Showing 39001 words to 42000 words out of 122360 words
Chapter 14 - A sanadin Son ki Hausa Novels Document complete by Aisha A Muhammad Sanaz.txt
but yanzu insha Allah zan cigaba da yi muku daidai iyawata, inason ku oll my fan's_❣
*PAGE 48-49*
Sai after mangarib Sabeer ya tashi daga wahalallen baccin da ya d'auke shi, lokacin da ya tashi zugin k'afar ya ragu babu laifi nan ya yunkura ya tashi bathroom ya shiga alwala yayi ya fito yana d'ingishi haka ya gabatar da sallahr la'asar da ta tsere mishi tare da mangarib, bayan ya idar ya zauna yin addu'o'in neman za6in Allah akan neman auren Suhaima, da haka har aka kirawo sallahr ishsha ya gabatar.
Bayan ya idar ne ya tashi ya shiga bathroom wanka yayi da ruwa mai d'umi kafin ya fito ya shirya cikin sleeping dress koma wa yayi ya kwanta a ringingine ya fad'a kogin tunani, ta yanda zai tunkari k'auyen su Suhaima don neman soyayyar ta, yana cikin haka 'yan uwan shi da k'annen Daddy da kuma matansu suka shigo duba Sabeer, dakyar ya iya k'ak'alo yak'en dole ya sanya saman fuskar shi yana amsa musu sannun da suke mishi, kowanne fuskar shi da tausayin Sabeer ganin yanda k'afar shi ta kumbura sai wurin 9 na dare suka bar bedroom d'in nashi wanda har zuwa lokacin ba ga Mumyn shi ba da Hajjah.
Bayan fitar su babu dad'e wa Daddy ya shigo bedroom d'in bayan shi kuma 'yar aikin Mumy ce da babban plate a hannun ta saman shi cike da kaya ajiyewa tayi saman k'aramin table d'in d'akin sannan tayi wa Sabeer sannu da jiki ko amsawa bai yi ba ta fita don shi ba wannan ne a gaban shi ba.
"Son ya kake jin jikin naka?"
D'an yatsina fuska yayi kafin yace
"Daddy na samu sauk'i"
D'an ajiyar zuciya Daddy ya saki tare da cewa
"Allahmdullilah Son naji dad'in abin da ka ce, oya zo kaci abinci nasan rabon ka da abinci tun breakfast da kayi "
Girgiza kai Sabeer yayi tare da cewa
"Na k'oshi Daddy"
D'an zaro ido yayi tare da cewa
"What! Son kanason illata kanka ne? "
Sai kuma ya sassauta murya cikin sigar rarrashi yace
"Haba Son tun da na amince da buk'atar ka ya kamata kaci wani abin zan jure duk wata matsala da zan fuskanta a wurin Abba, Hajjah da kuma Mumyn ka duk don farincikin ka ".
Kallon Daddy yayi sai yaga kamar ya fad'a a fuskar shi wani tausayin Daddy ne ya kama Sabeer har yana kok'arin fitar da kwalla duk don farincikin shi Daddy ya zama haka, yasan yanda bai ci wani abincin kirki ba yinin yau haka shima ya zauna.
Tashi tsaye Sabeer yake kok'arin yi da sauri Daddy ya taimaka mishi ya tashi tsaye zuwa saman kujera wanda kujeru guda biyu ne kacal daga gefe tsakiyar su kuma table ne nan Daddy ya zaunar da Sabeer a d'aya daga cikin kujerar, sannan shima ya zauna a baki ya fara baiwa Sabeer abinci haka shima Sabeer yake bawa Daddyn shi a baki.
Bayan sun kammala ci ne Daddy ya lalla6a Sabeer yasha maganin shi don sam baya k'aunar shan magani, k'ofar bedroom d'in aka bud'e aka shigo kallo d'aya Sabeer yayi mata ya d'auke kanshi gaban shi yana fad'uwa, Mumy ce ta shigo fuskar ta a had'e babu alamar fara'a bata yiwa kowa magana ba ta wuce bathroom babu dad'ewa ta fito hannun ta rik'e da wani d'an madaidaicin bowl ruwan d'umi ne a cikin shi sai wani small towel a hannun ta.
