Showing 9001 words to 12000 words out of 122360 words

Chapter 4 - A sanadin Son ki Hausa Novels Document complete by Aisha A Muhammad Sanaz.txt

da Jiddah suka kwashe kayan da ta kawo wa Suhaima suka wuce cikin d'akin Suhaima, kan bed suka zube suna hira don sun jima basu had'u ba.


Yinin ranar hira sosai suke har Jiddah na bawa Suhaima labarin an kawo kud'in ta an sanya rana nan da two month's biki su Abban ta suka sanya, da yake kuma Jiddah har ta shiga University tana level 2, mass com take karanta bata da ra'ayin sai ta gama schl zata yi aure, ta fison tana cikin karatun tayi idan yaso zata k'arasa a gidan ta da yake iyayen ta irin basu da shiga hak'ik'in yaran su a kan abin da suke so suna yi musu, sai dai idan abu bai yi musu wannan ne kuma akwai tashin hankali.


Suhaima ta taya murna sosai tare da yi mata fatan alkhairi tare da alk'awarin zuwa gidan su biki, d'an hararar ta tayi tare da cewa
"Ba daga baki ba fad'ar Allah yasa ki zo "
Dariya ce ta tahowa Suhaima da sauri ta sanya hannu ta rufe bakin tana cewa
"Ni na isa ace bikin besty guda ban je ba, da ban yiwa kaina adalci ba "
"Kada ki zo d'in yarinya kiga yanda ake rashin mutunci "
"Ah Ah ma basai kinyi rashin m ba zan zo ba "


Daga nan kuma ta fara kok'arin tafiya gida ganin yamma tayi, Yaya Aliyu da Aunty Aliyah sun taya Jiddah murna sosai na auren da zata yi sannan sun yi mata alk'awarin zuwa idan lokacin yayi, sannan tayi musu sallama ta tafi, har wajen mota Suhaima ta rako ta suka sake yin sallama sannan ta shiga motar ta rufe driver yaja motar suka tafi suna d'aga wa junan su hannu, sai da motar ta k'ule Suhaima ta daina hango ta tukunna ta sauke hannun ta tare da sauke numfashi ta wuce cikin gidan su zuciyar ta fal farinciki yau Jiddah tazo don rabon da tazo anyi wajen one month's.


*** *** ****


Wata hamshak'iyar mata na hango tana rik'e handle d'in kofar wani d'aki tana bud'e wa tare da shiga ciki, kallo d'aya zaka yiwa matar kasan ta jik'u da naira, d'akin duhu dulum da ta shiga ciki.


Da yake ta lak'anci wajen makunnar bulbs na bedroom d'in sai ta k'arasa ta kunna nan take haske ya gauraye cikin d'akin, wow nice room na furta lokacin da naga had'uwar d'akin, komai na d'akin blue and white ne hatta fentin bangon d'akin gashi k'ato ne room d'in sosai.


Kai tsaye matar wajen tafkeken Italian bed d'in ta nufa, inda one and only lovely son nata yake sleeping hankalin shi kwance, ya lullu6e hatta kanshi da lallausan blanket wanda ya kasance shima blue ne and kwalliyar flower's white ajikin shi.


Zama tayi gefen bed d'in tare da sanya hannun ta tana bud'e blanket d'in, har tayi nasarar bud'e face d'in, tubarkallah masha Allah nace a time d'in da na hango beautiful face d'in shi, bacci yake amman fuskar shi a sake tamkar wanda yake murmishi.


A hankali ta sanya hannun ta tana bubbuga shi a nutse tana cewa
"Hey son wake up "
Sai da ta fad'i hakan sau biyu ana ukun ne ya fara bud'e lumshashshun eye's nashi wanda dogayen eyelashes ya rufe su, ya kallo Mummyn tashi cikin muryar shagwa6a yace
"Why Mummy da zaki tashe ni a bacci, shiyasa sam ban so na dawo nigeria ba coz yanzu za'a fara sawa mutum headache "
Ya k'arasa fad'i yana yatsine fuska, da kan ganshi kasan d'an shagwa6a ne na ajin k'arshe ma.


