Showing 15001 words to 18000 words out of 122360 words

Chapter 6 - A sanadin Son ki Hausa Novels Document complete by Aisha A Muhammad Sanaz.txt

rayuwa ce bata tunanin makomarta anan gaba matsayin ta na d'iya mace.




Hira suke tsakanin Mumy da Fadilah har suka k'arasa gida driver yana yin parking suka fito a motar direct part d'in Mumy suka nufa, suna shiga cikin parlourn babu kowa amman a gyare yake tsaf dashi sai tashin k'amshin turaren wuta yake da air freshener, upstairs suka nufa nan Mumy ta nunawa Fadilah room d'in da zatayi amfani dashi, amman sai Fadilah tace
"Mumy ina ne bedroom na Sabeer naje mu yi hira kinsan har yanzu yak'i sake min sosai "
Murmishi Mumy ta saki tare da nuna mata wani d'an corridor da hannunta tace
"kin ga bedroom d'in shi can nasan yanzu yana ciki " tana gama fad'in haka Mumy ta nufi hanyar da zai kai ta bedroom nata ta bar Fadilah anan.


Wani dad'i ne ya kama Fadilah cikin rawar jiki ta juya zata nufi room d'in Sabeer sai ta kalli kayan jikin ta wani d'an Tunani tayi kad'an kafin ta juya kuma da sauri ta koma bedroom d'in da Mumy ta nuna mata.


Da sauri ta shige bathroom ta fara yin wanka bata dad'e ba ta fito babu batun yin alwala balle sallah, cikin sauri ta gyara jikin ta sannan ta shirya cikin wata white d'in sleeping dress tsayin ta iyakar shi cinya mai siririn hannu sannan ta d'ora 'yar saman ta wadda take har k'asa sai dai gaban ta a bud'e yake sai 'yan igiyoyin rigar da ake d'aure wa, perfumes ta sanya masu matuk'ar k'amshi da tada hankali sannan ta fito zuwa room d'in Sabeer.




Tura kofar room d'in tayi ta shiga tare da rufe kofar ta jingina bayan ta a jikin ta, shak'ar k'amshin turaren Sabeer tayi tare da lumshe ido tana sauke ajiyar zuciya, kafin ta bud'e idanun ta a hankali ta zube su akan Sabeer da yake baccin shi hankali kwance, wani shu'umin murmishi ta saki tana mai k'arasa wa wajen bed d'in, hankalin ta kwance ta cire 'yar saman rigar ta tukunna ta haye kan bed d'in.


Kallon Sabeer take tamkar wata kura taga nama, sai wani had'iyar yawu take musamman da takai eyes nata kan kirjin Sabeer a hankali ta d'ora hannun ta inda take Buk'atar ajiye shi a cikin jikin Sabeer ta fara shafawa cikin kwarewa da gwanin ta....








Aishat A Muh'd ✍🏻
💝 A SANADIN SON KI 💝




Written by
Aishat A Muh'd


♻EXCLUSIVE WRITERS FORUM


Dedicated to my Sadeey (saNaz)




Where are U Bilkisu Bk this page is for U autan Exclusive thanks for luv and care, Allah ya bar zumunci thanks once again dear 👄








PAGE 19-20








Sabeer yana tsaka da yin sleeping nashi mai dad'i yaji tsikar jikin shi yana tashi, wani yanayi yana shigar shi a hankali mara fasaltuwa ya rasa tantanci shin mafarki ne ko ido biyu yake jin haka.




Fitinannen k'amshin Fadilah ne ya cika kofofin hancin shi har takai da ya fara kok'arin bud'e idon shi, gaba d'aya Sabeer ya gama tsorota don yana tunanin ko aljanna ce ta zo mishi tun da a lokacin ya tabbatar da ba mafarki ba ne kuma yasan wace mace ce zata zo mishi a wannan daren idan ba aljanna ba, har jiki shi ya fara d'an rawa don Sabeer akwai tsoro dakyar ya iya yunk'urin bud'e idon shi ya zuba su akan Fadilah da take kok'arin kissing lips nashi, don ta had'a fuskar ta da tashi daf take da ta had'e lips nasu waje d'aya.




