Showing 1 words to 3000 words out of 110841 words

Chapter 1 - BAKIN CIKI BOOK COMPLETE BY ESHAT.txt

12 Sep 2025

51


HADA DOCUMNTS BY
ESHAAT SMILER HOM OF HAUSA AND ENGLISH NOVELS
@ WASAPP 08066360176


BAKIN CIKI 1***1 Sarautar Uban dawaki babbar
sarauta ce a garin fandagori can cikin jihar naija.
Babban gari ne wanda al'ummar cikinsa suka
bunkasa wajen noma da kiwo. Gidan uban dwk
Alh Awaisu Malami katafaren gida ne cike da
zuri'a masu yawa na kannensa guda 2 kuma
shine babbansu kat! Sassan sa yafi na kowa
girma da tsari ginin zamani. Matarsa daya Haj
Halima da yaya maza uku a jere. Abdulkadeer,
Abdulkareem da Abdulrahman sai kandensu "ya
mace tilo a cikinsu Sakina, sunan mahaifiyar
uban dwk gareta shiyasa suke kiranta "Mama".
Santaleliyar yarinya wacce Allah yayiwa sura
tamkar ita tayi kanta kusan zuri'ar gidan haka
suke da kyau na fulani. Amma ita mama ta fita
daban wajen cikar sura daka gganta dole
gabanka ya fadi sbd tsabar kyau. Shiyasa tun
shekarunta basu kai ko'ina ba samari suka
yanyameta kowa na so, musamman cikin
gidansu watau yan'uwanta abin har yana so ya
zama rigima a tsakaninsu. Saida Uban dwk da
kansa ya tara su ya soke maganr soyayya da
Mama ya kuma kar wanda ya kara kiranta da
sunan tadi. Yayi haka ne don a sami masalaha
da zaman lfy. Allah kuwa ya taimaka kowa ya
gama bacin ransa ya hakura. Baya ga haka yana
ganin Sakeena bata kai shekarun da zata tsoma
kanta kogin soyayya ba alhali tana tsaka da
karatunta mafarin kenan da zata tafi babbar
sakandire yayi kokari ya samar mata makarantar
kwana ta yanmata dake bakori (FGGC Bakori)
Sannan hankalinsa ya kwanta amma wann
hukunci nasa yayiwa wasu daga cikin iyaye mata
ciwo har suna ganin sbd kyaun da Mama take
dashi ne yasa ake wulakanta yayansu suka rinka
ganin kamar suna sn su dauki dogon buri ne su
dora mata. Tabbas uban dwk nada buri akan
yarsa tilo mace saidai yasha bamban da irin
burin da matan gidan ke nufin ciki zukatansu
wanda bazai wuce ya aurar da ita ga hamshakin
me kudi ba ko basarake. Shi burinsa yarsa tayi
zurfin karatu kamar sauran yayyinta maza
wadanda a halin yanzu Abdulkadeer major nr na
soja, Abdulkareem accountant ne a CBN, sai
Abdulrahman dake NYSC a Jalingo. Ya kuwa
lashi takobin ko bashi da rai yan'uwanta su cika
masa wann buri nasa. Kwanci tashi Mama ta
shiga SS2 kuma yau sukayi hutun 2nd term tun
safe Uban dwk ya tura drivernsa ya daukota,
basu iso fandagori ba sai bayan la'sar kowa na
ta murna musamman yara da suka yanyameta
suka kwashe mata kaya zuwa sassansu. Ta shigo
da sallama Ummanta ta tarbeta ta rungumeta, ta
shiga sauran sassan ta gaishesu, Salisu da
Danlami kadai ta samu acikin samarin sassan.
Ta zauna suka taba yar hirar skul sannn ta tashi
koma sassansu tana shiga ummanta tace
Abbanki na nan ya dawo ta wuce da sauri ta
sameshi a falonsa, bakinta har kunne ta dan
rankwafa tace Allah ya taimaki mai martaba!
Fara'arsa ta karu: Allah yabar min Mamana na
shigo akace kin shiga sassa. Ta zube gabansa
tace eh naje gaishesu ne, ina yini Abba? Lfy lau
ya karatu? To mungode Allah, yace ina report
sheet a kawo na gani. Ta mike taje ta kwaso duk
takardun yayi ta dubawa yana fadin da kyau!