Murmishi Mummy ta saki tare da cewa
"Haba my son kasan yau ne na had'a partyn murnar dawowar ka gida lafia da kammala karatun ka koh"


D'an yatsina fuska yayi tare da sake 6ata fuska yace
"No need Mummy kinsan ban son hayaniya right? "
Hannun ta ne saman gashin kanshi tana shafawa tace
"Nasan da haka son but kamar kai ka dawo daga wata k'asar ka kammala karatu cikin sa'a kace bazan had'a party ba I'm sorry to say son sai nayi "


Bai kulata ba ya yaye blanket d'in jikin shi ya zuro k'afafun shi a k'asa tare da tashi tsaye daga shi sai short niker white colour irin skin tight d'in nan ya wuce toilet a fusace, don sam bai jin dad'in dage wa da Mummy tayi ba aka wannan party da ta had'a mishi.
Da murmishi Mummy ta bishi da kallo cikin so da kaunar shi tace
"Son d'an rigima kenan, bazan biye maka balle ka hanani nuna wa duniya cewar kai d'an gatan family d'in Alhaji D'an fillo ba ne gaba da baya "
Tana gama fad'in haka ta bar bedroom d'in don ba k'aramin aikin son ba ne yasa ta a gaba ba sai ta shirya shi saboda tsabar gata da sangarta irin ta d'an nata SABEER...




AISHAT A MUH'D ✍🏻
💝 A SANADIN SON KI 💖


Written by
Aishat A Muh'd
♻EXCLUSIVE WRITER'S FORUM


DEDICATED TO MY SADEEY SANAZ




PAGE 11-12








Yana fito wa daga bathroom yaga Mummy bata cikin bedroom d'in, ta6e fuska yayi kamar zai saki kuka ya dafe gishin shi yana cewa
"Oh my God shine Mummy kika gudu koh? "
Yana gama fad'in ya k'arasa wajen tafkekiyar wardrobe d'in shi ya bud'e ta a kasalance, don Sabeer ba k'aramin sangartacce ba ne komai idan zaiyi a sangarce yake yi.


Dakyar ya iya d'auko wani white 3quater da T-shirt yellow mara hannu ya sanya su, tukunna ya k'arasa wajen dressing mirror ya gyara gashin kanshi sannan ya sanya perfumes different colour designer, masu matuk'ar k'amshi yana gama wa ya sanya hannun shi ya d'auko d'aya daga cikin favorite phone nashi.




Sannan ya nufi hanyar fita daga d'akin nashi, idan mutum ya kalle shi sai ya zaci irin jarumin namijin nan saboda k'irar k'arfi da yake da ita, amman idan mutum yasan irin yanda yake matsoraci gashi sangartaacce ne na ajin k'arshe, don iyayen shi ba k'aramin sangartashi suka yi ba gashi Shagwa66e6e ne.


Cikin takun tafiyar shi ta kalar Shagwa6a ya k'arasa sauka zuwa k'asan stairs, kai tsaye inda parents d'in shi suke ya nufa a dinning table inda suke breakfast, wajen dinning table d'in kanshi abin kallo ne ya had'u sosai gashi babba wanda a k'alla zai d'auki mutum goma.


Suna hango shi suka fad'ad'a fara'ar su kallon shi suke cikin so da k'auna tamkar yau suka fara ganin shi, a tsakanin Mummy da Daddy baza ka iya tantance wanda wani yafi k'aunar tilon d'an su ba, tashi Daddy tsaye yayi tare da yin hugging d'in shi har da wani bubbuga bayan shi kad'an yana cewa
"My lvly son good morning"
Cikin shagwa66iyar murya Sabeer yace
"Morning Dad "
Bayan sun gama gaisawa Daddy yaja mishi kujera ya zauna, sannan yace
"Son me zaka ci Mummyn ka tayi serving naka "
"Nothing"
D'an zaro ido yayi kad'an yana kallon Sabeer kafin yace
"What! Son kasan bazan barka da yunwa ba don haka oya tell me "
Duk wannan maganar da suke Sabeer ko kallon inda Mummy take bai yi ba sai wani 6ata fuska yake tamkar irin wanda ake mintsina sannan aka hana mutum kuka haka Sabeer yake.


