Showing 63001 words to 66000 words out of 110841 words

Chapter 22 - BAKIN CIKI BOOK COMPLETE BY ESHAT.txt

12 Sep 2025

75

bari,
kamar in kwanta inyi ta barci wlh. To ki kwanta
mana, ai ba kya jin yunwa ko kinaji? Ta kada
kai, banji, to ki kwnta ki huta ne, xuwa karfe
goma sai in tashe ki, ki koma gida. Haka za'ayi,
ta jawo filo ta yada kai, suna kallon juna suna
musayar murmushi. Ya lukuce mata hanci, yace
baby na kenan. Ta juya gefe tana 'ya dariya. Ya
mike ya dubi ayuba yace, to muje dogari. Ya
juya yana murmushi, ina tsarabata? Yace yauwa
ka tuna min, ya suri jakar leda suka fice da ita.
Ya xauna bisa kujera ayuba na kan tabarma, ya
zazzzage kayan kedar a gabansa. Gaba daya
kayan sawa ne. Na gayu ya siyo masa, ya dube
shi suka hada ido, yace ga tsarabar legos nan.
Baki sake yace babu wai, har ma ga tsaraba nan
duka naka ne. Ya washe baki m amma na gode,
watau shi ya sana kunyi jajur abinku, ashe kuna
bakin teku. Yace, hutu ba karya bane ayuba, ga
kuma lafiyayyar bebi na, nake gaya ma. Yayi
shiru yana kallon sa, fuskarsa gaba daya
tabayyana babu abinda bai faru ba. Ya numfas
duk jikinsa ya mutu yace, bakaji Danliti. Me nayi
ma tukunna? Ko kaji surutu ne a gari? Ya gyara
zama yace ba'a tonawa Danliti, abinda nake son
ka da shi, ku sasanta ka aureta kawai, ka ba
masu surutu kunya, donn sunce ba auranta
zakayi ba, tayi saki reshe ne, ta kama ganye, ya
shafa habarasa yace, ko? To ai ba suyi karya ba,
shagali kuma basu ga komai ba daga nan ma
illa masha Allah ba za mu daina ba. Ya kada kai
yace, meye nawa a ciki? Idan ka huta ko xuwa
gobe mayi lissafi. Yace ina fatan akwai kudi
sosai, don wanda na tafi da su naci uabansu, ya
amsa ciniki na na ba laifi, sati biyu ma da suka
wuce na je kno na karo kaya da cinikin yafi
haka. Da kyau mutumina, shi yasa nke sonka
wlh. Yayi 'yar dariya yana daga kayan da aka
kawo masa, ni kuma ina sonka da nutsuwa ba
amma kakiji. Ya mike ya nufi daki yana cewa,
kai ka fiye surutu, bari in baka wuri. Ya shige
dakin ya bar ayuba da kallonsa. Ya kada kai
yace aransa, Allah ka shiryemu. Shi kuwa Danliti
komawa yayi ya hana mama barcin. Karfe 10 ta
dan gota, dan liti ya umarci Mama da ta koma
gidan iyayenta, su san ta dawo, dan su san
matakin karshe da zau dauka. Watakila hakan su
ta cimma ruwa. Watau su amince da auransu
cewarsa madugu uban tafiyar. Ya hado mata
kayanta taf! Da katuwar jaka, tana xaune tana
kallonsa, kafin tace gaskiyya ba xan dauki jakar
nan ba, guda uku kawai dauka cikin kit, in tafi
dasu. Ido waje ya tambaya, sabda me? Ka sani
ko su koroni? Ka bari tukunna mu gani, idan
suka kyale ni, sai in dawo in kwashe sauran.
