Showing 54001 words to 57000 words out of 122360 words
Chapter 19 - A sanadin Son ki Hausa Novels Document complete by Aisha A Muhammad Sanaz.txt
Babaa Lantana da Baba Adamu sun yi matuk'ar farinciki da kar6ar soyayyar Sabeer da Suhaima tayi.
Yammaci ne irin na bayan sallahr la'asar Sabeer da Suhaima suna zaune a tsakar gidan saman wata babbar tabarma hira suke yi irin ta masoya.
"Assalamu Alaikum "
Suhaima ta tsinkayi sallama da muryar da bazata ta6a mance ta ba, don haka zumbur ta mik'e da sauri ta nufi k'ofa nan suka had'u da juna, wani ihun murna Suhaima ta saki tare da yin tsalle ta rungume Jiddah cikin tsananin farincikin ganin ta.
Sai dai kuma jin abu ya tokare ta yasa ta sakinta tare da yin baya kad'an tana kallan d'an tudun da cikinta yayi, cikin dariya tace
"Besty kaddai mun samu Baby "
Dariya Jiddah tayi tare da kawo hannu ta d'an bugi kafad'ar Suhaima cikin k'asa k'asa da murya tace
"To sarkin tonon silili kina son ki kunyata ni gaban su Yaya "
Hannunta ta rik'o tare da juyawa da nufin su k'arasa wajen tabarmar su zauna, sai suka had'a ido da Aunty Aliyah wadda ihun Suhaima ya fito da ita daga d'aki ba shiri.
Cikin farinciki Aunty Aliya tace
"Jiddah yau kece a gari"
Cikin dariya Jiddah tace
"Ni ce wallahi Aunty ina Yaya Aliyu da Ameer ne ban gan....... "
Sauran maganar Jiddah ta mak'ale a bakinta saboda had'a ido da Sabeer da tayi.
Cikin mamaki tace
"Yaya Sabeer! "
Da murmishi kan face nashi yace
"Sai yanzu kika kula dani kenan "
Tana dariya tare da rufe bakinta tace
"Yah Sabeer ba haka ba ne wallahi d'okin ganin Besty ne ya sanya ban kula da kai ba "
D'an murmishi kawai yayi kafin ya wuce ya tafi, da mamaki sosai Jiddah take bin shi da kallo ko a mafarki bata zaci Sabeer zai zauna a irin wannan yanayin ba, kuma tayi farinciki da hakan don tun ba yanzu ba take sha'awar wani nata ya auri Suhaima saboda son da take mata, kama hannun ta Suhaima tayi suka zauna nan ta kawo mata ruwa kafin su fara gaisawa da Aunty Aliyah tana yi mata barka da samun Baby sun d'an ta6a hira kafin su wuce cikin d'akin Suhaima.
Nan suna shiga hira ta 6arke tsakanin su Suhaima sai tsokanar Jiddah take yanda tayi k'iba, Jiddah na dariya tace
"Yarinya sai kin yi uku nama don nasan Yah Sabeer zai baki kulawa ba kad'an ba"
"A haba taya zan yi ukun ki da ban ganu ba"
"Babyn kune ya sanya min wannan k'ibar don kiji yana zuwa nan duniya zan koma kamar yanda nake "
Da haka suka cigaba da hirar su inda Jiddah take fad'awa Suhaima abin da ya sanya bata zo ba lokacin da suka dawo daga honeymoon laulayin ciki ne ya sanyata a gaba sai yanzu ta samu dama dama.
Sai wajen mangarib Jiddah ta tafi cike da kewar Suhaima bayan ta ajiye musu tsarabar su har ta tafi dai basu k'ara had'uwa da Sabeer ba.....
Aishat A Muh'd ✍🏻
*A SANADIN SON KI*
Written by
Aishat A Muh'd
Dedicated to my Sadeey SaNaz
*PAGE 65-66*
Suhaima ta shigo gidan kenan daga rakiyar Jiddah k'ofar gida sai taji rik'o hannunta a d'an tsorace ta juya don duhu ya fara yi gaf ake da kiran sallahr mangarib.