Ganin hankalin Daddy ya tashi ne yasa shi cewa
"Okay Daddy na don't worry, a bani one cup of coffee ma"
"Yawwa Son ko kai fa "
Sai lokacin hankin Daddyh ya kwanta but yasan an 6atawa Son nashi rai cox haka yake fushi da abinci idan an 6ata mishi rai.


Cikin murmishi Mummy tace
"I'm so sorry my son nasan dalilin fushin ka"
Ta k'arasa fad'a tana rik'o hannun shi cikin sigar rarrashi take mishi magana, kallon ta Daddy yayi tare da cewa
"Oh I know ke kika 6ata mishi rai, tun da naga yak'i kallon inda kike "


"Bafa wani abun babba ne ba fah Daddy"
Cewar Mummy.
"Fad'a min abin da ya had'a ku "
Murmishin dai har yanzu Mummy take tana had'a wa Sabeer coffee sai da ta gama had'a shi tukunna ta bawa Sabeer cup d'in a hannun shi, sannan ta kalli Daddy da har yanzu kallon ta yake yana jiran ta fad'a mishi abin da ya had'a ta lvly Son d'in shi.


Cikin yanayin k'sisina da karya murya tana wani fari da eye's nata tace
"Daddy ka tuna lokacin da na sanar da kai idan Son ya gama karatun shi zan had'a mishi party na gayyato k'awaye na da abokanan arzik'i mu taya shi murnar kammala karatun shi lafiya, akan na sanar da shi fah ya fad'a min baya so shine ni kuma nace yayi hak'uri zan yi, shine fah yake fushi da Mummyn shi "


D'an murmishi Daddy yayi don yasan halin Mummy wajen son nuna wa duniya d'an nata d'an gata ne duk abin da Sabeer yake so a wajen ta zata siya mishi indai akwai shi a duniyar nan, bata wasa da al'amarin Sabeer indai kuwa abin yayi mata tana rawar jiki zata yi mishi.


Kallon Sabeer yayi yaga ko kallon inda suk bai yi ba hankalin shi yana kan wayar time to time yana kur6ar coffee nashi tamkar baisan abin da suke magana akai ba.


Daddy ya rasa yanda zai yi baya son 6atawa d'an nashi rai haka kuma baya son ran Mummy ya 6aci, gashi ta zuba mishi eye's d'in ta da suke matuk'ar rud'a shi sai wani salo na daban take mishi.


Da ido yayi wa Mummy alamar bari ya gwada rarraso shi, hannun Sabeer ya rik'o tare da cewa
"My son kayi hak'uri da abin da Mummyn ka zata yi, kasan saboda son da take maka shi yasa take yin komai don taga ta faranta maka rai, gashi ta gama kashe kud'i masu yawa domin tayi maka abun da zai sanya ka farinciki, please Son kayi hak'uri ka bata wannan damar kada kace a'a son "


Shiru suka yi dukannin su suna jiran abin da d'an lele zai ce, cikin zuciyar Mummy tana addu'ar Allah ya sanya Sabeer ya amince, sai da ya k'arasa shanye coffee d'in shi tukunna ya mik'e tsaye har ya juya bayan shi zai tafi.


Gaba d'aya Mummy ta gama hak'ura da zai amince da party, sai kuma suka ji amon sautin muryar shi yana cewa
"Alright naji Mummy but 30 minutes only zanyi a wurin "


Yana gama fad'in haka ya juya ya tafi, cikin Farinciki Mummy tace
"Yes! Daddy i can't believe ya amince min"
Murmishi Daddy tare da cewa
"Daman kece baki bishi ta rarrashi ba kinsan d'an naki sometimes sai da rarrashi "
Mik'e wa tsaye suka yi Mummy saboda jin dad'i tayi hugging d'in Daddy tare da bashi peck a cheek d'in shi.
Murmishi suka sakarwa junan su a lokaci d'aya, tukunna Daddy yace
"Hey Mrs Hussein d'an fillo thanks for ur fantastic kiss"
Fari da eye's nata Mummy tayi tare da kama hannun shi suka nufi upstairs don ta shirya shi zuwa fita office.




WANE NE SABEER HUSSEIN D'AN FILLO?








