Showing 90001 words to 93000 words out of 270738 words

Chapter 31 - NAMA YA DAHU ROMO DANYE COMPLETE TRUE NOVEL BY BADI'AT.doc

kunya ba, daga zuwa aiki, in bari tarbiyata ta taSu ba" Murmushi p.a tayi mun tace.
"Wani hanzari ba gudu ba Iyabo. Da dirinki da kyanki ni nayi mamaki ma da kika zauna a gidan aikatau harna tsawon wata shida. Nayi tunanin harkar samun ma?udan kuWi cikin sau?i shi zaku Wauka daga ke har Uwani na ganku tubarkalla. Da a fita Waya ma zaku biya bashin da kamfani take binku, kuma ku zama ?an lele a wajen Hajiya " Da mamaki na dubeta.
Dama akwai hanyar da ake samun kuWi cikin sau?i shine ba'a nuna mana ba?" Dariyar cin nasara p.a tayi mum ta dafani.
"Yanzu ki koma. In Hajiya Babba ta fita zanzo Wakinku mu tattauna kafinnan Uwani sun dawo" Da wannan zancan muka rabu da p.a. Ina juyawa da zummar komawa Waki na jiyo muryar uwani.
"Iyabo" Ta kirayi sunana. Da sauri na juyo muka haWa idanu, ba ?aramin ramewa Uwani tayi ba, sai naga tayi wani irin haske. Take gabana ya faWi. Tana ?arasowa muka rungume juna sai kuka kamar ?ananun yara. Su maryam kuma su kai shigewarsu. ?ago Uwani nayi na ri?e kafaWarta.
Uwani kin rame da yawa. Sai naga kinyi Wanye kamar me yaron ciki" Sai ta sake fashewa da kuka. ?akin da babu kowa a ciki ta jani muka shiga.
"Iyabo ina cike da nadamar baro ?asata Najeriya, ina mai cike da fargaba da tashin hankali marar misalin da za'a musalta balle har a fahimta. Iyabo ciki ne dani na tsawon wata biyu" Da sauri na toshe mata bakinta tsabaren tashin hankalin dana tsinci kaina a ciki. Matar aure da cikin da bana mijinta ba Na faWa a cikin raina, a fili kuma nace.
Uwani baki faWa mishi ke matar Aure bace to?"
"Na faWa mishi da kwaSaSSen turancina. Amman Iyabo ya?i yarda. Kullum cikin dare sai ya baro matarshi yazo ya tare a Wakina. Kuka da majiya baya hanashi aikata komai. Na dawo da tarin kuWin da bansan iyakar yawanshi ba. Musamman da nace mai cikine dani. Ya bani kuWi masu yawa yace in na tafi kar in dawo, in matarshi ta gane shi yai mini ciki dani dashi zata haWa ta kashe.
Iyabo abinda bakai da ?uruciya ba, sai da aure a kan ka. Me zance da Hafizu, me zance da su Hajiya?" Kukane yaci ?arfinta. Niko sai kallonta nake yi ina auna girman abun. Cikin dauriya nace.
Da Hadiza tace jibi zaki koma, can gidan kike son komawa?" Kai ta Girgiza.
"Inata tunanin ta hanyar da zan Sulloma da Hajiya Babba ne. Naga irin Wibar albarkar da taima Hadiza data bu?aci sauya gidan aiki.
Ni Iyabo yaya zanyi da cikinnan?"
Wallahi Uwani ban sani ba, ?asa ba taka ba. Amman bari Hajiya Babba ta dawo, ya zame mana dole mu tunkareta ko dafamu zata yi taci.
Ki share hawayenki Allah zai kawo mana mafita. Taso mu koma cikin mutane" Hannunta na kama muka koma Wakinsu Hadiza. Duk cikinmu in aka cire Maryam babu wacce take walwala, sai kuma ba?i da basu san dawar garin ba. P.a ce ta le?o ta yafitoni ni da Uwani. Ta shigar damu wani Waki kamar na ajjiyar kayane haka, amman da halamu anan ita take kwana.
"Ku zauna ga katifa" Zama mu ka yi kamar yadda ta umarcemu. Cikin sakewa p.a ta soma yi mana bayanin da tuni ya kwance lissafi da notikan kaina. Uwani kuma sai hararar p.a take yi.
