Showing 99001 words to 102000 words out of 122360 words
Chapter 34 - A sanadin Son ki Hausa Novels Document complete by Aisha A Muhammad Sanaz.txt
da Allah kina son komawa gidan Sabeer? "
Da sauri ta d'ago kanta ta kalli Baba Adamu kafin ta mayar da kallonta kan Sabeer gaba d'aya ya wani marairaice fuskar shi ta koma kalar tausayi sosai yana rok'an ta da tayi hak'uri ta amince, d'auke idonta tayi akan shi ta mayar dashi kan Yah Aliyu sai taga yanda ya wani had'e fuska gashi ya tsattsare ta da ido, ta rasa yanda zata yi zata bi bayan Sabeer ko zata bi bayan Yayan ta idan bata mance ba Yayan ta shine uwa ubanta don bata da wanda ya fishi duk duniyar nan, idan matsala ta sameta shi zata tunkara taya zata dubi tsabar idon shi ta za6i miji wanda bashi da tabbas.
"Kin shiru ke muke jira Suhaima "
Cewar Babaa Lantana kenan.
Kasa magana kawai tayi ta fashe da kuka sosai don batasan wanda zata bi bayan shi ba da gudu ta shige d'aki tare da sanya key.
Wata ajiyar zuciya Aliyu ya sauke yayin da Sabeer kanshi yake sunkuye wasu hawaye na zuba daga cikin su duk shi yajawa kanshi yayi wasa da damar shi gashi komai ya rikice mishi, tsugunnawa yayi tare da cewa
"Ina rok'an ka Aliyu ka taimaka min kayi hak'uri akan abin da nayi wa Suhaima wallahi nayi nadamar korar ta da nayi bazan sake maimaita hakan ba insha Allah kuma zan sanya ido sosai tare da d'aukan mataki ga duk wanda yake kok'arin cutar min da ita "
Tsaki Aliyu ya saki tare da d'auke kanshi yana cewa
"Tun da Suhaima tak'i amincewa sai ka tashi ka koma inda ka fito "
"Babu inda zanje har ina nan har sai lokacin da Suhaima ta yafe min ta amince zata koma gidana "
Ta6e baki Aliyu yayi kan yace
"Ba dai agidan nan ba kuwa "
"Bashi da inda ya wuce nan Aliyu dole ya zauna tare da ku "
Cewar Baba Adamu yayin da Aliyu yace
"Baba ni bani da wani d'akin kwana anan gidan "
"Ga d'akin matar shi nan "
Fad'in Babaa Lantana kenan da duk tausayin Sabeer ya lullu6e ta.
"Babaa kiyi hak'uri amman gaskiya ban amince mishi da ya kwana anan d'akin ba "
Duk yanda yaso su Baba Adamu su taushi Aliyu yak'i basu had'in kai har sai da ran su Baba Adamu da Babaa Lantana ya 6aci sosai kafin dakyar ya amince da sai dai ya kwana a zauren gidan.
"Kana ji Sabeer zaka iya kwana a zauren gidan? "
Da sauri Sabeer yace
"Eh Baba zan kwana nagode sosai Allah ya k'ara girma "
"Amin Sabeer ba komai, yanzu Aliyah tashi ki zuba mishi abinci yaci "
Aunty Aliyah da tunda aka zauna bata tsoma baki ba ta tashi ta nufi kitchen tana zuba mishi abinci, bayan ta zuba ta kawo mishi gaban shi ta ajiye tare da kawo mishi ruwa mai sanyi na randa ta ajiye mishi.
Saboda yunwar taci ta cinye shi kad'an ya iyacin abincin yasha ruwa, zama yayi kawai tare da zabga tagumi abin duniya yayi mishi yawa, bayan su Baba Adamu sun gama ta6a hirar su ne suka yi sallama suka tafi nasu gidan.
Tashi Sabeer yayi ya koma zaure saman wani dutse ya zauna wanda ake tokare k'ofa dashi duk kayan jikin shi sunyi squeezing gashi sunyi datti wanka yake son yi sai dai babu fuskar hakan, had'e kai da gwiwa kawai yayi ga wani zafi, kukan sauro da cizon shi da suka addabi Sabeer dashi.
Yah Aliyu ne ya shigo gidan ya dawo daga rakiyar su Baba Adamu kenan, rufe k'ofar gidan yayi sannan ya wuce cikin gidan ko kallon inda Sabeer yake bai yi ba.
