Showing 69001 words to 72000 words out of 122360 words

Chapter 24 - A sanadin Son ki Hausa Novels Document complete by Aisha A Muhammad Sanaz.txt

irin kallon da Sabeer yake mata, kunya ce ta lullu6e ta kawai dakyar ta iya k'arasa wa inda suke tayi musu sallama amsawa sukayi kafin ta gaida su, nan Sabeer ya k'ara gabatar mata da Musaddiq a matsayin abokin shi na sosai, nan suka k'ara gaisawa tana tambayar shi iyalan shi.




Sannan Musaddiq ya shige cikin mota don shi ba mai son magana ba ne, zama Suhaima tayi saman wani dutse mai d'an fad'i da tsayi ta kasa magana duk a tak'ure take, ajiyar zuciya ya sake saukewa a karo na biyu sannan yace
"Baby nah ji nake tamkar na d'auke ki na gudu da ke, kinyi min kyau sosai "


Ya k'arasa fad'i eye's nashi akan lips nata har sai da ya had'iyi yawu har ya hango shi irin shan da zai mishi bana wasa ba kuwa idan ya kama shi.


"Baby kin yi shiru fah kin bar ni da surutu ni d'aya "
D'an murmishi kawai tayi kafin tace
"Ba haka bane ni na rasa abin da zance ne?"
"Haba yarinya daman mata tana rasa abin da zata ce idan zasu yi hira ita da mijinta "


Ya k'arasa maganar yana zama kusa da ita, d'an turo mishi bakinta kad'an tayi tukunna tace
"Toh! Ni mai zance maka"
"A'a babu komai kiyi ta kallona ma kawai "
D'an hararar shi tayi ta gefen ido kad'an, ashe ya gani d'an girgiza kai yayi yana murmishi yace
"Ni kike harara yarinya koh!?, ki cigaba komai da lokacin shi nima nawa ya kusa"


Sunkuyar da kanta tayi tana wasa da zoben azurfar hannun ta yayi da shi kuma ya tsurawa dogayen 'yan yatsun ta ido ji yake tamkar ya lashe su kai shi da yana da dama gaba d'ayan ta zai yi mata don yanda ta k'ara yi mishi wani kyau na daban.


"Duk naji event's d'in da zaku yi Baby sun isa ko zaku k'ara? "


"A'a sun ishe mu ni da ba wasu kawaye ne dani sosai ba, da Jiddah ma zata yarda iya walimah kawai zamu yi ''


"Haba Baby ayi mana har da dinner saboda aboki nane ya had'a mana gashi family d'ina sun had'a mana wata ranar da aka kawo min ke"
D'an shiru yayi yana kallonta kafin ya cigaba da cewa
"Ni sai naga kamar zasu takura min yaushe har aka gama dinner mu dawo gida sannan mu bawa junan mu kulawa... Uhm kin dai gane? "


Ya k'arasa maganar yana d'aga mata gira wata kunya ce ta sake lullu6e Suhaima daman haka Sabeer yake, ta rasa abin cewa tayi tsit da ita tamkar babu ita a wurin.


"Ya dai Baby ko kin gaji ne? "
"Uhmmm"
Kawai ta iya cewa don tana tsoron ya Kara 6aru mata wani sabon rashin kunyar tashi, nan dai sai ya sako wani zancen na daban sannan ta saki jikinta suka d'an ta6a hira.




"Washhh! Baby bari mu zo mu wuce gida kinsan wancen mutumin duk ya dame ni da kira yana tsoron kada matar shi ta rufe mishi k'ofa yak'i shiga gidan baya son yin nesa da matar shi sai dole "


"Uhm ai ya kyauta gwara yana bata kulawa matsayinta na matar shi, don mazan da basa kula da matansu haushin su nake ji"


"Eyyye Baby kice nima haka za'a na rik'e ni a gida "


"Ai bani zan ma rik'e ka ba da kanka zaka zauna ma " ta k'arasa maganar da murgud'a baki.
Er dariya kawai yayi yana cewa
"Huh Baby rigima ni ake murgud'a wa baki koh, to bari nazo na tafi baza ki k'ara gani na ba sai ranar dinner "


Nan suka yi sallama da junan su kamar kar ya tafi haka yake jin shi don gani yake 1 week d'in da ya rage musu ya mallaki Suhaima yayi mishi nisa, haka suka tafi duk jikin shi yayi sanyi har Musaddiq na tsokanar shi.




