Showing 57001 words to 60000 words out of 110841 words

Chapter 20 - BAKIN CIKI BOOK COMPLETE BY ESHAT.txt

12 Sep 2025

78

ku akan
wannan maganar. Wlh har yanxu ina ji ajikna
sakeenna tawace. Dady ya rungumo kafadunsa
yace, shikenan,ya Isa, munji rokonka mun amsa.
Zamu cigaba da taya ka addu'. Yanxun abinda
nake sonka da shi shine, ka kira Dr. Lawal ka
gaya masa, don su sani. Sai dai in baka
lambobin ka kira shi dady, bakina ba xai iya
furta mummunan labarin nan ba. Ya mike ya jao
durowar dadi ya dauki biro da paper ya rubuta ya
bashi, ya mike xai fice, ya kusan kaiwa kofa
mamy ta kira shi, ya juyo tace kayi nafilfilu cikn
dare. Allah zai saurareka, ya nisa kafin yace
xanyi mami. Ya sa kai ya fice. Mami ta dubi
dady ta hadiye hawayenta, tace gobe in Allah ya
kaimu xan koma Lafai wajen baba liman in samo
masa ruwan addu'a ya sha ya sami sanyi cikin
ransa. Yace hakan ma yayi, Allah ya sa mu
dace. Tace amin. Ta jawo wa dady kan waya ya
nemi Dr. Lawal, ya sanar masa. Yace an fasa?
Subhanallahi? Wannan abu baiyi dadi ba. Don
girman Allah dady a samu a daidaita, wlh Al-
ameen yana son yarinyar nan ba kadan ba. Ya ce
ba sai ka rantse ba Lawal, ni kaina nasan hakan,
amma fadan da ya fi karfinka dole ka maida shi
wasa. Mu nan muna ta addu'a Allah ya zaba
mafi alkhairi. Ya numfasa, yace amin. Ina Dr.
Yake? Ai sai da ka neme shi xuwa gobe, yanxun
kam babu sukuni yana dakinsa. Yayi dan jim,
kafin yace Allah shi kyauta, amma ayi kokari
Dadi idan xai yuwu a sasanta. Ba komai mun
gode a gaida Iyali. Zasuji, ya aje wayar tare da
tsananin mamakin wannan abu? Me ya faru haka
da xafi? Haka ya kwana da tambayar kansa, don
babu alamar wata mishkila a tattare da soyayyar
abokinsa da sakeena, ko daya zo sanar da
xancen auran ma babu alamat akwai matsala
babba. Labarin barci dai babu shi a wajen Al-
ameen kuma xuciyarsa bata daina karyata masa
xancan ba. Ko alama ta ki amsar sakon, saboda
tsabar shakkun da yake ciki, wai sakeena taci
amanarsa? Har 8am yana kan sallaya, ba don
wai yana sallah ba, a'a kasala ce ta hana masa
tashi. Mami tayi sallama ta shigo da tiran kayan
karin safe. Ya xubo mata ido. Mami tayi sallama
ta shigo da tiran abinci, ya xubo mata ido, ta aje
a agbnsa, ta xauna gefe, sannan yace, ina kwana
mami? Lfya lau, ina fatan ba ka tsananta wa kan
tunani ba? Ya kada kai, ya xanyi mami? Kin san
ba yin kaina bane? Ta dafa shi a sanyaye, kllm
ina kara gaya maka Al-ameen, kai kadai ne
garemu, kuma ka zama tamkar dubu, ba gare mu
kadai ba, gabadaya al'umma za su so rayuwarka
ta daure cikin fciki da walwala, saboda
muhimmancinta, ina so ka san wani abu yau.
Wlh na yi maka rantsuwar da ba kaffara da
rayuwarka ta salwanta, gara ni in mutu, don
na..... Ya rufe bakinta, a hankali, idanuwansa
taf, da hawaye yace, kiyi shiru mamina! Da ni
dake zamu rayu da yardar Allah cikin farinciki da
kwanciyar hankali. Har ga Allah na hkra da
sakeena mami, kawai ciwon fitar son ta ke
azabtar da ni. Ka kwantar da hankalinki mamina,
a hankali zaki gan ni yadda kike so. Tayi dan
murmushi tace, Allah yayi ma albarka! Da sauri
ya kwanta a kafadarta yana fadin amin mamina.
