Showing 78001 words to 81000 words out of 122360 words
Chapter 27 - A sanadin Son ki Hausa Novels Document complete by Aisha A Muhammad Sanaz.txt
zan had'a maka? "
"Komai ma Baby zanci tunda ke zaki dafa min"
Tana kok'arin kunna gas ne suka ji an danna door bell, kallon ta yayi sannan ya yamutsa fuska yana cewa
"Yanzu haka Jiddah ce zata zo ta dame mu muna cikin hutawar mu ko lokacin da tayi nata auren wane ya tak'ura mata da zata dame mu"
Dariya ta kusan kubcewa Suhaima amman sai ta danne don taga fuskarshi d'auke da damuwa, amman gaskiya har cikin zuciyar ta taji dad'i zuwan Jiddah har idan itace d'in.
"Har kasan Jiddah ce ta zo? "
"Of course don nasan itace zata yi zuwan wannan wurin "
Tunawa da Suhaima tayi ko lokacin da zasu fito a d'aki da 11 na safe yayi shine zuwan wuri, Sabeer yasan ba mai zuwa cikin family d'in shi sai Jiddah shi yasa ya kawo ta cikin ranshi itace.
Fita yayi tare da bud'e door d'in aikuwa tunanin shi ya zama gaskiya Jiddah ce da sauran friends na Suhaima wad'anda anjima kad'an zasu koma gidan su, shine suka zo yiwa Suhaima sallama.
Wata harara da Sabeer ya watsawa Jiddah sai da dariya taso kubce mata amman ta danne ta tare da turo baki tace
"Wai... wai kai Yah Sabeer indai muka had'u sai kayi ta harara ta ni me nayi maka? "
Share Jiddah yayi yana amsa gaisuwar friends d'in Suhaima da suke mishi yana gama amsa wa ya basu hanya zasu wuce, aikuwa ya sanya hannun shi ya rankwashi kan Jiddah har sai da ta saki k'ara ta rik'e kanta nata wanda sauran kad'an ta zubar da basket d'in hannun ta.
Jin k'arar Jiddah ya sanya Suhaima fitowa daga kitchen duk saurin da taso yi amman ta kasa sai a hankali ta taho, Jiddah na hango ta da sauri ta k'arasa wurinta had'e da rungume ta.
"Lafiya naji kina k'ara? "
Tana turo baki tare da kau da kanta daga kallon Sabeer tace
"Ba mijin ki bane ya rankwashe ni akaina ba, duk abin da nayi mishi bai gani ba"
Had'a ido tayi da Sabeer taga yana shafa bayan kanshi, d'an murmishi tayi tare da girgiza kai kawai wannan abu tsakanin su ne ita me zata iya yi akai, hannun Jiddah Sabeer ya kamo yana cewa
"Sorry sweet sister ke kika ban haushi ina cikin hutawa zaki zo ki katse min hutu, yanzu me kika kawo mana? "
Duk a hankali yake mata maganar, yayin da Suhaima ta k'arasar da friends nata cikin parlour suka zauna.
"Yaya breakfast na had'awa Besty na da kai, ko an kawo muku daga gida? "
Girgiza kanshi yayi cikin takaici ya furzar da numfashi, hannun shi ta kamo cikin jin tausayin shi tace
"Yaya kayi hak'uri komai zai wuce insha Allah "
"Nagode 'yar uwata "
Dinning table suka k'arasa zama yayi sannan Jiddah ta fara jera kayan breakfast d'in kan table sai da ta gama sannan ta shiga kitchen ta d'auko su plate, cups, spoons and sauran abubuwan buk'ata na kayan tea, sai da tayi serving Sabeer tea ne sai pepper chicken and chip's da egg's, sannan ta had'awa Suhaima ta kallo inda take zaune acikin parlour ta d'an d'aga murya tace
"Babyn Yah Sabeer kizo kiyi breakfast "
Murmishi Suhaima tayi kan ta tashi ta taho zama tayi ta d'an fara shan tea d'in, da yake su Jiddah sunyi breakfast a gida sai kawai ta d'auko musu ruwa da drinks ta zauna a parlour cikin k'awayen Suhaima suna hira tare da kallo.
Ganin yanda take cin abincin ne yasa shi cewa
"Baby lafiya kuwa? "
"Me yafaru? "
Ta fad'a tana kai cup na tea bakin ta.
