Showing 24001 words to 27000 words out of 270738 words

Chapter 9 - NAMA YA DAHU ROMO DANYE COMPLETE TRUE NOVEL BY BADI'AT.doc

ba sai dai kawai bana daga cikin jerin kalar matan da yake burin rayuwar aure dasu. Ni ina da ?iba sosai, gani da cikar kumatu dan har idanuna da hancina sun shige ciki, ga mazaunai masha Allah. Shi kuma baya ra'ayin mace mai irin zubina. A cewarshi siriraya doguwar mace yake so, wacce zai iya bi da gudu ta zura ya rufa mata baya. Akan wannan dalilin ya kafe dole cikin fishi da hasala Iyaa ta janye batun aurenmu dole ta Wauki idanu ta zuba mishi, har kwsnciya jinya ssida yayi. Bayan aurena da shekara biyu ya auri Yemisi ?ar ?awar Iyaa.
"Me yasa daya kawo baki bari na zo kin nuna mun ba?" Kai na sauke ?asa ganin yanda fuskar Gwadabe ta sauya launi.
Ka yi ha?uri in karSar da nayi ya Sata maka rai. Amman ba ro?a nayi ba, har gida ya kawo mun. Gwadabe ka rage ?iyayyar da kake yi ma Burodami Debisi, dan shi ya Wauki Wawainiyar rayuwata tun daga yarintata har tasowata. A matsayin wa nake ganinshi, shima bani da wani matsayi a wajenshi daya wuce na ?anwa"
"Ki tsahirta mun haka nan Iyabo. Ai nasan wanki ne, sai dai ai wa ne irin wanda akwai aure a tsakani. Danni na kasa gane menene manufar Debisi sonki yake yi ko tausayinki" Zim naji jikina yayi, ba wannan bane karo na farko da Gwadabe yake ?umaji sabida debisi ba, kuma ba fa zargina yake yi ba ni na Wauka a matsayin yana tsare mutuncina da nashi ne baki Waya.
Gwadabe..." Hannu ya Waga ya dakatar dani. Ya soma cin abincinshi zuchiyarshi cunkushe da kishin Debisi har ya gama tsakanin ni dashi babu wanda yayi ko tari, sai ja da sauke numfashi da muke yi.
"Batun kuWin asibiti kuma shima Debisinne ya biya ko, so kike ya samu hujjar ganin kamar bana ?o?ari a kan ki ko? Bayan kinsan komai da irin tsanar da ake nuna mana. Kina fa gani ?an uwana ma bana neman taimakonsu"
Nasan idanun Gwadabe ya rufe da kishine, shi yasa nayi murmushi nace.
Ashe na fika dauriya da ha?uri tunda har na iya haWa Waki da matar da akeson a aura maka. Matar data baro gidan mijjinta sabida kai. Haba Gwadabe in hankali ya gushe hankali ake turawa ya nemo shi. Ko da Burodami ne ya biya kuWin asibitina bai kamata ace an yi fishi dashi ba, ballema Burodami kokodeen ne ya biya komai da komai." Shiru yayi mun, yasha jinin jikinshi, dan maganata tamkar na Waureshi da jijiyoyin jikinshi ne.
"Kiyi ha?uri da fishin dana nuna, kishinki ne yai mun yawa. Amman nasan har ga Allah kin fini dauriya da mayar da komai ba komai ba. Mala'ikun Allah ku shaida na sa ma rayuwar Iyabo albarka." Ajjiyar zuchiya na sauke tare da yin dariya. Shima dariyar yayi.
"To leshi da kika Winka mana shi kuma ta ina kuWin ya Sullo?"
Labarin yanda akayi na tara kuWin na bashi tare da kayan kwancen da aka bani a gidan aiki. Mi?ewa tsaye nayi na Webo mishi duk kayayyakin da na samu na suna, da duk kuWaWen da aka babbani.
Ka gansu duk albarkar haihuwa ne, kasan ?an biyu akwaisu da farin jini" Dani dashi mu kaita wauware kayayyakin muna kallo, muna hirarmu ta yaushe gamo, ina bashi labaran abubbuwan da suka faru shima yana bani labarin yanda suka kwashe da Babala kan batun sunan yara da ya saka. Da ankon leshi da muka yi, ashe Babala har kuka saida tayi, wai Gwadabe ya zama beyeraben dole.
