Showing 96001 words to 99000 words out of 122360 words
Chapter 33 - A sanadin Son ki Hausa Novels Document complete by Aisha A Muhammad Sanaz.txt
cigaba da zaman ki kamar da nasan ta inda zan 6ullowa al'amarin "
Gid'a kanta take kamar k'aramar yarinya tana goge hawayen face nata, bayan ya gama rarrashin ta ne sai ya tafi yayin da ita kuma Mumy ta nufi upstairs zata fara hawa steps sai ga Daddy nan zai sakko.
Suna had'a ido ya sakar mata harara kafin yace
"Me kike har yanzu baki bar min gida na ba!? "
Ko kallon inda yake Mumy bata yi ba ta wuce shi da sauri zuwa side d'inta da kallo ya bita kafin ya girgiza kanshi kawai, ya wuce zuwa 6angaren masu aiki ya bud'e Larai da take cikin d'akin wadda ta kasa zaune ta kasa tsaye tsabar firgita da razana.
Jin an bud'e k'ofar nan ta jiyo a rikice ganin Daddy ne ya sanya ta zubewa a k'asa cikin tsorata tace
"Don girman Allah Alhaji kayi hak'uri ka barni na tafi nayi alkawarin bazan sake maimaita abin da nayi ba wallahi "
"Ya isa haka zan barki ki tafi amman kiji tsoron Allah a duk inda kike kisan yana ganin ki komai zaki aikata, ina son ki tafi kada ki k'ara dawo min gida "
Abin da ya sanya Daddy kyale ta ganin ga babbar mai sanyawa a aikata laifi amman an hanashi d'aukan mataki akanta shi ya sanya rabuwa da ita, nasiha yayi mata kan ya bar d'akin.Aikuwa cikin rawar jiki ta sungumi ghana must go d'inta ta k'ara gaba da sauri ko waiwaye bata yi.
Cikin kwana 2 gidan ya koma shiru babu walwala acikin shi kamar da, Sabeer baya iya zuwa ko'ina kullum yana cikin bedroom a kwance yana tunanin ta yanda zai tunkari Suhaima da wanne ido zai kalle ta yace ta koma gidan shi baya ga cin mutuncin da yayi mata tare da 'yan uwanshi tun da ta tafi wajen 7 months bai je inda take ba.
Wad'annan tunanin ne idan yayi suke matuk'ar hargitsa mishi kai ya rasa sukuni cikin zuciyar shi, ta 6angaren Mumy da Daddy ma babu wata jituwa tsakanin su kowa yana side shi gashi babu mai shiga harkar wani acikin su, duk da Mumy kusan kullum sai tayi kuka a 6oye saboda ganin d'anta da mijinta sun guje mata amman bata ta6a nuna musu hakan a fili ba.
Sabeer kasa hakura yayi sai kawai ya nemi Jiddah a waya dakyar Jiddah tayi picking wayar saboda haushin shi take ji ya rabata da Suhaima da tasan sanadin auren Yah Sabeer zai kawo matsala a tsakanin ta dasu Suhaima da bata bayar da goyon baya.