"Bakya cin abincin sosai "
Kamar zata yi kuka tace
"Ni bana jin dad'in baki na ne "
Tausayin ta ne ya kamashi cikin kulawa ya rik'o hannun ta sannan yace
"Sannu Baby amman ki daure kici abincin zaki ji dad'in jikin ki"
Fork d'in ya kar6a daga hannun ta bata yake abaki a hankali take kar6a har tace mishi ta koshi sannan ya rabu da ita, tashi suka yi daga dinning table d'in parlour ta dawo yayin da shi kuma ya shige upstairs.
Cikin 30 minute's ya fito ya canja kaya zuwa wani black boyel takalmi ma black da watch d'in shi but bai sanya hula ba sai ya gyara gashin kanshi, sosai yayi kyau Suhaima ma binshi da kallo tayi kan ta d'auke kanta kuma tana yiwa Allah godiya da ya bata Sabeer a matsayin miji.
Saukar numfashin shi taji kan face nata, d'ago eyes nata tayi suka had'a ido kafin ta janye nata, d'an murmishi yayi yana daf da k'arasa cire wannan kunyar.
"Baby zan tafi gida wajen su Daddy mu gaisa "
"Okay, ka gaida su Allah ya dawo da kai lafiya "
Sai da ya lumshe idon shi yaji dad'in abin da ta fad'a, kafin yace
"Amin Baby nah "
Yayi kissing nata a kumatu sannan ya fita.
Hira suka yi sosai har zuwa lokacin da 'yan uwa Suhaima suka zo, gara suka kawo kamar yanda al'adance ake yiwa amarya sai su dublan, alkaki da su cincin, wani abin dad'in a wajen Suhaima har da Baba Lantana da Aunty Aliyah aka zo.
Don Aunty Aliyah kasa jurewa tayi sai da ta biyo su aikuwa Suhaima rungume ta tayi k'am tana kuka, dakyar dai aka rarrashe ta tayi shiru sannan Suhaima ta canja kayanta zuwa wani lace milk and touch pink ajikin shi sai mayafi pink da shoes nan Jiddah ta fesa mata perfumes masu sauk'in kamshi suka tafi gidan su Sabeer don damk'a amanar Suhaima a hannun su.
Sakin baki da hanci suka yi suna kallon had'uwar gidan, inda Allah ya taimake su basu da yawa suka zo su 5 ne sai Suhaima, Jiddah da friends nata.
Jiddah ce tayi musu jagora har zuwa part d'in Alhj Dr Ahmad d'an fillo, Hajjah Hauwaa suka tarar a parlour tana zaune ta wani hamshak'e kan kujera eyes nata d'auke da medical glass tana kallon tashar Arewa 24 suna yin film na india mai translation in hausa.
Sai Dr Faridah da take gefen ta suna d'an ta6a hira jifa jifa a tsakanin su, a wani kyamace suka amsa sallamar tasu ko wajen zama ba'a basu, sai da Jiddah tayi magana cikin bak'inciki tace
"Babaa Lantana Aunty Aliyah ku zauna "
Nan suka zauna jikin su a sanyaye da irin tar6ar da aka yi musu, Jiddah fita tayi ta kirawo Umman ta da sauran matan gidan duk suka taho part d'in Hajjah Hauwaa sannan taje kitchen d'in Hajjah Hauwaa ta d'ebo musu soft drinks and snack's sai ruwa ta ajiye musu.
Suna yamutsa fuska suka amsa gaisuwar su, sannan Babaa Lantana ta damk'a musu amanar Suhaima babu dai wanda yace komai saboda takaici Jiddah barin parlourn tayi, tana kyamar halin family d'in su.
Ko drink's d'in da Jiddah ta kawo basu sha ba suka taso suka fito gaba d'aya gwiwoyi a sanyaye, sosai Jiddah ta basu hak'uri a hanyar dawowar su ta gidan Suhaima.
Abinci ma sai takeaway Sabeer ya sanya akayi musu saboda lokaci ya k'ure zasu tafi, bayan sun gama ci suka yiwa Suhaima nasiha sosai Aunty Aliyah ta d'ora da bata shawarwari masu kyau.
