Showing 138001 words to 141000 words out of 270738 words

Chapter 47 - NAMA YA DAHU ROMO DANYE COMPLETE TRUE NOVEL BY BADI'AT.doc

mana. Uwani ce ta nutsu ta soma yi mishi bayani da larabci kasancewar ta fini ?warewa a yaren. Salim hankalinshi ba ?aramin tashi yayi ba har ?walla saida ya zubar wallahi.
"Allah shine shaidar son da nake yi miki. Ni nasan harda tsoro yasa kika ?i aminta dani Iyabo. Yaya zanyi da sonki, kinsan sonki zai iya zautani kuwa?"
Wasu siraran hawayene suka gangaro a kumatuna. Salim duk ya birkice abinka da farin mutum har fuskarnan tashi ta Zama jawur da'ita haka ma idanunshi.
Salim kayi ha?uri bazan iya saSa ma iyayena domin faranta nawa ran ba. Yayana suka zaSa mun. Ina mai baka ha?uri , Allah ya Sillo maka da wacce ta fini alkhairi a rayuwarka da addininka. Na yaba nayi godiya da soyayyarka a gareni kayi ha?uri " murmushi yayi mun yace.
"Ina sonki Allah. Amman na ha?ura har ga Allah kuma ina ro?on Allah ya baki zaman lafiya da mijinki ya baki zuriya Wayyiba. In na haifi yarinya zan saka mata sunanki Iyabo"
Sai zuchiyata naji ta tsinke ainun. Babu shiri hawaye ya shiga gudu a kumatuna. Billah da zan iya amsar son Salim da zan amsa. Amman kash ko wacce zuchiya da abin sonta, kuma ko wacce ?warya tana da abokin burminta.
Jabu zaka saka ma yarinyar taka. Sunana kenan ta Sangaren mahaifiyata." Dariya yayi yace.
"Jabu what a nice name" Mi?ewa yayi tsaye hannayenshi a cikin aljihun jallabiyarshi yana kallona yana nazartata, ko kuma karanta wasi?ar jaki.
"Zan koma Kano. Jibi zan koma inda nafi wayau. Zaki ga sa?ona inna koma ga wannan gudunmawatace ki sai gadon da angonki zai hau ku raya sunnah nayi imani zan samu lada. Kiyi al?awarin siyan gadon kar ki saSa Jabu.'
KuWi masu kaurin gaske ya bani, wanda a wannan lokacin inna canja kuWin zasu iya kaiwa dubu Wari biyar irin ta da bata wannan zamanin na tinubu ba.
Godiya nayi mishi har tashar mota ni da Uwani muka rakashi dan ita tace zata kwana biyu ta tayani jinyar Dada. Sai da muka ga tashin motarsu yanata Waga mun hannu idanunshi fal ruwan hawayen bankwana.
Kuka na saka rikitaccen gaske na runtse idanuna tsigar jikina sai tashi take yi. Tausayin Salim ya dirarmun sosai."
"Ki dena kuka Iyabo, na fahimci ke kanki bawai son Saleem bane bakya yi ba A'a. Son da kike yima wancan figaggen ne yafi na Saleem. Kamar yadda Hamma yake sonki fiye da Saleem Win. Muje magriba ta kawo kai, kiyi ha?uri ki fuskanci yadda zaki fahimtar da gogan naki naga ya Wauki zafi, fulani dama suna da tsantsar kishi gaskiya. Nifa mamaki iskancin Hamma yake bani "
Wallahi Uwani ni tausayi ya bani. Jibi yadda yake kuka kamar ?aramin yaro fa. Uwani ni nasan raWaWin son maso wani. Sannan ni ina gujema matsaltsalun rayuwane. Na tsorata da auren mijin da ba yarenku Waya ba. Fulani da yarbawa kuma suna da daWaWWen tarihi na zamantakewa da auratayya. Bugu da ?ari Hamma jininane, ina tsoron kada son abin duniya yasa in zaSi Saleem harga Allah Hamma nake so" Uwani ta ja gwauron numfashi tace.
"Iyabo na fahimta, ni kaina waWannan tunane tunanenne du banyi su ba. Duk da dai masu iya magana suna cewa abinda aka gasa shi yaji wuta"
Fitowa mu ka yi daga tasha muka tari abin hawa zuwa bakin asibiti. Gogan yana tsaye a bakin asibiti da halama ya kafane ya tsare yana son ganin ta inda zan Sullo. Gabana ya yanke ya faWi ganin irin kallon tuhumar da Hamma yake yi mun.
"Uwani ba?on ya tafi ne?" Ya tambaya yana kakkafe ita uwanin da ido.
"Ya tafi Hamma. Dama dai ya matsa ne yana son yaga Jabune, sabida kayan da yawa bazai yiwu ace ya tafi ba tare da ya ganta ba." Murmushi yayi kawai ya kalli tsakiyar idanuna, saiya soma kallon ?wayar idona da Waya da Waya. Ta gefena Uwani ta shige.
"Wannan soyayyar taku inna tsaya anan Hamma sai zuchiyata ta buga" Cewar Uwani data yi shigewarta ciki.