"Kaya sun yi kyau an gwangwajeki da kaya gaskiya, babu abinda zance sai Allah ya amfana. Sunan yazo mun da sau?i wallahi ko da yake ance ko wanne yaro da arzikinshi yake tafe"
Gaskiya ne kam. Allah ya ?ara rufa mana asirinmu fid duniya wal akira"
Gwadabe yace.
"Ameen dai Maman ?an biyu. Toh yanzu me kike ganin ya dace kiyi da kuWinnan tunda kinga suna da kauri, in yaso sai ki ha?ura da zuwa gidan mutane aiki, dama ba asan raina kike zuwa ba, tunda na samu aiki ?wa??wara a hannuna kema ki mi?e ?afarki ki huta kamar yadda ko wacce mace take hutawa ko?"
Mi?ewa nayi na tattare kwanukan daya gama cin abinci na fito falo dasu. Abun mamaki Laila na gani a laSe tana sauraren hirarmu da Gwadabe. Tana ganin fitowata tayi kamar maiyar da aka kamata ?iri_?iri tana lashe kurwar surukarta, har wayarta tana faWuwa a ?asa tsabaragen kaWuwa. Tsaki nayi mai ?arfi na harareta. A cikin bahun na zuba kayan wanke_wanken na rufe da bahun na yi komawata ciki. Gwadabe ya sake dawo da maganar sana'a tsabaragen Sacin rai yasa ban iya ce mishi komai ba, na tuSe kayan jikina na zura doguwar rigar baccina, nayi hayewata gado na juya bayana ina hawaye." Cikin Sarin jiki Gwadabe ya hayo gadon yasa hannunshi a kafaWata, yayi amfani da ?arfi wajen juyo dani, hawayen da yaga yana tsiyaya ta gefen idanuna ne yasa ya kasa magana. Cikin rishin kuka nace.
Yaushene Laila zata bar Wakinnan Gwadabe ka sanar dani a darennan, wacce hanya ka sama mana ta yanda Laila zata bar gidannan? Ni da Wakina Laila bata Isa ta hanani zaman lafiya ba, nagaji Gwadabe ni gidanmu zan tafi" Na ?arashe zancen da rushewa da kuka mai gunji, ji nake yi zuchiyata na yi mun tu?u?i. Rungumeni Gwadabe yayi tsam a ?irjinshi yana rarrashina, amman fur na?i rarrasuwa. Ana cikin hakane muka jiyo wani ihu daga falo mai razanarwa, wanda yai sanadiyyar farkarmun da yara daga bacci suka saki kuka a tare. Kafin in Waukesu muka sake jiyo ihun a karo na biyu. Da sauri Gwadabe ya fita na mara mishi baya da ?an biyu a hannuna. Me zamu gani hmm Laila muka gani a kwance tana burgima tsaraicinta na fitowa, sai ihu take kwarmayawa. Har Wan diras Winta muna hangowa fari sol dashi, da sauri Gwadabe ya kawar da kanshi gefe. Kafin kace me matan gidan sun cika Wakin, Laila na ganin haka saita soma kwaSe suturarta tana fatali da'ita. Ba shiri Gwadabe ya fice a Wakin. Sai adda'a aketa faman tofeta dashi ita kuma tana ta surutai. Mamanta na ?urama idanu farare sol dasu luwai_luwai ko wacce mace nayi imani zata so dama itama mamanta haka yake. Kuma Gwadabe fa ya ga maman nata, dan sai da ta yar da rigar maman kafin ya fita har yana tuntuSe hawayena na share dan nayi imani babu wata iskar dake damun Laila tsagwaron iskanci da makircin data ri?a a matsayin makamin da zai fitar dani daga Wakina ita ta maye gurbina kenan. Ina tsaye a gefe na kasa daidai da motsawa jiri ne ke shirin zubar dani, da zanyi gigin Waga ?afata tabbas da jiri ne zai kwasheni ya zubar a ?asa tim.
"Sannu Laila Allah ya baku ha?uri. Haula kawo ruwa a bata tasha, ?ilama wani agumun aka mata danta bar gidan a haukace, tunda mu a iyakar saninmu Laila bata da iska." Cewar Yaya Halima wacce take ri?e da kafaWun Laila. Gude ta Wauki zani a kujera ta suturta mata ?irjinta dashi. Ni dai ina tsaye ina kallon bariki. Ruwa aka bata tasha, Babala tace ta kwanta ta rufe idanunta. Ta ko kwanta ta rufe idanta ruf.