Sabeer na zaune anan yaji motsi d'ago kanshi yayi suka had'a ido da Aliyah saboda akwai hasken farin wata, tabarma ta mik'a da pillow tace
"Gashi nan Sabeer kayi hak'uri "
Girgiza kanshi yayi kan yace
"Auntyn mu nine da baku hak'uri don ku nayiwa laifi, nagode da kulawar ki agare ni ina rok'an ki da ki cigaba da bawa Suhaima hak'uri har ta huce "
Girgiza kanta tayi cikin tsananin tausayin shi don kallo d'aya zaka yi mishi kasan yana tattare da damuwa sosai, kar6ar tabarmar yayi da pillown yayin da Aunty Aliyah tace
"Insha Allah zanyi kok'arin daidaita ka da Suhaima da Yayanta "
Tana gama fad'in haka ta wuce da sauri don fakar idon Aliyu tayi ta fito ta kawowa Sabeer tabarmar, kallon ta yake irin kallon tuhumar nan d'an 6ata fuska itama tayi kan tace
"Lafiya kake kallo na haka kamar wadda tayi mata sata? "
D'an girgiza kanshi kawai yayi baice komai ba ya kwanta, ajiyar zuciya Aliyah ta saki ganin bai fahimci inda taje ba, kwanciya ita ma tayi gefen shi tana tunanin yands zata 6ullo wajen ganin Aliyu ya sassautawa Sabeer............
Aıʂɧąɬ A Mųɧ'ɖ ✍🏻
*A̺͆ S̺͆A̺͆N̺͆A̺͆D̺͆I̺͆N̺͆ S̺͆O̺͆N̺͆ K̺͆I̺͆*
Wྂrྂiྂtྂtྂeྂnྂ bྂyྂ
Aྂıʂɧąɬ Aྂ Mྂųɧ'ɖ
ɖɛɖı¢ąɬɛɖ ɬơ ɱყ ʂąɖɛɛყ ʂąŋąʑ
♻ *єχ¢ℓυѕινє ωяιтєя'ѕ fσяυм*
*PAGE 104-105*
Cikin wannan daren Suhaima bacci kasa d'aukan ta yayi ta rasa abin da yake damunta tun da Sabeer yazo ta rasa nutsuwar ta wanda har takai da yiwa kanta tambayoyi tana son Sabeer ne har yanzu, tausayin shi take ji ko kuma har yanzu zuciyar ta na son sake zama da shi a matsayin mijinta.
Ta 6angaren Sabeer kuwa kusan kwanan zaune yayi saboda zafi da cizon sauro ga duhu dulum ko'ina sai buge bugen sauro yake ya rasa inda zai sanya kanshi yaji dad'i, yayi dana sanin abin da yayiwa Suhaima sau ba iyaka yayi nadama sosai akan tsayawa binciken da bai yi ba gashi ya janyo kanshi shiga cikin tashin hankali.
Wajen k'arfe 3:25 ne gari hadari ya had'o sosai sai walk'iya da cida wato tsawa ake yi ga wata irin iska mai k'arfi da take kad'awa sosai, nan Sabeer ya shiga mugun tashin hankali sosai don yasan idan ruwa ya tsinke babu shakka sai yayi mishi jagab musamman idan mai feshi ne, kawai sai ya fashe da wani irin kukan tausayin kanshi, yana cikin kukan ne ruwa ya zuge kamar da bakin kwarya kafin Sabeer ya ankare ruwa ya jik'e shi jagab tunda kanshi har k'afafun shi.
Tak'urewa yayi waje d'aya ya had'a kai da gwiwa yana faman shashshak'ar kuka da rawar sanyi, ga ruwan sai zubo mishi yake jikin shi amman ya kasa tashi daga wajen toh idan ma ya tashi ina zai je bashi da wajen zuwa a yanzu wanda ya shige inda yake zaune.
Tun da aka fara walk'iya Suhaima ta farka tana zaune tsakiyar gado ta zabga tagumi duk ta rasa abin da yake mata dad'i, don tasan irin yanayin zauren gidan nasu ruwa zai jik'a mutum Yah Aliyu yana da niyyar gyaran shi cikin satin nan, amman tasan halin Yayanta sai yak'i gyara shi saboda Sabeer, kasa jurewa tayi ta sakko daga kan gadon ta nufi bakin window wanda za'a iya hango filin tsakar gidan zuwa cikin zaure.
