Showing 111001 words to 114000 words out of 122360 words

Chapter 38 - A sanadin Son ki Hausa Novels Document complete by Aisha A Muhammad Sanaz.txt

da ya d'aura ma aure da Ladidi da yake d'an shi likita ne, bayan na d'an fara magana ne na saki Ladidi saki uku wadda itama alokacin ciwon yaci k'arfin ta har ta kwanta, daga nan liman ya taimaka min da kud'in mota na taho gida na nemi afuwar ku don nasan hakk'in ku ne yake bibiyar ta dakyar na iya kawo kaina garin nan wannan shine tak'aitaccen labarina tun bayan bari na gida, ina sake neman afuwar ku 'ya'yana ".




Suhaima kuka take sosai najin irin azabar da mahaifin su yasha a hannun muguwar matar nan, Cikin rad'a Sabeer yace
"Baby ba kuka zaki yi ba godewa Allah zakiyi da ya tseratar da Baba daga hannun ta "


Nan Aliyu ya dad'a saukowa daga fushin da yake da mahaifin shi jin irin azabar da yasha, sosai Baba Adamu ya dad'a yi musu nasiha kafin kuma ya nunawa Baba surukin shi wato Sabeer da kuma surukar shi Aliyah sosai Baba yaji dad'i da ganin yanda yaranshi suka dace da samun abokanan rayuwa nagari, bakin shi yak'i rafuwa saboda jin dad'in yanda su Baba Adamu da Babaa Lantana suka rik'e mishi yaran shi godiya sosai yayi musu da addu'o'i sun sha shi a wajen shi, daga k'arshe Baba Adamu yace


"Idan Allah ya kaimu gobe Aliyu ya kamata ka kaishi asibitin birni ya dad'a ganin likita sannan kuma tunda babu d'aki anan wanda zai na kwana sai ya koma gidan mu tunda muna da d'akuna ya zauna aciki kafin ya warware asan abin yi "


Kowa ya aminta da abin da Baba Adamu yace Aliyu da Suhaima sun rasa wace irin godiya zasu yi wa bayin Allahn nan tun suna yara suke d'awainiya dasu gashi har girman su basu kyale su ba, daga haka Baba Adamu ya tashi suka tafi don Mahaifin su Suhaima yaje ya kwanta ya huta.




Bayan sun tafi ne Jiddah take kiran Yah Aliyu a waya bazata samu damar zuwa yau ba sai gobe, sun d'an ta6a hira da Suhaima duk da ba'a cikin nutsuwar ta take ba, kiran sallahr azahar ne ya tashe su daga nan kowa ya fara kok'arin haramar yin sallah.






Bayan sallahr ishsha ne hadari ya had'u a garin sosai dole ta sanya Suhaima d'aukan abincin su ta shigo dashi d'aki saboda yau babu zaman waje ruwa daf yake da ya sakko, agurguje ta dafa ruwan wankan su ta d'ura wani a flaks ragowar kuma ta zuba a bokiti mai murfi ta wuce d'aki, cikin toilet takai ta ajiye sanann ta koma d'akin Aunty Aliyah wadda take zaune tana sanyawa Ameer kayan sanyi saboda yanda garin iska take kad'awa, zama Suhaima tayi tana jan kumatun Ameer shi kuma yana yi mata dariya.


Hirar su suke yi inda Aunty Aliyah take taya Suhaima murnar dawowar mahaifin su, bayan ta gama sanya mishi kayan Suhaima ta d'auke shi tana mishi wasa, Aunty Aliyah ta mik'e ta shiga cikin bedroom d'in ta bata dad'e ba ta fito hannun ta rik'e da wata roba da abu aciki sai wani cup kuma a hannun ta, zama tayi kusa da Suhaima tana cewa


"Kin ga tun safe na had'a zan baki amman dawowar Baba yasa na mance kinsan dama baki k'arasa sha ba koh? "
Ta fad'i tana kallon Suhaima wadda ta ta6e fuska take son yin shagwa6a tace
"Kaiii Aunty wallahi ni nagaji da shan irin wad'annan abubuwan fah? "


'Yar dariya Aunty Aliyah tayi kan tace
"Yarinya yanzu kika fara sha kuwa wani abin ma sai kin haihu kuma ba abu ne wanda zai cutar da ke ba "


Tana gama fad'in haka ta bata na cup d'in ta shanye sannan ta tsiyaya mata na robar ta shanye daman ragowar cup biyu ne dakyar ta k'arasa shan kamar zatayi kuka ita dai Aunty Aliyah dariya tayi cikin zuciyar ta tana cewa da kanki zaki dawo neman shi yarinya.




