Showing 120001 words to 122360 words out of 122360 words
Chapter 41 - A sanadin Son ki Hausa Novels Document complete by Aisha A Muhammad Sanaz.txt
ruwan dake jikinsu.
Suna had'a eyes ne suka tsaya kallon junan su cikin tsananin kewa da shauk'in junan su, kallon ta yake kamar ya had'iye ta anutse ya k'arasa inda take tsaye ya zuba hands nashi cikin aljihun jeans d'in dake jikin shi, lumshe eyes tayi tana mai jin fad'uwar gaba kamar yau ta fara kasancewa dashi, kamshin perfumes d'in shi ya cika mata hanci yana k'arasa wa wajen ya cire hannun shi daga aljihun ya zuba su saman kafadun ta cikin tattausar murya yace
"Baby haka zaki yi min koh? "
Cikin shagwa6a tace
"Me nayi maka kuma? "
"Lallai Baby har kin mance koh, idan na kirawo ki kizo bedroom d'ina bakya son zuwa why? "
"Ni Allah kunyar Daddy da Mumy nake ji amman kayi hak'uri "
Murmishi yayi kafin yace
"Okay tun da haka ne yau zamu koma gidan mu "
D'an waro eyes tayi sannan tace
"Wayyo my Dear dare yayi fah ka bari sai gobe please ".
"Okay naji amman sai na rage zafi tukunna ".
Kafin ta sake magana taji ya had'e ta da jikin shi sannan ya sanya lips nashi cikin nata wani soft kiss yake mata wanda yake ratsa kowanne jijiyar jikinta, kok'arin cire towel d'in yake ya mance ma a inda suke gaba d'aya ya tafi wata duniya ta daban sai ji yayi Suhaima ta kwace bakinta da gudu ta shige ta rufe, yayin da Sabeer ya bita da wani irin kallo jikin shi asanyaye ya k'arasa kan bed ya kwanta yana mayar da ajiyar zuciya.
Kwanciyar kenan Mumy ta shigo bedroom d'in agajiye daga hospital take kallon d'an nata take cikin kulawa tace
"Son ya haka lafiya? "
Cikin shagwa6a yace
"Mumy bakin rik'e min mata ba kunyar ku tasa ko side d'ina bata zuwa gaskiya gobe kisa a gyara mana gidan mu zamu koma nagaji "
Kallon shi Mumy take har sai da ya k'arasa maganar sannan tace
"Toh sarkin mara kunya kai kuma koh, babu inda zata je sai ta huta nan da koh 1month ne "
Azabure ya tashi kamar wanda kunama ta d'ana yace
"What! Mumy kashe ni zaki yi ne "
"Ba'a mutuwa sai kwanan mutum ya k'are mara kunya "
Juya kanshi yayi gefe yana k'unk'uni tare da turo baki, dariya sosai ya bawa Mumy don sauran kad'an ta kubce mata amman ta danne ta.
Ana cikin haka Daddy ya shigo d'akin lokacin Mumy tana kok'arin cire lapcot d'inta, taimaka mata yayi yana tayata cirewa sai kuma ya hango Sabeer yana 6a66ata fuska yace
"Ah! Son what wrong with U? "
Kauda kai yayi bai yi magana ba kallon Mumy yayi yace
"Sweetie nah me akayi wa Son ne? "
Bashi labarin komai Mumy tayi ta k'arasa da fad'in
"Shine fah ina gama fad'a mishi ya tsaya yana wani 6ata fuska "
"Gaskiya Mumy baki kyautawa Son ba a bashi matarshi please ina rok'an mishi wannan alfarmar "
Murmishi Mumy tayi kan tace
"Okay Daddyn Sabeer an gama gobe sai su koma gidan amman gaskiya za'a bar mana twin's "
Wani tsallen murna Sabeer ya doka tare da rungume Mumy yana cewa
"Indai twin's ne Mumy mun bar miki nasan zamu samu wasu very soon "
D'an bige bakin shi kadan Mumy tayi tare da cewa
"Baka da kunya wannan yaron "
Sosa kai yayi da d'an gudu ya bar bedroom d'in, dariya Mumy da Daddy kawai suka yi zuciyar su fal farinciki, Suhaima ma da take cikin toilet murmishi kawai tayi da yake duk tana jin su wani sabon son mijinta taji yana ratsa kowanne lungu da sak'o na zuciyar ta, sai da taji fitar Mumy da Daddy daga bedroom d'in sannan ta fito ta shirya.
