Showing 84001 words to 87000 words out of 122360 words

Chapter 29 - A sanadin Son ki Hausa Novels Document complete by Aisha A Muhammad Sanaz.txt

aikuwa ganin haka suka kwashe da dariya tare da tafawa, sannan Aunty Fadilah ta bud'e bottle d'in faro da yake hannun ta sai kawai Suhaima jin saukar ruwa mai sanyi da taji ajikinta har sai da ta saki ajiyar zuciya mai karfin gaske.


"Shegiya mara zuciya idan kin cika ke mai zuciya ce kare bai d'auke ba ki rabu da Sabeer daga yau "


"Aunty mu taya ki "
Cewar Zahra da Khairat sarakan tsiwa.
"Ku taho mana 'yan 'ya'yana masu kishin 'yan uwan su "


"Don Allah Aunty kuyi hak'uri kada ku min haka "
Cewar Jiddah tana kuka da karfi tana kare Suhaima, ture ta Aunty Fadilah tayi nan Zahra da Khairat suka dunga bud'e bottles na faro suna shek'a mata a jikinta suna zaginta da yi mata rashin mutunci duk gaba d'aya sun jik'e jikinta jagab da ruwa gashi don mugunta da ruwan sanyi suke amfani.


Yusrah yayar Jiddah da batason hayaniya tabar dakin bata jin dad'in abin da suke mata ba amman da yake miskilace sai kawai ta bar wajen.


Jiddah tana cikin kuka ne d'ago kan da zata yi sukayi 4 eye's da Sabeer tsaye ya hard'e hannun shi a kirjin shi eyes nashi sunyi ja tare da fuskar shi, sai da gaban Jiddah yayi mugun fad'uwa ganin yanda d'an uwan nata ya rikid'a kamar ba Sabeer ba, bata ta6a ganin shi cikin makamancin irin wannan yanayin ba.


Zahra ce ta fara arba da Sabeer ta ankara dashi tuni tayi cilli da bottle d'in hannun ta jikinta ya fara rawa na tsoro, haka ma Khairat itama ta cillar da robar tana rarraba ido Aunty Fadilah kuwa sai da gabanta ya fad'i da suka had'a ido da Sabeer don bata ta6a ganin shi a haka ba batasan lokacin da ta saki nata robar ba.




Cikin wani irin taku na fusata ya k'arasa shiga d'akin bai kalli inda suke ba ya k'arasa inda Suhaima ke zaune jikin ta jagab da ruwa har tsiyaya yake d'ago ta yayi tare da kallon Jiddah yace
"Kai ta wani bedroom d'in ki bata kaya ta canja "
Muryar shi dakyar take fitowa saboda tsananin 6acin rai jikin shi har wani rawa yake, da sauri Jiddah taja hannun Suhaima wadda take kuka sosai suka fita.


Aunty Fadilah, Zahra da Khairat kuwa suman tsaye suka yi ko motsin kirki sun kasa yi, Zahra bata ankara ba taji saukar wani zazzafan mari mai saurin kurmanta mutum wani ihun k'ara ta saki da karfin gaske ya fara dukanta yana ball da ita cikin zafin nama, Khairat tun kafin azo kanta take rusa kuka sosai tana dana sanin biyewa zuciyarta da Aunty Fadilah.


Bata ankara ba taji saukar nata marin wanda har sai da bakin ta ya fashe, belt d'in jikin shi ya cire ya fara narkar su cikin tsananin 6acin rai har wasu hawaye ne suke zuba a eyes nashi zuciyar shi tana zafi.


"Sabeer mene haka kashe su zaka yi ne akan wannan matsiyaciyar yarinyar ne "
Bata gama rufe bakin ta ba taji saukan mari akan face d'in ta da mamaki ta d'ago kanta ta d'auka Sabeer ne ya mare ta sai taga ashe Daddy ne.


Zaro ido tayi cikin tsorata tace "Yaya! "
Sake kwad'a mata mari yayi tare da cewa
"Rufe min baki mara kunya banza mara kunyar wofi "
Cikin 6acin rai Daddy yake fad'in haka ashe Jiddah ce ta kirawo shi tana kuka tana yi mishi bayanin abin da yake faruwa shine ya taho.


Dakyar aka kwaci Zahra da Khairat a hannun Sabeer aka fita dasu daga d'akin duk ya farfasa musu jikin su ko kuka sun kasa saboda azaba, zubewa yayi kan carpet tare da rik'e kanshi da hannun shi yana sakin wani ajiyar zuciya.


