Showing 63001 words to 66000 words out of 122360 words

Chapter 22 - A sanadin Son ki Hausa Novels Document complete by Aisha A Muhammad Sanaz.txt


"Auuu! Sunan da muka koma kenan? "
"Kun ma fi haka "
Girgiza Suhaima tayi tana murmishi ta zauna tana shan kunun ta, nan Jiddah ta bud'e k'atuwan bag d'in da tazo da ita ta fara fito da kayan ciki.


Duk abubuwan kusan irin su dilka, kurkum da sauran nau'ikan kayan gyaran fata har dasu sabulu na wanka da cream da akayi mishi had'e had'e na abubuwan da suke sanya fata laushi da santsi da turaren da zata nayin amfani dashi idan zata yi wanka, sai kayan gyaran ciki masu kyau da nagarta sosai kayan suke da yawa kuma da ganin su kaya ne masu kyau da inganci amman fah za'a kashe kud'i ba karami ba.


Daga Suhaima har Aunty Aliya sakin baki suka yi suna kallon kayan nan Jiddah ta fara yi mata bayanin kowanne yanda zata yi amfani dashi kafin daga k'arshe tace


"Abin da ya sanya naje wajen mai mana gyaran jiki na auren mu nace ta had'a miki saboda kun yi nisa, shine nace ta bani wanda zaki amfani dashi kafin sauran sati d'aya biki tazo ta yi miki da kanki amman don Allah Suhaima ki d'aure kiyi amfani dasu suna da kyau wallahi don nagani akaina bama su cutar wa ba ne "


Jiyowa tayi ta kalli Aunty Aliya sannan tace
"Aunty don Allah ki sanya ido tana yi kullum don so nake Yah Sabeer ya rikice mana "
Ta k'arasa fad'i da dariya, Suhaima dai da Aunty Aliya sai addu'a suke yiwa Jiddah don ta hanasu godiya, addu'a sosai tasha ta musamman ta rabuwa da cikin jikinta lafiya.


Kayan suka d'auka zuwa d'akin Suhaima bayan sun ajiye Suhaima rungume Jiddah tayi kawai sai ga hawaye yana fita a idanun ta karamcin Jiddah na daban ba k'aramar masoyiyar ta bace batasan da me zata saka mata shi ba.


"Haba tawan mene kuma na hawaye share hawayen ki, kin fi k'arfin komai a wajena tun lokacin da Allah ya nufa na ganki naji kin shiga raina, yanzu bari na fara gwada miki yanda zaki yi ki gani "


Zama Suhaima tayi nan Jiddah ta fara had'a dilka da sauran abubuwa kayan had'in bayan ta gama ne sai ta fara mutstsuke jikin Suhaima bayan ta gama ne suka jira zuwa 30 minute's kafin ta murje shi sai kuma ta shafa mata had'in kurkum shima sai da ya d'auki 30 minute's d'in sannan tayi wanka da ruwa wanda aka sanya turare acikin shi, tun daga wajen wankan Suhaima ta tabbatar ta fara canjawar fatar jikin ta yanda take zuba santsi da k'amshi ga wani irin laushi da skin nata ya dad'a yi duk da kuwa fatar ta mai laushi ce amman yanzu ta k'ara laushi.


Tana fitowa ne kuma Jiddah ta gama had'a garwashi tana jiranta tana zuwa ta zuba turaren jiki acikin wutar nan Suhaima ta shiga tana turare jikinta yayin da Jiddah ta fito ta barta a d'akin, sai da ta d'auki wajen 10 minutes sannan ta gama turaren kafinx ta zauna ta shafa cream d'in nan bayan ta gama ne ta zura wata yellow d'in gown har k'asa sai dai hannun vest ne da ita, wani irin mugun kyau na daban Suhaima ta k'ara yi ga gashin ta mai kyau na asalin fulani mai laushi da santsi ya zubo mata a kafad'unta tana cikin tajewa Jiddah ta shigo.


