Showing 108001 words to 111000 words out of 122360 words
Chapter 37 - A sanadin Son ki Hausa Novels Document complete by Aisha A Muhammad Sanaz.txt
da rik'e nata kafin kuma ya janyo ta gaba d'ayan ta jikinshi ya rungume ta tsam, wata wawiyar ajiyar zuciya ya sauke cikin kunnen ta ya rad'a mata
" i luv U Baby nah "
Murmishin jin dad'i tayi bata ankara ba taji ya d'auke ta gaba d'ayan ta bai ajiye ta ko'ina ba sai saman bed kwanciya a jikinta yayi hannun ta yana saman kanshi tana wasa da gashin yayin da shi kuma yake fad'a mata irin matsayin da take cikin zuciyar shi yana bayyana sirrin zuciyar shi wanda wasu abubuwan baza su fad'u a baki tsakanin shi da DANGARTAKAR ZUCIN shi ne wanda yana godiya ga Allah da bai sanya YAYI SAKEN sakin Suhaima ba wanda yasan sai ya fad'a kogin tsantsar nadama amman Allah ya takaita mishi K'ARSHEN WAHALAR shi, zai kasance mai godewa Allah har karshen rayuwar shi akan bashi Suhaima da yayi kamilar mace wadda ta had'a komai kuma wadda kowanne namiji yake fatan ajiye irinta a gida, yasan yasha wahala duk A SANADIN SON ta amman gashi komai ya wuce K'ARSHEN WAHALAR shi yazo yana fatan insha Allah babu abin da zai sake rabashi da Babyn shi sai mutuwa.
Kiran sallahr mangarib ne ya katse su Sabeer ya tashi yayi alwala ya wuce masjid ya bar Suhaima na kok'arin shiga toilet don yin alwala.
Bayan ta idar da sallahr ne ta tsaya karatun Qur'an har zuwa sallahr ishsha bayan tayi addu'o'in ta ne sannan ta sake gyara d'akin sosai ta fita ta sami garwashi ta kunna turaren wuta, sannan ta koma wajen Aunty Aliyah suna d'an ta6a hira duk da har yanzu tana jin kunyar ta akan maganar d'azu.
Sai wurin 9 na dare suka shigo gidan Yah Aliyu da Sabeer nan inda suke zaune a saman tabarma suka zauna kowanne kusa da matar shi, nan Suhaima ta zuba abincin aka fara ci bayan an gama ci aka zauna er hira zuwa 10 na dare suka yi sallama kowa yaja matar shi suka wuce d'akin su.
Duk yanda Sabeer ya so kasancewa da Babyn shi tak'i bashi had'in kai saboda tak'i mance ya tsane ta da ya furta mata, k'arshe da zai takura mata ta sakar mishi kuka dole ya hakura ya fara lalla6a ta har ya samu bacci ya d'auke ta, zuba mata ido yayi bayan bacci ya d'auke ta Baby rigima ya furta hakan kan ya sake rungume ta ajikin shi wani sonta na sake ratsa mishi cikin zuciya da haka shima bacci yayi awon gaba dashi.
*_WASHE GARI DA SAFE_*
Suna zaune gaba d'ayan su a tsakar gidan suna breakfast da yake Yah Aliyu sai da rana yake da lecture sai hira suke cikin jin dad'i da annushuwa.
Sallama suka ji ana yi lokaci d'aya gaban Aliyu da Suhaima yayi mugun fad'uwa wanda har ya kasa yunkurar tashi don yaga wane, sai da aka kuma yi har sau biyu amman ya kasa tashi har sai da Sabeer yace
"Babban Yaya ko naje na duba? "
Da sauri Aliyu ya mik'e tare da cewa
"Barshi bari naje "
Fita yayi jikin shi a matuk'ar sanyaye, yana bud'e k'ofa ya fita ras ras gaban shi ya fad'i ganin wani tsohon mutum duk kanshi da gemun shi furfura ta mamaye su gashi kamar ka hure shi ya fad'i d'an siriri dashi duk yayi bak'i ya zama wani kala gashi yana rik'e da sanda da ita yake dogarawa kallo d'aya zaka yi mishi kasan bai dad'e da tashi daga wannan muguwar cutar ba ta paralyzed ba, jiyowa mutumin yayi suka had'a ido da Aliyu lokaci d'aya Aliyu ya d'ago hannun shi yana nuna shi bakin shi na rawa dakyar bakin shi ya iya had'a kalmar
"Ba... Bab..... Babaaaa! "
Sorry Fan's na kusan gama muku ku cigaba da yi min uxiri.