Ganin an fara yayyafi ne yasa Aunty Aliyah fad'a mata ta tafi d'akin ta, haka ta tashi tare da yi mata sai da safe ta wuce d'akin ta, tana shiga d'akin aka saki wata tsawa batasan lokacin da ta fad'a kan bed ba ta tukunkune jikin ta na 6ari saboda tsorata.


"Washhh Allah nah! Baby kin karya ni "
Taji an fad'a a kusa da ita da wata irin murya da ta sanya Suhaima k'ara rikicewa ga d'akin da duhu, tana kok'arin sauka daga kan gadon taji an sanya hannun an kamota tare da janyo ta jikin shi, bud'e baki tayi zata saki ihu taji an rufe mata da bakinta ashe Sabeer ne ya dawo batasani ba lokacin tana d'akin Aunty Aliyah.


Had'e lips d'in shi yayi da nata yana wani irin passionate kiss jikin Suhaima rawa yake sosai don ta tsorata walk'iya akayi wanda har haskenta ya ratso ta window d'in d'akin nan Suhaima taga ashe Sabeer wata ajiyar zuciya ta sauke kafin ta kwace bakinta ta d'auki pillow tana bugun shi na wasa cikin kukan shagwa6a take cewa


"Shine ka tsorata ni koh?, sai na rama nima"


Kare dukan yake yana dariya yace
"Haba sweetie nah sai dai ki rame kuwa "


Gajiya tayi ta ajiye pillow tare da cewa
"Bazan ma kwana a d'akin ba komawa zanyi d'akin su Yah Aliyu "


Kok'arin tashi take ya sake janyo ta jikin shi ya rungume ta yana cewa
"Ke yanzu aka ce kije sai ki tafi? "
"Eh mana bama sai ance naje ba "
"Lallai Baby da sauran yarinta akan ki, sai ki tafi ki bar mijin ki anan suma tak'ura musu zaki yi babba dake ki wani tafi d'akin su "


Har ta bud'e baki zata sake magana ya sanya hannu ya rufe tare da cewa
"Yunwa nake ji Baby "
Sai lokacin ta tuna ko abincin rana bai ci ba saboda baccin da ya d'auke shi sai daf da la'asar ya tafi kuma ya tafi masallaci bai dawo ba sai yanzu gashi daman a makare aka gama abincin ranar.


Hannun shi ta kamo ta zaunar dashi kan carpet sanann ta zuba mishi tuwon shinkafa miyar bushashshen ku6ewa tare da manshanu ga yajin daddawa mai dad'i agefe, langa6e wa yayi a baki zata bashi bata da yanda zata yi ta fara bashi da hannun ta shima yana bata, kad'an suka iya ci ya 6ata lokaci yana lashe 'yan yatsun nan nata dakyar ya saki ta bashi tea mai lemon tsamin da ta dafa mishi ya sha, kwashe kwanukan tayi ta ajiye su waje d'aya ba damar fita kai su kitchen saboda ruwan da yayi k'arfi, rufe k'ofar d'akin tayi tare da sanya key sannan ta saki labulen window bayan ta gama ta wuce toilet don wanke hannun ta sannan ta had'a mishi ruwan wanka.


Tana tsaka da had'a ruwan ne ya shigo cikin bathroom d'in da sauri Suhaima ta juya taga Sabeer ne ya cire kayan shi sai k'aramin towel nata da ya d'aura a kugun shi wanda dakyar ya ritsa shi, hannu ya sa ya matsar da ita ya had'a musu ruwan dukka su biyun kafin ta ankara ya janyota jikin shi ya fara cire mata kaya zata yi magana kenan ya girgiza mata kai idonshi cikin nata, sunkuyar da kanta tayi kawai tana jinshi ya cire mata kayan nata tsaf.




