Showing 105001 words to 108000 words out of 122360 words

Chapter 36 - A sanadin Son ki Hausa Novels Document complete by Aisha A Muhammad Sanaz.txt

riga ta sanyi aciki wanda mutum zai sanya ya ji d'umi.


Ahaka ta zura mishi T-shirt mai dogon hannu sannan ta lullu6e shi da blanket idanun shi har zuwa lokacin a lumshe yana jan numfashi dakyar gashi jikin shi yayi zafi sosai, jik'akk'un kayan ta d'iba ta fitar dasu waje ta ajiye sannan ta dawo dakin ta zauna kusa da Sabeer tare da rik'e mishi hannu tana kallon shi hawaye na fita a idanun ta...........






Aıʂɧąɬ A Mųɧ'ɖ ✍🏻


*A̺͆ S̺͆A̺͆N̺͆A̺͆D̺͆I̺͆N̺͆ S̺͆O̺͆N̺͆ K̺͆I̺͆*








Wྂrྂiྂtྂtྂeྂnྂ bྂyྂ
Aྂıʂɧąɬ Aྂ Mྂųɧ'ɖ




ɖɛɖı¢ąɬɛɖ ɬơ ɱყ ʂąɖɛɛყ ʂąŋąʑ




♻ *єχ¢ℓυѕινє ωяιтєя'ѕ fσяυм*





*PAGE 108-109*














Da sauri ta mik'e tsaye tare da matsawa can nesa da Sabeer saboda jin ana kok'arin shigowa d'akin, Yah Aliyu ne ya shigo hannun shi rik'e da magani sai Aunty Aliyah dake bayan shi tana rik'e da k'aramin flaks na tea da k'aramin cup na shan tea suka shigo cikin d'akin da sallama, Suhaima ce ta amsa musu sallamar.


"Ya samu bacci ne? "
Yah Aliyu ya tambayi Suhaima, girgiza kanta tayi kafin tace
"A'a idanun shine a lumshe amman bai yi bacci ba "


Juyowa Aliyu yayi tare da cewa
"Sannu Sabeer zaka iya tashi kasha shayi da magani? "
Ahankali ya bud'e eyes nashi tare da d'aga mishi kai, yunkura ya fara yi zai mik'e ya zauna amman sai ya koma ya kwanta don jikin shi babu k'arfi, ganin haka ya sanya Yah Aliyu taimaka mishi ya zauna bayan shi ya sanya mishi pillow biyu don yaji dad'in zaman.


Shayin Aliyah ta mik'awa Aliyu nan ya dunga bashi da spoon yana sha da d'an zafin shi kad'an yanda bazai k'ona shi ba, sai da ya sha wajen cikin cup d'in don yaji dad'in tea d'in sannan Yah Aliyu ya bashi magani yasha, bayan ya gama shan maganin Yah Aliyu ya kalle shi tare da cewa


"Sabeer na yarda na amince Suhaima zata koma gidan ka da zama, nasan kai masoyin ta ne na gaskiya Allah ya baku zaman lafiya "


Duk da Sabeer jikinshi babu k'arfi sai da yayi kok'arin rungume Yah Aliyu cikin tsananin farinciki ga hawaye suna zuba a eyes nashi, cikin muryar mara lafiya yace


"Thank U Babban Yayah bani da bakin yi maka godiya naji dad'i sosai Allah ya saka maka da alkhairi, kuma insha Allah zan rik'e Suhaima sosai bazan k'ara kwatanta hakan ba "


Bubbuga bayan shi Yah Aliyu yayi then yace
"Yanzu ka kwanta ka huta sosai gobe ma k'arasa maganar "


Yana gama fad'in haka ya gyara mishi kwanciyar shi sannan ya kalli Suhaima wadda tayi mutuwar tsaye jin abin da Yah Aliyu ya fad'a, cikin murmishi yace
"K'anwata ki cigaba da hak'uri tare da yiwa mijin ki biyayya Allah yayi miki albarka "


Yana gama fad'in haka ya janyo hannun Aunty Aliyah suka fita daga d'akin tare da ja musu k'ofar d'akin su suka wuce kowannen su zuciyar shi fes musamman Yah Aliyu sai yake jin shi sakayau kamar wanda aka d'auke mishi wani gungumeman dutse akanshi.




