Showing 81001 words to 84000 words out of 110841 words

Chapter 28 - BAKIN CIKI BOOK COMPLETE BY ESHAT.txt

12 Sep 2025

76

yazo shago ya
kwashi kudi ya wuce yanata zage zage dama
haka takeso aci kudina tana jin ciewo tayi
zamanta bataje asibiti ba zata farfado ta hadu
dani kudin dana kashe saita biya su don ubanta
.......ayuba yayi tagumi yana juyayin karfa
mamatarasa ranta .yana isa asibiti a ka turata
emergencylikita yace tiyata za'a yi mata sunan
bukatar jiningaggawa. Babu yanda Danliti ya iya
dole yaceagwada nasa jinin a gani ko zaiyi daidai
Aka gwadaamma bai yi ba. Mai daukar jinin ke
gaya masa akwai wanda ya saba bada jininsa
ana biyansa, idan yayarda a kira shi au tsadance
ya biya. Ba ason ransaya amince ba nan da nan
aka kirashi, suka tsadance,ya biya shi dubu biyu
aka diba, ga kuma kudin aikidubu goma sha biyu
da dari bakwai da hamsin. Donhaushi kamar
yace bashi dasu wannan shiri Maimakon yaci
bulus ya dawo yana cacan kudi donneman
lafiyarta. Wucewar minti talatin aka fito da itada
jariri namiji. Santalele dashi ga kyau ga girma
shikansa likitan sai da yaji kamar ace babyn
nashi ne.Malaman jinya kuwa kamar su lashe
yaron. Ahi kuwaDanliti yake kawai yakeyi cikin
dan kankanin lokaci da bai wuce awa daya ba an
wawure masa kusandubu sha biyar, bai ma san
me zataci ba nan gaba namagungunan. Ya na
tsakar wannan tunanin watanurse tazo ta gaya
masa akawo kayan da za asawababy kudin
aljihunsa kaf sun kare sai da ya komaFandogari
rai bace. Ayuba yayita masa dariya yana masa
kirari, "angon karni angon karni!!", bai kulashiba
ya shiga ciki ya sake lalo wasu kudin ya fito
yakoma. A kagaran ya shiga wani shago, ya
sayo kayanjarirai kala hudu da rigar sanyi, sai
sabulu da Omonwanki ya koma asibiti ya kai
musu aka sayaron.Mama tana kwance bata
farfado ba tukuna. A ka kawo masa jariri ya
karba ya zura masa ido gaban saya fadi. Yace a
ransa "kaga shegen yaro kamar mudaya dashi?
Maimakon ka kwashi uwarka, sai kadebo ni? Tun
yanzu kenan ka nuna min baka dakunya". Ya
bawa kansa dariya ya shiga yi kamarsakarai"
kwana bakwai mama ta gyagije tare da taimakon
nurses da wasu masu jinya saboda karyarda
sukayi, wai daga nesa suke kuma iyayensu
basason aurensu, shi yasa babu wanda yazo
jinyarta.Babynsu sai kara kyau yakeyi, shi ya
kara jawo musufarin jini a wajen ma'aikatan
asibiti da masu sontaimaka musu. Ranar da ta
cika kwana 7,aka sallamesu likita yagindaya
mata sharudda banda aikin qarfi,sannan
tatabbata tana samun ishashen kayan qarin
jini....dantayi saurin maida jikinta.sati daya aka
basu su dawoakara duba lafiyarta sukayi sallama
da kowa cike dakewa,,,,don anriga ansaba
dasu.danliti ya kwashesu a mota suka kama
hanya. sunfara tafiya ta kallesa idokode tace
haryanxu banji kafadi sunan yaronba,kawaiqarya
nayi wa mutane ake kiransa adamu...jitayikawai
yamake mata baki..kar insake ji bakinki ya
kirawannan sunan.dama na kyaleki ne dan
ganinmutane,,don iskanci kirasa sunan da zakisa
wa shegen danki sai sunan ubana? Tuni take
rungume da baki ido waje takekallonsa,,tace
haba danliti!baka tausayina? dana sansunan
babanka ne zanfada?wlh zuwa kawai
sunanyamin nafada musu shiyasa ranan da kazo
da ayubasuke ta kiranka baban adamu... yasake
kawo matawani dukan,yace sake fadi kikayi??
