Showing 72001 words to 75000 words out of 122360 words

Chapter 25 - A sanadin Son ki Hausa Novels Document complete by Aisha A Muhammad Sanaz.txt

perfumes d'in da akayi amfani dashi, tana tafiyar ta a nutse yayi da wasu kawayen ta biyu suke rik'e da karshen gown d'in ta inda yake jan k'asa suka nufi motar da ango yake, suma friends nata biyar sun sha gayun su cikin wani material pink da blue sun yi kyau kam ba laifi, Jiddah ma ta shirya cikin wata gown ta material pink colour tayi kyau itama hannun ta yana rik'e dana mijinta Khaleel shima yayi kyau cikin wata lallausar shadda fara.




Tun da suka taho Sabeer ya saki baki da hanci yana kallon Babyn shi yanda ta koma tamkar ba ita ba, duk da yasan Babyn shi mai kyau ce ko batayi kwalliya but wannan kyan da tayi na daban ne har baisan lokacin da ta shigo motar ba sai jin daddad'an k'amshin turaren ta cikin hancin sh.


Wata ajiyar zuciya ya sauke mai d'an k'arfi baisan lokacin da ya rik'o hannun ta ba d'aya ya d'ago fuskarta da d'ayan hannun yana mata wani irin kallo da eyes nashi wanda suke a wani lumshe lumshe, bakin shi yakai saman goshin ta yayi kissing d'in shi sannan ya cika fuskar ta yana cewa


"Masha Allah "
Abin da ya fad'a kenan a lokacin da suka bar harabar gidan Jiddah but still hannun shi yana cikin nata yana wani irin murza su a hankali, ita kuma Suhaima kunya ce ta kama ta sosai ganin abin da Sabeer yayi mata wanda bai ta6a kwatanta yi mata sai yanzu kuma tasan kwalliyar tace ta burgeshi sosai.




Sabeer bakin shi yayi mishi nauyi ya kasa magana saboda wani irin abu da yake ji yana ratsa shi a cikin kowanne lungu da sako na jikin shi, da haka suka k'arasa wajen da za'a gabatar da dinner d'in kallon ta yake tamkar yau ya fara ganin ta.


A d'an sace Suhaima ta kalle shi yasha wata shadda milk colour mai d'an duhu milk d'in sai aikin jikin rigar brown zare akayi amfani dashi har da babbar riga karo na farko kenan da Suhaima taga Sabeer cikin shigar manyan kaya sai taga yayi mata kyau ya k'ara mata wani girma da kwarjini a idanun ta har da hula milk and brown ne kai Sabeer ya had'u kawai ta ko'ina gaskiya Suhaima tayi dacen miji haka shima yayi dacen mata sun dace da junan su sosai.




Motar su tana k'arasa wa wajen tayi parking but basu fito ba suna zaune aciki, sai da Jiddah suka k'araso sannan suka fito hannun su na sark'e waje d'aya suna gaba Jiddah da Khaleel, Musaddiq da Mufidah a bayan su sai kuma friends na Suhaima su biyar d'in nan a bayan su.


Wajen yasha decoration na peach, red, pink and white ko'ina sai kyalkyali yake ga mutane duk an zazzau suna zaman jiran shigowar ango da amarya wani slow music ke tashi na wakar india ta Piya O Re Piya Tere....., itace ke tashi a wurin suna shigowa kallo ya dawo kansu sai fesa musu wani spray mai kyalkyali ga wasu furanni farare da ja da ake watsa musu a jikin su har suka k'arasa inda zasu zauna wata kujera ce d'aya mai d'an fad'i da zasu zauna daga bayan su kuwa wani k'aton frame ne yasha decoration an rubuta anyi zanen heart sai aka rubuta S-S ajiki wato Suhaima and Sabeer.


Bayan an zazzauna ne kuma Jiddah ta bud'e taron wajen da addu'a sannan ta bayar da tak'aitaccen tarihin amarya da harshen turanci bayan ta gama Musaddiq ma ya tashi cikin tafiyar kasaita Mufidahn shi mak'ale dashi yaje shima ya bayar da tak'aitaccen tarihin ango Sabeer sannan kuma akan nemi ango da amarya su fito su d'an taka rawa.