Suna yin sallahr la'asar suka ci abinci suka tafi, driver Sabeer ya aiko ya mayar dasu gida tare da kyautar kud'i da ya basu mai yawa, Suhaima tasha kukan rabuwa dasu sosai, har jikin ta ya fara d'umi alamar zazza6i ne zai rufe ta kwanciya tayi tana kuka musamman idan ta tuna family d'in Sabeer basa sonta sai Jiddah da Daddyn Sabeer kawai, rarrashin ta Jiddah tayi sannan ta gyara mata gidan tsaf, sai da tayi wanka Jiddah tayi mata kwalliya ta shirya cikin wata gown tayi kamata sosai duk wani sura na jikin ta ya fito da yake irin roba d'in nan ce, ita ma Jiddah shawarwari ta bata sosai sannan tayi mata sallama ta tafi.
Kwanciya tayi kan kujera ga jikinta babu dad'i, ga abin da 'yan uwan Sabeer suka yi musu ga kewar gida da kad'aicin ita kad'ai agida sai kawai ta fashe da kuka aikuwa nan da nan zazza6i da ciwon kai suka tarar mata lokaci d'aya........
Aıʂɧąɬ A Mųɧ'ɖ ✍🏻
*A̺͆ S̺͆A̺͆N̺͆A̺͆D̺͆I̺͆N̺͆ S̺͆O̺͆N̺͆ K̺͆I̺͆*
Wྂrྂiྂtྂtྂeྂnྂ bྂyྂ
Aྂıʂɧąɬ Aྂ Mྂųɧ'ɖ
ɖɛɖı¢ąɬɛɖ ɬơ ɱყ ʂąɖɛɛყ ʂąŋąʑ
*PAGE 82-83*
Tana nan kwance ta kudundune cikin bargo tana rawar zazza6i ga hawayen da suke zuba a idanunta, kanta ciwo yake mata kamar ya cire duk eye's nata sunyi ja sun kumbura, tana cikin wannan halin Sabeer ya shigo bedroom d'in nata.
"Baby baccin yamma kike me yasa Jiddah bata zauna da ke ba har na dawo? "
Yana maganar yana hawa kan bed d'in, yaye blanket d'in yayi tare da sanya hannun shi zai d'ago ta jikin shi, sai yaji zafi sosai jikinta da ya ta6a jikinta, a rikice da kallo ta sai yaga hawayen da take nan da nan hankalin shi yayi mugun tashi har ya rasa me zaice yana tsoron kada ya kasance ya illata 'yar mutane, jiki na rawa ya d'auke ta ya shimfid'e ta saman k'afafun shi cikin tashin hankali yace
"Baby nah me ya same ki, ina ne yake miki ciwo, me yasa baki kirawo ni kin fad'a min na kirawo doctor ya duba ki ba, tun yaushe wannan zazza6in ya rufe ki haka? "
Muryar shi da d'an rawa yake maganar, kasa magana Suhaima tayi sai hawayen da suke zuba kawai ita abin da yake sake firgitata da tsorata ta kada 'yan uwan Sabeer su rabasu, tabbas ta kamu da son Sabeer wanda tasan idan suka rabu su ba k'aramin tashin hankali zata shiga ba.
"Kiyi min magana Baby please, ki daina kuka kin ga yanda idanun ki suka koma kuwa? "
Ganin yanda ya d'aga hankalin shi ya sanya bud'e idanun ta dakyar ta kalle shi kafin tace
"Zazza6i da ciwon kai ne kawai suke damu na"
"Sai me kuma? "
"Shikenan "
D'an kallon ta yayi sannan yace
"Baby fad'a min gaskiya abin da su Mumy suka yi muku shi ya sanya ki kuka ko? "
Da sauri ta d'ago kanta ta kalle shi cikin mamakin a inda yasan me akayi musu, d'an girgiza kai na takaici yayi then yace
"Nasan komai Baby, idan don wannan kike damuwa don Allah ki daina sanya shi cikin zuciyar ki kada ya janyo miki wani ciwon please, sannan zan d'auki mataki "
"Amman dai bai ka......."
Hannun shi ya sanya saman bakin ta ya rufe tare da cewa
"Baby kiyi shiru kawai, bari na kirawo doctor ya duba min ke "
Langa6e kanta tayi cikin yanayin shagwa6a tace
"Ni Allah bana son allura ne da shan magani, zan warke a hakan kawai "
"Ke kinma isa amarya fah kike taya ciwo yazo bazan d'auki matakin gaggawa akanshi ba sai yayi k'arfi ya hanani cin amarci nah tabbb yarinya naki wasa ne "
Sanya face nata tayi cikin kirjin shi tana d'an murmishi don ya bata kunya, tana ji ya kirawo Doctor Aishat wadda take babbar likitace ta gynecologist ce tana aiki a hospital d'in Dr Faridah wato Mumy.