wato raini ya shiga tsakaninmu koh? bakisan
cewa inajin haushinkiba ko?to kibi a
hankali,idan kina neman zaman lafiyadani,,idan
nasake jin adamu a bakinki sai na karyakiwlh.....
taguma ta doka tana kwalla tana kallonsa,Allahb
aka haquri danliti,yaron nan dai dankane,duk
sunanda kace akira dashi za'a na
kiransa.bannaso na bata maka rai danliti..amma
kai abu kadan sai fushi. yacebabu ruwana da
sunan yaro,,idan kinso ma kinakiransa BIRI ,duk
daya a wajena!tace Allah ya hucizuciyarka,,
maganar batakai hakaba,tunda ran talataaka
haifishi zamu na kiransa mai kudi...yadan
dubetakadan ya kauda kai yarage naki inkinso
ma kina kiransa miloniya wannan keya
dama..zatayi maganayadaga mata hannu banso
jin don Allah kimin shiru.tasunkuyar dakai tana
kallon yaron dayake jikintayanata bacci
abunsa.har suka iso gida,,basuyi wanimagana
ba.ya tsaya kofar gida tafito yatayata
kwashekaya..taron mutane nata kallonsu suna
mamakin wannan lamari..bai zaunaba yajuya
yana kokarin fitatace ya maganar abinci?zan
girka ne ko za'a na kawomin na sayarwa? Ya
kalleta sama da kasa yace,wai ke me
kikadaukeni?baki ganin kudin dana kashe a
asibiti? Koshagon kikeso ya rushe na tsugunna?
baga saurankayan tea a nanba?ki hada mana
kisha! Kedamaba'aso ki nannagi abu mai
nauyi.mtsssss..... Yajatsaki yayi waje,,,ta koma
gefen katifa tana tabe baki...a ranta tana fadin
Allah ya huci zuciyarka.tadangyara waje tamaida
kai ta kwanta ba'a jima ba bacciya dauketa...
Bayan sallar la'asar kukan yaro yatasheta.ta
tashi da sauri tabashi nono da ruwa..nandanan
yasake komawa barci.tafito tsakar gida
tanahamma tareda mikar yunwa..tayi dan
shawaginta a tsakar gida takoma daki..tajanyo
ledar kayan tea tazuba a kofi tajanyo fulas zata
tsoyayi ruwa taji baburuwan..tasaki tsaki ta nufi
kichen babu itace ko dayabare ta daura.haka
tadawo tasha tea da ruwansanyi..tasake
kwanciya dan babu abunda zatayi harqarfe taran
dare bataga danliti ba,,bare tasa ran wani abun
sanyawa a baka. Ga yunwa tana sha'awar
tacimai dan gishiri...nan take tayafa gyale ta
zura silifastadauki jariri taja kofa tayi waje ta
lallaba a hankalitayi wajen danliti.....yana
ganinta ya daurefuska,,,yayinda ayuba ya taso
ya karbi maikudi,,meya kawoki?inji danliti tace
naji shiru ne ga yunwa inaji.....ba akwai kayan
tea ba?we me kedamunki ne? Murya raunane
tace nasha wlh..dama ruwan sanyinasha babu
sauran ruwan zafi kuma babu itace...maidan
gishiri nake sha'awan ci kodan yayane! Ya
gyarazama nifa ba ubanki bane,bakuma
mijinkiba bare kinadauramin wannan
nauyin,,kingane koh?daga taimakosai ya zama
tsiya?ki dauki duk nauyinki ki dauramin? to bafa
zai yiyuwa kinjiko?karkisake biyoni shago
kicenabaki wani abu...abun da nasamu nabaki
basai kinmatsamin ba..karki sake dauko danki
kizominnan...idan kunne yaji..... Tace yi