Babu dad'ewa gaba d'aya kusan family suka had'u a gidan Jiddah har da Dr Ahmad d'an fillo, Hajjah Hauwaa wadda take kuka wiwi Sabeer zai kashe mata 'yan jikoki akan wannan shegiyar yarinyar amman ta kasa yiwa Sabeer fad'a saboda son da take mishi sai hucin da take saki.


Dr Faridah ma ranta a 6ace sosai da kanta tayi treatment d'in su Zahra da Khairat a inda suka ji ciwo dole ta d'auki mataki akan wannan shegiyar, Aunty Fadilah kuwa tayi tsit da ita sai raba ido take saboda ba k'aramin tsoron Daddy take ba.


Suhaima bayan ta canja kaya ne tana kwance wani zazzafan zazza6i ne ya rufe ta kuka take sosai yau taga karshen wulak'anci dole ta rabu da Sabeer duk da kuwa son da take mishi bazata jure wulak'anci da zagan mata da mahaifiya da suke wadda take kwance a kabari.




Dakyar Daddy ya rik'o hannun Sabeer suka fito zuwa parlour kallo d'aya Dr d'an fillo yayi mishi yaji duk haushin dukan da yayiwa su Zahra ya kau hankalin shi ya tashi sosai ganin yanda d'an lelen shi ya koma dole yayi wa su Aunty Fadilah tatas don kawai Sabeer yaji sassauci ya nuna musu abin da suka yi basu kyauta ba daga karshe kuma yayi musu iyaka da matar Sabeer.




Daga karshe tafiya suka yi gaba d'ayan su, Mumy kuwa aranta haka tace kowa ya gama nashi rashin mutuncin akan wannan yarinyar yanzu lokacin ta yayi dole tayi nasarar raba Sabeer da Suhaima rabuwa ta har abadaaa.........








Aıʂɧąɬ A Mųɧ'ɖ ✍🏻
*A̺͆ S̺͆A̺͆N̺͆A̺͆D̺͆I̺͆N̺͆ S̺͆O̺͆N̺͆ K̺͆I̺͆*








Wྂrྂiྂtྂtྂeྂnྂ bྂyྂ
Aྂıʂɧąɬ Aྂ Mྂųɧ'ɖ




ɖɛɖı¢ąɬɛɖ ɬơ ɱყ ʂąɖɛɛყ ʂąŋąʑ




♻ *Eҳ¢ʂųιı۷ɛ щγıɬɛγ'ʂ ʄơγųɱ*





*PAGE 87-88*










Shiga cikin bedroom d'in da take a kwance yayi hawa kan bed d'in yayi yana kok'arin had'a ta da jikin shi duk da jikinta ba kwari sai da tayi kok'arin matsawa da sauri, cikin marairaicewa Sabeer yace
"Baby please kada ki hora ni akan abin da akayi miki, bazan jure hakan ba "
Kamar zai yi kuka yake maganar, cikin muryar ta wadda ta dushashe tace
"Mu hakura da junan mu Sabeer 'yan uwanka basa sona sun tsaneni"


"Nooo! Baby ki daina fad'in haka bazan iya rabuwa dake ba, ni ina sonki kuma ni zan zauna dake basu ba "


Duk yanda yaso yanda yaso ya had'a ta da jikin shi don ya rarrashe ta tak'i yarda, gashi kukan ta yana ta6a mishi zuciya, bata ankara ba taji Sabeer yana fitar da hawaye.


Kallon shi ta tsaya yi kawai ana cikin haka Jiddah ta shigo da sauri ya goge hawayen shi don bayason ta gani, cikin sanyin murya yace
"Jiddah ki tayani rarrashin Baby tace bazata koma gidana ba"
Cikin jin tausayin su ta zauna tana kama hannun Suhaima tace
"Haba Suhaima mene hakan idan kika yi hakan ai abin da suke so kenan, taya zaki zalunci kanku bayan kuna son junan su kice zaku rabu, kiyi hak'uri don Allah kada ki rabu da Yah Sabeer yana son ki "


Rarrashin ta sosai Jiddah take dakyar ta ciyo kanta ta amince, rungume ta Sabeer yayi don jin dad'in abin da ta fad'a.


