Showing 3001 words to 6000 words out of 110841 words
sai a kansa. Zaki
tayani kawata?" tayi dan murmushi tare da kamo
habar ta, "mama kenan, sai ma kin tambaya?
Matsalarki ai tawa ce. Ki sha kuruminki, insha
Allahu by nxt year zamu sha bikin likitoci, ranar
duk wani mai ciwo a fandagori zai warke" Ta
fara dariya, "au dariya na baki ko? Kinag dai
PANADOL shine tekaway dinmu, ANTI BIOTIC
kuwa su kowa zai sha a wajen dinner, to ina cuta
zata zauna?" Ta buge kafadarta tana kara
darawa, "surutunki yayi yawa baraka, ubangiji ya
cika mana burnmu" ta amsa da amin. A bakin
titi suka yi sallama akan zata ji duk yadda
al'amarin ya kaya nan gaba. Ta tsallako hanya
tana tafe zuciyarta kunshe da sake-sake kala-
kala. Wani lokacin ta kanji kamar kwalla zasu
zubo mata sbd tsabar damuwa. Ta shigo gida
yaran gidan sunyi nisa da karatun allo, kamar
kullum. Malamin su ke zuwa ya basu darasi.
Taja birki ta gaishe shi, ta wuce da sauri ta
shige gida, ta mika wa ummanta dinkunan ta.
Bata tsaya bata lokaci ba ta sungumo Kur'aninta
da sauran littattafai ta koma wajen malam ta
kwashi karatu. Sai da ta tabbatar karatun ya
kama bakinta, sannan ta koma dakinta ta ci
gaba da nazari. Hakan ya dan kauda mata
damuwar da ta tsinci kanta ciki yau. Shi yas ma
taki sassauta wa karatun, don bata son ummanta
ta fahmci wani sauyi a game da ita. Sun Sallaci
Isha'I sun ci abinci tana like gefen Abbanta
Umma ke fadin wann karon kuma ina zaki hutu?
Kanta tasye ta bata amsa wajen Ya abdulkareem
zani. Baki sake take kallonta wai! Wai! Yau
kuma aljanun can suka buga? Tayi yar dariya
umma kenan ai dama ba wai bana son zuwa
minna bane kawai Anti rabi ce matsalata kayita
aiki kamar boyinta. Ta dan harareta uhumn ke
kuma malalaciya uwar son jiki ba a haka ake
koyo ba? Ta kada kai a'a wllh naje hutu kuma
inyi ta aiki ina amfanin hutun ko Abba? Yace
kyalle Umman nan kema kike zuwa gunsu kiyi
zamanki wajen Abbanki inga me samin ke aiki.
Umma tace oho! Shi zaki goya miki baya? Ta ai
gidan wani zata aiki kam dole tayi shi ko anan
dinma. Yace ok hakane? Kinga kiyi tafiyarki Abj
wajen soja. Ta kada kai bari dai in tafi minnar
Abba, kasan shima yaya yana ta korafi wai ban
zuwa gun sa. Yace amma nasha mamaki.....
Name Abba? Son zuwa minar nan koda yake duk
yarinta ce take saki zuwa hutun nan da zarar kin
fara jami'a ajewa zakiyi, Umma tace likita ba!
