Showing 18001 words to 21000 words out of 122360 words
Chapter 7 - A sanadin Son ki Hausa Novels Document complete by Aisha A Muhammad Sanaz.txt
su tukunna ya dawo da idanun shi jikin shi inda yaga yanda ya jik'e sharkaf da ruwa, wani irin sanyi ne yake ji yana ratsa cikin jikin shi sosai.
"Yalla6ai kayi hak'uri don Allah kada ka fad'awa su Alhj da Hajia nasan korata zasu yi, ka rufa min asiri amman sam wannan yarinyar bata kyauta ba "
D'an murmishi Sabeer yayi ya bud'e baki zai yi magana atishawa ta taho nan ya fara yin ta sai da ya jira ta sau 4 tukunna ta tsaya, driver sai sannu yake yi mishi gaba d'aya hankali shi a tashe.
"Don't worry driver kwantar da hankalin ka mu tafi gida sanyi nake ji "
Sai lokacin driver ya d'an ji hankalin shi ya kwanta, da sauri driver ya bud'e mishi kofar mota ya shiga sannan ya rufe tare da komawa driver sit ya zauna tukunna yayi wa motar key suka bar wajen.
Sanyi sosai Sabeer yake ji ga atishawar da yake faman yi but still idanun shi nakan hanyar da Suhaima tayi, sosai yake jin wani abu game da yarinyar da ya gani tsiwar ta ta birgeshi yana fatan ya sake sanya ta a cikin idanun shi anan gaba.
Har suka kusan k'arasa wa gida Sabeer na tuna abin da ya faru tsakanin shi da Suhaima yana wani murmishi shi kad'ai, abin ba k'aramin mamaki yake bashi ba ganin ta tsaye mishi a rai, gate man yana bud'e gate Sabeer ya hango ilahirin Iyalan Alhj Ahmad d'an fillo sun firfito suna tsaye kallo d'aya mutum zai yiwa Alhj Ahmad d'an fillo, Hajjah Hauwaa da Alhj Hussien Daddy da Hajia Faridah Mumy a karanto tsantsar tashin hankali saboda sun nemi d'an lele an rasa inda yake kuma ba'a san inda ya tafi ba ga wayar shi a gida ya barta, tuni jikin driver ya fara 6ari na tsoro.
A hankali Sabeer ya bud'e motar ya fito ko driven bai tsaya jira ba, suna ganin fitowar shi suka saki ajiyar zuciyar kwanciyar hankali tare da tahowa inda yake hankalin su a tashe ganin jikin shi jagwab da ruwa, cikin rud'ewa Alhj Ahmad d'an fillo ya rik'o kafad'un Sabeer yace
"Sabeer wane shege ne ya jik'a ka haka? "
D'an murmishi Sabeer yayi kafin yace
"Ba damuwar ku bace kada wanda ya sake min wani tambaya ku rabu da ni and then kada wanda yace zai tak'urawa driver ya fad'a mishi "
Yana gama fad'in haka ya jiyo zai tafi da sauri Mumy ta rik'o hannun shi tare da cewa
"Amman son........ "
Bata k'arasa fad'in abin da zata ce ba ya dakatar da ita da hannun shi tare da cewa
"Please Mumy "
Ya zame hannun shi yayi gaba zuwa part d'in su, gaba d'aya jikin su yayi sanyi sosai kuma hankali ya tashi sosai musamman ganin shi a jik'e kuma yana ta atishawa, suna ganin driver ya wuce ta gaban su bayan ya gama parking motar basu da ikon yi mishi magana saboda kada su 6atawa Sabeer rai.
Sabeer yana shiga bedroom d'in shi toilet ya shige wanka yayi da ruwan d'umi tukunna ya fito ya gyara jikin shi tsaf cikin wani 3quater ash colour da T-shirt white mara hannu, fesa different perfumes yayi bayan ya gama ya kwanta tare da lullu6e jikin shi da lallausan blanket, lumshe idanun shi yayi tamkar mai jin bacci amman ba baccin yake tunanin kawai Suhaima yake ya dad'a tuno d'an k'aramin bakin ta tana mishi tsiwa, shi kad'ai yake juyi kan bed yana murmishi, yana tuna yanda ta watsa mishi ruwa ta gudu dakyar bacci ya d'auke shi mai nauyi zuciyar shi fal tunanin yarinyar da suka had'u da ita.