Had'a ido tayi da Sabeer yana mata wannan kyakkyawan murmishin nashi
"Matsoraciya kawai "
D'an sauke ajiyar zuciya tayi kafin tace
"Ni Allah kaban tsoro na kusa sanya ihun neman taimako "
'Yar dariya yayi kafin yace
"Sorry Baby nah kin cika tsoro, haka jiya kika cika mana kunne da ihu don kinga lizard ya shiga toilet kina wanka "
Murmishin dariya Suhaima tayi don ta tuna lokacin Allah yaso ta ko cire zanin jikinta bata yi ba ta hango shi manne jikin bango.
"Baby ki rage tsoro please bana son ganin abin da zai na tsorata ki "
D'aga kanta tayi alamar toh kawai nan ya cika mata hannu tare da cewa
"Baby anjima zamu yi magana fah da kai lokaci yayi da ya kamata mu yi aure na bar rungumar pillow koh yah? "
Ya k'arasa fad'in haka yana d'aga mata gira ya cigaba da cewa
"Nasan kema kina buk'atar hakan koh? "
Kunya ce ta rufe Suhaima don haka sai kawai ta ruga da gudu zuwa cikin gida tana 'yar dariya a hankali, bayanta Sabeer yabi da kallo yana murmishi kafin kuma ya juya ya fita zuwa masallaci.
Suhaima tana shigowa tsakar gida ta nufi wajen alwala, nan tayi alwala ta wuce d'aki tana shiga ta shimfid'a abin sallah ta fara sallahr mangarib after ta idar ne ta janyo Qur'an ta hau karatu har zuwa sallahr ishsha bayan ta idar ne sai tayi addu'o'in ta daga k'arshe ta rufe addu'ar da neman za6in Allah tare da yiwa mahaifiyar ta addu'a kamar yanda ta saba, bayan ta kammala ne sai ta kwanta saman sallayar tana mai fad'awa duniyar tunani ta yanda zata iya d'auke kai daga duk wani wulak'anci da family d'in Sabeer zasu yi mata, ta jima tana wannan tunanin kafin kunnen ta ya jiyo mata kiran sunan ta da Aunty Aliyah take mata.
Tashi tayi tare da kallon k'aramin agogonta taga har 8:32 na dare, da sauri ta rarumo hijab nata ta d'an fesa turare ta fito tunawa da tayi Sabeer ya fad'a mata zasu magana anjima, tana fitowa ta tarar da Aunty Aliyah a zaune tana bawa Ameer mama.
Zama tayi kusa da ita tare da cewa
"Aunty ga ni "
Yawwa Suhaima daman Sabeer ne yake kiran ki yana k'ofar gida"
Tashi tayi ta wuce ta fita a k'ofar gida ta hango shi zaune shi da Ashiru wajen ta nufa tayi musu sallama cikin sanyin murya, Sabeer sai da ya lumshe idanun shi kafin ya bud'e su akanta ya amsa sallamar ta.
Ashiru ya gaida Suhaima ta amsa cikin fara'a kafin ya tashi yace
"Toh Yaya ni sai da safe zan shiga gida "
"Okay Ashiru sai goben"
Yana gama fad'in haka ya wuce gidan su, sannan Sabeer ya dawo da hankalin shi kan Suhaima wadda take tsaye yace
"Amarya ta zauna mana kada ki gaji da tsayuwa "
D'an nesa kad'an dashi ta zauna saman wani dutse, nan ya fara tsokanar ta yana dariya ita kuma kunya yake bata don har yanzu ta kasa sakin jiki dashi musamman idan ta tuna abin da tayi mishi a baya.
Bayan ya gama tsokanar ta ne sai kuma ya gyara zama cikin nutsuwa yace
"Suhaima! "
D'an d'ago wa tayi ta kalleshi kad'an saboda jin yanda ya ambaci sunan nata kafin tace
"Na'am! "
D'an ajiyar numfashi yayi kafin yace
"Suhaima ina son gobe zan koma gidan mu fah"
A d'an razane ta d'ago tana kallon shi don lokacin da ya fara maganar kanta a k'asa yake tana wasa da 'yantsunta.
"Yes! Baby gida zan tafi zanje na samu Daddy yazo neman min auren ki, mun gama magana da Yah Aliyu dasu Baba don sam ban so awuce 2 month's ban mallake ki matsayin mata ta ba"
"Wata 2 fah Sabeer haba me ma laifin nan da 2 year ".