Bayan kwana 2 Jiddah ta dawo gidan su Suhaima tare da mai yin gyaran jiki wanda zata yi mata na tsayin kwanaki 5, sannan ta taho mata da d'inkunan ta gaba d'aya, a lokacin duk suka fitar da wanda zata yi amfani dasu komai da komai aka had'e su bag guda 2, sauran kayan lefen kuma Jiddah zata tafi dasu ta kai su gidan Suhaima, bayan duk sun gama shirye shiryen su sannan Jiddah ta tafi baza ta dawo ba sai ana gobe za'a yi kamu zata kai Suhaima wajen lalle da gyaran gashi ta tafi ta bar mai gyaran jikin anan.


Nan mai gyaran jikin nan ta cigaba da yiwa Suhaima duk da kyau da Suhaima ta k'ara wannan karon kuwa da Sabeer zai ga Suhaima mybe ya rud'e iya rud'ewa don kuwa wani irin laushi da santsi da fatar ta take yi na daban ne ga wani ni'imtaccen k'amshi da take fitarwa ta ko'ina a wajenta fatar ta har wani yellow yellow yake tsabar gyaran da tasha, ban da wanda Aunty Aliya take mata wanda fulani suke yi idan zasu aurar da yaran su.


**** **** ****




*KOMAI NISAN LOKACI....*




Kamar yau aka sanya bikin Sabeer da Suhaima tsayin 3 month's sai gashi lokaci yazo kamar kiftawar ido, tun ranar talata da safe wajen 10am Jiddah tana gidan su Suhaima har Yaya Aliyu yana mata fad'an yawan zirga zirgar ta yayi yawa kada ta cutar da Babynta ko ita kanta don gashi cikin nata ya d'an fito kad'an ana ganin shi don ma dogowa ce shi yasa ya 6oye a jikinta, zum6ura baki tayi tana cewa
"Ni dai Yaya Aliyu ka kyale mu nan da kwana 3 ma fah har angama bikin "


Murmishi kawai yayi ya girgiza kai sannan ya fita daga gidan soyayya tsakanin Suhaima da Jiddah daga Allah ce had'in Ubangiji ne.


Agurguje suka gama breakfast sannan suka tafi zuwa cikin gari har da mai gyaran jikin suka tafi zasu ajiye ta a gidanta, suna ajiye ta kuwa suka nufi wajen wani katafaren shago wanda ake gyaran gashi, kunshi da komai ma wanda ya kunshi gyaran jiki.


Suna zuwa mai shagon musulma ce nan ta tar6e su cikin fara'a bayan ta basu wajen zama sun zauna suka gaisa sannan Jiddah tace
"Sister gyaran gashi da lalle irin na amare zaku yi mata wanda zaku zage iyakar fasahar ta ku yi mata, don inason Yah Sabeer ya ganta ya rud'e da yawa "


Dariya suka yi Jiddah da mai shagon tare da tafawa tace
"Kada ki damu Hajia Jiddah kinsan mu ba yabon kai ba mun iya abubuwa na kwarewa a wajen nan don haka zaki sha mamaki da kaina zan yi mata ma don nasan Yalla6ai Sabeer ya cika miki bag da money"


"Kamar kuwa kinsani don ba k'aramin ji da Babyn nan nashi yake ba"
"Naga alama ai gashi sun dace da junan su kyawawa dasu "


Daga nan aka fara yiwa Suhaima gyara tun daga wankin k'afa zuwa manicure and pedicure, sannan aka fara yaryad'a mata lalle ja da bak'i irin na amare, amaren ma 'yan gata.




Bayan an gama yin lallen ne ya kama iya lokacin da ake buk'atar shi aka wanke shi, wow masha Allah kowa awajen haka yake fad'i ganin irin wani mugun kyau da yayi wa Suhaima tamakar lik'ashi aka yi ba zanawa shi aka yi ba.


