Showing 60001 words to 63000 words out of 122360 words

Chapter 21 - A sanadin Son ki Hausa Novels Document complete by Aisha A Muhammad Sanaz.txt

5 minutes kayi sauri don kada dare yayi mana "
"Okay Daddy yanzu zan dawo "


Yana gama fad'in haka ya wuce da D'an saurin sa don yiwa Suhaima sallama, bashi ya taho ba sai da ya kusan 30 minute's sannan ya dawo su Daddy sai tsokanar shi suke shi dai kawai murmishi yake nan suka yi sallama cikin farinciki suka tafi gida.....






Aishat A Muh'd ✍🏻
*A SANADIN SON KI*






Written by
Aishat A Muh'd


Dedicated to my Sadeey SaNaz










*PAGE 71-72*










Sai bayan mangarib su Sabeer suka k'arasa gida, yana shiga part d'in su ya hango Mumy kusa da dining table tana shirya abincin dare fuskarta d'auke da damuwa wanda mutum kallo d'aya zai mata ya karanci hakan.


Yana zuwa ya rungume ta tare da bata peck a cheek d'in ta cikin farinciki yace
"Mumy yau ina cikin farinciki sosai na kusan mallakar Suhaima ki tayani murna "


Wani abu ne ya tokare mak'oshin Mumy wanda ya sanya ta d'an jimawa kafin ta bud'e bakinta tace
"Son nasan ka gaji da yawa kaje kayi wanka da sallah tukunna "


Ta k'arasa maganar cikin murmishin yak'en da yafi mata kuka ciwo, da yake Sabeer na cikin farinciki shi ya hanashi fahimtar yanayin Mumy, don haka kawai sai ya wuce up stairs.


Bin bayanshi da kallo Mumy tayi kafin ta zauna saman kujerar dining table ta zabga uban tagumi, duk wannan abin da suke Daddy yana kofar shigowa parlourn yana kallon su.


Ganin Mumy ta zauna ta zuba tagumi ya sanya shi k'arasa wa cikin parlourn hannun shi ya sanya ya janye tagumin da tayi kafin yace
"Haba sweetie nah me yasa kike son shiga tsakanin farincikin d'anki, kinsani Suhaima itace farincikin Sabeer yana sonta rabuwa da ita ba k'aramin wani hali zai shiga ba, a matsayin ki na uwa kina mishi addu'ar fatan Alkhairi a wannan auren nashi, ni kaina da fari ban yarda ba da hakan ba, zama nayi tare da yin nazari kafin na amince mishi sannan da naje yau naga gidan da Son yake neman aure sai naji hankalina ya sake kwanciya da wannan auren don kuwa gidan gidan mutunci ne sosai, ina son ki kwantar da hankali kada wani ciwo ya shige ki matar mutum kabarin shi Allah yayi Suhaima ce zata kasance matar d'anki don haka kawai ki bisu da fatan alkhairi "


Yana gama fad'in haka ya tashi ya wuce side d'in shi don kada a kirawo sallahr ishsha bai yi ko mangarib ba, Mumy tasan Daddy gaskiya ya fad'a mata but zuciyar ta tak'i amincewa da hakan.




Bayan Sabeer yayi wanka tare da yin sallahr mangarib da ishsha ne, ya zauna saman sofa yana kok'arin kiran Suhaima hannun shi d'aya kuma yana rik'e da cup aciki fresh milk ce don baya jin zai iya cin abincin dare cikin shi a k'oshe yake ji Babyn shi ta cika mishi ciki.




Lumshe idanun shi yayi jin sanyayyar murya Suhaima tana tambayar shi sun je gida lafiya, sake gyara kishingid'a yayi tare da cewa
"Alhamdullilah Baby mun isa gida lafiya yanzu kin ganni a d'aki ni d'aya duk nagaji "


"Ayyah sannu "
Cewar Suhaima cikin tausayin shi.