Cewar Suhaima kanta a sunkuye don bazata iya jurar ganin irin kallon da Sabeer yake mata, ji take kamar ta kwashe da dariya saboda tasan tsokanar shi take so take taga yanda zai yi don haka danne dariyar ta.
Aikuwa wata harara ya dank'ara mata kafin yace
"Sun yi kad'an ma 2yrs a barshi nan da shekaru goma ma yafi"
Ba shiri dariyar da take danne wa ta kubce mata aikuwa ta fara kyalkyala dariya amman ta nutsuwa, sakin baki Sabeer yayi yana kallonta sai a time d'in ya lura tsokanar shi take, lallai kuwa idan ya kama Suhaima a hannun shi zata yi bayani.
"Ya hak'uri mai da wuk'ar tsokanar ka nake a daina harara ta"
D'an murmishi yayi tare da cewa
"Lallai yarinyar nan kin rainani da yawa but zaki bayani idan kika shigo hannuna duk sai na rama abin da kike min "
Marairaice fuska Suhaima tayi tare da cewa
"Wayyo Allah kayi hak'uri ni fah tsokanar ka nake yi amman bazan k'ara ba"
Mak'e kafad'a yayi tare da cewa
"Nak'i wayon yarinya sai nima na rama "
Ya k'arasa fad'i yana dariyar mugunta, baki ta murgud'a kafin ta turo shi gaba
"Lallai ma yarinya ni kike murgud'a wa baki?"
Girgiza kanta tayi sannan tace
"Ni fah ba da kai nake ba ".
"Toh naji dawa kike? "
A shagwa6e tace
"Ni kawai nayi ne".
Murmishi kawai yayi kafin yace
"Baby mu dawo maganar mu, mene ra'ayin ki? "
Kanta a sunkuye tace "ni mezance toh Allah ya za6a abin da yafi alkhairi ".
"Amin Baby nah, ko zaki rakani mu tafi tare? ".
D'an zaro ido tayi tare da dafe kirji tace "waiii ni! rufa min asiri don Allah "
D'aga kafad'un shi yayi kafin yace "to mene aciki "
"Tabbb ni dai bazan iya ba wallahi "
"Sarkin kunya kawai kin cika kunya Baby amman ina daf da cire miki ita kad'an zan rage miki ita"
Waro idanunta tayi gaba d'aya tare da cewa
"Tabbb daman ana cire kunya "
"Eh mana sosai, idan kina so ma yanzu sai na fara cire miki " ya k'arasa fad'a yana dariyar mugunta
Da sauri ta girgiza kanta tare da cewa
"A'a bana so ina son kayata "
Hannun shi ya sanya a gefen shi ya d'auko d'aya daga cikin phone's nashi, ya mik'o mata cikin mamaki take kallon shi ta kasa kar6a
"Baby kar6i mana "
Hannu tasa ta kar6a sannan yace
"Ki rik'e wannan a hannun ki kafin kizo gidana mu je ki za6i wadda kike so "
"A'a Sabeer baza mu yi haka gaskiya ka rik'e wayan ka, sai muna magana da wayar Yah Aliyu ".
D'an 6ata rai yayi kafin yace
"Baby bana son irin haka king kin 6ata min rai, idan kina son raina yayi sanyi ki kar6a "
"Ayyah sorry na kar6a nagode sosai Allah ya saka da alkhairi naji dad'i "
Wani sassanyar murmishi ya saki sannan yace
"Baki k'arasa mana addu'ar ba fah Baby? "
"Kamar yah fah"
"Ki gane mana kamar kice Allah ya barmu tare Allah ya bamu yara masu kamar ku "
Murmishi kawai tayi ta kasa magana daga k'arshe dai tattarawa suka yi suka nufi gida don dare ya fara yi, haka suka rabu cikin tsananin begen junan su.
Washe gari wajen 10 na safe Sabeer yayi sallama da kowa ya fito Yah Aliyu ya d'auke shi a machine don fitar dashi titi, gaba d'aya kayan da yazo dasu ya bawa Ashiru su iyakar jakar laptop d'in shi sai phone nashi d'ayar kawai.
Sun d'an jima a tsaye a titi kafin dakyar su samu taxi wanda zata kai Sabeer gida, shiga cikin motar yayi yayin da Yah Aliyu yaja driven taxi d'in gefe ya bashi kud'in motar Sabeer shi kadai zai dauka har gida ba tare da Sabeer ya sani ba, sai da Aliyu yaga tafiyar Sabeer tukunna ya koma gida zuciyar shi fal kewar Sabeer don su saba da junan su.......
