Showing 15001 words to 18000 words out of 110841 words
mata kujera,
"zauna nan!". Ta zauna kai a sunkuye, ya shigo
da yaran, yaynda mami ke fadin, "ki saki jiknki
sakeena, nan gdnku ne, kuma ni bana surukar,
'yata ce ke. Kinji?". Ta kara rufe fuska da mayafi
tana dan murmushi, ta silalo ta kwashi gaisuwa,
mami na amsawa baknta kamar gonar auduga.
Yaran ma suka gaisheta, ta tambayi sunaynsu,
kowannensu ya gaya mata. Kusa da mama
al'ameen ya zauna baknsa har kunne, "mami ya
kika ganmu? Munyi matchn ko?" tace, "ai kana
zama kawai naji na kosa ta shigo gidan nan,
yanda kasan in boyeta". Yace, "kinsan ynda za'a
yi? Mu kulleta a wani daki, muce bamu ganta
ba". Dariyar mama ta karu, ta kara sunke kai
tana jan mayafi. Mami tace, "idan ma muka yi
hakuri dan lokaci kankani ne, Ubangiji dai ya
bamu aron rai da lfya. Kuma Allah yayi muku
albarka, na gode kwarai da gaske sakeena. Duk
mai son tilon dana gaskiya nima bani da kamar
sa. Sbd haka ku rike amanar junanku, kinji
sakeena?". Ta amsa da kai. Yace, "ina su Iya?
Basu san amaryata ta iso bane?" tace, "suna
kicin tun safe suke shirya mata abncin tarba".
Ya mike, "bari in kirasu, ai ko ladi bata zo ba ya
kamata Iya tazo taga amaryar dan Iya.!" tace,
"maza jeka". Ya fice. Mami na masa drya,
wannan amarya ana ji da ita. 'Yar dattijuwar na
zaune tana yankar ganyen latas, ya fado yana
kira, "ina Iya ta ne?" tace, "gani nan dan Iya". Ya
tsugunna baynta ya yada kansa a kafadar ta, a
shagwabe yake magana, "baki san amaryar dan
Iya ta iso bane?". Ta kara fadada fara'arta, ta
aje wuka, "ina na sani? Ynzu tana nan ciki?"
"tana dakin mami, taso muje. Iya yau mu 2 zaki
goya". Tace, "ya zama dole". Ta yunkura ta tashi
tana kiran Ladi, "maza kizo amarya ta iso!". Tayi
gaba ya biyota suka shigo dakin, yayi azama ya
koma kusa da mama. "ya kika ganmu?". Ta
rangada guda, daidai ladi na kawo kai, "lallai iya
harda guda?". Tace, "abnda yafi guda ma zanyi
ladi, wannan amarya zubin larabawa? Gskya dan
iya kayi sabe, Allah ya tabbatar da alkhairi".
Gaba daya suka amsa, amin. Shi kuwa ji yake
tamkar yau yake angwanci, bai san lokacin da ya
kai hannu ya rungumo kafadarta ba yace, "Iya
kenan, mai raino na". Da sauri ta zame ta sulale
kasa ta makure. Mami tace, "hayaniyar ta isa
haka, aje a kawo musu abin sha" Kafn kace
kwabo tsakar dakin mami ya cika da kayn lashe-
lashe da jus kala-kala. Al'ameen ya zuzzuba
musu, ya mikawa yaran. Sannan ya juya kan
gimbiyar ya miko mata, taki karba. "nifa ban son
kauynci, kinsan Allah zan miki dure!". Mami
tace, "wai tsaya, bakuwarka ce ko tawa?" yace,
"taki ce maminmu". Tace, "to tashi ka bamu
wuri. Don me zaka dameta? Duk ka kanainaye
min ita, maza tashi ka tafi harkoknka". Ya
marairaice, "baki tausayina mami? Daga yau fa
bazan sake ganinta ba sai karshn watan da zamu
shiga, sannan ba waya ba komai? Pls mami ki
barni in zauna". Ta tafa hannu, "ya Rasulu, ni
indo! To bari in tashi, watakila ni take jin
kunya". Ta yunkura zata tashi, "don Allah kar ki
daka ta tashi, ki dauki komai ki ci, ki sha lemu
kinji? Sai kinci kin koshi a gidan nan zan
tabbatar kina son dan Aminu na". Ta fice,
al'ameen din yana drya. Ya kara matsowa, "kinji
abnda tace ko? Nima yau zan gani, kina sona ko
a'a". Ya jawo tiran soyayyen naman kaji, meat
pie, donat, lafiyayyen cincin da samosa, yace,
"to Bismillah, iya cinki iya son da kike min". Ta
dubeshi tace, "wannan wayau ne, a wane ckn zan
zura tulin kayan nan?" yace, "oho! Ni dai na kare
magana, kuma kina jin abnda mami tace". Tayi
shiru tana kalln tire, kafn ta dubeshi, "don Allah
ka tayani ci". Yayi 'yar drya, ya dauki samosa ya
kakkara wa yaran. Ya sake daukar daya ya kai
baknsa, "mu tayaki, kema fara ci". Duk kunya ta
isheta, da kyar tasa hannu ta dauki meat pie, ta
juya gefe ta gutsira. Ya zura mata ido jim!