haquri,,,yacewaayuba bata danta ta koma.ta
karbeshi tajuya zatawuce taji yana fadin bata
taliya daya taje tadafa karta cinyeni....ta karba
tana murna ya wurga mata nairaashirin tasaya
itacen..jikinta na rawa ta dauka hardagodiya ta
sabo yaronta takoma gida..sai yanxu matake
tunanin a ina zata samo icen dare yayi?ta
sauqenumfashi numfashi takoma takwanta
dayunwarta.dasafe da kanta taje ta nemo
itace,ta tafasa ruwa ta dura a filas,tayi wa danta
wanka itamatayi..tahada tea tasha da ragowar
biredi. Tayi wanka tayi wanki duka ita
kadai,,anjima kumadole ta bararraka taliyan da
zataci.ko ta ci gaba dashan shayi...aikin yamata
yawa ita daya shisa dakwantawarta zazzabi ya
rufeta. Maganar haihuwartakuwa naci gaba da
yaduwa a gari,wasu emmata masukarambani
haar suna zuwa mata barka.haka tci gaba da
manejin rayuwa sai abunda danliti yaga dama
yakekawo mata taci,a lokacin da kuma
yagadama! .......kwana 7 suka cika tayi masa
maganarkomawarsu asibiti,,,kai tsaye yace bai
zuwa,Allah daikonsa jikinta ya hade kamar yana
samun kyakkyawarkulawa.haka mai kudi yayi
bulele dashi alamun ruwan nonon dayake sha
yanada kyau...batadai zuwa koina,,,saboda
danliti yahana.komaisa oho?shi kadaiyasan
dalillin yin hakan. wannan satin shine ake bikin
baraka da muhddinta,mama na gida mai kudi
goye a bayanta.tunsafebatasa komai a
cikintaba,,,har zuwa yanxu da akaidar da sallan
la'asar.tagumi hannu bibbiyu tayi tunanitake
lafiya meyafaru da danliti baizoba?bata
samuamsarba taji tsayuwar motarsa. Farin ciki
ya lullubeta ta taso ta tarbesa.babu walwala ya
wuceta yashigedaki...t abiyo sa abaya tazauna
kusa dashi tanatambaya,,,waya tabamin cweethrt
dina?ko fushin netunna jiya? Ya ballo mata
harara yace kinason wanimarinko?to kici gaba
da tadamin wannanzancen,,tadan kada kai tana
murmushi tace sha kuruminka,indai maganar
aure ne bazan sakeyimakaba duk lokacin dakaga
ya dace saimuyi,,shiyasa bangankaba
tunsafe?.......ido zuruyana kallonta bansaniba!
tace yi haquri shalele mezanci yau?yace babu,ki
tashi kishirya kije gidan bikikici..tace bikinwa?
yace ke saboda sakarci ma bakisan ana bikin
yar uwarkiba?bikin yarinyar nanakeyi baraka...ta
ware ido ta washe baki,bikin barakaakeyi?to ina
zan sani ka hanani fita? Yayi matabanzan kallo
ai dama ni kike gani na hanaki fita?toubanwa
zakiyi a waje?kina samun ci kina
samunsha...kinfiso kirinqa yawo kwaroro kwaroro
da goyo ana nunaki?to shikenan tunda kinfison
hakan gahanya nan,,,,amma kisani kwayar dawa
bazan kawomiki gidan nan ba..da sauri ta
rungumeshi,Allah sarkidan litina,ba haka bane
,nima bana sha'awarfitan,tunda baka so.yanzu
bari in shirya ka saukeni agidan bikin...a razane
ya kalleta,wai ke meyasa jaka ce?kawai sai in
daukeki a mota in kaiki gidan biki anakallonmu?
idan ke mahaukaciya ne nida hankalinanasan
abun da nakeyi....
