Showing 51001 words to 54000 words out of 122360 words

Chapter 18 - A sanadin Son ki Hausa Novels Document complete by Aisha A Muhammad Sanaz.txt

ta k'arasa kusa dashi da sauri tace
"Ashiru don Allah ko kaga Sabeer? "


Da murmishi a fuskar shi yace
"Eh yana cikin gonar Yaya Aliyu a zaune yanzu na barshi acan na taho d'auko abu "
ajiyar heart Suhaima ta sauke tare da hamdala jikin zuciyar ta kafin tace
"Yawwa nagode Ashiru"


Tana gama fad'in haka ta wuce da sauri zuwa cikin gonar Yaya Aliyu, yayin da Ashiru ya wuce cikin gida.


Tana k'arasa gonar ta fara dube duben inda yake ta d'an jima tana dubawa kafin ta hango shi kan wani dutse mai d'an girma a zaune, kallo d'aya zaka yi mishi ka fuskanci yana cikin damuwa.


Ta jima tana kallon shi hawaye na zuba a idanunta na tausayin Sabeer kasa k'arasa wa inda yake tayi kawai ta tsaya tana kallon shi, jikinshi ne ya bashi ana kallon shi yasa shi d'ago kanshi yana dubawa ya hango Suhaima a tsaye ta zuba mishi ido, d'an murmishi ya saki na yak'e kafin kuma lokaci d'aya ya zaro ido waje fuskarshi d'auke da tsantsar tashin hankali da k'arfi ya furta


"Suhaima! "
Bazato Suhaima taji ya kirawo sunanta fuskarta d'auke da murmushi itama ta furta
"Sabeer! "
Ganin batasan abin da ya hango ba ne bane yasa shi zabura ya mik'e da wani irin gudu da zafin nama ya k'arasa inda take tsaye bai yi wata wata ba ya ture ta gefe guda ta fad'i k'asa.


Arud'e ta d'ago kanta ta kalle shi inda kuma a daidai lokacin Sabeer ya saki wata k'ara da k'arfin gaske ya fad'i k'asa yana wani irin abu kafin kuma jikin shi ya sandare kamar matacce ya zama, cikin hargitsi Suhaima ta mik'e tsaye ta taho inda Sabeer yake kwance, sauran taku d'aya tayi ta k'arasa wajen ta hango abun da ya matuk'ar firgitata ya tsorata ta lokaci d'aya jikinta ya hau rawa na tsoro ko kwakkwaran motsi ta kasa balle ta nemi agaji.......






Uhm ga Sabeer a kwance kamar matacce ko mene ya same shi sai ku biyo ni don jin abin da ya faru, mu had'u a next page don jin yanda zata kasance, ku cigaba da hak'uri fan's.




Aishat A Muh'd ✍🏻
*A SANADIN SON KI*




Written by
Aishat A Muh'd


Dedicated to my Sadeey SaNaz







*PAGE 61-62*








Ba wani abu Suhaima ta gani ba wanda yayi matuk'ar razana ta sai wani k'aton snake baki wuluk dashi wanda batayi tantama ba shine ya harbi Sabeer, ganin yayi kanta ne yasa ta bud'e muryar ta gaba d'aya ta zuba wata k'ara ta firgita, gaba d'aya jikinta rawa yake yi saboda tsabar firgita rufe idanunta tayi kawai ta sadakar kasheta zai yi.


Kafin ya k'arasa inda take ne Aliyu da Ashiru wanda suka taho gonar suka jiyo k'arar Sabeer a rud'e suka taho da gudu suna gaf da k'arasa inda suke ne suka sake jin k'arar ihun Suhaima da gudu suka k'araso ganin abin da yake kok'arin cutar da ita ne ya sanya su nufar inda yake nan Ashiru da Yaya Aliyu suka far masa da duka sai da suka kasheshi tsab tukunna suka k'arasa wajen da Sabeer yake kwance Suhaima tana rik'e dashi tana kuka kamar ta shid'e.




Hankali a tashe suka k'arasa wajen sannan Yaya Aliyu da Ashiru suka d'auki Sabeer suka nufi gida, Suhaima tana biye dasu kamar tayi hauka saboda tashin hankali.