"To harkace ta arziki tasa na kira ku. Matsawar kuka amince da abinda na kawo muku wahalarku tazo ?arshe. Ai kamarku kun girmi gidan aiki sai dai a haWaku da manyan alhazzai, ko manyan hajiyoyi da zaku dinga ban gisiri in baka manda. Ku ba yara bane kun dai gane wannan lissafin ai " Uwani ta balbalin ta mi?e cikin jaraba da nasifa tana nuna p.a
"Mu rasa a ?asar da zamu yi iskanci har sai mun zo Riyahd a inda muke jin ?amshin Wakin Allah. Kuma har kike mana tayin maWigo? Ta Allah ba taki ba Allah ya tsaremu da sharri irin naki tur da tsufa da furfurarki dattijuwar biri. Iyabo muje kinji kafin in hallasa in kashe matsiyaciya." Jikina a mace na mi?e muka fice. Fitar da tayi dai_dai da dawowar Hajiya Babba da tarin mata. Matan aure da ?ananun yara da ?an bana bakwai.
"Sannu da dawowa Hajiya Babba" Uwani ta faWa a tsorace wani kallon uku saura kwata tai mana dai dai fitowar pa.
"Ince dai lafiya ko?"
A'a ba lafiya akwai gagarumar matsala" Nayi maza nace. Kallonmu tayi, ta kalli jama'arta da su kuma daka gansu a galabaice suke.
P.ai ki ji da waWannan ayi musu yadda ya dace. Ku kuma mujenku." A baya muka bita izuwa inda take ganawa da ba?inta. Labarta mata halin da Uwani take ciki nayi, da halin da nake ciki a nawa gidan aikin. Tare da ro?on a sake mana gidan aiki, kuma ta taimaka a zubar da cikin jikin Uwani.
"Lallai na Webo jagwal, ko kuma in kiraku da ?a?ai. Kusa kunnuwa da kyau a garinnan ganin maganin zubar da ciki ai aikine jajazur. Za a iya kamaku ma matsawar kuka zubar da cikinnan. Wata shida da kama aikinku sai tarin matsaloli. Shi wanda ya Wibga miki cikin yasan abinda ya aikata kin faWa mishi?"
MRS BUKHARI
Tofa wasa farin girki.

*Ina kuke mata ?an ?walisa irin Shanono? Ku firfito ga Uom Taufiq veils bead work and Abaya stone work gliter veils lafaya. Ta zo muku da haWaWWun aikin beat na hannu domin kwalliyarku da fito daku ku yi tsab.*
*Aikinta babu ha'inci ni na tabbatar. Nima Badiat Ibrahim zan bata aikin lafayata ta zuba mun aikin beat work kuzo muje tare ta gwangwajemu*
Masu neman ?arin bayani saiku tuntuSeta
07082649563 whats app number kira 07036028230
NAMA YA DAHU....
ROMO ?ANYE
BADI'AT IBRAHIM MRS BUKHARI B4B GIDAN ?AMSHI


9
"E ya sani, harma ya bani kuWaWe yace inna tafi kar in dawo dan in matarshi ta fahimci shi yaimun ciki zata kashemu dukka" Dariya Hajiya Babba ta kwashe dashi ta Wauki waya ta daddanna, jim kaWan ta soma larabci tana faWa ta inda take shiga ba tanan take fita ba. Ajjiye wayar tayi tana tsaki.
"Ku tashi ku bani waje, yace zai kawo miki maganin zubar da cikin zuwa gobe. Sai ki zauna da shirinki. Ke kuma zan duba lamarinki, ku tashi kuje" Ni na tallafama Uwani ta mi?e jikkunanmu a mugun mace, haka wunin wannan ranar ya kasance mana cikin tubka da warwarar al'amura. Yaya Hamma na tuno da irin kishinshi. Take na lumshe idanuna hawaye suka gangaro mun. Yarana na kuma tunowa da ubansu. Take murmushi ya suSuce mun. Takaddar da Khalifa ya bani na ciro a ledar kayana na farketa. KuWine sababbi suka zubo masu yawa a mimmi?e. Uwani ta dubeni tace.
"Wannan kuWaWen fa Iyabo?"
Hmmm Saurayin da nake faWa miki Khalifa na gidan da nake shine ya bani da suka saukeni a ?ofar gidannan. Uwani baki bani labarin wuyar aikin gidan larabawa ba." ?an murmushin dole tayi mun tace.