"Da munyi aure Baby nasan da ban da matsala zaki min tausa har na warware bama iya tausa ba har irin wanka da....... "




Bata bari ya k'arasa maganar ba da sauri cikin jin kunya tace
"Kaiii Sabeer baka jin kunyar fad'in wannan maganar? "


"Keee Baby bana jin kunya indai da ke zanyi irin wannan maganar"
Ya fad'i hakan cikin kwaikwayar maganar ta, dariya suka d'an yi kafin yace
"Baby ina son ki da yawa kada ki wahalar da rayuwa, kada kiyi amfani da son da nake miki ki wahalar dani please "


Ya k'arasa maganar kamar zai fashe mata da kuka, wani tausayin shine ya rufe Suhaima tare da wani irin son da yake k'ara shiga cikin zuciyar ta.




"Sabeer don me zan wahalar da rayuwa bana fatan na kasance daga irin wadannan mutanen masu amfani da son da ake musu suke wulak'anta mai son su, ina maka son da bazan jure ganin ka cikin wahala ba balle ni na wahalar da kai, daga lokacin da ka zama mijina zan kasance mai yi maka biyayya dai dai iyawata"


Wata ajiyar zuciya ya sauke wadda har sai da Suhaima ta jiyo shi kafin yace
"Naji dad'in abin da kika ce Baby nah thank U very much"


"Uhmmm "
Abin da tace kenan, d'an murmishi yayi yana cewa
"Baby ya neh koh bacci ya fara zuwa ne? "


"A'a me kagani? "
"Just naji kin ce uhmm"
"Ba komai "
"Okay bari na barki ki huta gud night and sweet dreams "
"Same 2 U"
A haka suka yi sallama kowa ya ajiye waya.






Soyayya mai zafi suke nuna wa junan su tsakanin Sabeer da Babyn shi, duk wata kulawa wanda ya kamata suna bawa junan su, soyayya mai tsafta suke nunawa junan su, yayin da Daddy ya matsantawa Mumy da dole ita zata had'a lefen Sabeer saboda da fari da yayi mata maganar k'in amincewa tayi sai da yayi da gaske sannan ta yarda dakyar, ta 6angaren su Suhaima ma Yaya Aliyu da Aunty Aliya sai shirye shirye suke yi sosai na hidimar biki.


Sabeer sai da ya nunawa Aliyu kada ya sha wahalar yi mata kayan d'aki zuwa kitchen don shi tuni ya gama shirya musu gidan su shi da Babyn shi, amman sam Yah Aliyu yak'i yarda ya kafe sai yayi dole tasa Sabeer hak'ura tunda baisan dalilin shi ba.




*** **** ***




*_After 2 week's_*




"Hello Suhaima kina jina? "
"Ehh Jiddah ina sauraren ki "
"Yawwa Babyn Yah Sabeer gobe ina son zuwa zamu tattauna akan maganar bikin fah"


Cikin rashin fahimta Suhaima tace
"Kamar wanne shiri? "


Hararar ta Jiddah tayi duk da tasan ba gani zata yi ba tun da a waya suke magana tace
"Har kinsa na harare ki wallahi, da kin d'auka zamu yi biki lami ne kamar bikin Yah Sabeer da Besty na ai dole mu kwashi shoki "


Dariya Suhaima ta tuntsire da ita kafin tace
"Kinyi nauyin zaki kwaso shokin a haka? "


"Dallah malama ina ruwan ki sai fah anyi duk wani zagaye zagayen ki yarinya "


Suhaima na dariya tace
"Toh sarkin masifa naji na yarda "
"Yawwa ko kefa, kin ga zan d'auko mai gyaran jikin da zata yi miki ke dai kawai sai nazo don my dear ya dawo gud night "


"Okay Allah ya kaimu "
"Amin kiyi min d'an wake don Allah "
"Zanyi miki kodan Babyn mu "
Dariya suka yi kafin su yi sallama, sauke numfashi Suhaima tayi tare da gyara kwanciyar ta, wayar ta ne ya sake k'ara nan ta d'auka da sauri ganin Sabeer ne, hirar su ta soyayya suka sha sosai kafin su yi sallama, addu'ar bacci Suhaima tayi babu dad'e wa bacci mai dad'i ya d'auke ta..........






_Fan's kuyi hak'uri da page's d'in nan don ban samu damar yin editing ba dafatan za'a yi min afuwa duk inda aka ga error typing_




Aishat A Muh'd ✍🏻
*A SANADIN SON KI*






Written by
Aishat A Muh'd


Dedicated to my Sadeey SaNaz










*PAGE 73-74*










Washe gari kuwa tun safe bayan ta gama had'a breakfast ta karya nan ta gyara d'akin ta tsaf da tsakar gidan zuwa wankin toilet da wanke wanke sannan ta fara yiwa Jiddah d'an waken da take buk'ata, wanda ta hada filawa da garin rogo kad'an a ciki.