_Na gaishe ku masoya na ina jin dad'in yanda kuke bibbiyar labarin nan nawa_❣
_bazan mance karamcin ki ba my Momma nah (Aunty maijiddah musa), Ni Aishat ina matuk'ar kaunar ki kirkin na daban ne wallahi, Allah ya bar mu tare ya raya zuri'a, Amin ya rabbi_. ❤
Aishat A Muh'd ✍🏻
*A SANADIN SON KI*
Written by
Aishat A Muh'd
Dedicated to my Sadeey SaNaz
*PAGE 67-68*
Wata sassanyar ajiyar zuciya Sabeer ya sauke a lokacin da driven taxi yayi parking a k'ofar get d'in D'AN FILLO FAMILY kallon gidan yake tamkar yau ya fara sanin shi, fitowa yayi daga cikin motar tare da rataya jakar laptop d'in shi a kafad'a sannan ya kalli d'an taxi yace
"Malam nawa ne kud'in ka? "
D'an taxi murmishi yayi kafin yace
"Yalla6ai ai wanda ya rako ka d'in nan ya biya ni kud'ina "
D'an zaro ido kad'an Sabeer yayi tare da cewa
"Da gaske ne maganar ka"
"Kwarai kuwa ya bani"
Cikim tabbatar wa driven taxi d'in ya fad'a, gid'a kai Sabeer yayi cikin zuciyar shi kuwa wani son Suhaima da Yayan ta ne ya Kara ji sun shiga zuciyar shi gaskiya Aliyu yana karamci, amman duk da haka sai da Sabeer ya k'arasa d'an taxi d'in kud'i.
Nan yayi ta godiya tamkar bakin shi ya tsinke saboda godiya yasan yau koda gida ya koma zai samu abin ciyar da iyalan shi na kwana biyu daga k'arshe yaja motar yayi gaba.
Knocking d'in k'ofar gate yayi nan gateman ya bud'e, duk da ramar da bak'in da Sabeer yayi hakan bai hana shi gane d'an lelen family d'in D'an fillo ba ne ya dawo, washe baki yayi tare da bud'e k'ofar yana yiwa Sabeer sannu da zuwa, da D'an murmishi akan face nashi ya amsa mishi kafin ya wuce zuwa part d'in su.
Yana shiga part d'in ya tarar Mumy bata nan haka ma Daddy don haka kawai ya wuce bedroom nashi, bude shi yayi ya tarar da ko'ina tsaf sai kamshin air freshener yake tamkar yana gidan, sai duhun da d'akin ya d'an yi sannan yayi zafi don haka k'arasa wa yayi ya kunna ac da fanka tare da kunna light d'in d'akin, ajiye jakar yayi saman sofa sannan ya hau cire kayan jikin shi.
Yana gama cirewa toilet ya fad'a ya jima yana wanke jikin shi sosai a bathroom sannan ya d'aura alwala ya fito, lotion ya shafa tare da sanya white 3quater and T-shirt red colour mara hannu yayi kyau don kayan sun amshe shi, perfumes ya fesa different colours bayan ya taje kwantaccen gashin kanshi ya shafe shi da mayukan gyaran gashi tamkar wata mace.
Bayan ya kammala gyara jikin shi tukunna ya shimfid'a abin sallah, nan ya gabatar da sallahr la'asar bayan ya idar ne yayi en addu'o'in shi sannan ya fito zuwa parlor.
Tun daga kan steps d'in stairs ya hango Mumy zaune a saman dining table tana cin abinci, d'an girgiza kai yayi don ganin yanda Mumyn shi ta d'an rame alamar akwai abin da yake damunta cikin zuciyar ta, cikin tafiyar sand'a ya zagaya ta bayan ta ya sanya hannun shi dukka biyun ya rufe mata idonta yana murmishi.
Mumy na cikin cin abinci taji an rufe mata ido da farko ta tsorata amman da taji wani kamshin turaren tilon d'anta sai ta d'an nutsu don fuskantar wane, don tasan dai Sabeer baya gidan sai dai ko Daddyn shine yake son zolayar ta sai ta sanya hannun ta saman hannun wanda ya rufe mata idon tana kok'arin zame hannun shi, amman ta kasa zame hannun sai kok'arin cirewa take but Sabeer yak'i bud'e idonta yana yin wata dariya k'asa k'asa.
