Showing 33001 words to 36000 words out of 122360 words
Chapter 12 - A sanadin Son ki Hausa Novels Document complete by Aisha A Muhammad Sanaz.txt
ba sai ke ina son ki bani had'in kai na nemi soyayyar ki auren ki nake son yi da gaske Suhaim..... "
Kasa k'arasa abin da zai fad'a yayi sakamakon ganin Suhaima da yayi a tsaye tana girgiza kanta cikin wani irin yanayi wanda na kasa banbance na tsoro ne ko na firgita da tayi daga jin abin da Sabeer ya fad'a mata.
Mik'e wa tsaye shima yayi tare da cewa " ina son ki! Ina son ki Suhaima zaki aure ni? "
Toshe kunnen ta Suhaima tayi da dukka hannun ta biyu don batason jin abin da Sabeer yake ce mata tana cewa
"Bana son ka Sabeer bazan iya auren ka zaka iya neman wata "
Tana gama fad'i haka ta juya zata fita daga parlourn da tasan wannan shirmen maganar zai fad'a mata da bata biyo shi ba balle ta tsaya sauraren shi don ko a mafarki bazata ta6a aminta da abin da Sabeer ya fad'a mata balle ido biyu.
Fisgo hannun ta yayi da k'arfi wanda ya sanya ta fad'a wa cikin jikin shi ta buge kanta da faffad'an k'irjin shi, d'ago kanta yayi da dukka hannun shi biyun ya matse kan nata da k'arfi wanda ya sanya d'an kwalinta ya fad'i lallausan dogon gashin kanta ya bayyana a sarari, kallon shi Suhaima take wanda taga idanun shi sun yi ja sosai idan ba gizo idanun ta suke tamkar ruwan hawaye take hangowa cikin eye's nashi, ko kwakkwaran motsi ta kasa saboda rik'e mata kan da yayi cikin kakkausar murya yace
"K'arya kike Suhaima dole ki soni tun da har na soki, ina son ki fad'a min kina sona? "
Duk da tsoro da fad'uwar gaban da Suhaima take ga kuma zafin matse mata kan da yayi sai da ta bud'e baki tace
"Sabeer na fad'a maka bana son ka ba'a so dole ka rabu da ni please you're hurting me"
Idanun shi na zubar hawaye yace
"Are you sure baki sona? "
"Yes I'm very sure "
Cikin tabbatar wa Suhaima ta fad'a ba tare da shakka ba, a hankali taji ya cika ta ya koma ya zauna jagwab saman kujera kafin ya had'e kan shi da gwiwa hawaye ne masu zafin gaske suna zuba a idon shi yau wai Shi Sabeer Hussein d'an fillo mace yarinya k'arama take cewa bata son shi why? "
Suhaima kuwa ranta a 6ace ta d'auki d'an kwalinta ta daura tana me shafa wuyanta da d'an k'age, ko kallon inda Sabeer yake bata yi ba ta fita daga gidan ta barshi.
Ta d'auki wajen 10 minutes a tsaye ta rasa inda zata nufa sai ta ga motar Sabeer wanda yayi amfani da ita yanzu kauda kanta tayi gefe guda ganin an tsaya.
"Yalla6ai yace ki shigo na mayar da ke gida "
Wata murya ta daban ta furta mata hakan, kallon wajen tayi ta ga wani bak'on fuska ne ba Sabeer ba ne, ajiyar zuciya ta sauke kafin ta shiga motar bayan ya bud'e mata k'ofar motar.
Babu dad'e suna tafiya ba aka suka k'araso gidan su Jiddah bayan yayi parking ta kwashe kayan ta da tayi shopping ta fito daman a motar ta bar su, tana shigowa d'akin Jiddah sak'on harara ne ya fara ziyartar Suhaima a wajen su Zahra da sauran cousin's d'in Jiddah sa'annin ta, bata kula su ba ta k'arasa wajen Jiddah taya zata iya aminta da soyayyar Sabeer alhalin 'yan uwan shi suna kyamatar ta bazata kai kanta cikin matsala ba.