Suna k'arasa gida suka shigar dashi gida nan aka kirawo mai magani na gargajiya ya fara aikin shi har ya cire dafin a k'afar Sabeer inda macijin ya cijeshi, sannan ya sanya magani a wurin nan yace musu zai iya farkawa a koda yaushe don ya auna arzik'i saboda macijin da ya harbe shi yana da dafi sosai, sannan ya ba da maganin da zai yi amfani dashi daga k'arshe kuma yace idan ya farka a kirawo shi sannan yayi musu sallama ya tafi.




Aliyu da Aunty Aliyah hankalin su ba k'aramin tashi yayi ba kada d'an mutane ya mutu ta sanadin su haka kuma ta 6angaren Suhaima kuka sosai take tana zaune kusa da Sabeer idanun nan tamkar wad'anda zasu zazzago saboda kuka duk ta d'auki laifin ta d'ora wa kanta me yasa Sabeer bai bari ya harbe ta ba ya tureta, da dare wajen 11pm dakyar Yaya Aliyu da Aunty Aliyah suka lalla6a Suhaima ta tafi d'akin ta sai dai sam babu bacci a idanunta balle kuma maganar abinci.




Wanda rabon da taci tun da rana shima ba wani ci tayi sosai ba, ko yunwar ma bata ji baccin ma k'in yi tayi don gani take idan bacci ya d'auke ta kafin ta tashi Sabeer ya mutu tayi kukan har hawaye sun daina fita daga idanunta gashi sun kumbura sunyi ja sai zugi suke mata da rad'ad'i, daga k'arshe alwala ta d'aura ta shimfid'a abin sallah ta fara sauke sallahr mangarib da ishsha sannan ta fara nafila tana mai mik'a kukanta wajen Ubangiji ya tashi kafad'ar Sabeer tsayin daren nan a haka ta d'auka tana nafila sai da tayi sallahr asubah bacci yayi awon gaba da ita mai nauyi.






*_ Washe gari 11am_*


Firgigit Suhaima ta farka da baccin da yayi awon gaba da ita idanunta ta sauke kan agogo taga har 11 na safe mamakin nauyin baccin da ya d'auke ta take kafin kuma brain nata ya tunano mata abin da ya faru jiya da yammaci.


Zumbur tayi ta Mike cikin kid'ima ta fita daga d'akin, babu kowa a tsakar gidan kai tsaye d'akin Sabeer ta nufa ta shiga ko sallama bata samu damar yi ba.


Ta kutsa kai ciki a kwance yake sai Yaya Aliyu da yake sanya mishi magani a k'afar wajen harbin micijin daga gefe kuma Aliyah ce zaune ta zabga tagumi fuskarta d'auke da damuwa.


Zubewa Suhaima tayi a k'asa kusa da Sabeer cikin rawar murya tace
"Yaya bai farka ba har yanzu? "
Cikin damuwa Yaya Aliyu yace
"Eh Suhaima bai farka ba amman ki cigaba da yi mishi addu'a Allah ya tashi kafad'un shi "


Wani marayan kuka Suhaima ta saki nan Aunty Aliya ta janyo ta jikinta tana rarrashin ta, ana cikin haka sai ga Babaa Lantana, Baba Adamu da kuma Ashiru sun shigo kowanne hankali shi a tashe Ashiru har da kukan tausayin Sabeer.




Nan suka zauna kowa yayi jugum sai sautin kukan Suhaima ne yake tashi a cikin d'akin, sai da azahar tayi tukunna suka fita don yi sallah, Suhaima kuwa a d'akin tayi sallah ko wanka yau babu saboda tashin hankali (oh su Suhaima ashe dai ana son Sabeer ana tsoron kada ya margaya......lol ).


Bayan ta idar da sallahr ne ta zauna kusa dashi tana mishi addu'a duk ta wani rame saboda tashin hankali, har yammaci dai Sabeer bai farka ba kuma still har zuwa yanzu Suhaima na zaune a d'akin babu abin da yake fitar da ita sai alwala.


