Showing 6001 words to 9000 words out of 122360 words
Chapter 3 - A sanadin Son ki Hausa Novels Document complete by Aisha A Muhammad Sanaz.txt
Babaa Lantana, ganin haka ya sanya shi kutsa kai cikin d'akin, lokaci d'aya kuma gaban shi na bugawa da k'arfi sosai.
Aliyu yana sanya k'afar shi cikin d'akin idanun shi suka hango mishi Umman shi kwance an lullu6e da zani, da sauri ya k'arasa wajen gaban shi na tsananta fad'uwa, hannun shi na rawa ya sanya akan zanin ya fara janye shi a hankali, fuskar Fatima ce ta bayyana kamar an kirata ta amsa, sai kace ba matacciya ba, tuni Aliyu ya durkushe tare da sakin wani irin kuka yana cewa
"Umma ki tashi don Allah kada ki tafi ki barmu a wannan duniyar mu kad'ai"
Kuka sosai Aliyu yake yana sumbatu, ganin haka ya sanya Baba Adamu ya janye shi daga gaban gawar Fatima dakyar don shima hawayen yake yi, Babaa Lantana kuwa da Aliyah Suhaima kuka suke yi sosai.
Daga k'arshe Baba Adamu ya fita don sanar wa da jama'ar gari, cikin k'ank'anin lokaci mutuwar Fatima baiwar Allah ta zagaye cikin k'auyen nasu, sosai mutane sun jimanta rasuwar ta tare da yaba kyawawan halayen ta, da irin yanda take hak'uri da jure irin rashin mutunci irin na mijin ta wanda sam kanshi ya sani.
Babu jimawa mutane suka taru akayi wa Fatima wanka aka had'a ta cikin likkafani, sannan daga k'arshe aka sadata da gidan ta na gaskiya, gidan da shi muke jira Allah ya jik'an wad'anda suka mutu mu kuma Allah yasa mu cika da imani Amin.
Aliyu da Suhaima sun sha kuka kuwa, musamman Aliyu don yafi Suhaima hankali sai yafi jin rad'ad'in mutuwar fiye da ita, su Baba Adamu da Babaa Lantana ne suke tausar su tare da yi musu nasihar yarda da k'addara, lokacin Fatima ne yayi don haka Allah ya d'auki abarshi, kowanne mutum da iyakacin lokacin da Allah ya d'ibar mishi yanzu Fatima addu'a tafi buk'ata fiye da komai, Allah yasa mu dace duniya da lahira Amin.
Haka Aliyu da Suhaima suka rungume maraicin su, sun koma abin tausayi, bayan sadakar bakwai ne 'yan uwan Fatima suka nemi tafiya da Suhaima shi kuma Aliyu ya zauna a wajen 'yan uwan uban shi, amman k'ememe Aliyu ya yak'i yarda da tafiya da Suhaima, anyi rarrashin sunyi fad'an amman ina yak'i aminta dole suka damk'a amanar su hannun Babaa Lantana da Baba Adamu, tukunna suka tafi bayan su bawa Aliyu wani d'an taimakon da zai nemi wata sana'ar ta domin kula da kansu.
Haka rayuwa ta cigaba da tafiya, inda Aliyu da Suhaima suka sake shak'uwa da junan su, komai Aliyu ya samu zaka ji bakin shi na ambatar Suhaima, kulawa sosai yake bata don shi yafi tausayin ta fiye da kanshi, sai dai ita Suhaima ta koma gidan Babaa Lantana da zama sai dai tana shigowa wajen Yayan nata tana tayashi 'yar hira.
Aliyu ya dage da yin sana'a kowacce iri ce indai zai samu halal d'in shi, aiki yake yi sosai na k'arfi kuma, haka ya dunga tara kud'i har ya sanya Suhaima a makarantar primary tana nan cikin k'auyen nasu tare da islamiya, babu dad'e wa Suhaima ta fara zuwa makaranta hankali kwance, kullum shi zai kai ta a tsohon keken da Baba Adamu ya cika mishi kud'i ya siya, haka idan aka taso su zai zo ya d'auke ta.