Suna tsaye wajen da aka tanada don yin rawa hannun Sabeer d'aya zagaye da kugun Suhaima d'ayan hannun kuma yana rik'e da d'ayan hannun ta ita kuma hannun ta yana zube saman kafad'un shi da haka suke d'an jujjuyawa don babu wanda ya iya wata rawa acikin su, sun birge mutane sosai yana mata magana kasa k'asa saitin kunnen ta bayyana mata irin tarin son da yake mata yake yi.


Jiddah ce da Khaleel suka fara zuwa wajen suka fara yi musu lik'i nan Musaddiq da Mufidah suka taso suma daga nan sauran mutane suka fara yi musu lik'i, can na hango My Biebie dee, my Sadeey, Ummu Safwan, Zahra da sauran fan's suna faman lik'a musu 'yan five five a kunyace suke yi saboda babu mai lik'a k'asa da five hundred sai su lol 😂.




Nan daidai aka cigaba da gudanar da dinner har zuwa lokacin da za'a yanka cake, Sabeer na rik'e da Babyn shi suka k'arasa wajen cake d'in wanda ya kasance hawa 5 ne yasha decoration sosai na white da peach, Suhaima ta rik'e knife na yanka wa Sabeer ya d'ora hannun shi saman nata nan suka yanka sannan Suhaima ta gutsuro cake d'in sai da ta d'an russuna k'asa sannan ta sanya mishi abaki a d'an kunyace tayi hakan tana yin murmishi.


Shima Sabeer murmishin yake kafin ya sanya hannun shi ya d'ago ta tsaye tukunna ya d'an rungume ta a jikin shi ya bata cake d'in da d'an juice a cup daga k'arshe ya bita da kissing a cheek d'in ta sai d'an ihun birgewa mutane ke yi suna yi musu tafi daga haka suka koma wajen zaman su.




Sannan aka fara ciye ciyen abubuwan ci da sha wanda aka shirya su na alfarma, Sabeer ne ya kallo Babyn shi cikin wani salon kallo yace
"Baby nah i luv U, i really luv U bazan iya rayuwa babu ke ba ina fatan addu'ar Allah ya bar min ke har iyakar tsayin rayuwa ta "


D'an murmishi Suhaima tayi kawai, hannun ta ya rik'o wanda ke rik'e da cup da juice aciki ya kai bakin shi ya d'an kur6a kad'an kafin yace
"Baby baki ce komai ba fah, yanzu gobe kamar haka na zama ke kin zama ni babu zancen jin kunya kuma, kodan ma kunyar bin ta zanyi duk inda take na cire ta ko ba haka ba amarya ta? "


Kamar k'asa ta tsage Suhaima ta shige haka take ji lallai Sabeer ya fitsare da yawa, yanzu ma yana mata haka balle gobe an d'aura musu aure sai kuma abin da yafi haka nan taji gaban ta ya fad'i, yana kokarin sake magana Musaddiq ya k'araso yana cewa
"Ango kazo ayi pic's don dare nayi my wife ta gajiya zamu tafi gida"


Tashi suka yi nan aka fara d'aukan picture's sosai da mutane, nan na d'an kutsa na samu aka d'auke mu pic's da ango da amarya sannan na samu wani table na zauna a gajiye nake lik'is, d'an waigawar da zanyi ba sai na hango su My Sadeey, My Biebie dee, Zahra, Ummu Safwan ana faman kiciniya da cinyoyin kaji bakunan su yayi dumu dumu da maik'o amman basu san da hakan ba, wani huci na saki mai zafi ganin zasu sanya ni jin kunya idan aka tambaye ni wadannan wane ya gayyace su idan aka nuna ni dole naji kunya kuwa don haka harara na dalla musu sannan na d'auke kai na lol🤣😂, gaskiya naji dad'i sosai ganin yanda fan's na ASANANDIN SON KI sunyi k'arar zuwa wannan bikin na Sabeer da Suhaima mun sha hira dasu sosai gashi har da ankon su na daban suka yi daga k'arshe muka yi sallama dasu don ni bayan amarya zan bi don na cigaba da d'auko muku rahoto yanda zata kasance nayi musu fatan komawa gida lafiya.