Hannu ta sanya ta yaye labulen window wani irin mugun sanyi tare da feshin ruwa ne ya ratsa ta, bata hango Sabeer sosai ba saboda duhu sai kyallin farin kayanshi da ta hango, sakin labulen tayi tare da dawowa ta zauna kan gado kusan har aka gama ruwan gabannin asubah Suhaima na zaune ta kasa komawa bacci, da yake tana da toilet aciki ya sanya ta yin alwala tayi sallah tana idarwa ta fara addu'a tana cikin yi ne wani bacci mai k'arfi ya d'auke ta.
"Suhaima! Suhaima!! Ki tashi haka baccin ya isa "
Cewar Aunty Aliyah tana bubbuga k'afar ta, cikin nutsuwa take bud'e idanunta akan agogo ta d'ora eyes nata taga har 10:40 da sauri ta mik'e zaune daman haka lokaci yaja lallai tayi bacci mai nauyi.
"Aunty gaskiya nayi bacci mai nauyi haka lokaci yaja "
"Naji shirun yayi yawa har mun karya shine nazo duba ki ko lafiya?"
D'an murmishi tayi sannan tace
"Lafiya qlau Aunty kawai bacci ne "
"Kiyi sauri ki shirya kizo ki karya don ina son mu gama aiki da wuri zan fita suna da yamma "
"Laaa Aunty zan raka ki don Allah "
Cewar Suhaima cikin shagwa6a, 'yar dariya tayi kan tace
"Waiii rufa min asiri sai dai ki tambayi mijin ki tukunna "
Had'e fuska Suhaima tayi kan ta mik'e da sauri ta shige bathroom da kallo Aunty Aliyah ta bita kan ta girgiza kanta kawai fita tayi daga d'akin.
Agurguje Suhaima tayi wanka ta shirya cikin wata blue d'in jallabiya ire iren kayan da Yayan ta ya siya mata ne tunda bata taho da kaya ko d'aya ba, bata yi wani kwalliya ba wet lips ne sai powder kawai ta shafa duk da haka tayi kyau kuwa, d'an perfume ta shafa kan ta had'e gashinta da ribbon ta fito daga d'akin.
Hankalin ta akan hanyar zaure amman bata hango shi ba nan taji hankalin ta ya d'an tashi kaddai ya tafi, har tana yin tuntu6e saboda lek'e ashe Aunty Aliyah na kula da ita girgiza kanta tayi kawai tana murmishi don tasan Suhaima nason Sabeer haka shima yana sonta don haka zatayi bakin kok'arin ta wajen daidaita su.
"Lek'en me kike har kina yin tuntu6e "
Wani kunya ne ya kama Suhaima sai kawai ta sunkuyar da kanta tana shafa kai ta wuce kitchen don d'auko abin karyar ta tana cewa
"Ni babu abin da nake kallo fah Aunty "
Murmishi kawai Aunty Aliyah tayi, fitowa tayi daga kitchen ta zauna kusa da ita tana kok'arin zuba kunun tsamiya a cup tace
"Aunty ina Yaya ne? "
"Ya tafi makaranta yana da lecture d'in safe gashi zasu yi test ma "
Suhaima tana bud'e wani k'aramin flaks wanda kosai yake ciki tace
"Ayyah Allah ya taimaki Yayana "
"Amin "
Cewar Aliyah tana murmishi, kafin kuma tayi bismillah ta fara cin abincin cikin nutsuwa bayan ta gama ta wanke hannun ta tana kok'arin d'auke kayan da ta karya dasu don ta kaisu kitchen Aunty Aliyah tace
"Bar wannan aikin Suhaima ki rik'e min Ameer don kuwa sauri nake son yi "
Shagwa6e fuska Suhaima tayi kan ta ce
"Kaiii Aunty nima fah na iya wannan saurin gashi ke kadai kika had'a abin kari "
"Ni na isa na fad'i hakan ke dai zo ki rik'e min shi idan ba haka ba yana wannan rarrafen nashi zai hanani saurin aiki "
D'aukan Ameer tayi tana cillashi tare da cafe shi tana dariyar shima Ameer d'in dariyar yake mata da 'yan hak'oran shi, tana cikin haka ne taji tsayuwar mutum akanta da sauri ta d'ago kanta ido 4 tayi da Sabeer wanda yake tsaye ya hard'e hannun shi yana kallon ta cike da so da tarin sha'awarta don sosai ta birgeshi ji yake kamar ya kamota ya gudu da ita, d'auke kanta Suhaima tayi daga barin kallon shi ta cigaba da yiwa Ameer wasa amman jikinta ya bata har yanzu bai tafi ba kallonta yake lokaci d'aya taji wata kasala ta lullu6e ta har takai ta kasa d'aga Ameer sama sai kawai wasan da take mishi.
