Showing 57001 words to 60000 words out of 122360 words
Chapter 20 - A sanadin Son ki Hausa Novels Document complete by Aisha A Muhammad Sanaz.txt
farincikin ganin shi, musammam Alhj Ahmad d'an fillo da Hajjah don rungume shi sukayi tamkar zasu mayar dashi cikin jikin su saboda tsabar son da suke mishi.
Jiddah wadda agidan ta wuni ta d'ago kanta suka had'a ido da Sabeer wanda yake ta zuba musu shagwa6a su kuma sun shashance da lalla6a shi, dariya take son fashewa da ita amman ganin hararar ta da yake yi ne ya sanya ta kunshe dariyar ta, daga k'arshe sai ta faki idon shi tana mishi video don ta nunawa Suhaima ta shirya zama da shagwa6a66en miji.....
Aishat A Muh'd ✍🏻
*A SANADIN SON KI*
Written by
Aishat A Muh'd
Dedicated to my Sadeey SaNaz
*PAGE 69-70*
Tun bayan tafiyar Sabeer gida Suhaima ta shiga tsananin kewar shi ranar cikin kewar shi take duk ta sanyawa kanta damuwa ko abincin kirki ta kasa ci sai tunanin Sabeer, sam ta mance bata kunna wayar da ya bata ba duk a tunanin ta a kunne take.
Sabeer kuwa duk ya shiga tashin hankali da ya kirawo ta yaji wayar a kashe yana son sanar da ita ya sauka lafiya sannan ya fad'a mata yanda yayi kewarta na tsawon yini guda, daga k'arshe dai sai kiran Yayah Aliyu yayi bayan sun gaisa yake fad'a mishi ya sanarwa da Suhaima ta kunna phone nata zai kirata tukunna suka yi sallama.
Tana kwance still har yanzu har bacci ya fara fisgarta sai taji sallamar Yah Aliyu ya shigo d'akin, kallon ta yayi cikin kulawa kafin yace
"K'anwata me yake damun ki duk kinyi wani iri yau kodai duk tafiyar Sabeer d'in ne ya sanya ki zama haka"
Ya k'arasa maganar cikin zolaya, da sauri Suhaima ta rufe fuskar ta da hannayen tana 'yar dariyar jin kunya tace
"Kaiiii Yaya! "
"Eh mana gaskiya ce ina kula da ke fah ko abincin kirki baki ci ba sannan baki zo munyi hira ba "
Kasa magana tayi don batasan da me zata kare kanta ba don kuwa maganar shi haka take, ganin haka yasa shi mik'e wa tsaye yana murmishi yace
"Sabeer yace ki kunna wayar ki zai kirawo ki sai da safe "
Yana gama fad'in haka ya fita, d'an waro ido tayi kad'an tare da cewa
"Daman wayar a kashe take oops! "
Bata tsaya 6ata lokaci ba ta janyo wayar ta kunna ta sannan ta zuba mata ido tana sauraren kiran Sabeer.
Ko mintuna goma cikakku batayi da kunna phone d'in ba taji ta d'auki ringing, d'auka tayi ba tare da duba screen d'in ba saboda sauri da zak'uwan son jin voice d'in Sabeer.
"Hello Baby nah ".
Lumshe idonta tayi saboda jin saukar daddad'ar muryar Sabeer cikin kunnen ta har ta shagala ma sai da ta sake jin muryar shi yana mata magana sannan ta sauke ajiyar zuciya ta amsa mishi tare da gaida shi.
Bayan ya amsa ne suka d'an ta6a hira ta tsayin wajen mintuna 30 sannan suka yi sallama da junan su don ganin dare ya fara yi, kowannen su cikin kewar d'an uwanshi suke.
Bayan dawowar Sabeer da kwanaki uku ne ya buk'aci da iyayen shi su je neman mishi auren Suhaima, nan take Daddy ya aminta da hakan don haka ya had'a kan 'yan uwan shi maza suka had'u zuwa part din mahaifin su suka sanar mishi don ya tsayar musu da ranar tafiya neman auren Suhaima.
