Showing 54001 words to 57000 words out of 110841 words
kara daga musu
hankali babu kamar Marafa da ko alama baya
kaunar yaga dansa na kukan neman wani abu,
shi yasa nan take ya ji ko ana ba maza ha mata,
sai Al-ameen ya auri mama. Amma ita Mami
bata an ta dosa ba, don haka tace. Al-ameen
bania ron hankalin kanan, na ga alama baka
yarda Sakeena lfy lau take ba.... Ku kuka gaya
min ai Mami... Yanxun kuma ni na gaya maka
lfya, kawai cin amanar ka tayi, tunda kaje bata
saurare ka ba, kai ma ka manta da ita kawai, ka
roki Allah ya musanya maka da mafi alkahiri.
Bafa sakeena kadai ce ta yalwatu da dukkan
abubuwan da kake so ba. Saboda haka ka kama
kanka, ka nutsu ka gane cewa ko an daura
auran, ba zaku zauna lfya ba, tunda idon ta ya
bude, tana takamar tana da kyau, kowa na
kallonta, kajini? Ya girgiza kai, idonsa xuru yana
kallonta, tace au baka ji ni ba? Menene nufinka?
Marafa ya amshe don Allah, don Annabi ki kyale
shi, ba yace Uban dawaki na taf ba? Allah ya
kaimu goben lfya, shi aure ai nufi ne na Allah.
Yanun kaje ka kwanta mu saurari goben, kaji?
Yace naji dady, don Allah ku tayni da addu'a
sakeena kadai nake so. Yace na sani, addua
kuwa kullum munayi, kayi alwala ka sami koda
raka'a 2 ne kafin ka kwanta, na tabbata zaka
sami nutsuwa ok? Ya amsa da kai ya dan
bubbuga kafadarsa yace, yau dan Dady, Allah ya
bamu alkhairi. Bai dai tanka ba, ya mike ya bar
falon. Mami ta cire tagumi tace, sai Allah yayi
wa yaron nan sakayya! Yadda tai masa haka
Allah zai mata. In banda idon Al-ameen ya rufe a
kanta, me zaici da ita? Yarinyar da gwaggo tace
shagon saurayi take su raba dare suna.... Marafa
ya katse ta, don son Annabi, ki bar wannan
magana haba. Ki yi masa fatan alkkhairi kawai.
Cikin bacin rai ta mike ta koma daki. BAKIN
CIKI kamar ya kasheta. Shi kuwa Al-ameen yana
can yana nafilfili kamar yadda dadinsa ya
umarce shi. Da safe ya fito gaba daya ya zabge,
kallo daya za kai masa ka tabbatar da hakan.
Gaban mami ya fadi ta kwala wa Ladi kira ta zo
a gigice. Tace, to hajiya. Ta juya da sauri ta fice.
Mami ta dube shi tace, matso nan kusa da ni. Ya
kara matsowa yace, ina kwana? Ta amsa tana
shafar kansa. Ina dadina, bai tashi bane? Tace,
kwana yayi baiyi barci ba, sai bayan sallahr
asuba barcin ya sace shi. Tana rufe baki ladi na
sallama da tiran abinci ta dire gabansu. Tace ga
shi hajiya dr, Iya tace in gaida ka, yanxun xata
shigo. Yace ina amsawa. Ta fita ta bar dakin.
Mami ta jawo tiren ta hada masu shayi ta mika
masa, ungo nan dan iya. Daute ka sha kaji karfin
jikinka. Ya sanya kofi a baki ya kurba kadan.
Wlh daci mami ba xan iya sha ba. Tace don me?
