Showing 87001 words to 90000 words out of 122360 words

Chapter 30 - A sanadin Son ki Hausa Novels Document complete by Aisha A Muhammad Sanaz.txt

daga room d'in Dr Nabilah ta nufi office d'in Dr Faridah sauran nurses d'in kuma suka nufi nasu office d'in, tura k'ofar tayi a hankali ta shiga Sabeer na ganin ta ya tashi da sauri ya matsa kusa da ita yace
"Dr fad'a min awane yanayi Suhaima take, kada kice min ta mutu please"


Kallon shi Dr Nabilah take cike da tausayi dakyar ta iya cewa
"Yalla6ai munyi nasarar dawowar numfashinta yanzu haka nayi mata allurar bacci sai dai muna buk'atar jini don tayi bleeding sosai "


Ajiyar zuciya ya saki tare da hamdala kafin ya kuma cewa
"Cikin jikinta fah yana nan? "
Kasa magana tayi tuni Sabeer ya shiga cikin wani yanayi na daban mara misaltuwa.


"Am sorry Yalla6ai cikin ya fita duk iya kok'arin da muka yi bai zauna ba"


Sauran kad'an Sabeer ya fad'i da jin abin da tace mishi jikin shi har rawa yake ya zauna kan kujera cikin rawar murya idanun shi tap da hawaye yace
"Innalillahi wa'inna ilaihhir raji'un, Mumy.... Mumy shikenan d'ana ya tafi bazai dawo ba "


Dr Faridah wadda ta sauke ajiyar zuciya na kwanciyar hankali jin cikin ya fita sai dai kuma ta tausayawa yaron nata, da hannu tayi wa Dr Nabilah alama da ta fita.


Rungume Sabeer tayi wanda yake kuka sosai kafin daga karshe kuma ya daina kukan kiran Daddy yayi yana fad'a mishi kamar Daddy yayi wa Sabeer kuka haka yaji saboda yasan yanda Sabeer yake bala'in son ciki kodayaushe zancen shi Suhaima zata haihu ya samu Baby shima.




Sabeer fita yayi zuwa room na Suhaima wanda aka kwantar da ita, kallonta yake duk ta rame tayi wani irin haske daga ni bata da ishashshen jini ajikinta, hannun ta mara drip ya rik'e gam yana kallon ta hawaye na fita a eyes nashi.




Daddy ne ya shiga office d'in Mumy cikin fusata, kallon ta ya tsaya yi kawai har sai da Mumy ta tsorata sosai, kallon ta kawai yake amman sam bai yadda da zubewar cikin Suhaima ba sai da dalili don yasan halin Dr Faridah ciki da bai.


Hannun ta ya damk'o da k'arfi har sai da ta saki k'ara tana cewa
"Daddy da zafi fah "
Idanun shi cikin nata yace
"Faridah ki fad'a min gaskiya da sanya hannun ki cikin zubewar cikin matar Sabeer? "


Afrigice Mumy ta d'ago da kanta tace
"Ni..... Ni kuma Daddy ina ruwana da ita ne saboda me zan zubar mata da ciki gidanta nake zuwa kuma saboda irin haka na sanya Dr Nabilah ta tsaya akanta kada naje ace ni na zubar mata gashi nan ma duk da haka ban tsira ba "


"Uhmm Faridah na sanki ciki da bai fah zan bincika dalilin faruwar hakan idan zargina ya tabbata gaskiya zakiyi nadama don daga ni har Sabeer zamu guje ki! "


Yana gama fad'in haka ya tureta sauran kad'an ta kife akan table ya fice daga office d'in, Direct office d'in Dr Nabilah ya nufa.


Bayan ya shiga ne ya samu waje ya zauna yana kallon ta sannan yace
"Inason ki fad'a min gaskiya mene silar zubewar cikin matar Sabeer? "


"Yalla6ai a iya bincike na na gano zamewa tayi ta fad'i a k'asa wanda ya zama silar zubewar cikin "


"Kin tabbatar da hakan? "
"Sosai ma Yalla6ai "
Ta fad'a hakan tana k'ak'alo murmishin yak'e, don Dr Faridah ce ta tsara mata abin da zata ce idan ba haka ba zata koreta daga hospital nata.