Sai bayan sallahr mangarib ne Suhaima na zaune kusa dashi taga ya farka a razane tare da yin magana da k'arfi yana cewa
"Suhaima ki gudu maciji ne a bayanki Suhaima....! "
Ya k'arasa maganar da fad'in sunan Suhaima da k'arfin gaske, da sauri Suhaima ta k'ank'ame hannun shi ana cikin haka Yaya Aliyu ya shigo da gudu bayan shi Aunty Aliya ce yana ganin Sabeer ya farka sai dai a razane yake cikin farinciki Aliyu ya rungume shi yana zubar da hawaye cikin zuciyar shi yana godiya ga Allah da ya sanya Sabeer farka wa.


Nan dai aka kirawo mai magani ya duba shi ya bayar da wanda zai sha tukunna ya tafi, Suhaima tana zaune a gefe ta zubawa Sabeer ido hawaye farinciki na zuba a idanunta.


Tun da Sabeer ya fara nutsuwa daga firgitar da yayi suna had'a ido da Suhaima da yayi mata kallon seconds ya d'auke kanshi bai k'ara kallonta ba, a hankali ta matso kusa dashi cikin sanyin murya tace
"Sannu Sabeer "
Ko kallon inda take baiyi ba ya d'auke kanshi, sau uku tana mishi sannu amman k'arshe sai ya kwanta kawai ya juya mata baya kawai.


Tuni Suhaima ta tsure sai faman rarraba ido take gaba d'aya jikinta yayi sanyi, kallon ta Aliyu yayi tare da cewa
"Suhaima tashi kije kiyi wanka kici abinci, yau fa ko wanka da abinci baki yi ba tunda ya farka kije ki huta "


Cikin sanyin jiki da rawar murya tace
"Toh Yaya "
Tana gama fad'in haka ta mik'e jiki babu kwari ta fita yayin da Aliyu da Aliyah suka bita da kallon tausayi lallai Suhaima ta fara son Sabeer bana wasa ba.


Tana fita Sabeer ya tashi zaune tare da cewa
"Aunty ko zan samu ruwan d'umi nayi wanka "
"Sabeer ka hak'ura da wanka sai gobe yanxu kayi brush kasha ko tea ne sai kasha maganin "
Cewar Aliyu kenan.
"Toh amman bazan ji dad'in jikina ba wallahi"
Sabeer ya k'arasa maganar cikin shagwa6a abin ka da shagwa6a66e komai zai yi saiya sanyo shagwa6a murmishi kawai suka yi suna mai sake bashi hak'uri, daga nan yayi brush yasha tea sannan aka bashi magani dakyar yasha yana yatsina fuska saboda ya tsani shan magani balle wanda bai ta6a shan irin shi ba tunda Dr Faridah ta kawo shi duniya, a wannan daren dakyar bacci ya d'auki Sabeer saboda sharewar da ya yiwa Suhaima ta tsaya mishi a rai sam bai ji dad'in abin da yayi mata.




Haka ma Suhaima dakyar ta iya yin wanka ta d'an ci abinci sannan ta kwanta bacci sai lalla6awa yayi ya d'auke ta.






Abu kamar wasa Sabeer baya kula Suhaima duk da tana kok'arin shigowa sau biyu safe da dare tana duba shi wani lokacin har da rana tana kawo mishi abinci amman baya kallon inda take balle ya amsa sannun da take mishi, gaba d'ayan su ba k'aramin hora junan su suke ba har Sabeer ya warke ras yana fita amman bai daina share Suhaima ba duk da ya karanto tsantsar sonshi akan fuskarta da cikin idanunta, kullum itace cikin gyaran d'akin shi.




Da sallama ta shigo d'akin hannunta da k'aramin flaks da cup wanda tayi mishi kunun gyad'a ta shigo d'akin, wani sanyin dad'i ne ya ratsa Sabeer jin sautin daddad'ar muryar Suhaima don rabon da yaji muryar tun jiya da safe saboda ciwon kan da ya hanata zuwa inda yake, amman sai ya maze ya amsa sallamar dakyar tare da d'auke kallon shi daga saitin k'ofar.


Shiga tayi ta same shi zaune kan katifa yana danna laptop yana sanye da wani 3quater da T-shirt mai k'aramin hannu yayi kyau sosai ga gashin jikinshi sun kwanta luf dasu gwanin sha'awa, zama tayi a gefen katifar tare da ajiye abin hannun ta a k'asa tace
"Wash! Na gaji yau, ya jikin ka? "
D'an kallonta yayi na D'an second's tayi mishi kyau cikin wata gown light blue tayi rolling da black veil sai tayi kyau sosai duk ire iren kayan da Jiddah take bata ne, d'auke kanshi yayi cikin zuciyar shi yana cewa zai sanya a kawo wa Suhaima gowns masu kyau daga dubai don ganin yanda suke mata kyau sosai.