Ganin Aliyu ya fi karkata akan son yin noma da kiwo yasa Baba Adamu bashi aron gonar shi guda d'aya don yana yin amfani da ita, shi kuma ya rik'e guda d'aya, da yake gonakin nashi guda biyu ne manya, gashi gonar da ya bawa Aliyu aro a kusa da gidan su Aliyun take, idan ma mutum bai kula ba ya d'auka kamar gidan a tsakiyar gonar yake, sosai Aliyu yayi murna da wannan karamcin da Baba Adamu yayi mishi.
**** **** ****
Haka lokaci ya cigaba da tafiya watanni da shekaru na wuce wa kamar kiftawar ido, Suhaima an fara zama 'yammata an don har ta kammala makarantar primary sun zana commen interest tana gida ana jiran fitowar result sai makarantar islamiyya da take cigaba da zuwa.
Yayin da Aliyu an zama matashin saurayi, ya zama cikakken manomi a yanzu, don ya rik'e sana'ar noma da kiwo, da wannan gonar da Baba Adamu ya bashi aro yake noman shi and cikin ta har zuwa yanzu da ta zama mallakin shi, don tuni Baba Adamu ya siyar mishi da ita, bayan aikin noma kuma yana yin kiwo irin su kaji, awakai da shanu sai kuma yana siyar da kwan kaji sosai yake samu bud'i a harkar shi, ga taimakawar wani amintaccen yaron shi da Baba Adamu ya sama mishi yana taimaka mishi.
Ya gyara gidan su sosai yayi kyau, inda a lokacin kuma Baba Adamu ya nemi da yayi aure, babu 6ata lokaci ya sanar musu da Aliyah d'iyar shi yake sosai, babu wanda bai yi farinciki da hakan ba don haka babu 6ata Lokaci akayi aure amarya ta tare a gidan ta, nan kusa da gidan su tun da Aliyu a asalin gidan su ya zauna, a lokacin kuma Suhaima ta dawo hannun Yayan ta da zama, zaman su suke cikin kwanciyar hankali da farinciki, Aliyu ya mayar da hankalin shi sosai kan sana'ar tashi, ya dad'a zama wani babban mutum musamm da yanzu yayi aure.
Kamar yau ne ranar laraba ranar da kasuwar garin nasu take ci, tun safe Aliyu ya bar k'auyen nasu ya tafi cikin birni kai wasu kwai masu yawa, wajen mutumin da yake kaiwa ya siya a kan machine d'in shi, don haka gidan ya rage daga Aliyah sai Suhaima a ciki.
Ranar Suhaima cikin farinciki take saboda Yayan ta baya nan, zata je cin kasuwa don haka da wuri tayi wanka ta ci gayun ta cikin wata atampa mai kalar milk da brown a jiki, ta sanya hijab d'in ta k'arami kalar brown, sannan ta fito daga d'akin ta zuwa wajen da Aliyah take.
Aliyah tana zaune tana gyaran kayan miya don tana son gama girki da wuri kafin Aliyu ya dawo, ta hango Suhaima tana tahowa zuwa wajen ta, fuskar ta d'auke da murmishi tace
" Suhaima wannan gayun fa ina zuwa? "
Cikin dariya Suhaima tace
"Yaya Aliyah nayi kyau ne?"
Itama Aliyah tana dariya tace
"Sosai ma 'yar k'anwata kinyi kyau, ina zuwa? "
"Cin kasuwa zan je "
Zaro ido Aliyah tayi tare da cewa
"Haba Suhaima kin mance Yayan ki baya son kina zuwa koh, yanzu idan ya dawo bakyanan nasan fad'a zai mana ni da ke "
Shagwa6e fuska Suhaima tayi tare da cewa
"Haba Yayah Aliyah kafin ya dawo fah na dawo, ba dad'e wa zanyi ba "
"Toh shikenan amman don Allah kada ki dad'e "
"Yawwa Yayah Aliyah nagode, kuma bazan dad'e ba "
Murmishi suka yiwa junan su, sannan Aliyah ta d'auko kud'i ta bata, godiya tayi tukunna ta tafi cikin zuciyar ta fal farinciki.
Tana fita waje ta tarar da k'awayen ta suna jiran ta, nan suka tafi kasuwar suna tarar ana tacin kasuwa ga mutane daban daban har da na maraya ma suna zuwa cin kasuwar.