"Wow! Suhaima kin ganki kuwa yanda kika koma tabbb gaskiya Yayana zai more "


Ta k'arasa fad'i tana d'auko wayanta pic's ta fara d'aukan ta, cikin dariya Suhaima tace
"Don Allah Jiddah ki daina d'aukan pic's nawa please kalli fah ki ga yanda rigar take"


"Ina ruwa mijin ki zan nuna wa ya bani kyauta"
Ta fad'i hakan tana daukan Suhaima lokacin da take dariya, ita kanta Jiddah pic d'in yayi matuk'ar birgeta ba kad'an ba.


D'an waro ido waje tayi kafin tace
"Haba Jiddah kada ki tura mishi please "
Ta fad'i tana langa6e kai cike da shagwa6a, dariya Jiddah tayi kan tace
"Toh naji dake da mijin ki bansan wanda yafi wani shagwa6a ba gidan ku da kallo kuwa duk an tara shagwa6a66u"


"Yanzu dai tafiya zanyi don my dear yana hanya shi da driven da ya kawo ni, yace ya gaji da yi mishi mitar da nake yak'i zuwa su gaisa da Bestyna shine yau yace zai zo "


Murmishi Suhaima tayi kan tace
"Allah ya kawo su lafiya"


"Amin "
Fita Jiddah tayi bata dad'e ba sai gata da Aunty Aliya wadda ta saki baki tana kallon yanda Suhaima ta koma tamkar ba ita ba.


Hannu tasa tana shafa hannun Suhaima tace
"Wannan da fita kika yi da ita Jiddah da nace wankan inji kika yi mata "
Dariya suka yi dukkanin su jin abin da Aunty Aliya ta fad'i.


"Aunty kema kiyi don Allah "
Cewar Jiddah, rik'e baki tayi tana cewa
"A haba wannan ai na irin kune "


"Kaiii Aunty aikuwa ya kamata kiyi "
Cewar Suhaima.


"Suhaima ki had'a mata tayi itama kafin Yah Aliyu ya dawo yaga yanda zata canja idan na dawo zan kar6i tukwicin kyauta ta "


Suna nan zaune suna hira har mijin Jiddah yazo, shigowa har gidan yayi suka gaisa da Aunty Aliya da Suhaima bayan an ta6a hira ne suka yi musu sallama suka tafi har k'ofar gida Suhaima ta rako su sannan ta dawo gida bayan sun tafi.




Bayan Suhaima ta dawo gida ne ta had'a wa Aunty Aliya itama tayi kamar yanda Jiddah tayi mata, sosai tayi kyau ba laifi bayan angama ne Suhaima tayi wa Aunty Aliya simple make-up tayi kyau kamar ba ita ba sai da Suhaima ta d'auke ta a pic's.


Suna zaune tsakar gida suna hira sai ga Yah Aliyu ya dawo nan sauran sallamar mak'alewa tayi a fatar bakin shi ganin yanda matar shi ta koma kamar ba ita ba, kallon ta kawai yake yi don ya mance da wata Suhaima dake zuba mishi sannu da zuwa, duk kunya ta d'an kama Aliyah ganin kallon da yake mata.


Yayin da Suhaima ta tattara ta arce d'akin ta don kada taga abin da yafi k'arfin idon ta, dariya k'asa k'asa take don kuwa Yah Aliyu ya bata dariya, phone nata ta d'auko data ta kunna sai gashi Jiddah ta turo mata pic's d'in da ta d'auke ta d'azu, zubawa pics d'in ido tayi ita kanta tasan tayi kyau.






*_11:30pm_*




Sabeer ne kwance kan bed yana zuba murmishi gama yin wayar shi kenan da Suhaima, duba wajen pic's nashi yayi sam bashi da pic's d'in Babyn shi yana shirin kiranta ne yaji alamar shigowar sak'o a WhatsApp d'in shi don haka ya duba sai yaga Jiddah ce ta turo mishi da wasu pic's guda 5 daga k'asa ta sanya "Yah Sabeer kada ka nunawa Besty na turo maka pic's d'in nan don inason kaga yanda Babyn ka ta zama kuma ka bani tukwici idan ba haka ba na daina turo maka " ta k'arasa da sanya d'an aljanin murgud'a baki, sannan ta kuma cewa
"Asha kallo lafiya angon Besty " ta sanya aljanin dariya da gwalo.


