Showing 42001 words to 45000 words out of 122360 words
Chapter 15 - A sanadin Son ki Hausa Novels Document complete by Aisha A Muhammad Sanaz.txt
nasan gidan "
Wani sanyin dad'i ne ya kwararanya cikin zuciyar Sabeer cikin murna yace
"Yawwa don Allah taimaka min ka kaini gidan "
"To shikenan "
Nan saurayin yayi gaba Sabeer kuwa sai ya tsaya kamar an dasa shi ta ina zai iya d'aukar trolley d'in nan, ganin Sabeer ya tsaya yasa saurayin dawowa yace
"Lafiya? ".
"Ko zaka iya taimaka min da trolley d'in bazan iya d'auka ba please "
Saurayin bai yi mamaki ba don kallo d'aya zaka yiwa Sabeer kasan cewa d'an hutu ne, d'an murmishi yayi tare da kinkimar jakar, nan Sabeer ya rataya jakar laptop d'in shi suka tafi, tun ana tafiya ba'ayi nisa ba Sabeer ya fara gajiya ga wani uban tsoro da ya mamaye zuciyat shi ganin babu gidaje sosai, amman suna dad'a gaba sai ya cika da mamaki da yaga sun shiga wata unguwa duk gidaje sosai ba kamar inda suka baro ba.
A k'ofar wani gida yaga sun tsaya saurayin yace
"Ga gidan nan "
"Yawwa sannu thank U so much "
Nan ya shigar mishi da trolley d'in cikin zaure ya ajiye, laluba aljihun shi Sabeer yayi na jeans ya zaro 1k ya mik'a mishi tare da cewa
"Gashi abokina na gode sosai but ka kar6a don Allah "
Hannu biyu saurayin yasa ya kar6a tare da zuba godiya har zai wuce da sauri Sabeer yace
"Hmm jimana abokina ya sunan ka? "
D'an murmishi yayi tare da cewa
"Sunana Ashiru kuma ga gidan mu nan "
Ya k'arasa fad'i yana nunawa Sabeer gidan su wanda gida d'aya ne tsakanin su da na Suhaima.
"Ni kuma Sabeer "
"Sunan ka mai dad'i irin na 'yan birni "
Dariya ya bawa Sabeer wanda ya sanya sai da ya d'an yi murmishin dariya saboda ya kula zai yi abin dariya, daganan ya wuce ya tafi Sabeer kuwa babu neman isowa ya kutsa kai cikin gidan tamkar irin gidan nan nasu.
Suhaima tana zaune kan wani dutse tana alwala ta sallahr mangarib, ga Aunty Aliya kuma tana kok'arin sauke miyar abincin dare kenan daga saman murhu suka yi wata sanyayyar murya tayi musu sallama.
Amsawa Aunty Aliya tayi yayin da Suhaima ta tsinci kanta da bugawar zuciya na lokaci d'aya, kafin su ankare sunga mutum a filin tsakar gida a tsorace Aunty Aliya ta kalle shi yayin da Suhaima ta kusan zubewa a k'asa saboda tsabar kid'ima da tsorata na wanda ta gani a k'auyen su kuma cikin gidan su.
"Malam lafiya wa kake nema "
D'an murmishi yayi tare da d'auke idanun shi daga kallon Suhaima ya dawo dasu kan Aunty Aliya yace
"Nazo neman Suhaima ne sunana Sabeer "
"Suhaima kuma? "
Aunty Aliya ta furta hakan tana kallon Sabeer kafin ta jiyo da kanta zuwa kallon Suhaima wadda jikin ta yake rawa na tsorata.
"Eh Suhaima nake nazo nema, idan babu damuwa zanyi sallah sai nayi miki bayanin ko ni waye? "
Aunty Aliya sai tsoron nata ya ragu don kallon da tayi wa Suhaima ta karance ta tsaf alamar tasan shi amman tayi mamaki sosai na yanda Suhaima ta iya 6oye mata abu, don haka sai tace
"Toh ai babu damuwa "
Nan ta je inda suke ajiye botocin gidan ta d'auko babbar butar Yaya Aliyu da bata rabo da ruwa aciki ta ajiyewa Sabeer a gaban shi, d'an murmishi yayi tare da cewa
"Na gode "
Murmishin yak'e Aunty Aliya tayi, tana nan tsaye ya ajiye jakar laptop d'in shi dake rataye a kafad'ar shi saman wani dutse sannan ya tsugunna yayi alwala, abin sallah Aunty Aliya ta bashi sabida masallacin da nisa daga gidan ba lalle ya gane ba yana bak'o, kar6a yayi ya shimfid'a ya fara sallahr har zuwa yanzu Suhaima na tsaye tamkar wadda aka dasa a wajen ko kwakkwaran motsi bata yi, ganin haka ya sanya Aunty Aliya janyo hannun Suhaima suka wuce d'akin ta.