Suhaima bata dad'e ba tace wa k'awayen ta zata tafi gida, don kada Yayan ta ya dawo ya tarar bata dawo ba yayi mata fad'a, aikuwa suka ce sai dai tayi gaba su ba yanzu ba, haka Suhaima ta kamo hanya tana tafiya ita kad'ai cikin sauri.
Sauri sauri take gaba d'aya hankalin ta yayi gida, tana tsoron kada Yayan ta ya dawo ya tarar bata nan.
D'ago kan da zatayi ta hango wata kyakkyawar yarinya a tsaye kusan sa'ar ta, sai dai zata ba Suhaima wajen shekara biyu, sai wani dattijo a tsaye shima a gefen ta a tsaye da alama sun k'agu da tsayuwar da suka yi.
A hankali Suhaima ta k'arasa inda suke tsaye har zata wuce su, da sauri yarinyar nan ta k'arasa wurin Suhaima tace
" 'yar uwa idan baza ki damu ba don Allah muna son ki taimaka mana da ruwa zamu sanya a mota "
D'ago kanta Suhaima tayi ta kalle ta sannan tace
"Toh ba matsala bari na k'arasa gida na d'ebo muku"
Murmishi yarinyar tayi tare da cewa
"Idan baza ki damu ba zan bi ki don na gaji da tsayuwar "
"Ba komai mu je "
"Ngde 'yar uwa "
Kallon dattijon nan tayi tare da cewa
"Malam Habu bari mu je gidan su mu kawo ruwan "
Sai da dattijon nan da yarinyar ta kirawo da Malam Habu yayi d'an jim kad'an kafin yace
"Toh amman kada ki dad'e kinga kada yamma tayi mana a hanya "
Gid'a kanta tayi sannan ta juya wajen Suhaima tace
"Mu tafi koh? "
A nutse suka fara tafiya yarinyar tana yiwa Suhaima hira sai dai bata fiye bata amsa ba daga ehh sai a'a, can sai kuma tace
"Ni sunana Hauwaa amman 'yan gidan mu na kirana da Jiddah saboda sunan kakar mu ne "
Murmishi Suhaima tayi tare da cewa
"Sunan ki mai dad'i "
"thank you, ke fah what's your name? "
"My name is Suhaima Umar"
"Wow nice name, daman kina jin turaci? "
"Yeah but kad'an kad'an."
"Good, kin gama primary ne "
"Ehh na gama ina jiran result ya fito na cigaba "
"Amman kin birge ni Suhaima, zamu iya zama friends? "
"Why not "
Cewar Suhaima, nan kowacce ta bada d'an yatsan ta suka k'ulla friendship, tukunna suka k'arasa shiga gidan da sallama.
Gaban Suhaima ne ya fad'i ganin Yaya Aliyu a tsaye yana safa da marwa, ga Yaya Aliyah ma a tsaye fuskar ta d'auke da damuwa da alama dai ita ake nema.
Suna ganin ta gaba d'aya sukayo inda take Aliyu ya sanya hannun shi saman kafad'ar ta ya rik'e da d'an k'arfi yace
"Ina kika zauna Suhaima, ba na hana ki fita kasuwa ba "
Idanun tane yayi raurau kamar zata yi kuka, batason ganin damuwar Yayan nata ko kad'an, don haka sai tace
"Kayi hak'uri Yaya bazan sake ba "
Kallon ta kawai yake bayason wani abu ya samu tilon k'anwar tashi.
"I'm so sorry Yayah bazata sake ba "
Aliyu da Aliyah suka ji saukar muryar Jiddah, da sauri suka kallo inda take don sam basu kula da ita ba hankalin su gaba d'aya yana kan Suhaima.
Kallon Suhaima Aliyu yayi irin na neman k'arin bayanin ina ta samu wannan yarinyar, fahimtar hakan da Suhaima tayi ne ya sanya ta bud'e baki tayi mishi bayanin had'uwar su.
Ba wanda yayi magana sai da Jiddah ta gaida su sannan suka amsa, kallo d'aya zaka yiwa Jiddah kasan ta samu tarbiyya mai kyau a wajen manyanta.
Babu 6ata lokaci Aliyu ya samu jarka ya zuba ruwa taf a ciki, sannan ya d'auko ta Suhaima da Jiddah na bin shi a baya har zuwa wajen da motar su tayi parking.