Washe gari kuwa da safe Mumy ta tura en aikinta tare da Jiddah suka gyara gidan tsaf Jiddah na kula da yanda suke gyaran gidan, zuwa bayan sallah issha suka koma gidan nasu amman ban da su Na'eem da Shaheed don su Mumy sun kar6e su sun zama nasu.
Kula tattalin juna da kuma soyayya ta gaskiya ita tace jigon zaman lafiyar da Suhaima da Sabeer suka ginata cikin gidan su, zaman su suke cikin jin dad'i da kwanciyar hankali, Suhaima yanzu bata da wata matsala yanzu sai tason cigaba da karatun ta kuma tasan komai lokaci ne idan Allah ya nufa zata yi ne.
*AFTER 2 YEAR'S*
Abubuwa da dama sun faru acikin wad'annan shekarun ta 6angaren Yah Aliyu ya kammala karatun shi na mass com har ya samu aiki a freedom radio a 6angaren labarai, Sabeer kyautar gida yayi mishi don yafi samun sauk'in zuwa wajen aikin da kuma sabuwar mota amman sam Yah Aliyu yak'i kar6a sai dakyar aka shawo kanshi ya kar6a, tuni suka tashi suka dawo cikin gari wannan gidan nasu na kauye kuma suka barwa Mahaifin su bayan Sabeer ya k'ara gyarashi tare da gidan su Babaa Lantana da Baba Adamu, anan aka matsawa mahaifin su Suhaima da yayi aure babu 6ata lokaci ya sami wata mata wadda auren ta d'aya mijin ya rasu ko haihuwa bata yi ba don haka ya aureta suna zaman su cikin kwanciyar hankali.
Haka kuma sun samu en uwan Umman su (Fatima) wad'anda suka zo kauyen suna neman su har suka dace wajen samun Baba Umaru, a lokacin aka nemo su Aliyu da Suhaima suka zo don ganawa da family d'in su wad'anda basu ta6a gani ba, sunyi mamaki sosai na ganin irin manyan mutanen da suka zo a matsayin en uwan Umman su, labari aka zauna yi bayan ansha koke koke da neman gafarar juna inda suke ba da labarin su en asalin garin kd ne, ashe Mahaifin su ne maraya ne Mahaifin Fatima ya d'auke shi aiki matsayin drivern shi so daga nan suka fara soyayya babu wanda ya sani bayan ta gama schl ne aka had'a ta aure da wani d'an uwanta wanda bama a k'asar 9ja yake aiki ba tak'i yarda sai tace sai Umar shine kadai wanda zata aura a k'arshe suka gudu sai neman su akayi aka rasa, shine en uwanta suka yi fushi da ita sosai har suka k'i neman ta sai kuma daga baya zuciyoyin su suka yi sanyi aka fara neman su amman ba'a gansu ba sai yanzu Allah ya tak'aita musu wahalar su.
Atime d'in da suka ji Fatima ta mutu sunyi kuka sosai iyayen ta sun yafe mata abin da tayi musu, nan fah aka gabatar musu da Suhaima da Aliyu saboda tsabar murna rungume su suka yi, Suhaima da Aliyu sunji dad'in ganin family d'in su sosai, sai yamma suka fara shirin tafiya Aliyu yayi musu alkawarin zasu zo har kd d'in, nan suka tafi kamar kada a tafi haka suke ji.
Daren ranar Suhaima take bawa Sabeer labarin komai ya tayata murna sosai, bayan sati d'aya suka shirya suka tafi kd sosai suka yi mugun mamakin ganin irin had'add'un gidajen su ashe manyan en boko ne, en siyasa da kuma en kasuwa da yake Umman su ita kadai ce mace duk maza ne yayyannin ta wajen su bakwai kuma suna raye har da yaran su manya ma.
Tar6a sosai suka yi musu ji suke kamar su had'iye su don so tattalin su suke sosai har sukayi kwanak biyu aka zagaya dangi sosai sannan suka dawo gida Suhaima har da kuka ta na rabuwa dasu sun shak'u da Hajia mahaifiyar Umman su sosai.