Murmishin mugunta Dr Faridah ta saki bayan ta gama kallon maganar da Daddy yayi wa Dr Nabilah ta laptop d'in ta, kwantar da kanta tayi jikin kujera tana juyi tace
"Daddy duk binciken ka bazaka ta6a gane gaskiya ba dole Sabeer ya rabu da matsiyaciyar yarinyar nan "
Ta k'arasa maganar tana dad'a sakin wani murmishin.
Mumy ta mance da _rana dubu ta 6arawo rana d'aya ta mai kaya, za'ayi walkiya duk daren dad'ewa zaku ma a gane abin cikin dubu_






Aıʂɧąɬ A Mųɧ'ɖ ✍🏻
*A̺͆ S̺͆A̺͆N̺͆A̺͆D̺͆I̺͆N̺͆ S̺͆O̺͆N̺͆ K̺͆I̺͆*








Wྂrྂiྂtྂtྂeྂnྂ bྂyྂ
Aྂıʂɧąɬ Aྂ Mྂųɧ'ɖ




ɖɛɖı¢ąɬɛɖ ɬơ ɱყ ʂąɖɛɛყ ʂąŋąʑ




♻ *Eҳ¢ʂųιı۷ɛ щγıɬɛγ'ʂ ʄơγųɱ*





*PAGE 91-92*










Sabeer k'in yarda yayi a zubawa Suhaima jinin kowa sai nashi hakan ba k'aramin k'ara fusata Mumy yayi ba amman ta danne don batason nunwa.


Jiddah itama tayi kuka ta tausayawa Sabeer sosai mutane sosai suka zo dubiyar Suhaima har dasu Yah Aliyu, Aunty Aliyah, Babaa Lantana da Baba Adamu duk sun zo, haka ma friend d'in Sabeer wato Musaddiq da matar shi Mufidah sun zo, kowannen su da abubuwan kayan duban shi.


Sati d'aya Suhaima ta d'auka a hospital ta samu sauk'i sosai don kulawa sosai Jiddah da Sabeer suke bata gashi ma yak'i yarda Babaa Lantana ta zauna saboda shi yake kwana da ita dole ta hakura da zaman jinyar Suhaima, duk da har yanzu tana cikin takaicin zubewar cikinta bata sanya shi cikin ranta sosai ba ita take ma da k'arfin gwiwar rarrashin Sabeer da yayi hak'uri ya kar6i kaddarar da Allah ya d'ora mishi.


Kwanakin ta goma a hospital aka sallame ta don ta warke garau da ita, bayan an sallame su gida suka dawo abin su sosai Jiddah ta gyara mata gidan tsaf sai da tayi mata girki na dare sannan ta tafi gida.


Awannan daren Sabeer yayi addu'a Allah ya sanya kwallon shi ya fad'a raga, sun nunawa junan su so da kulawa sosai a wannan lokacin sai gabanin asubah suka samu damar yin bacci.








_*After 4 Month's*_






Da dare misalin wajen 10 na hango Suhaima tana fitowa daga bedroom nata, tana sanye cikin wata white sleeping dress irin transparent d'in nan gashin ta yasha gyara sai kyalli yake ta zubo shi ga wani k'amshi mai dad'i da take fitarwa tayi kiba abin ta.


K'arasa tayi inda Sabeer yake ta shige jikin shi, wanda tun tahowar ta yake kallonta kasa k'arasa aikin yayi a laptop d'in ya rufe ta tare da janyo ta jikin shi yana shinshina ta yace
"Baby kinyi kyau sosai "
"Thank U "
"Ni fah ice cream nake son sha yanzu "
D'an zaro ido kad'an yayi kan yace
"Baby yanzu fa 10 ta wuce fah kiyi hakuri sai gobe please "


"Allah idan bansha ba bazan iya bacci ba ka taimaka min Yah Sabeer please "
Ta k'arasa maganar kamar zatayi kuka, bubbuga bayanta yake yace
"Okay Okay naji Baby za'a kawo miki yanzu, amman ya akayi na koma Yah Sabeer kuma"


Kashe mishi ido tayi tare da kad'asu tace
"Abin sirri ne "
Yana dariya yaja hancin ta sannan yace
"Bari na dawo a fad'a min sirrin "


Tashi yayi yana kok'arin fita tace
"My dear a sanya min flavours na vanilla and strawberry "
"Okay Baby na"


Fita yayi ya samu driver da bai riga ya tafi gida ba ya tsaya hira da maigadi Sabeer ya aike shi siyo mata ice cream d'in sannan ya dawo ciki.