Sannan ya dauki kofin lemun ya miko mata, "sha
in kara ganin ynda kike so na". Ta karba ta dan
kurba. Ya jawo ameera jiknsa ya rungume,
"kinga ynda antinki ke so na?". Oho! Ina ruwan
ameera, me ma ta sani banda drya, tana amsawa
da kai. Sai ga ladi dauke da wani tiren ta aje
wani dan matsaikaicn kek da duminsa. Yace, "a
gaida ladi". Tace, "likita irin wannan zaman da
kake yi kyanshi a buga muku hoto". Yace, "ko
ladi?" "gaskiya". Ya fice suna masa drya, jimawa
kadan ya dawo da 'yar karamar kyamara a
hannunsa. "ai kema zaki iya daukar mu ladi, ba
wuya. Duba nan ki gani, saman nan kawai zaki
latsa". Yana saitawa ya fara bada misali, sai dai
kawai mama taji wal! Haske ya wuce. "ai kin
gane ko ladi?" "na gane likita". Ya mika mata.
Mama kuwa sai kalln ikn Allah take yi, ya dawo
gefnta ya zauna, ya taro su ameera, ladi tayi ta
yi musu hotuna. Wasu tare da yaran, wasu su
kadai. Ladin ya tura ta kira mami, itama ta
zauna suka yi hotunan tare, fadi take, "wannan
shagali yayi kyau". Mama kuma bata sake ba sai
da al'ameen ya tafi sallah. Sunci sun sha, sun
bar gara birjik! Kamar ma basu taba ba. Kafn ya
dawo ta gama shirin tafya. Ga ledoji tuli,
kayayyakin da mami ta bata. "ban gane ba?" Ya
tambaya, har da kama kugu hannu 2. Tace, "gida
mana". Ya langabe kai, "gaskya ba haka ake yi
ba, ba haka ake yi ba sakeena. Ai dai sai la'asar
ya kamata ko?'. Tuni take ta drya zancnsa, kafn
tace, 'ka manta yaya na jirana ne?'. Ya runtse
ido tamau! "oh my God!". Ya bude ya kara
matsota, ya zura mata ido, "kamar ki ta zama a
gidn nan sakeena, bana so ki tafi". Ta sauke
numfashi, "kayi hakuri". Yace, "yaya zanyi
sakeena? Ya zama dole, amma ki bari zuwa
karfe 3 sai mu tafi" "Allah yaya zai yi fada, kana
so ya bata min rai ne?" ya kada kai, "bana son
kowa ya bata miki rai sakeena, kin gama
shiryawa?". Ta amsa, "na gama. Ka ga kayan da
mami ta ba ni? Sunyi yawa Dr, kace ta rage".
Yace, "me yasa ke baki ce ta rage ba?" "kunya
nake ji" "oh, nine mara kunya kenan?". Tayi dan
murmushi, "ba haka nake nufi ba yallabai". "to ai
mami tasan kinfi karfn wadannan tarkacen ne,
shi yasa ta baki su. Gaba daya shopping din
makarnta ne. Bari in zuba miki a mota ko?".
