Showing 114001 words to 117000 words out of 122360 words

Chapter 39 - A sanadin Son ki Hausa Novels Document complete by Aisha A Muhammad Sanaz.txt

da ke damunshi sai dai ya fad'a mata rashin lafiyar tace take damunshi kyale shi kawai tayi amman tasan da wani abin sai dai ta dage da addu'a Allah ya yaye mishi koma mene.


Bayan ya gama bata ta shanye shi gaba d'aya cikin tausayin ta ya kalle ta tare da cewa
"Na k'ara miki wani? "
Murmishin yak'e tayi kafin ta girgiza kanta kawai.
"Okay ni zan fita Baby zamu fita da Ashiru amman bazan dad'e ba"


Cikin sanyin murya irin ta mara lafiya tace
"Allah ya kiyaye hanya ya dawo min da kai lafiya "
Cikin murmishi yace
"Amin Sweetie nah "
Ya k'arasa maganar yana bata peck a kumatu itama tayi mishi a saman lips d'in shi daga haka ya fita daga d'akin Suhaima tabi shi da kallon tausayi.




Haka lokaci ya cigaba da tafiy har aka shiga watan ramadan zuwa wannan lokacin jikin Suhaima ya d'an warware zata ci kowann abinci sai dai har idan ita zata dafa da kanta ba zata iya ci ba, kulawa babu irin wadda bata samu, har azumin ma tun da aka fara take jarumtar yinshi batason tasha, Sabeer kam matsalar kud'i ta yi mishi sauk'i don Daddyn shi ya sanya Jiddah kawo mishi atm card nash duk lokacin da yake buk'ata zai je ya cira amman sai dai idan ya kasance muhimmiya ce saboda yana ganin Aliyu bazai ji dad'i ba zai yi tunanin ya raina duk kulawar da yake bashi.




Da haka suka cinye wata ramadan aka shiga hidimar sallah, Yah Aliyu yayi matuk'ar kok'arin yi musu d'inkunan sallah haka aka cinye bikin sallah lafia, sosai cikin Suhaima yake girma zama dakyar tashi dakyar sosai cikin yake da girma.






Sabeer ba k'aramin tausayin ta yake ji ba haka da dare zai sanya ta a gaba yana faman kallonta tare da shafa cikin kafin ya tashi ya d'aura alwala yana kai kukan shi gun mai dukka akan ya sauki Suhaima lafiya, har wata rama yayi ta fargaba idan ya tuna yasha jin labarin haihuwa akwai wahala, daman tana zuwa awo amman a asibitin cikin gari duk ranar awo shi yake kaita ya jira ta gama su shiga adaidaita sahu ko taxi su dawo gida.




Cikin haka cikin Suhaima ya shiga watan haihuwar shi sai zuba ido ake ana jiran haihuwa shiru, yayin da Jiddah da siyo duk wani abin daya danganci kayan jariri unisex da duk wani abin buk'ata Sabeer ya bata atm card nashi taje ta ciri kud'i ta siyo, duk an gama shirin komai sai jiran haihuwa duk wani masoyin Suhaima yana mata addu'a ta Allah ya rabata lafiya da abin da yake cikinta saboda girman cikin kadai ya isa firgita mutum duk ta wani kumbura tayi wani iri kamar ba ita ba kaya sai dai ta zura dogowar riga saboda riga da siket ko da zani bata jin dad'in amfani dasu dogowar rigar ma irin buba nan mara shape, Baba Adamu kullum cikin yi mata rubutu yake na sauk'in nakuda tana sha.




Sai da cikin Suhaima ya shiga wata goma cif cikin wata safiya ta monday ta tashi da azababben ciwon nakuda Allah yaso Yah Aliyu da Sabeer duk suna gida basu fita ba nan da nan aka samo taxi suka tafi asibitin da take zuwa awo, suna zuwa aka kar6eta cikin gaggawa suka wuce da ita labour room Sabeer ji yake kamar ya bita ciki amman Yah Aliyu ya rik'e shi gam ganin yanda jikin shi yake rawa yace
"Sabeer addu'a kawa zaka yi mata "
Nan ya zube akan benci kawai yana faman yin addu'ar duk wadda tazo cikin bakin shi.