Bayan dawowar su ne Jiddah ta haifi d'anta namiji ansha suna sosai su Suhaima, acikin lokacin ne ita ma Suhaima ta samu ciki sai dai mai sauk'in laulayi ne ba kamar cikin Na'eem da Shaheed ba, Sabeer yaji dad'i sosai sai kula yake bata da tattali kamar shine cikin farko haka ma su Dr Faridah ba'a barsu a baya ba suma sosai suke kulata, haka ta cigaba da rainon cikinta cikin kwanciyar hankali.
After 9 months ne Allah ya sauki Suhaima lafiya ta haifi twince d'inta dukka mata tsakanin Sabeer, Mumy, Daddy da Dr Ahmad d'an fillo bansan wanda yafi murna ba acikin su, bayan sun dawo gida nan fah gida ya cika da en uwa da abokanan arzik'i sai taya murna ake na samun wannan karuwar da akayi, washe garin haihuwar ne mutan kd suka taho da abubuwan arziki sosai sai lokacin Mumy take ganin en uwan Suhaima sosai tasha jinin jikinta don tasan bazasu nuna musu komai ba nan zuciyar ta ya dad'a kyashin halinta tabbas ba'a son wulakanta d'an adam don bakasan irin baiwar da Allah yayi mishi ba.
Ranar suna yaran suka ci sunan Dr Faridah da kuma Fatima suna kiran su da Shaheeda da kuma Afnan, sosai ansha suna da walima an kashe kud'i sosai a wannan sunan sai fatan Allah ya rayasu.
Haka lokaci ya cigaba da tafiya har sukayi arba'in duk family na Suhaima sai da suka je sosai sai da sukayi wurin 1week a kd Hajia sai da ta gyara jikarta sosai sannan suka dawo gida, twince na da 5months Aunty Aliyah ta sake haihuwar mace wadda taci Sunan Suhaima Yah Aliyu ya mayar da sunan k'anwar shi nan aka sha suna aka watse.
Duk wani jin dad'i da kwanciyar hankali Suhaima tana samun shi wajen gwarzon mijinta Sabeer, itama ta bashi duk wata kulawa da ta kama zaman su suke cikin jin dad'i, Na'eem da Shaheed tuni Dr Faridah ta sanya su a tsadaddiyar wata prvt schl sai hutu suke zuwa gidan iyayen su don har islamia da tahfiz duk an sanya su ban da extra lesson da ake musu a gidan masha Allah kuma yaran brain nasu naja gasu nutsattsu basu da hayaniya sosai.
Bayan wasu en shekaru Shaheeda da Afnan sunyi wayo sosai har an yaye su, a lokacin Sabeer ya samawa Suhaima schl a Buk tana karantar medicine sosai Suhaima ta nuna farincikin ta haka ma Yah Aliyu yaji dad'in barin Suhaima da Sabeer yayi ta cigaba da karatu har godiya yayi wa Sabeer.
Ta 6angaren Yah Aliyu kuwa Alhmdllh duk wani bud'i yana samu ta 6angaren aikin shi, gashi sun had'a hannu da Sabeer sun bud'e wani tafkeken gidan gona a kauyen nasu Suhaima da kuma wurin hutawar su inda sunje sosai wajen yayi kyau sun d'ibi ma'aikata suna biyan su, sosai en kauyen sun ji dad'i hakan don an rage masu zaman banza babu sana'a.
Duk sunje sunyi aikin hajji da Omarah sun yawata k'asashe sosai musamman Suhaima ma don Sabeer yace honeymoon d'in da basu yi ba suna farkon auren auren yanzu zasu yi shi nan suka zube Shaheedah da Afnan hannun su Dr Faridah suka wuce honeymoon d'in su, sai da sukayi wajen wata hud'u sannan suka dawo gida har da tsarabar ciki.