Ka cigaba da sha za kaji bakin ya washe. Ga
kuma farfesun, bude bakin in xuba maka. Ya
bude 'yar kular ta debo a cokali ta mika masa,
karbi ka gani mana. Ya bude bakin ta xuba masa
tace, yauwa ko kai fah? Yanxun idan Abba ya zo
maganar auranta kankama, haka za'a ga ango a
rame? Dadi ya lullubeshi yayi wani lallausan
murmushi yace, mami na rame ko? Kai baka ji
ajikin ka ba? Bana so kayi angwanci a rame, don
haka ma za ka kama abinci ka ci. Nan da nan ta
ga ya gyara zama ya hau shan farfesu yana
kurban shayi, kinsan wani abu Mami? Sai ka
fadi, shayin nan ya daian min daci. To yi sauri
ka shannye. Ya kuraba ya sake kallonta, yanxu
Mami idan aka daura auran anan xan barta? Eh
mana, ko ba xan iya kula da ita bane? Yayi dan
murmushi, a'a mami na, amma ni na fison mu
tafi tare can, kin ga kafin mu dawo ta mance da
sakaran Yaron da ya hure mata kunne. Ko ma
muyi xaman mu can tana karatunta ina aiki na,
ko kuwa? Ta dafa kafadarsa, gaskiyya ne, ina
goyan bayanka, sai dai in ta haihu ka kawo min
maigida ko kishiya. Ya kyalkyale da dariya,
kwalla suka cika idanuwan mami ta bisi da kallo
tana gyada kai. Yayi gyatsa kafin yace, ina son
twins mami, ko? Sai dai an mai son su baya
samun su? Da sauki ya katse ta, no duk canfi ne
Mami, ni dai ina so kuma Allah xai bani ameer
da ameera. Tayi 'yar dariya tace, duk naji, idan
ma 'yan hudu ne Allah ya kawo masu albarka,
yanxun tunda ka koshi, kaje ka yi wanka kafin
dadin ka ya tashi. Xai ji dadi idan ya ga ango
shar! Yace haka ne mamina. Ina xuwa, ya tashi
da sauri ya fice. Mami ta ta tallafe kunci ta ce
nikam tawa.... Nikam tawa ta sameni, ni Ya su,
Allah ka duba mana. A bakin kofa suka hadu da
iya suka gaisa. Sannan ya wuce bangarens, ya
fada bayi ya sheko wanka, ya kimtsa jikinsa da
wani lafiyayyen farin boyel mai taushin gaske.
Ya fesa turare, ya dawo dakin Mami, ita ma
wanka yi ta sauya kaya. Ta dube shi tana fara'a
tace, haba yanxu na ga daidai. Ina ganin ma dai
daga yau aka angwancin nan. Ya xauna kusa da
ita yana dariya. Tsokanata kike sonyi Mami, me
kika gani yanxun? Sai ma ranar kenan. Ki gane
Mamina, ranar ba zaki shaida ni ba. Ta ware ido
tana 'yar dariya zai hana? Sai dai ko amarya ta
kasa shaida kai, amma ina mami zata mance da
dan tilon dan ta. Dadi ya kara lullube shi, ya
rungumo ta yana fadin Allah sarki mamina, Allah
ya bar min ke tare da Dady na. Dadin ne kansa
ya amsa, amin amin. Ya kara sa shigowa suna
masuayar fara'a. Dadyna ya tashi lfya? Na tashi
lfy Doktna. Suka gaishe shi cikin annushuwa,
duk da bai san sirrin ba, xuciyarsa tayi masa
dadi. Don haka ya xauna aka kawo masa
abincinsa su ka fara ci tare suna kara kwantar
masa da hankalin. Sosai kuwa hankalinsa ya
kwanta, yana ganin tamkar an daura auransa da
mama, tunda yana da magoya baya ta kowanne
bangare
BAKIN CIKI 2***9 Abba bai ga ta zama ba, 7:30
suka kama hanyar minna shida Alh. Adamu tare
da Umma, domin ita tana bukatar ganin likita.
Saboda ha ane aka tafi da Inna saude don ta
rinka taimaka mata. Basu iske abdulkareem a
gida ba, ya riga ya fita aiki. Hankalin Aunty Rabi
ya dugunxuma nan da nan ta dauki waya ta kita
wayar ofis dince, Yaya abdul yaji kamar zai
mutu, saboda tsabar bacin rai, amma ba yadda
zaiyi ya fito saboda tsarin aiki irin na banki.