Aıʂɧąɬ A Mųɧ'ɖ ✍🏻
*A SANADIN SON KI*
Wྂrྂiྂtྂtྂeྂnྂ bྂyྂ
Aྂıʂɧąɬ Aྂ Mྂųɧ'ɖ
ɖɛɖı¢ąɬɛɖ ɬơ ɱყ ʂąɖɛɛყ ʂąŋąʑ
♻ *єχ¢ℓυѕινє ωяιтєя'ѕ fσяυм*
*PAGE 111*
Cikin tsananin mamaki da razani Aliyu ya sake furta
"Baba me ya kawo ka wajen mu kuma yanzu?"
Dattijon ya fashe da wani irin kuka yana cewa
"D'ana kayi hak'uri ku yafe min abubuwan da nayi kuma ciki har da tafiyar da nayi na barku sama da shekaru masu yawa ban waiwaye ku ba "
Ran Aliyu ne ya k'ara 6aci da ya tuna saboda bak'incikin shi mahaifiyar su ta rasu da irin wulak'ancin da ya dunga yi musu, sam bazai ta6a yafe mishi akan abubuwan da ya aikata a gare su, don haka ya bud'e baki cikin rawar murya yace
"Baba ni da k'anwata bama buk'atar sake ganin ka kamar yanda mu ma ka gudu ka barmu don haka kawai ka kyale mu zamu k'arasa rayuwar mu babu uba "
Yana gama fad'in haka ya juya zai koma gida, yayin da Baba yake faman kuka yana furta
"Ku yafe min Aliyu hakk'in ku ne yake bibiyata ku yafe min ko na ji dad'in rayuwata "
Amman ina Aliyu bai saurare shi ba ya wuce gida tare da rufe k'ofar ya jingina bayan shi kan k'ofar duk dauriya irinta Aliyu sai da ya kasa rik'e kukan shi ya fashe da wani irin kuka mai ban tausayi har yanzu yana jin amon murya Baban nashi yana furta su yafe mishi.
"Lafiya kake kuka? "
Yaji saukar muryar Sabeer kusa dashi yana mai rik'e shi hankalin shi a tashe don a iya sanin shi Aliyu jarumi ne ba kamar shi ba dole akwai wani babban abu da ya d'aga mishi hankali.
Girgiza kanshi yake kawai ya kasa magana, suna cikin haka Suhaima da Aunty Aliyah suka shigo zauren jin kamar sautin kuka, hankalin su ba k'aramin tashi yayi ba ganin yanda Aliyu yake kuka, nan take suka fara kukan ita Aliyah zuciyar ta ce ta bata Baban ta ko Babaar tane wani daga cikin su ya rasu.
Da sauri Suhaima ta k'arasa wajen Yah Aliyu ta shige jikin shi tana kuka tace
"Yaya me.... me ya faru kake kuka? "
Ganin yanda hankalin su ne ya tashi sosai ya sanya shi bud'e baki dakyar cikin muryar kuka a shak'e yace
"Suhaima Bab..... Baban mu ne ya dawo "
Awani firgice Suhaima ta d'ago kanta ta kalli Yah Aliyu cikin tsananin tashin hankali da rud'ani kafin ta rushe da kuka tace
"Yaya don Allah kace ya tafi ina tsoran shi wallahi kada ya kashe mu kamar yanda ya fad'a, Yaya zai dawo yana dukan mu da zagin mu ina tsoran shi..... "
Ganin abin nata ya had'ar mata da tsoro, firgici da kuma sumbatu har ta rasa me zata ce ya sanya Sabeer ya janyo ta jikin shi ya rungume ta yana bubbuga bayan ta alamar rarrashi yayin da Aliyah ma ta k'arasa wajen mijinta tana bashi baki da ya bud'e k'ofar duk da kuwa da irin kallon da yake wurgata, gashi sai wani sauke huci yake kamar wani tsohon zaki.
