Showing 90001 words to 93000 words out of 122360 words

Chapter 31 - A sanadin Son ki Hausa Novels Document complete by Aisha A Muhammad Sanaz.txt

ba nayi fad'a da family na iyayena na bar inda suke na tafi wajen ki nasha wahala kafin ki kar6i soyayya ta ashe duk kallon wawa kike min bansan me nake ba, kin zubar min da cikin jikin ki sau biyu nasan baki sona dama don haka get out from my house i hate you Suhaima i hate you so much nasan bazan yi regretting wannan abin da nayi ba kuma da sannu Allah zai saka min "


Yana gama fad'in ya nufi upstairs zuciyar shi na wani irin zafi, tashi Suhaima tayi tana faman kukan tashin hankali zata fita daga parlour tabar gidan taji muryar Daddy yana cewa
"Suhaima kada ki tafi zansa ayi bincike ban yarda da wannan abun ba"


Girgiza kai take tana cewa
"A'a Daddy kabar na tafi bazan zauna ba "
Tana gama fad'in haka ta fice daga gidan da gudu tana kuka, Jiddah ce tayi kok'arin bin ta amman Mumy ta rik'e ta gam tana faman hararar ta..................








Aıʂɧąɬ A Mųɧ'ɖ ✍🏻
*A̺͆ S̺͆A̺͆N̺͆A̺͆D̺͆I̺͆N̺͆ S̺͆O̺͆N̺͆ K̺͆I̺͆*








Wྂrྂiྂtྂtྂeྂnྂ bྂyྂ
Aྂıʂɧąɬ Aྂ Mྂųɧ'ɖ




ɖɛɖı¢ąɬɛɖ ɬơ ɱყ ʂąɖɛɛყ ʂąŋąʑ




♻ *єχ¢ℓυѕινє ωяιтєя'ѕ fσяυм*





*PAGE 93-94*












Suhaima gudu take tana kuka har ta samu ta fito daga gidan, sannan ta d'an tsaya tana yiwa gidan kallon k'arshe don tasan bazata ta6a komawa cikin shi ba har abada kuwa.


Fara tafiya tayi tana goge hawaye da hijab d'in jikinta ko takalmi babu a k'afar ta, wani mai taxi taga ya sauke wata mata bata tsaya tambayar shi ta fad'a cikin motar tana kuka kawai, daga matar har mai taxi d'in suka bita da kallo kowanne fuskar shi ta d'auki alhini suna tunanin ko mutuwa akayi mata mai zafi yasanya ta haka dad'in dad'awa da suka ga ko takalmi babu a k'afar nata, canjin matar mai taxi ya bata sannan ya tada motar suka fara tafiya sai da suka hau kan titi sannan yace
"Baiwar Allah ina zan kai ki? "
Dakyar ta iya tsayar da kukan tayiwa mai taxi bayanin inda zai kaita, mai taxi bai zaci wajen da nisa ba sai da ta fad'a mishi sunan kauyen da zai kaita yaso yi mata maganar ba nan zai je ba but ganin irin halin da take ciki ne kawa yayi niyyar taimaka mata.




*****


"Faridah ina jiye miki duk ranar da gaskiya tayi halinta, idan har da sanya hannun ki cikin wannan abun to kiyi gaggawar warwarewa tun kafin kizo kina nadama "


Turo baki tayi kan tace
"Wai ni duk kun tattara laifi akaina ina ruwana da ita da har zanyi yunkurin zubar mata da ciki kawai ta samu sake ne kasan halin talakan mutum bai iya samun waje ba, kuma nagodewa Allah da ya sanya suka rabu da d'ana yaje ya auri wadda zata haifa min 'yan jikoki na, yanzu kawai saki nake so naji yayi mata yanda zasu rabu har abada"


"Allah ya shirya ki Faridah "
Cikin wani irin murmishi tace
"Amin my Dear "


Tashi Daddy yayi zai fita itama ta mik'e tana cewa
"My Dear ka tsaya mu tafi da Son mana kada mu tafi mu barshi shi d'aya "
Cikin jin haushin abin da Sabeer yayi wa Suhaima tunda bai tsaya yayi bincike ba kawai ya yanke hukunci yace
"Ai ba yaro bane shi kuma yasan hanyar gida "
Yana gama fad'in haka ya wuce ya fita daga palon, Jiddah ma d'aukan Islam tayi ta wuce da sauri ta bi bayan Daddy da harara Dr Faridah ta bita tukunna ta wuce upstairs inda Sabeer yake.