Har an fara yayyafi suka tafi gida, bayan sun je gida Suhaima tana yin wanka wani zazza6i mai zafi ya rufe ta sosai da ciwon kai sai kuma amai sosai ranar basu iyayin baccin kirki ba saboda yanda jikinta ya rikice sosai don Sabeer ba k'aramin tsorata yayi da jikin ba.


Washe gari da safe ya kirawo Dr Aishat don ta dubata, babu jimawa tazo tayi mata gwaje gwaje nan ta hango ciki d'an wata 2 ajikin Suhaima sai kuma damuwar da ta saukar mata da zazza6i, ganin yanda ta gala6aita ne ya sanyata sa mata drip don taji kwarin jikinta sannan tayi mata allurar bacci.


Nan tayiwa Sabeer albishir d'in cikin jikin Suhaima, dad'i da farinciki ne ya rufe Sabeer saboda tsakanin murna sai da yayiwa Dr Aishat kyautar mota, dad'i ya ishe shi Dr Aishat nan tayi ta zuba godiya da addu'a sannan tace da zarar Suhaima ta farka ya kirawo ta awaya tukunna ta tafi, Sabeer ya koma d'akin Suhaima kallon ta yake kawai wata zazzafar kaunar Suhaima take sake mamaye cikin zuciyar shi sai shafa cikinta yake Daddy ya iya kira yayi mishi albishir sosai Daddy ya nuna murnar shi.




*** **** ****






Dr Faridah ce zaune a katafaren office d'in ta sai jujjuyawa take cikin kujera idanun ta a lumshe, turo kofar akayi tare da shigowa.


Bata bud'e ido ba taba da umarnin azauna, wadda ta shigo ce ta zauna kan kujera kanta sunkuye tana jiran abin da Dr Faridah zata ce.


"Dr Aishat ina kika je bakizo office akan time ba? "
Cikin girmama wa tace
"Ranki ya dad'e naji gidan Yalla6ai Sabeer ne duba matar shi bata jin dad'i "
"Okay me ya same ta "
Cikin fara'a Dr Aishat tace
"Ai abin farinciki ne ya same mu Doctor don Matar shi ciki ne da ita har tsayin 2 months "


Wani shegen murmishi Dr Faridah ta saki mutum ya zaci murmishin farinciki ta saki har da wani cewa
"Masha Allah Dr Aishat naji dad'i sosai da wannan albishir d'in "
Bud'e bag nata tayi ta d'auko kud'in da batasan adadin su ba ta mik'awa Dr Aishat tace
"Ga nawa tukuicin "
Kar6a Dr Aishat tayi cikin fara'a tace
"Kaiii wannan d'a da farinjini yake tun kafin yazo duniya nake samu alkhairi yanzu Yalla6ai fah ya bani kyautar mota "
"Babu komai zaki iya tafiya "
Tashi tayi tana godiya ta fice daga office d'in, wata shegiyar dariya Dr Faridah ta saki tare da cewa
"Lokaci na yayi dole cikin nan ya zube ta kowanne hali "




*** **** ****




Bayan ta tashi daga bacci ne Sabeer yayi mata wanka tare da bata tea ta d'an sha kad'an da maganin da Dr Aishat ta bata, sannan ya kirawo Dr Aishat ya fad'a mata ta farka babu 6ata lokaci tazo ta sake dubata tare da bata shawarwarin yanda zata kula da kanta daga nan tayi musu sallama ta tafi.


Kulawa sosai Sabeer yake bawa Suhaima don haka cikin kwana 2 ta d'an warware tunda cikin ba mai laulayi bane, tana cin abinci babu laifi, sai dai baccin da yake damunta don sai ta yini tana bacci ganin haka ya sanya Sabeer tunanin samin 'yar aiki don tana tallafa mata da wasu abubuwan.




Suna zaune da Daddy a parlour yake gaya mishi yana son 'yar aiki da zata na taimaka wa Suhaima saboda yawan baccin da take yi, abin da Mumy ya kamata ya fad'awa hakan amman babu fuskar hakan.


Suna cikin tattauna yanda zasu samu house girl ne can daddy yace
"Sabeer ina tunanin ka nemi Jiddah ta samo mata"
"Yawwa haka za'a yi Daddy "
Yana kok'arin zaro wayan shi ne a aljihu yaji muryar Mumy tana cewa
"Haba Son basai ka kirawo Jiddah ba, zan baka d'aya daga cikin house girl's nawa su taimaka mata "
Kallon ta suke da mamaki sosai ganin yanda take fara'a, duk yanda suka so su fahimci akwai wani nufi cikin zuciyar ta suka kasa gane hakan da yake Mumy 'yar duniya ce baka gane gabanta balle bayanta green snake ce.