Sai wurin 12am na dare aka tashi daga wannan dinner d'in Jiddah tayi tayi da Sabeer yabar Suhaima su tafi gida tare ya 6ata rai tare da cewa
"Ke ni fah kin dame ni Jiddah ranki zai 6aci cinye ta zanyi kome, nace zan kawo ta har gida? "
Zum6ura baki Jiddah tayi had'e da cewa
"Toh gaakiya kada ku dad'e sannan ayi ahankali ba'a d'aura ba don naga rawar kanka ta fiye yawa"
Fad'in Jiddah tana tafiya tana maganar k'asa k'asa kamar gunguni don bai ma ji k'arshen maganar ta ba.


Sai wajen 12:40 na dare Sabeer da Suhaima suka taho don sai da ya gama sallama da friends nashi da suka zo tukunna suka taho, driver yana parking Suhaima ta sanya hannu zata bud'e k'ofar ne da sauri Sabeer ya rik'o hannun nata yana cewa
"Baby wai har tafiya baki jira mun yi sallama ba? "
Tana lumshe ido tace
"Bacci nake ji Sabeer wallahi gashi na gaji "
Ta k'arasa maganar tamkar zata fashe da kuka, d'an murmishi yayi sannan yace
"Baby sarkin raki huh, bari na kyale ki don nasan kin gajin "


Kissing d'in bayan hannun ta yayi sannan ya bud'e motar ya fito ya zagayo ya bud'e mata hannun ta ya kamo suka fito har zuwa k'ofar shiga parlourn gidan Jiddah, knocking yayi sau d'aya kamar wanda ake jikin k'ofa ana jira aka bud'e da sauri.


D'ago kanshi yayi ya watsa wa Jiddah harara don yasan itace zatayi hakan, dariyar da ke neman kubce mata ta had'iye tare da cewa
"Ni me nayi Yaya kuma kake harara ta? "
"Bansani ba "
Juyowa yayi ya kalli Suhaima yace
"Baby kiyi bacci sosai gobe karfe 8 na safe zan aiko driver ya mayar daku gida "
Ya k'arasa fad'i yana kissing goshin ta, d'an waro idon Jiddah tayi cikin tsokana tace
"Yaya agabana koh? "
Harara ya sake watsa mata sannan ya wuce Jiddah ta tuntsire da dariya sannan ta kama hannun Suhaima suka wuce ciki.


Washe gari da safe wajen 8 na safe Suhaima, Jiddah da sauran friends nata suka taho k'auyen su Suhaima, friends na Suhaima jiya sun ga abin da basu ta6a gani ba sai jin labari sun rud'e sosai da ganin wannan dinner da akayi lallai kud'i suna wajen masu shi kowacce cikin su tana fatan Allah yasa ta a danshin Suhaima.


Sai wurin 11am suka isa nan suka tarar gidan ya cika da 'yan uwa da abokanan arzik'i, suna gaisawa da en uwa tukunna suka tafi gidan Babaa Lantana can suka nufa, shima ba zama suka yi ba sai shirye shiryen walimah suke yi don kafin a d'aura aure zasu yi don ana gama d'aurin zuwa la'asar za'a tafi kai Suhaima gidan ta.


Daman sun gama tsara inda za'a yi har malamar da zata yi lecture sun gayyato, don haka gyara wajen akayi aka shirya ko'ina yayi kyau sosai, zuwa karfe 12 mutane sun zo sosai har shahararriyar malaman nan My Momma Aunty Maijiddah tazo tare da tawagar ta don haka babu 6ata lokaci su Jiddah su zo wajen tare da amarya Suhaima tana sanye cikin wani ash da pink colour lace sai ta d'ora alkabba ash mai adon flower's pink da sliver ajiki tayi kyau sosai sai zuba k'amshi take zaunar da ita suka yi kan kujerar sannan kowa ya samu waje ya zauna.