"Sawun giwa ne ya take na ra?umi. Amman duk wata azaba ta tabbata a aiki a gidan larabawa. Wuni guda cur mutum a tsaye kamar jaki. Sallah ma sai kayi da gaske kake ?wacewa kayi. Iyabo abun babu sau?i ni duk ?asar ta isheni gida nake son komawa. Hafizu kuma baya nan yana can Canada ko a wanne irin hali yake sai Allah. Dan ba mui waya dashi ba hajiyarmu ce take faWa mun. Sai hankalina ya koma gida. Ya kamata ki kira Burodami Debisi kema ai." Baki na taSe nace.
Wannan rayuwa cike take da ?alubale Uwani. Sai yanzu nake dana sanin ?in bin shawarar Yaya Hamma da Burodami. Yaya Hamma har shanu ya siyar ya bani jari in dinga zuwa kano ina sare_sare amman wallahi na?i fur, sabida ni manyan kuWi nake hari. Uwani shekara na zagayowa ni dai zan tafi gida magana ta gaskiya, da dai na samu ?an kuWaWen juya kasuwanci, da Wan kuWin da zan saima Dada Wan gidan da zata zauna shikenan ni daman ba wani abun nake nema ba. Bani number Burodami in kira ko zan sameshi" Jakarta ta buWe na hango kuWi sosai a saman jakar, takaddar da na rubuta lambar ta mi?o mun, na daddana number, na kira ta ?araci ringing babu wanda ya Waga, na sake gwadawa bata sauya zane ba.
An?i Waga wayar Uwani, zuwa gobe na sake gwadawa .
Washe gari da safe muna kan karyawa sai hira aketayi a Wakin. P.a ce ta le?o tai kiranmu baki Waya ni da Uwani.
"Tashi muje Iyabo. Kinsan halin almurar matarnan bata da daWi sam." Tashi nayi ina lashe hannuna muka je muka sameta da wani mutumi a zaune a kujera. Ashe shine wanda yaima Uwani ciki. Magani Hajiya Babba ta mi?o ma Uwani a farar leda. Jikinta na rawa ta amsa.
"Ga maganinan na zubar da ciki. ?aya zaki sha, sai ki tura biyu gabanki. Ki jirayi zubar jini minti talatin da sha. Sannan ya bada kuWi wanda har yafi ?arfin kuWin da nake binku ke da ?ar uwarki. Amman ki sani sisin kwabo ba zaki gani ba, wanda ya baki ma in kika bani haWawa zanyi in karSe. Ku shirya Zan mai da ku Jidda kuci gaba da zama. Dan yana bu?atar kiyi nesa da garin da yake, dake da wanda ma ya sanki. Dan haka kuje ku Webo kayanku yanzu mu wuce, kamfani bata binku ko sisi, sai kuje ku nemi kuWi a Jidda." Kasa magana mu ka yi dan takaici, da mamakin zalunci irinna Hajiya Babba. Haka muka Wakko kayanmu, mu kai Sallama dasu Hadiza, nan muka kama hanyar Jidda.
A wannan gida na Jidda anan muka ga abubbuwa na tashin hankali, anan muka ga masu ciki iri daban daban. Yaranmu sun zama wasu ?ananun ?an iska, yarinya ?arama da buWaWWen idanu. Sai girke_girke wasu daga cikinsu suke ta faman yi. Abun mamakin ma abincin gida Najeriya suke dafawa, dangin dambu, shinkafa da wake. Can gefe kuma ga wasu tsofaffin mata sai ?ulla gyaWa soyayya da aya suke yi. Sai yima Hajiya Babba sannu da zuwa suke yi. Ni dai ina ri?e da hannun uwani dam. Duk inda Hajiya Babba ta cire ?afa anan muke Wora tamu har zuwa wani Waki mai cike da kayan more rayuwa. Sai wasu dilolin kaya a zube a tsakar Wakin da halama na siyarwane. Wata tsohuwar ?ar duniya muka tarar a kwance tana waya sai zabga larabci take yi tana dariya. Bayan ta ajjiye wayar ta dubi Hajiya Babba tace.
"WaWannan sune matan da kika ce zaki kawo Win" Hajiya Babba tace.
"Gasunan kin gansu. Duk abinda kike ganin ya dace a kansu ki zartar kawai. Kinga me juna biyun ita dai za a iya jefata a kasuwanci dan Abu Khadija ya faWamun ya bata wadatattun kuWin da zata lura da lafiyarta. Ita waccan ko gidan aiki ne sai ki jefata, Allah bashi in ta tara kuWinta ko kasuwancin tura kaya Najeriya ne sai ta soma itama. Tunda dai sun biya kamfani kuWinta. Ga fasfo Winsu nan" Ta zuge jakarta ta ciro ta mi?a ma wannan mata. Kallonmu tayi tace.