Bayan ta gama yin d'an waken ta ne ta daka mata yaji mai dad'i wanda yasha citta da garlic sannan ta yanka cucumber, tomatoes and onion, tana kammala wa ta wuce wanka, bayan ta fito ta shirya kanta cikin wani lace black and touch flower's pink colour d'inkin riga da skirt ne sunyi mata cif tayi kyau kam abinka da farar fata, tana cikin fesa perfumes ne ta jiyo muryar Aunty Aliya tana fad'in


"Ashe kai ne tafe sannu da zuwa "
D'an mamaki ne ya kama Suhaima ita dai tasan Sabeer baice mata zai zo ba, Jiddah ce ta sanar mata zuwan ta, amman bari taje ta duba ko bak'on Aunty Aliya ne, don haka sai ta janyo wani k'aramin veil pink tayi rolling dashi sannan ta fito.


Kusan suman tsaye tayi ganin Sabeer da suka had'a ido dashi yana jifanta da wani sanyayyan murmishi har da wani d'aga mata gira.


Tana kok'arin k'arasa wa inda yake ta jiyo sallamar Jiddah don haka sai kawai ta juya da sauri ta taro ta cikin farinciki, cikin tsokana tace
"Maman twin's sannun ki da zuwa "
"Yawwa Amaryar mu wallahi har kin fara kyallin amarcin gashi sai wani cika kike mene sirrin me Aunty Aliya da Yah Aliyu suke baki ne?"




D'an murmishi Suhaima tayi tana sunkuyar da kai tare da cewa
"Ke koh! Kin cika surutu"
Ta k'arasa fad'i tana turo bakin ta, dariya Jiddah tayi kafin tace
"Allah zan fad'awa Yah Sabeer idan ya kama wannan bakin kada yayi mishi ta sauk'i tunda aikin shi murgud'a baki da turo shi sai ya koya mishi h...... "
Kafin ta k'arasa fad'in hankali sai kawai ta had'a ido da Sabeer yana faman kallon su, turus taja ta tsaya saboda mamaki kafin kuma ta wayance tana cewa


"Ah Yah Sabeer kai ne?"
Yana d'an hararar ta yace
"A'a bani ba ne "
Er dariya tayi tana k'arasa wa inda yake tana cewa
"Ayyah Babban Yaya ban kula da kai ba ne "
"Dole kice haka tunda gulma ta rufe miki idon tun da kika shigo kike gulmata ina kallon ki "






"Kaiii Yaya ni ba gulmar ka ba fah nayi ba hirar mu muke ko Suhaima?"
Ta k'arasa maganar da shagwa6a tana langa6e kai ta kalli Suhaima tana kifta mata ido alamar kada ta sanar shi abin da ce, batasan duk yaji ta ba d'auke kai kawai yayi yana murmishi shi dai kusan tsaf familyn shi sun d'an fi jituwa da Jiddah saboda kusan halayyar su d'aya, dariya Suhaima take kafin tace
"Ni ba ruwana bansan me akai ba "
"Auuu! Haka ma zaki ce shikenan "
Tana gama fad'in haka ta mik'e fuuu tare da wuce d'akin Aunty Aliya, er k'aramar dariya Suhaima ta saki don Jiddah ta bata dariya, yayin da Sabeer yake binta da kallo cike da sha'awa don sosai dariyar tayi mata kyau dimples nata da yake so duk sun fito.




Ganin yanda yake bin ta da kallo ne yasa ta d'an tsargu ta nutsu kafin tace
"Au ashe bamu gaisa ba, ina kwana? "
Ta fad'i tana rufe bakin ta da hannu, d'an murmishi yayi yana cewa
"Baby bana cikin nutsuwata gaba d'aya "
Gabanta ne ya d'an fad'i kafin tace
"Subhanallah me yasa meka? "
Fuskarta d'auke da damuwa ta furta hakan.


