Showing 66001 words to 69000 words out of 122360 words
Chapter 23 - A sanadin Son ki Hausa Novels Document complete by Aisha A Muhammad Sanaz.txt
shigo gidan nan matsayin matar Hussein wallahi duk wadda tayi gigin shigowa kuwa sai tayi dana sani kuwa.
Tana gama fad'in haka haka ta wuce side d'in ta tana shiga bedroom saboda tsabar takaici ta rushe da kuka kamar wata k'aramar yarinya, Allah yayi ta mace mai tsananin kishin sosai ji take har numfashin ta yana kokarin d'aukewa tsabar tashin hankali.
Anutse Daddy ya shigo bedroom d'in jin kukanta ba k'aramin d'aga mishi da hankali yayi ba don shi yaushe rabon yaga kukan matar shi kamar haka har ya mance.
Cikin sanyin jiki ya k'arasa inda take ya zauna kafin ya dafa kafad'ar ta yace
"Yake matata kukan me kike haka? "
D'ago kanta tayi ta kalle shi idanunta suna zubar da hawaye ta fad'a jikin shi ta k'ank'ame shi tare da cewa
"Ina tsananin son ka Hussein ina kishin ka bana son wata mace ta ra6ar min kai but why da zaka yi min haka kaje wajen wata kai da Son har kuci abincin ta? "
Murmishi Daddy yayi kafin yace
"Haba Faridah kinsan bazan iya kallon wata d'iya mace da sunan ina sonta ba, banyi hakan tun k'uruciya ta ba sai yanzu da na girma kinsan ke kadaice cikin zuciyata daga ke babu dad'i, duk wannan maganar tsokanar ki Sabeer keyi"
Kallon idanun shi take don son tabbatar da gaskiyar maganar shi, gid'a mata kai yayi tare da lumshe eye's nashi alamun haka maganar take.
"Toh ina kuka je da Son har kukayi dare? ".
Fuskar shi d'auke da murmishi yace
"Muna part d'in Hajjah ana hira "
Rungume Daddy tayi tana sauke ajiyar zuciya ta kwanciyar hankali don sai yanzu taji ta a nutse nan kuma suka 6ige da nunawa juna kauna.
Washe gari da yammacin ranar Jiddah da Yusrah suka d'aga zuwa dubai don siyayyar kayan lefe, sosai Daddy da Sabeer suka saki kud'i don a had'o kaya masu kyau da tsada.
**** **** ****
Satin su Jiddah 2 suka dawo Nigeria da tarin had'add'un kayan lefen da suka had'a, kaya sunyi ta ko'ina sosai kayan Daddy da Sabeer suka yaba za6en su ko Mumy sai da ta jinjina irin dukiyar da aka narka anan ko ita kayan sun birgeta duk hassadar mutum yaga kayan sai sun birgeshi, har da tukwici Daddy yayiwa Jiddah da Yusrah don sun mishi yanda yake so.
Har zuwa lokacin Sabeer tsakanin shi da Mumy gaisuwa sam yak'i sake mata kamar da, don ba k'aramin 6ata mishi rai tayi ba akan lefen da ta had'a wai za'a kaiwa Babyn shi idan ya tuna hakan har ranshi 6aci yake.
Duk wannan kayan da aka had'o sai da Jiddah ta kar6i kud'i na musamman hannun Sabeer ta siyawa Suhaima kayan da zata yi amfani dasu wajen biki komai sai da ta had'o yanda ya kamata.
Bayan kwana 2 duk 'yan uwa sun gama ganin lefen sai zuzutashi suke saboda had'uwar shi but idan suka tuna 'yar kauye za'a kaiwa wannan duk sai ransu ya 6aci su fara jan tsaki da k'ananun maganganu, babu mai goyon bayan Sabeer akan wannan bikin sai Daddy don ko Dr Ahmad d'an fillo kadaran kadahan don farincikin Sabeer ya hak'ura.
Shiyasa Sabeer da Daddy ne kawai suke kid'an su da rawar su, duk wadannan tarin kayan da aka had'a sai da Daddy ya k'ara da wata dank'areriyar sark'ar gold mai matuk'ar kyau da tsada ba kad'an ba da kuma key na mota, don Daddy tuni ya zubar da makaman yak'inshi na k'in talaka yanzu sosai yake tsayawa sauraren talakawa masu neman taimako yana taimaka musu kuma hakan ba k'aramin jin dad'i yake ba da kuwa daga iya fidda zakka shikenan.