Inda Sabeer yake ta nufa tana zuwa ta zauna kan carpet tare da d'aukan k'afar Sabeer mai ciwon ta d'ora saman k'afar ta, towel d'in ta sanya cikin ruwan d'umin ta fara gasa k'afar Sabeer, daga Sabeer har Daddyn babu wanda ya samu fuska wajen Mumy balle su yi mata magana, runtse ido Sabeer yayi wani rad'ad'i da zafi yana shiga cikin zuciyar shi gefe d'aya na cikin zuciyar shi kuma yana tunanin hanyar da zai bi ya shawo kan Mumyn shi ta hak'ura ta kar6i Suhaima matsayin surukar ta.
Bayan ta gama gasa mishi k'afar ne ta d'auko wani cream ta shafa mishi a k'afar sannan ta sauke ta a hankali daga kan k'afar ta kafin ta yunkura ta mik'e tsaye ta kwashe kayayyakin da tayi amfani dasu zata wuce kenan.
"Mumy! "
Taji saukar muryar d'an nata mafi soyuwa cikin zuciyar ta, runtse ido tayi wasu hawaye na kok'arin zubo mata amman sai ta had'iye su ta wuce toilet da sauri ta ajiye bowl d'in da towel kafin ta fito tabar d'akin da sauri.
"Kada kayi kuka Son zan rarrashi Mumyn ka"
"Daddy Mumy tana fushi da ni "
Cikin rarrashi Daddy yace "Mumyn ka bazata iya fushi da d'anta ba abin da yake sone baiyi mata shi yasanya ta 6acin rai but nasan zata huce bazata iya jure fushi da yaron ta ba kamar yanda nima na kasa jurewa"
Gid'a kai Sabeer yayi kawai, suna cikin haka Alhj Ahmad d'an fillo ya shigo d'akin sannu yake yiwa Sabeer amman bai kalli inda yake ba da yaga yana kok'arin ta6a shi ma sai ya tashi yana d'ingishi ya bud'e kofar baya ya fita ko kallon shi bai yi ba.
Da kallo duk suka bishi na mamaki kafin Alhj Ahmad ya zauna yana goge gumi na tashin hankali yace
"Hussein anya yarinyar nan ba asiri tayiwa Sabeer ba? "
D'an murmishi Daddy yayi kafin yace
"Abba ba wani asiri asali ma yarinyar bata son shi "
D'an zaro ido Alhj Ahmad yayi kafin yace
"Batason shi kamar yaya? Kana nufin Sabeer ne kawai yake son ta? "
"Ehh Abba so yake yaje neman soyayyar ta "
Cire hular kanshi d'an fillo yayi yana firfita da ita don wani gumi da ya keto mishi na tashin hankali, daman ashe Sabeer son maso wani yake wanda ake ce mishi k'oshin wahala innallahi, tuni jikin Alhj Ahmad yayi mugun sanyi da yaji jarrabar da Allah ya d'orawa jikan shi na son maso wani gashi yarinyar 'yar k'auye shi yanzu mene mafita?.
Shiru suka yi gaba d'aya babu mai yin magana a tsakanin su har wurin 10:30 suna zaune jigum jigum suna jiran shigowar Sabeer amman bai shigo ba haka suka tashi suka bar bedroom d'in kowanne zuciyar shi cike da tunani kala kala.
Wasa wasa yanzu gaba d'aya Sabeer baya kula Alhj Ahmad d'an fillo da Hajjah, Daddy kawai yake kulawa kawai Mumy kuma bata shiga harkar shi sai dai zata zo ta gasa mishi k'afa sau biyu ta sanya mishi magani, tsakanin ita da Sabeer bansan wanda yafi wani ramewa ba a tsakanin su, ta 6angaren Daddy kuma yana ta kok'arin shawo kan Mumy ta amince don samin farincikin tilon d'an su amma tak'i yarda da maganar tashi ko baccin kirki bata iyayi saboda tunanin tilon d'anta ta rasa samun mafita don mafitar ta d'aya ta bari Sabeer auren Suhaima kuma sam abin da bazai ta6a yiwu ba.