SORRY FANS BAN DA CHARGE NE, MU HAD'U A NEXT PAGE DON SANIN WANE SABEER.






AISHAT A MUH'D ✍🏻
💝 A SANADIN SON KI 💝




Written by
Aishat A Muh'd


♻EXCLUSIVE WRITERS FORUM


Dedicated to my Sadeey saNaz




PAGE 13-14








Family d'in Alhj d'an fillo asalin su irin fulanin nan ne wanda suke da arzik'i sosai na dukiya da ababan kiwo, Alhj Ahmad d'an fillo shine d'a d'aya a wajen mahaifin shi da mahaifiyar shi sai 'yan uba k'annen shi su uku dukka mata shi d'aya ne namiji mazauna garin adamawa state, shi yasa mahaifin shi ya tsaya akan bashi ilimin boko, duk da su ma matan ya sanya su a makarantar iyakar su secondary ya aurar dasu.


Bayan Ahmad ya kammala karatun shi na fannin Lafiya ya samu aiki sai iyayen shi suka aura mishi wata Hauwaa wadda ta kasance 'yar uwar shi ce, watannin su uku da aure iyayen shi suka yi accident a hanyar su ta zuwa airport don zuwa k'asa mai tsarki domin gabatar da hajji, dukannin su suka rasu, mutuwar ba k'aramin girgiza Ahmad da matar shi Hauwaa tare da sauran 'yan uwan su tayi ba, sosai mutuwar ta shige su amman haka suka rungume hak'uri don sunsan haka Allah ya tsara zata faru.




Bayan shekara d'aya da rasuwar iyayen shi matar shi Hauwaa ta haihu 'yan biyu suka samu, sunyi matuk'ar murna da farinciki, inda suka bar musu sunan su na Hassan da Hussein, sun cigaba da rainon yaran su cikin kulawa, watan su uku da haihuwa Hassan ya rasu sakamakon zazza6i mai zafi da ciwon ciki da yayi wanda kwanaki biyu yayi yana jinya a hospital ya rasu, sosai mutuwar Hassan ta bige su don sai zafin mutuwar iyayen shi ta dawo mishi sabuwa a lokacin, haka suka dangana suna masu bawa Hussein kulawa.




Hussein yana da shekara hud'u Dr Ahmad d'an fillo ya samu transfer zuwa Malam Aminu kano teaching hospital, ba 6ata lokaci ya tattara komai nasu suka dawo garin Kano, sai da ya fara zama a gidajen hospital d'in kafin ya gina nashi gidan, don zaman garin Kano yayi mishi dad'i.




Bayan an gama mishi ginin suka dawo cikin sabon gidan su a lokacin Hauwaa ta haifi d'an ta na biyu Omar, bayan shekara biyu ta sake haihuwar Usman, daga Usman sai Aminu sannan autar su Fadilah, sun cigaba da rainon yaran su cikin kulawa da k'auna makarantu masu kyau da tsada Dr Ahmad d'an fillo ya sanya yaran shi, sai dai sun fi bawa boko mahimmanci fiye da ilimin Islam, a lokacin Dr Ahmad d'an fillo ya tsunduma harkar business sosai wanda nan da nan kud'i sosai suka fara samuwa ba kad'an ba.




Haka lokaci ya cigaba da tafiya yaran shi dukka sun girma kowannen su ya gama karatun shi yana aiki, Hussein business d'in da mahaifin shi yake ya tsunduma a ciki, Omar kuma yana aikin Bank, Usman kuma a wani babban company na abokin Dr Ahmad d'an fillo yake aiki a matsayin GM na company d'in, sai Aminu da yake lecturing a BUK, sai k'aramar su Fadilah da take karatun degree a wannan lokacin, wanda gab take da ta kammala har an sanya lokacin auren ta da wanda zata aura, iyayen shi masu kud'i ne shima haka yana da kud'i abokin yayan ta Omar ne, lokacin da ya nuna yana son ta sosai iyayen ta suka yi farinciki da hakan, saboda suna da kud'i don Dr Ahmad d'an fillo da 'ya'yan shi basa harka da talakan mutum sai ta kama, don akwai su da kyamar talaka harkokin shi sai da masu kud'i 'yan uwan shi.