Zaro ido Sabeer yayi cike da tsantsar mamaki yana kallon ta, ranshi a 6aci sosai so yake ya tuna inda ya santa, amman kafin ya tuna d'in tuni Fadilah ta had'e bakin ta da nashi, wasu abubuwa take yiwa Sabeer wanda duk d'a namiji cikakke mai lafiya bazai iya jurewa ba, tuni Sabeer ya fara sakin layi yana mayar mata martanin abin da take mishi.




Tuni Fadilah an saki jiki sosai tayi luf a jikin Sabeer tana mai kar6ar sak'onnin da yake aika mata dashi cikin rawar jiki, sun yi nisa cikin wannan yanayin sosai kamar wanda wutar nepa taja haka Sabeer yaji a jikin shi wanda ya haddasa mishi barin jikin Fadilah da sauri ya mirgina can k'arshen bed d'in, yana mayar da wani irin numfashi tare da sauke ajiyar zuciya.




Kafin kuma ya fara tunanin abin da ya kusan faruwa a yanzu tsakanin shi da Fadilah, zumbur ya mik'e tsaye yana furta kalmar innalillahi wa'inna ilaihir raju'un yana dafe da kanshi cikin zuciyar shi yana mai godewa Allah da ya tseratar dashi daga hannun wannan shaid'aniyar 'yar iskar yarinya.


A zuciye yayi kan Fadilah wanda idanun ta a lumshe tana jiran Sabeer ya fara aiki gaba d'aya cikin wani buk'atuwa take dashi, don ta d'auka ya tsaya cire 3quater d'in jikin shi yake, don haka ita ma sai ta fara kok'arin k'arasa cire sleeping dress d'in jikin ta daman gashi room d'in babu haske sosai, don haka bata ga tahowar Sabeer wurin ta ba bata kai da gama cire rigar ba a fusace yakai hannun shi saman fuskar ta ya wanka mata mari har guda biyu wanda sai da Fadilah taga wasu star's a idanun ta jinta ya d'auke na wucan gadi, don tun da Maman ta ta haifeta ba'a ta6a yi mata irin wannan marin ba, kafin ta dawo hayyacin ta daga marin Sabeer ya zage iyakar k'arfin shi ya hau dukan ta da belt, tuni Fadilah ta fara ihun kuka da neman agaji da k'arfi sosai take ihun wanda ya sanya k'arar ihun ta ya tashi Mumy da Daddy daga baccin su, a kid'ime suka fito daga bedroom d'in Daddy suka yo d'akin Sabeer don tanan haka suke jin k'arar ihun.




Da k'arfi suka tura kofar suka shiga hankalin su a tashe sosai, ganin duhu ne ya sanya Daddy kunna bulbs d'in room d'in tuni haske ya gauraye d'akin, hango tilon d'an su suka yi yana dukan Fadilah cike da fusatar da basu ta6a tsammanin yana da ita ba.




Da sauri Daddy ya nufi wajen shi yana cewa
"Son What wrong with U? "
Amman Sabeer bai kula shi cigaba yake da dukan ta kawai wanda yanzu babu bakin kuka sai hawayen da suke zuba cikin idanun ta, ganin bazai tsaya da dukan ya sanya Daddy rik'e shi gam a cikin jikin shi tare da kallon Mumy yace
"Janye Fadilah ki fitar da ita "
Jiki ba kwari Mumy take kok'arin d'aga tana kallon fuskar d'an nata wanda take hango kwantaccen 6acin rai akan fuskar tare da wasu hawaye da suke zuba a kan fuskar tashi gaba d'aya sai taga ya rikid'e mata ya zama wani mutum na daban kamar ba Sabeer ba, gashi idanun shi sunyi ja da fuskar shi, jikin Mumy gaba d'aya yayi sanyi haka ta ja Fadilah suka fita daga bedroom d'in ta tana tunanin me ya had'a Fadilah da Sabeer har yayi mata wannan mugun dukan.




Bayan sun fita daga bedroom d'in Daddy ya zaunar da Sabeer kan bed amman sai Sabeer ya zame ya zauna akan lallausan carpert d'in d'akin ya dafe kanshi da dukka hannu biyun yana hawaye wai yau shine yake kok'arin aikata zina wannan wacce irin bak'ar rana ce a wajen shi.