Bayan sun k'arasa ne Aiyu suka gaisa da Malam Habu sannan ya kar6i ruwan ya zuba a mota yana godiya, mik'a wa Aliyu jarkar ruwan yayi yana sake godiya, girgiza kai Aliyu yayi tare da cewa
"A'a ka barshi a wurin ka idan buk'atar hakan ya taso muku a gaba kwayi amfani dashi "
Malam Habu cikin girmama karamcin Aliyu yace
"Mun gode d'an samari Allah ya saka da alkhairi "
Daga haka Malam Habu ya shiga cikin mota yayi mata key ya tasar da ita, sannan ya d'ago kanshi ya kalli Jiddah da bata da alamun shigo wa motar yace
"Jiddah taho mu tafi yamma nayi "
Maimakon ta bawa Malam Habu amsa, sai ta juya wajen Aiyu ta rik'e hannayen shi duk biyun tace
"Don Allah Yaya Aliyu zan na zuwa nan ganin Suhaima, Allah tun da na ganta naji ina sonta sosai, gashi mun k'ulla k'awance da ita, kuma ina son ka zama Yaya nah "
D'an murmishi Aliyu yayi shi duk wanda yake k'aunar 'yar k'anwar shi, to shima yana son shi, dafa kan Jiddah yayi tare da cewa
"Kada ki damu Jiddah na d'auke matsayin k'anwa, kuma duk lokacin da kike son zuwa wajen Suhaima ki zo ki ganta "
Dariya Jiddah ta sanya ita da Suhaima kafin tace
"Nagode sosai Yaya Aliyu "
Sannan ta jiyo wajen Suhaima suka rungume junan su, dakyar ta iya sakin Suhaima ta shiga mota har da d'an hawayen ta, don ji tayi kamar ta zauna a wurin su, suna tsaye Aliyu da Suhaima suna d'aga musu hannu har suka daina hango motar su.
Sannan Aliyu da Suhaima suka juya zuwa gida, sosai Suhaima ta fara jin kewar Jiddah kamar wad'anda suka shekara da sanin junan su, ita haka kawai taji Allah ya sanya mata son Jiddah kamar irin 'yar uwar nan ta jini...
Aishat A Muh'd ✍🏻
💝 A SANADIN SON KI 💝
Written by
Aishat A Muh'd
♻EXCLUSIVE WRITER'S FORUM
DEDICATED TO MY SADEEY SANAZ
PAGE 9-10
Haka lokaci ya cigaba tafiya, zumunci tsakanin Suhaima da Jiddah ya k'aru sosai wanda takai duk weekend sai ta zo ganin Suhaima, sai dai Aliyu sam yak'i bata fuskar ta tambaye shi taje gidan su Jiddah, sai dai ita duk weekend k'afar ta yana hanyar zuwa gidan su Suhaima ko kad'an bata damu da rashin zuwan Suhaima gidan su ba, tasan komai lokaci ne akwai lokacin da zata zo mata gidan su, aminci sosai suke yi.
Haka Aliyu, Aliyah dasu Babaa Lantana da Baba Adamu duk sun saki jiki sosai da Jiddah, saboda kirkin yarinya ga kuma yanda take girmamasu, duk da sun san daga gidan kud'i ta fito, don da ganin irin sutturar da take sanya wa da irin motar da ake kawo ta a ciki kasan iyayen ta ba k'aramin masu kud'i ba ne, gashi indai zata zo kowa a cikin su da irin tsarabar da take kawo mishi, musamman Suhaima k'awar ta, yini guda cur zata yi musu suyi ta zagaya gonar Yaya Aliyu da wurin da ya ke6en ce don yi kiwo a ciki, sam Jiddah ko a fuska bata nuna tana kyamar su.
Ana cikin haka exam d'in su Suhaima ta fito taci wata makarantar secondary da take a birni, nan Yayan ta yayi mata ciko ciko ta samu gurbin karatu na jss 1.
Cikin k'ank'anin lokaci Suhaima ta fara zuwa makaranta, Jiddah tayi murna sosai da cigaban makarantar Suhaima, gashi kuma Jiddah idan tazo wani lokacin tana k'ara fahimtar da ita wasu abubuwan na fannin boko, ga kuma kwalliya da gayu da take koya mata, saboda Jiddah tana son duk ranar da Suhaima zata gidan su ya kasance ta iya komai na wayewa yanda 'yan uwan ta basu su kyamace mata ko su raina saboda sanin halin su da tayi, sosai Suhaima ta mayar da hankalin ta tana karatu babu wasa, Aliyu ne mai kaita ya kuma d'auko ta daga makaranta yana alfahari da 'yar k'anwar tashi.
