Showing 117001 words to 120000 words out of 122360 words
Chapter 40 - A sanadin Son ki Hausa Novels Document complete by Aisha A Muhammad Sanaz.txt
Stairs yana cewa
"Bana wa bane aron su aka bani na kwana 2 "
Cikin d'okin murya tace
"Da gaske kake Daddy?"
"Ban ta6a yi miki wannan wasan ba gaskiyar kenan "
Washe baki tayi duk yanda jikinta babu dad'i amma sai taji lokaci d'aya kamar an cire mata ciwon cikin farinciki take cewa
"Nagode Thank U very much Daddy naji dad'in ganin yaran ji nake kamar my Son nake gani Allah ya biyaka "
Ta k'arasa maganar hawaye na fita daga eyes nata sosai Daddy yaji wani mugun tausayin ta lokaci yayi da Dr Faridah ya kamata tasan ainahin inda d'anta yake yana gama wannan tunanin ya wuce stairs da sauri.
Dad'i ya ishe Mumy ta rasa inda zata sanya yaran duk wasu kayan kwad'ayi na yara haka ta cika musu gaban su dashi, koya ta kalli yaran wani sonsu ne yake sake ratsa zuciyar ta ji take tamkar da Sabeer take tare lallai idan tasan iyayen yaran nan dole ta k'ulla zumunci dasu kodan suna zuwan mata, a baki ta dunga basu abinci bayan sun gama ci ne ta shiga bedroom d'in Daddy tana tambayar shi kayan yaran ce mata yayi bai taho musu dashi ba.
"Don Allah ka barni muje wani mall d'in sai na siyo musu kayan har da na wasa kada kace a'a please dear "
Murmishi yayi sannan yace
"Okay, amma ke da baki da lafiya zaki fita? "
"Zan iya wallahi "
Ta fad'i hakan tana yin gaba da sauri kamar wata yarinya da kallo Daddy ya bita dashi kafin ya sauke ajiyar zuciya yana cewa
"Ina son ki Faridah naji dad'in yanda kika daina daukan kanki kamar kin fi kowa "
Cikin farinciki ta shirya agurguje ta fito car key kawai ta d'auka tare da rik'o hannun su suka fito zuwa compound na gidan shigar dasu tayi ta zaunar dasu sannan ta rufe k'ofar, sit na drive ta zauna da kanta tayi motar key cikin kwarewa take driving d'in ta tana jin wani nishad'i cikin zuciyar ta.
Bayan sun shiga wajen kayayyakin wasan yara nan ta sake su aikuwa da gudu suka tafi wajen kowanne na d'aukan abin da yake so, sosai ta kashe kud'i wajen siya musu kayan wasa, sannan ta siya musu kayan sawa masu kyau da tsada 6angaren kayan ciye ciye ma haka ta siya musu duk abin da suke so sannan daga k'arshe suka taho gida, idan kaga Na'eem da Shaheed tare da Mumy bazaka d'auka jikokin ta bane zaka fi zaton yaran ta ne wanda ta haifa...........
Aıʂɧąɬ A Mųɧ'ɖ ✍🏻
*A SANADIN SON KI*
Wྂrྂiྂtྂtྂeྂnྂ bྂyྂ
Aྂıʂɧąɬ Aྂ Mྂųɧ'ɖ
ɖɛɖı¢ąɬɛɖ ɬơ ɱყ ʂąɖɛɛყ ʂąŋąʑ
♻ *єχ¢ℓυѕινє ωяιтєя'ѕ fσяυм*
*PAGE 114*
Cikin kwanaki biyun da Na'eem da Shaheed suka yi Mumy tayi matuk'ar sabawa dasu sosai sai kace 'ya'yanta kaunar su take tamkar ita ta haife su tana musu wani irin so da baki bazai iya misaltawa ba, ko hospital bata zuwa kullum tana cikin basu kulawa da tattalin su, ganin yanda take kula su ya sanya Daddy jin sanyi cikin zuciyar shi duk wani fushi da yake da ita gaba d'aya ya daina koda ta rok'i ya yafe mata abin da tayi a karo na ba adadi a lokacin kasa jurewa yayi ya yafe mata don yaga tayi matuk'ar yin sanyi sosai, rungume shi tayi tsabar farinciki da jin dad'i.