Dokta Sakeena! Ta langwabe jikin Abbanta tana
dariyar dole amma cikin ranta tausayawa junan
su takeyi musamman Al-Ameen da kansa yake
rawa yana ganin matsalar me sauki ce abin ya
kara kashe mata jiki data dubi Abbanta taga
yadda muraran fuskarsa ta nuna alfahari da
kalaman Umma. Kwance bisa gadonta amma
barci yaki yuwuwa dabarar ta taje hutu minna ko
Allah yasa su kara ganawa da Al-Ameen koda
Uban Dwk ya soke bukatarsa. Shin yaya zatayi
ne? Mafita kam babu sai abnd Allah yayi. Ta
kuwa kwana gayawa Allah don ya zaba mata
abnd yafi alhairi. Ko karatu ko auren Al-Ameen
wanda zamu iya kiransa mai sa'a gwarzon da
yayi nasarar ciwo zuciyar Mama da yaki har take
tunanin dama ace burin Abban ta aure ne bason
zama likita ba. Shawara ta zauna kan jibi da
yardar Allah zata wuce minna. Sha biyun rana
daidai tana shimfide bisa gadonta tare da
muguwar kasala, shigowar Uban Dwk gida
dawowarsa kenan daga kewayen gonakinsa. Ya
daga labulen dakinta tare da fadin yaya dai yar
gidan Abba? Ta tashi zaune tana murmushi,
babu komai Abbana har ka dawo? Yace na dawo
Mamana lfy dai? Naga kamar jikinki a mace
yake. Ta amsa Allah ya taimaki mai martaba lfy
kalau Mamanka take bacci ne bai isheni ba. Ya
karasa shigowa dakin ya tsaya akanta yace ni
kuwa banason ki saba da yawan bacci Mamana
kin fa san karatun da zakiyi mai wahala ne
bayason lalaci ko kin manta ne? Ta dan rausaya
kai tana murmushi ban manta ba Abba ko
yanzun ma rashin abin yine yasa. Rashin abin
yi? To taso muje in dai abin yine ni zan baki shi
yanzun nan. Ta fara dariya meye shi Abbana?
Yace ki zagaye tsakar gidan nan sau 12, ta kame
baki wuuu! Abbba a tsakar ranar nan? Ai sai in
zube sumammiya, duk suka dauki dariya yayin
da wani matashin yaro yayi sallama sassan yace
ana sallama da Alhaji. Umma dake waje ta
karaso da sakon. Shi mutum ne me girmama
bakinsa don haka bai bata lokaci ba ya fice don
ansa sallama, wata zungureriyar marsandi ya
fara cin karo da ita a kofar gidan sannan
idanuwansa suka kai ga bakinsa maza su 2 a
tsaye wanda kallo daya zakai musu ka tabbatar
manyan mutane ne. Kai! Guda a cikinsu ma Uban
Dwk ya sanshi farin sani kuwa domin fitaccen
mutum ne a gwamnatin data shude ambassador
ne 10yrs back, watau Alh Saifullahi Sodangi
Lafai kuma marafan lafai. Take nan mamaki ya
saukarwa Uban Dwk ganin cewa babu abnd ya
taba hadasu na mu'amala. Cike da mamaki ya
bisu da sallama cikn fara'a suka yi musabaha,
sannan ya kira yaronsa Kalla yace maza ya bude
masa falon baki. Can suka rankaya da bakin
nasa, ya nuna masu kujeru yana fadin "bismilla!
Kai sannunku da zuwa!" Sun fara gaisawa kenan
kalla yayi sallama ya shigo da gorunan ruwan
(Swan) bisa tire da kofuna, ya aje gabansu. Ya
sake dibar gaisuwa ya fice ya bar falon. Uban
dawaki ya shayar da bakinsa suwan sanyi. Bayan
sun natsa Ambasada ya soma da cewa,
"watakila ka shaida ni, watakila kuma baka taba
sanina ba". Uban dawaki ya cafe, "farin sani
kuwa, mai girma marafan lafai". Suka yi 'yar
dariya, "babu shakka, to wannan kuma kanina
ne uwa daya uba daya, alh. Nuhu lafai". Uban
dawaki ya jinjina kai, "tabbas kuwa, ga kama
nan, sannunku da zuwa" Suka kara amsawa,
sannan alh. Nuhu ya zarce da bayani, "Allah mai
yadda yaso, kuma shi yake shirya al'amuransa
yadda yaga dama. Watau jiya yaron wajenmu
yazo garin nan, domin mahaifiyarsa, ya kuma ga
'yar wajenka wacce ta tabbatar masa cewa ita
'yarka ce. A hakikanin gaskiya dai yaro ya gani
yana kuma so da aure, shi yasa yana zuwa ya
sanar mana, mu kuma muka ce ai babu bata
lokaci dole mu kawo gaisuwa, tare da neman
izini. Domin a haln ynzu bamu da wani buri da
ya wuce Allah ya nuna mana aurensa, tnda ya
kammala karatu har aiki ya samu. Don a gaskiya
mun yaba da bayanin da yayi mana, yarinyar ta
fito daga babban gida. Ina fatan za'a karbi
kokon barar mu?