Suhaima kuwa abin ba'a cewa komai iyakar wahala tasha ta kamar bazata iya haihuwa da kanta ba ma, tasha kukan har hawayen suka daina fita daga idonta saboda azaba addu'a kowacce yin ta take tana fatan Allah ya rabata da cikin nan lafiya, tun safe ake abu d'aya har zuwa k'arfe 9 na dare sannan wahalar ta tazo k'arshe inda ta haifi kyawawa yaran ta guda biyu duk maza wanda suka kasance lafiyayyu masu koshin lafiya, tana gama haihuwar su da taja wani numfashi sai ta zube nan nurse suka yi kok'arin wajen farfad'owar ta sannan suka gyara mata jikinta tsaf bayan sun gama suka sanya mata drip na k'ara k'arfin jiki da kuma allurar bacci don ta samu ta huta sosai don ta wajugu ba kad'an ba.




Sai da aka gyara Baby's d'in tsaf suka sanya musu kaya sannan suka duba lafiyar su, su kansu nurse's d'in yaran sun matuk'ar birgesu da basu sha'awa gasu identical twins ne masu kama da junan su sosai.


Sabeer kusan suman tsaye yayi tsabar farinciki a lokacin da aka mik'a mishi yaran shi, kallon su yake cikin wani irin masifar kaunar su d'in nan had'e su yayi ya rungume su cikin kirjin shi yana jin wani irin farinciki da shaukin son yaran shi addu'a yayi musu kafin ya bawa su Yah Aliyu da Aunty Aliyah yaran.


Room d'in da aka canjawa Suhaima ya nufa zama yayi kusa da gadon yana kallon fuskar ta yanda ta wani rame ta k'ara haske sosai, hannun shi ya sanya yana shafa face d'in ta wani irin kaunar ta ne yake ratsa mishi heart din shi, ta gama yi mishi komai tunda ta haifa mishi yara har biyu masu matuk'ar kama dashi da me zai sakawa Suhaima saboda farincikin da ta sanya shi, daren ranar Sabeer kasa bacci yayi idan yaran suka yi kuka ya d'auki wannan ya d'auki wannan Yah Aliyu ne kadai ya koma gida don Aunty Aliyah zama tayi saboda taimaka mishi da rik'o ln yaran.




Sai wurin asuba Suhaima ta farka lokacin Sabeer ya tafi masallacin asibitin, nan Aunty Aliyah ta taimaka mata ta gyara jikinta sannan ta zauna kan bed wata mahaukaciyar yunwa ce take kwakwular cikinta kamar wanda aka kwashewa kayan ciki gaba d'aya, sai da Aunty Aliyah ta mik'a mata Baby's d'in nan sannan ta had'a mata tea tana firfita mata don ya huce.


Kallon su take hawaye na zuba daga idonta suna d'iga kan fuskar yaran godiya take yiwa Allah da ya bata wannan kyautar da babu wani d'an adam da ya isa yayi maka ita, hakika ko a mafarki Suhaima bata ta6a tunanin zata haifi twince ba duk wannan wahalar ta haihuwar ta mance da ita ta rungume yaranta cikin tsantsar kaunar su.


Duk abin da take Sabeer na jingine a bakin kofa yana kallonta cikin wani irin kaunar ta sun bashi sha'awa, a hankali yayi tattaki ya k'arasa kusa da ita ko kunyar Aunty Aliyah bai ji ba ya rungume ta yana faman yi mata godiya kok'arin had'a lips d'in shi yake da nata ta tuna mishi da Aunty Aliyah a room d'in dole ya hakura da abin da yayi niyya, kar6ar tea d'in yayi yana bata a hankali a baki har ta shanye shi tas sai wurin 10 na safe Doctor ya salllame su bayan ya dad'a duba su an tabbatar basu da matsala sannan suka taho gida har da Aliyu wanda zuwan shi kenan ya tsaya kar6ar kayan abin karyawar da Babaa Lantana tana bashi ya kawo musu.


Tun kafin su k'arasa gidan Jiddah ta ruga su zuwa suna shigowa ta nufi wajen Suhaima da gudu ta rungume ta cikin farinciki har Sabeer na hararar ta yana cewa kada ta k'arasa mishi mata, kar6ar yaran tayi ji take kamar ta had'iye su don so gaba d'aya ta kidime sai taji tana son itama ta haifi twince sun bata sha'awa sosai.