Daga nana aunty amina ta kira, itama ta shaida
mata, kafin ayi haka labari ya gauraye ko'ina.
Asibiti suka fara aje Umma tare da inna saude.
Aunty Rabi itace jagora domin asibitin da banki
ke da reg da su ne. Daga can da Abba da alh.
Adamu suka dumfari gidan marafa. Da ganin su,
gaban Mami ya fadi, fara'ar karfin hali kawai
takeyi. Bayan su natsu a falo. Abba ya tambayi
marafa? Tace, ai kuwa yayi sammako ya tafi
Lafai, don shaidawa mutannan gida maganar
daurin auren, shi kuwa ango na san ya ma kai
zariya yanxun Insha Allahu. Kasan a can
yawancin abokansa suke saboda can yayi krt.
Ina fatan lfya? Ya sauke numfashi idanuwan sa
suka kara juyewa yace, babu lfya Hjya, Ki
Innalillahi Wa inna ilaihir raji'un! Alh. Adamu ya
gaya mata. Ya gayara xama, yace hajiya
wannnan al'amari babu dadin ji, a takaice dai
sakeena ta gudu tun jiya har yanxu ba mu san
inda take ba. Tsaye ta mike dafe da kirji, ta yi
me? Ta kame a hakan bata iya kara komai ba.
Abba yace, nayi iya yina Hajiya, amma mama ta
nuna min ta karfina, hanyar da zabarwa kanta ta
wuce da sani nan. Kuyi hkr hajiya, ni ban ma san
da kalmar da xan gaya maku ba. Ta koma a
hankali ta zauna cikin kasala tace, ai shikenan,
duk abinda Allah yayi daidai ne, mu mun hkr,
Allah ya musanya wa Al- ameen da mafi
alkhairi, sukayi ji. Shiru kafin Abba yace mu na
nan garin nasan har Alhji ya dawo. Itama hajiya
tana nan na kawo ta asibiti tun jiya ciwon ta ya
tashi abin sai yadda Allah yayi. Ta maida tagumi
tace, dole Umma tayi ciwo, ubangiji Allah ya
bata sauki ya kuma shirya mana zuri'a, suka
amsa amin. Suka mike sukayi mata sallama
suka tafi. Hawaye suka kubcewa mami, hannunta
a kunci tace, ta faru ta kare kowa sai ya hkr!
Tab, wannan yarinya ta daure min kai. Allah
kayiwa Al-ameen sakayya! Iya da ladi suka jiyo
hajiya na sambatu, suka fito suka taushi
xuciyarta, babu bata tym ta sa driver ya kaita
Lafai. Gado aka ba Umma, saboda yanayin jikin
nata, yana bukatar kulawar likita sosai domin
jininta ya hau, har ya haye yadda ko alama ba 'a
so. Anan su abba suka ci gaba da zama har
karfe 4. Yaya abdulkrm ya samu ya baro ofis.
Kai tsayr asibitin ya nufa a sukwane. Da ka dube
shi, kasan ransa a nbace yake, yana ganin
Umma kuma al'amarin ya kara gigita shi. Ya
dubi Abba ido jajur! Yace, yanxun wane mataki
aka dauka? Abba yace, ni na sallama mama,
tunda ta iya toazarta ni haka. Na kuma je gidan
su Al-ameen, matslar kawai ban same su bam
duk sun tafi raba goron gayyata, sai hajiya na
samu shaida mata. Alh. Adamu yace amma ni
ina ganin zai fi kyau abada cigiyar a gidajen
Radio da Tv. Abba ya amshe, da kudin wa?
Saceta akayi? Ba xan kara asara ba, yadda ta sa
kafa ta bar gidana, ta tozarta ni, ta wulaknata
ni, ta nuna min ban isa da ita ba. Wlh ni ma na
hkr da ita. Ba xan yi mata baki ba, dan ko bance
wani abu, tabbas ita da kanta ta kai kanta
mkrntar koyo hankali. Za ku ce na gaya maku.