"Ke me juna biyu, kina da sha'awar kasuwancin tura gumama gida Najeriya ire iren dogayen riguna haka?" Ta nuna mata na zube a tsakar Wakin. Kana ta Waura da cewa.
"Harkace mai riba sosai, domin a Najeriya da tsada ake siyen dila. Da sai ki soma ko da da dila Waya ne kina turawa gida. Da zaran kinga harkar ta karSeki sai ki dulmiya kuWi a dama dake. Ga harkar zannuwan gado, ga harkar barguna ma itama tana tafiya( Anty Zee me zanin gado ana magana) ga atampa ?ar leda matan Najeriya na sonta sosai." Uwani dai ita damuwarta cikin dake jikinta ne, kuma a zahiri tana son taimakon iyayenta sosai. Kuma tasan mahaifiyarta ?ar kasuwace zata tsaya tsayin daka ta siyar da kaya in an tura mata yadda ya kamata.
"To Hajiya kamar yadda kika ce sai in soma da dilar gumamar mu jarraba. Itama ?awata bata bu?atar gidan aiki. Tana da kuWi inma ba zasu isa ba, in nawa zai kai a sai mana dila biyu shikenan sai a siya mana. Mahaifiyata zata dinga siyar mana ana turo kuWi muna tura wasu kayan." Hajiyarnan tace.
"To da zafi _zafi ake dukan ?arfe tunda dai da kuWaWenku dilolima akwaisu iri da kala a gidannan. Zan kaiku ku zaSa sai ayi batun kuWi. Sabida jirgin kayan ana Wan samun jinkiri zaki ga bai isa da wuri ba. Kuma za a iya saro muku kaya daga can gida Najeriya kuma kuci kasuwarsu. Zaku fi ganin afkin kuWin."
Nan dai Uwani ta fito da kuWi aka haWa da nawa duk muka Wungume kuWi muka bata. Ashe wannan shine somin shigarmu cikin tarin tulin matsaloli. A ta?aice dai ashe damfara ce kawai Hajiya Babba ta haWa domin ta karSe wannan kuWi da shi Abu Khadija da yaima Uwani ciki ya ambata mata ya ba ita Uwani. Gashi a gidan haya ake biya, kai zaka sai abinci da kuWinka, kai zaka sai sabulun wanki da abun goge baki."
Uwani dai tana kwance tana jinyar jikinta dan ta sha ciwon cikin da harna fidda rai da ci gaban rayuwarta. Cikin hikimar Allah kuma sai ya tashi kafaWunta a cikin kwana na goma da zuwanmu gidan. Abinci bashi nake karSa mana a wajen masu abincin gidan. ?an cirani babu irin waWanda babu a gidan. Har mabarata mata da ?ananan yara akwai. A kwana na goma sha biyu sai gani a titi ina faWin sabil_sabil ina kuka. Hajiya Zuwaira macece maras mutunci da rashin tausayi a hakan tazo take tambayarmu kuWin hayar Waki wai kwana goma_goma ake biya. Watsi tayi mana da ?ar jakar kayan namu. Sai Fati wata yarinyace ta taimaka mana muka dawo Wakinta.
"Sai fa ha?uri. Amman me zai hana ku nemi gidan aiki. Tunda dai ba zaku iya irin rayuwar da mu muke yi ba, muma ?addara da wahalar aiki a gidan larabawa ne ya ja mana, kuma sai ka fi shekara nawa baka tara wani abun arziki ba. Ai ina ganin zai fi muku ko?" Ina sharar hawaye nace.