Bayan sunyi wankan ne sukayi brush sannan suka fito daga bathroom d'in, Suhaima ta shirya cikin wata doguwar riga ta bacci mai siririn hannu cotton ce ta shafa perfume da humrah ta had'e gashin ta cikin ribbon tayi parking d'in a gefe don kada ya hanata bacci, Sabeer kuwa yana sanye da boxer d'in shi duk abin da take yana bin ta da kallo jira kawa yake ta gama shiryawa yaji ta a cikin jikin shi.




Kasa jira yayi ta gama shirin ya tashi ya d'auko ta saman bed ya sauke ta tare da kashe fitilar d'akin wadda take amfani da batir, kafin Suhaima ta fara yi mishi korafi ya had'e lips d'in su waje d'aya, nan fah Suhaima ta fara kuka tana zame jikinta aikuwa Sabeer ya rikice mata sosai wasu zafafan sak'onni yake turata mata wanda ya sanya Suhaima sakin jikinta ta biye mishi ba tare da ta sani ba.


Wannan daren sun faranta shi ya zame musu tamkar daren su na farko, Sabeer ya nuna mata tsantsar son da yake mata yana kuka yana rokanta kada ta rabu dashi, bayan komai ya kammalu ne ta fara zum6ura baki tana k'unk'uni, abin ma dariya ya bashi sosai nan ya 6ige da aikin rarrashi kan su wuce suyi wanka suna kwanciya bacci mai dad'i yayi awon gaba dasu, zuciyar kowa fes da farinciki ga kuma yanayin garin da yayi dad'i suna rungume da junan su suka yi bacci............










Aıʂɧąɬ A Mųɧ'ɖ ✍🏻


*A SANADIN SON KI*








Wྂrྂiྂtྂtྂeྂnྂ bྂyྂ
Aྂıʂɧąɬ Aྂ Mྂųɧ'ɖ




ɖɛɖı¢ąɬɛɖ ɬơ ɱყ ʂąɖɛɛყ ʂąŋąʑ




♻ *єχ¢ℓυѕινє ωяιтєя'ѕ fσяυм*





*PAGE 112*














Washe gari tun safe da wuri Aunty Aliyah ta kammala abin karin safe ta aikawa da Baban su Aliyu, har Aliyu ya fita schl bata ji motsin Suhaima ba, ganin ta gama komai ne ya sanya ta zura hijab ta d'auki Ameer suka tafi gidan su don gaida Baba Umaru.




Suhaima wadda tsabar gajiyar da tayi ya hanata tashi da wuri tun sallahr asuba da tayi ta koma bacci ko shima Sabeer yana dawowa daga masallaci ya rungume kayar shi suka cigaba da baccin su hankali kwance.




Suna tsaka da baccin su mai dad'i ne Jiddah ta k'araso gidan cikin d'oki da zumud'i take rafka sallama, kamar a mafarki Suhaima taji muryar Jiddah na sallama don haka da sauri ta sauko daga gadon ta fito zuwa waje, had'a ido suka yi da juna wani ihun murna suka saki tare da nufar juna da gudu suka rungume junan su cikin farinciki kamar wad'anda suka shekara basu ga junan su ba.


Ihun sune ya farkar da Sabeer daga baccin da yake gane muryar Jiddah ne ya sanya shi jan d'an k'aramin tsaki yasan yanzu zata zo ta dame su bayan yau yana son kasance wa da Babyn shi kusa dashi, don ba k'aramin kewarta yake ba wannan Jiddah duk zata 6ata mishi planning d'in shi tashi yayi ya shiga toilet don yin wanka.


Sakin junan su sukayi tare da k'urawa junan su ido na tsayin mintuna can Suhaima tace
"Jiddah kin k'ara k'iba da kyau ko dai an samu k'anin Islam ne? "


Dariya Jiddah ta saki tare da cewa
"Tabbb lallai yarinya don bakisan wahalar haihuwar bane ai sai na huta sosai kafin na sake, ke dai muna jiran naki nan da 'yan watanni "


Murmishi Suhaima tayi tare da juya eye's ball d'in ta tace
"Ni dai yanzu amarci muke ci sai mun gama tukunna "


Kama ha6a Jiddah tayi tare da cewa
"Iyyyyeee! Lallai yarinyar nan naga alama Yah Sabeer ya koya miki rashin kunyar shi "