Tsayin 5 minutes suka d'auka suna waya kafin ya kashe ya kalli Suhaima wadda ta lafe ajikin shi dauriya kawai take amman kanta ciwo yake sosai, shafa kanta yayi da hannun shi yana cewa
"Sannu Baby nah yanzu Doctor Aishat zata zo ta duba ki "
"Amman bazata yi min allura ba koh? "
"Eh zance kada tayi miki tunda bakya so"
D'aga kanta tayi kawai.
"Baby jikin ki yayi zafi sosai sannu dama zan iya dawo da ciwon jikina dana dawo dashi"
Hannunta ta d'ora saman face d'in shi tana shafa kwantaccen gashin sajen shi zuwa gefen bakin shi, lumshe eyes nashi yayi yana jin wani abu na ratsa shi kai hannun ta yayi bakin shi yayi kissing d'in tsakiyar tafin hannun ta, wanda daga shi har ita da bata jin dad'i sai suka ji wani yanayi atattare dasu.
"Kada ka damu zan samu sauk'i insha Allah"
"Amin Baby nah "
Sunan zaune suka ji door bell kafin ya tashi kuma ya bud'e yaji phone nashi na ringing, bayan ya d'auka ne Doctor Aishat take mishi bayanin gata a k'ofar parlour a tsaye.
"Baby bari naje na bud'e mata door ta k'araso "
Yana gama fad'in hakan ya fita daga bedroom d'in, yana shigo da ita ya koma bedroom ya d'auko Suhaima cak kamar wata Baby ya kawo ta parlour duk kunya ta kama Suhaima sosai sai wani sunkuyar da kai take shi kuwa gogan ko ajikin shi sai ma kok'arin had'a ta da jikin shi yake, yayi da Suhaima sai nok'ewa take.
"Yalla6ai me yake damun amaryar taka? "
Cewar Dr Aishat kenan ganin idan ta cigaba da shiru Sabeer zai bata kunya yanzu.
"Uhm Dr Aishat zazza6i ne ke damunta da ciwon kai sai kuma..... Uhmmm kin dai gane bansani ba ko taji ciwo? "
Ya k'arasa fad'a yana shafa bayan kanshi, kamar k'asa ta tsage ta shige ciki haka Suhaima taji a lokacin, yayin da Dr Aishat ta maze don tasan tatsuniyar gizo bazata wuce k'ok'i ba.
"Yalla6ai na fahimta inason zan duba don nagane ko taji ciwo "
"Okay ba damuwa "
Kafin Suhaima ta ankara ya d'auke ta sai bedroom ya kwantar da ita saman bed yayi da Dr Aishat take binsu a baya, ganin ya tsaya bashi da alamar fita ya sanya tace
"Yalla6ai ka taimaka ka d'an bamu waje kad'an"
Ba dan yaso ba ya fita daga bedroom d'in, bayan ya fita ne Doctor Aishat ta duba Suhaima nan ta gane bata ji wani ciwo sosai ba idan tana amfani da ruwan d'umi ma zuwa nan da kwanaki biyu zata warke, nan ta fara kok'arin yi mata allura aikuwa Suhaima ta sanya kuka tare da rirrik'e hannun Doctor d'in, sai Sabeer ta kirawo dakyar ta yarda akayi mata da rarrashi da lalla6a tare da sanya ta ajikin shi aka samu akayi guda biyu sannan ta bata magungunan da zata sha, kuma ta basu shawarwari na yanda Suhaima zata kula da kanta har ta samu sauk'i.
Tukunna tayi musu sallama ta tafi bayan Sabeer ya taka mata zuwa bakin k'ofar fita parlour, kitchen ya wuce ya bud'e frige fresh milk ya d'auko tare da cup ya dawo d'akin lalla6a ta yayi har tasha maganin da fresh milk d'in babu dad'e wa bacci ya d'auke ta da yake har da maganin sanya bacci aciki.
Yana zaune kusa da kanta ya rik'e hannun ta yana aikin kallon ta kawai jinshi yake kamar a mafarki yau wai shine da Suhaima a matsayin ma'aurata, sannan abin da su Mumy suka yi yaji haushi sosai Jiddah ce take fad'a mishi a waya bayan tabar gidan Suhaima, da yaso yin magana dasu Mumy but Daddy ya rarrashe shi kan yayi hak'uri komai mai wuce wa ne wataran sai labari ya zuba musu ido kawai, shi ya cigaba da kula da matar shi don bata da kowa a kusa sai shi.