Sannan Momma ta fara da bud'e taro da addu'a kafin ta shiga yiwa amarya nasiha da shawarwari na zaman gidan aure, hak'uri, biyyaya, iya tsabta, kwalliya da tattalin miji kowanne sai da ta d'auke su tare da yin bayanin su sosai, taja hankalin mata sosai akan kishiya da zuwa wajen boka, kaiii gaskiya My Momma ba k'aramin nasiha da shawarwari ta bawa mutane ba don ba iya Suhaima bama har wad'anda suka halacci wajen sun k'aru sosai daga k'arshe aka yi aka sha tare da yin kyautittaka ga duk wad'anda suka zo karfe 1 aka tashi daga walimar kowa ya watse.




Bayan an sako daga masallacin juma'a ne aka d'aura auren Suhaima Omar and Sabeer Hussein Ahmad d'an fillo akan sadaki mafi neman albarka aure ansha pics sosai tare da rabon kud'i don family d'in D'an fillo ba k'aramin bajinta suka yi ba, bayan an gama d'aura auren ne aka tafi yin walima ta maza wanda Dr Ahmad d'an fillo ya shirya don farincikin Sabeer.


"Hello! Mata ta! "
Cewar ango Sabeer kenan, shiru Suhaima tayi don gaba d'aya tun lokacin da aka d'aura auren jikin ta yayi sanyi sosai.
"Baby nah yau ina matuk'ar farinciki wanda ban ta6a kasancewa acikin shi ba, yau ni Sabeer Suhaima ta zama mata ta ji nake kamar a mafarki ina godiya ga Allah da ya nuna min wannan ranar, anjima kad'an za'a zo d'auko min ke wanne tanadi kika yi mana Baby a wannan daren? "
Kittt ta katse wayar nata, dariya Sabeer yayi don yasan kunya ce ta sanya ta hakan d'an lumshe idon shi yayi yau zuciyar shi fes yake jin ta wata k'aunar Suhaima ce take k'ara shiga cikin zuciyar shi.


Suhaima tana kashe wayar kawai sai ta fashe da kuka wanda na kasa tantance kukan me take, Jiddah ce ta rarrashe ta sannan ta kama hannun ta suka tafi can gidan Yaya Aliyu, anan Aunty Aliya da Yaya Aliyu, Babaa Lantana suka yiwa Suhaima nasiha mai ratsa jiki sosai kafin 'yan uwa su zo suyi mata kowa idan zai mata nasiha sai ya ambaci kalmar hak'uri.




Daga nan suka dawo gidan Babaa Lantana wanka Suhaima take amman kuka take har ta fito ta shirya cikin wani maroon lace da touch na silver ajiki d'inkin riga da siket ne sun yi mata kyau sosai, dakyar Jiddah ta rarrashe ta tayi mata makeup sannan ta nad'a mata laffaya bak'a mai kyalkyalin silver ajiki sai shoes black da purse black ita ma suna cikin shirin ma motocin d'aukan amarya suka k'araso.


Kuka Suhaima take sosai tana rungume da Aunty Aliyah da Yaya Aliyu dakyar aka 6an6are ta daga jikin su tana kuka aka sanya ta mota shima Yah Aliyu sai da yayi hawaye Aunty Aliyah kuwa kuka ta fashe da shi sosai suna kallo har aka tafi da Suhaima, da gudu Aunty Aliya ta shige cikin gida tana kuka nan Yah Aliyu ya bita yana rarrashin ta don gaba d'aya mutane sun wuce kai Suhaima.




Aljannar duniya abin da nace kenan don ganin tsararren gidan da Sabeer ya gina, kaiii tsayawa ba fad'in had'uwar gidan 6ata lokaci ne mai karatu kawai kayi hasashe da kanka, kud'i sunyi kuka a wajen ginin gidan, nan mutane suka fara santin gidan tun daga farfajiyar gidan, da suka shiga cikin gidan kuwa sakin baki da hanci suka yi suna kallo.


Jiddah bata bari an shiga bedroom d'in Suhaima na ainahi ba don kuwa tsarin da tayi mishi sai amarya da angon ne zasu shiga, da yake bedrooms biyu ne na Suhaima sai aka wuce da ita d'ayan Babaa Lantana ce rik'e da hannun ta zaunar da ita tayi kan bed kafin kuma a fara fita daga d'akin zuwa kallon yanayin tsarin gidan.