Jingina tayi da bangon d'akin ta d'aga kanta sama idanun ta a lumshe wasu hawaye ne suke fita cikin idonta wanda ta kasa banbance hawayen mene.




Tun d'azu ya tsura mata ido yana kallonta ji yake da zai iya mik'ewa tsaye zuwa inda take zai yi ya rungume ta cikin jikin shi ta fad'a mishi dalilin zubar hawayen ta ya kuma rarrashe ta tare da nuna mata tsantsar k'aunar ta ya nuna mata yanda yake jinta cikin ran shi sai dai ba damar hakan sai ido ya zuba mata.




Hannu ta sanya tare da goge hawayen face nata ta bud'e idonta a hankali tare da sauke su kan Sabeer had'a ido suka yi da junan su da sauri ta janye nata eyes d'in ta wuce zuwa wajen wardrobe nata ta bude shi d'ayan bargo ta d'auko ta shimfid'a a k'asan carpet sannan ta wuce ta rufe k'ofar d'akin da key kafin ta shiga toilet ta d'an jima a ciki ta fito.


Wajen bed ta k'arasa ta gyara mishi lullu6ar jikinshi sannan ta d'auki pillow ta kashe fitilar d'akin sannan ta koma inda ta shimfid'a bargon ta kwanta tare da yin addu'ar bacci ta shafe jikinta ta juyawa Sabeer baya.






Duk abin da take yana kallonta har lokacin da ta kwanta ta juya mishi baya, d'an murmishi ya saki kawai zuciyar shi fal farin ciki da haka bacci mai nauyi ya d'auke shi da yake cikin maganin da Yah Aliyu ya siyo mishi yasha akwai na mura aciki.






Washe gari da safe Suhaima ta makara sosai wajen tashi daga bacci don har wurin 7am takai tana bacci, duk da shima Sabeer d'in ya makara amman ya rigata tashi ya lalla6a ya shiga toilet ya d'aura alwala yayi sallah bayan ya gama addu'o'in shi ne ya tashi domin ya k'arasa wajen Suhaima ya tashe ta.




Tsugunnawa yayi a gabanta yana kallonta d'an murmishi yayi ganin yanda ta k'ank'ame jikinta alamar tana jin sanyi don har zuwa yanzu da sanyi garin gashi da duhun hadari, hannun shi ya sanya yana shafa mata face nata cikin nutsuwa.




Far tayi ta bud'e eyes nata wanda ya haddasawa Sabeer wata muguwar kasala wanda ya sanya shi zama a kan carpet ya k'ura mata ido cikin wani yanayi daban, d'an hararar shi tayi tare da murgud'a mishi baki ta mik'e ta wuce toilet da kallo ya bita yana murmishi sannan ya girgiza kanshi har yanzu tsiwar tana nan ba'a daina ba.




Bayan ta idar da sallah ne agurguje ta wanke toilet tsaf tazo ta gyara bedroom d'in amman ban da kan bed saboda Sabeer da yake kwance akai yana bin ta da mayataccen kallon shi, bayan ta gama ta fita zuwa tsakar gida ta tarar har Yah Aliyu ya wuce schl Aunty Aliyah kuma ta gama komai ta gyara gidan tsaf.




Gaida ta Suhaima tayi tana tambayar ta mai jiki bata amsa ba ta wuce kitchen tana cewa
"Aunty da akwai ruwan zafi zanyi wanka? "


Murmishi tayi kafin tace
"Da akwai na dafa muku don nasan zaku nema "


D'an zaro ido kad'an Suhaima tayi gabanta ya fad'i kada Aunty Aliyah ta zargi ko sunyi wani abun bayan babu abin da ya faru tsakanin su, sai kuma ta share kawai ta d'ebo wanda zai ishesu wanka ta wuce d'akin bata k'ara bi takan Aunty Aliyah ba don ta bata kunya.




"Idan ki kai ruwan ga abin karyawa nan kizo ki d'aukar muku "


"Toh "
Kawai tace ta shige d'akin, had'a mishi ruwan wanka tayi sannan ta fito tana kok'arin yi mishi magana yace
"Baby nah kin tashi lafiya?"


Kauda kanta tayi bata amsa ba sai kawai tace mishi
"Na had'a maka ruwan wanka "
Tana gama fad'in haka ta wuce ta fita zuwa waje, kayan breakfast d'in ta d'auko musu ta kawo d'akin ta tarar dashi har ya shiga wanka, gyaran kan bed tayi ta d'ameshi sosai yayi kyau.