Tace, "na gode!". Sai ga mami ta shigo. "mami
barin in maidata gida, yaynta na jiranta zasu
wuce". Tace, "yana da kyau! Sakeena na gode, a
gaida min mutan gidan. Insha Allahu duk ranar
da na shigo fandagorin zanje mu gaisa da
umman taki". Tace to. Ya kwashe kaya ledoji
hudu, mami ta riko hannayen yaran suka fito,
tayi sallama da su iya. Har mota mami ta raka
su, tana tsaye suka fice. Suna tafe a mota suna
hirar Mami, zcyar mama gwanin dadi, surikarta
na sonta, kuma ta nuna mata kauna. Yayanta na
waje yana ta faman duban agogo. Al'ameen yayi
fakin suka fito. Yaran suka ruga gunsa, take nan
suka fara bashi labarin ina da ina suka je, kamar
shi ma bai sani ba. Bayan sun gaisa. Yace mama
tayi sauri ta fito da kaynta, don shi a shirye
yake, ita kadai yake jira. Ta shiga ciki da sauri
dauke da kayan da ta samo, sbd tana so ta nuna
wa anti Rabi, kuma ta dibarwa su ameer wani
abu. Haka kuwa aka yi, anti rabi na ta sa
albarka, ita kanta ta samu mayuka masu tsadar
gaske, da turare guda 2. Mama da yara suka fhto
da kaya suka zuba. Hankalnsa a tashe yake.
Ganin suna satar kalln juna, shi yasa yaya yace,
"ina zuwa". Ya shiga daga ciki don ya basu guri
suyi sallama. Ya zura mata ido yace, "sai nazo
visting, Ok?"tace, "shikenan, ina saurarnka".
"zanzo miki da pictures din da muka dauka ki
gani". "to". Suka yi shiru sai kalln-kalln suke yi.
Idanuwnsa tam da kwalla yace, "gskiya gobe ba
don da wuri zaku wuce ba, zuwa zanyi. Ban
ganki ba, banji muryarki ba. Anya kuwa zan
jure?". Haka nan nata idanuwn suka yi ja, ta
bishi da kallo, amma ta kasa cewa wani abu.
Motsin fitowar yayanta yasa tayi firgigi, ta wuce
da sauri ta bude mota ta fada. Muryar anti rabi
taji bisa kanta tana fadin, "to matar likita a
sauka lfya, ace ina gaida umma da kyau da
kyau". Tace, "zata ji". Ameera kuwa kuka take yi
zata bi ta. Hnkaln mama ya kara tashi, tace,
"yaya mu tafi dasu mana" yace, "islamiyya ce
bana son suyi missing, kyale su kawai sai wani
lokaci". Ya ja murfin mota ya rufe, yayi mata
key. Al'ameen ne ya dauke ta, "yi hakuri kawata,
anjima kadan muma zamu bi su". Bata yi shiru
ba, amma ta rage sautin kukan. Suna kalln
motar ta bar harabar gidan, ameera kuwa ta
kara wage baki. Al'ameen ya jefata a kafadarsa
ya rungune, kirjnsa shima sai bugawa yake. Shi
kansa yana bukatar rarrashin, shi yasa yayi
tsaye jiki ba kwari. Tsawn lokaci sannan ya
dagota ya share mata hawaye. "Manta da anti,
ba ma yi da ita, tnda ta tafi ta barmu. Yi shiru,
yi shiru. To jeki wajen momi, sai na dawo ko?".
Tace, "yaushe zaka dawo?" "duk lokacn da nazo
garin nan zanzo insha Allahu". Ya ajeta gaban
mominsu, yace, "anti zan wuce, sai wani lokaci".