Daga baya ma sai suka zame suka bar musu d'akin daga Jiddah sai Suhaima, nan Suhaima ta bawa Jiddah gift's din da ta siyo mata hannu biyu Jiddah tasa hannu ta kar6a tana yiwa Suhaima godiya, tuni Suhaima ta watsar da abin da ya faru da ita da Sabeer ta fara harhad'a kayanta don gobe ana gama bud'an kai Yaya Aliyu zai zo ya d'auke ta zata koma k'auyen su inda hankalin ta zai fi kwanciya.
Da dare kuma dinner d'in da friends na ango suka had'a aka gabatar wanda iya k'awayen amarya da na ango ne kawai, daga nan kuma aka wuce da amarya gidan ta wanda yake nasarawa GRA gidan ya had'u sosai, nan Suhaima da 'yan uwan amaryar suka kwana.
Washe gari kuma da safe akayi walima anan farfajiyar gidan nata wanda ya had'a manyan malaman addinin musulunci mata suka gabatar da lectures akan rayuwar aure da tarbiyyar yara zuwa 1 aka tashi daga walimar bayan anci an sha.
Sallahr azahar Suhaima tayi bayan ta idar ta ne babu dad'e wa Yaya Aliyu yayi wa Jiddah waya yana k'ofar gidan, nan Jiddah da Suhaima suka rungume junan su suna kuka sosai dakyar dai Suhaima ta zame jikin ta ta d'auki bag nata suka fito babu wanda Suhaima tayi wa sallama cikin families d'in Jiddah don basu yi maraba da bak'unta suka yi ba.
Har compound d'in gidan Yaya Aliyu ya shigo suka gaisa da Jiddah tare da bata hak'urin rashin zuwan su da basu yi ba saboda jikin Aliyah sai a hankali, nan ta nuna ba komai yayi mata fatan alkhairi na zama lafiya, sannan suka yi Jiddah sallama suka tafi bayan kayan da Jiddah ta had'a wa Suhaima sosai, tana tsaye a wurin har suka fita daga gidan kafin ta koma ciki tana zubar hawaye na kewar Suhaima don tasan zasu kwana biyu basu had'u ba sai a waya.
Bayan Yaya Aliyu ya tada machine d'in shi suka fara tafiya Suhaima na bashi labarin yanda bikin ya kasance amman ba komai ta sanar mishi ba don bata sanar shi had'uwar ta da Sabeer ba da kuma yanda 'yan uwan Jiddah suka kar6e ta, murmishi kawai Yaya Aliyu yake na jin dad'in ganin tilon k'anwar tashi cikin koshin lafiya.....
Sai dai kuyi manage da page d'in nan ban samu time d'in da zan yi editing ba, mu had'u a next page don jin ko Sabeer zai hak'ura da Suhaima? Ko mai zai kasance a gaba?...
Aishat A Muh'd ✍🏻
A SANADIN SON KI
Written by
Aishat A Muh'd
♻ EXCLUSIVE WRITER'S FORUM
Dedicated to my Sadeey saNaz
PAGE 42-43
Bayan sun k'arasa gida ne Yaya Aliyu nayin parking d'in machine Suhaima ta sauka da d'an gudunta ta nufi k'ofar shiga gida, a zauren gidan suka yi ki6is da Aunty Aliyah fuskar ta d'auke da murmishin farinciki, rungume Aunty Aliyah tayi cikin farinciki tace
"Aunty nayi kewar ki "
Cikin murmishi Aunty Aliyah tace
"Nima haka Suhaima ba k'aramin kewar ki nayi ba, tun da kin dawo lafiya Alhmdullilah naji dad'i "
"Aunty ya jikin ki da babyn mu? "
"Jiki Alhmdullilah Suhaima, ya kika baro Jiddah amarya? "
"Jiddah mun kaita gidan ta Aunty yayi kyau gidan tace tana gaida ke nayi miki sannu da jiki kuma ta gode sosai, bari dai anjima zan baki labarin yanda bikin ya kasance"
'Yar dariya Aunty Aliyah tayi tare da kamo hannun Suhaima suka wuce cikin gida, suna shiga Yaya Aliyu ya shigo hannun shi d'auke da bag d'in Suhaima da sauran kayan da Jiddah ta had'a wa Suhaima su.