"Uhm... Uhm ga kunun gyad'a nayi maka na zuba maka? "
"Bana sha tafi da abin ki "


Da d'an sauri ta kallo shi sai taga hankalin shi yana kan laptop, wani abu ne ya tokare mata makogaro muryar ta na rawa tace
"Don Allah kasha tun d'azu nake aikin yi maka shi fah please "


"Nace bana sha ana dole ne ko kuma na sanya ki "
Hawaye ne suka zubo akan face nata kafin kuma ta fashe da kuka ta fara diddira k'afa a k'asa kamar wata small babe, hankalin shi a tashe ya ajiye laptop d'in tare da cewa
"Toh ni me nayi miki da kike min kuka? "
Cikin shagwa6a tace
"Ba... Ba kai ne ba kace min baka sha kuma sai fushi kake dani bakason kula ni"


Nan ta cigaba da kukan sosai ta bashi dariya hannun shi ya sanya ya rik'o hannunta don bazai jure ganin Suhaima a haka ba tana mishi kuka agaban shi, had'uwar hannun su waje d'aya shi ya saukar musu da wani yanayi a tsakanin su, sake runtse hannunta yayi da d'an k'arfi har sai da Suhaima tayi d'an k'ara kad'an.


D'an sassauta rik'on yayi tare da cewa
"Sorry! "
Can k'asan mak'oshi yayi maganar.


"Don Allah Sabeer kayi hak'uri bana jin dad'in baka min magana idan na duba ka "


Girgiza kanshi yayi idanunshi cikin nata yace
"Komai ya wuce Suhaima but zan tafi na bar muku gidan ku "
D'an zaro ido tayi tare da cewa
"Saboda me? "
"Saboda wanda nazo domin ita bata sona gwara na hak'ura na koma inda na fito "


D'an shiru tayi kafin ta d'ago kanta tace
"Waya ce maka ba'a son ka "
"Ke kika fad'a min "
Ya k'arasa fad'i yana nunata da hannu.
"Ni.... ni ba haka ba fah nake nufi ba kawai dai...... "
Kasa k'arasa fad'a tayi don ganin yanda ya zuba mata ido tamkar wanda zai cinye ta da idanun shi......






Aishat A Muh'd ✍🏻
*A SANADIN SON KI*




Written by
Aishat A Muh'd


Dedicated to my Sadeey SaNaz







*PAGE 63-64*








Kasa k'arasa fad'in maganar tayi ganin yanda ya zuba mata ido tamkar wanda zai cinye ta da idanun shi, jin tayi shiru ne kuma ta sunkuyar da kai yasa shi sanya hannun shi ya d'ago face nata kafin yace


"Uhm ina jin ki Baby kawai dai me ".
Kasa jure kallon cikin idanun shi tayi sai ta lumshe idonta, kallon eye's lashes nata kawai yake cike da sha'awar kissing nasu sai dai ba yanzu yake son aikata hakan ba, d'an bud'e idonta tayi suka had'a eye's nasu kafin cikin d'an jin kunya Suhaima ta janye idanunta saboda ganin har idonshi ya fara canja launi tace
"Ya wuce fah, yanzu ka hak'ura zaka sha kunun ? Kada kace min a'a please "


Mak'e kafad'a yayi cikin shagwa6a da langa6e kai yace
"Nak'i wayon sai kin fad'a min idan ba haka ba bazan sha ba yarinya "


Sam Sabeer ya mance da duk wani shiri da yayi na share Suhaima, lallai ba k'aramin so yake mata ba, maganar tace ta katse mishi tunanin shi da yaji tana cewa
"Haba Yaya nah na zuba maka "
Dariya ta bashi sosai jin sunan da ta kirawo shi.
"Yaya na koma yau kuma?, wannan ai sunan Babban Yaya ne ni miji ne ba Yaya ba "