Kwana su biyu kamar yanda Daddy yayi alkawarin zai mayar wa dasu Sabeer yaran su don haka a ranar da safe ya sanarwa Mumy ta shirya su za'a mayar dasu gidan iyayen su, kuka sosai Mumy ta fashe dashi don ta shak'u da yaran acikin kwana 2 wani irin son su take, dakyar Daddy ya rarrashe ta tayi shiru nan ta shirya su tsaf tare da had'a musu kayan wasan su da ta siya musu su kansu Na'eem da Shaheed har da kukan su lokacin da zasu tafi, yini guda Mumy tayi a kwance saboda tsabar kewar Na'eem da Shaheed duk gidan yayi mata babu dad'i picture d'in Sabeer ta d'auko tana shafa face d'in shi cikin muryar kuka take cewa
"Ina ka tafi ka barni Son, ina son ganin ka ina son jin muryar ka nayi kewar d'ana ka dawo wajen mahaifiyar ka zanyi maka duk abin da kake so Son zanje da kaina na dawo maka da Suhaima ku haifa min jikoki nima kamar su Na'eem da Shaheed "
Wani kuka ne yaci k'arfin ta nan ta kife kanta akan bed tana yin kuka sosai cikin tsananin kewar d'an nata.
*******
Kwance yake akan carpet yayi ringingine yau tsayin kwanaki uku kenan yana mafarki da Mumyn shi tana kuka tana ce mishi ya dawo gare ta, yanzu lokaci yayi da zai bayyana kanshi wajen Mumy shi kanshi yana cikin tsananin kewar ta yana son ganin mahaifiyar shi ya neme afuwar ta akan d'aga mata hankalin da yayi don yasan yanzu hankalin ta a tashe yake sosai, ga tsananin kewar yaran shi da basa tare dashi yanzu yanda ya kwana 2 kawai bai ga yaran nashi ba yana tsananin kewar su ina kuma Mumy da ta shafe wajen 2yrs bata sanya shi a idonta ba ko taji muryar shi dole ya gaggauta komawa gida wajen Mumyn shi.
Yana cikin wannan tunanin ne Suhaima ta shigo d'akin ta jima tana kallon shi baisan ma ta shigo d'akin ba, cikin kwanakin nan tana kula dashi da yanda yake cikin damuwa, cikin sanyin jiki ta k'arasa inda yake ta kwanta cikin jikinshi lokaci d'aya suka saki ajiyar zuciya, k'ara k'ank'ame ta yayi cikin jikin shi, kallon face d'in shi Suhaima tayi tace
"My dear har yanzu tunanin ne, ka fad'a min abin da yake damun ka please "
Shafa face nata yayi kafin yace
"Baby ina son ganin Mumy nah ne "
Murmishi ta saki mai sanyi kan tace
"My dear abu mai sauk'i kawai gobe ka shirya ka tafi, nima kaina ina son kaje kaga Mumy don nasan hankalin ta yanzu yana tashe "
"Yawwa Baby nah ki shirya mu je zan yiwa Daddy waya kada a kawo su twin's gobe muka je sai mu taho dasu "
"Lokaci yayi da zaka koma ka cigaba da rik'on company d'in ka my Dear kabar Daddy da nashi shima "
"Allah Baby da gaske kike zamu koma gidan mu? "
Mak'e kafad'a tayi cikin sigar wasa tace
"A'a ni dai zamu zauna anan duk weekend sai kazo kana ganin mu "
Ta6e fuska yayi yana son yin kukan shagwa6ar da aka kwana 2 ba'a yi ba yace
"Haba Baby baza ki tausaya wa d'an mijin ki ba, idan muka zauna waje d'aya sai yafi min kwanciyar hankali please please Baby nah"
"Uhm uhm wayo kake son yi min nak'i yarda "
Da ya gane tsokanar shi take nan ya cafkota tare da cewa
"Baby kin rainani da yawa don kin ga kwana 2 kin huta baki samawa su twin's k'annen su ba koh, bari yanzu zan baki ajiyar Baby nah "
Dariya sosai Suhaima take yi ganin yanda yayi, tashi yayi da sauri ya rufe k'ofar d'akin sannan ya dawo kusa da ita ya shiga aika mata da sak'onnin shi bata yi musu ba itama ta shiga mai da mishi da martani, sun jima suna faranta ran junan su kafin su yi wanka kuma ya shirya ya tafi masjid don sallahr la'asar yayin da Suhaima kuma ta zauna gyara jikinta.