Bottle d'in faro Daddy ya d'auko a frige tare da glass cup ya tsiyaya a ciki tukunna ya rufe bottle d'in ya d'ora saman frige sannan ya k'arasa wajen Sabeer ya dafa mishi kafad'a tare da d'ora mishi bakin cup d'in a tsakanin lips nashi bai yi musu ba ya bud'e bakin ya sha ruwan sosai tukunna ya zame bakin shi ya kwanta a k'asan yana d'ora kanshi saman k'afafun Daddy.




Hannun shi Daddy ya sanya yana shafa lallausar suman kan Sabeer sun d'auki wajen 5 minute a haka, tukunna Daddy yace
"Sabeer sanar da ni abin da ya faru tsakanin ka da Fadilah har kayi mata wannan mugun dukan? "
dakyar Sabeer ya iya bud'e bakin shi yace
"Ba komai "
Hangame baki Daddy yayi yana kallon shi cikin mamaki har zai sake magana sai ga Mumy ta shigo room d'in cikin tashin hankali zata fara magana Sabeer ya dakatar da ita yana cewa


"Mumy leave me alone please"
Zata matso kusa dashi da sauri ya tashi ya koma saman bed ya kudundune cikin blanket zuciyar sai wani tafasa take sosai yake jin haushin Mumy don yasan duk ita ce ta nuna mata room d'in shi, kallon Daddy Mumy tayi ta marairaice fuska hannun ta ya rik'o tare da cewa
"Yana buk'atar hutu ne na fuskanci ranshi a 6ace yake sosai "
Cikin damuwa Mumy tace
"Yanzu bai fad'a maka abin da ya faru nima Fadilah tak'i fad'a min sai kuka kawai take"
Ta k'arasa maganar tamkar zata fashe da kuka, cikin kwantar da hankali Daddy yace
"Ki bari zuwa gobe nasan ya huce zai yi bayani amman nasan Fadilah tayi mishi laifi babba "


Haka suka fito duk jikin su a sanyaye sosai baccin ranar basu iya bacci ba tsakanin Sabeer, Mumy, Daddy da kuma Fadilah kowa sai juyi yake akan bed da tunani kala kala cikin zuciyoyin su.


Bayan sallahr asubah ne Sabeer ya fito daga side d'in su cikin shigar white T-shirt da 3quater yellow ya shiga motar shi k'irar Benz driver yaja shi, sai da suka yi tafiya mai d'an nisa tukunna driver yace
"Yalla6ai ina zamu je? "
D'an shiru Sabeer yayi yana tunani kad'an kafin yace
"Ina son ka kaini d'aya daga cikin wani k'auye mai kyau da ke makwabtaka da mu "
D'an murmishi driver d'in yayi tare da cewa
"Angama yalla6ai "
Yana gama fad'in haka ya nufi wata hanya, yayin da Sabeer ya kishingid'a a bayan motar a hankali yake jin zuciyar shi na yin sanyi...










Aishat A Muh'd ✍🏻
💝 A SANADIN SON KI 💝




Written by
Aishat A Muh'd


♻EXCLUSIVE WRITERS FORUM


Dedicated to my Sadeey saNaz




Wannan shafin naki ne kyauta Zahra Maman Kausar da Ahmad thanks for luv and support, ina jin dad'in yanda kike k'aunar nvls d'ina, Allah ya bar zumunci ya raya mana Kausar da Ahmad, Amin ❣








PAGE 21-22








Cikin nutsuwa Suhaima ta fito daga d'akin ta cikin shirin uniform na tahfiz da yake ranar asabar ce, cikin kitchen ta k'arasa inda Aunty Aliyah take had'a abin karin kumallo ganin sinasir take yi ne ya sanya Suhaima sakin murmishi da yake tana son sinasir sosai, cikin jin dad'i tace


"Wow Aunty sinasir kike mana yau amman naji dad'i sosai bari nayi sauri na tafi kada nayi latti "
Murmishi itama Aunty Aliyah tayi tare da cewa
"Ai shikenan sai kin dawo, zaki sha 'yar tafiya kuwa yau don Yayan ki ya fita tun asuba zuwa kai kaji da kwayaye kasuwar birni "


D'an murmishin ta mai kyau Suhaima tayi tare da cewa
"Yeeeeee ai ni yau naji dad'in haka zan tafi a k'afa saboda kullum shi Yaya shi yake kaini kuma yaje ya d'auko ni ko'ina mutum zai je sai dai a kai shi ni fah yanzu na girma " ta k'arasa fad'i tana rawa har da juyi duk dad'i ya ishe ta.