Wannan abun da Daddy yayi wa Suhaima ba k'aramin bak'anta ran Mumy yayi ba don ita aganin ta taya zai tsaya siyawa 'yar k'auye wannan gold d'in mai tsada bayan wad'anda aka zuba mata a lefe gashi har da wani kyautar mota ko'ina 'yar k'auye da tukin mota me zatayi da ita, banzatar dasu zata yi tunda batasan darajar su ba, Daddy sai da ya toshe kunnen shi don kuwa Mumy da Hajjah sai mitar abin suke yi, shi kuwa ganin farincikin tilon d'an shi yafi mishi komai.
Ko ranar da za'a kai lefe motoci 3 Daddy yace za'a yi na mutane saboda bayason a had'a su da wahala kuma bayason ayi hatsaniya don sosai sai da ya gargad'i wad'anda zasu kai wanda suka kasance daga kanwar su Daddy sai k'annen matanshi da yaran su mata kad'an daga ciki, sai kuma motar Suhaima wanda aka zuba kayan lefen ta a ciki nan suka d'auki hanyar k'auyen su Suhaima.
Sai wurin 3 na yamma suka k'arasa kowanne ya fito daga mota sai faman yatsina fuska da ta6e baki suke suna yiwa mutane kallon d'ai d'ai, koda suka shiga gidan su Suhaima sunsha mamakin ganin yanda gidan yake don kuwa Yah Aliyu ya kashe kud'i sosai wajen gyara gidan har da sabon fenti akayi, shi yasa ko'ina yayi kyau yayi fes ga an tsabtace gidan sai k'amshin turaren wuta yake.
Anan tsakar gidan suka zazzauna saman tabarma, su Aunty Aliya da Babaa Lantana da wasu daga cikin 'yan uwan su Suhaima sun d'an zazzo kar6ar lefen, wasu kuma don ganin kwakwaf suka zo don sunji ance d'an mai kud'i Suhaima zata aura suna son tabbatar wa aikuwa da ganin irin motocin da suka zo acikin ta sun tabbatar da gaskiyar zancen.
Babu wanda yayi gigin shiga toilet sai alwala da suka yi suna tsoron kada su shiga su ga abin da zai sanya su amai, dai dai da ruwan alwala da bottle na faro suka dunga yi saboda tsantsanin ruwan suke.
Jiddah ranta ya 6aci sosai da wannan wulak'ancin da 'yan uwanta suka yi don an zuba musu ruwa a botoci suka k'i amfani dashi suka d'auko bottles na faro, kasa magana tayi don tsabar takaici, yayin da mutane suka saki baki da hanci suna kallon wannan sabon salon nasu, awurin sallahr ne kawai basu da yanda zasu yi suka yi akan tabarmar da aka shimfid'a musu bayan sun idar aka sake gaisawa sannan aka fara fito musu da abinci zuwa drink's da ruwa na bottles.
Sunyi mamakin na ganin irin abincin da suka gabatar musu dashi don basu yi zaton samun hakan ba, basu san wannan duk aikin Jiddah ba ne don kawa batason a 'yanuwanta su wulak'anta mata Suhaima.
Sun ci abincin bayan sun kammala aka gabatar da kayan lefen da car key sai kuma kud'in da ake d'ora wa saman kaya har 1 million, sakin baki, hanci sukayi 'yan kauye don ganin irin wannan abun da basu ta6a tsammanin zasu ganshi da ido ba nan kowa ya fara kokwanto cikin zuciyar shi anya ba siyar da Suhaima su Aliyu suka yi ba yo banda hakan ina za'a bayar da irin wannan kayan lefen haka har da mukullin mota da 1 million akai.
"Kada ku damu wannan ba wani babban abu bane a wurin mu don mun bayar da wadannan 'yan kayan don haka ku dai na mamaki, kodan nasan dole kuyi mamakin don ido bai ta6a ganin irin kayan ba "
Cewar Aunty Fadilah kanwar su Daddy tana wani yatsina fuska banda kallon raini da take bin su dashi, don 'yar gaban goshin Dr Faridah ce tana taya matat wan nata bak'in cikin wannan abu.