Cikin tsoro tace
"Suhaima wane ne wannan? "
Suhaima itama a tsorace tace
"Na shiga uku Aunty yanzu sai da Sabeer ya biyo ni "
"Ki fad'a min wane shi kafin Yayan ku ya dawo daga masallaci "
Murya na rawa ta bud'e baki zata yi magana suka ji sallamar Yaya Aliyu daga tsakar gida, kallon kallo aka tsaya yi tsakanin Aunty Aliya da Suhaima ko motsin kirki sun kasa......
Aishat A Muh'd ✍🏻
*A SANADIN SON KI*
Written by
Aishat A Muh'd
Dedicated to my Sadeey SaNaz
PAGE 51-52
Murya na rawa ta bud'e baki zata yiwa Aunty Aliya bayani suka ji sallamar Yaya Aliyu daga tsakar gidan, kallon kallo aka tsaya yi tsakanin Aunty Aliya da Suhaima ko motsin kirki sun kasa gaban su sai dukan uku uku yake na tsoron yanda Aliyu zai saurare su na shigowar wani kai tsaye gidan.
A haka ma a tsakar gida kallon kallo aka tsaya yi da Aliyu da Sabeer wanda idar da sallahr mangarib d'in shi kenan, da fara'a Aliyu ya shigo gidan anman had'a idon da suka yi da Sabeer ya sanya fara'ar fuskar shi ta d'auke lokaci daya ya 6ata fuska gefe d'aya na cikin zuciyar shi yana mamakin wannan wane ya shigo mishi gida haka kai tsaye haka har yana sallah.
Sabeer ganin Aliyu ya d'aure fuska sosai yasa shi tsorata gaban shi ya fad'i kada ya kore shi daga gidan, murya na rawa yace
"Sannun ka ina yini? "
Cewar Sabeer kanshi a k'asa don ya fara tsarguwa da wannan kallon da Aliyu yake mishi, tamkar bayason amsawa yace
"Lafiya k'alau "
D'an matsawa yayi kusa da k'ofar d'akin Aliyah yana mamakin da har yanzu babu wanda ya fito ya amsa mishi sallama tsakanin ta da Suhaima tunda ba haka suke mishi ba matuk'ar suna gidan kuwa.
"Aliyah, Suhaima kuna ina? "
Muk'ut Suhaima da Aliyah suka had'iye yawu lokaci d'aya, idanun ta saman fuskar Suhaima tace
"Gamu a d'aki mun yi sallah ne "
Alhalin babu wanda yayi yunk'urin yin sallahr har gwara Suhaima tayi alwala.
"Ku fito ina son ganin ku "
"Toh gamu nan "
Fad'in Aliyah cikin dakiya don ita tafi ma Suhaima jarumtar amsawa, sun d'an d'auki mintuna biyu sannan suka yi shahadar fitowa gaba d'ayan su.
Yaya Aliyu yana zaune saman tabarma kusa da k'ofar d'akin Aliyah, yayi da Sabeer yake zaune saman abin sallah a tak'ure hankalin shi a matuk'ar tashe saboda uban cizon da sauro yake galla mishi a hannu da k'afar shi ga kukan shi da ya dameshi cikin kunnuwan shi ga zafi don sai had'a gumi yake.
Fitowa suka yi tare da zama kusa da Yaya Aliyu sai da ya kalle su na 'yan mintuna kafin yace
"Na shigo gida sai na tarar da wani abin mamaki dana gani, shin wane? Kuma me ya kawo shi cikin gidana ba tare da yarda ta ba? "
K'uwwww cikin Suhaima da Aliyah ya fitar da wannan sautin ganin yanda Aliyu ya d'aure fuska tamkar bai ta6a dariya, basu ta6a ganin shi cikin wannan had'e fuskar ba sai yau don haka suka tsorata.