"Baby abin da yake damuna lokacin auren mu yayi nisa da yawa, 2 month's fah aka sanya ni da nafison 3 week's, yanzu gaba d'aya fah 2 week's muka ci acikin wata 2 "




Kallon shi take kawai idan banda abin Sabeer wata biyu nawa yake idan Allah ya basu aron rai, wasu ma shekara ake sanya wa ko wata 6 amman basu damu ba sai shi, amman sai ta danne mamakin ta saboda ganin yanda duk ya koma sai fitar da huci yake idanun shi har sun d'an canja launi saboda damuwa gashi ya wani kafeta da ido tamkar zai had'iye ta haka yake jin shi ga tsugunnawar da tayi ta k'ara wani sanya tunanin cikin zuciyar shi sai a lokacin ya sake tabbatar wa Suhaima yarinya ce k'arama.




Anya bazai d'aga mata k'afa ba yana ganin tamkar zai iya cutar da ita a yanda yake jin shi, amman da wuya ya iya juriyar hakan don ma yau yaga ta k'ara cika kamar yanda Jiddah ta fad'i ga hips nata da boobs nata sun dad'a fitowa, wani had'iyar yawu yayi lokacin da ya kai idanun shi kai wanda ya sanya shi kusan kwarewa, da sauri ya kau da kai lallai Annabi yayi gaskiya da yace kada kana kallon matar da ba taka ba don bakasan inda idanun ka zasu kai gashi yau idanun shi sun ja mishi ganin abin da zai hanashi bacci cikin jin dad'i, daman can ba wani jin dad'in baccin yake ji ba tun lokacin da idanun shi suka fara ganin Suhaima.




Muryar Suhaima da yaji ne yasa shi d'ago wa ya kalleta yana sauke ajiyar zuciya, sai da gaban ta ya fad'i da ganin yanda eyes nashi da face nashi suka canja, cikin kwantar da murya tamkar mai rad'a tace
"Sabeer bana son kana sanya damuwa cikin ranka kada ya janyo maka wata matsalar please , wata 2 d'in kamar yau ne"


D'an murmishin yak'e yayi kafin yace
"Ba komai Baby na hak'ura amman ki tabbatar idan kika zo hannuna Hmmm.... "


Yak'i k'arasa maganar tashi, cikin rashin fahimta tace
"Kamar ya idan nazo hannun ka? "


"A'a ba komai Baby "
Ya k'arasa maganar da dariyar mugunta a d'an tsorace ta kalle shi don ta gama tsarguwa, ganin haka ya sanya shi danne dariyar shi don kada ya tsorata ta yace
"Calm down Baby matsoraciya ba fah wani abun nake nufi ba, yanzu me zaki ba ni naci? "


Ya fad'i hakan yana bagarar da zancen don baya son ta sanya shi a ranta.


"Me kake so nayi maka? "
"Baby fura ma ta isheni"


"Ita kadai kawai? "
D'an girgiza kai yayi kafin yace
"Kaiii Baby anya zan iya shan furar nan kuwa kada ta dame ni fah "
D'an zaro ido kad'an tayi sannan tace
"Furar ce zata dame ka, me take maka? "
D'an murmishi yayi sannan yace "zaki san kome take min amman ba yanzu "
Ya fad'i yana d'aga mata gira kan ya cigaba da cewa
"Eh Baby kiyi min kunun da kike min zan je na dawo "
"To shikenan "




Daga haka ya mik'e ya fita, ita kuma ta fad'a falon Aunty Aliya ta tarar da ita suna hira da Jiddah.


Jiddah na ganin ta ta harare ta kan tace
"Shine nace zan zo kika fad'a mishi yazo koh? "


D'an murmishi Suhaima tayi tana cewa
"Kinsan Allah Jiddah bansan da zuwan shi ba ko da safe munyi waya bai fad'a min, idan ya fad'a min zai zo ai zan fad'awa Aunty Aliya koh? "


Murmishi kawai Aunty Aliya tayi,
"Ni fah kinsan abubuwa zamu tattauna masu mahimmanci kin je kun wani lik'e kuna hira "
Er kunya ce ta kama Suhaima don ga Aunty Aliyah a zaune a wurin, d'ago kanta tayi ta harari Jiddah tana tuna mata da akwai Aunty Aliya a wurin fah.