Zauna da kyau na hada maka brkfst. Kaga masa
na sa iya ta shirya maka da sassafe, na san
kana so kuma kana kewarta, don ba'a samu a
Rasha. Ya bita da kallo dauke da tausayi. Yace
nagode mamina, amma tare xamu ci ko? Ta jawo
fileta tana fadi ah! Me zai hana? Bari ka gani. Ta
loda waina a plate tana xuba miya ya ware ido,
yace mami kin cika abincin nan! Ita ma ta ware
idon tace injiwa? Ni da kaine fa? Sa hannu ka
gani ko asa man shanu? Ya kada kai, a'a kinsa
banso kayan karni. Ka bar dadi yaro. Yayi 'yar
dariya yace Allah ko? Ta tura masa a baki tace,
haba ai ba sai na fadi ba. Dady yai sallama
dakin ya karaso da sauri yana cewa iye! Masa
kuke ci kuka nuna min 'yan ubanci? Gaskiya ba
ha akeyi ba, ai sai ku kira ni ko? Ya tambaya
yana kallon al-ameen cikin ido. Ya gayara masa
wwuri, yace laifin mami ne, xauna abinka
Dadyna. Ya xauna yasa hannu ciki, yace ai mami
akwai rowa, Allah dai ya tsaga da rabona. Suna
dariya ta bashi amsa, ka san kuwa da na kawai,
na aka yi ma. Kaji ko? Tafi son ka akaina. Yayi
wuf ya rike hannu da yake kokarin kai loma
yace, ba xaka ci ba sai ka fadi! Gaya min, mami
ta hau dariya shima ita yake yi. Dady na ga dai
da ta rikice kanka. Tace babu wani sai kai,
sannan aka sameni, ko ba haka bane mami?
Tace ni xaka tambaya? Dady ya karbe yanki
wainar daga hannunsa ya tura masa baki, yace
cinye dana, ka bani amsa daidai. Bai gama
cinyewa ba ya dauko cinyar kaza ya tura msa, ka
ra da wannan kayi brush! Duk suka sa dariya,
ganin al-ameen na neman kwarewa, kan kace
kwabo sun yaudari Al-ameen ya cinye wainar da
mami ta zo da ita, domin dai shi suka yi ta
turawa da wasa da dariya ya take cikinsa. Bayan
sun kare, mami ta dube shi tace yanxun ka tashi
ka shiga wanka ka kimtsa, muje asibiti ka gaida
Umma.... Umma? Me ya sameta? Tashin hankali
ya sa ta sami hawan jini tuntuni, maganar jiya
kuma ta kara birkita ta jininta yayi mugun hawa.
Tana nan asibitin sun bata gado. Jiyan abba ya
taho da ita. Ya marairaice yace, Umma na asibiti
tun jiya baku gaya min ba? Ban dadin hakan ba,
dady yace kayi hrk, ganin kai ma baka da sukuni
ya sa muka kyaleka, kaji da guda 1. Ya mike
yace ba sai nayi wanka ba, yanxun xan tafi, idan
na dawo nayi, bai saurara ba ya wuce ya jawo
dirowa ya dauko key ya fice. Mami ta biyo shi
tace Al-ameen, ya tsaya cak! yana dubanta, ta
matsi sosai ta dafa shi, ka tafi a hankali, idan
kaje kace ina gaishe ta, ni ma xan biyo in na
dawo daga Lafai, ya dan lumshi ido, ya bude
yace xan kula mami, amma me xaki je yi Lafai?
Tace uzurina xai kaini. Allah ya kiyaye hanya, ta
amsa amin. Ya daga kai dubi dady dake tsaye
yace, sai na dawo dady, to ina jin ma xan
sameka asibitin. Yace shikenan sai kazo. Ya juya
yayi waje, su iya na kokarin fitowa su gaisa.