"Baby fad'a min sirrin da ya sanya aka kirawo ni da Yah Sabeer "
'Yar dariya tayi tukunna tace
"Kaiii my Dear baka mantuwa ni fah ba komai "


"Aikuwa yarinya sai kin fad'a min "


Nan ya fara yi mata cakulkuli tana tuntsira dariya shima dariyar yake sauran kad'an ta fad'o daga saman kujera ya rik'o ta tare da d'orata kan k'afar shi yace
"Baby naga fah alamun Allah ya amshi addu'a ta don kin sake canjawa musamman hips d'in ki da boobs nake sun k'ara cika anya ban ajiye miki ajiyata ba, ga kwanaki biyun nan wani irin kwad'ayi kike ji dashi dama Doctor na karanta kamar yanda Mumy taso nayi da yanzu na gane "


Sai da gaban Suhaima ya fad'i da taji ya ambaci sunan Mumy amman sai ta share tace
"Nima bansani ba my dear amman nasan tunda na dawo daga hospital sau d'aya nayi period d'ina kuma yanzu muna 4 Month's fah "


"Allah nagode maka insha Allah shine ma gobe zan kirawo Dr Aishat ta duba min ke "


Suna cikin haka aka danna door bell Larai mai aiki ce ta bud'e k'ofar ta kar6i sak'on ta kawo wa Sabeer, kallonta Sabeer yake shi sam yarinyar bata kwanta mishi a rai ba shi yasa yake sanya mata ido aduk wani motsinta.




"Hajiya na tabbatar da abin da na fad'a miki don naji suna hirar yanzu "
Daga can 6angaren akayi mata magana nan ta dunga gid'a kai kamar k'adangaruwa alamar tana fahimtar abin da ake fad'a mata, sun d'an jima suna waya kafin ta ajiye wayar nata.


Apalo kuwa bayan Suhaima ta gama shan ice cream d'in ne Sabeer ya d'auke ta suka nufi side nashi, a wannan lokacin kowannen su sai da ya zage wajen nunawa d'an uwanshi irin son da yake mishi, sunyiwa kansu alk'awarruka acikin wannan daren wanda har daga cikin alk'awarin su na zasu rayu da juna har abada bazasu rabu ba da junan su, soyayya sosai suka gwada wa junan su, sai bayan Suhaima ta samu bacci ne Sabeer yaje yayi wanka tare da d'aura alwala ya fito, shimfid'a abin sallah yayi ya fara nafila sai da yayi raka'a biyu sannan yayi addu'a sosai Allah ya sanya Suhaima ciki ne da ita ya dad'e yana addu'ar samun yara nagari tare da addu'ar Allah ya kad'e duk wata fitina da tashin hankali azaman su na aure, sai bayan yayi sallahr asuba bacci mai nauyi ya d'auke shi, ko da Suhaima ta idar da nata sallahr ta tarar ya koma bacci itama jikin shi ta kwanta suka koma baccin nasu da yake weekend ne.






_*10:35 am*_




A lokacin suka tashi daga bacci suka yi wanka simple gown Suhaima ta sanya ajikinta shima Sabeer ya shirya cikin 3quater white da T-shirt white itama a palo ya zauna yayin da Suhaima a gurguje ta shirya musu breakfast.




Kallon Larai tayi tace
"Don Allah d'an had'a min kunun gyad'a cikin cup d'aya "
Jiki na rawa tace
"Toh Aunty "
Sannan Suhaima ta fita daga kitchen d'in, ta kaiwa Sabeer breakfast d'in kan dining table ta had'a mishi komai, zama tayi alokacin ya k'araso inda take yace
"Baby taho nayi feeding d'in ki "
"A'a ni bana son cin komai kunu zan sha kawai "
"Ayyah Baby gashi ni ban iya ba kizo mu je kitchen kina fad'a min nayi miki "


"Kabar shi na sanya Larai ta dama min "
D'an 6ata fuska yayi yana shirin magana Larai ta k'araso wajen gaida Sabeer tayi bai amsa ba sai ma kau da kan da yayi.