Idan basu kyaleki ba fah? Sai na dawo nan ka
yanke hukunci duk da zaka yanke. Ya xura mata
do, ai iyayenki na san ba su ki karbarki ba,
hasalima ai laifin su ne, na tabbata yanxun sun
gane kuskurensu, dole su lallabaki. Ta doke
kafadarsa tana dariya, har ma kasan dole su
lallabani? Kai dai ka yi fatan su amince da
auranmu. Yace shikenan, yanxun ki dauki abinda
xaki dauka na rakaki, dare nakara yi. Ta bude kit
ta xuba kaya kala 3, yasa hannu ya dauko wata
'yar karamar doguwar riga yace..... Yace ba xaki
dauki wannan rigar ba? Tace wannan shegiyar
rigar? Shegiya? Lallai ba ki san yadda take mi ki
kyau bane, a'a ka dai barta anan, sanin kanka
ne, su Abba bna za su barni na sanya taba cikin
gidansu. An wuce wurin, ki barta kyasa a gidana.
Ta yada kai kan kafadarsa tace ashe ka gane. Ya
tsikare ta, ta mike xumbur! Ban fa so Danliti
banso! Ta figi kit dinta, tayi waje baki a ture. Ya
kwaso mata gyale da takalmi ya biyota yana
fadin sorry 'yar bebi na! Taja ta tsya tana
haraarsa, ya yafa mata gyalen, ya aje takalmin
gabanta ya jawo kafufuwanta, sa abinki mu tafi.
Ta xura kafar tace wa Ayuba, sai da safe. Yake
yayi ya amsa, Allah ya kaimu. Suka fice, Danliti
na cewa, har kin tabbatar da xamanki a gidan ne
kike ce masa sai da safe? Tace gane min hanya
wai, makaho ya so gulma. Ya ci gaba da dariya,
suna tafe suna hira. Gab da gidan, ya tsaya
sukayi sallama, idan kuma ya gan ta ta dawo
shikenan. Y koma ita kuma taci gaba da tafiya
hankalinta kwance yake, don bata saka komai
illa in su koroto, ta koma inda ta fito. Daga
bisani ma wata dabara ta fado mata. Tana
dosowa kofar gidan, ta hangi kamar ana hada
hadar jama'a, duk da dare ya fara yi, kana iya
gane wa ana sha'ani a gidan. Bata yi wa kowa
magana ba,a haka suma babu wanda ya
shaidata. Sai da ta shige xauran karshe ta aje kit
dinta, ta xauna akai ta hade kai da guiwa ta
kirkiro kukan dole ta shiga yinsa har da
shesheka, sannan hankulan masu wucewa ya
fara xuwa gunta kuma, Ya ali shine mutum na
farko daya fara dosar ta da tambaya, wai wacece
xaune? Gida kike son komawa? A zata son cikin
'yan kawo amare ne, yayi dan murmushi, don ta
bashi dariya. Da girmanki da komai kike
kauyanci? Dan Allah tashi ki koma cikin gida
tun kafain yara su fara miki dariya. Ko an yi miki
wani abu ne? Daga ji ta gane mai magana, shi
yasa ta dago sosai ta dube shi, kawai batare da
tayi magana ba. Gabansa ya tsinke ya fadi
xuciyarsa ke ambato sunan, mama? Sannan ya
tsugunna gabanta ya furta a hankali, mama!
Hawayenta suka kara tsunkewa, ta sadda kai,
tana gogewa da bayan hannu. Innalillahi wa Inna
illaihir raju'un! Ya waiwaiga babu mai kallonsa
yayi sauri ya ja mayafinta ya rufe fuskarta, yace,
taso muje, kar ki bari kowa ya ganki. Ya ja
hannunta suka sulale dakinsy Danlami. Babu
kowa cikinsa, duk suna can wajen fatin da
sukeyi da abokansa. Ya xaunar da ita gefen gado
ya tsugguna. Yace, yaushe kika dawo mama?
Baki na rawa ta amsa, yanxun, idanuwansa suka
kawo kwalla a raunane. Yace abinda kikayi kin
kyauta kenan mama? Da mtuncin ki da komai?