Taje duniya cem ta ishi kowa riga da wando har
da mayafin yafawa. Ya abdulkrm ya numfasa,
yace ta yiwa knata, Allah ya shiryar da ita, yasa
ta gane, suka amsa da amin. Jimawa kadan ya
ba Aunty Rabi mukullin mota ta wuce dauko su
Ameera daga sch. Kai tsaye ta wuce da su gida.
Ta kama hidimar shirya abinci. Tana gamawa ta
kwashe gaba daya da yaran suka koma asibiti.
Ta iske kofar dkin da Umma take dankam! Da
Jam'a, ashe bayan tafiyarta kadan su ya Abdul
kadir da abdulrhmn suka iso. Can kuma sai ga
dady da mami. Al-ameen ne kadai bai dawo ba.
Duk tabisu ta gaida su. Dady kam yama rasa
yadda xai fassara al'amarin Allah ya sa bai riga
ya yayyada xancen ba ko 'ina, iyakar sa cikin
babban gidansu. Allah ya kawo Mami tayi masa
birki. Shi kansa yadda yakeji a tym din, idan
xa'a gwada jininsa dole ace ya hau, amma daya
iso ya dubi halin da iyayen Mama ke ciki sai
yaga ashe shi nafila ne, tashin hankali na inda
yake. Shi yasa ya nutsu sukayi magana ta
fahimta da abba...... Ya Dubi halin da Iyayen
Mama ke ciki sai ya ga ashe shi nafila ne, tashin
hankali na inda yake. Shi yasa ya nutsu sukayi
magana ta fahimta da Abba. Suka dauki komai
suka barwa Allah tare da rokon Abba daya
amince ya bawa mama wanda ta sake xaba.
Abba bai ce komai ba anan. Don baya jin zai iya
ba Danliti 'yarsa su hada zuri'a da mutuncin sa
da komai a gari. Yanxun tunaninsu dan gogan.
Yaya al'amarain zai kasance? Bayan abba ya
kauda masa duk wani shakku, ya bashi tabbacin
babu wani face shi, shi ya kara karfafa masa
gwiuwa har ya sami kafar tafiya gayyato abokan
taya shi murnar angwanci? Wannan amsa sai
wanda ya gani da idanuwansa. Gab! Da kiran
sallah magriba duk suka bar asibitin, aka bar
Inna saude ita kadai tare da Umman, wacce har
yanxun barci takeyi, domin allurar da akayi mata
mai karfi ce sosai, saboda ana son ta samu hutu
kwarai da gaske. Su dady na isa gida, kamar
tare suke da Al-ameen. Bai fhimci komai a
fuskokinsu ba, don basu yarda yaga sauyi ba ya
baje a kujera yace, wsh! Ai fah an fara kenanm
kinji yadda naga ji Mami? Ta danyi murmushi
tace, dan Iya kena, to abinda ya kamata ka
hanzarta yin wanke ne, don gab ake da kiran
magriba. Haka za'ayi Mami na, dadi ya aka baro
mutanan Lafai? Ina fatan zaka jaddada musu su
taso da wuri? Wannan ai dole ne, kama san
kawunka ba shi da wasa. Yana ta far'a gaskiyya
ne ni ma frnds dina ne ce masu kai tsaye su
wuce Fandagori, ai gidan Uban dawaki ba
boyayye bane, suna tambaya za'a nunna masu.
Dadi yace, kayi daidai, yanxun tashi ka shiga
wankan nnima shi xanyi aga wanda xai riga
fitowa cin abinci. Ya mike xumbur! Yana dariya
ni ne xan riga Dadi, to shikenan, mami ki na ji
ko? Idan kuma na riga shi bulala tara, tace ni
kuma xan cikashe dayar, su zama goma. Na
yada. Bai jira komai ba ya kwasa da gudu, ya
shige bangarensa. Mami ta bishi da kallo. Dadi
ya sa hannu ya cire mata tagumi yace, ke ma
tashi ki daina damuwa. Ta sauke numfashi,
amma ba tace komai ba, ta yunkura ya taimaka
mata ta tashi suka wuce. Kowa ya shige
dakinsa. Al- ameen ya fara fitowa falon, ya nufi
gefen tebur inda ya hangi ladi na jera abinci. Ya
isa wajen yana fadin, angaida Maman abinci.