Agefen gado ta ganshi yayi ruf da jiki rabin jikin shi a saman bed rabin a k'asa sai wani irin shashshak'a yayi na kuka idanun nashi sunyi ja sun kumbura hatta face nashi tayi ja sai maimaita kalmar
"Why! Why! Suhaima zaki yi min haka na tsane ki i hate U "
. wani sanyin dad'i ne ya kwaranya cikin zuciyar Dr Faridah jin yanda Sabeer yake furta ya tsani Suhaima kamar tayi tsalle da ihun murna haka take ji amman sai ta danne, zama tayi akan gadon ta tare da d'aukan kanshi ta d'ora kan k'afafun ta shafa mishi gashin kanshi take a hankali tana rarrashin shi but still Sabeer eyes nashi basu bar zubar da tears ba.


"My Son kayi hak'uri mu tafi gida kaji bazan iya barin ka anan kai d'aya ba "
"No! Mumy ki tafi ki barni zuciya ta yana daf da tarwatse wa, ina jin zafi acikin zuciya na idan na tuna Suhaima ta cuce ni taci amanata ta yaudare ni tayi min butulci Mumy! "


Dafe saitin zuciyar shi yayi da hannun shi d'aya yana jan wani irin numfashi, wani irin zabura Dr Faridah tayi ganin yanda eyes d'in Sabeer suka kakkafe.


Hannu ta d'ora saman kanta tana kuka tace
"Wayyo Allah nah na shiga uku zan kashe d'ana da kaina! "


******




Sai bayan sallahr ishsha ne suka k'arasa kauyen su Suhaima har k'ofar gida mai taxi ya kaita har zuwa yanzu Suhaima bata bar kukan bak'inciki da takaicin hukuncin da Sabeer ya yanke ba batare da bincike ba aure ko shekara baiyi ba ace har an rabu daman ashe ba sonta yake tsakani da Allah ba yaudare ce yake mata irin ta mazan yanzu nima na tsane ka kamar yanda ka tsane ni Sabeer!.


Maganar da d'an taxi yake mata ne ya dawo da ita daga duniyar tunani fitowa tayi daga motar cikin dushewar murya tace
"Bari na kar6o maka kud'in ka "


Ko taku uku bata yi ba taji ta bige mutum d'agowar da kanta da zatayi suka had'a ido da Yah Aliyu cikin tsakanin mamaki yace


"Suhaima! "


ai Suhaima batasan lokacin da ta fad'a jikin shi ba ta saki wani irin marayan kuka, wani irin tashin hankali da fad'uwar gaba ne ya ziyarci Yah Aliyu tuni fuskar shi ta fara canja yanayi.


"Yay... Yaya ka biyashi kud.... kud'in shi "
Ta fad'a cikin kuka tana nuna mai taxi da hannun ta, zuciyar Yah Aliyu tana tafasa yace
"Malam nawa ne kud'in ka? "
Nan d'an taxi d'in ya fad'a hannu Yah Aliyu ya zura a aljihu ya d'auko kud'in shi ya bashi yana bashi ya rik'o hannun Suhaima suka shiga cikin gida.


Aunty Aliyah da take zaune tana jijjiga Ameer yayi bacci taga shigowar mijin nata batasan lokacin da ta kwantar da Ameer saman katifa ba ta mik'e a razane tana cewa
"Suhaima kece da daren nan? "
Jikinta Suhaima ta fad'a tare da fashewa da kuka da k'arfi, ruwa Yah Aliyu ya d'ebo mai sanyi a randa zama yayi tare da zaunar da Suhaima akusa da shi ya bata ruwan da hannun shi, bayan ya gama bata ne sannan cikin nutsuwa yace
"Suhaima fad'a min me yafaru kada ki 6oye min komai don baki da kamata a duniyar nan "


Kallon Yah Aliyu tayi kafin ta sauke ajiyar zuciya ta fara zayyana mishi abubuwan da suke faruwa gaba d'aya bata 6oye musu komai ba tana gama fad'in ta sake fashewa da kuka, Aunty Aliyah wadda take kukan tausayin Suhaima ta janyo ta jikin ta tana rarrashin ta.