Daga nan aka fara yi mata gyaran gashi shima an d'auki tsayin lokaci ana yin shi Suhaima ta fito tsaf da ita gwanin sha'awa ko mace ta ganta zata birge ta balle uban gayyar ya ganta ai ba magana, itama Jidda sai da akayi mata lallen da gyaran gashin tukunna suka biya ta.


Har sun fita Jiddah ta dawo tace
"Sister gobe fah kizo gidan nawa wajen 4pm zaki mata makeup don gobe ne kamu bama son african time ne"
"Kada ki damu Hajia Jiddah zan zo akan lokaci "
"Okay sai anjima "


Fitowa tayi daga shagon ta shiga bayan motar inda Suhaima take zaune nan driver yaja su sai gidan Jiddah
, suna zuwa sallah suka yi sannan suka ci abinci suka zauna hutuwa.


"Washhh! Allah na gaji Jiddah sosai "
Cewar Suhaima tana yatsina fuska, dariya Jiddah tayi kafin tace
"Yarinya ai agajiya baki yi komai ba sai an fara event's don ma ba wani event's da yawa zamu yi ba"


D'an zaro ido Suhaima tayi kan tace
"Ke ce sai k'asusuwa na sun kusa 6a66alewa"
Tuntsire wa da dariya Jiddah ta sake sannan tace
"Idan ma sun 6alle Yayana zai gyara su"
Murmishi kawai Suhaima tayi nan suka suka cigaba da hirar su, kafin kuma suka k'ara fita zuwa wajen da zasu gabatar da event na kamu wajen yayi kyau sosai duk da ba'a yi mishi decoration ba sai gobe da safe wad'anda aka d'auko zasu yi, bayan sun gama ganin wajen ne suka dawo gida.


Sai wajen 5 na yamma Suhaima ta fito drive zai mayar da ita gida, nan Jiddah tace
"Gobe fah da safe za'a zo a d'auke ki ke da kawayen ki wad'anda zasu je nasan Aunty Aliya ma zata zo da Babaa Lantana ma duk su zo"


Gid'a kai kawai Suhaima tayi ta rufe murfin motar suka tafi sai after ishsha su iso gida tana fita daga motar driver ya juya ya tafi yayin da Suhaima ta k'arasa shiga gidan agajiye take lik'is.






Wanka kawai ta iya yi tabi lafiyar katifa ko takan abinci bata bi don a k'oshe take, bacci mai nauyi ne ya d'auke ta don ko kiran da Sabeer yayi bata ji ba, shima a nashi 6angaren yasan gajiya tayi kawai don haka shima ya kwanta amman yaso jin muryar ta kuwa.




Washe gari da safe kuwa Suhaima kusan makara tayi ma don lokacin da take breakfast ma wajen 11 na safe a lokacin Jiddah ta kirata ta shirya driver ya taho, tana kashe wayar ne ta lalubo number Sabeer ta kirawo shi don taga kiranshi na jiya da dare, bai d'aga ba sai ya kashe kiran nata shi ya kirawo ta.


"Amaryar ta ina son ganin beautiful face naki nayi kewar ki da yawa kodan anjima zamu had'u a wajen kamu zan ga yanda Baby na ta koma tsayin kwanaki 6 ban gan ki ba nasan kin k'ara girma ta ko'ina koh? "


Shiru tayi mishi murmishi yayi don yasan bazata amsa ba, kafin kuma su d'an ta6a hirar su irin ta masoya daga k'arshe suka yi sallama da junan su, tashi tayi ta zura hijab nata fari mai hannu kawai ta fito don taji Aunty Aliya tana ce mata ga driven yazo.


"Yanzu Aunty babu da wanda zan tafi ni kadai zan tafi"
"Eh Suhaima ki tafi kawai zamu taho da yamma kafin a fara kamun kin ji "
Gid'a kanta tayi cikin sanyin jiki ta fice daga gidan.