Iyayen mu masu girma da daraja a gurin jama'a,
kika tozarta su? Haba mama, kamar baki sami
tarbiya ba? Ta goge kwalla. Tace, ba haka bane,
Ya ali me yasa zaku rinka ganin laifi na ni
kadai? Nace ga wanda nake so, ba sai a ba ni
shi ba. Ina ruwan kowa da rashin asalinsa? Ai
dai ba daga sama ya fado ba, da uwarsa da
ubansa. Yace, Maganar banza ce wannan mama,
don na tabbata Daliti bai fi miki iyayenki ba. Kin
kuwa san halin da umma ke ciki tun ranar da
kika sa kafa kika bar gidan nan? Kin daure min
kai, ban taba xataon zaki aikata irin wanan
mummuna aiki ba. Tace hakan kadai xai memin
mafita kuma akan bakana na dawo ko Danliti, ko
su rasa ni baki daya. Ya xura mata ido, yana
kada kai. Afuwa ya kamata ki nema ku sulhunta
da iyayenki, su sa miki albarka, ko kin ga
rayuwa mai kyau da anfani nan gaba. Saboda
haka ki xauna anan ki jirani, xan shiga wajensu
in kwantar musu da hankali tukina, gaskiyya
bana so ayi miki taratsi cikin jama'a, kuma
gidan cike yake da baki. Baki? Me akeyi a
gidan? Ya amsa, biki na akeyi dana seed. Kana
nufin kunyi aure? To Ya xanyi, tunda kinki ni
Mama? Akan dole na yi auaran nan, su Baba sun
matsa min. Ina muku murna, nima Allah yasa ni
a danshinku. Ya xura mata ido gwanin tausayi.
Yace, nasan ba xaki ji komai a ranki ba, tunda
ba so na kike ba, amma ni har kwanan gobe ina
sonki, shi ya sa abinda ke faruwa da ke ya xame
min ciwon cikin raina, ki yiwa girman Allah
mama ki sanya tunanin ki dawo sak! Yadda
kowa ya sanki. Karka damu dani Ya Ali, ko da
yaushe ina gaya ma kai dan uwana ne, kauanar
mu ta jini ce mai asali. Kwanciyar hnakalina
kuwa Danliti ya zama mijina. Ina fatan iyayen
Al-ameen sunyi xuciya su fasa? Ko baka ji
komai akai ba? Ya xuba mata ido yana
mamakinta, ya jima bai amsa ba, kafin yace, Al-
ameen ya koma Rasha da ciwon xuciya Mama.....
Ta katse shi ido rufe ta dafe kirji. Tace, nagode
Allah! Har naji sanyi cikin raina. Ya kada kai
yana kallonta. Yace, baki masa adalci ba, baki
tsoron amanarsa ta ciki? Akan me? Bafa dole
bane na aure shi, ina son kowa ya gane wannan,
kawai kaje ka gaya masu na dawo din, kaji me
xasu ce? Yace ni ne nayi niyyar yin hakan, ba
sai kin bani umarni ba. Yi hkr Yaya, bai tanka
ba, ya tashi ya five, ta bi bayansa da kallo tana
fadin cikin ranta, je ka dawo, duk na kosa in san
babin da nake. Cikin dakin yayi sallama, abba
ya amsa masa yana kokarin hadawa Umma shayi
ta samu ta dan sha, ya akayi Ali? Ya xauna gefe
kusa da shi, yace babu komai abba, wata
alfarma naxo nema wajenku. Hankalin abba ya
dawo gare shi, yace ina jinka. Allah ya sa batafi
karfi na ba. Ya kada kai ya amsa, bata fi ba
Abba, duk mai laifi idan ya nemi afuwa, me
yakamata ayi masa? Ya dube shi da kyau da
mamaki yace, ayi masa afuwar, domin Allah
yana son masu yafiya ga bayinsa. Su kuma masu
laifin su yi alakwarin ba xasu sake komawa ga
wancanm laifin ba. Laifin me kayi? Ya amsa,
laifin mai girma ne Abba, a misali Mama ta
dawo ta nemi gafara, abba xa ka karbi tubanta?
Ba abba kadai ba harda Umma dake kwance ta
xubo masa ido, abba ya jima kafin ya numfasa.