Bayan ta kammala ya dubeta kinyi kokari sosai
Mamana na baya miki amma har yanzu kina da
yar matsala a biology sai kin kara bada himma
kinsan dalili? Ta kada kai yace kara matsowa
kiji ta matso kusa dashi sosai kafin yace: buri na
ki zama likita Mamana, sbd a rayuwa ta ina
sha'awar in ga ya mace likita, abin yana burgeni
kwarai, shiyasa tun ranar da Allah ya bani ke
nake ta addu'ar Allah ya raya minke in samu in
cika burina, ko kuwa ke bakya sha'awa? Tace
sosai ma nakeson zama likita Abbana. Kuma
I.S.A zan kara himma don ganin na gama da
biology. Ya dafa kanta cike da farin ciki yace
yauwa Mamana, Allah yai miki albarka tace
ameen Abbana. Daga nan suka ci gaba da hirarsu
saida akayi sallama dashi ya tashi ya shiga
babban zaure inda Majalisarsa ke taruwa.
Mamana ta koma gurin Ummanta a kicin suna
aikin abinci tana bata labarin abnd Abbanta
yace, Umma tace yallabai kenan Allah dai ya
cika masa wann buri nasa tace I.S.A Umma
saina zama likita. Tace Allah ya yarda wai waya
gane min Mama da farafen kayan nan? Mama
tana dariya tace na dan ratayo wann abun da
suke sawa a kunne ina takawa ana ga Dr
Sakeena nan zuwa. Suka fashe da dariya.
Washegari misalin 10:am Mama ta fesa ado da
koriyar atamfa sannn ta dora after dress ta yafa
mayafinta ta sami Umma a daki, sai ina? Zani
gaida Inna saude ne. A'a kice dai zaki gun
Baraka. Tayi dan murmushi Umma ai duk dayane
Idan na gaida Inna ta sai muyi hira da Baraka
kawata... Uhummmn... To kodai lauya zaki zama
a fasa likitan nan? Tayi dariya wai kinaso ki
hada ni da Abba kenan.. Lallai kam to kice ina
gaida Sauden idan ta gama dinkunan ta baki
kizo min dasu, shikenan amma ina fata akwai
nawa aciki. Umma tace babu naki aciki duk
nawa ne, Mama ta dan kirne fuska kai umma ai
kuwa zan zabi daya aciki, tace duk zannuwa ne
ciki da alakum rigunan kuma masu hannu ne,
zan canja style ni inaso a haka, to ban yarda ba
ki anso min kayana kawai idan ta gama. Ta
jinjina kai shikenan umma nina tafi, adawo lfy
karki dade... Ta saba jakarta tana fadin to
Umma.. Salis ne zaune a kofar gida tana fitowa
ya kare mata kallo sama da kasa kafin yace sai
ina kuma? "Gidan Inna Saude zanje" 'Okay na
kuwa ga Baraka jiya itama ta dawo". Ya mike
muje in rakaki ko bakiso? "Muje mana ta wuce
ya biyota suka jera. Wai Mama meyasa Abba
yake takuraki dayawa? "Kamar yaya?" Baya son
kina kula samari kin kuwa san har yanzu yaya
Ali yana sonki? Ta dube shi farin sani kuwa
tunda yana gaya min a sace amma fitinar duk
waya fara daukota? Yace a'a ba don muna uwa
daya uba daya dashi ba, abnd yaya Sa'ed yayi
bai kyauta ba, tunda yasan shi yana sonki
menene na shi na shigo nemanki? Ya fa san
halin Yaya Ali ba hakuri ne dashi ba yanzun nan
sai ya nuna maka hauka. Ta dan tabe baki tace
hmmmnn... Kai nifa karatu ma zanyi dama sun
sa ransu a inuwa, babu wanda zan aura acikinsu
koda Abba bai dakatar dasu ba.. Ya zura mata
ido kina wulakanci Mama kice dama kema ba
sonsu kike ba? Baka gane ba.. Me kikeso ki
fada? Karatu zai hanaki aure ne? Ta kada kai
nutsuwa nafi bukata sbd karatuna mai son
nutsuwa ne.. Me zaki karanta? "Akikin likita" ya
ware ido Uhmmnn.. Dokta Sakeena kenan! Tayi
murmushi har kasa naji gingiringin! Yayi dariya
daidai lokacin da suke tsayawa gefen babban
titi.. To Dr Sakeena ni anan zan juya.. "Ngd ai
kaga har nayi sauri da yake ana hira" yace dadin
abokin rayuwa kenan, don ma ba Ya Ali bane
tayi dan tsaki get lost donAllah ka rabani da
wann zancen, yana dariya ta tsallaka titi ta
barshi hanya shi kuma ya juya ya koma gida.