Amma ina saurin da yakeyi, ya hana su su same
shi falon, tuni ya kai ma'ajiyar motocin, ya
murza ya bar gidan. Umma na xaune an jera
mata filo, ruwan lipton kawai ta iya kurba, ya
xuna cikinta. Likitan ne yace ta dan jingina
kadan ta huta. Duk 'ya'yan sun kewayeta, abba
na xaune gabanta bisa kujera. Gaba daya tausar
xuciyarta suke yi don ta fidda abin a aranta.
Sallamar al-ameen cikin dakin ita ta dauki
hankalin kowa, suka amsa kona masa duban
tausayi, ganin yadda ya xabge kamar mai ciwo,
wai don ma su mami na yin iya kokarinsa
akansa. Ya bisu daidai sukayi musabaha, sannan
ya tsugguna gaban Abba suka gaisa. Tuni
ganinsa ya sa hawayen Umma suka tsinke, yayi
shiru a tsugunne. Abba ya dafa shi, yace sai ka
dawo ka sami labari maras dadi? To ina so ka
kwantar da hankalinka kayi imani da kaddara, ka
sani yau da ace mama na da 'yar uwa xan baka
ita, don in nuna maka iya kaunar da muke maka.
Mama ta zabi ta wulakanta mu, shi yasa na ke
son kowa ya cireta a ransa, mu manta da ita mu
kyaleta duniya ta hora ta. Kayi hkr kaji? Ya goge
kwalla yace naji abba, kuma nagode akan iya
kokarin da kukayi min, amma abba ina rokon ka,
don girman Allah ku ya fe mata, sannan ku
sanya mata albarka, a auran da xatayi. Duk
sukayi shiru, kowa ya xuba masa ido. Tausayin
sa na ratsa su, umma ta goge kwalla. Tace
Mama ba abar tausayi bace Al- ameen, don haka
ka daina rokon ayi mata afuwa laifin data aikata.
Ya kata matsowa gaban gadon yace, ba haka
bane Umma, ki san sharrin shaidan, sannan
xuciya bata da kashi, ba 'a son ran mama zata
aikiata wannan abin ba, xuciya ce ta saka mata,
na tabbata duk ranar da ta nutsu tayi tunani
xata gane lallai bata kyauta ba. Don Allah Umma
ko ina nan ko ba nan, idan Mama ta dawo ku
amshe ta hannu 2, ku samata albarka. Insha
Allahu shaidanin daya rinjaye xuciyarta, xai
kyaleta, ta dawo diya ta gari kamar yadda take
da. Abba ya kara dafa shi, yace idonka ya riga
ya rufe a son mama, shi ya sa baka kallon
girman laifin da ta aikata. Ya juya ya dube shi,
ba haka bane Abba nasan ina son mama kuma
har na mutu ba xan daina son ta ba, amma ku
yafe mata, don rayuwar ta, tayi kyau nan gaba,
ba farin cikin mu bane ace mama ta lalace tabi
duniya, tunda gaba dayan mu nan, muna son ta.
Kun yafe mata ko Umma? Tace kayi hkr Al-
ameen ba xan iya cewa komai ba tukunna, ya
abdulqadeer yace, ko mu bamu goyi bayan su
Umma suyi afuwa gareta ba, har sai ta sauya
zabin da tayi da. Tunda tace ba kai ba, to ka
kawo wani dan mutunci tamkar kai, amma ba
Dan liti ba. Wanna itace shawarar da muka
yanke. Yana rufe baki dadi ya turo kofar ya
shigo tare da gaishe-gaishe. Ya dubi al-ameen
yace, dr na jiranka. Da mamai ya dube shi, dr.