"Suhaima don Allah kika yaye su zaki bar min su "
Fad'in Jiddah kenan harara Sabeer ya sake dalla mata tare da cewa
"Yarinya kada ma kisa a ranki bazan baki yara na ba "
"Kaiii Yah Sabeer kasan gaba nawa Allah zai baka watakila ma twince da twinkle zata yi ta haifa "


"Innallilahi Jiddah rufa min asiri idan ba mutuwa kike so nayi ba wannan ma sun ishe ni rayuwa "


Dariya aka kwashe da ita ganin yanda Suhaima gaba d'aya ta firgice, wanka Aunty Aliyah ta fara yiwa yaran yayin da Babaa Lantana kuma ta kama Suhaima tana kuka tana yi mata wankan ganye da tafasasshen ruwan zafi Suhaima ansha kuka fatar nan taji ja saboda dokan ganye jikinta, Sabeer kamar yayi kuka ganin yanda ake wahalar da Babyn shi.


Sai da aka gama gyara su tsaf sannan Baban su Aliyu yazo ganin jikokin nashi yayi musu addu'a sosai, daga nan ya tashi ya tafi sai yamma lik'is Jiddah ta tafi kamar bazata tafi ba haka take ji a wayar ta Sabeer ya kirawo Daddy yake fad'a mishi Daddy tsabar murna kamar yayi tsintsuwa ya taho har da hawayen shi na farinciki daman yana addu'ar Allah ya sanya Sabeer ya haifi yara masu yawa saboda shi kadai ne gare su sai gashi haihuwar farko da biyu Allah ya fara basu.


Washe gari kuwa sai ga Daddy yazo da kanshi saboda tsabar murna rungume Suhaima yayi yana mata godiya sosai har sai da taji kunya sosai nan ya d'auki yaran yana kallon su ya rasa ina zai sanya kanshi saboda murna.


A lokacin Sabeer yake musu hud'uba Hassan yaci sunan Dr Ahmad d'an fillo kamar yanda Daddy yace ya sanya Hussein kuma sunan Baban su Suhaima aka sanya mishi Omar dakyar Daddy ya iya tafiya har yana tafiyar Sabeer yaushe zasu gidan su don ya sanya an gyara gidan an canja komai hatta da fentin gidan sai da aka canja.


"Daddy sai lokacin da Suhaima taso dawowa har yanzu tsoron Mumy yana nan cikin zuciyar ta "
Gid'a kai Daddy yayi tausayin d'an nashi fal cikin zuciyar shi kafin suyi sallama ya tafi. Suhaima da Aliyu tare da Mahaifin su sunyi matuk'ar murna da jin sunan shi aka sanyawa Hussein har kukan farinciki yayi sosai.


Ranar suna anyi taron suna dai dai gwargwado Suhaima ta samu kyautittika tun daga kan uban gayya wato Sabeer, Yah Aliyu, Aunty Aliyah, Jiddah da mijinta Khaleel, Baba Adamu, Babaa Lantana, Baba Umaru, Ashiru abokin Sabeer na kauye, Daddy da kuma Musaddiq da matar shi wanda sai lokacin yake fad'a mishi komai da ya faru, kowannen su yayi mata kyauta daidai k'arfin shi anyi suna lafiya an gama lafiya, raguna 2 da sa 2 Sabeer da Daddy suka yanka duk wannan abin da yake faruwa babu wanda ya sani cikin family d'in d'an fillo sai da Daddy da Jiddah kawai, haka su Suhaima suka cigaba da yin wanka cikin kwanciyar hankali gashi Na'eem da Shaheed suka cigaba da girma kamannin su da Baban su na k'ara fitowa da haka har sukayi arba'in...........
