"Haba Aunty Fadilah don Allah ki daina irin wannan maganganun babu dad'i "
Cewar Jiddah tana turo baki wata uwar harara Aunty Fadilah ta aikawa Jiddah kafin tace
"Daman ina zaki ga rashin dacewar hakan bayan an shanye mana ke da Sabeer har da Yaya Hussein, idan ban da k'addara ina mu ina neman aure a irin wannan wurin "
Ta k'arasa maganar tana jan tsaki, cikin rashin kunya Jiddah tace
"Allah Aunty kika sake magana sai na gayawa Daddy tun da har kin mance abin da Daddy ya fad'a kafin mu taho "
Wata hararar ta sake zabga mata tamkar idanunta ya fad'o amman bata sake magana ba don tasan sarai halin Jiddah tsaf zata fad'awa Daddy kuma tasan tsaf zai ci mutuncin ta.
Sai bayan la'asar da suka yi sallah suka taho da tarin kayan snacks da drink's d'in da Jiddah ta bayar akayi, sai kuma cikin kud'in da suka kawo aka basu tukwicin dubu d'ari biyar, a wulak'anci suka kar6a kud'in babu sallamar arzik'i suka tafi.
Sai bayan tafiyar su ne aka saki jiki ana kallon lefen akwatina har 15 kowacce cike da kaya damk'an dakyar bag's ake zuge zipe saboda cikar kayan.
Duk kwakwkwafar mutum dai ya hak'ura da ganin kayan, k'arshe bayan an gama gani Aunty Aliya suka tattara su aka zuba su cikin d'akin Suhaima, daman Suhaima bata gidan tana can gidan Babaa Lantana ita da wasu kawayen ta biyu wad'anda suke shiri dasu.
Sai dare Suhaima ta dawo gida kasa kallon kayan tayi sabida kunya sai da Aunty Aliya ta dunga fito mata dasu tana gani a haka shima Yah Aliyu ya tarar dasu ya d'an kalla sama sama kafin yace
"Masha Allah kanwar tawa tayi goshi sai dai gaskiya kayan sunyi yawa sosai wallahi"
"Gaskiya kam sunyi kyau sai dai yawan su mu muke ganin haka amman su ba wani abun ne rabon ta ne"
Cewar Aunty Aliya kenan tana bud'e bag d'in da aka zuba sark'ok'i, sannan ta d'ora da cewa
"Yanzu ya zamu yi da motar ta? "
Sai lokacin Suhaima tasan har da mota haka ma Yah Aliyu.
"Tabd'ijam har mota fah kika ce Aliyah? "
"Kwarai kuwa baka ganta a waje ba? "
"Naga mota na d'auka ko lalace musu tayi "
"A'a ta Suhaima ce "
"Yanzu yanda za'a yi idan Sabeer yazo sai ya tafi da ita ya ajiye mata acan gidan nashi ko kuma Jiddah ta tafar mata da ita ta ajiye "
"Haka za'a yi kuwa don shine mafita nan ba wajen zaman ta ba ne "
Suhaima tana jin su duk wannan tattaunawar da suke bata ce komai ba sai tagumi da ta yi, bayan su Yah Aliyu sun fita daga d'akin har Yah Aliyu yana tsokanar ta da "ke fah yanzu Suhaima kin zama matar manya koh? "
Murmishi kawai tayi ta turo mishi baki dariya yayi ya fice abin shi Aunty Aliyah na taya shi.
Suna fita wayar Suhaima ta d'auki k'ara ganin Sabeer ne ya sanyata d'auka had'e da yin sallama, lumshe idanun shi yayi kafin ya bud'e su yana amsa sallamar ta throughout yau bai ji wannan muryarta ta ba.
"Amarya ta kinsha k'amshi nayi missing naki fah Baby yaushe zan zo? "
D'an murmishi ta saki mai d'an sauti sannan tace "sai nan da 4 week's zaka zo "
D'an zaro ido yayi kamar tana ganin shi yace
"Washsh! Allah nah kice Baby sai dai ki zo dubiya ta asibiti don nasan sai Doctor ya kwantar dani "
Dariya ta kyalkyale da ita tana cewa
"Haba lallai da ka cika rago kuwa"
Da sigar tsokana ta fad'a.