Suna zuwa gidan Jiddah mota nayin parking Jiddah ma ta shigo gidan ita take driving d'in ma.
"Amaryar mu kin ganni ko wallahi daga wurin da za'a yi kamun nake naje naga yanda suka shirya wajen yayi kyau "
Cewar Jidda tana rik'o hannun ta suka k'arasa cikin gidan.
"Ya banga su Aunty Aliya ba? "
"Zasu taho anjima sun ce "
"Okay Allah yasa su zo"
"Amin, ni fah agajiye nake har yanzu fah "
Fad'in Suhaima kenan tana hamma, dariya Jiddah tayi kan tace
"Sai ki je ki kwanta kafin lokaci yayi "
Nan ta wuce bedroom na Jiddah tayi kwanciyar ta babu dad'e wa bacci ya d'auke ta kuwa.






Sai azahar Jiddah ta tashi Suhaima bayan tayi sallah suka ci abinci sannan Jiddah ta fara fito da kayan da Suhaima zata sanya suna yin er hirar su, bayan sun yi salllahr la'asar ne Suhaima ta shiga wanka tana shiga mai yin makeup ta zo don haka tana fitowa ta shafa wani cream mai kyau da k'amshi ta sanya underwears sannan ta zura wata gown har k'asa ash and silver, ash colour ne sai touch d'in flowers silver, bayan ta gama sawa ne ta zauna aka fara tsantsara mata makeup wanda suka kwashi tsayin lokaci suna yi sannan aka d'aura mata abin head silver sai takalmin ta hill ne ash & silver haka ma purse d'in hannun ta take, wow masha Allah tubarakallahu ahasanul kaliqeen duk hassadar mutum sai yasan Suhaima tayi kyau bana kad'an ba sannan aka d'ora mata wani veil mai d'an girma kad'an saman kafad'un ta.


Nan ta fah Jiddah da mai yin makeup suka fara sumbatun kyan da Suhaima tayi nan Jiddah ma tayi gayun ta cikin wani maroon lace sai ta d'aura silver asaman kanta itama tayi kyau, suna gama wa lokacin har 5 ta wuce da wajen 10 minutes agurguje suka tafi wurin kamu, wajen yayi kyau sosai ga mutane nan sosai an zazzau haka families d'in Sabeer sun zo su ma da yawa Dr Faridah ce kawai ban hango ba ko Hajjah Hauwaa ma na hango ta anci gayu an cakare.


Jiddah tana rik'e da hannun Suhaima a mazaunin da zasu zauna da Sabeer, sai da Jiddah ta zaunar da ita sannan ta bar wurin aikuwa tasha harara a wajen 'yan uwanta sai kawai ta d'auke kanta, slow music ne ke tashi a wurin kawai mai dad'in saurare.


Babu jimawa ango Sabeer ya shigo yana sanye cikin wani d'anyen boyel ash colour hular shi ash da ratsin bak'i takalmin shi bak'i sai agogon hannum shi k'irar gucci black shima sai tashi wani k'asaitaccen k'amshi yake bayan shi friend's nashi 2 ne Musaddiq da Khaleel suma sun yi gayun shi sunyi kyau sosai, nan Sabeer ya zauna kusa da Suhaima sannan friends nashi suka zauna inda aka tanadar musu don zama.


Kallon ta Sabeer yake har yaso ya mance ma a inda yake don gaba d'aya Babyn nashi ta canja mishi kamar ba ita ba, sunkuyawa yayi da kanshi dai dai kunnen ta yace
"Baby nah kin had'u da yawa kinyi kyau sosai dama zamu dawwama a haka ni da kai "
D'an murmishi ta saki tana yin k'asa da kanta don kunya hannun ta ya lalubo ya damk'e cikin nashi wani tattausan laushi yaji ya ratsa shi lokacin da ya rik'o hannun ta har sai da ya lumshe eyes nashi, yayi da Suhaima taji wani irin shock ajikin ta tana kok'arin zame hannun ta ya Kara damk'e su duk kunya ta gama lullu6e ta don kamar tana ganin mutanen wurin suna kallon hannun su sark'e cikin na junan su.




