Showing 12001 words to 15000 words out of 122360 words
Chapter 5 - A sanadin Son ki Hausa Novels Document complete by Aisha A Muhammad Sanaz.txt
kuma ya bawa Dr Faridah kyautar wani gida babba mai kyau da wata had'add'iyar mota jeep duk gift ne na jin dad'in haihuwar Sabeer, Hajjah Hauwaa kuwa gift d'in sark'ar gold ta bata tsadaddu dasu tun daga sark'a, d'an kunne abin hannu (warwaro), sark'ar k'afa da kuma rings guda biyu kud'i sosai ta fitar ta siya mata su.
Haka Sabeer ya cigaba da girma ana ji dashi sosai, makarantar shi dukka a k'asar waje yayi su, Sabeer kyakkyawan matashin saurayi ne d'an shekara 27-28 ya had'u ta ko'ina ga kyau ga kud'i, sai dai sangartacce ne na ajin k'arshe gashi d'an shagwa6a don iyayen shi da kakannin shi sunyi matuk'ar sangartashi, so suke nuna mishi sosai gashi daman shi kad'ai Allah ya basu ba kwa6a ba harara duk abin da yake so suna yi mishi sosai, Sabeer bai ta6a neman wani abu ya rasa ba, duk abin da yace yana so jiki na 6ari ake yi mishi don kada ranshi ya 6aci, gata sosai yake samu gashi yanzu ya kammala karatun shi ya dawo gida.
**** **** ****
CIGABAN LABARI...
Yana fita daga side d'in nasu part's d'in kakannin nashi ya nufa yana wani yatsina fuska tamkar wani mai jin amai, ya sanyo kanshi cikin babban parlour d'in sai ga wata house girl ta taho fita hannun ta d'auke da tire wanda saman shi jug ne mai d'auke da so6o sanyaye sai k'ananun cups akai guda biyu da d'an wani bowl guda uku 'yan manya d'aya na d'auke da cup cakes, d'aya kuma egg rolls sai na k'arshen samosa, irin tazo zata wuce ta kusa da Sabeer sai tsautsayi ya sanya tsantsin tiles ya kwashe ta gaba d'aya tayi baya kayan hannun ta kuma suka yi kan Sabeer.
Unexpected yaji saukar abu mai sanyi da d'umi a jikin shi sai wani cup d'aya da ya fad'o kan k'afar shi ya had'u da tiles ya tarwatse har ya yanki Sabeer a k'afa kad'an jini ya fito, baisan lokacin da ya bud'e baki ya kwalla wata k'ara mai k'arfi tare da yin wani tsalle don ba k'aramin firgita yayi ba don ko kula da tahowar ta bai yi ba, ga zafin yankewar da yayi.
Hajjah Hauwaa tana bedroom d'in ta taji k'arar d'an lele da sauri ta tashi ko takan d'an kwalin ta bata bi ba tayo downstairs da d'an gudu irin na tsofaffi a rud'e.
House girl d'in nan kuwa tuni ta tashi daga fad'uwar da tayi a k'asa duk da kuwa zafin da taji na fad'uwar haka ta daure ta tashi ta tsugunna tana kuka tare da bawa Sabeer hak'uri, don tun kafin ya dawo ake jan kunnen su da 6ata mishi rai su kiyayi 6acin ran shi, sai gashi yau tsautsayi ya ritsa da ita daga dawowar shi jiya.
Sabeer tsalle da ihu kawai yake yi, a dai dai lokacin Alhj Ahmad d'an fillo ya sanyo kanshi cikin parlour ranshi a 6ace, saboda bak'on da yayi yana jiran a kawo musu abin ta6awa a baki ba'a kawo ba shine ya taso da kanshi, abin kamar a mafarki yaji ihun Sabeer aikuwa da sauri ya k'arasa parlourn jiki na 6ari.
Lokaci d'aya Alhj Ahmad d'an fillo da Hajjah Hauwaa suka shigo parlourn, wajen Sabeer gaba d'aya suka yi cikin matuk'ar tashin hankali don sam basu kula da house girl d'in da take durk'ushe tana zunduma kuka.