Sam Alhj Ahmad d'an fillo ba'a son ranshi yayi magana ba don kana kallon fuskar shi zaka karanci hakan, don farincikin Sabeer kawai ya aminta da auren nan amman sam baya so Suhaima, nan ya yanke lokaci zuwa nan da sati biyu su Daddy zasu je, aikuwa Sabeer najin haka ya tubure bazai yadda ba don sati biyu sunyi mishi nesa shi fah da ason ranshi ne aranar a d'aura auren Babyn shi ta tare a gidan shi, ganin yanda ya tada rigima ne ya sanya shi tambayar shi yaushe yake son aje.
Bud'ar bakin Sabeer yace shi gobe yake son aje kuma a tsayar da lokacin biki nan da sati uku, don fah shi har ga Allah satin ukun ya fad'a ne kawai amman sunyi mishi nisa, yanda ya buk'ata haka Alhj Ahmad d'an fillo ya amince ba don yaso ba sai don baya k'aunar 6acin ran d'an lelen shi, don haka ya kirawo 'ya'yanshi ya shaida musu gobe kowa ya tashi cikin shirin tafiya don zuwa neman wa Sabeer aure nan take suka amince da hakan.
Sabeer ba k'aramin farinciki yayi ba da jin sun amince da abin da yake so, da dare Daddy yake sanarwa da Mummy yanda suka tsara shi da 'yan uwan shi ko uffan Mumy bata ce ba k'arshe sai juya mishi baya tayi ranta a k'untace batason Suhaima bazata ta6a son yarinyar da ta fito daga k'auye ba kuma 'yar talakawa ta had'a zuri'a da ita dole ta sami mafita ta tarwatsa auren kafin lokaci ya k'ure mata.
*** *** ***
Duk wasu shirye shirye sun kammala shi na saukar bak'in su, anyi musu lafiyayyen girki sannan Yah Aliyu ya siyo musu drinks na kwali da faro, d'akin da Sabeer ya zauna nan suka tsaftace shi aka sanya mishi turaren wuta aka shimfid'a tabarmi don nan zasu sauki bak'in su.
Bayan Suhaima ta k'arasa gyaran gidan taje tayi wanka ta shirya cikin wani maroon less d'inkin riga da skirt sunyi mata kyau sannan ta zuba hijab agurguje ta fice daga gidan don tana kunyar su zo su sameta, ban da wani irin nishad'i da take ji a cikin zuciyar na daban a yau d'in nan gashi tana son ganin kyakkyawar fuskar Sabeer.
Tana shiga gidan Babaa Lantana da sallama a bakin ta suna had'a ido da Babaa Lantana ta sanya dariya tare da cewa
"Oh amarya Suhaima ai na d'auka bazaki bar gidan ma zama zaki yi da na ji ki shiru "
Akunyace tayi 'yar dariya tare da zama a gefen ta tana cewa
"Haba Babaa kinsan bazan iya zama ina jin kunya ne "
"Ai na d'auka ku 'yan zamani babu wannan kunyar a wajen ku ashe da akwai masu ita "
"Uhmmm"
Kawai Suhaima tace kafin ta d'ora da cewa
"Ni daga zuwa kin isheni da surutu ko ruwa baki ban balle ki kawo min abin dad'in da Baba ya kawo miki "
"Lallai gidan bakon ki ne ko yau kika ta6a zuwa ai kinsan hanyar wajen ajiye ruwan"
"Tabbb d'an tsohon nan naki yana kok'ari nasan shima idan ya dawo gida ko ruwan sha bakya kawo mishi "
'Yar hararar wasa Babaa Lantana tayi wa Suhaima kafim tace
"Ku yanzu mai kuka iyama a yiwa miji hidima, wata ma miji ya dawo daga aiki ko sannu da zuwa babu balle aje batun kawo mishi ruwa mai sanyi ya jik'a mak'ogaran shi, wata ma ko kallon inda yake baza tayi ba balle yasa ran ayi mishi magana duk wata kulawar miji da hidimar shi ba'a fiye sauke mishi ba sai afkin kwalliya kamar ta aljanu da kyalakyalen da basu zu amfane su ba, wata ma ba don mijin nata zata yi kwalliya ba sai don zata fita anguwa gasu nan da yawa muna gani kuma muna jin labari, idan kika ga wata awaje ma fes da ita idan kika je gidan watak'il ko ruwan gidan baza ki iya sha ba sannan....."