Tun kafin ya bud'e yake murmishin abin da Jiddah ta rubuta, sakin baki, hanci da ido Sabeer yayi yana ganin pic's d'in sai da ya sake murza eye's nashi kafin ya dad'a zubawa pics d'in ido, wannan anya Baby nace?, ya fad'i haka cikin zuciyar shi kafin maganar ta samu matsugunun tunani a brain nashi tuni ya gama hashasho Babyn shi ce.


"Wow! Gaskiya Baby nah kin had'u ashe zan more woo"
Ya fad'i hakan yana cigaba da kallon ta tuni ya tafi mafarkin ido biyu, baisan adadin lokacin da ya dauka yana kallon pics d'in ba, sai da yaji Jiddah ta turo mishi da text d'in taji shiru bata ga tukwicin ta ba.


Cikin rawar jiki ya fara typing da cewa
"Me kike so k'anwata ta kaina? "
"Yah Sabeer komai ma "
"Car or Money wanne kike so fad'i?"


"Yah Sabeer Mota nake sooo"
"Angama sister gobe za'a kawo miki key "


Wani ihun murna Jiddah ta saki har phone nata na fad'uwa k'asa don tasan kyautar Sabeer baya k'arama, nan tayi mishi godiya tare da addu'ar Allah ya bashi Suhaima, na takaice muku Sabeer ranar har dasu mafarkin Suhaima suna tare don da asuba sai da Sabeer yayi wanka sannan ya iya yin sallah..... lol.






*_Washe gari_*




Sabeer ne ya fito daga bedroom d'in shi yana taka staircase anutse ya kusan k'arasa wa palour ne ya hango Mummy da Daddy zaune ga kayan bag's na akwatinan lefe nan barbaje a palourn tun daga kan akwatunan mutum zaisan basu da wani tsada ko kalar kyau basu dashi gashi guda 6 ne gaba d'aya kayan ciki kuwa ko arzik'in kyau basu dashi.


K'arasa wa yayi cikin palourn yana kallon kayan a wulak'anci yace
"Daddy Mumy kayan wane ne wannan?"


"Nima jira nake ta sanar dashi bansan na wane ne ba nafi kyautata zaton ko gate man ne zaiyi aure ta bashi kyautar su "


Cewar Daddy kenan, duk sun zubawa Mumy ido suna sauraren abin da zata ce dasu.........






*_Ya kuka ji wannan page d'in Fans dafatan ya k'ayatar ku, inason ganin comment's, yau nayi abin kirki koh?_*😜






Aishat A Muh'd ✍🏻
*A SANADIN SON KI*






Written by
Aishat A Muh'd


Dedicated to my Sadeey SaNaz










*PAGE 75-76*










Ganin Mumy tayi shiru tak'i magana yasa Sabeer yin magana cikin k'aguwa yace
"Mumy ke fah muke jira ki fad'a mana ki zo ki bani abinci yunwa nake ji "


Hankalin Mumy kwance ta bud'e baki tace
"Lefen da Daddy yace na had'a ne sune na gama had'a wa "


Cikin son sanin na waye Sabeer yace
"Na wane kodai gaskiyar Daddy ne gateman ne zai yi aure?"


Yayin da Daddy kuma ya saki baki yana kallon Mumy zuwa yanzu ya tabbatar lefen Sabeer ne da yace ta had'a shine ta had'a mishi wulak'antaccen kayan nan da ko wani talakan mai zuciyar nema idan ya sanya kanshi sai ya had'a wanda yafi shi had'uwa, ranshi ne ya soma 6aci yama kasa magana sai kallon mamaki da yake bin ta dashi,yana jiran yaji me Sabeer zaice kafin shima ya d'ora hukuncin da zaiyi don sosai wannan karon Mumy ta 6ata mishi rai, yana cikin wannan tunanin ne yaji muryar ta tana cewa Sabeer.
"Lefen auren ka ne da wannan talakar yarinyar 'yar k'auye don nasan sun fi dacewa da ita kuma zata kar6a su cikin murna don basu saba ganin irin su ba"


Wata 'yar dariyar ban yarda ba Sabeer yayi kan yace
" are you serious Mumy maganar ki nasan da wasa ne ai? "


"Sabeer kadaina sanya wasa cikin maganar nan da gaske nake duk abin da nace "


Wata dariyar Sabeer yayi wadda tafi kuka ciwo yace
"Yayi kyau Mumy "


Ya fad'i hakan yana barin parlourn cikin 6acin rai da taiaicin abin da Mumy tayi na niyyar wulak'anta shi yake hawa staircase d'in da sassarfa, bedroom nashi ya nufa yana shiga ciki ya bud'e tafkeken wardrobe nashi ya fara watso kayan ciki yana barbaza su a ko'ina, shi Mumy take neman wulak'antawa saboda kawai yana son d'iyar talakawa wadda ta rayu a k'auye.