Tace, "to mun gode kwarai da gaske. A gaida
mutan gidan". "zasu ji". Ya wuce yana dagawa
yaran hannu. har suka iso fandogari mama bata
cikin sukuni ranta bace yake kwarai. Ganin
Ummanta yasa ta saki jikinta. Kowane sassa
umma ta turata, tace taje ta gaishesu kuma ta
gaya mata an sulhunta. Gab da sallar magrib
uban dwk ya dawo daga Kd gaba 1 siyayyar skul
yai mata bayan isha' suka taru a falo suna cin
abnc. Umma ta baje masa kayan data sami a
gidansu al-ameen yasa abarka,sann yace ta aje
su tukunna. Umma tace a'a Alh naga akwai
abubuwan ci wadanda zasu iya lalacewa, yace
banason amsar kayayyakin nan amma bakomai
ki bata wadanda kike ganin zasu iya lalacewa
kibar sauran. Tayi murmushi Alh ho!
Abdulkareem yace danAllah kubar mata kayanta
tayi amfani dasu. Menene? Aiba fata akeyi ba
kuma sani kanka ne Abba babu abnd zai gagara
koda an sami akasi karka da mu Abba. Nasan
surutai sunyi yawa akan mama cikin gidannan
haka bazai hana ta amsar kyauta daga
masoyinta ba. Yace Allah ya shige mana gaba
suka amsa da amin. Yayan yaci gaba da fadin
gsky yaron nan yana son mama kullum waya sau
2 sau 3 wkend kuwa idan yazo tun safe sai
yamma. Umma tace ai ta kare kuma tunda ba a
waya a makaranta Abba yace baki tausayinsu
kenan? Tace ina ruwana? Suka fara dariya mama
ta hada rai. Abba yace ni inaji kyaleta kinji yar
Abba? Ta kara matsawa gunsa ta lafe. Yaya yai
yar dariya yace abin harda shagwaba? Ido kamar
an matse kwado ba inji Umma. Duk suka fashe
da dariya ita kuwa kukan shagwaba takeyi.
Washe gari da sassafe karfe 8am tare da yayanta
suka iso gidansu baraka sbd shima yanason ya
gaida innarsu. Ta kuwa ji dadin zuwansa ita da
megidanta su kuwa kawayen suna can kebe lbr
ya tsunke kamar kurna na zuba. Ita dai baraka
wangame baki kawai tayi tana mamakin wann
kasaitacciyar soyayya data kullu cikin kankanin
lokaci. Tabbas ta shaida domin itama na tattalin
kayan skul da mama ta kawo mata sun ishe ta
tafiya skul. Jaka inna tasa albarka banda
alhairin da AK yai mata da megidan. Kafin ya
gama sallama dasu inna mama da baraka sun
sulale sun tafi gidan goggo wato kakar alameen.
Harda manya goro guda 10 suka satowa inna
cikin wanda take siyarwa Goggo ta nuna nata
murnar taga kishiya suka bata goro ta amsa ta
jujjuyashi tace na toshiyar bakine wann? Lallai
kinsa in bar miki mijin. To naki wayon kenan?
Suna ta dariya suka fito ta rakosu har zaure tana
sa musu albarka. Suna fitowa suka hangi yaya
tsaye yana jira suka karasa da sauri, yi hakuri
yaya. Ina kukaje masu yawon tsiya? Baraka tace
mun danje wajen wata kawarmu ce. Yace I see..
Daga zaure inna ke fadin kaji karya ko? Ni
nasan gidan goggo Hausi sukaje kakar alameen.
Ya kama baki yace Allah ya shiryeku. Inna sai
wani lokaci. Ya bude mota ya shiga inna na
fadin Allah ya tsare agaida Rabi da yara. Mama
da baraka suka rungume juna sannan ta shiga
mota tana yiwa inna sallama yaja suka wuce.
BAKIN CIKI 1***8 Suna isowa gida, me mama
zata gani? Motar al'ameen aje gefe guda. Gabnta
ya yanke ya fadi, haka ma yayanta ke mamaki,
"wannan ba motar al'ameen bace?" "ita ce yaya".
"mama biyoki yayi?". Tayi shiru tana 'yar drya.
Yana fakin yabe fadin, "kai wannan mutum yana
damun kansa da yawa. Pls ki gaya masa ya rage
sonkh, kaq ya zame masa illa". Ta sauke ido
kasa tana murmushi, tana kuma murzar zobensa
da ke yatsanta". Yace, "je ki mana, tnda ba zaki
iya gaya masa ba". Tace, "yaya kenan". Ta fito
yaynda yayan ke fadin, "nayi laifi ko?". Ta kada
kai, "a'a wlh". Ba shi ckn motar, sbd haka ta
tabbatar yana falo. Don haka ta wuce ckn gida.