BAKIN CIKI 3***2 Yaja dogon tsaki ya tashi .da
sauri yatashi yafitayana fadin sakaryar yarinya
kullum sai ta bata wamutum rai!ta taso ta biyo
shi tana bashi haquri,baisauraretaba yafada
mota abinsa,,,,tadawo tanahawaye tana shirya
mai kudi.ta goyashi ta rufa gyaleta kulle
gidan...bata zame ko inaba sai gidansu
baraka.ana tsaka da biki kallo yadawo
kanta....dukyan uwa na kallonta a
wulaqance,tana gaishesu sunabasarwa.kai tsaye
inda inna saude take ta dosa,takuma zuba mata
ido harta qaraso gunta,,,sannu inna!Ta bita da
kallo daga ina?tace daga gida,yanxu danlitiyake
gayamin ashe auren baraka ake,nace ina nasani!
inna saude tace dama ya za'ayi ki sani?ke
kokunya bakijiba?kika ratso jama'ar nan da
goyo kikashigo?dubeki kamar ankoraki babu
mamaki ma bakiciabinciba. Duk baki ya wani
bushewa anya kuwamama...baza kiji magana
bako?wannan duniyarkagama da iyayenka lafiya
ma ya ka qare?belle ke kina kallo mahafiyarki
tafadi ta mutu saboda BAKINCIKi,,mahaifinki
nacan bisa keken nakasassu.ammaduk wannan
baisa kinyi nadama ba mama?ke kuwawata irin
iskar duniya ke kwasarki????? A marairaicetake
magana inna bai kamata ku ringa ganin laifina
bani kadai....ta katseta da sauri rufemin baki
sakarya! Da yana son aurenki da tuntuni baizo
yayi maganaba?tun yaushe kika haihu?ina
lissafi watanki biyarkenan! ya ajiyeki kawai kin
biye masa kunawatsewa..wa llahi ki guji
makomarki,,ki kuma gujiwalaqancin da
namiji.gashinan ai kinfara gani da hakakike?to
wlh ki kuka da kanki karma kice kin
sanni,,saboda haka juya ki koma inda kika fito!
Tace aidama shima dan liti yace inya shirya
zaizo yasameku a daura mana aure,ta watso
mata harara tajadogon tsaki zata wuce mama
tace banga amaryarbainna,ina take?ta juyo
tace,suna makwafta itadaqawayenta..tayi
tafiyarta sabgoginta.mama ta shigazabga
loma,rabonta da abinci da naman kaza harta
manta.tayi ta zabga tana zare ido gwanin
tausayi.kankace kwabo,ta tada shinkafar nan
cikin kwanotatas,ta kora ruwa da kunun aya tayi
gyatsa tayihamdala,sannan tajita aduniya..
Tananan tsuru kamarmujiya baraka tashigo cikin
gidan,inna ke gayamatamama tazo,,ta zagaya
bayan kicin din tasameta zaune tana bawa mai
kudi nono,,bakin ciki yaturnuketa kamar ta
hadiyi zuciya ta mutu.haka nan tacije ta qarasa
gunta fuska daure....amare!injimama,tace mama
kenan,ya kike?tace kuma dankowa ya gujeni
shine hardake koh baraka?zancenbikinma a
bakin danliti nakeji,,,banci arzikin da zakizo
kisameni ki gayaminba.ai kinsan inda nake.ta
kalletasama da qasa ni bansan inda
kikeba,,koda ma nasaniwannan ba gidan zuwana
bane..hasalima namantadake.bandan kinxo inna
tace kinanan ba wlh bazantaba tunawa dakeba.!
mama tace ba laifinkibane,,,,,,,ta rausayar dakai
tace thank god da kika gane ba laifina bane.bari
inkoma frnds dina na jirana.tajuya dasauri
tawuce ko kallon yaron batayiba.mama ta
tabebaki tace agayas mai qawaye,zakaran da
Allah yasoda cara,ko ana muzuru ga shaho sai
yayi.danliti nedai ba a kauna,nikuwa inason
kayana,bazan rabudashiba! yawwa! Ta mike ta
jefa mai kudi a baya ta goyeshi ta tafi neman
inna tasameta tace innazantafi,ta juyo ta
dubeta,bangane zaki tafi ba?bakijiabunda nace
bane?ko a zatonki wasa nake?nandanan ta
kumbura fuska.samu wuri ki zauna kafin nabata
miki rai!ta zauna gefen gado tana
kunkuni,kowana kallonta,masu taya inna fada
nayi........ana sallar magaruba gida ya gwaraye
da duhu sai inda aka ajiyefitulun kwai keda
haske.mama ta fakaici ido ta sulaleabunta ta
kullin wainar ta da miya,duk ta juye su
cikinleda.abincin dare ne da aka rabawa kowa
tajuye nataa leda,,ta cika wa zaninta iska ta
harba gida abinta.Hankalin inna bai dawo
garetaba,,sai da za'a wuce da amarya.ta nemi
mama sama ko kasa ta rasa.ta dokatagumi tana
sanar da Allah da manxonsa kafintace,kai
jama'a!wannan yarinyar tayi nisa batajin kira!