Aıʂɧąɬ A Mųɧ'ɖ ✍🏻
*A SANADIN SON KI*








Wྂrྂiྂtྂtྂeྂnྂ bྂyྂ
Aྂıʂɧąɬ Aྂ Mྂųɧ'ɖ




ɖɛɖı¢ąɬɛɖ ɬơ ɱყ ʂąɖɛɛყ ʂąŋąʑ




♻ *єχ¢ℓυѕινє ωяιтєя'ѕ fσяυм*





*PAGE 113*








Bayan sun yi wata biyu da en kwanaki ne Suhaima babu inda taje duk kuwa da nacin da Jiddah take akan Sabeer ya barta taje amman yak'i yarda sai dai ita tazo, duk wani gyara da ya kamata ayiwa wadda ta haihu Suhaima ta samu wannan gyaran daga 6angaren Aunty Aliyah, Jiddah da Babaa Lantana, tuni tayi er kiba kad'an ta murje tayi kyau abin ta duk da kuwa rainon biyu babu sauk'i amman Sabeer yana matuk'ar taimaka mata haka Aunty Aliyah da Babaa Lantana suna taya ta rainon su sosai.






Bayan ta gama yiwa Na'eem da Shaheed wanka ne da yake lokacin zafi ne ta sanya musu powder tare da kaya marasa nauyi gadon su taje ta kwantar dasu tare da yi musu addu'ar tsari ta bacci sannan ta wuce toilet tayi wanka, d'aure da towel ta fito d'an k'arami, had'a ido tayi da Sabeer wanda yake zaune kusa da gadon Na'eem da Shaheed yana lilasu a hankali murmishi suka sakarwa junan su cike da so, wani mayataccen kallo Sabeer yake bin ta dashi wanda tun safe ta kula da irin wannan kallon nashi, ita tsoron ma zuwa kusa dashi take hannun shi ya mik'a mata bata yi musu ba ta mik'a nata ya rik'e shi tare da janyo ta jikin shi ya fara shinshina wuyan ta zuwa bayan ta hura mata iskar bakin shi yayi cikin kunnen ta wanda ya haddasawa Suhaima kasala cikin muryar rad'a yace


"Baby nah ki bani wannan damar please ina son kasance wa dake nayi missing d'in ki da lot "


Duk da ta gane nufin shi amman da taji abin da yace sai da taji fad'uwar gaba amman ya zata yi tunda hakk'in shi ne wanda ya rataya kan wuyanta, don haka k'ara shigewa jikin shi tayi kawai tana cusa face nata a chest d'in shi.


"Bari naje nayi wanka koh? "
Ya k'arasa maganar yana d'aga mata gira, tashi yayi ya wuce toilet yayi wanka sannan ya fito ya tarar da ita har ta shirya cikin wata gown ta bacci iyakar rabin cinyarta (da yake Sabeer ya sanya Jiddah d'ebo mata kayan ta ba tare da wani ya gane ba) ta gyara gashin ta sai tashin kamshi take, kallonta yake kamar yau ya fara ganin ta.




Agurguje ya shirya ya taho wajen ta ya rungume ta cikin jikin shi yana faman aika mata da zafafan sak'onnin shi cikin wani irin salo mai wuyar fassara, wannan daren sun raya shi sosai cikin wani irin kaunar junan su anan Sabeer ya gama tabbatar wa Suhaima itace rayuwar shi haka ita ma a 6angaren ta gwarzon nata shine jin dad'in rayuwar ta suna addu'a da fatan Allah ya barsu har karshen rayuwar su.






Rayuwar su suke cike da jin dad'i da kwanciyar hankali suna kula da yaran su sosai da haka har Na'eem da Shaheed suka tasamma shekara d'aya yaran sunyi wani irin girma gashi suna wata goma suka iya tafiya gudun su suke ko'ina zuwa lokacin Aunty Aliyah tana d'auke da tsohon ciki itama, zumunci Jiddah da Suhaima kuwa kullum k'aruwa yake idan bata zo ba to za suyi waya junan su, tsakanin Suhaima da Sabeer kuwa kullum soyayyar su k'ara k'arfi take kula suke bawa junan su sosai, Daddy kuwa a weekend yake zuwa ganin jikokin shi.




Suna watanni goma sha bakwai Suhaima ta yaye su, yayin da Aunty Aliyah kuma ta haihu aka samu mace sunan Umman su Suhaima aka sanya mata wato Fatima suna kiran ta da Ameerah, Yah Aliyu ma karatun shi ya d'auki zafi yana daf da had'a degree d'in shi a Buk.