"Why Mumy why shi talakan ba mutum bane, ba Allah ne yayi shi ba yaso ganin shi haka a rayuwa ba, Mumy kada k'ureni muzo muna yin abin da kowa zai yi nadama "


Wani 'yar k'arar takaici ya saki yana sanya hannun shi cikin sumar kanshi wadda tasha gyara yana hargitsawa, can kuma kamar wanda aka mintsina ya mik'e zumbur ya fara cire kayan jikin shi ya canja da wasu jeans black da T-shirt maroon colour mai k'aramin hannu ya d'auko phone da car key's ya fito daga d'akin.




Yana saukowa daga upstairs yaji muryar Daddy yana yiwa Mumy fad'a sosai akan abin da ta aikata, suna ganin sai kuma suka dawo da hankalin su nan, cikin damuwa Mumy ta fara cewa


"Son ina zuwa baka ce min yunwa kake ji ba, ga breakfast fah na had'a maka favourite foods naka? "
"Bana buk'atar su "


Sabeer ya fadi hakan ba tare da ya kalli inda take ba ya k'arasa wajen Daddy yana cewa
"Daddy zan fita "
Rik'o hannun shi Daddy yayi tare da cewa
"Ina zaka Son? "
"Daddy zan je na nemi mai had'a min lefe wanda nasan baza su so na kunyata a rayuwata ba "


"Da kyau Son but da ka nemi Jiddah da Yusrah (Yayar Jiddah wadda take bi itama dai bata da tsaurarawa sosai akan abu wanda ya danganci talaka tana da aure har da yara 2), nasan zasu fitar da kai kunya baza su so kansu ba da yawa, kamar wasu mutanen da basu d'auki talaka a mutum mai mahimmanci ba, wanda kuma agaba zai iyayi mishi wani abin alkhairi mutum ya dawo yana jin kunyar aikata abin da yayi"


Mumy ta cika tayi fam sai huci take don tasan da ita yake don tuni ta tsargu.


Sai lokacin hankalin Sabeer ya d'an kwanta don dama shi baisan wurin da zai je ba kawai ya fito da niyyar barin gidan ko yaji sanyi cikin ranshi.


"Yanzu Daddy wanne k'asa zasu je? "
"Ina tunanin su je dubai su had'a acan idan ma bai wadatar ba sai a dad'a neman wata k'asan, yanzu zan kirawo mazajen su na rok'i wannan alfamar a wajen su, ka kwantar da hankalin ka Son "


Rungume shi Sabeer yayi cikin jin dad'i yace
"Nagode Daddy nah hak'ik'a kai uba ne na gari wanda yake faranta ran d'an shi koda yaushe Allah ya barmin kai "


"Amin Son nima ina alfahari da kai "


Yana gama fad'in haka yaja hannun Sabeer suka fita daga side d'in, suka bar Mumy da baki a sake tana mai bin su da kallo cikin mamakin gasa mata maganar da suka yi sannan suka fitar mata da waje ko sallama babu gashi ba wanda yayi breakfast a cikin su, kuma saboda su ta shiga kitchen ta tsara girki shine suka watsa mata k'asa a ido, zubewa tayi kan kujera tana faman kallon kayan da ta sanya house girl d'inta ta had'a su, da yake er aikin dattijuwa ce kuma er k'auye ce sosai sai tace ta had'a mata lefe kamar yanda suke had'awa a k'auyen su, amman irin wanda mai kud'in k'auye zai iya had'awa amman sai tace mata akwatina 6 zata siya shine fah ta had'o kayan, ko lokacin da ta gansu sai da taci dariya ta more saboda abubuwan da aka zuba aciki.