Su Daddy na hanya dawo da Na'eem da Shaheed ne Sabeer ya kirawo shi a waya akan suyi zaman su gobe suna tafe zuwa gida don yaga Mumyn shi, sosai Daddy yaji dad'in haka nan ya shiga sanyawa Sabeer albarka daman da wannan niyyar ya taho na wajen rarrashin shi ya zo Mahaifiyar shi ta ganshi, bayan sun gama waya ne Daddy ya sanya driver ya koma gida sai ganin su kawai Mumy tayi cikin jin dad'i ta rungume Na'eem da Shaheed suma sai murna suke da ganin sun dawo wajen ta sai da ta gama murnar dawowar su sannan ta kalli Daddy tace
"Yana ga kun dawo sun bar min su ne? "
"A'a gobe iyayen su zasu zo sai su tafi dasu basanan yau ne "
Yana gama fad'in haka ya wuce ya fita, dad'i sosai Mumy taji idan sun zo zata nemi alfarmar su barmata su don Allah idan yaso ta sanya su schl duk hutu sai suna zuwar musu hutu wajen iyayen su.
Da daren ranar Sabeer yake yiwa Aliyu maganar zuwan su gobe gida nan Aliyu yayi mishi fatan alkhairi shi da Aunty Aliyah, cikin daren nan Sabeer kasa bacci mai nauyi yayi yana zumud'in gari ya waye ya ganshi a jikin Mumyn shi yana zuba mata shagwa6a son ranshi.
Washe gari bayan sun gama breakfast ne Aliyu ya sanya aka taro musu taxi har k'ofar gida, basu dad'e ba suka fito cikin shirin tafiya Sabeer na sanye da wata shadda ash colour yayin da Suhaima take sanye da wani lace ash&pink d'in flower's sunyi kyau sosai nan suka yi sallama da kowa kafin su shiga motar mai taxi yaja su tafi, Suhaima murmishin yak'e kawai take amman gabanta sai fad'uwa yake batasan me zata je ta tarar acan ba don haka duk a tsorace take.
Tun safe da Mumy ta tashi take faman zirga zirga a tsakanin kitchen da dining area tana shirya abincin bak'i, dariya ta bawa Daddy ma sosai ganin ko baccin kirki ta kasa don tana son kyautata musu Sosai su ji dad'i, don su ji dad'in bar mata Na'eem da Shaheed cikin zuciyar Daddy cewa yayi yaran ki ne zasu zo ba wasu bak'i daban ba.
Sai da ta gama shirya komai sannan ta barwa en aikin ta gyaran palon da na kitchen, tattara Na'eem da Shaheed tayi suka tafi Upstairs d'akin ta suka shiga nan tayi musu wanka tsaf tare da shirya su cikin kayan su irin d'aya jean ne blue sai pink d'in T-shirt sunyi kyau sosai takalman su ma pink ne ta fesa musu perfumes masu k'amshi, zaunar dasu tayi saman bed tare da basu iPad d'inta bayan ta kamo musu game tace
"Oya ayi game ban da fita kuma ban da rigima yanzu zanyi wanka "
Gid'a mata kai suka yi don hankalin su nakan wayar murmishi tayi ta shafa kansu sannan ta wuce toilet, agurguje tayi wanka ta fito ta shirya cikin wata gown black mai adon silver tayi rolling kanta da veil d'in rigar sosai tayi kyau bakace ita ta haifi Sabeer ba bayan ta fesa perfumes ne ta kamo hannun su Na'eem da Shaheed suka fito zuwa downstairs a palourn suka zauna tana zaune ta zubawa k'ofar palo ido so take kawai taga iyayen Na'eem da Shaheed.
Motar na tsayawa agaban gate d'in gidan sai da gaban Suhaima ya fad'i sosai fiye da lokutan bayan, hannun ta Sabeer ya rik'o ya rik'e k'am tare da cewa
"Relax Baby na ki kwantar da hankali babu abin da zai faru insha Allah ina tare da ke "
Jikinta a sanyaye ta gid'a kanta kawai don bakin ta yayi mata nauyi, fitowa suka yi daga cikin mota daman Yah Aliyu ya biya kud'in duk kuwa da Sabeer yak'i yarda da hakan amman sai da biya, mai taxi ya juya ya tafi kallon gidan Sabeer ya tsaya yi yana nan yanda yake sai gyaran shi da akayi sosai, tura k'ofar jikin gate yayi suka shiga hannun shi rik'e dana Suhaima jikinta ko'ina rawa yake na tsoro.