Cikin mak'e murya Sabeer yace "canki ko wane sai na bud'e miki ido "
Jin muryar Sabeer tayi ta rikid'e mata kamar muryar Daddy don haka tace
"My dear bud'e min ido please na ganka daman yau throughout ban ganka ba "
A hankali Sabeer ya zame hannun shi a eye's nata ya jingina bayan shi da jikin bango yana sakin murmishi, juyawa Mumy tayi da nufin ganin Daddy sai eye's nata suka hango mata tilon d'anta, tsabar mamaki ne ya hanata gasgata abin da ta gani sai da ta mutsutstsuke idonta sannan tace
"Sabeer! "
Da mamaki da kuma rud'ewa da ganin shi ta sake ambatar sunan shi kafin wasu hawaye su fara zubowa daga idanun ta kallon shi take tamkar yau ta fara ganin shi.
Shima wasu hawayen tausayin Mumyn tashi ne suka zubo mishi cikin sassarfa ya k'arasa ya tsugunna agabanta ya dire gwiwar shi a k'asa sannan ya d'ora kanshi saman cinyar ta, hannun ta take saman lallausan gashin kanshi tana shafawa ta kasa magana ma gaba d'aya.
Muryar shi na rawa hawaye na zuba yace
"Mumy baki yi murnar ganina ba koh, saboda ba'a son ranki na tafi ba, kina fushi da ni ne?"
Girgiza kai take yi lokacin da yake magana, cikin sanyin murya tace
"Bazan iya fushi da kai ba Son"
"To gashi kin sanya damuwa a ranki kin rame ba"
D'an murmishi tayi kafin tace "tunanin halin da d'ana yake ciki ne ya sanya ni ramewa da shiga tashin hankali,amman yanzu tun da nagan shi a gabana zan kwantar da hankali na "
"Mumy kenan, nayi kewar ku ke da Daddy wai yana ina ne? "
"I missed U too Son, Daddyn ka yana office bai dawo ba, yaushe ka dawo, zo kaci abinci "
Duk ta rud'e da ganin tilon d'an nata sai faman tambaya take watsa mishi akan lafiyar shi don ta d'an razana da ramar shi da ta gani da duhun da D'an yi, hannun ta ya kamo yana kallon ta kafin yace
"Mumy ki nutsu ni ina cikin lafiya sosai "
"Okay zo kaci abinci, me zan zuba maka? "
D'an shiru yayi kafin yace "ki ban duk abin da kika ci"
Cikin farinciki tace "okay Son taso ka zauna "
Haka ta kamo hannun shi ta zaunar dashi kusa da ita, kafin ta mik'e tsaye ta fara zuba mishi abincin, da kanta take bashi tana faman kallon shi tamkar wata sabon halitta a gabanta, ita kanta tasan tayi kewar d'an nata da yawa duk saboda matsiyar yarinyar nan d'anta yayi mata nisa.
"Mumy tunanin me kike ne ba gashi na dawo ba"
Da murmushi kan face nata tace
"Son kawai ina tunanin irin wacce wahalar kayi a k'auyen da ko wutar nepa babu "
"Haba Mum aikuwa suna da wuta sai dai ba'a fiye samu sosai ba"
D'an ta6e bakin ta tayi sannan tace "kuma kana iyacin abincin su naga duk ka rame kayi bak'i "
"Mum kibar wad'annan tambayoyin please "
"Shikenan Son na bari "
Tana gama bashi abincin suka koma parlor tana rik'e da hannun shi gane take tamkar zai sake guduwa ya barta, basu dad'e da zama ba Daddy ya dawo agajiye sosai yake, amman had'a ido da Sabeer yasa shi neman gajiyar tashi ya rasa nan suka yi hugging d'in junan su cikin tsananin k'aunar junan su.
Nan babu dad'e wa Family d'in D'an fillo dashi kanshi Dr Ahmad d'an fillo da Hajjah Hauwaa suka samu labarin dawowar Sabeer, nan suka dunga shigowa ganin Sabeer kusan dukkanin su sunyi