D'an rufe hannunta tayi da tafin hannunta sai ta d'an wara yatsun tana kallon shi ta haka kafin tace
"Ai kaima kazama Yaya tunda Yayan Jiddah ne kuma ka girme ni"
Tana gama fad'in haka ta janyo cup ta had'a mishi kunun ta ajiye mishi a gefen shi.
"Koh! "
Ya fad'in hakan yana kashe mata ido d'aya wani kunya ne ya sake kama Suhaima sai kawai ta mik'e zata gudu har zata fice daga d'akin taji yace
"Suhaima har zuwa yaushe zaki furta min kina sona ne?, ki tausaya wa rayuwata Suhaima ki amshi soyayyata nayi alkawarin kasancewa dake cikin tsayin rayuwata bazan ta6a wulak'anta ki ba ko na guje miki ina yi miki wani so wanda baki bazai iya kwatanta miki ba "
Cikin sanyin murya ya k'arasa fad'in haka fuskar shi d'auke da damuwa.


Jikinta ne yayi sanyi sosai har ta gaza d'aga k'afanta sai kawai ta tsaya itama zuciyar ta yayi rauni sosai ga wani sabon son Sabeer da ya k'ara shiga cikin zuciyar ta, gashi yanda ya sadaukar da rayuwar shi don ya ceci nata lafiyar da rayuwar koda iya hakan tasan Sabeer ba k'aramin sonta yake ba don haka bazata bar wannan damar ta kubce mata, don haka batasan lokacin da bakin ta ya furta


"Ina sonka Sabeer nima bazan iya rayuwa babu kai ba "
Tana k'arasa fad'in haka ta juya da gudu tabar d'akin cikin jin kunya.


Sabeer kuwa zaune yake kamar mutum mutumi saboda tsabar mamakin abin da ta furta mishi, anya ba mafarki yake ba kamar yanda ya saba tunanin shi da ne ya katse a lokacin da hannun shi ya dangwarar da cup d'in kunun gyadar har yayi nasarar zubo mishi a hannun shi wata 'yar k'ara ya saki kad'an, kafin kuma ya wuntsala kan katifar ya fara juyi na jin dad'i tabbas ba mafarkin da ya saba ba ne, da gaske ne Suhaima tace mishi tana son shi, sai da ya gama juyin murna sannan ya d'auki phone nashi num d'in Daddy ya lalubo ya kira.


Daddy yana picking ko sallama Sabeer bai yi ba saboda tsabar zumud'i cikin murna yace


"Daddy ka tayani murna Suhaima tace tana sona zata aure ni Daddy! "
Wani sanyin dad'i ne ya kwaranya cikin zuciyar Daddy fuskar shi cike da fara'a yace
"Alhamdullilah congrats son, yaushe zaka dawo don muna kewar ka? "
Yana dariya Sabeer yace
"Very soon Daddy! "
"Okay ya kamata ka dawo sai a fara maganar aure, uhm son za'a zama babba "
"Kaiiii Dad! har da tsokana koh? "
Ya fad'a cikin shagwa6a, dariya Daddy yayi kafin su cigaba da hira har zuwa lokacin da suka yi sallama, kwanciya Sabeer yayi ya lumshe idanun shi yana tuno lokacin da Suhaima take fad'a mishi tana son shi zata aure shi da wannan tunanin bacci yayi awon gaba dashi.


Lokacin da Suhaima ta fito da gudu daga d'akin Sabeer sauran kad'an ta bige Aunty Aliya tayi saurin kaucewa tana cewa
"Sorry Aunty nah"


"Lafiyan ki kuwa Suhaima? "
Fad'in Aliyah kenan.
"Aunty lafiya qlau wallahi "
tana gama fad'in haka ta wuce d'akin ta da sauri yayi da tabar Aliyah baki sake tana kallonta.


Kan bed ta fad'a tana murginawa akai tana wani murmishi dagani murmishin farinciki ne take, jinta take sakayau kamar ta sauke wani babban abu akanta.


"Ina son ka Sabeer, i luv U so much "
Fad'in Suhaima a fili tana rufe fuskarta da hannunta kamar mai jin kunya wani na ganin ta.




Tun daga wannan lokacin wata tsaftacacciyar soyayya ake gudanarwa tsakanin Sabeer da Suhaima, bawa junan su kulawa suke tare da tattalin juna, Yaya Aliyu, Aunty Aliya da su

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login