Yace Bansan dalilin da yasa ka min tambayar
nan ba, amma ina so ka sani, mama ta aikata
laifi mafi muni a shafin tarihin gidan nan, da mu
karbeta da kar mu karbeta, bakin fentin da ta
shafa mana yana nan baxai goge ba, ina so ka
sani Ali, xaiyi wuya a fadin gari na Mama ta
sami wani mijin, face katon daya dauke ta ya
boye wani wuri tsowon watanni 3. Abu na karshe
da nake so ka snai, shine bai kai kadai ka rokeni
ba. Al-ameen ma ya rokar mata gafara kuma
nayi masa tare da alakwarin ba xanki karbarta
ba. Saboda haka ka kwantar da hankalinka,
muddin Mamma ta dawo gidan nan, ba xan ce ta
koma ba, haka xalika idan bata sauya ra'ayinta
ba, ba xan ce mata a'a ba, Allah na kallo, nayi
kokarin na, don nuna mata hanyar kwarai da
samun abokin zama na kirki mai kyan asali. Ko
duniya ta zageni, alhakin Na suka duka kuma
zamuyi shari'a da su gobe kiyama. Kawai ji yayi
kwallah na xubo masa, saboda tausayin Abba,
yasa hannu ya goge, abba ya riga shi sake
magana, ka daina kuka Ali, kaddara ce, tashin
hankalina daya, mahaifiyarta da ta kasa samun
nutsuwa. Ina jin tsoron kar ciwon xuciya ya
kamata kamar yadda likitocin da ke duba ta
suke gargadin ta kullum. Dalilin da yasa kenan
nake fatan Allah ya sa mama ta dawo, watakila
ya zama waraka ga mahaifiyarta. Na tabbata
hankalinta xaifi kwanciya idan tana ganin ta
koda a dakin auran Danliti ne. Ya Ali ya gyara
xama yace, gaskiyya ne abba, kuma naji dadin
bayanan ka. Saboda haka ina mai farin cikin
shaida maku cewar mama na nan ta dawo. Abba
ya xura masa ido. Umma kuwa ciccibawa tayi ta
tashi xaune. Ba fahimce ka ba Ali? Inji Abba,
yace Mama na nan a cikin gidan nan, idan kun
ban izini, zan shigo da ita ta roki gafararku.
Suka dubi juna shi da Umma baki sake, tuni
hawaye suka tsinke mata, tana kada kai tare da
salatin Manzo. Abba ya dube shi yace, je ka
ashigo da ita Ali. Har ya mike ya sake komawa
ya xauana, yace Abba ina fatan ba xaku daga
mata murya ba, kasan gidan na cike yake da
baki. Yace Insha Allahu, ba xan daga mata ba.
Yace nagde abba. Ya mike ya wuce, abba ya
bishi da kallon, sannan ya dubi Umma, ashe
haka Ali ke da hankali? Nayi kuskuran hana
masa auran Mama tunda farko. Umma ta goge
hwaye tace, hakika mama tayi asara masoya 2.
Haka Allah ya so, ba mu da abinyi, dai yi masa
godiya, abba ya sauke numfashi, sukayi xugum
suna sauraron ta yadda mama xata bayyana
garesu. Jimawa kadan suka tsinkayi muryar Ya
Ali yana fadin ki shigo mana! Na gaya miki
komai ya wuce, ki shigo kawai. Make-maken
munafurci takeyi ba wai ainihin tsoron bane cikin
ranta, da su abba xa suyi kuskuran cewa ta juya,
fes! Zata juya babu waiwaye sukayi sallama
dakin. Ya ali na dauke da kit dinta. Ta toge
bakin kofa, yasa hannun ya janyo ta har
gabansu abba dake sake da baki suna kallon
abin al-ajabi. Gata abba, umma ga Mama, ku
mance da abinda ya faru, ku amince da xabanta,
ku sa musu albarka, sai kuka ga Allah ya basu
zuri'a abin alfahari. Mama ki durkusa ki roke su
gafara. Ko dama a durkushen take kuma tuni
hawayen suka tsunke mata, murya na rawa,
tace..