Lawal? Yaushe ya zo? Bai dade ba, muna shirin
fitowa, sai gashi shine nace ya xauna xan biyo
na gaya maka. Ya mike yayi sallama da su ya
bar asibitin. Bai sami mami ba, don itama driver
ya wuce da ita lfya. Dr. Lawal na babban falon
gidansu, ladi sun adana shi da kayan kusa da
baka, amma da ka dube shu kasan baya cikin
sukuni. Yana shigowa ya mike da sauri ya tarbe
shi suka kama juna. Dr. Lafai! Yace banyi xanton
xaka xo ba. Dole na xo, wannnan mummanan
labari ya hanani barci jiya. Yayi dan yake, kai
dai bari, mu xauna aboki na. Suka zauna kujera
daya, dr lawal yace, me yayi zafi likita?
Idanuwansa suka kada yace, bansan me ke
faruwa ba dr sama da sati 4 ina can na daina jin
wayar sakeena, aka ce min bata da lfya ne,
dalilin da yasa na dawo kenan don hankalina
yaki kwanciya ita kawai nake son gani. Ina xuwa
na iske labari ya sha bambam, wai sakeena ta
sami wani ya hure mata kunne, har ta mance da
manyan alkawuran da ta daukat min. Kowa yayi
iya kokarinsa wajen nuna mata gaskiyya, amma
sam tace ba san wannan ba. Abban ta kuwa ya
sha alwashin ni da ta fara kawowa akayi mana
baiko, ya sani ba xai daura mata aure da kowa
ba, face ni don haka yace ba xan koma sai an
daura auran. So da kaunar da nakewa sakeena
yasa bana tunanin komai Illa xumudin a daura
mana auran, shi yasa koda naje jiya bana nuna
maka komai ba.a xato na bai kamata in tona
kwanne sirri na sakeena ba, do kar a zage ta
matsayin maci amana, ina ganin kamar idan
muka kebe matsayin miji da mata, xan iya
rinjayar ta. Son da take take min ya sake
dawowa xuciyarta. Ashe duk abin da nake zato
ya wuce nan dr.lawal kawai na dawo jiyan su
dady ke gaya min sakeena ta gudu cikin dare ba
a san inda take ba. Al-ameen ya jingina da
kujera ya runtse ido sai hawaye shar... Na
malala, hankalin dr. Lawal ya kara tashim ya
xura masa ido jim sannan ya sauke numfashi ya
dafa shi, yace, kana cikin tashin hankali aboki
na amma Allah yace duk inda tsanani yakem to
tabbas da akwai sauki. Pls ka zama jarumi a
cikin jarabawar nan, ka bari hkr ya xama
sanadin samun saukin tashin hankalin nan. Ya
bude ido taf da kwalla, yace inason sakeena Dr.
Kai kasan hakan, yace kwarai da na sani kuma
xato na itama tana tsananin sonka. Ya matso shi
sosai yace haka ne, wlh sakeena tana sona, to
me yasa ta kini tym 1? Yace mata kenan Dr.
Lafai. Balle sakeenna na da kyau da xata iya
wasa da hankalin kowane da namiji. Watakila
kuma wancan yafi ka duk abubuwan da take
bukta. Dan wani minister ne a abja? Yace ban
nemi sani ba, a yau ne nake jin sunansa bakin
yaanta wai shi Danliti, danliti? Daga jin sunan
kasan ba wani bane. Da sauri ya amsa ai kuwa
wani ne.... (Hahaha Allah sarki lazy Dr.) tunda
ya sace min sakeena. Ko da kuwa kwara masai
yake yi. Inda ace xan gan shi xan iya durkuwa
gwiuwa 2 in roke shi, ya bar min sakeena ta.