Alhj Ahmad d'an fillo kuwa ya rasa samun sukuni don Sabeer bayayi mishi koda shi yayi mishi magana bazai kalli inda yake ba balle ya amsa mishi k'arshe ma sai Sabeer ya bar mishi wurin, duk yanda ya so Sabeer ya saurare shi yak'i bashi had'in kai da wani cikin jikokin shi da tuni yayi watsi da al'amarin amman Sabeer kuwa na daban ne son shi cikin zuciyar shi mara adadi ne, tun kafin a haifi Sabeer yake nuna wa cikin so har aka haife shi a kullum son Sabeer k'ara yawa yake cikin zuciyar shi.
Duk yabi ya rame ya fad'a ga mafarkin da yake da Sabeer da wata kyakkyawar yarinya duk mafarkin da zai yi da wannan yarinyar yake ganin su da Sabeer, gashi Sabeer yana kuka yana rok'an ta da ta so shi amman sai tayi tafiyar ta, gaba d'aya d'an fillo ya hankalin shi a matuk'ar tase yake don ganin irin mafarkin da yake.
A haka aka d'ibi sati biyu cikin wannan yanayin alokacin Sabeer k'afar shi ta warke sosai duk babu kumburin ya koma tafiyar shi normal babu d'ingishi, har zuwa lokacin Mumy bata yi magana ba Daddy kullum cikin lalla6a ta yake.
"Daddy tun da na warke kayi min izinin tafiya wajen Suhaima "
Sabeer ya fad'i hakan cikin marairaice fuska, d'an shiru Daddy yayi yana tunani don rasa ta inda zai fahimtar da Sabeer cewa Mumyn shi bata amince da hakan ba da kuma Abbah da Hajjah, yana shirin bud'e baki yayi magana yaji ance
"Hussein basai kayi tunani ba ni na bawa Sabeer izinin tafiya wajen masoyiyar shi neman soyayyar ta na amince Sabeer ya tafi domin samun farincikin shi "
Da sauri suka jiyo suna kallon D'an fillo a tsaye yana murmishi daga ni na yak'e ne ba'a son ranshi ya fad'i hakan ba, ba har cikin zuciyar shi ya furta hakan ba amman Sabeer da Daddy saboda farinciki sam basu d'ago shi ba, da gudu Sabeer yaje ya rungume D'an fillo yana dariyar farinciki wata ajiyar zuciya ta kwanciyar hankali D'an fillo ya sauke jin Sabeer rungume dashi yaushe rabon da Sabeer ya rungume shi, yaushe rabon da yaga dariyar shi haka duk so ya canja shi tamkar ba Sabeer d'in da ya sani ba.
"Thank U so much kakanah! "
Ya k'arasa fad'i yana bashi peck a kumatun shi, dad'i ya ishi D'an fillo jin Sabeer d'in shi cikin farinciki kamo hannun shi yayi ya rik'e tare da cewa
"Ka yafe min marin da nayi maka Sabeer nayi regretting akan haka"
Girgiza kai Sabeer yayi yana murmushi yace
"Kada ka damu Abbah ya wuce "
Sake rungume Sabeer yayi yana bubbuga bayan shi.
"Ni an mance da ni da.... "
Daddy ya k'arasa maganar da hannun shi na alamar shima ayi hugging nashi, da sauri d'an fillo ya janyo shi ya had'asu ya rungume su acikin jikin shi.
Sun jima a haka kafin su rabu da juna nan Sabeer ya mak'ale jikin D'an fillo yana zuba mishi shagwa6a son ranshi shi kuma yana lalla6a shi, dariyar yak'e kawai D'an fillo yake yi, sun jima suna hira kafin kowa ya tafi ya kwanta zuciyar Sabeer fal farinciki a wannan daren yayi baccin da ya jima bai yi ba.
Washe gari da safe ya tashi saboda d'oki da kanshi yake had'a kayan shi cikin trolley bags nashi saboda zumud'i saboda a yau yake son tafiya zuwa k'auyen su Suhaima ya fara fayyace mata abin da yake damun shi.
Bayan ya gama had'a kayan ne ya d'auki phone nashi ya kirawo Jiddah maganar mintuna biyar yayi da ita ya kashe wayar, saboda tsananin mamaki Jiddah kusan sumen zaune tayi na jin inda Sabeer yake neman address a wurin ta na gidan su Suhaima, tura mishi tayi ta message saboda ita ma sauri take a yau jirgin su zai tashi zuwa yawan honeymoon wanda gama wayar ta da Suhaima kenan Sabeer ya kirawo ta kanta ya d'aure sosai amman ta bar komai sai sun dawo tukunna.