"Toh Allah shi kyauta, Allah yasa ba mayu bane ma suka kama mata kurwa ba, kunsan jiya an yi taron na ayya"
Cewar Babala wacce take hanyar ficewa daga Wakin. Ina tsaye duk suka watse suka barni, sai muryoyinsu nake jiyowa a ?ofar Wakina. Rigar maman Laila na bi da idanu kawai na yi ?uta tare da shigewa Waki na kwantar da ?an biyu da suka koma baccinsu nima na kwanta ina share hawaye mai zafi. A wannan dare Gwadabe ya sha rarrashi sosai, dan birkice mishi nayi kamar lalatacciyar besfa, da ?yar ya iya shawo kaina a wannan dare.
Washe gari muka wayi garin babu walwala sam daga ni har Gwadabe, dan shi kanshi ina ankare dashi da damuwar da tafi tawa ya kwana. Bayan sun dawo daga sallar asuba ya shigo, sai yace
"Bari in Wan kwanta kaina saramun yake yi sosai, zazzaSi ne ma yake son kamani"
Sai jikina yayi sanyi, a tausashe nace dashi.
Allah ya ?ara afuwa, sannu inka karya ina da fanadol sai in baka ka haWiya" Har ya kwanta sai kuma ya tashi, ina shirin ficewa a Wakin kenan zan juyo ruwan wankan ?an biyu.
"Dawo ki zauna Iyabo mu yi magana " Babu musu ko kafiya a tsakaninmu, cikin saurin bin umarninshi na zauna ina fuuskantarshi.
"Wallahi Iyabo ko tsirara Laila zata yi a gabana ba zata taSa burgeni ba, domin bana daga cikin mazan da suka fifita kyawun mace, ko dirinta. Ni kyawun halinki, da ha?urinki ya fi ye mun komai. Ai mace ta gari farin cikin rayuwar duniya ce. Zance na gaskiya bani da wata hanya da zan bi in kori Laila a Wakinnan. Ina gudun yawan fishin da Babala take yi a kaina. Dani dake mu yi ha?uri ki taya ni mu yi mata biyayya ta zauna Win,in taga dama ta zauna har mahadi ya bayyana, zata Sata ma kanta lokaci a banza, dan ko matan duniya sun ?are Gwadabe ba mijin Laila bane. Iyabo na ?ar duma_duma mai hanci a tsakiyar kumata itace nutsuwata. Kiyi ha?uri nasan na danneki da yawa" Shiru nayi kawai ina wani tunani, har ga Allah Ni kam ina yaye Taiwo da Kahinde aurena da Gwadabe yazo ?arshe ma, nasan ina tafiya babu makawa Laila burinta zai cika na mallakar Gwadabe a matsayin miji. Iyakar son da zan yima Gwadabe kenan in zama tarihi a cikin labarinshi, ko dan ya samu rabauta, dan fishin iyaye bala'ine babba akan yara musamman fishin uwa al'amarin da girma yake"
"Baki ce komai ba Iyabo" ?agowa nayi muka haWa idanu nace.
Babu komai Gwadabe, zan tayaka biyayya ma Babala ka samu aljanna ta hannunta, Laila taci gaba da zamanta kuma in sha Allah bazan sake asarar hawayena akanta ba. Dukkan wata ?addara ko jarabtar da zata samu bawa daga Allah ne, dukkannin wani tsanani baya dauwama face sau?i ya samu." Ina gama faWar hakan na mi?e na fita cikin dakiyar zuchiya muka gaggaisa da matan gida suna tsakar gida anata hada_hadar aikin daya zamema mata jiki a rayuwa. ?akin Yaya Haula na shiga na dur?usa a gaban Babala na gaisheta, saida nayi baki biyu kafin ta amsamun a yatsine. Yaya Halima kuwa ciki ciki ta amsa, ni banji sautin muryar tata ba ma, sai dai labSanta da naga sun motsa. Har zan fita Babala tace.
"Zo ki zauna Iyabo inason magana dake" Dawowa nayi na zauna kaina a ?asa ina wasa da gezar majanyin ashoke dana goye Taiwo da Kahinde dukansu a gadon bayana.