"Baby nine ragon koh, tabbb yarinya zaki bayani ne idan na rik'e ki a hannuna a time d'in ne zaki fahimci irin jarumta ta "
Gaban Suhaima ne ya d'an fad'i har ta kasa magana duk da bata fahimci maganar tashi sosai ba, jin tayi shiru ya sanya shi murmushi ya basar da zancen da cewa
"Baby kaya sun yi miki kuwa? "
"Laaa sunyi kyau sosai sai dai Sabeer gaskiya sunyi yawa, bayan haka har da mota fah sai kace wadda za'a siyar "
Dariya ya d'an yi jin yanda ta k'arasa maganar cikin shagwa6a.
"Baby nah kenan toh ai motar ba ni na baki ba Daddy nane ya baki, kuma zancen yawan kaya ki daina zancen su don kin cancanci fiye da haka "
"Ina godiya sosai a mik'a min godiya ta wajen Daddy "
"Toh Baby yanzu mene tsare tsaren bikin ne, mai kuke son yi, don ina son zan zo nida friend nawa Musaddiq "
"Daman kana da aboki ne? "
"Baby ina da aboki mana amman duk acikin su da d'aya na aminta dashi wato Musaddiq sai dai shi miskili ne na ajin k'arshe shi yasa baki san shi ba "
"Ayyah amman wannan kafin ya samu macen aure zai sha wahala "
"Baby ai yana da aure matar shi Mufidah da yaran shi twins sai dai yana rik'on d'iyar Yayan shi wanda ya rasu" (dafatan masu karatu baku manta labarin littafin YAYI SAKE ba), nan Sabeer ya bata d'an labarin shi a takaice sosai Suhaima ta matuk'ar tausaya musu jin irin gwagwarmayar da Musaddiq yasha a cikin rayuwar shi.
"Allah ya jik'an Abubakar Sadeeq"
"Amin ya rabbi Baby, yanzu kije ki kwanta dare yayi ranar friday ko Saturday zan shigo"
"Okay Allah ya kawo ka lafiya "
"Amin Baby nah kiyi bacci mai dad'i da sweet dreams dani aciki "
D'an murmishi kawai tayi nan suka yi sallama abin su zuciyar kowannen su cikin farinciki.
**** **** ****
Bayan kwana 2 da kawo lefe Jiddah tazo ta d'auki Suhaima don kai d'inkin kaya, kaya da D'an yawa ta zazza6o cikin kayan lefen ta had'a da wanda zatayi amfani dasu ranar bikin sannan ta had'a da wanda Yah Aliyu da Aunty Aliya suka yi mata, wajen tailor d'in Jiddah suka kai bayan sun gama za6ar irin style's d'in da suke so aka yi total na kud'i bana wasa ba nan take Jiddah ta biya su ko ragi babu don tana son su cika mata alkawari don nan da 2 week's zata dawo ta kar6e su dukka, duk wannan kud'in d'inkin a wajen Sabeer Jiddah ta kar6o, sannan suka zarce zuwa gidan Jiddah yini Suhaima tayi acan sai yamma driven Jiddah ya dawo da ita gida, motar Suhaima kuwa tana gidan Jiddah a ajiye don tun washe gari Yah Aliyu ya fad'a mata a waya ta turo driven ta ya dauka sai ya hau taxi drop har k'ofar gidan sai ya koma da motar.
Sai shirye shiryen biki ake ta koina duk da family d'in D'an fillo basa maraba da shigowar Suhaima cikin su hakan bai hanasu shirya bikin ba fiye ma dana kowanne d'a a gidan,har dinner suka shirya ta family da suke yi har da yin ankon su kamar irin gasken nan, haka ta 6angaren Suhaima ma sosai Yah Aliyu da Aunty Aliyah suka zage wajen shirya bikin nasu dai dai gwargwadon iyawar su, Jiddah sun gama tsara event's d'in da zasu yi dinner, walimah, kamu sai kuma dinner d'in family d'in Sabeer wadda zasu yi ranar da aka kawo amarya........