D'an ta6e baki tayi kan tace
"Ni ban ga wulak'anci anan ba nasan da gudu zasu kar6a suna murna tun da basu saba ganin kayan lefe masu yawa irin wannan ba"


Ta k'arasa fad'i tana kwanciya kan kujera wata tsanar Suhaima na k'ara shiga cikin zuciyar ta,tun kafin taga yarinya take jin tsanar ta kuma tabbas sai tayi nadamar auren d'anta don bazata barta tayi rayuwa cikin jin dad'i ba, (kun ji tunanin Mumy fah sai kace itace mai tsarawa mutum rayuwar shi).






Tun da Sabeer da Daddy suka bar gidan basu dawo ba sai wurin 11 na dare suka shigo part d'in, tun after sallahr ishsha suke cikin gidan ba tare da Mumy ta sani ba don ko dinner a Muh'd part d'in Hajjah suka yi, Mumy kuwa batasan sun dawo gidan ba don haka ta k'ule iyakar k'uluwa akan abin da Sabeer da Daddy suka yi mata don ko abincin dare da kanta ta shiga kitchen ta 6ata lokaci sosai wajen shirya musu abinci, tun tana zuba idanun ganin su har ta hak'ura ta kwanta kan kujera 3 siter tana sak'a da warwara ina mijin ta da d'anta suka yi.


Tana cikin wannan tunanin ne taji shigowar su palon don haka ta mik'e tana kallon su cikin mamaki yanda suke ta zuba fara'a abin su Daddy ya rik'o kafad'ar Sabeer tamkar wani abokin shi.


Kanta ne ya k'ara d'aurewa ganin zasu shige upstairs basu kulata ba, yanda ma suka nuna ko alamun sun san da ita a palon basu yi ba, kasa jurewa tayi don haka tace


"Hala baku kula da ni ba, ina kuka zauna har wajen 11pm baku dawo gida ba? "


Tsayawa suka yi tare da juyowa suka had'a ido lokaci d'aya suka had'e fuska sannan Daddy yace


"Ina ruwan ki da inda muka je wannan ba matsalar ki bace? "


Gaban Mumy ne ya fad'i kaddai ace adalilin Suhaima mijinta da d'anta su juya mata baya, ganin har sun fara taka staircase ya sanya ta katse tunanin ta da sauri tace


"Ga abinci nan fah na girka muku "


"Mun koshi Mumy wata k'awar Daddy ta bamu abinci mai dad'i mun ci don haka ki bawa masu aiki su ci "
Cewar Sabeer kenan wanda sauran kad'an dariya ta kubce musu shi da Daddy don haka da sauri suka fad'a bedroom na Sabeer suka rufe suna kyalkyala dariya, har da rufe baki da hannun su saboda kada Mumy ta jiyo sautin dariyar tasu.


"Son ka razana Mumyn ka da yawa fah kada wani abu ya samu mata ta ina jin tsoro "


"Haba Daddy daga wannan maganar sai wani abu ya faru da ita? "
"Eh mana Sabeer kasan yanda Mumyn ka take da kishi kuwa ni bama zan jure ganin ta cikin damuwa ba bari naje na rarrashi abata "


Daddy ya k'arasa fad'a yana kokarin fita a d'akin, da sauri Sabeer ya rik'o hannun shi tare da cewa
"Nooo Daddy kyale Mumyn nan, nima kaina bana son ganin ta cikin damuwa but Mum batason ganin farincikina i swear"


"Kada kace haka Son nasan nan gaba zata so Suhaima "


"Anya kuwa Daddy, na fahimci Mum ta gama tsanar Suhaima "


"Kada kace haka Son addu'a zaka cigaba da ni "


Gid'a kai Sabeer yayi kafin kuma su zauna suna hira akan tafiyar da su Jiddah da Yusrah zasu yi nan da gobe da yamma jirgin su zai tashi zuwa dubai, kafin daga bisani Daddy ya wuce side d'in shi don dare ya d'an yi.




Mumy kuwa tun lokacin da maganar Sabeer tayi mata dirar mikiya cikin kunnen ta, ta gama firgicewa kusan suman tsaye tayi tsabar kad'uwa da jin abin da Sabeer ya fad'a mata, wato dalilin da ya sanya su yin dare a waje kenan, aikuwa ba 'yar iskar da zata

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login