Murmishi kawai Suhaima ta sake yi kan tace
"Ina zamu zauna d'aki ko waje? "
"Kaiii bari nasha iska a waje tukunna ina Aunty Aliyah da Yah Aliyu, hala ma yanzu kika tashi daga bacci? "


Kallon kanta Suhaima tayi sai yqnzu ta tuna da sleeping dress d'in da yake jikinta don ma cotton ce kuma doguwa,


"Sallamar ki ce ta tashe ni fah, Aunty Aliyah ina tunanin ta fita Yah Aliyu kuma schl ya tafi"


"Yah Aliyu ya koma makaranta ne? "


"Eh an d'an jima ma da komawar shi, wai ni ina Islam ne? "


Dariya Jiddah tayi kafin tace
"Zamu shigo kenan muka had'u da Babaa Lantana ta dawo daga wata barka shine ta kar6e ta "


"Okay na d'auka baki zo da ita ba nace nayi fushi dake "


"Haba ni na isa Besty na, na taho miki da ita "


Murmishi Suhaima tayi tana cewa
"Kin kyautawa kanki ba don haka ba da sai dai ki koma gida "


Suna tsaka da hirar su Sabeer ya fito daga d'aki yayi wankan shi ya sanya wata T-shirt yellow da jeans black, suna had'a ido da Jiddah ya watsa mata harara abin sai ya bata dariya aikuwa ta kwashe da dariya tare da cewa


"Ohh ni Yah Sabeer me nayi haka daga zuwa na sai harara "


Kallon Suhaima yayi tare da cewa
"Baby nah tashi kije ki wanka ki rabu da wannan mai zuwan sassafe gidan mutane "


Murmishi Suhaima tayi ta tashi tare da wuce wa d'aki, sai da ta fara gyara d'akin tsaf sannan ta wuce toilet ta wanke shi sannan ta fara wanka.


"Allah Yaya kana tak'ura min yanzu fah 11:50 kace nayi zuwan sassafe "


Rage murya yayi kafin yace
"Saboda zaki hanani hutawa da mata ta ne na tsayin yini guda "


"Tabbb Yaya yanda nayi missing d'in Suhaima dasu Aunty Aliyah ai kwana zanyi anan sai dai ka koma kwanan zaure har na tafi "


Ta k'arasa maganar da tsokana tana dariya, harara ya dalla mata kafin ya murd'e 'yan yatsun ta kad'an yana cewa


"Kin fah rainani yarinyar nan amman zan sanya Khaleel yi miki kishiya ko zaki yi hankali "


"lallai ma Yayan nan an fad'a maka ina tsoron kishiya ne tazo mana ba'a kaina zata zauna ba "


Hirar su nan suka cigaba dayi har yana fad'a mata dawowar Baban su Suhaima tayi murna sosai da farinciki, da haka Suhaima ta fito har tayi wanka ta shirya cikin wata doguwar riga ta atampha tayi kyau sosai sai tashin k'amshi take, tun da ta fito Sabeer ya kafeta da eyes, cikin dariya Jiddah tace


"Yah Sabeer irin wannan kallo ai sai kasa ta fad'i "


Murmishi kawai yayi indai Jiddah ce bakin ta baya shiru idan taga abu, zama tayi nan kusa dasu bayan ta d'auko musu abin karyawar su anan take taya Suhaima murnar dawowar mahaifin su, murmishi kawai Suhaima tayi tare da cewa nagode, nan suka karya bayan sun gama ne Sabeer ya fita bai dad'e da fita ba Aunty Aliyah ta dawo da Islam a hannun ta d'ayan hannun kuma Ameer ne ta rik'e mishi hannu da yake ya fara tafiya, kar6ar Islam Suhaima tayi tana fad'in Masha Allah ganin yanda tayi 6ul6ul da ita gwanin sha'awa, cikin jin dad'i Aliyah suke gaisawa da Jiddah, suna gama gaisawa ne Aunty Aliyah da Jiddah suka fara kok'arin girkin rana yayin da Suhaima ta baiwa hankalin ta kan su Islam da Ameer tana musu wasa suna dariya.