Go to Home
BAKIN CIKI 1***3 Uban dawaki yayi jim, shiru
yana tunanin me zaice da manyan bakinsa da
suka wanko kafa takanas takano suka zo da
babban alkhairi gidansa? Girma da kwarjinin
Marafa sun cika masu ido, har ya rika ji ckn
zuciyarsa bazai iya kabar da kokon bararsu ba.
Amma abin tambayar shine, ina burinsa na
tuntuni da ya kwallafa akan mama? Tun tana ckn
zanin goynta? Muryar ambasada yaji yana fadin,
"nasa daliln shirunka alh., Al'ameen yayi min
bayanin komai game da burinka na sakeena tayi
zurfin karatu. Wannan kuduri ne mai kyau, kuma
ni kaina ina sha'awar hakan. To amma ina son in
tunasar da kai cewar aure baya hana ilimi. Ina
roknka da ka tausayawa halin da al'ameen ya
shiga na fadawa tarkon son sakeena. Shi kadai
gareni alh, kuma daidai gwargwado soyayyar da
na nuna masa bata gurbata tarbiyyarsa ba. Yaro
ne mai ladabi da biyayya ga kowa, tare da
tsananin bin dukkan abnda muka umarce shi.
Dalilin da yasa kenan nima nake tsananin son
abnda yake so. Bana sanya wajen taimaka masa
da addu'a, a duk lokacn da ya tsinci kansa cikn
wata matsala kamar ynda na lura ya shiga wani
hali daga jiya zuwa yau da muka baro shi. Babu
sukuni a zuciyarsa, alh. Ka taimaka ka amince
wa al'ameen auren sakeena da zarar ta kammala
sakandare, karatu kuwa ko wane iri ne, ko a ina
ne sakeena zata yi shi da yardar Allah" Wannan
dogon bayani na marafa ya kwabe wa uban
dawaki guiwa, zcyrsa tayi rauni, ba zai iya ja da
nufin Allah ba. Ya gyara zama sosai yace, "ba
shakka naji duk abnda kuka fadi, kuma nayi
farin ciki kwarai da gaske, sbd haka na amsa
kiranku, duk da cewar ya kamata in shawarci
sauran 'yan uwana, amma babu komai zan yi
musu bayana idan muka zauna. Al'ameen ya ci
gaba da neman sakeena, Allah ya tabbatar mana
da alkhairi" Kawai gani yayi marafa ya daga
hannu sama yana fadin, "Alhamdu lillah!" ya
maimaita har sau uku, sannan ya dubi uban
dawaki, "bansan kalmar da zan fada ba alh......."
yayi murmushi, "ai ka fadi alh., tnda kayi godiya
ga Allah". Ya jinjina kai, "haka ne, to mun kara
godiya gareka Allah, ka nuna mana lokacin" duk
suka amsa da amin. Alh. Nuhu ya zarce da fadin,
"yanzu dame-dame ake bukata na gaisuwa da
baiko?" yace, "kar ku damu da wannan, da zarar
mun zauna da 'yan uwana zaku ji bayani insha
Allahu". "to babu laifi, muna saurare. Ina
sakeenar take? A kira min ita mu gaisa, don in
cika alkawarin da na dauko......" "alkawari?"
"kwarai kuwa, har mota ya biyoni yana fadin,
don Allah daddy in kunje ku isar da gaisuwata ga
sakeena, koda mahaifnta bai amince min
auranta ba. To kaji, dole in cika wannan
alkawari. A kira min ita inga farin cikn
al'ameen" Farin ciki ya lullube uban dawaki,
bakinsa har kunne ya mike, "Allah sarki, to tana
zuwa". Yayi ckn gida da hanzari ya sami Hajiya
Halima, "ina mama? Ashe bakin nata ne" tare da
mamaki ta tambaya, "bakinta? Kamar yaya?"
"zan miki bayani, je kice ta shiryo tsaf ta sameni
falon baki". Ya juya ya koma. Ita kuma dakin
mama ta wuce, gaban madubi ta sameta zaune
tana shafe-shafe, fitowarta kenan daga wanka.