A tsakar gida ya tarar dasu a zaune saman tabarma Suhaima na yiwa Aunty Aliyah hira, d'an murmishi yayi kafin yace
"Oh Suhaima surutu ko hutawa baki yi ba zaki dame mu da surutu "
Dariya Aunty Aliyah tayi yayin da Suhaima ta turo baki na shagwa6a tace
"Kai Yaya daga dawowa ta zaka ce na dame ka da surutu bayan yanzu Aunty tace lokacin da na tafi har d'akina kake shiga ka zauna ciki saboda kewa ta da kayi "
Dafe goshin shi yayi yana girgiza kai kafin yace
"Oh Aliyah har kin sanar mata me yasa kika fad'a wa wannan sarkin surutun? "
Aunty Aliyah na dariya tace "ai gaskiya ne gwara na fad'a mata tasan ni da Yayan ta mun damu da ita sannan munyi kewar ta na tsayin kwanaki biyu "
"Yawwa Aunty naji dad'i da kika fad'a min, kai kuma Yaya nayi maka yajin aikin magana na minti d'aya "
Dariya suka kwashe da ita kafin Yaya Aliyu ya janyo hannun ta zuwa kusa dashi ya zaunar da ita, cikin k'asa da murya yace
"Haba 'yar k'anwata ayi wa wannan Yayan naki afuwa bazan iya jurewa ba "
Rungume shi Suhaima tayi kafin tace "Yaya ina son ka ina alfahari da kai Allah ya bar ka da Aunty Aliyah, Allah ya jik'an Umma "
Jikin su ne yayi sanyi sosai nan yasa hannun shi ya bubbuga bayan ta tare da cewa "Amin Suhaima, maza kije kiyi wanka kizo Babaa Lantana tayi miki gashin kaza mai dad'i irin wanda kike so"
K'ara yin kasa da murya yayi kafin ya cigaba da cewa "amman fah mun ci miki ni da Auntyn ki "
D'an murmishi Suhaima tayi tare da cewa "bakomai Yaya nah Aunty babyn mu yake so ci ai, kai kuma Yaya kwad'ayi ne koh? "
Dariya suka sanya dukkan su kafin Suhaima ta tashi d'aukan kayan nata tayi zuwa cikin d'akin ta, lumshe idon ta tayi saboda shak'ar k'amshin turaren wuta da taji ya daki hancina kafin ta bud'e idon, d'akin fes yake ko'ina a gyare tsab kamar tana nan, cire kayan jikin ta tayi ta d'aura wani zani wanda take wanka dashi sannan ta fito daga cikin d'akin zuwa tsakar gida inda toilet yake.
Yaya Aliyu da Aunty Aliyah suna nan zaune suna hira, ruwan d'umi ta gani akan murhu nan ta d'iba bokitin wanka ta had'a da ruwan sanyi dai dai yanda take buk'atar ruwan ya kasance ta d'auka ta nufi toilet.
Tana shiga ta ajiye bokitin har zata cire zanin ta sai ta had'a ido da abin da tafi tsana wato cockroach aikuwa ta runtse ido tare da sakin ihu da k'arfi ta fito, wanda ya sanya Yaya Aliyu da Aunty Aliyah taso wa da sauri, da gudu Aliyu ya nufi inda Suhaima take ya rik'e ta k'am yana cewa
"Suhaima meyafaru lafiya? "
Kusan lokaci d'aya suka yi mata maganar, cikin rawar murya tace
"Yaya kyenkyaso ce a cikin band'akin "
Shafa kanta yayi da hannun shi d'aya d'ayan hannun kuma yana goge mata hawayen fuskarta, tun Suhaima na k'arama yasan ta tsani wannan kwaron duk lokacin da ta ganshi ba k'aramin tsorota take ba shi yasa yake yawan yi feshin maganin kwari saboda ita.