Allah ka shirya mana ni saude..sauran mutane
sukace amin!haka aka wuce da baraka tana
kukan BAKINCIKI!da takaicin yar uwarta.ita
kuwa mama tana can hankalinta kwance,ta juye
wainarta a kwano miyarkuwa taji tantakwashi
masu taunuwa,zatafara cikenan danliti yashigo
gidan ,ya tokare bakin kofayana kallonta,,,tace
saboda me?yace saboda naxokafin magruba
naga baki dawoba. Tayi dan murmushidanliti
kenan,bikinma badan kaikace najeba maizai
kaini?kaga maganar inki dawowa ma
baitasoba.yaqaraso yana fadin Allah
yasoki,dama bell dina nadawo induba,idan baki
dawoba inbiki hargidan indawodake,,sannan
inmiki shegen duka! kinganshi ko?, Tace Allah
sarki danliti bai kamata kanadukanaba,,,iyakar
biyayya inamaka,amma dankuskure kadan sai ka
hassala..!ya zauna kan tabarmayace,ke dai kiyi
shiru tunda Allah ya kwaceki yau,aiku mata sai
da haka,domin kwakwalwar kifi Allah yayimuku.
Ta sosa kai tana kallonsa,batace komai.danki
yayi barci ne?tace eh! Meye wannan kike ci?
tacewaina ce inna ta bani.yajanyo kwanon
gabansa yacedama kuwa yunwa nakeji..tace to
muci tare mana aitana da dan yawa.yace ni
bazanci dakeba miko filet inzuba miki.ta jawo
filet din roba ta miqa masa,ya jefamata guda
daya..tace guda daya nagani?......a fusace yace
wannan wani tambayar banza ce?don kinxo
dawaina zanci? shine kike min kurilla?watau
nawa nebanza!ga tsiyarki cinye dani kike
zancen,,,,ya turamata kwanon.da sauri ta maida
masa ta tarairayo shikamar na goye,tayi ta
rarrashinsa,sannan ya aminceda cin wainar.
Tarinqa bashi a baki,,ya taune qashin ya
batse.ita kuwa ko guda dayar bata ciba,bata ma
kokwatanta ci ba,don karya ransa ya baci.sai
dayagyatse,sannan ya gaya mata bibikon da
yake nanemanta...babu musu tabada kai bori ya
hau Haka rayuwar mama ta kasance tamkar
tadabbobi,,duk inda danliti ya kadata can
zatadosa.tsakaninta da Allah kafin maikudi ya
shekarabiyu ya zubda mata ciki sau uku kuma
kowanne babuwanda batasha wahalar
zubansaba.,,duk ta jeme tayiduhu fatar jikinta
yafara yaushi saboda wahala da ukuba.(Allah zai
i sarmata) ......tabbas hakane,tundamasu ganin
rashin jinta ne yajawo mata halin da takeciki
sunayi mata addu'a, mussamman abba kullum
yadaga hannu samu bashi da abun nema wajen
ubangijiface Allah ya dafa masa akan qaddarar
data sauqaaka sakeena,wanda hakan shi ke
hana yan uwanta zuwa fandogari...amma kannen
abba sukanxo abujasu dubashi.haka ya ali
musamman yake zuwa damatarsa su duba abba
su koma. Shekarunta qarashudewa suke tare da
qara dumulmulewar rayuwarmama cikin kunci da
talaucin dole...duk yansuturunsu sun mutu,ko da
yaushe busu busu zaka gansu,musamman
lokacin sanyi.babu manshafawa ,babu sabulun
wanka,balle na wanki,sau ukutana zuwa neman
taimako wajen inna tanahanata.tace muddin
bazata dawo cikin yan uwantatazaunaba,ko
kwandala bazata bataba......mama tagammace
hakan shiyasa ma tadaina zuwa.wani lokacin
tsirara zakaga mai kudi yana yawo sabodarashin
sutura.sai makwafta sunga Allah sunga
annabizasu kamashi su sanya masa kaya
sadaka,anya?kaicon wadanda imani yayi musu
karanci! BAYAN SHEKARU GOMA SHA BIYu.