Ta matsa gareta tace, "dama kinsan da zuwan
wasu baki gunki?" "baki?" ta kada kai, "daga ina
umma?" "ni zaki tambaya? To kiyi maza suna
falon baki inji abbanki". Ta juya ckn juyayi ta
fice. Mama kuwa kasake tayi tana tunani,
"baki?" Al'ameen ya fado mata a rai, nan da nan
farin ciki ya rufeta, ta mike da gudu ta nufi
dirowar kaynta, ta zuba ado ta rufa mayafi, ta
fito ta doshi falon baki gabanta na harbawa,
amma zuciyarta fara sol! Duk da cewar bata
tabbatar da hukuncin da abbanta ya yanke ba.
Sai dai tana da yakinin akwai alamun nasara,
tnda aka ce taje da gaishe su . Tayi sallama ckn
kunya ta shiga, ta sami wuri gefe ta tankwashe
kafa, "sannunku da zuwa". Kai bakin marafa da
kaninsa kamar gonar auduga, su kansu mama ta
girgiza su, sun tabbatar da al'ameen ya darzo,
fatan da suke yi Ubangiji yasa kyanta har ckn
zuciyarta yake. Cikin ladabi da tsananin kunya ta
gaishesu, su kuma suka amsa ckn farin ciki da
nuna kauna a zahiri. Marafa ya taso yazo
gabanta, ya tsuguna yace, "al'ameen ya zabe ki,
nima haka. Sbd haka sai ku rike juna amana.
Har Allah ya nuna mana lokacin da muke dakon
zuwansa, kin ji?". Ta kara yin kasa da kai,
sannan ta amsa da kai. Yace, "madalla, to mun
gode". Yasa hannu a aljihu ya zaro sababbin
bandir 'yan wazobia ya aje a gabnta, "wannan
kyauta ce don nuna farin cikina gare ki, sbd
zabar dana ya zama mijinki". Kunya kamar ta
nutse, da kyar ta iya fadin, "na gode. Allah ya
saka da alkhairi". Yace, "to me zan ce wa
al'ameen idan mun koma?". Ta yunkura a guje ta
bar falon, suna mata dariya. Shi kansa Uban
dawaki yana mamakin kansa, irin farn ckn da ya
tsinci kansa. Alh. Saifullahi ya mike, "to bari
muyi harama, mun gode kwarai, Allah ya
tabbatar mana da alkhairi". Suka yi musabaha,
uban dawaki na fadin, "amin". Yayi musu rakiya,
sai da yaga tashnsu sannan ya shigo gida.
"Saboda Allah mama haka kuka yi da abbanki?"
ummanta ke tambaya, ta kada kai, "wlh umma
ba laifina bane. Babu abnda ban gaya masa ba,
yaki yarda. Kinga wannan turowar ma ni bansan
da ita ba, kawai ce min yayi shi yasan ynda zai
bullowa al'amarin, don haka in sa masa ido".
Tace, "ke din ma kina sonsa ne, ai nasan halinki
sarai mama, ba don haka ba ko kallo bai isheki
ba. Kin bani mamaki wlh, watau shi yasa jiya
kika ce minna zaki hutu, ashe da manufarki....."
Abbanta ya cafe, "tabbas haka ne....." ya karaso
ciki ya zauna, yana dubanta yaynda gabanta ke
ci gaba da harbawa da sauri. "ya aka yi haka
mama na? Ki turo min babban mutum irin
marafa, bayan kisan zai yi wuya ince a'a ko?".
Hankalnta ya kara tashi, ido tam da hawaye
tace, "wlh abba ba haka bane, hasali ma ni
bansan shine mahaifnsa ba, domin ni bai gaya
min ba, ka yarda dani abba, don bani da nufin
saba maka. Duk hukuncn da ka yanke akan
wannan al'amarin bazan bijire ba". Tasa hannu
ta goge kwallan da suka zubo bisa kuncnta.