Murya ciki ciki ta amsa mishi sallamar tashi, d'an murmishin yak'e yayi cikin zuciyar shi yana cewa, Jiddah da zaki fahimci halin da nake ciki yanzu da kin tausaya min amman a fili sai yace
"Uhmm Jiddah kina fushi da ni koh? "
"Ni kuma! Me kayi min da har zanyi fushi da kai? "
"Saboda na rabu da k'awar ki mana alhalin kina sane da ban saketa ba saboda son da nake mata "
"Tabd'ijam Yaya a haka kake son Suhaima bayan baka tsaya kayi bincike ba ka kore ta daga gidan ta? "
Wani irin abu ne ya taso ya lullu6e mishi cikin zuciyar shi na tsananin nadamar abin da ya aikata kafin ya sauke numfashi mai zafi yace
"Ina son Suhaima Jiddah har yau amman nasan bai kamata na kore ta ba, bincike ne farkon abin da ya kamata nayi sai na kasa controlling d'in zuciya ta har takai da na aikata hakan, amman yanzu na gane gaskiya "
"Da gaske kake Yaya an gane wanda ya shirya makircin nan!? "
"Ehhh Jiddah duk wannan shirin Mumy ne don kawai ta raba ni da Suhaima "
No wonder ai nasan itace zata aikata hakan don kuwa ita nake zargi fiye da kowa, fad'in Jiddah cikin zuciyar ta kafin ta d'ora da cewa
"Alhamdullilah nagodewa Allah da ya sanya k'awata ta fita daga zargi "
"Yanzu ki fad'a min ta ina zan bi don na dawo da mata ta na kasa tunanin mafita komai ya hargitse min wallahi"
"Tabd'ijam Yaya babu ruwana ni kaina ka shafa min laifi wajen Yah Aliyu sau biyu nake zuwa yake korata baya barina na shiga gidan haka nake dawo wa, bani na aikata laifi ba amman Yah Aliyu ya kasa tsayawa ya fahimci ne babu hannuna cikin aikata wannan abun wallahi "
Ta k'arasa maganar cikin rawar murya hawaye na zuba daga idanun ta, wani fad'uwar gaba Sabeer ya tsinci kanshi aciki kafin ya iya bud'e baki dakyar yace
"Yanzu kenan babu wani idea a wurin ki wanda zai sanya ni zuwa wajen Suhaima na dawo da ita? "
"Ni dai shawarar da zan baka kawai ka je wurin Suhaima duk abin da Yah Aliyu zai yi maka ka hakura ka daure zuciyar ka har zuwa lokacin da zai sakko ya hakura, don Yah Aliyu mutum ne mai zafi amman yana da tausayi sosai amman ina mai baka shawara kada Mumy taji labarin tafiyar ka can don zata iyayin wani abun don kawai Suhaima kada ta dawo wajen ka "
"Nagode k'anwata"
"Babu komai Yaya Allah taimaka "
Dakyar ya iya cewa Ameen sannan suka yi sallama, tunani ya fad'a sosai kafin daga k'arshe ya fito daga bedroom d'in shi.
Parlour ya fito ya tarar da Daddy yana zaune yana aiki a laptop yayin da Mumy take ta shirya kan dinning table duk da ba cin abincin suke ba wani lokacin idan tana free tana kok'arin had'a musu abinci da kanta.
"Daddy ina son zan tafi England akwai wani abu da zanyi mai amfani acan "
Kallon shi Daddy yake cikin mamaki kafin yace
"Son me zaka je kayi acan? "
"Daddy abun sirri ne idan na dawo zan fad'a maka shi "
Gid'a kai Daddy yayi kan yace
"Okay bari na sama maka visa wajen friend d'ina "
"No Daddy na gama komai nan da 2hrs jirgi zai tashi "
Kallon ban yarda da kai Daddy yake yiwa Sabeer, yayin da ya d'an yi murmishi kawai yana kauda kanshi don baya son had'a ido da Daddy.
"Shikenan Son sai kaje ka fara shiri, amman kwanaki nawa zaka yi?"
"Daddy ni kawai sai an ganni huh don na gaji da zaman gidan "
"Ni kaina Son na gaji da zaman don haka mybe na biyo ka can sai kawai mu huta "
Murmishi Sabeer ya d'an yi hannun shi zube cikin aljihun shi yace
"Okay Daddy amman ni sai na fara yin gaba "
'Yar dariyar farinciki Daddy yayi ganin yanda yau Sabeer ya sake yana hira har da murmishin shi, akwai abin da Son ya shirya yi dole na bincike shi, fad'in Daddy cikin zuciyar shi.
Sabeer bai d'auki wani abu masu yawa ba kayanshi set 3 ya sanya cikin k'aramar bag sai laptop d'in shi ko atm card's nashi bai d'auka ba, bayan ya gama ne ya shiga wanka a d'an jima a cikin bathroom kafin ya fito ya shirya cikin wani lallausan farin boyel perfumes different colour ya sanya.
Yana gama wa ne ya d'auki bag d'in tare da rataya ta saman kafad'ar shi ya fito hannun shi rik'e da phone nashi, Daddy shima har ya gama shiryawa don raka Sabeer airport har sun fito zasu tafi sai ga Mumy nan da car key a hannunta tana cewa
"Son muje nayi maka rakiya airport "
Ko kallon ta Sabeer bai yi ba ya wuce zuwa cikin motar da Daddy yake zaune, fita suka yi daga gidan gaba d'aya motar Mumy tana bin bayan tasu Sabeer.