Suna tsaka da haka ne suka ji ana bubbuga k'ofar cikin sauri Aliyah ta sanya hannu zata bud'e k'ofar amman kafin ta bud'e Aliyu ya sakar mata wata harara bashiri ta hakura kawai ta zubawa mijin nata ido yanda ya rikid'a ya koma mata wani daban kamar ba Aliyun ta ba.
"Aliyu, Aliyah, Suhaima, Sabeer ku bud'e k'ofar nan nasan kuna jin na"
Suka jiyo amon muryar Baba Adamu yana kwalla musu kira, Sabeer ne yayi kok'arin janye Suhaima daga jikin shi ya samu ya bud'e k'ofar, yana bud'e wa Baba Adamu da Babaa Lantana suka shigo bayan su kuma mahaifin su Aliyu ne yana dogara sanda.
Suna had'a ido da Suhaima ta wani saki k'ara mai rud'ewa wanda sauran kad'an ta wuntsila tsabar firgita da tsoran shi da sauri Sabeer ya taro ta ya rik'e ta k'am itama rik'eshi tashi sosai suka shige cikin gidan jikinta na 6ari don masifar tsoron shi take.
Daman tabarmar da suka karya akanta tana nan a shimfid'e zama suka yi dukkanin su ban da Suhaima da ta gudu d'aki tana kuka sai Yah Aliyu da yake tsaye ya kasa zama.
Tashi Sabeer yayi ya nufi d'akin ya tarar da Suhaima tana kwance a ruf da ciki tana kuka sosai, cikin sanyin jiki Sabeer ya k'arasa inda take ya zauna tare da janyota jikin shi ya d'orata saman k'afafun shi share mata hawayen face nata yake yi cikin sanyin murya yake rarrashin ta, dakyar ya samu tayi shiru sannan ya d'auko ruwa ya bata tasha, kad'an ta iya sha sannan yace
"Baby nah ki nutsu mu je, amman na rok'e ki kada kiyi kuka ji yanda idanun ki da fuskar ki suka yi ja gashi sun kumbura saboda kukan da kika yi"
Cikin sanyin jiki ta d'aga kanta alamar toh daga haka yaja hannunta suka fito zuwa tsakar gidan inda suke zaune jugum jugum kamar gidan makoki sautin kukan Baban su Suhaima ne kawai yake tashi, damk'e hannun Sabeer Suhaima tayi jikinta ya fara rawa don masifar tsoron Mahaifin ta take kallonta Sabeer yayi cikin zuciyar shi yana tunanin mai Mahaifin su yayi musu da har Suhaima take jin tsoron shi haka gashi ya karanto tsananin tsanar shi kan fuskar Aliyu da Suhaima.
Gefe suka samu suka zauna sannan Baba Adamu yayi gyaran murya tare da cewa
"Alhamdullilah dukkan godiya sun tabbata ga Allah subhanahu wata'ala da ya bamu aron rai har zuwa wannan lokacin da ya sanya ni ganin wai Umaru ne ya dawo gida"
Baba Adamu ya k'arasa maganar tashi cikin tsananin mamaki da jimamin yanayin da suka ganshi aciki, cikin sanyin murya da tsantsar nadama Baban su Aliyu yace
"Bani da bakin kare kaina a wajen ku don hak'ik'a na cika azzalumi mara imani kuma butulu a wajen iyalina, nayi nadama dana sani mara adadi nasan na cika mara tausayi wajen mata ta Fatima da yarana Aliyu da Suhaima, bansan ta inda zan fara neman gafarar ku ba ku tausaya min duk wani jin dad'i na rayuwa bana jin shi kuma nasan duk hakk'in ku ne ku yafe min 'ya'ya n........ "
Bai k'arasa fad'in maganar ba saboda wani kuka da ya kubce mishi na nadama, duk wajen shiru akayi ana sauraren shi sai da ya tsayar da kukan dakyar yace
"Ina Fatima ku kaini inda take na nemi yafiyar ta don Allah, Aliyu Suhaima ku yafe min ba don ni ba don girman Allah "
Baba Adamu ne yace
"Umaru sai dai kayi hak'uri amman Allah yayi wa Fatima rasuwa tun washegarin da ka tafi cikin ma dake jikinta shima ya rasu "
Neman mik'ewa yake amman jikin shi babu k'arfi ya k'asa tashi sai kawai ya fashe da kuka yana cewa
"Na shiga uku yanzu ya zanyi da d'unbin tarin hakk'in Fatima da yake kaina me yasa ma na tafi na barku Fatima ki yafe min "
Babaa Lantana tana zubar da hawaye tace
"Umaru ka godewa Allah kafin Fatima ta rasu ta yafe maka duk abin da kayi mata"
