa jim sun
kikara cewa komai yasa ta mike simi simi ta
janye jakar ta, ta wuce daki bakin nan tamkar na
agwagwa kai tsaye bayi tashige tayi wanka ta
dauro alwala ta fito ana ta kiran issha'i,don
haka tana yin magariba ta dora issha'i bayan ta
kammala ta fito neman abinci nan falo sukayi
kicibis da yaya ali wai me ki ke nufi baza kizo
kiga amarya ba?ta kama kugu hannu biyu tace
wannan amarya an damu nazo na ganta hala
tafini kyau ne ya kama dariya kafin yace soosai
kuwa tafi ki kyau muje ki ganta tace haka yake
amma duk kyanta dai ni aka fara so kifin ita
saboda haka a daga min kafa inci abinci
tukuna"kalamanta sun ruruta wutar zuciyarsa ba
kadan ba koda ganin yadda jikinsa ya saki
kasan ya fada wani yanayi ya zura mata ido
hannayensa rungume a kirjinsa murya sanyaye
ace zancan ki dutse yar uwata,.
BAKIN CIKI 2***13 hasalima rashinki yasa na
aure ta koda yaushe ki kace da ni kule da sauri
xan ce cas mama don son ki ya zauna a raina,
tayi yar dariya tace yaya ali ke nan kar kasa
amaryar ka ta tsane. Ni daga wasa sai ka hau
jera zance!ba haks nake nufi ba yaya ali muje
kawai naga amarya in na dawo na ci abincin
bata jira yace wani abuba ta yi gaba abinta tilas
ya biyo bayanta yana kada kai!Amare kam
masha ALLAH suna dauke da tasu baiwar da
ALLAH yayi masu musamman aminar yaya ali
har mama na masa tsiya wai ya kamata ya
maida sunan sa aminu dan su kara dacewa da
juna kallon ta kawai yake yi cikin ransa shi
yasan babu wacce tafi dacewa dashi face ita
kanta maman,bata wani dade ba ta dawo sasan
su ta dauko leda cike da kayan garar amare
bayan ta gama cin abinci ta zauna gaban madubi
tayi wa fuskar ta kwaskwarima tayi zaman jiran
Danliti har barci ya fara dibarta bataji aiken yaro
ba,ta kwana zullumi da juyayin abinda ya hana
Danliti zuwa alhalin ya sami izinin yin hakan ko
har yanzu bai amince wa ransa bane?ya gudun
kar yazo ya fuskanci wulakanci!wannan
tambayar taso ta hana ta barci domin ta kai
sama da karfe dayan dare bata sami barci ba,Da
sassafe ta tashi da ciwon kai wanda ya haddasa
mata jiri akai akai duk da haka ko karyawa bata
yiba karfe bakwai da rabi tasa kai ta fice babu
wanda ya sani ta nufi wajen Danliti dauke da
ledar kayan garar amaren da aka bata jiya ita ta
tashe shi barci ya tashi a gigice yana tambaya
lafiya kika bugo sammako haka?tace nayi zaton
zaka zo jiya hira me ya hana ka zuwa. ya ja
dogon tsaki ya kauda kai jim sannan ya juyo ya
dubeta wai me ke damun kine?ba kinzo nan ba
sai bayan magariba kika tafiba?to kuma me
zanje in yi maki saboda ALLAH ta zura masa ido
ya kare mata kwakwazo nan take idanuwanta
suka tara kwalla murya na rawa ta ba haba
Danliti laifi ne don ban gan kaba na biyo in duba
ko lafiya?ya bita da kallo tana ta gugar kwalla
ya kece da dariya kamar mahaukaci hakan yasa
ta daina hawaye ta zuba masa ido yayi dariya
mai isar sa sannan ya natsu shima ya bita da
kallo to meye abin kuka ni ina can ina ta billayin
neman mana waliyai ai banga ta zaman fira ba
sakeena"nan da nan ta hadiye tashin hankalinta
ta fara murmushi duk kin wani daga hankalinki
don baki ganni ba jiya kawai " kawai ne? In gaya
maka dai dai da sakwan daya bana son zama
babu kai,yayi wata budurwar dariya yace ko to
na kara baki tukuicin kaina ta kwanto masa tana
dariya kasan ALLAH da ciwon kai na tashi ga
wani jiri na diba na amma na kasa daurewa na