Ajiyewa Suhaima cup d'in tayi cikin murmishi tace
"Na gode Larai "
"Ah ba komai duk abin da kike so ki fad'a min Aunty "


Tana gama fad'in haka tabar wurin d'an hararar Suhaima yayi kan yace
"Baby ni fah i hate dis gurl zata bar gidan nan soon a sama miki wata"


"A haba dear me ta tsare maka? "
"Ni bata kwanta min ba a rai "
Murmishi tayi kawi ta fara shan kunun sam Sabeer kasa cin abincin yayi yana kallon ta don sai yaji zuciyar shi na ayyana mishi kunun nan bai yarda dashi ba, amman ganin bashi da wata hujja ne ya sanya shi kawai barinta tana sha.


Bayan ta gama shane ta fara bashi abinci abakin shi ganin yak'i cin nashi, bayan ta gama bashi suka dawo parlour zama Sabeer yayi ita kuma Suhaima ta mik'e tsaye kallon ta yayi kafin yace
"Baby ina zaki? "
"Fitsari nake ji Dear bari naji na dawo "


Shiga bedroom d'in ta tayi ya bita da kallo kawai, Suhaima na shiga bathroom ta tsugunna zata yi fitsari sai kawai ganin jini tayi yana zuba maimakon fitsari, a razane ta mik'e tsaye jikinta na 6ari lokaci d'aya taji marar ta tana k'ullewa kasa d'aga k'afar ta tayi sai kawai ta zube akasan tiles d'in bathroom ta kwallawa Sabeer wani irin kira da k'arfi.




Sabeer da yake zaune yana kallon film d'in furious 7 a mbc 2 yaji kiran da Suhaima take mishi da sauri ya tashi ya nufi d'akin nata kai tsaye bathroom ya bud'e ganin bata cikin d'akin, idanun shi ne suka sauka akan tiles d'in toilet d'in wanda ya kasance fari jini gaba d'aya ya rina wajen, ga Babyn shi durkushe tana murk'usus tare da kiran sunan shi.


Saboda tsabar tashin hankali sau ran kad'an Sabeer ya zube a k'asa jikin shi na rawa ya d'auke ta kawai ya fito daga d'akin da gudu ya nufi hanyar fita daga parlourn.


Larai tana ganin haka da sauri ta shige bedroom d'in Suhaima ta sanya wasu abubuwa cikin drower ta fito.




Gudu kawai Sabeer yake shararawa akan hanya har ya k'arasa hospital d'in Mumy, a rikice yayi parking tare da bud'e bayan motar ya d'auko Suhaima yayi cikin asibitin da ita.




Da Mumy ya fara cin karo fitowar ta daga room d'in operation tana zame hand gloves d'in hannun ta, ganin d'an nata ne tare da Suhaima ya sanya ta kiran nurses suka kar6i Suhaima zuwa wani room na daban, yayin da Sabeer ya zube a k'asa yana kuka sosai, dafa kafad'ar shi tayi jiyowa yayi ya rungume ta had'e da fad'in
"Mumy ina rok'an ki kada ki bari na sake rasa cikin nan please Mumy ki taimaka min "


Tausayin d'an nata ne ya kamata amman tasan dab take da rabuwa su bazata bari tausayin shi yayi rinjaye cikin zuciyar ta ba.


Da kanta ta jagoranci su Dr Aishat da Dr Nabilah zuwa room d'in da aka kwantar da Suhaima don tana son su zame mata shaidu, sunyi nasarar tsayar da jinin sai dai kuma tun kafin suzo asibitin cikin ya zube allurar bacci akayi mata tare da sanya drip suka fito domin neman jinin da zasu sanya mata.


"Mumy ina fatan ban dad'a rasa shi a karo na biyu ba? "


"Yalla6ai yanzu jini muke buk'ata da za'a sanya mata "
Cewar Dr Aishat kenan, dole Sabeer ya hakura da tambayar yaje aka d'auki jinin shi duk yanda Mumy taso ta hanashi yak'i yarda ya biye mata.




Bayan awanni biyar a lokacin Suhaima ta farfad'o in banda kuka babu abin da take yi haka ma Sabeer wanda yayi kuka ya more yana zaune agefen Suhaima ya kasa rarrashin nata.


Shigowa room d'in akayi Daddy ne da Mumy suka shigo sai Jiddah, ko zama basu yi ba suka fita daga d'akin gaba d'aya har Sabeer da Suhaima tare dasu Dr Aishat mota suka shiga sai gida.


Zama suka yi a parlour duk sunyi shiru kafin Daddy yace
"Muna son sanin mene ne musabbabin zubewar cikin Suhaima tun da kune kuka dubata".