Nan aka cigaba da gudanar da kamun har zuwa lokacin da su Aunty Aliya suka k'araso, Babaa Lantana da Hajjah Hauwaa ne suka fesa musu perfumes a jikin su nan aka saki gud'a sannan Sabeer ya mik'e ya fara zuba wa Suhaima kud'i a jikinta yana mata lik'i nan sauran friends nashi da en uwa suma suka taso ana ta zuba lik'i kafin daga k'arshe aka fara ciye ciyen abubuwan da aka tanada.


Juyowar da zan d'an yi da kaina sai na hango my Sadeey da Biebie dee sun wage baki suna yagar naman kaji tamkar yau suka fara ci... lol, can gaba kuma na hango Mommana Aunty Jiddah da twins nata a zaune suna shan drinks a nutse nan na k'arasa na kwashi gaisuwa ta, juyawar da zanyi na hango gungun en group d'ina suna wawason shinkafa kaza duk sunyi dumu dumu da kayansu gaba d'aya 🤣😜 sai kawai na d'auke kaina don kada su ganni su nuna sun sanni su ba da ni a gaban en uwan Sabeer lols, duk fan's nasu Sabeer da Suhaima sun halaccin wajen sosai sunyi karar zuwa.


Daga nan bayan an gama cin abubuwa ne aka d'ad'auki pic's sannan aka fara tafiya saboda har an fara kiran sallahr mangarib ma, dakyar Sabeer ya iya rabuwa da Suhaima don ji yake kamar ya tafi da ita gashi ko damar su dan ke6e ma basu samu ba, ko gidan Jiddah bata koma ba Sabeer ya sanya drive ya mayar dasu gida.




Kayan jikin ta kawai ta iya cirewa ta watsa ruwa ajikinta tana sanya sleeping dress ta kwanta, tana cikin yin addu'ar bacci Aunty Aliya ta shigo hannun ta d'auke da wani cup ta mik'awa Suhaima bata tsaya tambaya ba ta kar6a ta shanye tana yatsina fuska ta mik'awa Aunty Aliya cup d'in sannan ta janyo blanket ta rufa itam Aunty Aliya fitowa tayi daga d'akin, bacci mai nauyi ne ya d'auki Suhaima.






_gobe insha Allah zaku ga next pag fan's_






Aishat A Muh'd ✍🏻
*A SANADIN SON KI*






Written by
Aishat A Muh'd


Dedicated to my Sadeey SaNaz










*PAGE 79-80*












Washe gari kuma shine ranar dinner d'in da friend d'in Sabeer wato Muusaddiq ya shirya musu don haka Suhaima ma ranar ma wajen azahar driver ya d'auke ta sai gidan Jiddah ita da wasu friends nata guda 5 wad'anda suka yi islamia dasu kuma kawayen ta na cikin unguwa, lokacin da suka k'arasa ma Jiddah bata nan ta tafi gidan su nan suka zauna a palour suna hirar su mai aikinta ta shirya musu abubuwa ci dana sha ta kawo musu sai after la'asar Jiddah ta yakice jikin ta dakyar ta taho gidan don sun yi waya da Suhaima sun zo.




*_8:40pm_*


Wata had'add'iyar mota black sai shek'i take da ganin ta kasan sabuwa ce tayi parking a compound d'in gidan Jiddah, ko mintuna biyar bata yi da parking ba sai ga su Suhaima sun fito wow masha Allah nace ganin yanda Suhaima tayi wani masifar kyau cikin wata gown har k'asa take ja sosai hannun rigar dogo ne har karshen hannu peach colour ne mai d'an haske tana da adon flower's manya shima kalar peach ne da kyallin duwatsu silver ajiki, sai abin nad'in kanta peach ne mai d'an duhu sai veil mai d'an girma an yafashi a saman kafad'un ta, tana sanye cikin shoes hill peach da purse nata itama kalar takalmin tasha wata sark'ar gold babba mai d'an girma a wuyanta haka ma hannun ta warwaron gold ne kowanne hannu guda hud'u hud'u tasha heavy makeup irin na bride, fuskar ta sai wani shek'i take kyau iyakar kyau Suhaima tayi shi sai tashin wani sanyayen k'amshi take yi ajikinta mai rikita mutum ya rasa irin

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login