Rik'e baki Aunty Aliyah tayi tana cewa
"Tabbb kenan dad'i kike ji ai kyasha tafiya kuwa yau "


"Eh naji Allah ya dawo da Yaya lafiya ni na tafi kada ki ja min latti "


Suhaima ta k'arasa fad'a tana dariya ta fice daga gidan da sauri, tabar Aunty Aliyah itama tana dariya kafin ta mayar da hankalin ta kan abin da take yi.






Cikin d'an sauri Suhaima take tafiya saboda ganin ta kusa latti aikuwa tana shiga cikin makarantar aka rufe kofa lokacin kaman 'yan latti yayi, wata ajiyar zuciya Suhaima ta saki ganin Allah ya taimake ta bata sha dukan latti ba da sauri ta wuce cikin ajin su, da yake k'auyen nasu babu laifi akwai masana ilimin addini dana zamani dai dai gwargwado, musamman ma ilimin addini sun fi bashi muhimmanci fiye dana boko, shi yasa suke da makarantar islamiyya da tahfiz.






K'arfe 11 na safe aka tashi su Suhaima nan tayi sallama da k'awayen ta ta wuce zuwa gida, don ba 'yan kusa da su a makarantar, saboda sune kusan gidan su na k'arshe k'arshen k'auyen, a nutse take tafiyar ta kanta a sunkuye yake tana tilawar karatun alqur'an a hankali koda kana kusa da ita ba lallai kaji abin da take fad'a ba sai dai kaga le6en ta na motsawa a hankali alamar dai akwai abin da take karantawa.




Tayi nisa da tafiyar ta don tayi wajen rabin tafiyar da zata kaita gida, horn taji ana yi mata amman sam batasan da ita ake ba tafiyar ta take kawai abin ta hankalin ta kwance.




Bata ankara ba taji mota ta goge ta kad'an a jikin ta har sai da madubin motar na waje ya bige ta a gefen hannun ta, wani irin zafi Suhaima taji a hannun ta da sauri ta d'ago kanta tana kallon motar da ta bige ta zata wuce saboda hanyar bata da kyau sosai akwai 'yan kwazazzabai shi yasa bata sauri, ganin mai motar bashi da alamin tsayawa ya bata hak'uri ko yayi mata sannu ne yasa Suhaima cikin fusata tace


"Kan ubancan! lallai mutumin nan baka da mutunci a bige ka ko sannu babu ka wani wuci kamar ka bige dabba ba mutum ba "


Ta fad'a da k'arfin ta ranta a 6ace, ganin ba alamar tsayawa yasa ta d'auki wani dutsen wuta a k'asa ta saita glass d'in motar ta jefa da iya k'arfin ta sai dai bai samu glass d'in ba sai fitilar motar ta baya ta samu, aikuwa babu 6ata lokaci ya ba da sautin k'arar fashewa, babu shiri mai driving d'in motar yaja motar ya tsaya.




Suhaima kuwa dad'i ne ya kamata da taga hakan taso ma glass d'in ta samu ta fasa tun da bashi da mutunci har da sakin wani murmishin mugunta.


Cigaba tayi da tafiyar ta abin ta har ta k'araso inda motar tayi parking amman babu wanda ya fito daga motar gashi glass d'in motar mai duhu ne ba'a ganin na ciki, sai dai na cikin ya gan ka, ita Suhaima ko alamar tsoro babu a tattare da ita ta wuce motar, baifi taku hud'u tayi ba tsakanin ta da motar taji alamar an bud'e kofar motar amman bata jiyo ba saboda bata da ra'ayin ganin wanda ke cikin motar.