Nasan maitausayi da imani zai daura hannu akai
yanakururuwa,idan yadubi halin da mama take
ciki dayaronta kai duniya!ina zaki damu?
shekarunta nahaihuwa talatin da biyu cif
cif.amma idan ka dubetazaka rantse da Allah ta
zarce hamsin.tsufa ya bayyana kuru kuru a
jikinta,badan takai shekaruntsufanba sai don
wahala. Sau da yawa tanayin rashinlafea babu
kulawar data dace,saboda zata kwantaciwo sai
ta kusa sati akwance kafin danliti yakaitaasibiti.
koya sayo mata magunguna.muddin kuwahakan
ya kasance to tabbaci idan ta warke sai ya
kirkiro mata laifin da bai taka kara ya
karyaba,don yajibgi kudinsa...a wasu lokuta idan
taje rokonsa ayubake tausaya mata ya dauka
cikin shagon yabata aranar kuwa zai bita gidan
ya narketa yandayaso,dataga hakan ba riba sai
ta fara neman wankaua makwafta tana samun
abincin da zasuci itada danta. A wannan hali
mai kudi yatashi yagamahaifiyarsa cikin ukuba
da azabar duka wajenbabansa,wanda shikansa
yagane randa yazogidan,sai yaga mahaifiyarsa
na kuka.tunyana matamaganar makaranta har
yadaina.ya fahimci cewabashida gatan xuwa
makaranta kamar sauran yara!!... Daka
dubeshi,kaga yaro mai kyau amma babugata.sai
dai abun mamaki a game dashi yana danitsuwa
kuma a koda yaushe yana taredamahaifiya
rsa.,musamman inyaga tana kuka,daya farakawo
qarfi sai yafara fita nema,shine yankan ciyawaya
siyar,shine neman kwalabe da fasassun robobi
da tsofaffun karafuna a bola,yana kaiwa inda
akesayarwa,ya siyar ya kawo mata kudin. A
haka tasamu da kudin datake wankau
tahada,tajajarin AWARa,tana rabin tiya tana
sayarwa a zaurengida.a haka take dan saya
musu kayan gwanjo masuarha.duk wannan halin
da mama take ciki gaba dayajama'a namata
kallon rashin biyayyar iyayece ta jawomata
hakan.shiyasa kalilan ke tausaya mata.itada
gidansu sai gani sai hange,,ko a hanya ba
dukkansuke magana da itaba,rayuwa tayiwa
mama tsauri dayawa,tsawon shekaru ashe dole
tayi tsufan qarfi dayaji........yamma tayi sosai
lokacin da mama kezaune gaban kaskon suyar
waranta a cikin zaure.yaranata shigowa suna
saye naira biyar biyar,goma ashirin,duk yanda
takama.muna iya cewa tanaciniki,don bata
tabayin kwantaiba.maikudi ya shigosabe da
buhun tarkacensa a kafada.kayan jikinsaduku
duku,kafa babu takalmi,ta cire kai cike da
fara'ata kallesa,yaro dan umma andawo?ya
zagaya gefentaya zauna.nadawo umma.tace
angaisheka.to kaje kayi wanka kayi sallah,akwai
dumamenka yananan atukunya,ka zubo kaci.yace
to ya mike ya sungumibuhun kayansa yashige
gida.yayi duk abunda taumurcesa.ya zubo
tuwunsa yadawo zauren gefentaya zauna. Ta
dubesa sai kaki ci saboda riba?kai nalura kafini
son kudi,,,,yayi yar dariya yace umma kenan
yanxu saboda Allah gabadaya ribar
nawakikesamu?tace mungode wa Allah ko nawa
ne,ammaai dole aci,dauki guda biyu to,yace
barin gama cintuwon tace gama idan kuma ta
qare ka huta. Ya sa hannu ya dauki guda biyu ya