Tayi dan murmushi. Tace ni ma na gaida dr.
Yace na kusa dina cin abincinki Ladi, ina ganin
daga yau nai masa bye bye. Tayi 'yar dariya, to
aci gaba ne dr. Amma ina ganin akwai gobe
kafin amaryar ta iso ko? Ya gyada kai, yana dan
murmushi, wa ya gaya miki xan dawo ni kadai?
Tana 'yar dariya ta amsa, au can xaka zauna?
Kafata, kafarta, zata sake magana, ya dakatar
da ita, shisshhh... Tayi tsit! Tana kallon sa yana
boyewa bayan kujeru. Dadi ya fito mami na biye
dashi, madalla, kinga bulala ta hau kan danki,
kira shi na tsatstsala masa. Tace, yanxunn nan
ma xaka ganshi a sukwane, kwai ganin sa sukayi
yana gyara xaman kujera xai xauna. Gaba daya
suka kwashe da dariya. Ladi na tasya su sannan
ta bar wajen. Dady yace, gaskiyya ba haka ake yi
ba, ai dai sai ya bari mu fito tare ko mami?
Dariyar Al-ameen ta karu, yayin da Mami ke
fadun, kaji wayau! Ta xuba wa kowa abinci yaci,
suka kashi suna ta biye masa, suna labarin biki.
Bukatarsu ya cika cikinsa, kuma ya ci sosai.
Bayan su kammala Dady ne ya fara barin tebur
din Al-ameen ya byi shi xasu yi wata magana,
nan da nan ya mike ya bi bayansa. Mami ta
kwala wa Ladi kira tace ta gyara kan tebur din,
ita ma kai tsaye ta wuce, ta iske su xaune bisa
kafet. Dayan gefen ta xauna, suka sanya shi
tsakiya. Dadi yayi gyarn murya yace, wasu 'yan
tamnbayoyi xan yi maka Al- ameen, ina fatan
xaka nutsu ka bani amsa shakikiya. Da farko dai
shin Al-ameen wa yake badawa, wa yake
hanawa? Yace, Allah. To idan ya baka, sannan
ya dawo ya karba, me yakamata kayi? Ya amsa,
nayi masa gdya, watakila ya musanya min da
alkhairi, ko Mami? Tace, Gaskiyya ne! Dadi
yace, Madalla, abinda nake ka sanya wa ranka
kenan. Idan har ka tabbata tsakanin ka da Allah
ka amsa min tambayoyi na. Ka kuma san imani
shine cikar dan musulmi, ko ba haka ba? A
salube yace, sosai dady. Yauwa, to kayi hkr
maganar da xan gaya maka. Nasan ka na son
sakeena, sannan kayi imani Allah ne ya hadu ku
ya sanya maka sonta, a da mu na ganin kamar
itama tana sonka, kamar yarda kake sonta.
Amma yanxun ta nuna yaudara ce kawai, saboda
haka ka hkr da ita. Kamar yadda kace Allah xai
musanya maka alkhairi. Ya dubi Mami, ya juya
ya dube shi, Dady ban fahimce ka ba, ai sakeena
na so na, xuga ce kawai kuma na tabbata da
xarar aka daura auranmu, ni masan yadda xan da
hankalinta gareni. Dady ya ka kada kai, maganar
ka dawo da hankalinta gareka duk ya kau. Al-
ameen sakeena ta gudu tun jiya babu wanda
yasan inda take saboda haka nake rokonka
arziki da ka kwantar da hankalinka, kayi imani
da furucin da kayi daxu, Allah ba xai bari kasha
wuya ba. Ya Dubi Mami fuska kunshe da tashin
hakali yace mami ban fahimci ta gudu ba? Me
dady yake nufi? Tace iyakar kiyayya sakeena ta
nuna maka, tunda ta xabi ta dauki akwatinta ta
bar gidan iyayen ta ada ace ta aure ka. Ta xabi
ta ci mutuncin mahaifanta akan auranka.