Ku cigaba da hak'uri da ni Fan's.
Aishat A Muh'd ✍🏻
*A SANADIN SON KI*
Written by
Aishat A Muh'd
Dedicated to my Sadeey SaNaz
*PAGE 77-78*
*_AFTER 2 WEEK'S_*
Duk wasu shirye shirye na bikin kusan an gama kammala komai sai jirab ranar lokacin wanda ya kama nan da next week zasu fara shagalin biki.
Amarya Suhaima kuwa ta k'ara wani irin kyau da cika a jikinta duk wani gyara na saman fata da ciki yi mata ake yi amman masu kyau da inganci ake amfani dasu, har anje anyi mata jeren kayanta a gidan Sabeer, sosai Yaya Aliyu yayi mata kok'arin siya mata kayan d'aki zuwa na kitchen na zamani don Aunty Aliya da Jiddah sai Suhaima suka tafi zuwa kasuwa suka siyo duk abin da ya dace.
Suhaima ce gaban dressing mirror tana taje dogon gashin kanta bayan ta gama taje wa ne ta d'aure shi da ribbon sannan ta mik'e ta zura wata black gown mai touch d'in red a jiki sai tayi rolling kanta da veil d'in gown d'in black shima, nan 'yar beautiful face nata ya fito gwanin sha'awa gata daman abin ka da fari cikin bak'in abu, bata yi wani makeup sosai ba simple make-up tayi daga powder sai red na jambaki da ta sanya ta taje kwantaccen gashin girar ta sai kawai ta fesa perfumes different colours ajikin ta masu sauk'in k'amshi.
Black flat shoes ta d'auko ta sanya a k'afar ta, gama sanya takalmin kenan taji wayarta na ringing d'auka tayi tare da yin picking cikin sanyin murya tace
"Hello! "
"Hi! Mata ta kina ina gashi na k'araso"
Fuskarta d'auke da murmishi tace
"Gani nan zuwa kana ina? "
Sai da ya lumshe ido kafin yace
"Baby ina zaune cikin mota a k'ofar gida"
"Okay gani nan zuwa"
Tana gama fad'in haka ta kashe wayar, sannan ta fito zuwa tsakar gida Aunty Aliya ce tana zaune sai faman shirya Ameer tayi wanda tayi mishi wanka yanzu, kallon ta tayi fuskarta d'auke da smiling tace
"Amarya tasha k'amshi hala angon ya k'araso?"
"Eh Aunty Aliya ya k'araso"
"Naga alama ai irin wannan kyau haka kada ki rud'a musu d'a ya kasa kai kanshi gida"
Cike da zolaya Aunty tace, sunk'e kai Suhaima tayi cikin 'yar jin kunya tace
"Kaiiii Aunty! "
"Gaskiya ne ai, ki tafi kin barshi a waje shi kadai"
Tashi tsaye tayi ta nufi k'ofar fita a gidan cikin tafiyar ta na nutsuwa, Aunty Aliya ta bita da kallo don kwalliyar nata ya birge ta.
Tana fita suka yi 4 eye's da Sabeer wanda yake tsaye ya jingina bayan shi da mota ya hard'e hannun shi saman kirjin shi ya zubawa k'ofar fitowa ido yana kallon ta inda Babyn shi zata fito.
Ajiyar zuciya ya sauke wanda Musaddiq da yake kusa dashi sai da yaji shi har ya d'ago daga danne dannen da yake a phone nashi suna charting da Mufidah ya kalli Sabeer sannan ya kalli inda yake kallo, ko ba'a fad'a mishi ba yasan wannan ce Suhaima amman yayi mamakin yanda sam batayi kama da en k'auyen ba anya ba zuwa take family d'in en uwanta hutu ba, sai dai kuma da ganin ta k'aramar yarinya ce sosai don bata fi 17 zuwa 18 ba, d'aga kafad'ar shi yayi alamar ba damuwar shi bane na sanin ko ita wace, don haka sai kawai ya cigaba da abin da yake.
Kallon ta Sabeer yake tamkar ya had'iye ta haka yake ji ko kuma ya d'auke ta ya tafi da ita gaba d'aya ta kid'ima shi, gaba d'aya Suhaima ta rasa nutsuwar ta saboda