Kallon Babaa Lantana yayi tare da kura mata ido kamar yau ya fara ganin ta yace
"Da gaske kike Fatima ta yafe min? "
"Tabbas Umman mu ta yafe maka don ita ba macuciya bace kuma ba azzaluma bace ta kasance mai hak'uri da yafe wa mutanen da suka zalunce ta komai girman laifin da suka yi mata "
Cewar Aliyu kenan a fusace, matsowa kusa dashi yayi kan ya sanya hannun shi yana kok'arin rik'e Aliyu da sauri Aliyu yayi baya yana girgiza mishi kai tare da wurga mishi wani kallo yace
"Kada ka sake ka ta6a ni "
"Ka yafe min d'ana 'yata ki yafe ni "
Ya k'arasa maganar yana kallon Suhaima kauda kanta tayi daga kallon shi sai dai zuciyar ta ta fara rauni tausayin mahaifin nata ya fara shiga cikin zuciyar ta amman tana tsoron kallonshi balle tayi mishi magana.
"Haba Aliyu kada ka zama mutum mara yafiya, nasan ka da zuciya mai kyau kayi hak'uri ka yafe mishi mahaifin ka ne baka da kamar shi duk duniyar nan, Allah yana son masu yafiya idan an zalunce su, kayi duba ma da halin da yake ciki wannan kadai ma ya ishe shi "
Nan Baba Adamu da Babaa Lantana suka dunga yi musu nasiha tare da nuna musu mahimmanci mahaifi agare su koda wanne laifi ya aikata a wajen ka yana nan matsayin mahaifi ba'a ta6a canja shi k'addara ce da son zuciya suka rinjaye shi ya aikata hakan, nan Sabeer ma ya fara ya fara lalla6a su akan suyi hak'uri su yafe mishi haka Aunty Aliyah ma ta sanya baki akan maganar dakyar da sud'in goshi Aliyu da Suhaima suka yafe wa mahaifin su saboda ganin girman mutanen da suka sanya baki cikin maganar.
Yana kuka yana gode musu tare da sanya musu albarka Yah Aliyu dai tashi yayi kawai ya shiga d'aki baya tunanin ko makaranta zai iya zuwa yau wani abu ne yake nuk'urk'usar cikin zuciyar shi kwanciya yayi yak'i fitowa sai da yaji muryar Baba Adamu yana kira shi sannan ya fito idanun shi jawur ya samu waje ya zauna.
Cikin kuka Umaru ya fara basu tak'aitaccen labarin shi bayan barin shi gidan.....
"Tun da na d'auki jaka ta na tafi ban tsaya ko'ina ba sai cikin kaduna anan na tsaya cikin kasuwa ina buge buge na, na neman aiki ni ne dako da duk wani aikin k'arfi don kawai na samu kud'i na tara naji dad'in rayuwa ta,amman sai naga ko nayi aikin kud'in basa yi min albarka sai dai uban wahalar da nake sha da haka dai na samu dakyar na samu d'an rumfa ina siyar dasu kayan miya, ba laifi ina d'an ciniki akusa da inda rumfa ta take ne akwai wata mai siyar da abinci sunan ta Ladidi mai abinci 'yar duniya ce sosai awajen ta nake siyan abinci kullum, mun gaisuwar mutunci da ita gashi wani lokacin kyauta zata zuba min abinci ta aiko min shi har rumfata da haka muka d'auki tsayin lokaci ashe sona take sai daga baya take sanar min, da fari nak'i yarda ganin yanda idanun ta suke a bud'e sosai amman daga k'arshe ta shawo kaina na amince da ita, nan muka shirya yin aure nace mata banda iyaye ni maraya ne sai kawai na samu limamin unguwa ya zama wakili na ya d'aura mana aure daman agidan ta zamu zauna tun da tana da gida, farkon zaman namu munyi shi cikin kwanciyar hankali da jin dad'i amman da muka fara d'aukan shekaru komai ya canja ta fara yi min rashin mutunci kala kala na yau daban na gobe daban, gashi yanzu kasuwa taja baya d'an kayan miyar da nake siyarwa jarin ya karye mun cinye shi a abinci, daga nan fah wulak'anci take min kala kala har takai zaman gidan ya gagare ni saboda masifar ta duk wani hakk'i nawa na kanta bata sauke min na zama kamar matar ita mijin tunda ita take ciyar dani amman da sharad'in sai nayi mata aikace aikacen gidan ".