Zaune Sabeer yake durk'ushe gaban Mumy cikin bedroom nata, gwiwar shi a k'asa ya sanya hannun shi saman k'afar ta idanun shi hawaye ne yake fitar wa, gama shiryawar shi kenan zai tafi ya shigo bedroom d'in ta cikin rawar murya ta kuka yace
"Mumy nah! Ki yafe min kisa min albarka tare da yi min addu'ar samun nasara tafiya da fushin ki ba k'aramin barazana zai zame min ba"
Juyar da kanta gefe tana share hawayen fuskar ta, Daddy da shigowar shi kenan shima yabi sahun yanda Sabeer yayi yana cewa
"Sweetheart kiyi hak'uri ba laifin Sabeer ba ne so ne kiyi mishi fatan samun nasara please "
Jiyowa tayi ta kalli Sabeer da Daddy da suke durk'ushe a gaban ta wani kwarjini da cika ido d'a da uban suka yi mata ta rasa me zata ce bakin ta yayi mata nauyi ta kasa bud'e shi tayi magana.
Rarrashin ta da lalla6awa Daddy ya dunga yi wa Mumy sun dad'e a haka kafin Sabeer cikin dashashshiyar murya yace
"Mumy ki taimaka wa rayuwata please kada na mutu"
Kallon shi tayi da sauri gaban ta yana fad'uwa idanun shi sun yi ja suna fitar da hawaye, "please Mumy nah! "
Ya fad'a can k'asan mak'oshi, Mumy ta gaji da jin wannan maganar a wurin Sabeer ta gaji da ganin fitar hawaye a idanun d'anta, hannun ta yana rawa kamar mai jin tsoron ta6a abu ta d'ora hannunta saman gashin kan Sabeer tace
"Ka tafi Sabeer kaje Allah ya kare min kai "
Basu yi tsammanin jin wannan maganar a bakin ta ba don haka sai suka tsaya suna kallonta kamar was7 sokaye, d'an murmishin yak'e tayi hawaye na fita a idanun ta tace
"Ka tafi kada yamma tayi maka ka kula da kanka "
Rungume ta yayi cikin farinciki shi da Daddy suna zuba godiya kafin Daddy ya rik'o hannun ta zuwa compound d'in gidan Sabeer na rik'e da d'ayan hannun Mumyn, gaba d'aya family na D'an fillo sun fito suna sallama da Sabeer, sai da Sabeer ya bisu one by one yana rungume na sallama, sannan daga k'arshe driver ya bud'e mishi kofa ya shiga mota idanun shi akan iyayen shi yana kallon yanda Mumy ta fad'a jikin Daddy tana kuka.
Kauda kanshi yayi suna nan tsaye driver yaja motar suka fita daga gidan, kowa yana mamakin saukowar Alhj Ahmad d'an fillo har ya amince da buk'atar Sabeer wasu sun tausayawa Sabeer don sunsan Sabeer bazai jure zaman k'auye ba yayin da wasu kuma suka cika da farinciki daman a rayuwa dole ka samu mai tausaya maka idan kana cikin damuwa wasu kuma a lokacin zasu yi farinciki da ganin ka cikin haka.....
Hmmm fan's ya kuka ga wannan page d'in?
Anya Mumy da D'an fillo da Hajjah har cikin zuciyar su suka aminta da tafiyar Sabeer kuwa?.
Sai ku biyo ni next chapter don jin yanda zaman shagwa6a66en nan zai kasance cikin karkarar k'auye koya zata kasance?