"Yalla6ai mun gano inda matsalar take tablet d'in zubar da ciki akesha shine dalilin zubewar cikin "


Ba Suhaima da Sabeer ba hatta Daddy sai da ya d'ago a matuk'ar razane yana kallon Dr Aishat,


"Tabbas kuwa anyi hakan ko zubewar cikin farko ma shan maganin akayi Dr Faridah ce tace kada na fad'a a bari sai ta sake zubar da wani "


"Okay mun gode kuna iya tafiya "
Cewar Daddy kenan, tashi suka yi suka tafi, yayin da Suhaima, Sabeer, Jiddah da Daddy sun kasa cewa komai musamman Sabeer da Suhaima da suka ji abun wani iri.


Cikin kuka Mumy tace
"Innallilahi wa'inna ilaihi raji'un daman nasan za'a rina talaka bai iya samu wuri ba sai yayi rashin mutunci, daman bason Sabeer d'in take ba tun da har bazata iya had'a zuri'a dashi ba take zubar mishi da ciki "


Girgiza kai tayi tana tafa hannu tace
"Aikuwa tun da haka ne wallahi sai Sabeer ya rabu dake rabuwa ta har abada, yanda Allah shi kadai ya bani inason ganin ya tara min jikoki shine don bakinciki da munafarci irin naki kike zubar da cikin har sau biyu to wallahi baki isa...... "


Bata gama maganar ba Daddy ya d'aga mata hannu dole tayi shiru cikin nutsuwa Daddy yace
"Suhaima ki fad'a mana gaskiya shin wannan abin da ya faru da had'in hannun ki aciki?"


Cikin wani irin kuka na tashin hankali tace
"Wallahi Allah Daddy bansan komai akai ba ban ta6a shan wani magani ba na rantse da Allah "


"Daddy Allah Suhaima bazata sha magani ba don ta zubar da ciki tana son Sabeer bazata iya aikata haka ba sai dai idan sharri akayi mata wallahi a fad'i wanda yake bata abu taci a lokacin sai cikin ya zube anan za'a gano munafikin da ya...... "


Kafin Jiddah ta k'arasa maganar ta Dr Faridah ta kwad'a mata mari tare da cewa
"Daman Jiddah baki da hankali yanzu sai ki bi bayan wata bare bayan kina ganin d'an uwanki take cuta tana zaluntar shi amman kin ban kunya wallahi"


Basu ankara ba sai ganin Sabeer suka yi da sauri ya tashi a sukunye ya nufi bedroom d'in Suhaima ya fara hargitsa d'akin don yasan indai gaskiyar magana ne Suhaima na zubar mishi da ciki zai samu wani k'arin haske akai.


Birkita d'akin yake komai sai da ya hargitsa cikin wardrobe duk ya zubo mata kayanta k'asa har katifa ya d'aga cikin toilet drawer d'in gefen gado duk ya duba bai ga komai ba a lokacin zuciyar shi ta fara aminta da maganar da Jiddah tayi sharri akayiwa Suhaima daman shi bai gama yarda ba.


Har zai fito daga d'akin idanun shi suka sauka kan drower d'in jikin mirror da sauri ya k'arasa wajen yana bud'e su har ya janyo ta k'asan, lokaci d'aya jikin shi yayi wani irin sanyi ga66an jikin shi suka saki wata irin tsanar Suhaima ta fara mamaye cikin zuciyar shi ganin abin da idanun shi suka gane mishi.


Kwaso kwalin maganin yayi gaba d'aya ya fito daga d'akin a fusace kamar wani zaki yana zuwa ya watsawa Suhaima maganin akanta cikin kzakkausar murya yace
"Suhaima! Wannan mene? "


Suhaima wadda sauran k'iris fitsari ya zubo ta ta zubawa maganin ido duk da batayi karatun likita ba jikinta ya bata wannan maganin shine wanda ake magana akan shi.


"Alhamdullilah da Allah ya toni asirin munafuka"
Cewar Mumy kenan tana jijjiga kafa hatta Daddy mamaki ne ya hanashi magana.


"Yaya wallahi Suhaima bazata aikata haka ba "
Cewar Jiddah tana faman kuka kamar zata shid'e, cikin 6acin rai yace
"Jiddah close your mouth or I'll slap U wallahi "


Juyowa yayi wajen Suhaima tare da cewa
"Nagode Suhaima akan duk abin da kika yi min wannan shine sakayyar da zaki min A SANADIN SON KI mene banyi

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login