Kallon shi Yah Aliyu yayi ya tuna lokacin da Umman su idan bata gama abinci ba da wuri zagi kala kala zai yi mata har da duka kuma ya dunga ball da duk abin da ya ci karo dashi agidan yana kiranta k'azama abubuwa dai kala kala babu irin wanda bai yiwa Umman su ba lallai Allah ne ya nuna mishi ishara akan zaluntar su da yayi.
Ya cigaba da cewa
"Haka nake yi mata aikin don kawai ta ban abinci, gashi tana tara maza agidan musamman 'yan daudu, ashe Ladidi 'yar bariki ce ta k'arshe daga baya nake jin labari har shaye shaye take agabana babu abin da na isa nayi k'arshe sai ta ware min d'aki a zaure aciki nake kwana azaba da wahala nasha shi kala kala nayi bak'i na rame sosai nayi nadama sosai gashi kullum cikin mafarkin Fatima nake da yara na, ita kuwa Ladidi bata haihuwa kwata kwata gashi na rasa me ya sanya na zauna nake bauta mata duk zafin zuciya ta kuwa gaba d'aya nayi sanyi kamar ba ni ba ni kaina nasan Ladidi ba haka ta bar ni ba don tana bin malamai sosai, da haka muka kwashe shekaru da ita ina cikin wannan wahalar, nan na fara rashin lafiya sosai dakyar nake iya tashi amman ko kud'in da zan siyi magana ban dashi, daga k'arshe dai Ladidi ta kamu da cutar HIV ban san tana da ita sai kawai........ "
Wani kuka ne ya kubce mishi na tsananin bak'inciki da takaici, yayin da gaban Aliyu da Suhaima yayi mummunar fad'uwa kada Ladidi ta shafawa mahaifin su ciwon, kallon shi suke a tsorace don jin mai zai ce haka su Baba Adamu da Babaa Lantana, Aliyah da Sabeer suka tsorata suna addu'ar Allah ya sanya bata sanya mishi ba.
Cikin kukan ya cigaba da cewa
"Sai kawai ta yanke shawarar bazata mutu ita kadai ba sai ta goga min ciwon nata, bansan hawa ba ban san sauka ba wata rana kwatsam naga tana faman gyara gidan ta shirya lafiyayyen abinci ta kawo min amman ban iya ci ba saboda lokacin jikina babu sauk'i, na tashi zan shiga bandak'i ne naji tana magana da wata kawar ta a waya ashe abincin nan da ta kawo min duk sai da ta zuba musu jinin jikinta saboda yanzu ban da k'arfin da zan sauke mata buk'atar ta sai ta 6ullo ta wannan hanyar, ban k'arasa jin zancen ba na zube k'asa a sume don nayi matuk'ar kad'uwa da jin wannan maganar ta"
Wata ajiyar zuciya Aliyu da Suhaima tare da sauran mutanen wajen suka saki jin bata yi nasara akan shi ba lallai Ladidi ta cika macuciya kuma muguwa, share hawayen fuskar shi yayi kafin ya k'arasa da cewa
"Daga nan sa farkawa nayi naji ni agadon asibiti sai dai na had'u da lalurar shanyewar 6arin jiki wato paralyzed,nayi kuka nayi nadama sosai alokacin kullum cikin addu'a nake akan Allah kada ya d'auki rayuwata sai nazo na nemi yafiyar ku kullum da ku nake bacci nake tashi ina tsananin son naga na dawo wajen ku, naji ma ina jinya kafin na samu na 6arin jikina ya fara motsi da taimakon wannan liman d'in