Yah Aliyu kuwa wani zafi zuciyar yake yi sai wani huci mai zafi da yake fitarwa zagaye tsakar gidan yake hannun shi goye a bayan shi ya ma rasa abin cewa can ya bud'e baki cikin kakkausar murya yace


"Yau ni Aliyu za'a wulak'anta aci mana mutunci don kawai muna talaka, abin da Sabeer zai aikata mana kenan lallai yau koda bai sake ki ba ni ni Aliyu na sanya almakashi na datse igiyoyin da suke tsakanin ku dashi bake bashi har abadaaaa..........










Aıʂɧąɬ A Mųɧ'ɖ ✍🏻
*A̺͆ S̺͆A̺͆N̺͆A̺͆D̺͆I̺͆N̺͆ S̺͆O̺͆N̺͆ K̺͆I̺͆*








Wྂrྂiྂtྂtྂeྂnྂ bྂyྂ
Aྂıʂɧąɬ Aྂ Mྂųɧ'ɖ




ɖɛɖı¢ąɬɛɖ ɬơ ɱყ ʂąɖɛɛყ ʂąŋąʑ




♻ *єχ¢ℓυѕινє ωяιтєя'ѕ fσяυм*





*PAGE 95-96*










Yana sauke wani irin huci Yah Aliyu ya k'arasa maganar ga wasu hawaye na bak'inciki da suke zubo mishi idan ya tuna yanda aka zubar wa k'anwar shi ciki har sau biyu, an cuci k'anwar shi cuta ba k'arama idan ya tuna idan kuma shine iya k'wanta aduniya fa, idan ya kasance iyakar 'ya'yan da zata haifa ne a iya duniya fah shikenan angama cutar k'anwar shi ba ita ba ganin 'ya'yan da zata haifa wasu can daban sun zubar mata dashi.


"Inaaa! Bazai yiwu ba dole sai na d'auki fansar abin da akayi wa k'anwata koda zai kasance abu na k'arshe a rayuwashi, an cuce mu don abin da akayi wa Suhaima tamkar shi aka yiwa.


Komawa yayi ya zauna tare da janyo Suhaima kusa dashi ya sanya hannun shi ya d'ago kanta suna kallon juna yace
"Suhaima baki da kowa sama dani don haka wannan abin da akayi miki sai na d'auki fansar shi koda duk abin da na mallaka a duniyar nan zai k'are "


Girgiza kanta Suhaima kawai take cikin kuka take cewa
"Nooo! Yaya kada ka kula su na bar mutum da Allah duk wanda yayi min wannan abun shi da Allah "
Idanun shi jawur yace
"A'a k'anwata baza ayi haka ba sun zalunce ki da yawa bazan kyale su ba don suna tunk'aho su masu kud'i ko suna tunanin zan ji tsoron su to wallahi a'a sai na ja dasu kuma sai nayi nasara "


Hannun shi Suhaima ta k'ank'ame tana kuka tace
"Na had'a ka da girman Allah Yaya kayi hak'uri ka kyale su idan har kana son ganin farinciki na mu bar wanda ya aikata da Allah da sannu Allah zai saka min "


Tsayawa yayi kallon ta na wasu 'yan mintuna kafin yace
"Tabbas ina son ganin ki cikin farinciki k'anwata zan kyale su saboda ke kawai"..


Rungume shi tayi tana cewa
"Yawwa Yaya na nagode "


Shafa kanta yayi sannan yace
"Allah yayi miki albarka k'anwata, yanzu bari na kai miki ruwa kiyi wanka da sallah kici abinci"


"Amin Yaya na "
Har ta mik'e ya sake rik'e hannun ta sannan yace
"K'anwata kiyi min alkawarin kin rabu da Sabeer har abada "


Shiru Suhaima tayi tana mai sunkuyar da kanta ta rasa abin da zata ce ma, ta d'an jima ahaka sannan ta d'ago kanta ta kalli Yaya Aliyu wanda yake kallonta yana jiran me zatace, har ta bud'e bakinta zata yi magana da sauri Aunty Aliyah ta tari numfashin ta tare da cewa
"Yaya abar wannan maganar don Allah taje tayi wanka tukunna "


Aunty ta fad'i hakan ne don batason Suhaima tayiwa Aliyu alkawari don tasan irin soyayyar da Suhaima da Sabeer suke yiwa junan su rabasu abu mai wahala ne tasan kuma idan ya huce sai ya dawo inda Suhaima take, tasan mak'iya ne basa son ganin su tare musamman 'yan uwan Sabeer da tasan irin k'iyayyar da suke yiwa Suhaima saboda kawai don ta kasance talaka 'yar kauye, tana son Suhaima da Sabeer amman sai ya gane kuskuren shi na yanke hukunci kafin bincike.