"Ku nake saurare ku yi min bayani "
Fad'in Aliyu kenan ganin sunyi shiru kansu a sunkuye.
Aliyah ce tayi k'arfin halin cewa "Uhm da....daman yanzu mu... muke son kiraka a... a waya mu fad'a maka, ya dai... dai ce sunan shi... shi Sabeer "
Kallon baku da hankali yayi musu da sauri Aliyah ta sunkuyar da kanta ganin irin kallon da Aliyu yake jefan ta dashi, idan ba wannan kallon yayi musu me zaiyi taya ya kawai bakasan mutum ba ka barshi ya shigo cikin gidan ka kai tsaye namiji ma ba mace ba a yanda zamanin yanzu abubuwa suka ta6ar6are.
Bai k'ara bi takansu ba ya juya wajen Sabeer da lokacin hankalin shi ya gama tashi saboda cizon sauro tamkar zai fashe da kuka ko yayi ta ihu ko yaji dad'i, Suhaima tana ankare dashi cikin zuciyar ta tace "Allah ya k'ara da uban wani iyayi ne ya kawo ka inda bazaka iya rayuwa mai dad'i ba kamar yanda ka saba rayuwar jin dad'i da hutu maganin iyayin mutum kad'an ma ka gani" duk da a d'an tsorace take sai da ta saki murmishi mugunta sauran kad'an dariya ta kubce mata ta mugunta.
"Malam Sabeer muna son sanin kai waye? Me ya kawo ka kuma nan gidan? "
Sabeer d'an had'iyar yawu yayi kafin ya motso kusa da Yaya Aliyu cikin sanyin muryar shi yace
"Kamar yanda ka sani Sunana Sabeer Hussein d'an fillo Yaya ga k'awar Suhaima wato Jiddah "
Nan take Yaya Aliyu yayi murmishi da jin Yayan Jiddah ne ko ba komai d'an uwan Jiddah bai cancanci wulak'anci a wajen su ba.
"Masha Allah ashe d'an uwan Jiddah ne kai yarinya mai hankali da nutsuwa, toh Malam Sabeer muna son sanin lafiya kazo inda muke?".
Sai da yayi shi na d'an minutes kafin ya bud'e baki yace
"So da k'aunar Suhaima ne yasa ni zuwa nan domin na sami soyayyar ta, na kasance tun lokacin da na ganta naji inason ta so na tsakani da Allah kuma ba yaudarar ta zanyi ba wallahi auren ta zanyi "
"Ikon Allah! "
Fad'in Aliyu kenan, Suhaima da Aunty Aliya kuma sun baza kunnuwan su suna sauraren abin da yake fad'a.
"Shine idan baza ku damuwa ba ina son ku koma can birni zan baku gida, mota da kuma aikin yi sannan zan...... "
Kasa k'arasa maganar shi yayi ta mak'ale a fatar bakin shi ganin irin yanda fuskar Aliyu ta rikid'a ta koma wata iri na yanayin fusata ga wani d'an iskan kallo da yake jifan Sabeer jin yazo mishi da wani banzan magana.
Sabeer kuwa kasa magana yayi yana kallon Aliyu yanda yake mishi wani irin kallo alhalin a girmi bazai girme shi sai ma watak'il ya bashi shekara biyu.
"Gaskiya tun da ka biyo ta wannan hanyar ba lallai Suhaima taso ka koda ta so ka ni kuma bazan yarda ta aure ka, mu ba makwad'aita bane duk da mu talakawa ne muna rayuwa a karkara muna jin dad'i yanda muke rayuwar mu bama hangen wani abin don haka ka sake tunani Sabeer baza mu ta6a yarda da wannan maganar taka ba "
Nan Aliyu ya cigaba da masifa don ya d'auka Sabeer ya raina musu arzik'in su ne, baisan Sabeer ko kad'an ba haka bane cikin zuciyar shi da yasan yayi wannan tunanin amman sai ya watsar daga baya tun da iyayen shi sun amince da auren Suhaima a haka amman sai Daddy ya sanya shi furta hakan wanda yayi dana sanin fad'in haka.
Ana cikin haka sai ga Babaa Lantana nan da Baba Adamu sun shigo domin kwana biyu basu lek'o ganin jikin Aliyah ba, suka tarar da wannan hatsaniyar har Aliyu yana cewa Sabeer ya kwashi kayanshi ya koma inda ya fito, sosai hankalin Sabeer ya tashi tuni hawaye sun fara zuba a idanun shi.