Bayan sun k'arasa airport ne nan Sabeer yayi sallama da Daddy don uwa uwace kawai Sabeer ya sanya shi yiwa Mumy sallama ya wuce su ya tafi zuwa cikin airport ne, dad'i ya ishe Mumy ganin Sabeer ya kulata tana tunanin ko ya fara sakkowa ne, cikin mota ta wuce ta shiga driver yaja ta don hospital zata tafi.
Sabeer ya d'auki wajen 30 minute's azaune kan ya tashi ya fito daga cikin airport d'in zuwa waje, tsayar da taxi ya fara kok'arin yi yaji an dafa mishi kafad'a a razani ya juyo 4 eyes suka yi da Daddy wanda ke faman yi mishi murmishi, ajiyar zuciya ya sauke kawai.
Hannun shi Daddy ya rik'o zuwa cikin mota bayan sun zauna Daddy ya kalle shi kafin yace
"Son tunda ka fad'a min zaka tafi England nasan ba haka bane jikina ya bani akwai wani abun dalilin da ya sanya ni ban tafi ba kenan, ina zakaje? "
"Daddy kauyen su Suhaima zan tafi don na dawo da mata ta "
"Hakan yayi kyau Son ina goyon bayan ka, amman bai kamata ka 6oye min ba "
"Am so sorry Daddy bana son Mumy tasan da inda zan tafi don kada ta hanani dawo da Suhaima cikin rayuwa ta "
Hannunshi Daddy ya rik'o kan yace
"Ka tafi Sabeer idan ta kama duk tsayin lokacin da zaka yi acan kayi shi amman kada ka dawo gida babu Suhaima don yarinya ce mai hankali, ka daure duk wani yanayi da zaka fuskanta acan don nasan dole ka fuskanci hukunci awurin su, Allah yayi maka albarka ya taimaka maka ya tsare min kai a duk inda kake"
Rungume Daddy Sabeer yayi yana goge hawayen da suka zubo mishi sun d'an jima a haka kafin Daddy yace
"Ka tafi Son kada kayi tafiyar dare, amman kada mance ka kashe wayar ka saboda Mumyn ka idan ta ji shiru zata iya bibbiyar layin ka har ta gane a inda take ", gid'a kai Sabeer yayi.
Fitowa suka yi daga mota jikin Sabeer duk a sanyaye Daddy ne yayi k'arfin tsayar mishi da taxi ya biyashi kud'i masu yawa tare da ce mishi ya kai Sabeer duk inda yake so, sallama Daddy da Sabeer suka yi har taxi d'in ta wuce Daddy yana tsaye a wajen zuciyar shi fal tausayin d'an nashi kafin ya juya ya shiga mota driver yaja shi sai gida.
Idanun Sabeer a waje yana kallon yanayin gari amman tunani da fargaba tsoro fal cikin zuciyar shi ta yanda za'a kar6e shi gidan su Suhaima idan yayi duba da abin da Aliyu yayiwa Jiddah wadda bata da laifi ko kad'an a wannan abu da ya faru.
Har k'ofar gidan su Suhaima d'an taxi d'in ya sauke Sabeer, dakyar ya iya jarumtar fitowa daga motar gaban shi na dukan goma goma don baisan me zai je ya tarar ba.
Yana fitowa d'an taxi ya k'ara gaba sake gyara jakarshi yayi ta saman kafad'ar shi ya doshi gidan, amman duk takun da zai yi sai gaban shi ya fad'i a haka ya k'arasa k'ofar gidan.
Kallon gida yake da mamaki sosai cikin fuskar shi ganin yanda aka gyara gidan kamar a birni ba'a karkara ba, zauren gidan ya kutsa kanshi, dakyar ya iya bud'e baki yayi sallama cikin sanyin murya.
Amsa mishi sallamar akayi babu tantama yasan muryar Aunty Aliyah ce.
"Suhaima sanya hijab d'inki ki duba ko bak'on Yayan ki ne kice ya jirashi ya shiga wanka "
"Toh Aunty "
Suhaima ta fad'a cikin tsintar kanta da fad'uwar gaba, d'aki ta shiga ta d'auko hijab ta sanya tare da nufar k'ofar zauren still gabanta bai bar fad'uwa ba.