ajiye a gefe,yaceban nuna miki ciwona ba,wani
tsohon kwano ya yankemin gefen kafa!ta kamo
qafar cikin sauri da tausayitace wayyo dan
umma,sannu,shiyasa na kosaingama tara maka
kudin takalma ka sayo,gamacintuwon inbaka
naira goma kasayo ja da yalo in rinqa barbada
maka yana saurin warkar da ciwosannu.....yace
to umma!sukayi shiru yanata cintuwonsa yana
gutsurar awaransa,jim kadan yaceumma wai ni
bani da wani suna ne sai mai kudi?tayidan
murmushi tace kana da shi mana...yace
aibantaba jin kin kirani bane,zura masa ido tayi
tace sunan kakanka gareka shisa bana kira
shima yabitada kallo yace kigayamin inji,gobe
idan munhadu daabokina in gayamasa,tace
sunanka adamu,ya sakibaki yana murmushi,yace
lalle ai sunan tsofi neamma inason sunan.tayi
yar dariya tace amma karkabari babanka yaji
yasan nafada maka dan baya so,yace saboda
me?bashi ya radamin ba?tace shineamma
saboda sunan babansa ne baiso ana kira.yatabe
baki yayi tsaki,yace bani kudin ja da
yalon,tamika masa naira goma yafita yana sude
hannu,tabishida kallo ta kada kai,domin ta
fahimci bayasonmaganar babansa,,,bai taba
yabonsa ba kuma bai damu da
al'amuransaba.bai dade ba yadawo
damaganin,ya zauna ya kakkabe kasar jikin
ciwon,yamika mata kafar tasanya masa garin
maganin.nansuka zauna sunata hirrasu har wara
ta qare,ya kwasomata kayayyakin yadawo mata
dasu gida,yayin da itake zaune tana qirga
kudin,gaba daya dari uku tayi ta ware uwar kudi
Ta ware uwar kudi,tasamu ribar naira tamanin,ta
cirenaira goma tabawa mai kudi tace jeka wurga
a cikinasusun takalminka,kayi sauri kayo mana
cefane danaira saba'in din,sannan ka auno min
wakensuya,rabin tiya mai gwangwani biyu....yace
to ya karbikudi yafice,itama ta mike ta ddebi
ruwa a bokiti ta dauki sabulunta yankan qusa,da
soso tayo wankatafito.injin oil dinta a yar
roba,,ta dauko ta shafa tacanxa tsumman
zaninta da wankakke, ta hada dawata kodaddiyar
t shirt,ta fito tashiga kicin ta doraruwan tuwo.
Sallamar mai kudi ta amsa ta leqo dagakofar
kicin din jirgi dan umma,shiyasa nake sonka
saboda babu wasa,,yana murmushi ya zube
matacefane,ta duba komai dai dai yasayo ya
laluba aljihuya ciro naira biyar ya miko mata ta
me ce ce?yacemai waken suyane yamin ragin
naira biyar,ta dafakansa,tace Allah sarki
mungode,amma kaima kajekasha minti,,,ya kada
kai,umma me zanyi da minti kamar qaramin
yaro......ta kece da dariya!iye lalle maikudi
angirma ko?to je kasha rake..yace umma ki
ajiyeko farin maggi kya saya ko kuma a xuba a
asusu...tazura masa ido tadan kada kai jeka tura
a asusun,,,yawuce taraka shi da kallo harya fito
tana tsaye batamotsaba mezan tayaki umma?
tace kaga ka zauna ka huta ai ka sha gararanba
dan umma,,,ya kamata kahuta,kaga rauni a
qafarka.yace to. Ya jawo tsohuwartabarma ya
kakkaba ya shimfida a kofar kicin
din,yakwanta.it a kuma tana ta hidimar mada
miyar kukakamar yadda yayo mata cefane,.