Tun safe take faman zirga zirga a tsakanin kitchen saboda yau Sabeer zai dawo daga tafiyar da yayi ta tsayin wata 1, ta gama had'a mishi abubuwan ci dana sha ta gyara ko'ina sannan ta barwa er aikinta wanke wanke, upstairs ta haye ta shiga d'akin su Shaheedah wanka tayi musu ta shirya su cikin wasu English wears na gown sai dai tsayin ta iyakar gwiwar su ne sannan ta gyara musu gashin kansu style mai kyau tayi musu sunyi matuk'ar yin kyau gashi kayan iri d'aya komai da komai daman kuma komai iri d'aya ake yi musu peck ta basu a cheek nasu suma suka yi mata sannan ta mik'e tsaye tace
"Wow! Emmatan Daddy kunyi kyau bari naje nayi wanka sai mu d'auki pic's before jirgin su Daddy yayi landing koh "
Cikin tsallen murna suka ce
"Okay Mumy "
Nan ta wuce tayi wanka bayan ta fito simple makeup tayi da yake cikin ya fara girma sai ta sanya wata milk d'in gown tayi kyau tayi rolling kanta da veil d'in rigar tana cikin fesa perfumes ne taji tsallen ihun su Afnan suna kiran sunan Daddy da nasu Na'eem.
Agurguje ta k'arasa shiryawa ta fito zuwa downstairs inda take jin hayaniyar su, ko kunyar samarin yaran shi bai yi ba ya rungume ta yana kok'arin kissing nata ture shi tayi tare da yi mishi nuni da yaran duk da kusan hankalin su nakan tsarabar kayan su.
Marairaice fuskar yayi tare da cewa
"Haba Baby na nayi kewar ki sosai fah "
"Sorry Dear bari mu sallami yaran ka sai kayi koma mene "
Ta k'arasa fad'i tana kashe mishi ido, murmishi yayi sannan ya huro mata da kiss ta iska dole yau ya tura su Shaheed wajen Mumy don zasu tak'ura mishi idan ya barsu.
Bayan yayi wanka sun ci abinci sannan suka fita zuwa gidan su Daddy kowanne part suka shiga suka gaida su sannan suka dire a part d'in su Mumy ansha hira sai da sukayi dinner sannan suka bar gidan Shaheedah da Afnan ko bin iyayen basu yi ba daman haka Sabeer yake so.
Awannan daren Suhaima ta yabawa aya zak'inta don sosai ta wahala a hannun Sabeer, zuciyar su fal farincikin kasancewar su da junan su bayan komai ya kammalu ne suna rungume da junan su Sabeer cikin muryar shauk'i yace
"I luv U Baby nah "
"I luv U too sweetheart "
Daga nan suka wuce bathroom wanka sukayi sannan suka zo suka kwanta babu dad'e wa bacci yayi awon gaba dasu.
_*Alhamdullilah!*_
Dukkan yabo ya tabbata ga Allah da ya bani ikon kammala wannan littafin nawa.
_gaisuwar fatan alkhairi gare ku My Sadeey and my Momma nah (Aunty Maijiddah) hak'ik'a ku masoya na ne na gaskiya ina son ku sosai Allah ya bar mu tare Amin_.
♻ EXCLUSIVE WRITER'S FORUM
_Ina matuk'ar alfahari da wannan kungiyar tawa, ina yiwa sisters d'ina na cikin fatan alkhairi a duk inda kuke i really luv U guy's_
*MASOYA NA KUYI MIN UZURI DON AGURGUJE NA KAMMALA MUKU WANNAN LABARIN HAKA YA FARU NE SABODA GABATOWAR WANNAN WATAN MAI ALBARKA DA YAKE TUNKARO MU WATO RAMADAN, DAFATAN EN UWANA ZAMU HIMMATA GA AIKATA ABUBUWAN ALKHAIRI CIKIN WANNAN WATAN, MU DAGE DA IBADA MU KAURACEWA GULMA KALLACE KALLACE DA KUMA HIRA MARA AMFANI ALLAH YASA ZAMU GA WANNAN WATAN DA RAI DA LAFIYA, WAD'ANDA BASU DA LAFIYA ALLAH YA BASU LAFIYA, ALLAH YA JIK'AN WAD'ANDA SUKA RIGA MU GIDAN GASKIYA IDAN TAMU TAZO ALLAH YASA MU CIKA DA IMANI*
_Masoya na baza ku lissafu ba amman ku sani Aishat A Muh'd tana matuk'ar kaunar ku tana muku fatan alkhairi sai mun had'u a wani sabon nvl d'in nawa after sallah indan Allah ya kaimu_.