"Ba komai bane yasa nace kizo ba dama. KuWi nake son ki bani kamar dubu talatin haka, inason zan sai taki in tafi dashi, nayi magana da Baban Nazifi hidima tayi mishi yawa, ke kuma naga kin samu kuWi a wajen suna sosai"
To Babala bari in kawo miki"
Na mi?e na fita ina jinjina wannan lamari. Nera dubu talatin cib na ?irgi na kai mata, tako sa hannu ta amshe ba sannu bare madallah. Harna yi ma ?an biyu wanka na shiryasu ina ta'ajibin wannan al'amari. Toye na ja muka fita tsakar gida nayi mishi wanka a ?ofar Waki ya shigo. Ban gusheba sai da na Wauraye kayan da ?an biyu suka cire da wanda nasa naci suna, da wanda nasa jiya, dana Gwadabe duka. Kafin in gama wankin matan gidan suka cike igiyoyin da shanya tsab. Sai mayafi na yafa na shiga gidan ma?ota na yi shanyata. ?aki na shiga na shinfiWe ?an biyu a gado, Toye kuma na shafa mishi mai, yasa kaya. Ina juye ruwan wanka na mayar da ruwan kunu kan wutar. Ina fitowa na dama kunu na juye a jug Win silver na mayar da Wumamen tuwon jiya. ?aki na shiga na shirya tsab cikin jar atampa sabuwa fil Winkin dai buba da zani, yana cikin kayan suna da Iyaa ta hado mun dashi, na murza kwalli da jan baki, na bi jikina da body milk na Mrs Bukhari, na shafa har a ?asan mamana kunsan masu jego sai da ta'amali da ?amshi. Ina gyaran falo Gwadabe ya fito daga Waki. Murmushi nayi mishi, shima murmushin ya sakar mun.
YallaSai ka tashi, ya kan naka?" Bai amsa ba sai da ya haWe jikinshi da nawa, Laila fa duk abinnan tana naWe a doguwar kujera tana bacci.
"Lafiya lau Iyabo, sai kewarki a shinfiWata. Irin wannan kyau haka Babbar mace kenan, cinyar sa maganin mai haWama"
Dariya muka kwashe dashi kamar babu matsalar dake damun mu. Inason in ji Gwadabe ya kirani da Cinyar sa maganin mai haWama, ko Babbar mace, daya faWa sai in jii ?ibata ta sake burgeni, barenma in nai kwalliya, dan kwalliya tafi amsar masu jiki irinmu.
To yanzu dai karyawa zaka soma yi ko wanka?" Ido ya kashe mun yace.
"To ba sai ki zaSar mun ba kawai, tunda dai ni mijin Hajiya ne"
Ina dariya ciki_ciki nace.
To ka soma da wankan, zaka fi jin daWin karyawar. Ina faWar haka na fita, har na juye mishi ruwan a bokiti zan je rijiya in sirko, sai ya ri?e hannun bokitin ?arfen yace.
"In banda fitina irin taki kina jego ina ke ina aiki, gafara cus kawai."
Ya Wauki bokitin yayi bakin rijiya dashi. Baban Nazifi dake zaune a turmi yana rage ?asumbarshi da aska, ya ja tsaki yace.
"Allah wadaran naka ya lalace, Laila da majnun ma ?arshen tarihin soyayyarsu sam babu armashi a ciki. Gwadabe kayi asara shanyayye fitsararre"
Ya ci gaba da askinshi, ni kuma na shigewata ciki. Ina haWa mana abun karyawa a tire mandiya hamsha?iya ta tashi. Tsaki ta buga, ta fice fuu. Ni kuma na girgiza kai kawai na dure mana abincin a gefe, ni na tattare mata kayan rufarta na sa mata a saman akwatunanta. Na kunna turaren tsinke na Baba flora Wakin ya biWe da ?amshi. Ina zaune ina kallon wani kaset Win yarbawa, shiru_shiru yau Gwadabe zai shigo, gobe ne, har goman safe bai shigo ba. Ni kuma yinwa sai sasi?ata take yi, abinci na zuba na soma cin abuna. Ina kan ci wayata na jiyo kukanta daga uwar Waki, da sauri na shiga Wakin. Wata number ne ba suna, ina karawa a kunne na jiyo muryar Gwadabe.