Duk wannan abin da yake Mumy na tsaye ta jikin window duk abin da yake tana kallon shi cike da mamakin murmishin da yake, tana tunanin me yake tunani haka yake irin wannan murmishin, ganin ya samu bacci ne yasa ta bar jikin windown zuciyar cike da tunani.
***** ******** *****
Suhaima sai da ta k'arasa kofar gida tukunna ta tsaya da gudun da take, sai da ta daidaita kanta sannan ta shiga gidan da sallama a nutsen ta, kamar ba itace mai gudu yanzu ba, Aunty Aliyah da ke zaune kan kujera tana wankin kaya ta amsawa Suhaima sallamar tana d'ago kanta ta kalle ta tare da cewa
"Suhaima sai yanzu kin dad'e yau hala surutun kuka yi aka tsayar da ku "
Wata dariya ce ta kubce wa Suhaima ta fara yi har da rik'e ciki da hawaye, cikin mamaki Aunty Aliyah take kallon ta kafin ta kuma cewa
"Lafiya Suhaima dariyar me kike haka? "
Amman Suhaima ba bakin magana sai da dariyar ta take, sosai Aunty Aliyah ta saki baki da hanci tana kallon Suhaima da ke dariya tamkar wata mahaukaciya har abin ya fara bata tsoro har ta fara tunani ko gamo tayi a hanyar makaranta, dakyar Suhaima ta tsayar dariyar saboda ganin yanda Aunty Aliyah ta fara rawar jiki na tsoro, zama tayi kan saman kayan wankin da Aunty Aliyah ke wankewa tace
"Aunty wani abu ne ya faru lokacin da nake tahowa gida shi yasa kika ga ina dariya "
Ajiyar zuciya Aunty Aliyah ta sauke ta kwanciyar hankali don sai yanzu taji hankalin ta ya kwanta, kafin ta bud'e baki tace
"Me yafaru? "
Nan Suhaima ta bata labarin abin da ya faru tsakanin ta guy d'in nan, don Suhaima bata iya 6oyewa Aunty Aliyah abu saboda shak'uwar da suka yi da juna sosai sun zama tamkar wasu k'awaye ko irin Yaya da k'anwar ta, sosai abin ya bawa Aunty Aliyah dariya don har yanda Sabeer yayi Suhaima take kwatanta mata, cikin dariya tace
"Allah ya shirya ki Suhaima, yanzu da ace ya kama ki fah ko ya mare ki "
"Tabbb da sai na rama Aunty duk da yafi ni tsayi sai nayi tsalle na rama, amman fah Aunty kyakkyawa ne kingan shi tamkar wani balarabe mybe ma baya jin hausa shi yasa yake kallo na "
"Uhm Allah dai ya kyauta, amman Suhaima ki daina irin wannan gangancin don kada ki tsokani wani wataran mara hak'uri ya cutar mana da ke "
"Toh Aunty na daina insha Allah, har yanzu Yaya bai dawo ba? "
"Eh bai dawo ba mybe akwai abin da ya tsayar dashi "
"Allah ya dawo dashi lafiya "
"Amin "
D'an shiru suka yi na 'yan minutes Aunty Aliyah na cigaba da wanki, can tace
"Ni kuwa Suhaima ina Jiddah ne kwana biyu shiru? "
D'an murmishi tayi tare da cewa
"Aunty Jiddah tana nan lafiya, hidimar biki ce ta sanya ta a gaba amman mun yi waya da ita jiya da yamma a wayar Yaya "
"Oh haka ne fah sauran kwanaki nawa auren "
"Sauran 2 week's fah Aunty gashi na rasa me zan siya mata matsayin gift's "
Suhaima ta karasa fad'a cikin yanayin damuwa.
"Kada ki damu anjima zamu yi magana yanzu kije ki cire uniform kizo ki karya tukunna"
"Toh Aunty "
Tashi tayi ta nufi bedroom nata don canja kayan jikin ta, bayan ta canja kaya ne sai kawai ta k'urawa mirror ido tana kallon shi, ta fad'a tunani beautiful guy d'in da ta yi mishi tsiwa d'azu ta d'an jima tana tunanin shi a haka har sai da Aunty Aliyah taji ta shiru ta fara kwalla mata kira tukunna ta sauke ajiyar zuciya ta fito waje tana amsa kiran da take mata...