BAKIN CIKI 2***12 Abba kuyi hrk, Umma ki yafe
min. Abba ya numfasa yana kada kai. Ya ce a
rayuwata gaba daya Mama ba tba xataon xaki
min irin wannan mugun butulcin ba. Na dauke ki
'yar da na dauki burin duniya na dora a kanki.
Kece kika bambamta da kowa cikin xuciyata,
kuma na nuna miki dukkan gata amma dare
daya, kika numa mana akwai wanda ya fi mu
muhimmaci a rayuwarki. Tabbas na yarda da
hakan, don a tunani na xan ga kin dawo kin
bushe a lalace saboda tunanin kin barmu cin
BAKIN CIKI sai gaki Fes! Kinyi kiba. Ban miki
baki ba, ba kuma xan miki ba, amma ina mai
tabbatar miki in rasa masoyi, kin rasa mai
tsanin kaunar ki tsakani da Allah, kuma a yau na
kara nadamar hana Ali auaranki tun farko.
Maganata karshe itace, tunda kin nace sai
Danliti to ki gaya masa ya turo magabatansa,
muyi magana, sannan kiyi wa Yayanki Ali
godiya, domin yayi miki dukkan taimako.
Zaciyarta fara sol! Jin Abba ya ambato Danliti ya
turo. Ta kara dukawa tana goge kwalla. Tace,
ngde abba, kuma ina kara baku hkr, don Allah
ku yafe min. Ta rarrafa gun Umma ta cusa kanta
jikinta, umma kiyi hkr! Ta share hwaye tace ai ya
wuce Mama, kinci albarkacin al-ameen da ali.
Amma gyara kayanka, ai baya zama sauke mu
raba ba. Ki bi duniya a sannu, domin ita duniya
budurwa ce mai kyale-kyale da yawa, da zarar ka
biye mata, to ka bace ka kuma shiga uku ka
lalace. Ban da abin kari a gareki, don nasiha
anyi miki, amma kin rushe saboda batan basira.
Allah ya ganar da ke, ya sa ki a hanya
madaidaiciya. Ya ali ya amsa da amin, yayin da
mama ke ci gaba da gugar hawaye. Alin ne ya
cigaba da cewa, don Allah abba karku nuna
kowa ta dawo har tym din bakin nan xasu koma.
Ko su Baba a kyale su tukuna. Ke mama ina son
ki cigaba da xama cikin dakinku dan Allah, na
san xuwa gobe da yamma kowa xai watse, sai a
kam magana ta gaba, kinji? Ta amsa da kai,
Abba yace shikenan Ali, kana son ka rufawa 'yar
uwarka asiri, asirin kuwa da ya riga ya tonu.
Yace kayi hkr dai abba, yace babu komai, ta
tashi ta koma dakinta, idan tana jin yunwa,
akwai abinci, yace xaki ci abinci ne? Ta kada
kai, to taso na raka ki dakinki. Umma mun gode,
tace Allah yayi albarka, ya amsa da amin. Tare
suka mike suka bar dakin. Umma ta tafa hannu
tana salati, sannan ta buga tagumi. Yanxun alh.
Danliti xata aura? Yace, t ya xamuyi, wa kike
ganin xai fito neman auranta, bayan ya san
wannan kwamacala? Haka nan xamu hkr da
abinda Allah ya kaddaro, yanxun dai bana ce ya
turo ba? Sai mu sa ido mu ga wadanda xai turo
din. Ta numfasa, tace Allah shi kyauta yace
amin. Ke dai ki kwantar da hankalinki, ki daina
xa damuwa a ranki don Allah. Tace naji alh. Ya
ciga ba hada mata shayin suna tattaunawa.
Kamar yadda ake tattaunaea da mama da Ya Ali.