Mota yake kakkabewa ya cire shimfidar foot mat
lokacin da Mama tazo wucewa, yayi tsaye yana
kallon wata surar da bai taba gamo da irin ta
ba.. Kai ya kasa daurewa saida yayi mata
sallama.. Ta dago ido ta dube shi tare da
amsawa, sautin muryarta ya kara rikita shi ya
bita da sauri donAllah ko zaki 5mins kadai in
tambayeki? Ta tsaya caka tana dubansa, dogo ne
sosai "Allah yasa na sani" yace donAllah anan
garin kike? Tambayar tasata a mamaki tace eh
mana, amma ban taba ganinki ba sai yau. Tace
kasan daurowa take , gsky ne, ah suna nan Al-
Ameen ina minna amma nan gidan kaka ta ne,
na kawo Mamana ne ma yanzu sau dayawa ina
zuwa nan shiyasa kikaji na tambayeki. Haka ne
yau ne Allah ya nufa zamu hadu. Ya sauke
numfashi gsky ne, allah ya hadamu kuma take
nan kin kwanta min a rai ko zan san sunanki? Ta
dan kauda kai yanayin mata saida gabansa ya
fadi tsoro ya kamashi kada ya sha kayi. Ya
marairaice dan daure ki gaya min ba don hali na
ba, hali? Nasan halinka ne? Yace na mita da
bakin naci! Tayi dan murmushi Sunana Sakeena'
kai! Sunan nan ya dace da kykkyawar fuskar
nan! Anan unguwar kike? Ta dan kada kai can
gidan zani wajen kanwar Ummana, ok to gidanku
fa? Ta yatsuna fuska alamun ta kosa ta wuce,
harta fara takawa ya biyota na dameki ko? Yi
hakuri so ne ya kamani ki taimake ni, ta tsaya
ta dube shi da idanuwanta farare kal dasu tace
kasan Uban dawaki? Can tsallaken titi kenan? Ni
yarsa ce idan kasan gidan, nan ne gidan mu
saidai akwai matsala. Ya hadiye murmushin sa
Matsala? Na shiga uku a ina matsalar take?
Tace Abbana baya bari azo zance wajena yace
sai na gama karatu hasali ma bording skul
nakeyi daga hutu sai hutu ake ganina, ya danyi
shiru jim kafin yace to ya za'ayi yanzu Sakeena?
Gsky ba da wasa nakeyi ba ya kike ganin za'ayi?
Tace ban sani ba amma ina ganin hakuri zai fi
kyau, mu saurari lokacin kammala karatun, ba
kai kadai bane akwai wasu wadanda suka rigaka
magana kuma sun hakura. Yace su zasu iya ne
nikam bazan iya ba Sakeena! Ina sonki sosai
babu abnd nake rayawa a cikin rain aface na
aureki. Ta dan kara dubansa sai taji ya fara
zama cikin ranta. Matsalar kawai batasan yanda
zatayi dashi ba har tace yaje gidansu. Don haka
tace kayi hakuri Al-Ameen.. Ta wuce da sauri ta
barshi yana kira Sakeena! DonAllah tsaya mana
kiji.. Gidaje biyu ta wuce na ukun shien nasu
Inna Saude. Ta sa kai ciki tare da sallama
baraka dake tsaye tsakar gida tana gyara zaman
mayafinta ta juya da sauri baki sake suka
rungume juna.. Gidanku zan tafi yanzu a haba?