Aishat A Muh'd ✍🏻
💝 A SANADIN SON KI 💝
Written by
Aishat A Muh'd
♻EXCLUSIVE WRITERS FORUM
Dedicated to my Sadeey saNaz
Where are U guys dis page is dedicated to oll My sisters of (Exclusive Writers Forum), i luv U all my sisters i really luv U guys like totally 👄
PAGE 24-25
Bayan kwanaki 2 kamar yau ranar laraba da yammaci wajen 4:30,Suhaima tana zaune a bedroom nata gyaran wardrobe d'in ta take gefe d'aya kuma Aunty Aliyah zaune gefen gadon tana mik'o wa Suhaima kayan da ta linke ita kuma tana jera su a wardrobe sai hirar su suke cikin kwanciyar hankali.
"Assalamu Alaikum "
Kamar a mafarki Suhaima ta jiyo sallamar Jiddah, aikuwa da sauri ta wullar da kayan hannun ta da Aunty Aliyah ta mik'o mata, da gudu ta fita waje zuwa tsakar gidan cikin farinciki.
Jiddah tana tsaye a tsakar gidan sai murmishi take tana rarraba ido don hango ta inda Suhaima zata fito, tana hango fitowar ta a d'aki aikuwa da gudu ta k'arasa inda take suka rungume junan su suna dariya cikin tsantsar farinciki na jin dad'in ganin juna don anjima ba'a had'u ba.
Cika junan su suka yi cikin murmishi Suhaima tace
"My besty sannun ki da zuwa"
Kunshe da marmishi kan face d'in Jiddah tace
"Yawwa tawan kwana da yawa "
Ta fad'i hakan suna kok'arin k'arasa shiga d'akin Suhaima, cikin fara'a Aunty Aliyah tace
"Lale maraba da mutanen birni Jiddah kece tafe yanzu da yamma? "
Zama Jiddah tayi akan sallayar da Suhaima ta shimfid'a mata a k'asa ganin kan gadon kaya ne akai, sannan Suhaima ta fita zuwa kitchen don samo wa Jiddah abin motsa baki.
"Aunty kam nice tafe yanzu, ina yini? "
"Lafiya qlau Jiddah, ya gida da iyayen ki? "
"Duk suna nan lafiya Aunty suna gaida ku "
(Hmmm Jiddah ta fad'i hakan ne kawai, amman gaskiyar zance iyayen ta basu san wasu su Aunty Aliyah ba, kawai suna jin tana basu labarin Suhaima duk a zaton su friend nata ne na schl, ko zuwa nan gidan nasu da take basu san da zuwan ba).
"Muna amsa wa, ya fama da hidimar biki don nasan satin da zamu shiga shine na bikin koh? "
Aunty Aliyah ta tambaye ta tana mik'ewa tsaye, cikin d'an jin kunya Jiddah tace
"Ehh Aunty haka ne, ina Yaya Aliyu? "
"Ya zagaya cikin gona ne amman yanzu zaki ga ya shigo "
Har Aunty Aliyah zata fita daga d'akin da sauri Jiddah ta tsayar da ita tare da sanya hannu cikin hang bag nata ta d'auko wani kyakkyawan invitation card guda biyar ta mik'awa Aunty Aliyah tare da cewa
"Aunty wannan card d'in d'aurin aure ne na Yaya Aliyu da na Baba Adamu ne "
"To shikenan zan bashi idan ya shigo "
D'an marairaice fuska Jiddah tayi tare da cewa
"Amman Aunty zaku je ai? "
D'an murmishi tayi tare da cewa
"Me zai hana Jiddah insha Allah zamu je, Allah ya kaimu dai lokacin da rai da lafiya "
"Amin Aunty, sannan don Allah ki dad'a tunawa Yaya Aliyu sauran kwanaki 2 d'aurin aure zan zo na tafi da Suhaima "
"Zan fad'a mishi Jiddah kuma zai barta insha Allah "
'Yar dariyar farinciki Jiddah tayi tare da cewa
"Yawwa Auntyn mu ngde "
Daidai lokacin Suhaima ta shigo d'akin hannun ta d'auke da k'aramin tire wanda ta sanya abinci aciki da kuma lemon so6o acikin k'aramin jug na roba sai cup d'in shi k'arami, ajiye wa tayi gaba Jiddah Aunty Aliyah kuma ta fita don ta barsu su yi hirar su.