"Ka d'an jira shi ya shiga wank........ "
Suhaima bata k'arasa maganar ba da zatayi sauran ta maka'ale a saman fatar bakinta ganin mutumin da ta had'a ido dashi, rufe idonta tayi ta sake bud'e wa ko mafarki take but still Sabeer take gani cikin eyes nata, tsayawa kawai taji jikinta na rawa zuciyar ta na bugawa da k'arfi kallonta yake cikin wani irin tausayin ta da yake ratsa shi ga wani sabon sonta da yake sake kwaranya cikin zuciyar shi, ita ma kallon nashi take kawai cikin mamakin me ya kawo shi gidan su ko dai ya zo ya baki takardar saki ne wannan tunanin da Suhaima tayi ya sanya firgita da tsorata.
"Suhaima wane ne naji kin tsaya lafiya "
Cewar Aunty Aliyah, maganar da Aunty Aliyah tayi shi ya dawo da Suhaima hayyacin ta, da sauri tabar wajen da sauri Sabeer ya biyo bayanta yana cewa
"Suhaima ki tsaya ki saurare ni please "
A tsorace Suhaima tayi bayan Aunty Aliyah ta 6uya ganin sauran kad'an Sabeer ya cafkota, a firgice Aunty Aliyah take kok'arin cewa Sabeer ya gudu ya bar gidan amman kafin ta bud'e bakinta Aliyu ya fito daga toilet sanye da jallabiya ajikin shi.
Kallon Suhaima da Aliyah yayi ganin gaba d'ayan su a razane yasa shi kallon inda suke kallo aikuwa suka had'a ido da Sabeer, kamar wani zaki ya nufi inda Sabeer yake tsaye wanda ko gezau bai yi ba na nuna tsoro hasali ma gaba d'aya hankalin shi na kan Suhaima.............
Aishat A Muh'd
Aıʂɧąɬ A Mųɧ'ɖ ✍🏻
*A̺͆ S̺͆A̺͆N̺͆A̺͆D̺͆I̺͆N̺͆ S̺͆O̺͆N̺͆ K̺͆I̺͆*
Wྂrྂiྂtྂtྂeྂnྂ bྂyྂ
Aྂıʂɧąɬ Aྂ Mྂųɧ'ɖ
ɖɛɖı¢ąɬɛɖ ɬơ ɱყ ʂąɖɛɛყ ʂąŋąʑ
♻ *єχ¢ℓυѕινє ωяιтєя'ѕ fσяυм*
*PAGE 102-103*
Afusace Yah Aliyu cakumi wuyan Sabeer ya matse da k'arfi idanun shi tuni suka yi ja ya fara wani irin tari, cikin fusata yake cewa
'Me kazo yi kuma, bayan ka koreta daga gidan ka ina fatan takardar sakin ta ka kawo min don k'anwata bazata ta6a komawa gidan ka ba? "
Dakyar Sabeer yake jan numfashi don ba k'aramin shak'a Aliyu yayi mishi ba, cikin murya k'asa k'asa yake cewa
"Nazo ne domin na baku hak'uri akan abin da ya faru na kuma dawo da Suhaima gidana "
Dad'a shak'e shi Aliyu yayi kan yace
"Kaiii asuwa da har zaka sanya Suhaima dawowa gidan ka, k'anwata ta barka har abada bakai ba ita "
Sabeer na kok'arin magana Yah Aliyu yaja shi tare da watsa shi waje ya mayar da k'ofar ya rufe har da sanya sakata, kallon su Suhaima da Aliyah yayi ganin yanda suke kuka sosai hararar ya maka musu kan ya wuce d'aki yana huci.
Suhaima ma da gudu ta shige d'akinta tana kuka da ta rasa na mene, yayin da Aunty Aliyah ta tafi wajen Aliyu ko zata rarrashe shi yayi hak'uri amman tana fara magana da ya buga mata wata tsawa batasan lokacin da ta tsallake Ameer ta wuce d'akin Suhaima da gudu ba, wanda har taso sanya Aliyu dariya amman ya matse dariyar.