Aunty Aliya ya bata tausayi sosai Suhaima kuwa ko a jikin ta, nan Babaa Lantana da Baba Adamu suka shiga zancen dakyar Aliyu ya hak'ura sai lokacin kuma yaga hawayen da Sabeer yake fitarwa sai kuma jikin shi yayi sosai, bai kamata ya wulak'anta jinin Jiddah ba yanda taso su ba tare da kyamatar su ba. Suhaima kuwa dad'i ya kamata tasan yanzu Yaya Aliyu zai kore shi addu'a take cikin zuciyar ta Allah yasa kada Yaya Aliyu ya amince da dad'in bakinshi.
"Kayi hak'uri idan ka bani dama zan zauna a gidan ka na nemi soyayyar Suhaima "
Fad'in Sabeer yana goge hawayen fuskar shi.
Nan jikin Aliyu ya Kara sanyi sosai mene laifin Sabeer anan Allah ne ya jarrabe shi da son Suhaima bai kamata yayi mishi haka ba kodan 'yar uwar shi Jiddah wadda ko d'azu da safe sai da sukayi waya da ita gaba d'ayan su don haka cikin sanyin murya yace
"Nima kayi hak'uri da abin da nayi maka kuma na amince da hakan Allah ya taimaka"
Wani sanyi dad'i ne ya kwaranya cikin zuciyar Sabeer wanda har sai da ya rungume Aliyu yana godiya, yayin da Aliyu, Aliyah, Babaa Lantana da Baba Adamu suka yi dariyar farinciki, Suhaima kuwa wani bak'in ciki ne ya turnik'e ta sai kawai taja tsaki ta wuce d'akin ta da sauri duk suka bi ta da kallon mamaki.
"To kai gaka d'an birni anya zaka iya cin abincin mu ka kwanta a irin d'akunan mu kuwa "
Cewar Babaa Lantana, dariya Sabeer yayi kafin yace.
"Me zai hana kuwa Babaa "
Nan aka d'an ta6a hira cikin farinciki wanda a lokacin Sabeer ya shiga ransu saboda sauk'in kanshi.
Tashi Babaa Lantana da Baba Adamu suka yi da zummar tafiya nan Aliyu ya dage sai sun ci abinci aikuwa k'in yarda suka yi tare da tafiya.
Bayan sun tafi Aliyu ya umarci Aliyah da ta kawo musu abinci, babu dad'ewa ta shirya musu sannan ta wuce d'aki don yin sallah.
Bud'e kwanon Aliyu yayi tuwan biskin gero ne da miyar taushe tasha gyad'a da manshanu sai tashin k'amshi yake, nan Aliyu yayiwa Sabeer Bismillah ba don Sabeer ko yasan mene ba ya tsunduma hannun shi ya fara ci dakyar ya iya had'iye lomar da yayi saboda rashin sabo da cin irin wannan abincin .
Kasa cigaba da ci yayi fahimtar hakan da Aliyu yayi yasa shi girgiza kai yana tausayin Sabeer yasan wahala ce sai yasha don birni da karkara akwai banbanci musamman a irin gidajen da Sabeer ya taso.
Ruwan Sabeer ya runtse ido yasa ba don yayi mishi irin yanda yake so ba gashi cikin shi sai k'arar yunwa yake don rabon shi da abinci tun breakfast na safe saboda zumud'i ma bai ci abinci sosai ba.
"Zaka iya shan fura? "
Cewar Aliyu yana kallon shi d'an sosa k'eya yayi kafin yace
"Eh zan sha kasan mu ma family's d'in mu Fulani ne muna sha amman ni ba sosai ba "
Gid'a kai Aliyu yayi yana cewa "yanzu don duhu yayi zuwa gobe sai mu fita kaga yanda garin namu yake "
Tashi yayi ya shiga d'aki babu jimawa ya fito shi da Aliyah nan ta wuce kitchen tana kok'arin damawa Sabeer fura, babu dad'e wa ta dama shi ta kawo mishi a cikin k'ok'o da ludayi had'e da kofin roba ta ajiye mishi.