"Kaiii Babaa Lantana daga tsokana zaki d'auko dogon sharhi haka kamar wata ma'aikaciyar gidan redio sai zuba kike "
Cewar Suhaima kenan bayan ta katse Babaa Lantana daga maganar da take.
D'an hararar ta tayi kafin tace
"Yo ai gaskiya nake fad'a da kin barni na cigaba sai ki d'auki abubuwa masu amfani ke da zaki tafi birni ga mijin ki kyakkyawa kamar balarabe don nasan baza ya rasa mata masu rububin son shi ba, don yanzu mun zo wani irin zamani da sam wasu matan basu da alkunya sai kaga mace har mace amman ta zubar da k'imar ta tana furta wa namiji so babu kunya wannan abin yana ban takaici "
"Allah ya kyauta "
Abin da Suhaima tace kenan tana jin wani abu yana mata tuk'uk'i cikin zuciyar ta da taji Babaa Lantana tace yanzu haka da akwai wasu matan da suke son Sabeer wad'anda suka fita kyau, wayewa da ilimi na boko tunda ita iyakar ta secondary kawai.
"Yanzu me kika shirya mishi wanda zai ci idan yazo? "
D'an yatsina fuska Suhaima tayi tare da cewa
"Tabbb ni ban wani shirya mishi komai ba sai abubuwan da aka tanadarwa bak'in"
Kama baki Babaa Lantana tayi sannan tace
"Allah ya shirye ki Suhaima yanzu baki d'an yi mishi abu na musamman ba shi d'aya haka ake tar6ar saurayin"
Cikin yanayin shagwa6a tace
"Toh ni me zanyi mishi kawai yaci wannan na gaji tun safe nake aiki wallahi "
"Ke tafi can tsaya sanyin jiki na kwace miki shi "
Dariya Suhaima tayi kawai nan Babaa Lantana ta tashi ta fara kiciniyar aiki.
"Babaa me zaki yi ne haka? "
D'an hararar ta tayi kafin tace
"Tsaya ki gani yarinya kiga yanda ake tar6ar bak'o "
D'an ta6e baki Suhaima tayi tare da kwanciya tana ganin yanda Babaa Lantana take zirga zirga k'arshe ma fita tayi daga gidan, tayi mintuna goma da fita sai ga ta da kaji biyu yankakku ta cigaba da aikinta bata k'ara bi takan Suhaima ba.
Phone nata ta d'auka ta bud'e data da yake tayi downloading what's app da Instagram sai fb da yake taga yanda Jiddah take charting shi yasa batasha wahala wajen iyawa ba, message's ne suka fara shigowa duk da iya Jiddah da Sabeer ne kawai take what's app dasu sai wani group na kitchen da na novels sai na make up wanda Jiddah ta sanya ta.
Kan number d'in Jiddah ta shiga nan taga ta turo wani video tare a tsokanar ta amarya, bud'e videon tayi bayan ya gama bud'e wa sai ta fara kallo tun tana murmishi har ya sanya ta fara tuntsira dariya ganin irin shagwa6ar da Sabeer yake yiwa su Daddy sai kace wani d'an yayen yaro k'arami dariya tayi sosai har da hawaye, Babaa Lantana kuwa sakin baki tayi tana kallonta kafin kuma ta girgiza kanta tana cewa
"Allah ya shirya "
Ta wuce ta cigaba da aikinta.
Bayan ta gama dariyar ta fad'a dogon tunani daman haka Sabeer yake duk da tasan daga yanayin shi zai yi shagwa6a bata zaci shagwa6ar zata yi haka wani murmishi kawai take saki wanda ita kadai tasan ma'anar shi.
Wajen misalin karfe 2 na rana su Daddy suka k'araso tare da jagorantar Sabeer don yana son ganin Babyn shi, suna k'araso wa sun samu kyakkyawar tar6a daga wajen Yaya Aliyu, Baba Adamu da kuma wasu amintattun dattijai biyu abokanan Baba Adamu kuma mak'obtan su, su Daddy sunyi mamakin ganin irin wajen da Sabeer yaje neman aure duk da haka kuma k'auyen ya basu sha'awa gashi sun ji dad'in tar6ar karamcin da aka yi musu.