fito ko karyawa banyi ba, yace ai ya bebi na
sannu ko ya kamata mu karya ki sha magani
bari inzo. Ya fice ya bar ta kwance bisa katifar
wucewar minti ashirin ya dawo da soyayyun kwai
da naman kaza da doya itama hade da kwai ta
hada masu shayi suka batse cikinsu harda ayuba
anan ta yada kafada daga fira barci ya kwasheta
Danliti ya dawo shago ya zauna tare da ayuba ya
zura masa ido yace don ALLAH ka tasheta ta
koma gidan su yayi banza dashi ya fito yana
zuba fito kamar katon arne. -Ayuba ya kada kai
yace karshen alewa kasa Danliti idan an ciza a
rinka hurawa ya ballo masa harara ya ce ba
ruwanka malam ka kyale ni in ci lokacina ya
tabe baki yace na barka zaifi kyau suka yi shiru
kowa na harkan gabansa, a gida kuwa tunda
suka shafa babu mama a dakin ta suke ta
kwasar BAKIN CIKI don sun tabbata tana can
shagon Danliti karfe tara uban dawaki ya gama
shirin sa zai fita ko karyawa bai yi ba saboda
tsabar takaici yasa umma ta fito masa da jakar
kayan da mama ta shigo dasu ya sunkuta yayi
waje da ita kalla ya tarbe shi da sauri ya amsa
ya bude but ya saka Abba yace minna zasu tafi
amma zasu tsaya shagon Danliti, kalla yaja
mota suka wuce yayi fakin kofar shagon abba ya
umarci daya fito masa da jakar nan kai tsaye ya
wuce shagon lokacin da su Danliti ke ta
harkokinsu yayi tsaye babu sallama har
hankulansu suka juyo gareshi Danliti ya matso
yana fadin sannu alhaji ina kwana yace nasan
mama na nan tare da kai ina take baki sake yace
tazo amma ta tafi yayi jim yana kallonsa kafin
yace ba shi ya dame ni ba wannan ya rage kuda
ubangiji ina fatan. Ta gaya maka yace ta gaya
min kokarin da nakeyi ke nan na samu na turo
yace kar ka bata lokaci domin na kosa na kauda
kazantar da nake gani ya dan sunkuyar da kai
yana murmushin izgilanci naji abba in ALLAH ya
yarda zuwa anjima ko gobe zan turo yace shike
nan ina sauraronka amma ga kayan ka nan ka
aje idan ta tare gidanka sai ka bata ba na
bukatar komai daga gareka sai sadakin da
ALLAH ya wajabta ga jakar nan bai saurari wani
abu ba yasa kai ya bar shagon ya fada motarsa
kalla ya ja suka dauki hanya Ayuba ya matso
gare shi yace, Allah na tabaka dama, don ka
gyara kuskuran ka Danliti, kar ka bari ta subuce
maka, ka dawo kana cizo yatsa. Ya watsa masa
harara yace bana bukatar wa'azinka alaramma
karfa ka manta da ni da kai duk daya ne. Na ma
dai san abinyi, ayuba ya xuba masa ido ya rasa
ta cewa babu abinda ya sami Danliti, yasa
hannu ya dauki jaka ya shige da ita. Hannu 2 ya
rike kugu, yana kallon mama xucyarsa na masa
sake-sake. Kusan 5mins yana tsaye, sannan ta
tsugunna ya bubbugata. Ta farka tana yamutsa
fuska, menene? Tashi kiji? Ta yunkura ta tashi
xaune, yasa hannu ya kara janyo jakarta, don ta
ganta sosai. Cike da mamaki tace waya kawo ta?
Yace, abbanki mana! Wannan kadai ya tabbatar
min baya sona, baya kaunta. Bai dameni ba,
amma me yasa zai uzzura min dole sai na turo
magabata na yanxu-yanxu? Hankalinta ya tashi,
ta matso a hankali ta dafa kafadarsa. Don
girman Allah kar hankalinka yatashi Danliti....
Cikin sababi. Yace ki daina gaya min wannan
maganar! Kora da hali abba ke min, saboda
haka ki hkr, kije su baki wanda suke so! Tashi
ki bar dakin nan, kar kuma ki sake xuwa, ni
babu ruwana! Ta narke da kuka, murya na rawa
tace, karka yi min haka Danliti, ina mai tabbatar
maka xan kashe kaina idan ka juya min baya.