Ido waje tana magana, "umma sai naga motar
al'ameen a waje?" tace, "nima haka abbankuya
gaya min. Yana can falo tare da alhajin"". Ta
nemi waje ta zauna har da tagumi. "au zama
kuma zaki yi?" "ummi kince suna tare da abba,
sai kuma imje?" tace, "to zauna. Amma kinsan
dama ku yake jira ku dawo ya maida ki makrnta
ko?". Tayi shiru. "saura kije ki shantake da
surutu. Sannan ki gaya masa don Allah ya rage
sonki, zai iya zame masa damuwa". Tuni take
kallon umma ido waje, har ta wuce ta bata wuri.
Ta zabga tagumi hannu biyu zugum! Tunaninta
yaya zata yi ta dumfari al'ameen da wannan
maganar? Tabbas ita kanta tasan al'ameen ya
makance a sonta, da zai rage din da zata so
hakan, don bata son duk wani abnda zai raunana
mata shi. "Mama!" taji an kwala mata kira, ta
dawo daga duniyar tunani firgigi, ta dubesu tsaye
bisa kanta. Abba yace, "tunanin me kike yi?"
tace, "ba komai abba". "to yana falo, kiyi sauri
ki ganshi muce. Wai rokona yake in barshi ya
kaiki, tnda duk hanyar daya ce. Nace masa a'a,
ya barshi yaje gun aiknsa". Jiknta ya kara
mutuwa, ta juya salalau-salalau. Yayanta na
fadin, "ni dai nace ta gaya masa ya rage sonta.
Dis is 2 much!". Abba yace, "duk wannan ma bai
taso ba, amma a ganshi tare da ita a mota, ai
zan shiga bakin duniya, kuma daga ckn gdn nan
maganar zata fara. Ba ni a ckn wannan tsarin,
ba wai kuma don ban yarda dashi bane. Je kayi
wanka kayi shirn komawa". Ya wuce, shi kuma
ya wuce sashn da ya kwana don yin wanka.
Kwalla ta tsaya take sharewa a kofar falon,
zallar tausayn al'ameen ne ya tilasta mata zubar
su. So ba zai taba zama laifi ba, amma ya
kamata al'ameen ya rika bi a hnkali, kar son da
yake nuna mata ya zama laifi a wajn iyaynta.
Sai da ta natsu sosai ckn ranta, sannan ta tura
kofar ta shi shiga tare da sallama. Ya amsa yana
kallnta, ta wuce ta zauna rai bace. Da sauri ya
matso gunta ya tsuguna, "da inga irhn wannan
fuskar taki gara na kwanta gadn asibiti sakeena.
Gaya min waye ya taba min rayuwa ta?". Gaba
daya tsigar jiknta sun tashi, ta dan numfasa
tace, "kai da kanka ka tabani Dr." "ni? Me nayi?"
"nasan kana sona Dr, ni kaina zan iya dafa
Kur'ani in rantse. Wlh yadda kake ji haka nima
nake ji. Bana son kana tsananta damuwa ckn son
da kake min, domin ina jin tsorn kar wani abu ya
illata min kai. Ganinka da nayi yau ya fadar min
da gaba ba kadan ba. Wnda ya tabbatar min
cewa zaiyi wuya jiya in kayi barcin kirki, sbd ba
muyi waya ba. Me yasa? Kar ka mance makrnta
zan koma, inda ba waya, sai fa in kazo visiting.