Yace, "matso nan mamana". Da rarrafe ta isa
gunsa, ya kamo kafadarta yace, "dubeni nan". Ta
dago manyan idanuwnta da suka fara jirkita ta
kalle shi, "na yarda da ke dari-bisa-dari
mamana, sai dai abnda nake hangowa watakila
ke ba zaki hango shi ba. Bayn aure mata sukan
fuskanci 'yan matsaloli musamman idan Allah
ya kawo rabo ckn gaggawa, wanda idan ba ayi
sa'a ba sai ya jawo koma baya ga komai nata,
ba ma karatu ba kadai. Amma bazan matsa ba
mamana, ya kasance nayi jayayya da shirn
Allah, don haka ina muku fatan alkhairi". Ta rufe
fuska da tafin hannunta, fuskarta na bayyanar da
murmushi. Jiknsa ta langwabe, dadi kamar ya
kasheta. Yace, "ho 'yar nema! Watau kice kina
son al'ameen ko?". Ta tashi a guje ta bar musu
dakin. Uban Dwk ya numfasa sannan ya dubi
Umma to ya kika ce? Kinga dai yanda al'amarin
ya kasance. Fuska sake tace yaya kuwa za'ayi
Alh? Tunda ka amince ai shikenan Allah yasa
hakan shine mafi alkhairi, yace Ameen. Baki ma
sani ba wai shima likita ne mun fito ina musu
rakiya shi baban nasa ke gaya min. Nace itama
abnd take son ta karanta din kenan. A hakikanin
gsky ya tabbatar min babu damuwa I.S.A zataci
gaba da karatunta, kinji inda muka tsaya dasu.
Sauran maganar gaisuwa da baiko nace su bari
mu zauna da yan'uwana. Ta numfasa gsky ne
hakan kuma yayi kyau saidai kana ganin bazasy
dora wani abu a zukatansu ba? Kasan fa su Ali
sun so ta ka hana kace karatu zatayi. Yayi dan
shiru jim, kafin yace kinyi magana amma ba
komai nina san bayanin da zanyi musu. Tace
shikenan sun dan jima suna maida zancen.
Mama kuwa tana dakinta rayuwa ta zame mata
sabuwa. Duk. Inda tajefa ido Al-Ameen din take
gani kwarjininsa murmushinsa salon maganarsa
da taushin murya mai dadi. Bayan sallar la'asar
lokaci ne da kannen Uban dwk ke dawowa daga
gonakinsu. Yaran nata daukar darasin
Muhammadiyya kamar kullum. Uban Dwk ya tara
kannensa a falonsa ya zayyane musu komai
game da abnd ya faru, nan taje ransu ya sosu ba
kadan ba kallon juna suke cikin al'ajabi suna
tambayar zukatansu. Ina karatun da akace
Mama zatayi? Ya kara gyara zama yace nasan
zakuyi wa zukatanku wann tambayoyu a game da
magana ta, sbd Aliyu da Sa'aeed dama sauran
samarin da suka yo caa akan Mama, suna neman
aurenta amma na hana, sbd dalilin zurfin
karatunta. Wannan magana wllh haka take cikin
zuciyata kuma shine buri na saidai marafan lafai
ya cika min ido kwarai da gaske, banjin kuma
zaku goyi bayan na bada masa kasa a ido ba,
alhalin da kansa yayi tattaki neman alfarmar da
bata fi karfina ba. Abnd nakeso in rokeku shine
donAllah don son Manzon Allah SAW kuyi min
uziri akan wann hukunci dana yanke karku zargi
komai sai alkhairi, ina fatan zaku bani hadin kai
dari bisa dari. Alh Basiru mahaifin su Aliyu kuma
yafi kowa yaya a gidan ya gyara zama yace Alh
ai wann al'amari na Allah ne kuma abin
alfaharinmu ne ace Mama ta sami cigaba domin
cigaba ne samun irin wann hamshakin zuriya ta
marafan lafai. Mama yar mu ce kuma muna farin
ciki tare da fatan Allah ya tabbatar da wann abu
kome kace Adamu? Alh Adamu karamin cikinsu
ubansu Sa'eed yace wann magana haka take Alh
mu munsan cewa Mama bazata auri kowa ba sai
wanda Allah yace shine mijinta sbd haka muna
murnar samun wann babban rabo daga Allah.