Fitowar Aunty Aliyah daga kitchen ne ya sanya shi katse kallonta, kallon shi Aliyah tayi kafin ta girgiza kanta ganin lokaci d'aya ya rame gashi kayan shi sunyi datti sosai tace
"Sabeer kana buk'atar wani abun ne? "
Cikin dashashshiyar muryar shi wadda mura tayi mishi mugun kamu yace
"Auntyn mu wanka nake son yi sannan ina son bak'in tea da lemon tsami aciki "
"To amman wannan murar taka ko chemist zaka je kada ta ssukar maka da zazza6i "
Cikin murmishin yak'e yace
"A'a basai naje ba zata warke "
"Anya kuwa Sabeer za'a yi haka kada fa ta baka matsala? "
"Auntyn mu kada ki damu zata warke nagode da kulawar ki, wadda ya kamata ta nuna damuwa akan ciwon bata damu ba sai ke don haka ki share zancen zuwa chemist "
Da sauri Suhaima ta d'ago kanta ta kalli shi har zata yi magana kuma sai kawai ta d'auke kanta tana murgud'a baki, duk abin da take yi akan idanun Sabeer, yayin da Aunty Aliyah tace
"Yanzu sai kayi wankan zaka sha tea d'in? "
"Eh "
Ya fad'i a takaice
"Ka shiga d'akin Suhaima akwai toilet aciki sai kayi wankan ka aciki "
Daga Suhaima har Sabeer da sauri suka d'aga kansu tare da kallon Aliyah, gid'a kanta tayi sanann tace
"Kada ka damu kaje kayi "
"Aunty amman...... "
Cewar Suhaima sai dai bata k'arasa fad'in abin da zata ce ba taja bakin ta tayi shiru ta had'e fuska.
"Aunty nayi kawai a wannan toilet d'in "
"A'a bazai yiwu ba, Suhaima kije ki had'a mishi ruwa nace idan har na isa na sanyaki abu kiyi "
Tashi Suhaima tayi tana 6a66ata rai zata wuce d'aki taji tana cewa
"Dawo ki d'ebi ruwan zafi tun da garin da d'an sanyi gashi yana fama da mura ".
Kitchen ta shiga ta d'ebo ruwan zafi ta wuce d'akin ta tana cika tana batsewa don me Aunty Aliyah zata ce yayi wanka a d'akin ta, ko ta mance da irin yanda ya koreta daga gidan shi ne.
"Auntyn mu 6atawa Baby nah rai fah? "
Ya fad'i hakan bayan wucewar Suhaima.
"Kyaleta Sabeer sakkowar Suhaima daga fushin da take da kai shi zai sanya Yayan ta ya huci daga d'aukan zafin da yayi maka, kai dai kayi kok'arin shawo kan Suhaima "
Gid'a kanshi yayi kan ya wuce zuwa zaure ya d'auko bag d'in kayan shi ya wuce d'akin Suhaima, yayin da Aunty Aliyah ta cigaba da aikinta bayan ta goya Ameer.
Yana shiga cikin d'akin wani k'amshi ne ya fara mishi sallama mai dad'i har sai da ya lumshe eyes nashi, tsayawa yayi yana kallon d'akin cike da sha'awar shi yayi mishi kyau duk da ba wasu kaya ne masu tsada ba sosai amman yanayin yanda aka tsara d'akin ne ya birge shi, daga gado, wardrobe sai dressing mirror k'asan kuma carpet ne sai kayan kallo gashi d'akin babba ne sai labulaye masu kyan tsari gadon nan an gyarashi sosai tamkar ba'a ta6a kwanciya akan shi ba.
Yana nan tsaye Suhaima ta fito daga toilet d'in ba tare da ta kalli inda yake ba ta fara kok'arin fita daga d'akin, hannun ta ya rik'o cikin sanyin murya yace
"Baby nah kiyi hak'uri please ki daina fushi da ni "
Bata ko kalle shi ba ta fara zame hannunta daga nashi sannan ta fice daga d'akin, da kallo ya bita kafin kuma ya nufi hanyar da ta fito ya shige toilet d'in.