Sakin hannun ta Aliyu yayi sannan yace
"Je ki kiyi wankan "
Cikin sanyin jiki ta wuce yayi da Yah Aliyu ya bita da kallon tausayi yarinya k'arama an mayar da ita bazawara auren da ko shekara bai rufa ba, da ace ana dawo da abin da ya wuce da ya dawo rayuwar su baya ko dan ya goge Sabeer daga rayuwar Suhaima, amman ina kaddara ta riga fata Allah ya rubuta sai hakan ya faru dasu zasu rungumi kaddara su koma zasu cigaba da godewa Allah a duk halin da suka tsinci kansu aciki, wasu hawaye ne suka zubo mishi da ya tuna mahaifiyar su da irin bak'incikin da ta fuskanta awajen d'a namiji kafin ta mutu.


Baisan ma hawayen na zuba ba sai da yaji hannun Aunty Aliyah suna goge mishi hawayen, cikin sanyin murya tace
"Kayi hak'uri Yaya komai tsanani yana tare da sauk'i rayuwar Suhaima zata inganta agaba insha Allah "


"Amin mata ta! Na gode da kulawar ki agare ni "


Tashi yayi yana kok'arin had'awa Suhaima ruwan wanka nan Aunty Aliyah ta kar6a ta had'a mata sannan ta kai mata toilet.


Shiga d'akin ta tayi ta tarar da Suhaima a zaune ko kayan jikin ta bata cire ba nan tayi zaman rarrashin ta kafin ta cire kayan ta d'aura zani ta fita wanka inda Aunty Aliyah take fad'a mata bayan tayi wankan ta zauna cikin ruwan d'umi sosai.


Bayan ta gama wankan ne ta sai kayan Aunty Aliyah ta sanya saboda kayanta sunyi datti gashi tafiya bata kwanciyar hankali ba bata taho da wasu ba, abinci ma kasa ci tayi sai fura Aunty Aliyah ta dama ta Yah Aliyu da kanshi yake bata a baki, bayan ya gama bata ne sai tasha paracetamol saboda yanda kanta yake ciwo sosai ta kwanta kan 3siter d'in d'akin Aunty ta lumshe eyes nata hannunta d'aya dafe da kanta, tunanin kawai maganganun da Sabeer yayi mata take da yanda yace ta fice mishi daga gidan shi ya tsane ta, hawaye masu zafi ne suke zubo wa daga eyes nata.


Yah Aliyu da Aunty Aliyah ne suka zage wajen gyara mata d'akin Suhaima na da gyara shi sukayi tas, suka share har zasu fito daga d'akin Yah Aliyu ya tsaya kallon d'akin na 'yan mintuna kafin ya sauke ajiyar numfashi yace


"Aliyah ya kamata na gyarawa Suhaima d'akin ta yayi kyau sosai duk wani jin dad'i ma zan tanadar mata koda duk abin da na mallaka zai k'are, don haka cikin satin nan zan nemi mai siyan d'ayan gonata na siyar sai na bar d'ayar kawai ta ishemu zaman duniya dai "


Gid'a kai Aunty Aliyah tayi kafin tace
"Gaskiya kam ka kyauta Allah ya k'ara had'e kanku Allah kuma ya k'ara bud'i "
Yana murmishi yace
"Amin mata ta "
Har zasu fito daga d'akin Aunty Aliyah tace
"Ni kuwa ina maganar cigaba da karatun ka da kayi min maganar kwanaki naga baka k'ara cewa komai ba? "
"Tana nan maganar don har na samu gurbin karatu na k'arasa secondary yanzu zan zana jarabawar wec da neco"
Murmishi Aliyah ta saki tare da cewa
"Masha Allah abu yayi kyau Allah ya taimaka ya bada sa'a "
"Amin Amin "
Daga haka suka fito daga d'akin zuwa d'akin Aliyah tarar da Suhaima tana kuka ne ya sanya su tsayawa suna rarrashin ta dakyar tayi shiru sannan suka rakota d'akin ta nan ma sun jima sannan suka yi mata sai da safe suka tafi.


Cikin wannan daren ya zamewa Suhaima wani irin dare na bak'inciki musamman idan ta tuna jiya kamar yanzu suna tare da Sabeer suna nunawa junan su zazzafar soyayya, tayi kuka Suhaima awannan daren har sai da taji kamar kanta da idanun ta zasu zazzago da ciwon da zafin da suke mata.