Cikin fusata na cikin motar ya nufi inda Suhaima take tafiyar ta cikin zafin nama ya sanya hannun shi ya janyo hijab d'in ta na baya, tare da jiyo da Suhaima saitin inda yake ya d'aga hannu zai mare ta cak ya tsayar da hannun shi ya kasa karasar dashi kan fuskar Suhaima kamar yanda yayi niyya, sakamakon had'a ido da yayi da ita duk wani 6acin rai da ya kwaso shi yaji ya tafi a lokaci d'aya.


Kallon kyakkyawar face nata yake da eye's nata masu matuk'ar d'aukan hankali, runtse idon ta Suhaima tayi cikin tsoro jikin ta har ya fara 6ari na tsoro don ta zaci mari zata sha, eyelashes d'in ta yabi da kallo yanda suka bi idon suka kwanta kan beautiful face nata.




Jin bataji saukar mari ba ya sanya ta bud'e idanun ta a hankali ta sauke su kan fuskar kyakkyawan saurayin da yake gaban ta, ganin yanda ya zuba mata ido yana kallon ta ya sanya ta fincike hijab d'in ta da ya rik'e mata tare da gyara taayuwar ta aka wani rik'e kugu cike da tsiwa tace


"Malam lafiya da zaka wani rik'e min hijab? "


Sai da ya guy din ya lumshe idanun shi don jin saukar dadad'ar voice d'in Suhaima kafin ya sake bud'e idon nashi yana cigaba da kallon ta tamkar wadda ya samu wata tv yana kallo ko motsin kirki baya yi, sosai abin ya bawa Suhaima mamaki cikin zuciyar ta take cewa shi wannan baya jin tana magana ne ko kurma ne shi? da alamar ma daga birni yake.




Cikin tsiwa ta sake cewa "wai malam baka ji ina maka magana ko kai kurma ne? "


Ganin again ya kuma share ta sai kallon ta kawai da yake yi ne har da wani hard'e hannaye saman kirjin shi yasa Suhaima juya bayan ta cikin sa'a ta hango wani yaro na kusa da su hannun shi rik'e da robar ruwa a kanshi ya d'auko zai tafi gida.


Dad'i ne ya ishi Suhaima har da d'an murmusawa na mugunta don tasan abin da zata yiwa wannan mayen d'an birnin, yaron yana k'arasowa inda suke zai wuce da sauri Suhaima ta sanya hannunta saman kanshi ta d'auke robar ruwan.


Kafin yaron ya juyo tuni ta watsawa wannan guy d'in ruwan a jikin shi dukka tare da jefar da robar gefe d'aya, lokaci d'aya drivern da yake tsaye jikin motar da wannan yaron da Suhaima ta d'auki ruwan shi suka d'ora hannu a kansu cikin tashin hankalin da abin da Suhaima ta aikata, wata k'atuwar ajiyar zuciya ya sauke lokaci d'aya jin wannan ruwan mai shegen sanyi a jikin shi tsikar jikin shine ya tashi kafin ya sanya hannun shi a fuskar shi yana goge ruwan da yake di'gowa daga saman gashin kanshi yana kok'arin bud'e idon shi.




Ganin haka ya sanya Suhaima kwasa da gudu ita da yaron har ma yafi Suhaima gudu tamkar shi yayi laifin daman tuni ya mance da wata robar shi don anashi tunanin aka tashi kama da Suhaima har dashi za'a had'a, sai abin ma ya bawa guy d'in dariya sosai ganin yanda suke gudu kallon su yake fuskar shi d'auke da murmishi har sai da ya daina ganin su....








Ku hak'uri da wannan ban da charge wollah, ku biyo ni next chapter don jin abin da zai faru.






Aishat A Muh'd ✍🏻
💝 A SANADIN SON KI 💝




Written by
Aishat A Muh'd


♻EXCLUSIVE WRITERS FORUM


Dedicated to my Sadeey saNaz




Ina kike Basmah Er lele wannan shafin naki ne kyauta ina tayaki murnar kammala littafin ki TAURA BIYU Allah ya Kara basirah da k'arfin ido, Allah ya bar zumunci. 👄






PAGE 22-23








Sai da ya daina ganin

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login