"Nine Iyabo. Kiyi ha?uri muna asibiti tare da Babala. Na je dubata na tarar zasu koma asibiti shine muka tafi tare, muna gamawa zan dawo. Kici abincinki kinji? Zan tawo da cefane"
To Shikenan Gwadabe Allah ya ?ara mata lafiya, sai kun dawo. Dan Allah ka gaisheta sosai da jikin."
"To shikenan Babbar mace zata ji, ki kula mun da kan ki" Mu kai sallama na ajjiye wayar. Ina gama karyawa sai na shige Waki har bacci ya soma Wibata sai naji ana tattaSani kamar a mafarki naji ana kiran sunana. Ina buWe idanu naga ashe Uwani ce."
Kai Uwani irin wannan duka haka" Na faWa ina mi?ewa zaune.
"Ke dai bari Iyabo, damuwace ta ciyo ni shine na kasa ha?uri sai da na tawo. Amman kafinnan akwai abinci a gidan in Wan sama cikina, tun duku_duku na bar gida babu abunda naci"
Ki fita falo zaki ga tire akwai dumamen tuwo da kunu"
"Yanzu kuwa zaki ji labari Iyabo in na take cikina"
Fita tayi sai gata da tuwo sha?e da kwano da kununta cikin ?aton kofi, bayan taci ta yi gyatsa tace.
"Tun safe ni da matan gidanmu muka fita muka bazama gari neman aikin yi yinwa na shirin halakamu da yaranmu. Da ?yar muka samu aiki mu huWu. Wani sabon asibiti da aka buWe a bakin titin layinmu to anan ni na samu nawa aikin na wanke bayangidun asibitin, Hafizu kuma Allah ya so shi ya samu gadin get da ?yar wallahi, a hakanma saida nayi mishi jan ido ya karSa, gani yake shi yafi ?arfin gadi, matar gidanmu kuma nata aikin shara da goge gogen ?asa ne. Iyabo albashin bashi da yawa sam wannan rayuwa ni nama rasa yadda zan tsoma kaina a ciki ga matsalar gidan haya. Shaddarmu fa wata biyu kenan data rufza me gidan yace bazai gyara ba mu da muke haya a gidan mu zamu gyara. To mu bamu ci ba balle har mu iya gyara masai sai dai fa ko wacce mata tayi kashinta a po ta Wauka taje ta watsa. Gabaki Waya gidan sai wari kawai"
Jigum nayi ina saurarenta, yinwa bata da daWi sam ni kaina a baya mun sha kwana da yinwa mu wayi gari babu abinda zamu ci sai ruwa.
Uwani rayuwar ta zama sai a hankali, gashi mutane basa son taimako daga ?wauri sai guiwa kowa nashi ya sani. Amman a ?alla aikin zai rage muku sosai, sai ku gina rayuwarku akan albashin da kuke Wauka kusan yanda zaku tsara komai. Allah yasa dai mu dace kawai amman rayuwarma wataran sai kaji duniyar ta fice maka fit a ranka in matsaloli suka haWu suka cakuWe maka. Jiya da kinga irin tashin hankalin dana faWa da daddare da kin tausaya mun sosai" Nan na kwashe labarin iskancin Laila na bata.
"Kusun uwa kuma baki yi kukan kura kin dira a wuyanta kin narki shegiya ba?"
Kai na girgiza tare da cewa.
Hmmm motsi ma wannan na kasa. Ni da nake zaune a Wofane Uwani ai ina taSata zata jijjigemun auren nawa ne, kinga burinta ya cika ai ko?" Sai kuma ta sakko tace.
"Sai dai dan hakan amman in ba haka ba wallahi da saita gane kuranta. Amman ke haka zaki zuba ido kuci gaba da zama da'ita ko yaya kike so?" Mi?ewa nayi tsaye na Wauki Taiwo na saSa a baya, na sake sa hannu na Wauko Kahinde sima na sashi a kusa da ?ar uwarshi, na Wamaresu tamau da zanin goyo na bisu da majanyi. Hijabina na zura, na sa?a hannu a ?asan kayana dake jere a wadrop na ciro kudaWe na soke a giyo.
Mu je ki rakani in yo cefane kinji in Waura abincin rana, dan Gwadabe suna asibiti da Babala, bansan ko gado za'a kuma basu ba, ko zasu dawo gidaba, ya kamata in gama abinci da wuri" Fita a gidan mu ka yi muna tafe sai tauna matsalolin dake ci mana tuwo a ?warya muke ta ta faman yi.

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login