Wani zuwa weekend da Daddy yayi yace yana son Na'eem da Shaheed su bishi suyi mishi kwana 2 sunyi matuk'ar shak'uwa da Daddy sosai, a tsorace Sabeer ya barwa Daddy yaran shi don yana jin tsoron kada Mumy ta kashe musu yara, tsaf Daddy ya karance shi girgiza kai kawai yayi yana murmishi bai ga laifin shi ba yana da gaskiyar shi baisan yanzu yanda Mumy ta koma ba ne duk wannan ji da kan babu shi.


**********




Duk wani jin dad'i gashi nan akwai shi sai dai babu kwanciyar hankali, duk tayi bak'i ta rame Dr Faridah kenan wato Mumy abin duniya yayi mata yawa wajen shekara 2 bata sanya tilon d'anta a idon ba tayi neman tayi binciken duk a banza tayi kok'arin tambayar Daddy akan inda d'anta yake but yace shima neman shi yake k'arshe ma rufe ta da fad'a yayi ai duk laifin ta ne gashi ta salwantar mishi da rayuwar d'an shi ba'a san inda yake ba.




Ta 6angaren Dr Ahmad d'an fillo dasu Hajjah Hauwaa suma suna cikin wannan tsantsar tashin hankalin na rasa sanin inda Sabeer sunyi binciken iyakar iyawar su amman basu ji d'uriyar inda yake amman Dr Ahmad d'an fillo yaso d'ago Daddy yasan inda Sabeer yake ganin yanda hankalin shi yake kwance bai d'aga hankalin shi sosai ba akan 6atan Sabeer amman sai Daddy ya nuna mishi ba haka, tun daga lokacin Dr Ahmad d'an fillo ya kwanta rashin lafiya saboda 6atan Sabeer d'an lelen shi yayi kuka sosai yana mai nadamar da tun lokacin yayi magana matar shi ta dawo gare shi tun da dalilin ta suka neme shi suka rasa, Haka ma Mumy ta kwanta ciwo a tsaitsaye ko hospital bata iya zuwa jinin ta hau sosai damuwa biyu ce ta had'e mata rashin tilon d'anta da kuma juya mata baya da mijinta yayi duk a dalilin Suhaima, wadda zuwa wannan lokacin tayi nadamar abin da ta aikata yafi sau ba adadi tayi kukan sosai da bata aikata hakan ba da tuni d'anta na kusa da ita har da jikokin ta ma, har tana fatan ta d'an samu sauk'i ta nemi garin su Suhaima taje ta nemi yafiyar ta ko zata samu sassauci cikin zuciyar ta da rayuwarta gaba d'aya.


Tun safe yau jikin ta ya rikice ga Daddy baya nan yafita tana kwance a falo wajen 4 na yamma ne jefi jefi tana kallon tv tana kallon African Tv suna wa'azi na marigayi sheik Ja'afar Mahmoud Adam (Allah ya jik'an shi da rahma Amin), lokaci zuwa lokaci gaban ta na fad'uwa.




Sallama Daddy yayi ya shigo palourn hannun shi rik'e da Na'eem da Shaheed suna d'an tsalle tsallen su, wata zabura Mumy tayi ganin wasu kyawawan yara masu matuk'ar kama da junan su kuma abin da ya k'ara hargitsa ta ganin yanda suke matuk'ar kama da Daddy da kuma Sabeer, nan take wani tunani ya d'arsu cikin zuciyar ta ko Daddy aure ya sake bata sani ba matar ta haifa mishi yara.




Da d'an gudun su suka k'arasa inda take tare da rungume mata k'afafun ta, sakin baki kawa tayi tana kallon su wani irin sanyi taji jikinta yayi ta zame ta zauna lokaci d'aya wani mugun son yaran ya ratsa mata cikin zuciyar ta da zuciya d'aya ta d'ago su zuwa jikin ta cikin murmishi take cewa


"Ya sunan ku yara nah?"


Na'eem da yafi surutu cikin muryar shi wadda bata kware ba yace
"Ni sunan Na'eym wannan kuma Sha'eed"


Ya k'arasa fad'i yana Shaheed da d'an yatsan shi,
"Masha Allah sunan masu dad'i Allah ya albarkaci rayuwar ku "


"Amin "
Daddy ya amsa cikin zuciyar shi, d'agowa tayi ta kalli Daddy tare da cewa
"Daddy yaushe ka sami yara masu kama da kai bansani ba? "
Murmishi yayi yana tafiya

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login