Sunsha hira sosai tsayin yini guda don tun da suka ci abincin rana akayi sallahr azahar suka k'ule a d'aki suna fama zuba hira, sai wajen biyar driven Jiddah ya k'araso suka yi sallama dasu Suhaima ta tafi gida ko had'uwa da Yah Aliyu bata yi ba.






AFTER 3 MONTH'S




Acikin wad'annan watannin abubuwa da d'an dama sun faru daga cikin abubuwan da suka faru akwai warkewar mahaifin su daga lalurar da ta same shi da kuma samun cikin da Suhaima tayi, sosai Sabeer yayi matuk'ar farinciki da wannan cikin tsabar murna har kuka sai da tayi don yana masifar son yara, sai dai kuma wannan cikin akwai shi da laulayi fiye da na baya sosai Suhaima take shan wahalar shi duk ta rame tayi fari koda yaushe cikin amai abinci kuwa sai ta kusan yini batasa komai a bakin ta ba, duk abin da tayi sha'awar ci Yah Aliyu da Sabeer suna kok'arin nema mata shi kulawa sosai take samu daga mijinta, Yayanta da Aunty Aliyah ga su Babaa Lantana nan har Baban ta ma kullum sai ya shigo dubata kuma sai ya taho mata da d'an abin kwad'ayi gaba d'aya yayi wani sanyi kamar ba Umaru ba, Jiddah tayi farinciki sosai da albishir d'in da Sabeer yayi mata na Suhaima tana da ciki.




"Baby nah yau me zaki ce ne? "
Sabeer ya tambaye ta yana sanya kaya fitowar shi daga wanka kenan.


Kallon shi tayi idanun ta tap da kwalla tace
"Ni bana sha'awar cin komai "
K'arasa sanya kayan yayi sannan ya zauna kusa da ita tare da d'ago ta ya d'aura ta kan k'afafun shi, kallon ta yake cikin tausayi yace
"Bazan barki baki ci komai ba Baby ki fad'a min please "


Shiru tayi na d'an mintuna kafin tace
"Zan sha fruits toh sun ishe ni "


D'an murmishi yayi kan yace
"Yawwa Baby nah haka nake son ji bari naje na samo miki "


Kwantar da ita yayi saboda jikin ba k'arfi, ya bud'e mata curtains d'in window da na k'ofa don ta samu iska tana shigowa, sannan ya dawo yayi kissing nata a goshi ya fita, ya dad'e tsaye a k'ofar gida yana tunani don duk kud'in da yazo dasu sun k'are ragowar d'ari biyar ce dashi yanzu ya siyowa Suhaima fruit's da ita sun k'are, gashi gobe ko anjima idan tana son wani abu baisan yanda zai yi ba kuma shi bazai ta6a neman kud'i wajen Aliyu ba wanda shima fama yake da hidimar karatu ga d'aukan ciyar su abin da yawa gaskiya gashi duk master card d'in shi da atm card's nashi duk suna gida bai taho dasu ba da wannan tunanin ya tafi.




Wajen 30 minute's da fitar shi ya dawo lokacin Aunty Aliyah ta shiga duba ta kuma tana tambayar ta abin da zata ci, d'auko wani bowl na silver yayi da wuk'a bayan ya wanke fruits d'in zama yayi saman carpet din d'akin zai fara yanka mata Aunty Aliyah tace


"Sabeer kawo na yanka mana "


Murmishi yayi yana cewa
"Mamin Ameer ki barni aiki nane kije ki huta kawai "
Itama murmishi tayi kafin ta wuce ta fita, Suhaima na kallon shi har ya gama yanka rabi iya yanda zata iya sha anjima sai ya yanka mata sauran.


Kusa da ita ya dawo tare da tashin ta zaune ya jingina bayanta da pillow ya fara bata fruit d'in a hankali take bud'e bakin yake bata, duk da Sabeer yana iyakar d'auke damuwa akan fuskar shi ta rashin kud'i da kewar iyayen shi da 'yan uwan shi ga kuma rashin lafiyar Suhaima duk dashi wannan laulayi ne sai anyi hak'uri na d'an wani lokaci amman lalurar ta tsaya mishi a rai har wani d'an rame wa yayi amman duk da haka sai da Suhaima ta gane akwai wani abin da yake damun shi koda ta tambaye shi baya sanar da ita abin

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login