Wllh yanzun nan kewa Inna sallama har ta bani
dinkunan Umma tace dama nima ta aikoni
akansu, ina Innar? Tana ciki suka shige tare Inna
tace au Mama ce? Har kin rigata kenan tana
dariya ta zauna sannu Inna ina kwana? Ta amsa
lfy lau an dawo lfy? Tace wllh lfy lau inna, kinga
dinkinta dama za'aje kai mata Mama ta fiddo su
a leda ta daddaga kai amma atamfofin masu
kyau. Suka dan taba hira suka wuce dakin
Baraka kowacce ta cire after dress. Mama ta
fada katifa tace tun dazu ya kamata in shigo
gidan nan bakon unguwarku ya tare ni. Bako? A
ina?tace oho! Wai nan gidan Alh lado suke cewa
ko? Eh nan ne gidan kakarsa Al- Ameen yace
min sunansa, bakinta har kunne ta jawo
hannunta suka tafa ban mu kashe yar'uwa bakar
fata kice kinyi gamao da katar. Likita bokan
turai yau shiya kawo Maman tasa kenan. Ta ware
ido kina nufin Dr ne? Kwarai kuwa ko bai
kammala ba kiris ya rage, don tuntuni naji ana
fadin sabis yake, ta kama baki har kin kara min
son shi ina ma ace wann abu ya tabbata kusa
bikin likitoci, au kema likitance? Tace zauna nan
in gaya miki jiy-jiya Abba ya gaya mina bnd zan
karanta kenan, kuma gsky Al- ameen yayi min
matsalar kawai Abba. A'a ina cewa ya soke
maganar su Ya Ali? Eh mana to ai baki sani ba
soke maganar ita ta janyo min tsiyar. Kina zaton
su kawu baza suji haushi ba? Ance karatu zanyi
kuma wani yazo an bashi? Ai sai Umma tayi
bakin jini acikin gidan. Bansan yanda zanyi ba
shi kanshi yaban tausayi tahowata kawai nayi na
barshi kinsanni da karfin hali Baraka ta bata rai
kai yakamata a nemi mafita Al-Ameen yayi
kawata zan soki dashi don na hango kun dace
kwarai. Ta sata ta zabga tagumi ta zuba mata
ido, ina tsoron Abba Baraka bazan iya
dumfararsa da wann maganr ba bayan jiyan nan
yaja min kunne ya gaya min burinsa akaina ina
zansa raina nima inason Al-Ameen! Ta dafe
goshi ga koshi ga kwanan yunwa, Baraka tayi iya
tunaninta ta rasa mafita, sbd tsoron hanyar da
za'abi a dumfari Uban dwk don haka ta numfasa
tace to ai shikenan sai ku dauki hakuri idan
kuma yana iya dakatawa ya jiraki ko kuwa? Tace
kyaleni haushi ya isheni dauko wani topic din
kona manta da wann. Tayi yar dariya to ya skul?
Mu koma wancan fannin dame-dame suka faru?
Ta gyara zama suka tsinke da hirar makaranta
daga abinci sai sallah har zuwa bayan la'asar
lokacin da Mama ke niyyar tafiya da zarar ta
idar da sallah.Tana sallamewa yaro ya shigo wai
ana kiran Mama ta leko tace jeka kace ta tafi
Inna ta leko tace uwaki baki zuwa ko wanene?
Kai kace gata nan zuwa. Yaro ya fice inna taci
gaba da fada ba kyau wulakanci ko baki son sa
ki saurare shi ki bashi hakuri a zauan lfy, ta
shige daki Inna kenan bazaki gane ba. Ta maida
after dress dinta tasa mayafi tace Baraka zoki
rakani, donAllah ki tafi ke kadai kinsan sirrin da
zakuyi? Ta ja tsaki ta fito yana tsaye a kofar
gidan haba gimbiya, kuma saiki tafi kibarni da
tension? Ina kikeso nasa raina yau wllh ko abinci
na kasa ci sbd tunanin matsalar da kika ambato.