Dariya Jiddah ta sanya kafin tace
"Uhm sabon salo yau ke ake jin kunya Aunty Aliya fah "


Dariya tayi sannan tace
"Allah ya shirya ki Suhaima yau wani sabon salon aka fito dashi to wallahi tun wuri yarinya ki cire iyayin kunyar da kika yafa a toh"
Cewar Aunty Aliya kenam dariya suka sanya kafin Jiddah ta k'ara cewa
"Yanzu sai ki kawo min d'an wake na mu fara maganar da ta kawo ni koh yah amaryar mu? "






"Ban yi ba kuwa don ki ji"
"Tabd'ijam yarinya kinma isa tun wuri kije ki kawo min "


Tashi tayi tana murmishi taje ta kawo mata duk ta zuzzuba ta yawun Jiddah har wani tsinkewa yake, tana gama hadawa ta mik'a mata, kar6a tayi tana cewa
"Da kuwa baki yi ba da sai na kaiwa my dear k'arar ki kuma yau sai anganmu a rana "
Dariya Suhaima tayi tare da cewa
"Aci lafiya Maman twins"


Mik'e wa Suhaima ta sake yi don tafiya yiwa Sabeer kunun da yake buk'ata, kallon ina zaki je Jiddah tayi mata duk ta wani tsatstsare ta da idanu abin ya bawa Jiddah dariya don haka tace
"Keee Jiddah irin wannan tsatstsare ni da eyes haka "


"Dole na tsatstsare da ido mana naga kin mik'e kuma kinsan ban da ishashshen time da wuri zan koma "


"Had'a mishi kunu zanyi yanzu zan gama"
"What! Wa zaki had'a wa kunu Yah Sabeer koh? "
"Eh shi "
"Tabbb aini tun da nagan shi nasan yau bazai barmu yin abin da ya kamata ba wallahi duk tak'ura mana zai yi ji har da wani cewa kiyi mishi kunu tsabar sanya mutum aiki "


"Eh d'in ina ruwan ki tun da bake aka sanya ba "
Ta k'arasa fad'i tana murgud'a bakinta tabar d'akin, Jiddah wadda ta saki baki tana kallon Suhaima da D'an k'arfi yanda zata ji tace


"Eheyyy yarinya ni kike fad'awa haka lallai Aunty Aliya kinji Yah Sabeer zai shiga tsakanin mu "


Dariya tayi sannan tace
"Kun fi kusa don ba'a shiga tsakanin ku yanzu mutum zai ji kunya don anjima kad'an zaku jone ".


Cikin shagwa6a Jiddah tace "au haka zaki ce Aunty? "
"Eh mana idan na shiga ni za'a bari da jin kunya"


Murmishi Jiddah tayi ta cigaba da cin d'anwaken ta suna ta6a hira da Aunty Aliyah.


Suhaima kuwa bayan fitar ta a palon tana jin abin da Jiddah tace murmishi kawai tayi, nan ta fara aikin had'a kunun da yake tana da gyadar shi yasa aikin yazo mata da sauk'i don tana son shan kunun gyada shi yasa take ajiye markad'add'iyar gyad'a, bayan ta gama ne ta zuba mishi a dogon jug na silver sai k'aramin cup shima na silver ta ajiye mishi a kitchen sannan ta zuba musu nasu a cup ta d'auka ta koma d'akin Aunty Aliya ta mik'a wa Jiddah da Aunty Aliya nasu.


"Yawwa tawan shi yasa kike birgeni kamar kinsan inason sha tun lokacin da kika ambaci sunan shi raina ya biya"


"Ai daman nasan Babyn mu naso shi yasa na dama"


Bata dad'e da zama ba Sabeer yayi mata text ya dawo ta kawo mishi, nan ta d'auki k'aramin tiren silver wanda ta shirya kunun akai ta kai mishi sun d'an ta6a hira har yasha kunun da yawa kafin kuma yayi mata sallama don akwai inda zasu je da Daddyn shi, mota ya shiga drive yaja suka tafi sai da taga tafiyar shi sannan ta dawo gida.


"Lailah ina Majnun d'in? "
Fad'in Jiddah wadda take zaune tana kallon Suhaima da take warware veil d'in kanta, d'an yatsina fuska tayi kafin tace

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login