Kayan shi ta duba taga duk sunyi datti da squeezing sai iya wanda ya sanya jiya da dare masu kyau daman kayan gaba d'ayan su kala 4 ne ya taho dasu, tana nan tsaye tana tunanin mafitar wanne kaya zai sanya sai gashi ya fito daga toilet d'in yana daure da towel d'in Suhaima wanda dakyar ya ritsa shi d'ayan hannun shi kuma rik'e da kayan da ya cire su.




Kallo d'aya Suhaima tayi mishi ta d'auke kanta kawai ta tattaro kayan shi masu datti ta k'arasa inda yake ta fisge masu dattin wanda ya cire tayi fita daga d'akin da sauri, da kallo ya bita yana murmishi kawai.




Tana fita kayan ta had'a ta fara wanke mishi tana gama wanke su ta koma cikin d'akin har zuwa lokacin yana zaune gefen gado dashi da towel d'in kanshi a sunkuye yana ciccila k'afa.




Had'a mishi tea tayi sannan ta zuba mishi jellop d'in da akayi na taliya a plate, kusa dashi ta ajiye mishi tare da maganin shi dakyar ta iya cewa


"Ga breakfast d'in ka nan "


Tana gama fad'in haka ta wuce toilet don yin wanka, a nutse yake shan tea d'in har yasha rabin cup sannan ya d'auki taliyar kad'an ya iya ci ya ajiye yasha maganin shi da ragowar tea d'in.




Fitowa tayi daga toilet tana daure da zani ta dubi dressing mirror k'ara had'e fuska tayi ganin yana bin ta da mayataccen kallon shi, tana tsaka da shafa mai ne taji lallausan hannun Sabeer yana yawo a jikinta da sauri ta sanya hannun ta tana kok'arin cire hannun shi amman sai taga ya zube saman gwiwowin shi ya kama hannunta dukka biyun ya had'e dana shi yana kallon cikin idonta yace


"Baby nah da farko ina neman yafiyar ki akan abin da nayi miki, ina rok'an ki da ki yafe min nasan nayi kuskure ban kyauta miki ba da na kasa gane makirci aka had'a mana don kawai a raba mu nayi nadamar hakan, wallahi Baby ina son ki sosai kullum sonki k'ara shiga zuciyata yake i luv U with oll my heart "


Shiru tayi mishi hawaye ne zasu zuba daga idonta da sauri ya girgiza mata kanta kan yace
"No Baby kada kiyi kuka please, kukan ya isa haka bana buk'atar sake ganin zubar hawayen nan "
Dole ta had'iye kukan amman duk da haka sai da wad'annan hawayen da suka fara fitowa suka zubo, hannun shi ya sanya ya goge su yana cewa
"Baby kice kin hakura kin yafe min zamu koma zama da junan mu kamar da "


Rungume shi Suhaima tayi tana cewa
"Komai ya wuce a wurina, sai dai ina tsoron komawa gidan ka "
Ta k'arasa fad'a duk alamar tsoro ya bayyana a face nata, wani tausayin ta ne ya kamashi yasan da gaske take fad'in haka har cikin zuciyar ta, bubbuga bayan ta ya fara yi yana cewa


"Baby anan zamu zauna baza mu tafi ko'ina ba har sai kin amince da kanki zaki koma gidan ki, kin yarda da haka? "


Cikin jin dad'i ta saki murmishi wanda shine na farko da tayi mishi tun zuwan shi kauyen su tace
"Na yarda da hakan sosai "
Jan hancin ta yayi kad'an yace
"Naji dad'in haka Baby nah zan kasance mai faranta miki rai har k'arshe rayuwata insha Allah "


Ya k'arasa fad'a yana matse ta ajikin shi har sai da tace
"Wash! You are hurting me "
Sannan ya sassauta ruk'an da yayi mata kafin tace
"Kaje ka kwanta tunda baka da lafiya "


"Waya fad'a miki aini na warke daman ciwon so ne ya kwantar dani gashi kuma na samu maganin shi "


D'an hararar shi tayi tana turo baki bata ankara ba taji lips d'in shi kan nata, sun d'auki wajen 5 minute a haka kafin su rabu da junan su suna sauke ajiyar zuciya kallon junan su suke cikin wani shauk'i.