Alhj Ahmad d'an fillo janyo Sabeer jikin shi yayi ya rungume shi cikin rawar murya ya fara cewa
"Sabeer what happened to U?
"waya ta6a min kai? "
Duk wannan tambayar Alhj Ahmad d'an fillo yayi ta a rud'e.
Cikin sangarta da salon shagwa6a Sabeer ya nuna jikin shi da k'afar shi da take fitar da jini, a kid'ime suka kalli jikin nashi da k'afar shi saboda tsabar rud'ewa sai yanzu suka kula, cikin tashin hankali Hajjah Hauwaa tace
"wa yayi maka wannan rashin mutuncin Sabeer? "
Ta fad'a tana mai dafe kirjin ta tare da zaro idon ta waje, Alhj Ahmad d'an fillo kuwa saboda tsabar tashin hankali kasa magana yayi sai zuciyar shi da take bugawa da k'arfi.
Hajjah Hauwaa ta kama hannun Sabeer tare da cewa
"Sabeer open your mouth and explain me please "
Bai yi magana ba sai hannun shi da ya d'aga dakyar ya nuna saitin da 'yar aikin take tsugunne tana kuka jikin ta na rawa, zaro idanun su suka yi lokaci d'aya sannan Alhj Ahmad d'an fillo ya bud'e baki cikin tsawa mai matuk'ar firgita wa yace
"keeee zo nan "
'yar aikin a kid'ime ta tashi ta nufi inda suke tsaye, jikin ta na matuk'ar rawa ga hawaye na zuba a idanun ta, hannun ta gaba d'aya a saman kanta don tasan ita yau ta ta, ta k'are....
Aishat A Muh'd ✍🏻
💝 A SANADIN SON KI 💝
Written by
Aishat A Muh'd
♻EXCLUSIVE WRITERS FORUM
Dedicated to my Sadeey saNaz
_This page is for you my Namecy Ayusher Ilias writer d'in YA SAYYADI, ina tayaki murnar kammala littafin ki YA SAYYADI Allah ya k'ara basirah da k'arfin ido ina yin ki sosai Namecy Allah ya bar zumunci😍
PAGE 15-16
Tana k'arasowa inda suke Alhj Ahmad d'an fillo ya sanya hannun shi ya wanka mata mari a kumatu, kafin ta dawo hayyacin ta Hajjah Hauwaa ita ma ta wanka mata marin a d'ayan kumatun, ihun kuka kawai 'yar aikin take yi saboda ba k'aramin shigar ta marukan suka yi ba, kallon ta suke sai huci sukeyi cikin harara Hajjah Hauwaa tace
"me kike kallo da zakiyi wa Sabeer haka, baki da hankali ne, ina so kafin cikar mintuna 5 Ki barmin gida "
Duk da tsananin zafin marin da 'yar aikin tasha hakan bai hanata durk'usawa a k'asa ba cikin kuka take cewa
"don Allah kuyi hak'uri tsautsayi ne amman kada ku kore ni bazan sake kwatanta hakan ba "
Cikin 6acin rai Dr Ahmad d'an fillo yace
"baki ji abin da aka ce miki ba sai na kira police sunyi gaba da ke, wlh kika bari na kirawo police gidan nan sai kin yabawa aya zak'in ta "
A kid'ime 'yar aikin ta mik'e jikin ta na rawa ta fara kok'arin barin parlourn, Sabeer wanda yake jikin Dr Ahmad d'an fillo ya lafe yana sauke ajiyar numfashin ihun da ya gama ya bud'e baki dakyar yace
"keee ki zauna kada ki tafi but ki kiyaye gaba, kika sake min haka bazan Kyale ki ba "
Cikin mamaki Dr Ahmad d'an fillo da Hajjah Hauwaa suke kallon shi sun ma kasa furta komai, da sauri 'yar aikin ta tsugunna tana murmishin farinciki cikin rawar murya tace
"Ngde yalla6ai Allah ya kare ka yanda ka taimake ni kai ma Allah ya taimake ka a duk inda kake, kuma zan kiyaye gaba insha Allah ngde ngde sosai "
D'aga mata hannun shi yayi d'aya tare da cewa
"is okay zaki iya tafiya "
Jiki na 6ari ta bar wajen Sabeer ya bita da kallon tausayi don tabbas tausayin ta ne ya sanya shi barin ta don ta cigaba da aiki.