"Kiyi k'anwata bari na fitar miki da ita kin ji? "
D'aga kanta tayi kafin ta cikata ta rik'e Aunty Aliyah, toilet d'in ya shiga da tsintsiya ya maketa tukunna ya fito da ita ya yar cikin shara, sai lokacin hankalin Suhaima ya d'an kwanta amman duk da haka sai da tace
"Yaya ka duba babu wata "
"Na duba Suhaima babu komai kije kiyi wankan ki "
A tsorace ta shiga band'akin don ji take kamar zata sake ganin wata ko ma ta hak'ura da wankan gaba d'aya, yayin da suka juya suka koma inda suke zaune suna hirar su daga k'arshe Aliyu ya fita daga gidan gaba d'aya.
Sai fitowa daga wanka tayi taga baya nan sai Aunty Aliyah a zaune, tsokanar ta ta fara yi na ihun da take musu murmishi kawai tayi ta shige d'aki, shiryawa tayi cikin wata gown mara nauyi mai k'aramin hannu ta gyara gashin kanta sannan ta sanya hula ta fito nan inda Aunty Aliyah take zaune hira suke tana cin gashin naman da akayi mata cikin jin dad'i saboda dad'in da yayi mata bayan ta gama ci ta d'ora da madarar shanu mai d'umi, suna nan zaune akayi kiran sallahr mangarib suka yi alwala kowa ya wuce dakin shi don gabatar da faralli.
******************
Tun lokacin da Sabeer ya zube kan kujera ya had'e kanshi cikin jikin shi, yana jin fitar Suhaima ya kirawo driven shi a waya yazo ya kai Suhaima gida yana gama wayar ya koma ya kwanta saman kujera ya tuk'unk'une jikin shi waje d'aya hawaye ne masu zafi suke zuba cikin idon shi.
Wai shi yau yarinya k'arama take duban tsabar idon shi tace bata son shi, wad'anda suka fita girma da komai ma na wayewa suna nuna mishi so tamkar su cinye shi amman ita ta samu ma yace yana son ta zata wulak'anta shi, wayyo Allah nah yanzu ya zanyi gashi son yarinya ya shiga zuciya ta dole nasan yanda zan shawo kanta ta amince ta kar6i soyayya ta, duk wannan maganar cikin zuciyar shi yake tashi zaune yayi idon shi sunyi ja sun kumbura kallo d'aya mutum zai mishi yasan cewa yayi kuka daman abin ka da shagwa6a66e bashi d wahalar yin kuka, kanshi ciwo yake tamkar ya cire haka yake ji.
"Dole ki soni Suhaima sai nasan yanda nayi na cusa miki son na cikin zuciyar ki, A SANADIN SON KI zan iya shiga kowacce matsala na sani amman har idan zan samu nasarar ki soni komai mai wuce wa "
Yana gama fad'in haka ya tashi tsaye kafin kuma ya fita daga parlourn a compound na gidan ya had'u da driven da ya mayar da Suhaima gida mota kawai Sabeer ya shiga ya zauna nan driven ya gane me yake nufi da sauri shima ya tashi ya shiga motar yayi mata ya tada ita suka fita daga gidan.
"Yalla6ai ina zamu je? "
Driver ya buk'aci son inda zasu je, dakyar Sabeer ya iya cewa "gida zaka kai ni"
Yana gama fad'in haka yayi shiru nan driver ya cigaba da tuk'i har suka k'arasa gida ko gama dai daita parking bai yi ba Sabeer ya fito daga motar.
Daf da zai shiga part d'in su ya kusan cin karo da Alhj Alhmad d'an fillo wato kakan shi, ganin Sabeer d'an lele a yanayin da bai ta6a ganin shi a haka ba yasa gaban shi ya fad'i tare da kamo hannun shi yace
"Sabeer what wrong with U?"
Fincike hannun shi Sabeer yayi tare da yin gaba don gaba d'aya ba'a cikin nutsuwar shi yake ba yana tafiya hawaye na zuba cikin idon shi "
Cikin tashin hankali Alhj Ahmad ya bishi a baya yana kiran shi amman ko waiwayen shi bai yi ba, yana shiga parlourn a dai dai lokacin mai aiki ta fito daga kitchen hannun ta d'auke da babban farantin saman shi foodflaks ne da plates zata jera a dinning table.