Afirgice Suhaima ta juyo jin an shigo d'akin ta da gudu ganin Aunty Aliyah ce ya sanya ta sauke ajiyar zuciya tana goge hawayen fuskar ta tace
"Aunty lafiya kuwa "
Zama tayi kan tace
"Hummm Suhaima Yayan nan naki ya d'auka da zafi sosai wallahi don zuwa nayi na bashi hak'uri amman wata tsawa da kwantsama min bansan sanda na sanya gudu ba, ina tausayin Sabeer nasan ba laifin shi ba ne laifin shi d'aya da yace ki bar mishi gidan shi "
Suhaima bata ce komai ba kawai sai ta zame ta kwanta tare da d'ora kanta saman k'afar Aliyah zuciyar ta a cunkushe take sam ta rasa abin da yake damunta.
Sabeer kuwa tun lokacin da Yah Aliyu ya watsa shi waje kasa tashi yayi awajen kawai ya zauna tare da janyo bag d'in shi ya d'ora saman k'afar shi ya fad'a kogin tunanin yanda zai shawo kan wannan matsalar, gaba d'aya wuyan shi ya rik'e ko iya juyashi sosai baya yi sabida shak'ar da yasha a hannun Aliyu, wai shi Sabeer shine aka watso shi waje kamar shi da kud'in shi da gatan shi amman duk A SANADIN SO komai na rayuwar shi ya canja.
Yana nan zaune aka yi kiran sallahr mangarib yana kok'arin tashi ya tafi masallaci ko zai samu ruwan alwala yaji an bud'e k'ofar an fito, sai da gaban Sabeer ya fad'i ganin yanda Aliyu ya tamk'e fuska tamkar bai ta6a dariya ba.
Kallon Sabeer yake cikin mamaki kafin yace
"Wai kai wanne irin mutum ne nace kabar min gidana bama buk'atar ba ana dole ne k'anwata ta tsane ka bata sonka ina son kawai ka rubuta mata saki ka bata tun muna mu biyu da kai kaji na fad'a maka "
Yana gama fad'in haka yaja tsaki tare da wuce wa, wani bak'inciki ne ya lullu6e Sabeer ganin wanda a girme bazai girme shi ba yake fad'a mishi magana son ranshi, da zai iya cire son Suhaima ya ajiye shi gefe da yayi don kawai samun sauk'in halin da yake ciki da me zai ji abubuwa gaba d'aya sun hargitse mishi ya rasa samu mafita.
Dakyar ya lalla6a yaje masallaci can ya samu ruwa yayi alwala tare da bin jam'in sallahr mangarib bayan an idar ne yana zaune a masallacin yana addu'ar Allah ya sassauta zuciyar Aliyu ya kyale mishi Suhaima kada ya rabasu, har aka kira sallahr ishsha bayan an idar da sallahr ne kowa ya watse sai shi kadai ya rasa wajen zuwa.
Yana nan zaune har wurin 9 na dare ga wasu sauro da suke kai mishi cafka ga zafi da duhu dulum a wajen ga wata azababbiyar yunwa da take k'ulle mishi ciki, kamar a mafarki yaji ana kiran shi cikin mamaki da sauri ya tashi ya fito daga cikin masallacin.
Baba Adamu ya gani tsaye da torchlight a hannun shi, tsugunnawa Sabeer yayi ya gaida shi amsa wa yayi kan ya kama hannun Sabeer suka doshi gidan Aliyu.
Atsakar gidan ya tarar da Aliyu, Suhaima, Aliyah, Babaa Lantana suna zaune ran Aliyu a 6ace yake don sosai Aliyah ta shammace shi taje ta fad'a wa su Baba Adamu halin da ake ciki sai aika mata da harara yake yi saboda yaso ya kar6i takardar sakin Suhaima ya fatattaki Sabeer kafin su ankara, sai gashi Aliyah ta shammace shi.
Zama Sabeer yayi gefen Baba Adamu sanann ya fara magana akan rashin kyautawar da Sabeer yayi na tsayawa yayi bincike kafin ya kori Suhaima, sanann ya d'ora da yiwa Aliyu nasiha tunda ya gane gaskiya bai kuma kyauta da abin da yayi ba har yazo domin ya nemi afuwar su ya kamata ya hakura kowanne d'an adam bai cika goma ba.
"Baba ni kawai ya bata takardar ta kawai yayi tafiyar shi Suhaima bazata koma gidan shi ba"
"Baza'a yi haka ba Aliyu a tambayi Suhaima tana son komawa tunda ya gane laifin shi har ya bada hak'uri kamata yayi ayi mishi afuwa "
Kallon ta Baba Adamu yayi kan yace
"Suhaima ina son ki fad'a min tsakani