Kallon Hajjah Hauwaa yayi wadda take mishi kallon mamaki ya yamutsa fuska yana cewa
"a had'a min ruwa a toilet zan yi wanka "
Sai lokacin bakin ta ya bud'e ta iya cewa
"yanzu shikenan Sabeer an barta baza'a d'auki mataki a kanta ba "
"ni tayiwa laifi koh, kuma nace ta zauna kada ta tafi ko'ina don haka ku Kyale ta idan kuma naji anyi mata wani abun raina zai iya 6aci kum......"
Kafin ya k'arasa fad'i abin da zai fad'a Dr Ahmad d'an fillo yace
"kayi hak'uri kada ranka ya 6aci Sabeer baza'a yi mata komai ba komai ya wuce " ya k'arasa fad'i yana shafa kanshi tamkar wani k'aramin yaro.
Kan shi ya gid'a idon shi na kan ciwon da ya d'an ji akan k'afar shi, Dr Ahmad d'an fillo ya kalli Hajjah Hauwaa yace
"ba'a haka yace a had'a mishi ruwa zai yi wanka ba? "
Dafa kafad'ar Sabeer tayi tare da cewa
"zo muje da kaina zan had'a maka "
Kamo hannun shi tayi ta jashi zuwa upstairs inda bedroom d'in shi yake (da yake yana da bedroom a side d'in kakannin nashi), da kallo Dr Ahmad d'an fillo ya bi Sabeer har ya daina hango shi tukunna ya juya ya fita.
Bayan Sabeer yayi wanka ya fito ya shirya cikin Kayan da Hajjah Hauwaa ta ajiye mishi saman bed, ya sanya su sannan ya kwanta kan sofa hannun shi d'auke da I pad d'in shi yana research a ciki.
"Assshhh "
Ya furta a hankali sakamakon maganin da Hajjah Hauwaa ta sanya mishi a d'an ciwon da glass cup ya ji mishi, bakin ta ta sanya tana hura mishi k'afar tare da cewa
"sannu "
Ta furta hakan tana rufe robar cream d'in da ta shafa mishi, d'an 6ata fuska yayi yana cewa
"shine baki fad'a min zaki sa min ba koh? "
Da shagwa6a ya fad'i hakan, nan ta fara rarrashin shi sai da ta ga ya hak'ura tukunna ta fita daga bedroom d'in don ta barshi ya huta.
8pm
Sabeer ne tsaye gaban dressing mirror yana sake gyara necktie d'in suit d'in shi, yayi kyau sosai cikin blue d'in suit ba kad'an ba shoes d'in shi black ne haka watch d'in hannun shi samfur d'in Gucci yayi kyau gashin kanshi yasha gyara sai shek'i yake.
Turo kofar bedroom d'in akayi Mummy ce ta shigo tasha gayun ta cikin wani tsadaddan black less mai adon flowers ash Sai ta nad'a laffaya ash colour mai kyallen duwatsun silver sai manya flowers black a jikin laffayar tayi kyau sosai baka d'auka ta haifi Sabeer ba gefen ta kuma wata matashiyar kyakkyawar yarinya ce tana sanye cikin wata gown na English wears sun kamata sosai daganin ta kasan idon ta a bud'e yake tasha wani uban hill shoes ga attachment da tasha sai farce daga ni sanya su tayi, fuskar nan tasha heavy make up sai wani iyayi take, kallo d'aya zaka yi mata kasan kusan sa'anni ce da Sabeer a shekaru.
Kallo d'aya Sabeer yayi mata ya d'auke kai don bai ga alamun tana da hankali ba irin wannan haukan kwalliyar da tayi, matsalar shi da Mummy kenan jajibo irin wad'annan yaran marasa kamun kai.