Sabeer yana k'arasa wajen zai haura stairs ya sanya hannun shi ya ture abin da ke hannun ta, ai kuwa gaba d'aya tayi baya ta zube haka foodflaks da plates din suka zube a k'asa na fashewa suka fashe, ko takan ta Sabeer bai bi ya haye stairs still kuma hawayen na zuba don ya kasa rik'e su zuciyar sai bugawa take da k'arfi kanshi yana mishi ciwo sosai.
Duk wannan abin akan idon Alhj Ahmad aikuwa ya dad'a rud'ewa sosai ya bi bayan Sabeer da sauri, haka ma Mumy wadda take kitchen k'arar fad'uwar abu ya fito da ita da sauri hango tilon d'an nata tayi yayi upstairs kamar a fusace ga surukin ta yabi bayan shi ya sanya itama ta bisu cikin tashin hankali.
Babu wanda ya kula 'yar aikin haka ta tashi cikin sanyin jiki da zafin fad'uwa ta fara tattara wajen da ya 6aci dakyar take aikin saboda ba karamin buguwa tayi ba da alama wani abin ne ya faru da d'an lelen don ba haka Sabeer yake musu ba sai dai idan ranshi ya 6ace shi da Jiddah su kad'ai ne masu kirki a gidan.
Kai tsaye bedroom d'in shi ya wuce yana shiga ya rasa me yake mishi dad'i gaba d'aya zuciyar shi da idanun shi Suhaima suke son gani muryar ta suke son ji.
"Bana son ka Sabeer bazan iya auren ka ba "
Muryar Suhaima yaji cikin kunnen shi tamkar a lokacin take furta mishi hakan, runtse idon shi yayi da k'arfi yace
"Nooo Suhaima sai kin so ni!"
Ya k'arasa fad'in haka yana zubar da kayan saman dressing mirror a k'asa nan perfumes wasu suka faffashe, nan ya dawo cilli da pillows d'in kan bed da na sofa cikin lokaci kad'an ya hargitsa d'akin cilli yake da duk abin da ya samu saboda ya rasa yanda zai yi kuwwar muryar Suhaima ce take mishi amo a kunnen shi.
Yana kok'arin zubewa a k'asa ne yaji an rik'o shi kallon wanda ya rik'e shi yake sai yaga Alhj Ahmad ne ga Mumyn shi kuma a gefe tana kuka hankalin ta a tashe sosai me yake damun Sabeer d'in ta, kwace jikin shi yayi ya samu k'asa ya zauna cikin tashin hankali Alhj Ahmad yace
"Sabeer me......? "
D'aga mishi hannu Sabeer yayi tare da cewa "ku fita ku ban waje "
"What! Kana nufin zamu tafi mu bar ka a wannan halin? "
Idanun shi sun ja haka fuskar shi ma ga hawaye suna zuba ya d'ago kanshi ya kalle shi, sai da gaban Alhj Ahmad da na Mumy ya fad'i ganin yanda Sabeer ya koma tamkar ba Sabeer d'in da suka sa ni ba. Cikin magana da k'arfi yace
"Leave me alone please don't disturbing me".
Yana gama fad'in haka ya sanya hannun shi dukka biyun cikin gashin kanshi yana hargitsawa su kuma kallon shi suke tamkar wasu sokaye sun rasa abin yi dakyar Alhj Ahmad ya zauna yana goge hawaye don ya d'auka Sabeer ya haukace haka Mumy ma kuka take sosai, sun dad'e a haka kafin ya tashi ya shige bathroom ya sakarwa kanshi shower, ya dad'e sosai a ciki kafin ya fito d'aure da towel.
Ko'ina an gyara tsab tamkar ba yanzu ya gama hargitsa d'akin ba, kwanciya yayi kan bed yana tunanin ta inda zai fara shawo kan Suhaima don yafi jin haka fiye da shawo kan iyayen shi...
Ya kuka ji page d'in