Kana nufin ba zaka yi sukuni ba tsawn wannan
lokacin? Rashn sukuni ba shi zai tara maka
damuwa ba? Kai fa likita ne. Ka gaya min me
yawan sa damuwa a rai yake haifarwa?" Yayi
zuru yana kalln ynda idanuwnta suka kawo
kwalla. Ta kara fadin, "tmbayarka nake, ka gaya
min?". Ckn sanyin murya yace, "abubuwa masu
dama da kan iya nakasa lafyar mutum. Amma
kar kiga laifina sakeena, sonki nake yi". Kwalla
suka malalo bisa kuncnta, lebe na rawa tace,
"yayi yawa Dr.! Ka rage don Allah, bana son na
rasa lfyrka". Tasa hannaynta da sauri ta rufe
fuska, ta ja numfashi mai sarke da kuka mai
tsuma rai. Wani kululu ya tokare masa wuya,
kansa ya dau zafi, zcyrsa na zugi tare da tashn
hnkali. Da kyar ya kalato miya a baknsa, ya iya
fadin, "SA... SAKEENA!". Ta dago ido jajur! ta
dubeshi. Ya mika mata hankicif, "don girman
Allah ki gnge hawayn nan Sakeena. Kin kuwa san
ciwon da kika dasa min yazu? Komai zai iya
faruwa dani, muddin hawaynki ya ci gaba da
zuba". Tasa hannu ta karba ta goge kwallan ta
numfasa ta dubeshi a hnkl alkawarin da mukayi
wa juna Allah zai tabbtr mana dashi nima ina
sonka Dr. Ya koma dirshan ya zauna farin ciki
ya mamaye zuciyarsa yace duk jawabin ki na
yarda dasu sakeena. Kuma zan kiyaye
shawarwarin da kika bani, tare da yin adduar
Allah ya sanyaya min zuciyata duk lokacin da
ciwon son ganinki ya kamani, rokona gareki
shine ki taimakeni ki daina zubda hawayen ki ko
alama banason ganinsu. Tace daga yau bazan
sake ba, muddin ina ganin ka cikin nutsuwa.
Yayi dan murmushi an gama my princess. Tace
to yanzu ka tashi in rakaka ka kama hanya ka
isa wajen aiki da wuri. Yace a'a kar muyi haka
dake kije ki shirya ku fito kina gaba a motar
Abba ni kuma ina take miki baya. Kash! Saidai
babu jiniya dana makala kowa yaji ya kauce
hanya gimbiyata zata koma skul. Ko ba haka
ba? Ta dan shagwabe gsky ba haka akeyi ba, ba
haka akeyi ba Dr! Aidai zaka sa Abba yayi min
fada. Ya zura mata idanu yana dariya to
shikenan bari inyi gaba tunda kin amince min.....
Ka zama prince ba ta tari numfashinsa. Ya kara
rausaya kai ah! Lallai ngd. Ya mike to muje ki
rakani. Ta tashi suka jero na shiga na gaida
goggo. Ah haba yaushe? Dazu da mukaje gidan
Inna ta da yaya. Amma kin kyauta naji dadi
nima idan nabar nan zan shiga in kai mata cfane
karfa kiyi kishi. Tayi yar dariya aini bana kishi
da goggo, sbd me? Ya tambayeta yana kallonta
ido cikin ido ta bashi amsa sbd aronka na bata!
Ya fashe da dariya zan kuwa gaya mata idan ta
zauneki ba ruwana. Sukaci gaba da dariya har
gaban mota ya bude ya shiga ta rufe nasa "take
care" Allah ya tsare. Ameen kikace arona kika ba
goggo ko? Ta tura masa hula gaban goshi ta
ruga cikin gida yabita da kallo duk kasala ta
rufeshi. Ya sauke wawan numfashi ya gyara
zaman hular yana kada kai fuskarsa dauke da
murmushin kauna. Yayiwa motar key yayi ribas
zai wuce kamar walkiya ta bullo ta daga masa
hannu da sauri ya dago nasa fara'arsa ta karu.
Hanklinsa ya kwanta yaga abar sonsa. Bayan ya
gama da goggo da kanta ta kaishi ya gaida inna
daga nan ya tambayi baraka don ya sha jin
lbrnta a bakin mama. Ta fito suka gaisa babu
wanda baiyiwa hasafi ba musamman baraka da
yake ganin zuwa wajenta shine silar haduwarsa
da mama yarinyar da yakeji tamkar itace ransa.
yana fitowa ya shige mota ya doshi babban titi
yana kawo kai motar Uban dwk na hayewa
kwalta. Abba bai sahida shi ba Amma ita mama
tuni suka hada ido sukaiwa juna murmushin
mmki nan da nan ya