Bud'e plate d'in Jiddah tayi aikuwa ta had'a ido da wani lafiyayyen dambu wanda yasha zogale da gyad'a ga ainahin man k'uli da kuma yajin da aka daka da kayan k'amshi da tafarnuwa, muk'ut Jiddah ta had'iyi yawu saboda tana son dambu sosai, dariya ce ta kubce wa Suhaima ganin yanda Jiddah take had'iyar yawu don kawai taga dambu.
Hararar wasa Jiddah tayi mata tare da cewa
"Tun da dariya kike min na fasa baki cup cakes d'in da nayi miki Aunty Aliyah da Yaya Aliyu zan bawa "
Danne dariyar ta Suhaima tayi tare da rik'o hannun Jiddah tana cewa
"Haba tawan just kin ban dariya ne ganin yanda kike had'iyar yawu but na daina"
Gid'a kai Jiddah tayi kawai saboda ta cika bakin ta da dambu ba damar tayi magana har wani lumshe ido take saboda dad'in da yayi mata, hannu Suhaima takai kan jug ta zuba mata so6on a cikin cup ta ajiye mata kusa da ita, sannan ta koma wajen wardrobe tana cigaba da gyaran kayan suna d'an hira da Jiddah jefe jefe har ta kammala cin abincin ta taya Suhaima k'arasa gyaran kayan, bayan sun gama suka fita zuwa tsakar gidan inda Aunty Aliyah da Yaya Aliyu suke zaune a saman tabarma shigowar shi kenan babu dad'e wa, nan suka gaisa da Jiddah tare da yi mata fatan alkhairin auren da zatayi tare da 'yar nasiha, sosai Jiddah taji dad'in haka tare da yi mishi godiya duk jikin ta yayi sanyi.
Suna nan zaune akayi kiran sallahr mangarib nan Yaya Aliyu yayi alwala ya wuce masjid, yayin da Suhaima, Jiddah da Aunty Aliyah suka yi nasu alwalan tare da gabatar da tasu sallahn.
Bayan sun idar ne da sallahr Jiddah tayi wa driver d'in ta waya, babu dad'e wa yayi sallama a kofar gidan Jiddah ta tashi taje inda yake tsaye kofar gida ta kar6i abin da ta buk'aci ya kawo mata wata 'yar bag ce black mai kyau madaidaiciya wadda zata cinye kayan mutum set 5 a ciki.
Shigowa gidan tayi tare da ajiye bag d'in gaban Suhaima tace
"Besty ga ankon ki fah ki duba ki ga yayi miki "
Sakin baki Aunty Aliyah da Suhaima suka yi suna kallon ta cike da mamaki, bayan d'azu da safe Yaya Aliyu yace gobe zai bata kud'in ankon da na gifts d'in da zata siya mata sai gashi kuma Jiddah ta zo mata dasu.
Murmishi Jiddah tayi ganin yanda suke kallon ta kafin tace
"Aunty wannan kallon fah, ni ku duba kuga yayi? "
Ta k'arasa magana cikin shagwa6a ganin sun k'i bud'e bag d'in tamkar masu jin tsoron akwai wani mugun abun aciki, ya sanya Jiddah ta janyo bag d'in kusa da ita ta bud'e, sai ga wasu tsadaddun kaya kala hud'u ta fito dasu masu matuk'ar kyau da tsada, swiss atampha, lace guda biyu da kuma wa wani material Light pink mai haske da abin nad'in kai pink shima amman mai duhu, anyi d'inkin gown ajiki yayi masifar yin kyau, sai shoes and hang bag set d'aya da su watch k'irar gucci na mata da kuma abin hannu, sark'a d'an kunne kai abubuwan kyalakyale sosai Jiddah ta zuba wa Suhaima.