Kiran sallahr mangarib ne ya tashe shi daga zaunen, addu'a yayiwa Suhaima sannan ya tashi ya fita side nashi ya shiga yayi alwala ya wuce masallaci sai after ishsha ya dawo gidan, yana shigowa farfajiyar gidan ya had'u da driven Jiddah bayan ya gaida Sabeer ne ya bashi sak'on Jiddah na basket mai d'auke da foodflaks 3 sai Jug kar6a Sabeer yayi sannan ya d'auko kud'i ya bawa driven, sosai driven yayi godiya kafin ya tafi, shiga cikin gidan yayi hannun shi rik'e da basket d'in cikin zuciyar shi yana jinjinawa Jiddah da matuk'ar kok'arin da take akan su, yaji dad'in kawo abincin nan daman yanzu yake shirin fita yi musu take away sai gashi na kuma ta hutar dashi, addu'a yayi mata cikin zuciyar shi na Allah ya sauke ta lafiya.
Ajiye basket d'in yayi saman dinning table sannan ya wuce bedroom ya tarar har Suhaima ta tashi tana bathroom don yaji k'arar zubar ruwa, don haka sai yawuce nashi side d'in yayi wanka ya shirya cikin wani catton na kayam bacca and sky blue ya fesa different perfumes masu dad'in kamshi, tukunna ya koma bedroom d'in Suhaima ya tarar har ta fito daga bathroom sallah ma take.
Shiga yayi cikin d'akin ya zauna kan sofa ya d'an lumshe idanun shi, bacci ne sosai cikin eyes nashi ga gajiya, tana idar da sallahr mangarib and ishsha ne bayan tayi shafa'i da wutiri tare da addu'o'in ta ne sai ta tashi ta cire hijab d'in jikinta.
Tana sanye da wata sleeping dress white tsayin ta iyakar shi tsakiyar cinyar ta sai zanin da ta d'aura tayi sallah, batasan Sabeer ya shigo ba sai kawai ta warware zanin ta ajiye shi sannan ta k'arasa wajen dressing mirror ta taje gashinta tare da sanya perfumes ajikinta.
Duk wannan abin da take Sabeer yana kallon ta yayi luf ne kawai ajikin sofa, tuni ya fara jin wani canjin yanayi a jikinshi don kuwa Babyn shi tayi mishi kyau amman sai dai ya had'iye abin da yake ji dole yabar ta taji sauk'i.
Tashi yayi tsaye yana wani binta da kallon k'asan ido ya k'arasa inda take tana d'aure kanta da ribbon hannun shi ya sanya ya cikin gashin kan nata yana wani yamutsa shi, a d'an tsorace ta jiyo ganin Sabeer ne ya sanya ta sauke ajiyar zuciya........
Aıʂɧąɬ A Mųɧ'ɖ✍🏻
*A̺͆ S̺͆A̺͆N̺͆A̺͆D̺͆I̺͆N̺͆ S̺͆O̺͆N̺͆ K̺͆I̺͆*
Wྂrྂiྂtྂtྂeྂnྂ bྂyྂ
Aྂıʂɧąɬ Aྂ Mྂųɧ'ɖ
ɖɛɖı¢ąɬɛɖ ɬơ ɱყ ʂąɖɛɛყ ʂąŋąʑ
*PAGE 83-84*
Ganin Sabeer ne ya sanya ta sauke ajiyar zuciya tare da juya kanta, rungume ta yayi ta baya ya sanya kanshi cikin gashin kanta da wuyan ta yana shak'ar kamshin daddad'an perfumes d'in ta saukar d'umin numfashinshi a wuyanta shi ya saukar mata da wani irin kasala, hannun shi ya sanya yana shafa dogon hannun ta daga kafad'a zuwa 'yan yatsun hannun, kasa jure abin da yake mata tayi sai kawai ta juyo tare da fad'awa kan kirjin shi tsam ya rungume ta ajikin shi yana saukar da ajiyar zuciya, suna nan tsaye wajen 5 minutes ahaka kafin kuma ya bud'e baki yace
"Baby muje kici abinci sai kisha magani "
Hannun ta ya rik'o zuwa parlour har kan dinning table ya zaunar da ita kan kujera,