Daddy duk da haka sai da yaji shakku da abin da tace bai yarda da ita ba amman sai yabar abin cikin zuciyar shi kawai, sai kuma ta zauna sosai ana hira da ita wanda rabon ta sakewa Sabeer tun lokacin da ya fara son Suhaima.


Da ya tashi tafiya ta had'a shi da house girl d'in yarinya ce bata fi 18yrs ba suka tafi amman bata bi motar Sabeer ba sai drive ne ya kaita, Suhaima taji dad'in zuwan 'yar aikin sosai gashi kuma taga bata da rawar kai.




Cikin kwana 2 ta tsaya tana aikin ta sosai yanda ya kamata gashi bata da k'iwa Suhaima najin dad'in zama da ita.


Da wani yammaci ne Suhaima tana zaune a parlour tana ta6a charting ita da Jiddah ne, sai ga Larai mai aiki ta kawo wa Suhaima wani had'in so6o acikin jug ga cup nan ta ajiye su kan center table tace
"Aunty ga so6o nan na had'a miki "
D'an yatsina fuska Suhaima tayi kan tace
"Anya zan sha so6on nan Larai bana sha'awar shanshi "
Murmishi tayi kan tace
"Haba Aunty ki daure kisha na 6ata lokaci ina shirya miki shi fah "
"To shikenan zuba min "
Cikin rawar jiki ta fara zuba mata har Suhaima taso d'ago wani abun atattare da ita ganin yanda take rawar jiki amman sai ta share zancen ta kar6i glass cup d'in ta fara shan sa6on, bata ji wani canjin wani yanayi aciki ba sai ma kamshin cocomber da kayam kamshi kawai taji sai zak'in sugar, taji dad'in so6on don har cup biyu ta shanye, tana gama sha ne Larai ta tattara ta d'auke gaba d'aya takai kitchen ta zubar cikin sink ragowar ta wanke jug da cup d'in tas ta goge su tare da jera su.


Tana gama wa ta bud'e k'ofar baya ta fita garden, zaro waya tayi cikin zanin ta tare da lalubo wata number ta danna kira, babu dad'e wa aka d'auka.


"Hajiya nayi duk yanda kika umarci ne nayi tasha har cikin so6o biyu "
Daga can akayi mata magana banji dai abin da akace ba sai naga Larai ta washe baki tana zuba godiya tare da kashe wayar cikin tsananin farinciki ta koma cikin gidan.




Suhaima kuwa ko 10 minute's bata yi da shan so6on nan ba taji cikin ta marar ta da bayan ta yana wani irin ciwo na daban tun tana daurewa har ta kasa ta fara kuka sosai tana kiran sunan Allah, zaro ido tayi gabanta yana bugawa mai tsanani ganin jini yana bin k'afar ta da yawan gaske saboda tsabar firgita da razana ga azabar ciwo ta fad'o daga kan kujera kanta ya bugu da center table lokaci d'aya numfashin ta ya d'auke...........








Aıʂɧąɬ A Mųɧ'ɖ ✍🏻
*A̺͆ S̺͆A̺͆N̺͆A̺͆D̺͆I̺͆N̺͆ S̺͆O̺͆N̺͆ K̺͆I̺͆*








Wྂrྂiྂtྂtྂeྂnྂ bྂyྂ
Aྂıʂɧąɬ Aྂ Mྂųɧ'ɖ




ɖɛɖı¢ąɬɛɖ ɬơ ɱყ ʂąɖɛɛყ ʂąŋąʑ




♻ *Eҳ¢ʂųιı۷ɛ щγıɬɛγ'ʂ ʄơγųɱ*





*PAGE 89-90*










Sabeer yana zaune a office kawai yaji gaban shi yana fad'uwa sosai Suhaima ce kawai ta fad'o mishi arai don haka phone nashi ya d'auka tare da lalubo number d'in Suhaima ya fara kiranta, sai dai wajen 10 missed calls ba'a d'auka ba.