Tayi masa zuru tausayinsa ne zalla ke bin jinin
jinkinta tace kasan Allah nima tunani na ya kara
na rasa me zancewa Abba ganin yan'uwana ma
na jini ya dakatar dasu balle wani kuma
watakila kana bukatar auren ne da wuri kaga
Abba bazai amince ba. Ya goge zufar goshinsa
da hankici, don dai in jure ki karee sakandire zan
iya jira mana. Idan ma kinaso cigaba ne bayan
munyi aure ni zan dauki nauyin ki karanta duk
fannin da kikeso donAllah ki taimakeni kiyiwa
Abba wann bayanin. Ta dafe goshi! Wane zan
masa ya gane? Ya fada a ransa yace na dameki
ko? Yes nima nasan na fiye naci ga duk abnd
nake so. Yace mata tunda baki da abinyi ni ina
dashi abnd nake bukata daga gareki kawai ki
tabbatar min tsakaninki da Allah har cikin mind
dinki kina sona? Ki fada kanki tsaya kawai!
Mamana tana gab da fitowa zamu tafi.Tace Al-
Ameen na amince kar kaji wani shakku a ranka
amma...... Ya dan daga mata hannu don't sai it
pls! Kin faranta min rai Sakeena na tabbata zan
samu inci abinci ya wuce min. Sauran magana ki
kyale min, nace yanzu me zaki bani na rike na
alkawari? Al-Ameen fa na bata mmk na yadda
gaba daya ya sallama kansa gareta ko shiyasa
itama ya mamaye mata ko ina? Tayi dan
murmushi me zan baka kuwa? Ya nuna yatsanta
wann ring din yayi min kyau shi zaki bani, ai
bazai yi maka ba, inji wa? Miko shinan ki gani.
Ba musu ta zaro ta mika masa ya turawa
karamin yatsarsa zobe yayi zamansa daram
kamar daman can na sane.
BAKIN CIKI 1***2 Ya dubeta yana murmushi U
see? Mu biyu akayiwa zoben nan kika kama ke
kadai kika rike, tayi yar dariya "haka naji" "nima
kuwa hakan naji" amma matsalar ni bani da jar
azurfa dana baki wann kuma saidai kiyi warwaro
dashi ba dai zobe ba. Ta zubawa zoben ido yana
ta daukar ido ko in baki zoben haka? "Kawo" ai
yayi miki yawa gimbiya ayi min hakuri a biyoni
bashi in Shaa Allahu zan biya. To Allah ya baka
iko, ya kara zubo mata ido yace to ameen
gimbiyata. Ya cigaba da kallonta sannan ya
sauke numfashi wai yanzu zamu tafi gashi ban
gaji da ganinki ba. Yadda kikasan in saki a
aljihu in tafi dake. Tace ka saceni kenan? Yayi
yar dariya me karawa fuskarsa kyau da kwarjini
kamar yanda kika sace ni ba. Ji sukayi ana
tambaya ina Al-Ameen din ya nufa ne? Yace
gani Mama anan. Ta fada zaure da saurinta ta
fara dariya zoki ganta Mama donAlla! Ta kama
baki Oh ni Hafsatu Goggo fito kiga ikon Allah!
Itama yar tsohuwa ta fito ina kishiyar tawa duk
ta susuta min miji! Mama ta manne da bango ta
rufe fuska ruf da mayafi. Ta sulale kasa tun
kafin su karaso, Goggo zoki sha kallon yar bebi
ba irinki ba bude fuskar su ganki. Maman da
kanta ta bude fuskar yayin da take gaishesu. Ta
amsa cike da fara'a ah! Mashaa Allahu Al-
Ameen ka iya zabe, Allah yasa albarka Goggo
tace ameen dai. Ai ka kwantar da hankalinka nan
gida ne babu abnd zai gagara In Shaa Allahu!