Da yake atime d'in rana tayi sosai kowa yana part d'in shi, maigadi sakin baki yayi yana kallon d'an lelen gidan d'an fillo, murmishi Sabeer yayi mishi aikuwa nan ya k'araso wajen Sabeer zai tsugunna ya hanashi bakin shi yak'i rufuwa yake gaida Sabeer da Suhaima yana murnar dawowar shi.
Sallamar maigadi yayi sannan suka wuce cikin gidan kai tsaye part d'in su ya shige dasu, door bell ya danna sau biyu zai danna na ukun ne aka bud'e k'ofar parlourn.
Kallon junan su suka tsayi cikin wani irin shauk'in so na tsakanin uwa da d'anta kowannen su idanun shi taf da hawaye, ji suke tamkar a mafarki hawayen eyes d'in Mumy ne ya sakko kan face d'in ta tana cewa
"My Son kai nake gani da gaske? "
K'arasa shiga cikin parlourn yayi still hands d'in shi cikin na Suhaima, d'ayan hannun shi ya sanya yana goge mata face d'in ta cikin rawar murya yace
"Mumy ni ne Sabeer d'in ki ba mafarki kike ba "
D'aga hannun ta sama tayi tare da cewa
"Allah Yah Allah nagode maka da ka dawo min da yaro na cikin koshin lafiya "
Tsugunnawa k'asa suka yi daga Sabeer har Suhaima wadda bata kula da ita ba yace
"Mumy I'm so sorry nasan na 6ata miki rai da yawa kiyi hak'uri ki yafe min please "
Dafa kanshi tayi kafin tace
"Son ni ce wadda ya kamata na rok'i ka yafe min don ni na aikata maka abubuwa da dama ka yafe min d'ana"
Ta k'arasa maganar tana had'a ido da Suhaima, da sauri Suhaima tayi k'asa da kanta gabanta na fad'uwa jikinta na rawa sosai don batasan me zata yi mata ba.
Cikin mamaki sosai Mumy tace
"Son daman kana tare da Suhaima "
"Yes! Mumy ina tare da Mata ta "
"Alhamdullilah Allah nagode maka da ka dawowa da d'ana farincikin shi "
Tashin Suhaima tayi ta rungume ta k'am ajikinta lokaci d'aya ta fashe da wani irin kuka tana fad'in Suhaima ta yafe mata, cikin hawayen farinciki da na tausayin Mumy Suhaima tace
"Mumy komai ya wuce wallahi na yafe miki tuntuni, mu ma ki yafe mana "
"Na yafe muku duk da babu abin da kuka yi min ni ce na zalunce ku"
"No Mumy ki daina fad'in haka komai ya wuce please "
Had'a su tayi ta rungume su sosai suna zubar da hawayen farinciki, Daddy ne yayi clapping hand's nashi duk suka jiyo suka kalle shi face nashi fal farinciki yace
"Alhamdullilah wannan rana itace nake addu'a koda yaushe Allah ya nuna min ita ina raye, hak'ik'a naji dad'i sosai nayi farinciki da haka "
Murmishi Mumy take duk da kuwa tears ne ke zuba daga eyes nata, nan Sabeer ya nemi yafiyar iyayen su suka yafe mishi tare da yi musu addu'o'i na fatan alkhairi acikin rayuwar su kowannen su cikin zuciyar shi fal farinciki.
"Abbah! Mamee! "
Suka jiyo voice d'in su twin's suna kwala musu kira da sauri suka taho inda suke da gudu suka rungume iyayen nasu suna masu farincikin ganin su, kusan suman tsaye Mumy tayi kallon Daddy tayi tana neman k'arin bayani a wajen shi.