Na amince zan tafi gidan aikin Fati. In shekara ta zagayo sai mu koma ?asarmu abinda muka tara Allah ya amfana." Nan muka amince Hajiya Zuwaira ta sama mana gidan aiki. A can wani gari me nisa. Ni na soma tafiya wannan karon. Gidan wasu tsofaffin miji da mata aka kaini. Gidan akwai tarin aiki, ga tsofaffinnan da tsari, gasu da yawan yin ba?i. Haka na kama aiki ka'in da na'in kullum mafarkina bai wuce in buWe idanuna in ganni a gida Najeriya ba. Ga dakon soyayyar Yaya Hamma da zuchiyata take ta faman Wawainiya dashi. Duk tarin gajiya da tarin matsaloli daidai da sakan zuchiyata bata taSa barin tunanin Yaya Hamma ba. ( Ina kira ga mata masu tsallake ?asarsu su tafi wata ?asar da zummar yin aiki. Ku sani in kinga wata taje ta samu kuWi baki san irin sana'ar da take yi ba harta samu wannan kuWin ba. Wasu har rasa rayukansu suke yi. Wallahi babu iriyar azabar da ba'a ganawa waWannan mata masu barin ?asarsu zuwa wata ?asar. In baizo kanki bane kawai zaki ga kamar duk waWannan abubbuwan basa faruwa. Amman akwai da yawa waWanda suka shiga tarin matsalolin daya dama na su Iyabo ya shanye. Amman fa bance ba'a dacewa ba. Wasu suna iya zuwa saudiyya su ?araci rayuwarsu a gidan aiki Waya ba tare da sun sake ba. Kuma in har za a rabu ma kiga iyayen gidan sunyi ma ?ar aiki kyautuka na alfarma. ?alilanne masu dacewa da hakan. Da yawan yaranmu in suka tafi lalacewa suke yi su shiga harkar banza. Ke uwa, ko miji kuna gida gaho damuwarku ayi muku gini, a dinga turo muku kuWi. Baku damu da halin da yaranku suke ciki ba. Kuma da yawan agait agait Winnan da yawansu basu da kirki cuta da ha'inci kawai suka saka a gaba. Da kin taSasu sai suce suma hakan akayi musu. ?alilanne daga cikinsu zuchiyarsu take a tsabtace.)
Gaga_gaga haka rayuwar tayi ta faman tafiya. Aiki kamar zai kasheni. Ba hutu, ga ciwon baya mai tsananin gaske da nake fama dashi. Musamman wayewar garinnan ta yau. Nama kasa mi?ewa sallar asuba ma sai a zaune nayi. Gashi uwar Wakina yarinyarta dake aure a Madina suna gidannan ita da yaranta huWu tazo duba mahaifiyarta. In mi?e tsaye fa na kasa. Wallahi Allah sai da rarrafe na samu na fito. Ina ganin Uwar Wakina na fashe da kuka nake cakuWa mata larabci ina kwatanta mata zanje gida bayana ba lafiya. Hankalinta ya tashi. Take ta taso ?arta aka Waukeni zuwa gida. A lokacin watana biyu da zuwa gidan kenan. Da ?an kuWaWena a lalita dasu nake kwana kuma dasu nake tashi.
Fati ce ta samu tawul da ruwa ta dinga dannamun bayan nawa, wanda a wannan lokacin har kumburi yayi. Ta mulke mun bayan da man zafi. Sai sannu wani Wan daudu yake yi mun ?awar Fatyne.
"Subhanallaah ni kam ku rufa mun asiri kar ki mutu muna Wakinnan ki jaza muna jafa i" Ha?orana suna kakkarwa nace dashi.
Dama mutuwar zata zo ta Waukeni kaga shikenan nima na huta." Sai yayi shiru, can kuma yace .
"Kinma ci abinci kuwa" Kai na girgiza mishi halamar A'a.
"Kawo kuWi a haWo miki tea ki Wumama cikinki, sai a Wan haWo miki da farfesu" Gudun kar susan akwai kuWi a jikina, domin na fahimci rayuwar Saudiyya ba wanda yake yarda da kowa sai nace.
Faty Ki ranta mun, dana samu dama_dama zan baki kuWinki dan Allah" Cikin minti talatin sai gata da shayi me kauri da farfesun kaza, naci sa a na samu naman ?irji. A daddafe na sha farfesun, na haWa da tea. Magungunan ciwon jiki ta SaSSallo mun na watsasu. Cikin ikon Allah sai bacci ya Waukeni. Bani na farka ba sai da duhu ya rufa, dana mi?e tsaye sai naji da dama inji mutan nijar suka ce da dama. Alwala na Wauro a ?aramin toilet dake cikin Wakin. Raak'a Waya na iyayi a tsaye, dana yi ruku'u kasa Wagowa nayi sai zarcewa sujuda nayi, sabida ji nake dana tankwara bayan wani ?ashin ka iya Sallewa in shiga uku.


GWADABE
MARA?I
Da daddare sosai Gwadabe ya shiga gida. Dan Hadiza ma ta ?araci jiranshi, da sunturin zuwa Sarayinsu harta ha?ura ta kwanta.
"Kaine

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login