Bayan sun yi sallahr azahar ne don a hanya ta riske su, sai aka yi zaman gaisawa kafin kuma a fara cin abinci, a d'an kyamace suka fara kai abincin bakin su amman da suka ji irin dad'in d'and'anon shi tuni suka zage suka fara ci.
Ganin sun fara cin abincin ce yasa Sabeer zamewa zuwa cikin gidan suka gaisa da Aunty Aliyah sannan ta fad'a mishi a inda Suhaima take wani murmishi ya saki kafin ya fita kuma.
"Wannan 'yar tsohuwar me kike girkawa ne duk kin cika min hanci da k'amshi yawu na sai tsinke wa yake "
Cewar Suhaima tana shiga madafin Babaa Lantana wadda ke zaune akan kujera 'yar tsugunno tana faman yin aiki.
"Tafi can ki ban wuri kina kallo ina faman aiki ko kizo ki taya ni da yake ci ne ai gashi kin taho, toh ko d'and'ane bazan baki ba na megidan nawa ne "
Dariya Suhaima tayi tare da cewa
"Yanzu duk wannan kamshin da nake shak'a ace baza'a sammin ba haba 'yar tsohuwa ta kaina "
"Yarinya duk dad'in bakin ki bazan bayar ba ki bari idan yaci ya rage kyaci sauran "
D'an turo baki tayi cikin sigar shagwa6a tace
"Nayi ma fushi bazan ci ba "
"Da naji dad'i kuwa "
Cewar Babaa Lantana tana tattare kayayyakin zuwa cikin kitchen, nan ta shirya farfesun kaza da tayi mishi guda d'aya sai gashashshiya kaza d'aya tasha kayan had'i da mai sai shek'i da tashin k'amshi take, sannan ta dama mishi fura da ruwan randa mai sanyi ta zuba ta a dogon kofin silver, sauran kayan ma a cikin kwanan silver ta zuba sai ta d'ora saman farantin silver, bayan ta gama had'a su ne ta fito daga d'akin girkin tana cewa
"Gashi nan na gama shirya komai sauran ya zo ki kasa kawo mishi don nasan an fad'a mishi kina nan zuwa kowanne lokaci zaki iya ganin shi ".
Suhaima na dariya tace
"Toh naji 'yar tsohuwa sannun ki da aiki don nasan yau kika kwanta sai kin kasa motsi saboda gajiya "
Da harara ta bita kafin tace
"An gaya miki jikina irin naki ne koda zan yini aiki ras zaki ganni, Allah Suhaima ki rik'e yaron nan sosai saboda yana son ki wallahi na tsakani da Allah "
Tana gama fad'in haka ko rufe baki bata yi ba suka jiyo sallamar Sabeer aikuwa da gudu Suhaima ta fad'a d'akin Babaa Lantana, sosai abin ya bawa Babaa
Lantana dariya.
Kallonta Sabeer yayi had'e da cewa
"Matar ke dawa kike dariya haka? ".
Cikin dariya tace
"Ni da wannan matar da kake kok'arin jajibowa ne daga jin sallamar ka ta kwasa da gudu sai kace wadda taga wani abin firgitarwa ".
Murmishi ya saki tare da cewa
"Babyn tawa ce kunya ce da ita Babaa, amman gashi ai kin hutashshe ta sai ki min sannu da zuwa "
Washe hakora Babaa Lantana tayi tana cewa
"Eh mana rabu da ita ni na kwace ka ai tun da babu abin da ta fini "
Sosai maganar ta bawa Sabeer dariya, Suhaima na jin su a d'aki tana mirmishi ita kadai.
"Ai sai ki fita ki kai mishi tabarma kyayi murmishin da dalili ba ki k'ule d'aki kina murmusawa ba ke d'aya "
"Kaiii Babaa "
"Ni dai ki tafi maza kin bar mutum a tsaye "
Babaa Lantana ta fad'a tana mik'awa Suhaima sabuwar tabarma, kar6a tayi sannan ta fito daman Allah ya taimake ta da hijab d'in ta a jikinta.