Aishat A Muh'd ✍🏻
*A SANADIN SON KI*
Written by
Aishat A Muh'd
EXCLUSIVE WRITER'S FORUM
Dedicated to my Sadeey SaNaz
Ina kike Khadijah Neenah cool wannan shafin naki ne kyauta na murnar taya ki kammala littafin ki mai suna WASU MAZAN.. Hak'ik'a kin fad'akar damu ya kuma nishad'antar Allah ya k'ara basirah da k'arfin ido, ina miki fatan Alkhairi! ❣
PAGE 49-50
Bayan tafiyar Sabeer Mumy kasa danne kukan ta tayi da gudu ta wuce side d'in su bedroom ta shige ta hau kuka sosai na tausayin halin da Sabeer zai shiga da kuma kukan takaici da bak'in ciki akan wata banza 'yar k'auye d'anta kamar Sabeer zai tafi neman soyayyar ta.
Da haka Daddy ya shigo ya fara rarrashin ta bayan ya janyo ta jikin shi, dakyar ta shiru tana sauke ajiyar zuciya, sai da Daddy yaga tayi bacci sannan ya kwantar da ita ya fita duk jinshi yake babu dad'i na tafiyar Sabeer.
Daddy yana fita daga bedroom d'in Mumy ta bud'e idanunta tare da sakkowa daga saman bed dama tayi hakan ne don Daddy ya fita ya bata waje, tana son ta samu nutsuwar da zatayi tunani na d'aukan mataki akan shegiyar yarinyar nan da zuri'ar ta don sam bazata ta6a amince wa Sabeer ya auro mata d'iyar talakawa ba, talakawan ma na k'auye wanda basusan komai ba sai nemo da kiwo inaaa abin da bazai ta6a yiwuwa ba, daman ta barshi ne don kafin ace za'a yi auren tasamu mafita haka ta tsunduma a tunani sosai na samun mafita kuma bazata yi abin da Sabeer da Daddyn shi zasu zargeta da hana wannan auren ba.
***** ***** *****
Suna tafiya a mota Sabeer kuma ya kwanta tare da tukunkune jikin shi waje d'aya tamkar mai jin bacci, hawaye ne suke fita a idon shi yana kewar iyayen shi yana kuma tunanin yanda zaman shi anan zai kasance shin Suhaima zata kar6e shi matsayin masoyin ta sannan ya 'yan uwanta zasu kar6e shi matsayin mai son 'yarsu, wannan tunanin shi yake dad'a dagula lissafin Sabeer kada su kore shi su hanashi Suhaima tsoron shi d'aya kada su hanashi neman soyayyar Suhaima.
Sai da driver yazo wurin da suka ta6a had'uwa da Suhaima anan Sabeer ya bashi umarnin tsayawa, bayan yayi parking ne sosai Sabeer ya tsaya yana kallon wurin yana tuna wani al'amari da ya ta6a faruwa a wajen har wani murmishi ne ya su6uce mishi.
Nan Sabeer ya yiwa driver magana akan ya fito mishi da kayan shi, bayan driver ya fito dashi ne nan Sabeer yace mishi ya koma gida, yana nan tsaye driver yaja motar ya tafi zuciyar shi fal tausayin Sabeer don yasan bazai ta6a iya zaman wannan k'auyen mai kama da daji ba nan cikin zuciyar shi yayi mishi addu'ar fatan dacewa.
Sabeer ya d'an jima a wajen yana dad'a nazarin wajen gaban shi na fad'uwa saboda ganin garin ya fara d'an duhu don dab ake da akirawo sallahr mangarib.
Wani d'an saurayi ne yazo zai shige Sabeer ya rasa ta yaya zai mishi magana da yaga yana kok'arin wuce shi ne yasa shi yin kar6in hali yace
"Assalamu Alaikum"
D'an jiyowa yayi ya kalli Sabeer kafin ya tsaya nesa kad'an dashi yace
"Waalaikumussalam "
"Ammm inason zan yi mata tambaya please "
Saurayin cikin mamaki ya ke kallon shi don bai zaci Sabeer yana jin hausa ba ya d'auka bature ne ko balarabe yazo yin wani abin a k'auyen nasu.
"Allah yasa na sani"
D'an sauke numfashi Sabeer yayi tare da cewa
"Don Allah ko kasan gidan wani uhm... "
Ya d'an yi shiru kad'an yana tuna sunan Yayan Suhaima da Jiddah ta sanar dashi d'an murmishi ya saki tare da ya tuna sunan yace
"Yawwa sunan shi Aliyu yana da k'anwa Suhaima kuma manomi ne "
D'an murmishi saurayin yayi kafin yace
"Na gane shi