Rasa bakin godiya Suhaima da Aunty Aliyah suka yi har sun bud'e baki zasu fara godiya Jiddah ta hana su dole suka hak'ura amman gaskiya Jiddah mutum ce tayi musu hallaci tayi musu abin da baza su ta6a mance wa da ita ba har abada, abun kyautata wa take musu tamkar wasu shak'ik'an 'yan uwanta na jini, babu tsangwama ko kyankyamin su da take duba daga inda ta fito, su kansu sun san Jiddah iyayen ta masu kud'i ne sosai bana wasa ba.
A haka Yaya Aliyu ya shigo ya same su sam ya nuna wa Jiddah bai ji dad'in abin da tayi ba da ta bari shi zai bata kud'i taje ta siyowa Suhaima kayayyakin ko nawa ne, nan Jiddah ta nuna mishi ita fah yanda ta d'auki Suhaima tamkar 'yar uwarta ta jini zata iya yi mata komai har idan tana dashi dole yasa Yaya Aliyu hak'ura yayi mata godiya daga k'arshe kuma ta tashi zata tafi har bakin motar su Suhaima da Yaya Aliyu suka rakata suna godiya tana nuna musu batasan godiyar nan, anan Aliyu yayi mata alk'awarin zuwa ta tafi da Suhaima idan ta dawo sosai Jiddah da Suhaima suka ji dad'in hakan, Kafin suyi sallama kuma ta shiga motar driver yaja suka tafi suna masu d'agawa junan su hannu har sai da motar ta k'ule tukunna Yaya Aliyu ya rik'o hannun Suhaima suka wuce gida.
****** ********** ********
Kwance yake saman kujera cikin garden ya zurfafa a cikin tunanin yarinyar da suka had'u, tsawon wajen kwanaki 5 da had'uwar su amman ya kasa manta ta koyaushe cikin tuna beautiful Face nata yake, cikin mafarkin shi da farke yake tunanin yarinyar da baisan sunan ta had'uwar su ta farko da junan su.
Shi yasan ba sonta yake ba duk da bai ta6a son wata mace ba, but why ya damu da ita har haka, duk san da ya tuna ta yana jin bugun heart nashi na k'ara k'arfi yana son tunano muryar ta da kyakkyawar surar ta yana son Allah ya k'ara had'a su koda sau d'aya ne ya ganta ya sake jin daddad'ar muryar ta.
Sake gyara kwanciyar yayi yana mai lumshe ido hango kyakkyawar face nata yayi lokacin da take mishi tsiwa tare da yanda cute lips nata suke motsawa kamar a lokacin take mishi tsiwar haka yake ji.
Ji yake bazai iya jure ba zumbur ya mik'e tsaye tare da nufar side d'in su da saurin shi kamar ba Sabeer ba, yana tashi a wajen Fadilah ta fito daga ma6oyarta ta zauna kan kujerar da ya tashi tana mai shinshina kan kujarer tamkar Sabeer ne zaune a wajen tsabar fitinar ta, d'ago eye's nata tayi wanda suka yi ja cikin wata irin murya tace
"I luv U Sabeer, ina maka son da bazan iya zuba ido ka so wata mace a rayuwar ka ba dole nasan ta yanda zanyi na karkato hankalin ka gare ni "
Tana gama fad'in haka ta tashi tare da wuce wa side d'in su Sabeer...
Aishat A Muh'd ✍🏻
💝 A SANADIN SON KI 💝
Written by
Aishat A Muh'd
♻EXCLUSIVE WRITERS FORUM
Dedicated to my Sadeey saNaz
PAGE 26-27
Yana k'arasa wa part d'in su bedroom nashi ya shiga yayi wanka tare da shirya cikin wani blue jeans da T-shirt red yayi kyau cikin sauri sauri ya fesa perfumes tare da d'aukan phone's nashi ya fito zuwa parlour.
Akan dinning table ya hango Mumy, Daddy da Fadilah suna yin lunch abin su, ganin shi da Mumy tayi yasa ta cewa
"Son k'araso kaci abinci "
Yana nufar hanyar fita a parlourn yake cewa
"Mumy sauri nake zan fita sai na dawo "
Kafin wani ya k'ara magana ya fice da sauri, da ido suka raka shi cikin zuciyar Mumy tana mai mamakin abin da ya canja mata yaro lokaci d'aya don da ba haka Sabeer