Fitowa tayi daga d'akin tana d'aga kai suka had'a ido da Sabeer sai kawai ta zuba mishi don yayi mata kyau sosai duk d'an bak'in nan da yayi da rama ya washe tsaf dashi, yana sanye cikin wani black jeans and T-shirt black mai kwala sai kuma ya d'ora wata yellown T-shirt mai dogon hannu daga sama, takalmin shi baki haka ma belt d'in shi sai agogon hannun shi k'irar Gucci shima bak'i, gashin kannan nashi yasha gyara sai shek'i yake gwanin sha'awa, shagala da kallon shi Suhaima tayi haka shima kallon ta yake don tayi mishi kyau ba kad'an ba.
"Idan kun gama kallon junan naku sai ka zauna ni na wuce d'aki zanyi bacci ".
Firgigit suka dawo hayyacin su tamkar wad'anda suka tashi daga bacci, saboda jin muryar Babaa Lantana da suka yi a kusa dasu duk kunya ce ta kama su ba irin Suhaima da take ji tamkar ta nutse a k'asa, wayance wa tayi da shimfid'a tabarmar yayi da Sabeer yake sosa kai, murmishi Babaa Lantana tayi ta wuce d'aki ta bar su.
Bayan ta gama shimfid'a tabarmar ne cikin sanyin murya tace
"Ka zauna mana "
Zama yayi yana cewa
"Baby ki k'ara kyau mene sirrin "
Kunya taji ta sake tuk'unk'une wa cikin hijab, sai kawai ta fara gaida shi amsawa yayi cikin murmishi.
Suna gama gaisawa ta tashi ta d'auko mishi abubuwan da Babaa Lantana ta had'a ta ajiye mishi tare da da ruwa da lemo wanda aka aka siyawa bak'i Babaa Lantana ta tura aka kar6o na Sabeer.
"Baby nah yanzu baza ki bud'e min fuskar na ganki sosai ba? "
D'an murmishi tayi har dimple nata ya lotsa kafin tace
"Ni dai kaci abinci kawai nasan mybe ko breakfast baka yi ba "
"Kamar kin sani Baby don ruwan tea nasha cup d'aya saboda kawai ina saurin nazo na ganki don nasan idan nazo baby nah zata had'a min irin abincin ta mai dad'i "
D'an murmishi kawai tayi cikin zuciyar ta tana sake godewa Babaa Lantana da tayi tunanin dafa mishi wani abin.
Zuba mishi tayi ya fara ci yana santi don gashin kazar yayi mishi dad'i sannan yasha furar sosai ba laifi, bayan ya gama ne suka d'an fara hira irin ta masoyan gaske.
"Wai ina Sabeer ne? "
Cewar uncle Aminu, nan suka dudduba bashi ganshi ba, Daddy ne yace
"Mybe yana wajen Babyn tashi can nasan zai gudu "
"Kaji ja'irin yaro shine yabar mu salon mu gama yanke magana ya dawo yana cewa ba haka ba "
Fad'in Uncle Aminu dariya suka yi kawai irin tasu ta manya, Daddy sai kallo Aliyu yake don yaron ya birgeshi da gani yana da nutsuwa da kamun kai, yana fatan haka itama Suhaima Allah yasa haka take.
Nan aka kirawo shi a waya, suna tsaka da hira yaji kiran nashi dole babu yanda zai yi ya tafi wajen su don shi fah gaskiya bai gaji da ganin Babyn tashi ba.
Bayan ya je wajen nasu aka fara tsaida lokacin biki inda Sabeer ya nemi a sanya sati uku, su Baba Adamu suka nuna yayi kusa dakyar nan dai aka bar shi a 2 month's, nan suka zube kud'ad'an neman aure har da na sadaki, kasa kar6ar kud'in su Baba Adamu suka yi don gani suke tamkar siyar musu da Suhaima zasu yi, dakyar suka lalla6a su suka kar6a anan suka sake tabbatar wa lallai 'yan uwan Suhaima basu da son abin duniya.
Cikin farinciki suka yi sallama da junan su, har sun shiga mota suka ga Sabeer zai bar wajen kamo hannun shi Daddy yayi tare da cewa
"Son ina zuwa ne? "
Yana sosa kai yace
"Daddy zanje yiwa Baby sallama ne "
Murmishi manya Daddy yayi tare da cewa
"Mun baka