Suhaima tana tsaye kusa da Aunty Aliyah tana mata mitar yanda ta sanya Sabeer shigar mata d'aki, yayin da Aunty Aliyah take murmishi kawai yaro yaro ne idan ban da haka yaci ace ta yafewa Sabeer don ita kanta Suhaima ya kamata ta baiwa Sabeer shaidar yanda yake nuna mata so da kulawa abu ne ya gifta a tsakanin su wanda mak'iyan su da basa son su gansu tare suka yi amfani da abin da Sabeer yafi so suka had'a makirci shi kuma laifin shi d'aya da ya biyewa zuciyar shi ya yanke hukunci cikin fushi sai dai kuma yayi kok'arin controlling din zuciyar shi tun da bai sake ta ba.
Sallamar da suka ji anyi ne ya sanya Suhaima da Aliyah zabura gaban su ya hau fad'uwa lokaci d'aya kafin su ankare ya shigo gidan, kallon su ya tsaya yi cikin mamaki ganin yanda suka zuba mishi ido kallo d'aya yayi musu yasan basu da gaskiya.
Tsarguwar da suka yi da yanda yake kallon su ne ya sanya su sakin murmishin yak'e tare da yi mishi sannu da zuwa, amsa musu yayi kawai yana sake bin su da kallon ban yarda daku ba.
Zuciyar Suhaima da ta Aliyah tamkar zasu faso kirjin su ta fito saboda yanda take bugawa sam basu yi tsammanin ganin Yah Aliyu yanzu ba sun sakankance sai da yamma, musamman Aunty Aliyah tafi kowa tsorata tayi dana sanin sanya Sabeer shiga cikin d'akin Suhaima yanzu idan ya fito daga d'akin batasan hukuncin da Aliyu zai d'auka ba akanta don itace da wannan shishshigin, gashi kafin ya fita sai da tasha gargad'i kada ta sake tsakanin Sabeer da Suhaima magana ta had'a su, nan ta fara addu'a Allah ya sanya kada Sabeer ya fito.
"Wai lafiyar ku qlau kuwa? "
Cikin sauri Aunty Aliyah tace
"Me kagani? "
"Gani nayi kunyi wani tsuru tsuru sai rarraba ido kuke kamar marasa gaskiya "
"A haba ba komai, lafiya ka dawo yanzu? "
"Nayi mantuwa ne "
Yana gama fad'in haka ya wuce d'akin su da sauri don kuwa sauri yake, bai dad'e ba ya fito daga d'akin ya fice daga gidan, sai lokacin suka saki ajiyar zuciya ta kwanciyar hankali.
"Aunty kinga abin da nake tsoro koh da yanzu ya gane fah "
Aliyah wadda jikinta ya mutu saboda tsoro ta aro dauriya tace
"Kai dai Allah ya kiyaye kawai ba don haka ba da yau zanyi bayani don nice da laifi "
Suhaima dariya ce ta kubce mata ganin Aunty Aliyah na goge zufa tace
"Haba Aunty kinsan Yah Aliyu bazai iya ce miki komai ba sai dai kisha harara da mita "
"Ke kyale Yayan nan naki kawai idan ya fusata "
Cup d'in da ta had'a wa Sabeer tea ta mik'o mata tare da cewa
"Gashi ki kai mishi da zafin shi yasha kada ya huce gashi jiya fah bai samu cikakken bacci ba don nasan ruwan nan ya jik'a shi sosai "
D'an ta6e baki Suhaima tayi kan tace
"Allah Aunty kina son wanann guy d'in ya rainani da yawa bakisan haushin shi nake ji ba wallahi "
"Hakuri zakiyi Suhaima kinsan kowanne d'an adam da irin tashi k'addarar Allah ya riga ya tsara hakan sai ya faru tsakanin ku"
Kar6a tayi kawai ta tafi tana zum6ura baki Aunty Aliyah ta bita da kallo tana murmishi kawai.
Tana shiga d'akin ta ajiye cup d'in tea saman drower na gefen gado ta jiyo da niyyar fita daga d'akin taji an janyo hannun ta da d'an k'arfi wanda ya sanya d'an kwalin kanta mai santsi ya zame lallausa dogon gashin kanta ya tarwatse, bata tsaya ko'ina ba sai saman faffad'an kirjin shi har sai da d'an kanta ya bige kad'an, kallon shi tayi da niyyar yi mishi tsiwa sai dai suna had'a ido duk wani abu ya kunce