Sai bayan mangarib aka tafi mayar da mutane Suhaima k'ank'ame Babaa Lantana tayi tak'i cikata sai dakyar aka kwaci Babaa Lantana don ba k'aramin riko Suhaima tayi mata ba, Jiddah ce ta rik'e ta tana rarrashin ta yayin da su kuma suka tafi Babaa Lantana har da goge hawayen ta na kewar Suhaima.




Gidan sai yayi tsit daga Jiddah sai friends na Suhaima gyaran gidan suka yi suna gama gyarawa kowacce ta fara shirin tafiya dinner na family d'in D'an fillo, Jiddah ta sanya Suhaima tayi wanka ta bata wata white gown ta material har k'asa take ja sosai sai adon flower's silver ajiki, dakyar ta tsayar da hawayen idon ta aka yi mata makeup sannan aka nad'amata net white akanta sai hill shoes and purse white sai d'igon silver ajikin su, sunyi mata kyau sosai kayan different perfumes Jiddah ta fesa mata kafin ta rik'o hannun ta suka fito zuwa compound na gidan.




Suhaima na shiga cikin motar tun kafin Jiddah ta rufe murfin motar Sabeer ya rungume ta ajikin shi yana sakin wata ajiyar zuciya gaba d'aya yabi ya wani matse ta cikin jikin shi k'am tamkar za'a kwace mishi ita.


"Kaiii Yah Sabeer agaba na ji yanda ka matse ta"
Jiddah ta fad'a tana rik'e da murfin motar, wata harara ya watsa mata don bazai iya magana ba dariya ta kwashe da ita kan ta rufe motar.


Kok'arin zame jikin ta take amman yak'i sakin ta sai faman shinshina wuyan ta yake yana wani sauke ajiyar zuciya da numfashi cikin murya k'asan mak'oshi yace
"Baby ki barni mana kinsan dai yanzu kin zama tawa ta har abada hakan da nake miki babu haramci aciki tunda an d'aura mana aure, Baby kinsan tun yaushe nake mafarkin zuwan wannan ranar kuwa? "


Ita dai Suhaima a tsorace take dashi ganin yanda Sabeer d'in ta ya rikid'a ya koma wani daban tamakar bashi ba jikin ta har ya fara 6ari na tsoro, da haka suka k'arasa wajen da za'a yi dinner, yana rungume da kusan rabin jikin ta suka shiga wajen.


'Yan uwan Sabeer gaba d'aya yawancin sun zo haka ma Hajja Hauwaa, Dr Ahmad d'an fillo, Daddy da k'annen shi Dr Faridah da sauran matan k'annen Daddy, haka ma yaran duk sun zo tun daga manya har k'ananu waje dai ya cika masha Allah gashi sun sha gayun su na kece raine, ga friends na Dr Faridah wato Mumy duk kusan sun zo manyan hamshak'an en boko da en siyasa da kuma likitoci gaskiya anyiwa Dr Faridah karar zuwa wajen bikin tilon d'anta.


Amman fuskar ta sam baza ka iya karantar yanayin da take ciki ba farinciki ko akasin haka, kusan nace gaba d'ayan su Daddy ne kawai yake faman zuba murmishi cikin zuciyar shi yana yaba za6en d'an nashi don sai yanzu yasan Suhaima da ido, bayan ango da amarya sun yi rawa an musu lik'i ne sun yanka wedding cake ne suka bi ko'ina suna gaida en uwa da abokanan arzik'i da suka zo an ci ansha sannan aka watse da tarin gift's d'in da Suhaima ta samu a wajen friends na Daddy da k'annen sai na Dr Ahmad d'an fillo tasha kyautittaka sosai a wajen su, zuwa lokacin gaba d'aya jikin Suhaima ya gama yin sanyi ganin irin kallon da mahaifiyar Sabeer take bin ta dashi da sauran en uwan shi ita duk ma kallon da Mumy take binta dashi yafi hargitsa mata kai ko gaisuwar ta bata amsa ba sai tashi tayi da sauri tabar wajen tana amsa kiran karya a wayanta don kuwa ba kiranta aka yi ba.




Sai karfe

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login