Shiyasa ba 6ata lokaci aka sanya lokacin auren Fadilah da Mustapha, bayan ta kammala degree d'in ta aka yi biki sosai sun kashe kud'i a bikin, bayan auren Fadilah suma Yayannin ta kowanne ya fito da matar aure duk yaran masu kud'i ne daman gashi akwai su da kyau irin na fulani ga kud'i kuma da wayewa, sai da ban da Babban Yaya Hussein don shi harkar neman kud'in shi ya sanya a gaba bai fiye, kuma iyayen nashi sam basu tak'ura mishi ba da yayi aure, kafin bikin ne Dr Ahmad d'an fillo ya gina k'aton gida mai d'auke da part's biyar kuma kowanne part babba ne sosai kuma upstairs ne, an kashe kud'i sosai a wannan gidan kafin bikin suka koma can da zama abin su.






Sai da Omar, Usman da Aminu suka haifi yara kowanne biyu biyu kuma kowanne yaro da tazarar shekara wajen uku a tsakani,tukunna Hussein ya kawo matar da zai aura Dr Faridah cikakkiyar likitar mata ce wato gynecology a k'asar India tayi karatun ta, iyayen ta masu kud'i ne sosai ne kuma abokin Dr Alhj Ahmad d'an fillo ne sosai da sosai, lokacin da Dr Ahmad d'an fillo yaji d'an shi Hussein Dr Faridah zai aura ba k'aramin farinciki suka yi ba shi da Hajja Hauwaa, nan aka sanya lokacin biki two weeks kawai, an kashe kud'i bana wasa ba a wannan auren, don su kansu matan Omar, Usman da Aminu sun san an auro matar so kuma ta gaban goshin surukan nasu don yanda suka ga ana ji da ita tun kafin ta shigo gidan.


Dr Faridah Bashir kyakkyawa ce kuma wayayyiya ce sai dai akwai ta da wulak'anci ba kad'an ba, gata kuma ta tsani wani talaka ya ra6e ta, kanta kawai ta sani, ga nuna tak'ama da tsantsar ak'idar Boko, kuma mahaifin ta hospital babba ya bud'e mata nata na kanta don su biyu kad'ai Allah ya bashi daga Faridah sai k'anwar ta Zahra, ga zata auri mai kud'i don Hussein duk yafi 'yan uwan shi kud'i, wad'annan halayen nata su suka k'ara mata matsayi cikin zuciyar surukin ta Dr Ahmad d'an fillo fiye da sauran surukan nashi, yana ji da ita matuk'ar gaske.


Bayan auren Hussein da Dr Faridah sai da suka yi wajen shekara uku ko 6atan wata bata ta6ayi ba, sosai hankalin su ya tashi nan aka shiga ziyartar asibitocin k'asashen waje domin bincikar lafiyar su, amman k'alau suke lokaci ne bai yi don komai kud'in ka sai lokacin da Allah ya nufa zaka samu abu zaka same shi, balle haihuwa da lafiya wanda kud'i baya ta6a siyan su sai lokacin da Allah yaso zai baka, gajiya sukayi da zuwa hospitals suka zubawa sarautar Allah ido tare da tsananta addu'a sosai a wajen Ubangiji, Dr Ahmad d'an fillo da Hajjah Hauwaa suma duk'ufa da addu'a suka yi sosai don suna k'aunar son ganin jikan su na wurin Hussein da Dr Faridah.






Sai da suka kwashe shekara hud'u da aure kafin Allah ya bawa Faridah ciki, murna da farinciki bazai fad'u ba irin wanda suka yi, nan suka dunga rainon cikin cikin so da k'auna.


Bayan wata tara Faridah ta haihu an samu baby boy kyakkyawan yaro dashi, anyi murna da farinciki sosai, ranar suna ansha taro an kashe kud'i duk wanda yaje sunan yasan an haifi d'an lele kuma d'an gata, anyi suna Lafiya an tashi Lafiya inda yaro yaci sunan shi Muhammad Sabeer wanda Dr Ahmad d'an fillo ya rad'a mishi sunan da kanshi, inda

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login