"Me yazo nema a wajenki, kuma me yasaki kukan da har fuskarki da idanunki suka sauya launi?"
Wannan tambaya tashi ta sake rikitani, bansan me zance mishi ba.
"Ki shiga ciki su Hama da Daso suna ciki. Ni zanje masallaci inna dawo zan raka Hama gida"
To Shikenan sai ka dawo"
A gurguje na wuce tare da sauke ajjiyar zuchiya a haka dai kamar fishin nashi ya sassauto.
A wajen gadon Dada kuma su Daso suna zazzaune a tabarma suna fira ita da Hama ?awarta. Gefensu kwanukan abincine da suka kawo. Uwani kuma tana zaune a kujerar roba inda nake zama. Ina isowa Hama ta dena hira ta haWe girarta ta ?asa data sama. Ita kanta Daso na ga canji sosai a yanayinta. Nasan yana da nasaba da tsaida lokacin aurenmu da Hamma.
Sannunku Daso ashe kunzo, ina wuninku?" Daso ce ta amsa babu yabo babu fallasa dai, Hama kuwa bata ce um ba, wasa take da hannun Wiyarta dake kwance a cinyarta.
Uwani wannan itace Daso yarinyar ?anwar Dada Yafendo Jabu me sunana. Wannan kuma Hama ce matar Yaya Hamma "
"Ayya, ai mun gaisa kice itace uwargidanki. Hama Allah ya sanya alkairi Allah ya haWe kawunanku"
"A gaskiya baiwar Allah baki kyauta ba ai ba'ayin haka. Sanin kanki ne babu macen da take son kishiya, ita kanta Jabun da ita za'aima kishiyar aka mata haka ba zata ji daWi ba"
Daso ce tayi maganar cikin fishi da fishin Hama. Sanin halin ?awata Tabalbalin yasa nace.
Kuyi ha?uri itama bata faWa da niyya ba" Tsaki Hama tayi, Uwani tace.
"Allah sarkin girma inji kishiyar mai ?uwayya. Allah ya baku ha?uri ni ba ba?uwar zafi bace. Amman fa ku iya bakunanku in kuma ba haka ba sai dai kuji jini na zuba, ?an iska ?auyawan banza duk kun cika waje da ?arni."
Duk wannan abun da akeyi Dada bacci take yi. Fulatanci da Hama ta soma zazzagowane ya farkar da'ita. Nasan dai ba alkhairi Hama take faWi ba. ?iyarta ta goya tana ta huci.
"Daso meke faruwa ne?" Dada ta tambaya.
"Babu komai Dada" Amsar da Daso ta bata kenan. Ana cikin haka sai ga Hamma ya iso.
"To muje ko dare nayi. Dada saina dawo zan kaisu gida"
"To dama ka zauna a gida. Jabu da ?awarta zasu kwana anan. Kaima ka huta. Ka sanar da Baffa Musa, inason ganinshi gobe da sassafe.
"Haba Dada. Kona koma gidan ma ni bazan iya bacci ba. Likita ma ya tabbatar mana zuwa gobe ko jibi zai sallamemu mu koma gida. Hama muje"
Fuuu Hama ta fice ko sallama batai mana ba, Daso ce kawai taima Dada sallama ni ko da uwar harara ma ta bini. Ni kuma nayi mata murmushi kawai nasan kishin rashin Hamma ke damun Daso, ba taya Hama kishi ba. Tunda data samu dama itace zata zama kishiyar Haman.
"Ga abinci kuci Jabu. Ba?on ya tafi ko?"
E Dada ya tafi"
Matashin kanta ta Wan Waga ta gefe ta zaro kuWin da Saleem ya bata ta mi?o mun."
"Ki ri?e a hannunki, ni bansan ma nawa bane. Jabu su Yusufu har yanzu basu zo sun dubani ba" Murmushi nayi mata nasa hannu na amshi kuWin
Dada nice na hanasu zuwa, kiyi ha?uri an kusa sallamarmu mu koma gida"
Maimakon naga tayi farin ciki. Sai naga saSanin hakan damuwa ta bayyana a fuskarta. Babu shiri na ?arasa wajen gadon na zauna a gefe guda.
Dadana na siya miki gidan da zaki zauna ki huta ki mori haihuwa kema. Kuma in sha Allah zan zuba miki kayan alatu da zaki more tsufanki. Kulawarki ta dawo hannuna Dada. Su Cubu zasu zauna tare dake, na Wauke miki nauyin komai Dada. Nasan ?ila tunanin inda zaki zauna kike yi" Hawayene ya gangaro ta gefen kuncinta, sai ta runtse idanunta tace.