"Sannu Aunty Aliyah na had'a ki da aiki "
Murmushi tayi tare da cewa "laaa ba komai wallahi dafatan zaka iya shan wannan furar "
"Zan iya mana "
Murmishi tayi ta wuce d'aki, nan Sabeer ya janyo furar ya fara sha da ludayin gard'in gero da kindirmon nono ya ratsa shi sosai furar tayi mishi dad'i.
"Da ka zuba a kofi koh"
Yana lumshe ido yace
"Barni kawai Yaya nasha a haka don na saba "
Dariya kawai Aliyu yayi, bayan sun gama ne Aliyu ya shiga wani d'aki na kusa da zaure ya fara gyarawa nan Aunty Aliya ta fito itama ta bishi d'akin tana tayashi aikin, Sabeer najin dariyar su da magana suna yi k'asa k'asa lumshe idanun shi yayi sun birge shi sosai yana fatan su yi irin wannan zaman da Suhaima idan ya shawo kanta ta kar6i soyayyar shi.
Tsaf suka gyara d'akin bayan sun share sun bud'e window na d'akin nan suka sanya labule na k'ofa dana window kafin su fito kuma su shiga d'akin Aliyah sai ga Aliyu ya fito da k'aramar katifa ta k'aramin gado ya sanya d'akin Aliyah kuma ta shimfid'a mishi zanin gado a jikin katifar ta kunna turaren wata na tsinke sai d'akin ya fito fes dashi, Aliyu ya d'auki jakar Sabeer ya shigar mishi da ita kafin kuma su d'unguma shi da Sabeer su tafi masallaci don yin sallahr ishsha....
Aishat A Muh'd 💃🏻
*A SANADIN SON KI*
Written by
Aishat A Muh'd
Dedicated to my Sadeey SaNaz
PAGE 53-54
Bud'e labulen d'akin Aliyah tayi tare da shigowa zama tayi kusa da Suhaim wadda ta kwanta rub da ciki a saman gadon ta, dafa bayan ta tayi kafin tace
"Suhaima tashi mu yi magana "
Tashi Suhaima tayi zaune tana goge hawayen fuskar ta da hannunta, kallon mamaki Aliyah take mata kafin tace
"Me yasa kika yi mishi haka Suhaima?, haba Suhaima bansan ki da halayyar wulak'anta mutane ba, ki tuna saboda sanadin son ki fah ya bar gatan shi da komai nashi na jin dad'i ya dawo nan k'auye wanda bai ta6a rayuwa acikin irin wannan yankin ba ya aminta zai jure kowacce wahala indai zai same ki, koda da iya abincin mu ma kafin ya saba aiki ne zai hak'ura ya jure duk don A SANADIN SON KI, haba Suhaima ki tausaya mishi kada ki bashi wahala don na tabbatar Sabeer son ki yake tsakani da Allah ba yaudarar ki yake, idan yaudara ce ma bazai zo har nan ba don haka kiyi tunanin kafin ki yanke hukunci tukunna "
Zum6ura baki Suhaima tayi tare da cewa
"Ni gaskiya Aunty bana son Sabeer hasalima kinsan na tsani auren mai kud'i saboda gujewa wulak'anci, musamman gidan su Sabeer tunda na baki labarin abin da suka yi min"
D'an shiru Aliyah tayi tana d'an tunani kafin tace
"Kina da gaskiya don wannan amman ni ina mai baki shawara kiyi tunani sosai kafin ki yanke hukunci,tare da addu'ar neman za6in Allah kada ki yanke hukunci da gaggawa"
Gid'a kai Suhaima tayi kawai tare da cewa
"Ni bama zan so shi ba"
"Hmmm na dai ji ki Suhaima kawai amman wannan zakad'ed'en sauryin ne kece bakya sonshi kawai ra'ayin ki ne ya hana ki tsayawa kiyi tunanin kin fad'a son Sabeer daga irin kallon da kike mishi d'azu "
Wayyo aikuwa Suhaima ji take kamar ta rusa kuka jin abin da Aunty Aliyah ta fad'a mata, zum6arar baki tayi tare da kwanciya ta juyawa Aliyah baya, abin ya bata dariya tashi tsaye tayi tare da cewa
"Abincin ki yana kitchen fah kije ki ci kada ya huce "
Tana gama fad'in haka ta fito daga d'akin, nan ta tarar da Sabeer da Aliyu sun dawo bayan tayi musu sannu da dawowa ta yiwa Sabeer sai da safe ta wuce cikin d'aki.
Sun d'an jima suna hira