Wulakanci ya kai makura Al-ameen, ya kamata
ka nuna mana ka haihu dan halas, kace kai ma
ka hkr da sakeena. Ya xura mata ido, du sun
kadu, mami kina nufin an fasa daura auran
gobe? Tace abinda Abbanta yayi sammakon
xuwa shaida mana kenan, ia ske ba ku nan kun
riga kun tafi gayyata, ni na bi dadynka Lafai na
dakatar da shi. Kai ma ina so ka dauki waya ka
kira abokin ka dr. Lawal ka gaya masa an fasa,
don ya gaya wa saura kar su yi wahala. Ya kada
kai yace, baxan iya ba mami, na rantse da Allah
sakeena na so na, ina xata gudu taje? Ban yarda
ba mami sace min ita kayi, don a raba mu....
Rufe min baki! Mami ta daka masa tasawa mai
karfi, daga nan ta balle da masifa, kar ka yarda
Al-ameen, amma ina son ka sani, babu maganar
auranka gobe da sakeena! Idan kuma ka sake
tak a wurin nan sai na tsinka mata mari, don ka
gane ba wasa muke yi da kai ba! Yaya ana
rarrashinka ana numaka gaskiyyar magana ka
naso ka akrya ta mu? Sakeenar banxa sakeenan
wofi? Ita kadaice mace a duniya? In sake jin
xancen ta abakin ka sai na saba maka! Ku ma
ka sani, daga daren yau ka fara shiri gobe xuwa
jibi xaka koma sch! Kaji ko baka ji ni ba? Ya aje
kai kasa. Dadi yasa hannu ya dago fuskarsa.
Tuni hawaye suka wanke masa kunci, shi ya fara
fadin, me yasa zata gudu ta barni Dady? Ko
baxan hkr da ita ba, ai bai kamata ta gudu ba,
hatsari ne babba ga diya mace, wa ya san hannu
da take yanxun? Mami tayi caraf? Ta cafke, tana
hannun wanda take so. Dama ka daina bata
hawayenka a banxa. Sannan kama kunnunwanka
da kyau ka ji ni, tun daga ranar da ka daina jin
muryar sakeena awaya ta daina sonka, ta mance
da kai, ta share ka a rayuwarta. Saboda kin da
ta ke ma. Sakeena ta diro daga mota, da abin ya
zo da karar kwana da yanxun an kusa mata
sadakar arba'in. Sakeena tayi kwana da kwanaki
tana yajin cin abinci, tayi ta suma ana mata
karin ruwa a asibiti. Kai saboda kiyayyar ka,
gabada dabi'iun sakeena suka sauya, bata
gannin kowa da daraja, nballe ta saurari fada, da
iayeynta da 'yanuwanta ke mata ba dare ba rana.
A karshe sakeena ta aikata abinda yafi komi
muni akan diya mace. Duk saboda bata sonka,
ashe ya kamata ka hankalta kasan halin da kake
ciki, don kai ba yaro bane, kuma ba alfahari ba,
ilimi muhammadiya da boko sai dai a yiwa wani
gori ba dai kai ba Al-ameen, duk kuma wanda
yayi imani da kaddara, baya tabewa Al-ameen.
Ka maida al-amarin ka wajen Allah shi xai maka
magani. Ya dube su daidai tamkar karamin yaro,
murya na rawa yace, gaskiyya ne Mami, duk
abinda ki ka fadi na yarda, kuma na hkr da
sakeena, sai dai son ta ba xan iya cire shi cikin
raina ba, saboda ba ni na aje shi ba, kuyi hkr, ku
yafe ni, idan furuncin danayi ya muku xafi,
sannan ina rokon ku don Allah da son Manxonsa,
kar ku kullaci sakeena cikin xukatan