Nan ya tabbatar babu lafiya don haka tashi yayi ya fito daga office hannun shi d'aya rik'e da coat nashi d'ayan hannun kuma jakar laptop da phone nashi, cikin sauri da sassarfa yake tafiya har ya k'araso compound na company d'in.


Driver na hango shi yayi saurin shiga mota tare da yi mata ya kawo ta gabanshi bai jira ya bud'e mish ba kawai ya sanya hannu ya bud'e murfin motar ya shiga tare da cewa
"Driver kayi sauri ka kaini gida "
"Toh Yalla6ai "
Tafiya suke cikin motar shiru gaban Sabeer ban da fad'uwa babu abin da yake yi lumshe eyes nashi yayi tare da jingina kanshi jikin kujera yana janyo addu'a cikin zuciyar shi.




Tafiyar 20 minutes suka k'araso gida da yake driver yayi gudu ko gama parking bai yi ba Sabeer ya fito daga motar ya doshi cikin gidan.


'Yar aikin da ke la6e ajikin window na parlour wanda za'a iya hango farfajiyar gidan tana raba ido irin na munafukai tana hango Sabeer ne ya sanya ta saurin k'ak'alo kukan dole tare da nufar k'ofar parlour ta bud'e tana kuka sosai har da k'ara.


Sauran kad'an ta bugi Sabeer tayi saurin ja baya ta tsaya cikin tashin hankali yace
"Keee lafiya kuwa? "
"Yalla6ai ka taimaka mana Aunty ce ina fitowa daga d'akina na ganta a parlour a kwance cikin jini kuma ta sume....... "


Kan ta k'arasa fad'a tuni Sabeer yayi wurgi da ita gefe da gudu ya shiga cikin parlour yana rarraba ido ina zai hangi Babyn shi.




Can idanun shi sukayi mummunan gani na ganin Suhaima a k'asa kwance saman carpet babu alamar numfashi a tattare da ita, da gudu ya k'arasa wajen tare da d'ago ta jikin shi yana cewa
"Suhaima! Kada ki tafi ki barni ki tashi please"
Wani irin kuka yake yana jijjigata amman ina batasan yana yi ba ma still har yanzu jini na zuba a jikinta.


"Yalla6ai ko zamu kai ta asibiti "
Cewar Larai mai aiki sai a time d'in Sabeer ya tuna da asibiti don tsananin rud'ewa ya hanashi yin wannan tunanin.


Cikin sauri ya d'auke ta tare da fita daga palon duk jikin shi ya 6aci da jini da karfin shi yake kwallawa driver kira, nan ya taso a tsorace ganin matar Yalla6ai ahaka ya sanya shi saurin bud'e mishi mota ya shiga.


Da gudu driver yake jan motar hanyar asibitin Mumy kawai driver yayi don yasan nan ne wurin zuwan su gaba d'aya 'yan gidan.


Suna shiga compound d'in hospital d'in suka yi kici6is da Mumy ta fito daga ciki zata tafi don time d'in tashin ta yayi, ganin motar Sabeer tayi parking ne ya sanya ta sakin wani shu'umin murmishi don tasan komai ya faru a yanzu.




Da sauri ta k'arasa wajen motar tun kafin ta k'arasa Sabeer ya fito daga motar cikin tashin hankali kamar gaske tace
"Son me yasamu Suhaiman ne? "


Idanun shi na zubar da hawaye yace
"Mumy ki taimaka min kada Suhaima ta mutu please "


Da sauri Mumy ta kirawo nurses suka taho da gadon daukan mara lafiya, kwantar da Suhaima Sabeer yayi nan suka nufi cikin asibitin da sauri, yayin da Mumy ta rik'e hannun Sabeer suka shiga ciki, saboda gujewa zargi ya sanya Mumy k'in shiga room d'in da Suhaima take don ta dubata.


Sai kawai ta kirawo Dr Nabilah don ta tsaya akanta tunda Dr Aishat ta tashi, yayin da Mumy ta rungume Sabeer ajikinta tana shafa bayan shi idan ban da ajiyar zuciya babu abin da yake saki.


Dakyar suka tsayar da bleeding d'in da Suhaima take duk yanda suka so cikin ya zauna amman hakan ya gagara sai da ya fita, gyara mata jikinta suka yi bayan sun samu nasarar dawowar numfashinta sannan suka sanya mata drip tare da yi mata allurar bacci don ta huta sosai.


Fitowa suka yi

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login