************


Cikin nutsuwa yake motsawa tare da kok'arin bud'e eyes nashi dakyar ya samu ya bud'e su saboda hasken da yake dallare mishi ido, kallon d'akin yake cikin mamakin me ya kawo shi, duk ya rame bakin shi ya bushe kallo d'aya zaka yi mishi kasan cewa bashi da cikakkiyar lafiya.


"Alhamdullilah Son ka farka? "
Cewar Mumy da shigowar ta room d'in kenan, cikin farinciki ta k'arasa inda yake ta zauna tare da rik'o hannun shi tana goge hawayen idonta da d'ayan hannun, don sosai lalurar Sabeer ta firgitata sosai don yau kwanan shi 3 a kwance sai drip kawai da ake sanya mishi tunda yayi doguwar suman nan.


Bai kulata ba duk yanda taso da yayi magana kawai sai ya kwanta tare da juya mata baya, runtse eyes nashi yayi yana tunano musabbabin abin da ya sanya shi cikin wannan halin, tar komai ya dawo mishi cikin brain nashi a hankali wasu hawaye masu zafi suka fara sauko mishi idan ya tuna yanda Suhaima ta cuce shi bai ta6a zaton Suhaima zata aikata hakan ba agare shi.


Tashi ya yunkura yayi dakyar sai dai ko taku biyu bai yi ba sai yayi luuu kamar zai fad'i da sauri Mumy ta taro shi ya fad'o jikinta a kid'ime tace
"Son ya zaka tashi cikin wannan yanayin kasan jikin ka babu kwari? "
Cikin fusata yake cewa
"Mumy ki barni na kai Suhaima k'ara akan abin da tayi min bazan kyale ta ba sai na d'auki fansa akanta na yanda take zubar min da yara na "
Wani dad'i ne ya kwaranya cikin heart d'in Mumy amman sai ta marairaice tare da cewa
"Haba Son ka kyale mata Allah sai ya saka maka yanzu samun lafiyar ka shine kwanciyar hankali na "


Nan Sabeer ya birkice mata sai yaje ya sanya an kama Suhaima sai sumbatu yake daga kasan ba'a ciki hankalin shi yake ba, gani haka ya sanya Mumy yi mishi allurar bacci babu dad'e wa bacci yayi awon gaba dashi ta gyara mishi kwanciyar zuciyar ta fal farinciki....






********




Cikin tsananin 6acin rai Yaj Aliyu yake cewa
"Ki fita daga gidan nan Jiddah bana son ganin ki daga ke har 'yan uwan ki macuta "


Cikin rikicewar kuka Jiddah take rik'e k'ofar shiga gidan saboda kok'arin rufeta da Yah Aliyu yake yi
"Yaya Aliyu don Allah kayi hak'uri ba laifi na bane inason ku wallahi baza'a ta6a had'a baki dani a cuce ku ba ka tsaya nayi maka bayani"


"Tun kafin naji miki ciwo Jiddah ki fita daga gidan nan nace zan iya illata ki idan baki tafi ba "


"Allah Yaya Aliyu sai dai ka kashe ni bazan tafi ba, Suhaima Aunty Aliyah kuce mishi ya tsaya ya saurare ni Suhaima ki fad'a mishi babu hannuna wajen aikata miki haka "


Jiddah ta fad'i tana kallon su Suhaima da Aunty Aliyah da suke gefe suna kuka ganin yanda Yah Aliyu yake korar Jiddah.


Wani irin k'ara Jiddah ta saki da k'arfi saboda yanda Yah Aliyu ya rufe k'ofar da k'arfi har yana mutstsukewa da hannun ta, a rikice Suhaima ta k'arasa wajen tare da bud'e k'ofar Jiddah ta zame hannun ta har sunyi ja sosai tana kok'arin k'arasa wa wajen Jiddah Yah Aliyu ya damk'ota tare da rufe k'ofar gidan 6am har da sanya sakata, Suhaima naji kukan Jiddah tana bubbuga k'ofar sai dai bata da ikon bud'e wa wani kuka ta fashe dashi tare da shiga d'akinta da gudu...........






Aıʂɧąɬ A Mųɧ'ɖ ✍🏻
*A̺͆ S̺͆A̺͆N̺͆A̺͆D̺͆I̺͆N̺͆ S̺͆O̺͆N̺͆ K̺͆I̺͆*








Wྂrྂiྂtྂtྂeྂnྂ bྂyྂ

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login