(Kuji banza mtsw :(). Ya cire hannunta daga
jikinsa yace, ni ban aikeki ba ya kamata ki gane
ki gane ba dole bane na aureki. Don me xa a
daga min hankali akan magabata? Banda su,
uban wa xanje na tura idan ban nema ba? Kinga
ki tshi kije ki gaya musu na fasa. Ta marairaice
kamar ranta xai fita ni ina sonka Danliti ba xan
iya rabuwa da kai ba, ai dai ni xa'a daurawa
aurenko? Xan gaya musu su kyaleka, sai ka
shirya. Shikenan? Ya kara murtue fuska, yana
kallonta bai tanka ba. Takara matsarsa sosai
taci gaba da fadin, muddin suka ki yarda da
uxurinka wlh na yi rantsuwa xasu sha mamaki
dan wlh nan xan dawo na tare..... Ok, ki sa a
daureni kenan? Tace wa xai daureka? Don Allah
ki kyaleni ni bana son surutu, tashi ki tafi kawai,
sai na nemeki! Dan..... Ya daga mata hannu,
idan baki so raina ya baci to ki tashi kawai ki
bar dakin nan! Ta cigaba da share hawaye, ta
xura takalmi ta dauki mayafi ta mike xata wuce,
amma ta kasa, tayi tsaye tana kallonsa, don
Allah kayi hkr Danliti. Ya dago ido ya dubeta,
hawaye keta ambaliya, yayi dan jim, kafin yace
nayi hkr, amma kije tukunna xan nemeki. Xaka
xo gidanmu? Eh xan xo ki share hawayen, ba
wani abu. Ta share da sauri ta duro bayansa,
Nagode Danliti na! To kayi dan murmushi mana
ko naji dadi mana. (mayya :() Ya banbare
hannayen ta ya mike tsaye, karki damu da
murmushina, muje in rakaki, kafin tace wani
abu, ya fice, dole ta biyo bayansa, bakin shagon
kawai ya tsaya, yace sai nazo ko? Tace, daga
nan xaka tsaya? Xan wuce neman wadanda xan
turo din ne. Nan da nan sanyi ya ratsa mata
xuciya, baki har kunne. Tace, Allah sarki nawan,
to sai mun hadu anjima. Ya daga gira yana
fadin, sai mun hadun, yana sakin tsaki. Tana
shigowa dakinta, ta shige, motsinta kawai Umma
ta jiyo ta biyo ta dakin, tana kokarin cire kaya,
don shiga wanka. Umma ta kare mata kallo, ta
kada kai, tace don girman Allah mama ki rinka
xama a gida. Tunda Danliti na sonki kuma
abbanki ya bashi dama ai shi xai biyoki. Kullum
inaga ya miki babu mutunci ga 'ya mace ta rinka
bin saurayi har makwancinsa. Ko bai aikata miki
komai ba jama'a ba za su dube ki da mutunci
ba. Me yasa Danlit ya sauya miki tarbiya.? Tayi
shiru tana ciccika tana batsewa, Umma tacigaba
ni rokonki nakeyi, ki taimakemu ki taimaki
kanki, don mu tsira da 'yar martabar da tareg
mana a idon jama'a. Kinji? Ta amsa da ka, kafin
tace, Umma idan abba ya dawo ki fada masa ya
daina matsawa Danliti akan turo
magabatansa...... Ta katseta kamar ya? To
umma tunda an gayama sa kuma ya amsa xai
turo din, ba sai asa masa ido ba? Ta mako mata
harara, bangane asa masa ido ba? Shi daman
can bai shirya auran ba, ya hanaki sauraron
wandan ya shirya? To baku isa ba, mu ba wasa
mukeyi ba, tunda ya hure miki kunne dole ya
gaugauta turowa, ya raba da mu da bakin ciki da
muke gani, kinji nagaya miki. Tayi ta tashi tana
fadin, to shikenan ai matsa masa ba shine xaisa
ya turo din ba. Me kikace? Ta shige bayi da sauri
ta rufe kofa. Mama ni kike wa rashin kunya?
Lallai kin rika, kina gab da tsinka min mari akan
Danliti. Sallamar da jiyo, shi yasa tayi shiru. Ta
mike ta fito tana amsawa. Inna saude ce da
Baraka, saude sannunku da xuwa. Duk suka
amsa, yayin da Baraka ta tsugunna ta cigaba da
gaisawa. Bayan sun nutsa