Cikin murmishi d'auke a fuskar Mummy ta k'arasa inda Sabeer yake tayi hugging d'in shi tare da cewa
"Wow son ka ganka kuwa U look so cute "
"Thanks Mumy"
Ya furta tamkar baya son magana, cikin murmishi Mumy tace
"Son ga Fadilah ko baka gane ta ba ne? "
D'auke kanshi yayi tare da cewa
"bansan ta ba"
Yana gama fad'in yayi gaba, kunya ce ta d'an kama Mumy don bata zaci Son zai mata haka ba ya kunyatar da ita a gaban d'iyar k'awar ta, wayance wa tayi da cewa
"Kyale shi Fadilah ranshi ne a 6ace don baya son wannan party da na had'a mishi "
Sai lokacin matashiyar yarinyar da Mumy ta kirawo da Fadilah ta saki murmishi don ta shiga damuwa a time d'in da Sabeer ya nuna baisanta ba.
Kamo hannun ta Mumy tayi suka fito zuwa compound d'in gidan friends d'in Mumy da yaran su zuwa 'yan uwan Sabeer ne sai shiga mota ake suna tafiya zuwa hall d'in da za'a yi party.
Wata black Range Rover na hango a tsakiyar compound na gidan sai shek'i da d'aukar ido take daganin ta kasan sabuwa ce, nan na hango Sabeer ya nufi wajen cikin takun tafiyar shi kamar bayason taka k'asa, kafin ya k'arasa wajen tuni driver ya bud'e mishi bayan motar yana k'araso wa shiga yayi ya zauna sannan driver ya rufe murfin motar, cikin sauri ya shiga mazaunin driver ya yiwa motar key ya fara tafiya a hankali don Sabeer bai fiye son ayi gudu dashi a mota ba idan bashi yake driving ba.
Suna k'arasa wa katafaren hall d'in da aka kama don yin partyn ko'ina yasha decorations na blue white, wajen yayi kyau sosai ta had'u ga wani cake mai hawa uku shima kalar shi blue and white ne yayi kyau sosai ya tsaru.
Ga manyan hamshak'an masu kud'i friends na Mumy da yaran su, ga 'yan uwan Sabeer nan mazan su da matan su kowa yasha gayun shi na kece raini don kowa yana ji da kanshi ta fannin kud'i da gogewar ilimi da wayewa.
Driver yana yin parking motar da Mumy take ciki tayi parking kusa da motar da Sabeer yake ciki, nan Mumy ta fito ita da wannan Fadilah suka k'araso inda Sabeer yake, Mumy ta bud'e kofar motar tare da cewa
"Son fito mu tafi mutane na jiran mu "
Cikin wani tak'ama da had'e fuska ya ziro k'afar shi d'aya waje sai da ya d'auki wasu seconds tukunna ya fito da d'ayar kafin kuma ya fito da dukka jikin shi zuwa waje.
Kallon shi Fadilah take tamkar ta lashe shi saboda tsabar maitar son shi da take, ita fah da zai aminta da ko bazai aure ta ya yarda suna biyawa kansu buk'ata don tasan Sabeer irin shine wanda zai yi mata yanda take so, amman zata fara gwada sa'ar ta ko zatayi nasara...
Aishat A Muh'd ✍🏻
💝 A SANADIN SON KI 💝
Written by
Aishat A Muh'd
♻EXCLUSIVE WRITERS FORUM
Dedicated to my Sadeey saNaz
This page is for U my Momma na (Aunty Maijiddah Musa) thanks for luv nd support, Allah ya raya zuri'a Allah ya bar zumunci ❣
PAGE 17-18
Yana gama fitowa a mota ne Mumy ta kama hannun shi suka fara tafiya zuwa cikin hall d'in, sai da suka kusan shigewa hall d'in tukunna Fadilah ta dawo daga duniyar tunanin da ta fad'a da sauri ta bi bayan su don tana Buk'atar jerawa da Sabeer.
Bayan sun shiga ciki ne Mumy da Sabeer suka zauna waje d'aya sai wani 6a66ata rai yake, gaba d'aya hayaniyar duk ta isheshi ya gaji ga 'yammatan da suka dame shi da hayaniyar su kowacce tana kok'arin cusa kanta a wajen shi, amman yanda kasan da dutse suke magana haka yake share su, Gashi kowacce da nata gift's da takawo mishi, Mumy sai wani murmishin jin dad'i take ganin yanda ake son d'anta.