Wlh itace rayuwata dr. Ya kada kai yace, ka
daina fadar haka Dr. Lafao kar fa ka mance wani
hani ga Allah baiwa ne, xa iya kasancewa
sakeena kyan dan miciji gareta.... Ya dakatar da
shi ta hanyar daga masa hannu.... Yace gaya
min kowace kalma dr. Amma kar ka aibata min
sakeena, ba xan taba ganin farinka ba. Ya xura
masa ido, kunshe da mamaki, kafin yace, ba nufi
nake nan ba aboki na, ina so ka gane cewar
bakomai da kake bane yake kasancewa alkhairi a
gareka, shi ya sa kullum ake son bawa ya roki
alkhairi wajen Allah. Yace sakeen alkhairi ce
gareni, tuni mafarkai na suke nuna min hakan,
har xuwa yanxun kuma jiki na yana bani sakeena
tawa ce, mishkila aka samu wani wurin, bana so
musu da su Dady ne kawai, shi ya sa nake nuna
musu na hkr da ita. Yace to idan baka hkr ba,
yaya xakayi yi? Tunda batayi da kai? Babu
abinda
BAKIN CIKI 2***10 Amma nan da iya shkrun da
xanyia duniya ba xan daina son ta ba har na
koma Ubangiji. Ya xura masa ido, yace Al-
ameen kar ka manta akwai gagaruminn aiki
gabanka wanda kowa ya xura ido don ganin
rawar da xaka taka, kasancewar kai kadai ake
tunanin xaka iya taka ta kuma mutanenan arewa
suna jiran daya tamakar dubu ya dawo masu da
abin alafahrin a duniya baki daya. Ina ka sami
nutsiwa ka fuskanci abinda ke gabanka ka tare
da jadda imani a cikin ranka, lallai Allah xai iya
baka wata. Ina fatan xuwa na ba xai xama abnxa
ba ba, kuma addu'ar duk masoyanka a zariya ba
zata fadi kasa banxa ba. Kowa yace Allah ya
musanya maka da lakhairi, na tabbata Allah xai
duba ya kawo sauyi na fadi daidai? Ya numfasa
yace ka fadi daidai abokina na, na gode ma kowa
bisa addu'ar da suka yi min. Xan koma rasha da
yardar Allah cikin yardarsa xan dage na fidda
kowa kunya. Sai dai abinda nake so ka sani har
in mutu ina son sakeena. Yace tuni na sani,
sannan ina da ilimin xuciya daya gareka, duk
abinda Allah ya xuba cikin ta, babu me iya
dauke shi. Ya koma ya jingina da kujrea,
rungume da hannayensa, ya dan numfasa ya
kada kai, dr. Lawal ya bubbuga kafadarsa ya
sake fadin, ka manta kawai abokina, ya wuce,
ya bishi da kallo kawai baice komai ba su dade
tare. Dr. Lawal na kara kwantar masa da hanakili
tare da nuna masa mahimmancinsa ga al-
aumma. Bayan azahar suke asibiti ya gaida
Umma, daga can ya wuce zariya, shi kuwa Al-
ameen gida ya dawo, don shima ba ya son yana
ganin Umma kwance tausayinta yana kara karya
masa xuciya. Ya rinka jin kamar su abba ba xa
su yafe wa sakeena ba. Wannan shine babban
tashin hankalin sa. La'asar ta kawo jiki yana
xaune shi kadai bisa gadonsa, tym-tym ya kan
dauki hoton da ke bisa kirjinsa ya duba. Hotonsu
ne shi da mama wanda sukayi a dakin Mami,
xuwan ta farko gidan. Karo barkatai kenan daya
daga hoton ya xura masa ido tsawon lokaci,
sannan ya mike ya sake kife shi. Ya laluba
aljihunsa ya dauko xoben da Mama da dawo
masa dashi, ya xare na hannunsa ya hada su
waje daya, ya xura masa ido. Sannan ahankali
yake wasa da su, ya rike kowanne yana hada su
karo. Cikin idanuwansa yake ganin ita ke rike da
wanda ya bata, suke karawa juna. Wannan karon
da karfinsa ya kara mata, na hannunta ya karye
nan da nan ta shagwabe, gaskiya ba hake ake yi
ba! Ba haka ake ba Dr. Al- ameen! Al-ameen
tsananin kiran ya dawo da shi tunaninsa duniya.