Bayan ta kammala,ta fito da robar gari
tanatankadewa tana fadin daga yau ma garin
tuwunmu yaqare,,,ya yunqura yatashi,yace ai
gara daya qare maumma.nagaji da cin tuwon
nan,ta dubeshi da kyautace yaro kenan!har ka
mance wata rana ma nemantuwon mike ido rufe?
bama samu?kadaina fadar haka komai Allah
yabaka kayi masa godiya sai ya qaramaka kaji
ko?yace naji umma amma kinsan waniabu?sai
ka fadi...yace in Allah yasa natara kudi dayawa
zanbaki mamaki.tana dariya tace aidamakasaba
bani mamaki yarona.....yace amma baki
tabaganin wannanba....kedai kiyimin addu'a
Allah yasa intara kaya da yawa,,,tace to Allah
yasa dan ummayace ameen..ya koma ya kwanta
yayi matashi dahannunsa.yana bata labari
tanashan dariya.ta qaregirkinta ana kiran
magrub..ta kwashe ta aje gefe gabadayansu
sukayi alwala sukayi salla,shiya dauko
musuabincin sukaci tare kamar yadda suka saba.
Bayan sallar isha'i ta koya masa karatun
alqurani kamaryadda suka saba haryakai
amma,mai kudi nason yinkrtu amma basu da
kudi shiyasa take koya masa dakanta.kullum
kafin su kwanta,,,musamman ranakunda
babansa bai xoba,,,shiyasa bayason
zuwansa.donyasan zuwansa baya haifar da
komai sai BAKIN CIKI .A Garesu Kwana uku
mama na ririta kudin da ke hannunta dankar dan
jarin da take taqama dashi ya qarye,,,gashidan
gogan yaqi waiwayarsu balle ya wurga masu
nairadarin datake samu tayi awo akai niqa,su
sami garintuwo....shikuma mai kudi yana can
kasuwa wajen yankyadi da tulin kayansa.. Daya
tara buhu buhu,,,kuma Allah da ikonsa wannan
karon yasamu manyan kayamusamman
karafa,aka auna kayansa sai gashi dakudi naira
dari bakwai da hamsin...kai farinciki kamarya
kasheshi,,,,nan da nan yafada
kasuwa.dafarkoshinkafa yasaya rabin tiya.......ya
wuce teburin mainama yasayi na dari da
hamsin,ya koma bangaren kayan miya aka hada
masa na naira dari,yabadamarkade,,,aka juye
masa aleda,,mai gwangwani biyuda maggi mai
tauraro dda fari,ya koma ya nemi wajeya nutsu
ya qirga ragowar kudinsa naira dari dasaba'in
yanade abinsa yamaida aljihu ya
kwasocefanensa ya dawo gida. Mama tasaki baki
tana kallonsa da ledodi,,,ina kasamo kaya haka?
yacedama nagaya miki zanbaki mamaki,kayan
da na tarane...ta bude ledodi tana fadin iye!
yanxu kayan nanharsun kai haka?yace naira dari
bakwai dahamsinfa...kinga harda canjin dari da
saba'in nakawomiki ki qara jari,,,,ta saki baki
tana kallonsa ya miko mata kudin,,,ta amsa
kina ta kallona umma ko bankyautabane?ta
janyo shi jikinta da sauri tace a'a
danumma..gani nayi ka kwashe kudinka ka
kashe,bakasayo wa kanka komaiba,,,,ai da
kasayo kodatakalmine,kaga wancan asusun sai
kaci gaba da zubamasa abunda yasamu
kawai.........yace babu komai umma,nima so
nake muci dadi yau,,rabonmu fa dashinkafa tun
na sunan maman fati kullum tuwo mukeci,,aiya
kamata mu canza,tunda nayi dabara
nasamukudin. Tayi dariya tana mamakin mai
kudi,,,,sannan tanumfasa,,gaskiyane,Allah yayi
maka albarka.ammaduk da haka kadauki saba'in
da biyr kasayosilifas,inyaso daga baya

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login