*** *** ***
AFTER SIX YEARS
"Suhaima! Suhaima!! Suhaima!!! "
Naga wata matashiyar kyakkyawar yarinya chocolate colour tana tsaye a tsakar gida tana kwallawa Suhaima kira, nima gaba d'aya na baza ido na hango fitowar Suhaima don na kwana biyu ban lek'o gidan ba daukan rahoto lol.
Wata kyakkyawar yarinya na hango tana fitowa daga d'aki da gudu jikin ta sanye da wata gown ash colour mai touch d'in red a jiki, gashin ta a sake ya kwanta a gadon bayan ta hannun ta na rik'e da veil na gown d'in shima red colour.
Da gudu ta k'araso wajen matashiyar yarinyar nan mai kiran ta, tana zuwa ta rungume ta tana dariya ita ma d'ayar dariya take, kafin kuma ta d'an ture ta tana 6ata fuska tace
"Ni ai nayi fushi Jiddah da ke ace ranar graduation d'ina ki k'i zuwa koh"
Wadda aka kirawo da Jiddah ta langa6e kai tare da cewa
"I'm so sorry friend kinsan a time d'in na tafi raka Ammi na london yin check off, nima kaina ban ji dad'in hakan ba please forgive me "
Wani kyakkyawan mirmishi Suhaima ta saki wanda ya fallasa dimple d'in ta sannan ta rik'o hannun Jiddah tace
"Tsokanar ki nake besty kinsan Yayah Aliyu ya fad'a min "
"Yawwa tawan har naji dad'i "
Sake rungume juna suka yi suna dariya, Yaya Aliyu da Aunty Aliyah suna tsaye suna kallon su sai murmishi suke su ma.
A dai dai lokacin kuma driver d'in da ya kawo Jiddah ya fara shigo da kaya yana ajiye wa, sakin juna suka yi sannan a lokacin idanun Jiddah suka sauka akan Yaya Aliyu da Aunty Aliyah sunkuyar da kanta tayi cikin jin kunya tace
"Auuu Yaya Aliyu da Aunty Aliyah daman kuna nan, ai ni ban kula da ku ba "
"Daman ina zaki kula damu hankalin ki yana wajen Suhaima "
Cewar Aunty Aliyah tana rik'e ha6a, Yaya Aliyu kuwa ban da murmishi babu abin da yake.
Langa6e kai tayi cikin shagwa6a ta had'e hannayen ta biyu waje d'aya tare da cewa
"Afuwan Babban Yaya da Aunty na bazan k'ara ba "
Dariya suka sake yi kafin Suhaima ta rik'e hannun Jiddah taja ta zuwa cikin wata rumfa wanda aka ajiye wasu kujeru na sak'i, zama ake akan su don hutawa, gaba d'ayan su suka zauna ana hira cikin farinciki da annushuwa, kafin daga bisani Jiddah ta d'auko wani kwali ta bud'e sai ga chocolate cake ya bayyana, nan ta ajiye shi saman table d'in da yake ajiye inda suke zaune, sannan ta tashi da sauri ta nufi kitchen.
Bata jima ba ta fito hannun ta rik'e da ashana, su dai bin ta da ido kawai suke, tana zuwa ta kunna ashanar ta sanya wutar jikin d'an candle d'in da yake tsakiyar cake d'in wanda ake sanyawa a jikin cake, kamo hannun Suhaima tayi sannan tace
"Are you ready? "
Gid'a kanta Suhaima tayi fuskar d'auke da murmishi, babu 6ata lokaci suka hure wutar a tare sannan suka yanka cake d'in kowacce ta bawa 'yar uwar ta a baki, sannan Suhaima ta bawa Aliyu ita kuma Jiddah ta bawa Aunty Aliyah.
"Happy graduation sister "
Rungume Jiddah tayi tare da cewa
"thank you so much dear"
"Haba never mind 'yar uwa"
Daga nan Yaya Aliyu ya fita Aunty Aliyah kuma ta wuce kitchen, sannan Suhaima