Murmishi yayi kafin yace
"Jikokin ki ne yaran Son d'in ki ne da Suhaima "
Wayyo dad'i Mumy rasa inda zata sanya kanta tayi don farinciki da tsabar murna kawai zuwa tayi ta rungume Daddy tana kuka, tapping hands nashi yayi kan bayanta yana cewa
"Is okay Mata ta kukan ya isa hakan godewa Allah zaka yi "
"Daddy bansan me zance ba "
"Godewa Allah zaki yi kawai "
Suna cikin haka ne suka ji anyi magana da bakin k'ofar parlour ana cewa
"Hussein da gaske maigadi yake cewa Sabeer ya dawo gida "
Da sauri Sabeer ya juya ganin kakan shi Dr Ahmad d'an fillo ne yake maganar daganin shi kasan bashi da cikakkiyar lafiya, da gudu Sabeer ya k'arasa wajen shi ya rungume shi yana cewa
"Ni ne Sabeer d'an lelen ka na dawo gare ku kakanah "
"Alhamdullilah naji dad'in haka sosai Allah yayi maka albarka da ka dawo gare mu kada ka sake yi mana irin haka d'an lele don ka tasar mana da hankali sosai "
Cikin kaunar d'an tsohon da tausayin shi Sabeer yace
"Insha Allah bazan sake ba "
Ana cikin haka Hajjah Hauwaa tazo itama ta gama d'an kukanta na dawowar Sabeer, anan suke ganin Na'eem da Shaheed wai duk yaran Sabeer ne, Dr Ahmad d'an fillo baisan lokacin da ya rik'e hannun Suhaima yana zuba mata godiya ba Hajjah Hauwaa kuwa rungume ta tayi, nan family's na cikin gidan suka dunga shigowa zuwa ganin twin's da taya su Mumy murnar dawowar Sabeer gida.
Dr Ahmad d'an fillo kwasar twins yayi suka wuce part d'in su dasu don bazai iya barin su ba son yaran yake har ma ya zarta son da yake yiwa Baban su, sai after la'asar ne su Suhaima da Sabeer suka samu zaman cin abinci bayan sunyi wanka, suna gama ci Mumy takai Suhaima bedroom d'in ta don ta huta komai ganin shi Suhaima take tamkar a mafarki wai yau itace Dr Faridah take rungumeta ajikinta tana mata godiya sannan kuma family's d'in Sabeer suke murnar kasancewar ta acikin su kowanne yana farincikin ganin ta lallai komai da lokacin shi duk tsanani yana tare da sauk'i hak'uri yana da riba babba a rayuwa haka kuma ka rik'e addu'a baza ka ta6a ta6ewa ba a rayuwar ka............
_Masu yi min addu'a ta samun sauk'i Alhmdllh na samu lafiya, nagode sosai Allah ya bar zumunci_Ameen
Aıʂɧąɬ A Mųɧ'ɖ ✍🏻
*A SANADIN SON KI*
Wྂrྂiྂtྂtྂeྂnྂ bྂyྂ
Aྂıʂɧąɬ Aྂ Mྂųɧ'ɖ
ɖɛɖı¢ąɬɛɖ ɬơ ɱყ ʂąɖɛɛყ ʂąŋąʑ
♻ *єχ¢ℓυѕινє ωяιтєя'ѕ fσяυм*
*THE END*
_Na sadaukar da dukannin shafin nan ga dukkanin masoya na da fan's d'in A SANADIN SON KI, ina gaida ku aduk inda kuke tare da yi muku fatan alkhairi cikin rayuwar ku_❣
*PAGE 115*
Kwanakin su biyu agidan suna zaune cikin farinciki Mumy tattalin Suhaima sosai tana bata kulawa haka sauran en uwan Sabeer ma haka duk wad'anda suka yi mata abubuwa marasa dad'i sunzo sun bata hak'uri kuma ta hak'ura daman bata rik'e su ba cikin zuciyar ta, Jiddah tayi farinciki yanda en uwanta suka kar6i Suhaima a yanzu matsayin suruka ta gaban goshi kowa tattalin ta yake.
Kwana su biyu agidan da dare Sabeer ya shigo side d'in Mumy ya gaji da kewar matar shi, kunya ce take sanya ta k'in zuwa side d'in shi koda ya nemi da ta zo inda yake, gajiya yayi da wannan abun ya tahi d'akin, yana shigowa d'akin tana fitowa daga bathroom d'aure da towel duk gashin kanta ya watsu a fuskar ta da wuyanta duk sun manne saboda