A firgice ya dubi Mami dake gabansa xaune. Ba
xai iya cewa ga tym da ta shigo ba, don haka
yake mata kallon mamaki, haka itama ta xura
masa ido mai dauke da questions. Mami! Yaushe
kika dawo? Ta sauke numfashi ta kada kai,
kafin tace, tsoron na Allah tsorona kar ka xaunce
al-ameen ka dawo cikin hankalinka mana! Yai
sauri ya runtse ido yana fadin Hasbunnallu wa ni
Imal wakil, Allahuma ajirni fi musibati wa
akhlifini khairan minha. Ya bnude ido jajur ya
dubeta, kiyi hrk mami.... Takatshe shi ba xan
bari rayuwar ka ta salwanta ba Al-ameen sai
inda karfi na ya kare, Allah na gani yarinyar nan
ta xalunce ni. Kafin yace wani abu, ta mike da
sauri tai waje, ya bita yana kira, ba su hadu ba
sai a dakinta... Mami.... Ta daga masa hannu.
Ban son jin komai, ta mika masa wani ruwa da
ke hannunta tace shnaye shi ka bani kofi. Yace
na menen? Ban son tambaya ni na umarce ka
kashanye, ka bani kofin. Ya daga kofin da sunan
Allah, ya kafa aabki ya kwankwade. Ta karbi
kofin ta aje gefe. Ya sake tambaya mami ruwan
me nasha? Tace baba liman ya bani taimako na
kawo maka, anjima zaka sake sha, gobe ka kara
da safe da yamma. Jibi in Allah ya kaimu lfya
za ka koma sch, domin fitar da dadin ka yayi
bookin ya je maka, ina fatan kajini? Jikinsa yai
sanyi, ya kamo hannnayenta 2 ya ja suka xauna
bisa kujera yace Allah sarki mamina. Allah bar
min ke. Nagode da karfafa min gwiuwar da
kukeyi. Idanuwanta taf da hawaye tace,
hankalina bai taba tashi ba irin na yau. Ban taba
jin faduwar gaba ba irin ta yaukai da zobuna
kake hira kana dariya, Al- ameen ban same xai
faru ba nan gaba. Kafadunta 2 ya dafa yace sai
alkhairi mamina, kawai xancen xuci ne ya fito
fili mami... Tace daga haka sai tabin hakali al-
ameen , yayi dan murmushi yace Allah ba xai sa
ba mamina, ya san ni kadai ya baki, kuma shi
mai tsananin tausayi ne. Allah sa ruwan da kika
bani ba wanda xai cire min son sakeena bane. Ta
xura masa ido cikin xafi tace, shine Al-ameen
Insha Allahu sakeena ba xata zama ajalinka ba,
ya numfasa yana murmushi da bai kai ciki ba
mami kenan, wa ya gaya miki sakeena xata
kashe miki tilon danki? Kuma wa ya gaya miki
danki xai ji dadin rayuwa ba tare da soayyar
sakeena ciknin xuciyarsa ba? Duka 2 tafiya suke
kafada da kafada mami, Allah yayi hukuncinsa,
don haka ban ji Baba liman xai iya cirewa. Bayin
kaina bane, kiyi hkr mami. Tayi masa xuru duk
jikinta ya mutu a hankali ta ce ko bai fita ba
xaka ji sanyi cikin ranka. Tunaninn ka xai
daidaitu da aikin kwakwalwar ka ta yadda xaka
yi mu'amula kamar sauran mutane. Wannan
shine farinciknm. Yace, Allah ya taimake ku
akan burin ku. Nima ya taimakeni akan nawa.....
Tace xamu ci gaba dayi da fada idan har kana
gaya min irin wadannan kalaman. Ya kada kai ba
xa muyi ba mami. To ka daina. Ya lumshe ido,
ya bude yace na daina, Allah yayi maka albarka.
Ya dora kansa kafadarta ya amsa da amin. Ta
ciga da yi ma nasiha yana sauraronta sai dai can
kasar xuciyarsa cike yake da xulumi, Allah ya sa
ruwan da mami ta ba shi

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login