Yace Allah yasa Goggo suka baro zauren Hajiar
na fadin kai fa nake jira karka shanya ni.. Gani
nan Mama, Mama tace Allah ya kiyaye ta amsa
da ameen. Ya gyara tsayuwa yace kingani? Bani
kadai nake sonki ba Sakeena sbd haka ki saurare
ni, tace ina nan ina sararonka Allah ya tabbatar
mana da alahiri, ameen gimbiyata to bari mu
lallaba tace Allah ya tsare amma zaka yi min
alkawari? Me zai hana? Fade shi indai ba zakice
in daina zuwa gunki bane , tayi yar dariya bashi
bane kayi min alkawarin zaka ci abinci idan son
samu nema mama ta dan jiraka kaci ko yaya ne,
kai Dr ne kasan matsalar rashin cin abinci ya
ware sosai yace waya gaya miki ni Dr ne? Tayi
nuni cikin gida yar'uwata dake nan gidan. Yayi
jim! Murmushi kawai yake fiddawa kafin yace its
true 4mnths back aka damka min letter of
appointment a ABUTH Zaria hope kinason Dr? ta
dube shi da gefen ido sai ya tsira mata ido
domin kallon yayi masa sosai ko shi kadai ya isa
amsar tambayarsa, in ba don son jin baki ba
bata ga ma dalilin wann tambayar ba don haka
ta juya zata shiga gida. Sakeena! Ya kirata a
sanyaye ta juyo dauke da murmushi tace a sauka
lfy Allah ya tsare ta karasa cikin gida don ta
lura idan ba hakan tayi ba bazai tafi ba kuma
ana jirransa. Gaba daya kasala ta sauko masa
ya sauke numfashi ya jima tsaye bakin zauren
sannan ya fito wajen mota inda Mamansa ke
jiransa. A hakikanin gaskiya Al-ameen ya kamu
da wata sabuwar cuta wacce shi kansa a
matsaynsa na likita bai taba cin karo da
maganinta ba. Duk iya karatnsa da yayi kuwa.
Sosai yake ji a ckn ransa idan bai auri mama ba
babu makawa zai fusknci matsala. Shi yasa
tunda ya damki hnya baya iya magana da kowa
illa addu'ar Allah yasa sakeena matarsa ce!
Hakazalika al'amarn yake wajn mama, tas!
Al'ameen ke neman rusa shirinta na son zurfn
karatu, kamar ynda tayi wa Abbanta alkawari. A
halin ynzu kam shirun da tayi bisa shimfida tun
shigowarta gidan, tunanin auren al'ameen take
yi, kuma da son samu ne kar aja lokaci mai
tsawo. Anya abbanta zai yarda kuwa? Baraka ma
taso ta kauda mata wannan tunanin, amma ta
kasa. Ta yunkura ta tashi zaune tace, "bari in
wuce baraka". Kallnta kawai take yi, ta mika
hannu ta jawo jakarta ta rataya, tayi waje.
Yaynda baraka ta dauko mayafi ta biyo ta. A
dakin inna ta sameta suna sallama, hannunta
daya rike da ledar kayan dinkin umman ta, "ki
gaida min ita da kyau, sai na zo" tace, "to zata
ji insha Allahu". Ta juya suka fito tare da baraka.
Sawun tayoyn motarsa ta tsaya tana kallo tsawn
lokaci, kafn ta dubi baraka, "al'ameen ya wuce,
ban jin zan sake ganinsa......." "wannan mugun
zato ne, me yasa kike wa kanki mugun fata?" ta
kada kai, "ba mugun fata bane, sauya ra'ayin
abba shine fargaba na, tabbas babu abnda zai
hana shi dakatar da al'ameen, tunda ya iya
dakatar da 'ya'yan 'yan uwansa na jini daya".
Tace, "ni kuwa a tawa wautar gani nake
al'ameen zai iya jiranki, tnda yana sonki". "lallai
kam wauta, baki ganin al'ameen ya girma sosai,
na tabbata a halin yanzu iyaynsa basu da wani
buri da ya wuce su ga yayi aure. Yaushe zasu
lamunci jirana shekaru barkatai masu zuwa?
Banzan tunani kike yi baraka, kawai ki yarda zan
iya rasa al'amee".! Ta fizgo hannunta suka wuce
tana fadin, "ni banji a jikina ba, kuma ai Allah
na nan, ba sai mu kai kukanmu gunsa ba" "haka
ne, dole in gayawa Allah, don gaskiya ban taba
jin wani sauyi a zuciyata ba,

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login