Cikin jin dadi Uban Dwk ke magana "godiya ta
tabbata ga Allah da yasa na sami hadin kanku
cikin sauki nayi godiya sosai, abu na gaba shine
sunyi maganar gaisuwa da baiko nace su dan
saurara min muyi shawara da yan'uwana. Me
zaku ce akai? Alh Basiru yace hakan shi ma yayi
kyau sai ta gama sakandiran ne ko kuwa yanzu
suke so? Yace a'a sai ta gama tukunna. Idan
haka ne zaifi kyau a bari ta gama din sai ayi
baiko a sa rana ko kuwa? Alh Adamu yace haka
yayi daidai. Allah ya nuna mana lokacin lfy.
Kowa ya amsa da ameen. Uban dwk ya shaida
musu kyautar kudin da Marafan yayiwa Mama na
tsabar kudi naira dubu hamsin. Aha! Gsky ta
bayyana abnd Uban Dwk yake so kenan ruwan
kudi. Haka zuciyoyinsu suka saka musu, ya
fiddo kudi ya nuna musu kafin yace saidai
maganata gsky wann kudi ko sisi bazan taba a
cikinsu ba zanci gaba da ajiyarsu cikin banki da
dukkan wata kyauta dazata zo daga baya har sai
wann abu ya tabbara iidan kuma an sami akasi
ba fata muke ba sai a mayar musu kayansu. Ko
yaya kuka gani? Sasan alh. Basiru suka tasu da
matansu suka kwnce musu abnda ya wakana a
falon uban dawaki. H. Hajo matar alh. Basiru ita
ta fara tsoma baki, "amma kuwa idan baka mutu
ba zaka ga abin mamaki kala-kala. Ynzu da
gske alh. Babba ne ya iya tararku da wannan
maganar? Ko ya mance abnda yayi a kan su ali
ne?" Alh. Adamu yace, "ya manta? Babu abnda
ya manta. Hasali ma sai da ya kara maimaita
zancn su". "tafdi!" inji h. Gaje, matar alh.
Adamu. "kai dai kaga dan-uwa kawai, ai dama
tun farko na fada, ba wani karatn da ake so tayi,
burnsu mai kudi ko basarake, sbd su ganin
mama tafi kowa kyau a duniya. Shi yasa suka
dauketa a matsayn wani jari gare su. Ai
shikenan, Allah ya bamu lfya. Muma namu
'ya'yan bamu fidda ran Allah zai azurta su ba.
Ba Dai kowannensu ya kama aiki ba? To muje
zuwa wai mahaukaci ya hau kura. Harda wani
za'a tara kudi a banki, don kawai kar ya baku
wani abu ne a ciki, shine yake muku 'yan
dabaru" "ni dama bance a bani ba, me zanci da
su?" inji alh. Basiru. Alh. Adamu yace, "balle
kuma ni, ai tuni na haramtawa kaina komai na
alh, tnda ya nuna mana kiyayya a fili". Ya tashi
yayi waje, alh. Basiru yabi baynsa. Yaynda h.
Gaje ke fadin, "sai musa ido mu gani, da wane
bakin h. Halima zata gaya mana zancan". H.
Hajo tace, "kema dai da son jin baki kike. Tnda
mijnta ya furta, ai ba sai ta maimaita ba, tana
nan tasa ido muje mata murna 'yarta tayi farin
jin". Tayi 'yar shewa, "Allah mai iko, kiri-kiri an
raina mana wayau?". H. Hajo ta ja tsaki,
"mtsww! Kina mamaki kenan, dama kin daina
wlh, domin an jima ana ruwa kasa na shnyewa.
Ba girin-girin ba dai, tayi mai. Ba auran gidan
kudin ba, kwancyar hnkali!" Tana rufe baki tare
da sallamar umma, suka amsa suna wani yatsina
suna yarfarwa. Ta zauna tana fadin, "na shiga
sasanki yara suka ce kina nan" "uhm! Ina nan"
"dama maganar 'yarku ce, ban sani ba ko su alh.
Sun gaya muku halin da ake ciki?". H. Hajo tace,
"sun gaya mana, yanzu haka ma shirn zuwa
sasan naki muke, sai kuma gaki. Ashe kuma
mama an fasa karatu aure za'ayi?" Tace, "to
yaya zamu yi, mutane sun cikawa alh. ido,
sannan da alama ita ma maman tana son yaron.
'ya mace kuwa idan ta nuna tana son aure, to yi
mata auran shine mafi alkhairi ga iyaynta". H.
Gaje tace, "gaskya kuwa,