***********




Hango Dr Faridah nayi cikin katafaren palourn ta tana faman safa da marwa kallo d'aya zaka yi mata kasan hankalin ta a matuk'ar tashe yake, don yau kimanin wajen sati 3 bata samun wayar Sabeer daga dukannin number's d'in na k'asar waje wanda yake amfani dasu.




Kullum tayi try numbers d'in a kashe harda ta gida 9ja ma, abin yayi matuk'ar d'aga mata hankali don kuwa hakan bai ta6a faruwa dasu ba, tananin wanne hali Sabeer yake ciki don ta tabbatar Sabeer baya cikin Nigeria tun da har da ita aka raka shi airport.


To ina ya shiga?, dum gaban ta ya fad'i da tuna ko yana tare da wannan shegiyar yarinyar, amman kuma tasan Sabeer baya k'asar, da sauri cikin rawar jiki ta d'auko phone nata ta shiga searching d'in numbers d'in shi na Nigeria domin ta bibbiyi layin nashi ko yana nan Nigeria bai tafi ba yaudarar ta yayi.


Sai dai har taga ma searching nata bata ga wata alama ba don nuna mata ake layukan suna kashe, jefar da wayar tayi tare da d'ora hannunta saman kanta gaba d'aya ta tallafi kan nata, gashi har zuwa yanzu Daddy baya bata fuskar tayi mishi magana balle ta fad'a mishi matsalar ta ina d'anta ya shiga, wasu hawaye ne masu zafi suka fara sauka kan fuskar ta na tsabar kewar d'annata da tayi ji take kamar ta shekara 3 bata ganshi ba............








Aıʂɧąɬ A Mųɧ'ɖ ✍🏻


*A SANADIN SON KI*








Wྂrྂiྂtྂtྂeྂnྂ bྂyྂ
Aྂıʂɧąɬ Aྂ Mྂųɧ'ɖ




ɖɛɖı¢ąɬɛɖ ɬơ ɱყ ʂąɖɛɛყ ʂąŋąʑ




♻ *єχ¢ℓυѕινє ωяιтєя'ѕ fσяυм*





*PAGE 110*


















Tana zaune a palourn tana wannan tunanin tunanin ga hawaye kaca kaca a face nata Daddy ya shigo parlourn kallo d'aya yayi mata ya d'auke kanshi kada ta karya mishi gwiwa don kwanakin biyun nan tana bashi tausayi ta sanya damuwa akanta saboda rashin jin muryar d'an nata, duk ta rame ta fara zama silent sosai, kok'arin hawa steps na bene yake yaji muryar ta na cewa


"Daddyn Sabeer ina son magana da kai please "


Ko kallonta Daddy bai yi ba ya fara hawa steps don har yanzu bai ga tayi laushi sosai ba na yanda zai sanar mata inda Sabeer yake.


Ganin Daddy ya shareta ne ya sanya ta tashi da sauri ta bi bayan shi, har zai shiga side d'in shi tayi saurin rik'o hannun shi cikin muryar kuka tace


"Don girman Allah Dear ka fad'a min inda Son yake? "


Hannun shi ya sanya wanda bata rik'e nashin ba ya zame nata hannun yayi gaba kawai ya shige side d'in shi, nan Mumy aka durk'ushe tare da sakin kuka na tashin hankali.


Daddy jingina bayan shi yayi da bayan door tare da runtse eyes nashi tausayin ta ne yake neman rinjayar zuciyar shi don yasan yana son Dr Faridah so bana kad'an ba, ba k'aramin wahala yake sha ba na wannan zaman da suke yi tare amman bashi da yanda za yi dole ya nuna mata kuskurenta na zubar mishi da en jikokin shi da tayi so yake tayu nadama sosai yanda a lokacin zai sanar mata da inda d'anta yake, amman fah kukan ta yana ta6a mishi zuciya sosai.




Sai da tasha kukanta ta more sannan ta mik'e ta wuce side d'in ta hawaye na zuba a eyes nata, kamar wata mahaukaciya sabon kamu take faman gwada kiran number's d'in Sabeer na dukkan k'asar da tasan yake zuwa har da ta gida Nigeria amman dukka abu d'aya nau'ora take sanar da ita a kashe suke, zaman tayi kan bed tare da rafka tagumi dole ta fara binciken inda Sabeer ya tafi bazata zauna ba batasan halin da Sabeer yake ciki ba.