Gaba d'aya Mumy ta mance da 30 minutes kawai Sabeer yace zai yi, bata ankara ba taga sun d'auki wajen 25 minutes a wurin ai kuwa da sauri ta kallo inda Sabeer yake zaune yana danna wayar shi gefen shi kuma Fadilah ce ke faman yi mishi surutu tana wani karairaya da iyayi ita a dole so take ta birge Sabeer, k'arasa wa Mumy tayi wajen ta dafa kafad'ar shi cikin k'aramin sautin magana tace
"Son kazo ka yanka cake "
Daman gaba d'aya a takure yake da yabar wajen don haka ya mik'e tsaye Mumy taja hannun shi har zuwa inda aka ajiye cake, knife Mumy ta bashi suka rik'e tare tukunna suka yanka nan Mumy ta bashi a baki shima ya bata, nan kuma kowa ya fara bashi kyautar gift nashi da zai bashi Sabeer sai faman jan tsaki da 6ata rai yake ganin har ya k'ara 5 minute akan 30 minutes d'in da zai yi, sai kallon Mumy yake yana son sun had'a ido dashi yayi mata magana, amman tak'i yarda su had'a ido kwata kwata saboda tasan halin d'an nata gashi duk wanda zai bashi gift idan baisan shi ba sai ya tsaya gabatar da kanshi.
D'ago kan da zaiyi ya kalli Mumy akayi sa'a ita ma ta kallo inda yake da ido yayi mata alamar ya gaji gashi time d'in da ya d'auka ya wuce yana nuna mata agogon hannun shi gashi kuma 'yammatan da suka bi suka dame shi Sabeer dai yaga ta kanshi tamkar zai fashe da kuka haka yake ji duk Mummy ce ta ja mishi, Mumy tamkar ta fashe da dariya haka taji lokacin da ta ga Sabeer yanda ya koma amman sai ta danne dariyar ta tare da marairaice mishi fuska da ya d'an yi hak'uri na d'an wasu minutes, daga nan kuma aka fara ciye ciyen abubuwan ci dana sha, a wannan lokacin Sabeer ya zame ya tafi abin shi gaba d'aya a wani gala6aice yake kanshi har ya fara ciwo.
Shiga mota yayi driver yaja shi sai gida, yana parking ya fito daga motar ya nufi side d'in su, kai tsaye bedroom d'in shi ya nufa yana shiga ya fara cire kayan jikin shi yana wurgi dashi sai da ya cire komai sai iya dogon wandon shi ya bari tukunna ya shige toilet, shower ya sakarwa kanshi na tsayin 2 minute kafin ya fad'a cikin bath tub ya fara wanka bayan ya gama ne ya d'aura alwalar sallahr ishha tukunna ya fito daga toilet.
Wata white jallabiya ya sanya cikin nutsuwa ya gabatar da sallahr ishha bayan ya idar ne bai wani tsaya yin wata addu'a ba ya mik'e tsaye tare da cire jallabiyar ya kwanta daga shi sai three-quarter a jikin shi kwanciya yayi saman bed yana mai runtse idanun shi hannun shi d'aya saman goshin shi ya dafe, a hankali ya wani bacci mai nauyi yayi awon gaba dashi daman ya gaji sosai.
Mumy koda ta duba bata ga Sabeer ba tasan ya tafi, don haka nan ta sallami friends nata da wad'anda suka zo, kowa ya tafi gida tukunna ta shiga mota zata rufe murfin motar taji an rik'e, cikin d'an mamaki ta jiyo don ganin wane, had'a ido tayi da Fadilah fuskar Mumy cike da mamaki tace
"Fadilah daman baki tafi gida ba "
Cikin marairaice fuska Fadilah tace
"ni Mumy bin ki zanyi fah acan zan kwana "
Murmishi kawai Mumy ta saki don tasan dalilin kwanan Fadilah a gidan nata, cikin kulawa Mumy tace
"alright dgter shigo mu tafi "
Fadilah jiki na rawa ta shige cikin motar ta zauna burin ta kawai a yanzu da tunanin ta shine yanda zata shawo kan Sabeer ya amince da ita ya aure ta ko suna hutawa da junan su, don ita Fadilah bata da ra'ayin aure a zuciyar ta sai da taga Sabeer, ita kawai 'yar aji dad'in