Shawarwari kawai yake bata, tana sauraronsa
kamar gaske. Har kusan sha daya da rabi suna
tare. Dagab bisani yayi mata sallama ya barya
cike da farin ciki da baya misaltuwa. Nan da nan
ta fada bayi tayi wanka, ta kintsa jikinta ta
kwanta. Kewar Danliti ta lullube ta, fadi take
cikin ranta, ba dan dare yayi ba da naje yiwa
sweety Na albishir. Da kyar barci ya sace ta
saboda murna. Washe gari hidima taci gaba,
mama na cikin dakin na kulle babu wanda ya
san ta dawo, daga Ya Ali sai su Umma. Kuma
anyi sa'a taji maganar Ya Ali batayi marmarin
fitowa ba, sai shi ne ma ya kan saci jiki ya
shiga wajenta, ya ganta yaji dan ji sanyi aransa.
Allah sarki! Garin dadi na newa, iska na ta
wahalar da mai kayan kara, bayan sallahr la'asar
baki suka koma muhallin su aka bar amare da
angwayensu. Shi kuwa Ubandawaki 'yan uwansa
ya tara falon baki yace, naki ku ne a matsayin
ku na kannena na in shaida muku cewar Mama
ta dawo daren jiya, kuma har na yanke hukuncin
ta gayawa Danlitin ya turo magabatansa, muyi
maganar aure. Ban san yadda zaku karbi abin
ba, ko da mahimmanci ko ya zama abin dariya a
gareku, duk daya ne, ni dai na fita hakkinku.
Suka dubi juna cikin sigar tsarguwa, sannan
Alh.basir yace, ai shikenan yaya, amma banji
dadin yadda kayi mana fassara ba, ya kamata
kayi mana uxuri tunda mun ce maganar nan
bada wata manufa muka fadeta ba. Amma ace
mama ta dawo tun jiya, sai yanxun mukeji? Ba
komai. Alh. Adam ya cage, tabbas naga Danliti a
shagonsa, sai dain banyi tunani tare suka dawo
ba, tunda banji labarin ba a cikin gida. Sai dai
Yaya a gaskiyya muna so mu ganar da kai cewa
ba farinciki mukeyi da abinda ya sami mama ba,
mutuncin gidan nan, ai duk namune, me zai sa
muyi murna da rugujewarsa? Abba yace duk naji,
magana ta gaskiyya, Allah kadai yasanta, don
shine masanin sirrin xukata. Abinda ya sa bau
san Mama ta dawo ba, sai yanxun. Ali ne ya fara
ganinta kuma ya xo ya sameni guiwa 2 ya roke
ni da kyale mama kar in daga murya, saboda
baki fa ke cikin gidan nan. Idan sun tafi ayi su
wacce xa ayi. To maga ma ta kare, nacewa
Danliti ya fito a daura musu auran, su karata.
Allah dai ya gani ba da son raina bane. Fuska Ya
mutse Alh. Basir ke cewa, Dan liti xata aura?
Yace bamu da abinyi, haka Allah ya so, sai dai
muyi mata fatan alkhairi. Saboda haka bana son
abin yayi tsawo, yana turo sai aure. Ya turowa
za'a sa rana kuma ba zata wuce sati 3-4 ba duk
abinda Allah ya hore min shi xa'a kai mata. Ita
kenan maganara, kowa na iya tafiya harkokinsa,
mu saurari xuwan magabatan nasa shikenan,
Allah ya nuna mana. Haka suka fadi baki
dayansu. Abba ya amsa da amin, suka bar falon
ba yabo ba fallasa, cikin xukatansu, ma'ana
intayi ruwa rijiya in ba tai ba masai. Suna shuga
sasan su, suka bajewa iyalensu babu bata tym
suka fara xuba sharhi. Haj. Gake kuwa har da
guda. Daga bisani suka baxama sassan Uban
dawaki, don gain Mama tare da yiwa Umma
murna dawowar Mama fida, amma a zahiri a
cikin xukantasu yanayin Maman suke son gani.
Suka kwarara sallama, umma ta amsa, sai
mukaji daddadan labari! Ina maman? Inji Haj.
Hajjo, tana dakinta, gaba daya sukace Allah shi
kyauta na gaba. Yanxun da Danliti xa'ayi auran?
Tace, nufi ne Allah, duk abinda ya rubuta bamu
isa mu goge Ba. Haj. Hajjo tace gaskiyya ba
haka

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login