***********




Zaune Suhaima take kusa da Aunty Aliyah suna aikin girki na dare suna er hirar su cikin nishad'i, Yah Aliyu ya fito daga palon Aunty Aliyah hannun shi rik'e da phone nashi kallon su yayi tare da girgiza kai kullum haka suke kamar abokanan juna ya fad'i hakan cikin zuciyar shi, mik'awa Suhaima wayar yayi ba tare da yace mata komai ba ya juya zuwa cikin palon.


Da kallo ta bishi cikin mamaki wane yake kiranta haka, kawai sai ta sanya wayar a kunnen ta jin ana magana, wani zabura tayi tare da tashi tsaye ta buga tsalle da ihu murna tana furta


"Jiddahhhh"


Sabeer da yake kwance kan bed cikin d'akin Suhaima da sauri ya taso jin muryar Suhaima tana ihu, turus yaja ya tsaya da yaji ta ambaci sunan Jiddah, tsayawa yayi bai k'arasa fitowa ba daga d'akin tare da hard'e hannun shi dukka biyun yana kallonta yanda take tsallen murna, murmishi ya saki cikin zuciyar shi yana cewa


"Baby nah har yanzu yarinta na damun ki halin nan yana nan bai canja ba "
Ya fad'i hakan cikin zuciyar shi yana kok'arin komawa cikin d'akin suka had'a ido da ita hura mata kiss yayi sannan ya shige cikin d'akin.






Murmishi Suhaima tayi da taga abin da Sabeer yayi mata nan ta cigaba da waya da Jiddah cikin farinciki taji dad'in sakkowar Yah Aliyu sosai kodan kewar Jiddah tayi sosai, bayan sun sha hirar su Jidda cikin d'oki take fad'a mata gobe zata zo daga k'arshe suka yi sallama cikin kewar junan su.


Aunty Aliyah na zaune tana kallon ta murmishi kawai take ganin yanda Suhaima suke waya cikin d'oki, zama tayi tana cewa


"Wallahi Aunty nayi kewar Jiddah sosai naji dad'in yanda Yah Aliyu shi ya kirawo ta da kanshi ya had'a mu "


"Nima kaina naji dad'in hakan Suhaima Allah ya bar wannan kauna dai"


"Amin Aunty, gobe ma tace zata zo "


"Allah ya kaimu sai kiyi shirin yin dambu ko d'an wake don nasan halin Jiddah da son cin su idan tazo gashi an kwana 2 bata zo nan ba "


Cikin murmishi Suhaima tace
"Haka ne kuwa Aunty nah kin ma tuna min gobe da wuri zan tashi na fara hidimar taryan ta kinsan Jiddah da d'oki da wuri zaki ganta"




D'an hararar wasa tayi mata kan tace
"Wanne tashi wuri kuma kimsan dai mijin ki na nan gashi baya jin dad'i zama zaki ki kula dashi naji da hidimar Jiddah "


Kwa6e fuska Suhaima tayi tare da shagwa6e wa har da karyar da wuya tace
"Kaiii Aunty bayan ya warke kuma gaskiya ni zan yi "


Girgiza kai Aunty tayi kafin tace
"A'a Suhaima ki bawa mijin ki kulawa yafi koma ni zanji da komai"




Bata son yin musa da ita don haka tace
"Toh Aunty "


"Yawwa tawan dad'i na dake bakya jayayya Allah ya bamu jikoki twins "


Wata kunya ce ta rufe Suhaima musamman da taji Yah Aliyu ya amsa da
"Amin Mata ta "
Wanda ya fito zai fita yaji Aunty Aliyah tana wannan addu'ar, da gudu Suhaima ta mik'e ta wuce cikin d'aki kunya sosai ta rufe ta kamar ta nutse, yayin da Yah Aliyu da Aunty Aliyah suka sanya dariya har da tafawa da hannun su.




Bayan ta yana jingine a bayan k'ofa eyes nata a lumshe tana murmishi bata ankara ba taji saukar kissing a wuyan wanda ya haddasa mata sauke ajiyar zuciya tare da bud'e idonta sauke su tayi kan na Sabeer wanda daman kallonta yake.




Da sauri tayi niyyar wuce wa cikin d'akin ya sanya hannu tare

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login