Ubangiji Allah ya kai haske kabarinka Akintoye. Ha?i?a kabar baya me kyau. Jabu kamar yadda sanadiyyarki matsalolin rayuwata suka gutsire. Ina ro?a miki Allah Hamma ya zama silar goge miki damuwar rayuwarki. Sannan inaso in faWa miki kibi Hama a sannu, sannan kibi Daso a sannu. ?azu ba bacci nake yi ba duk abinda suka tattauna duk a kunnena. Dansu a kuWirinsu shine aurenma bazai yiwu ba. Bokaye sosai Hama take bi duk dan a raba soyayyarku. Ke kuma saiki dage da ro?on Allah yai miki tsari da sharrinsu. Nayi imani da Jabu uwar Daso zata san abinnan da Daso tayi zata iya yi mata baki. Dan haka kija bakinki kiyi shiru komai ma yazo ?arshe daga gobe za'a yita ta ?are" Hannun Dada na dam?e na lumshe idanuna. Na lura a wannan tafiyar kamar da jarabawar kishiya kuma zan jarabtu na tsallake rijiya da baya akan uwar miji, ga kishiya kuma jama'a tana neman rayuwata.
Babu komai Dada, Allah shi ke da iko akan komai. Ki tayani da adda'a nima zan zage damtse. Ki kuma dena kuka Dada, Allah ya ji?an Baami"
Dawowa nayi kusa da Uwani a tabarma. Na zuba ma Dada jallof Win shinkafa dasu Daso suka kawo, har zan mi?a mata sai naga kamar yayi kaWan sai na sa?a cokali zan ?ara mata. Wallahi saiga dun?ulen magani a cure a waje Waya bai idasa cakuWuwaba.
Subhanallaah Uwani duba" Na nuna ma Uwani. HaSa ta kama tare da zaro idanu.
"Iyabo wannan ai dun?ulen maganine, hala kishiyarkice ta kawo abincin?" Da kai na amsa mata. Juye abincin nayi na rufe, na jawo kular Karima matar Amaduyal na zuba ma Dada abincin ciki. Shinkafa da miya da kifine. Na mi?a mata na bata ruwa. Na saka mana cokula biyu a cikin kular zamuci dan sabida ?auyanci a kan shinkafar ta kyaSo miyar.
"Iyabo jikina yayi sanyi tsoron Allah kuma ya kamani. Tofa wata sabuwa inji Wan caca. Shi kuma wannan auren na lura da kishiya za'a fafata. Nifa duk harkar asiri bana ciki. Ko kishinne nafi son muyi na kirsa duk wacce ta biya allonta saita wanke. Amman tun kafin ki shigo ciki an soma binki da bita da ?ulli?" Ni dai ko magana wannan na kasa yi. Sai cin abincin nake yi. Abincinma sharkab da mai dan masifa sai tea na haWa mana muke danne man dashi. Wajajen bayan isha Yaya Hamma ya dawo. Leda ya mi?o mun Waya cike da tsire, Wayar kuma lemun kwalba ne montin dew. Dada ta Wan jima da bacci sabida magungunanta kamar akwai masu saka bacci.
"Ni kam me ya haWaku da Hama da Daso Jabu"
Kallonshi nayi, sai na fahimci ranshi a Wan Saceyake sai nace.
Babu komai wani abun suka ce maka anyi?"
"E Hama tace mun wai kince kinfi ?arfin kiyi kishi da'ita dakin shigo zaki kaWata. Maganganu dai marasa daWi Daso tace har mahaifiyar Hama kika zage tas. Dan Allah meye gaskiyar wannan lamarin?" Kallon kallone ya shiga wanzuwa tsakanina da Uwani.
Tab wata sabuwa inji Wan caca, ni Iyabo gidan da zan faWa kuma kenan? Ga asiri ga makirci anya kuwa? Uwani ce naji tayi mishi bayanin abinda ya faru. Sai yayi dariya kawai yace.
"Kishi ne yake damunta sosai shi yasa ita da Dason suka ?ir?iri wannan maganar. Amman zan Wauki mataki akan ita Haman ni na isa da gidana.
Jabu ina jiranki a waje domin ki bani amsar tambayoyina"
Yana idasa maganarshi ya fice hannunshi ri?e da sandar da ba'a fiye raba bafulatani da'ita musamman ma masu fita kiwo. Idanuna na lumshe kaina sarawa yake yi sosai.
Uwani ci namannan bari inje in kashe wutar da kika kunnamun. Inna dawo zamu tattauna matsaloli Uwani"
Nan na bar Uwani tana cusa tsire da albass a bakinta. A inda yake kwanciya na sameshi kanshi a ?asa yana bubbuga sandarshi a ?asa. Harna zauna bai Wagoba, ko salllamata ya?i amsawa lallai ran maza ya Saci.
Angona masoyina wanda ya zama zaSina abun begena. Lafiya ka kasa amsa sallamata, ko dai maganganun da Hama tace na faWa mata ne suke damunka?" Shirune ya biyo baya na da?i?u kana ya Wago idanunshi ya saukesu a kaina. Na kasa karanta ha?i?atan Win abinda ke cikin idanun nashi, na hango kishi, da so mai wuyar fassarawa. Ajjiyar zuchiya na sauke tare da yin ?asa da idanuna, ina jiyo yadda idanunshi ke yawo a fuskata.
"Wallahi Allah ina da mugun kishi akan duk abinda nake so. Wannan dalilin yasa na kusan kashe Wan uwan Hama a filin shaWi a lokacin da ya zama daga cikin gwarazan da suka fito neman aurenta. Jabu kafin ki tafi saida na dam?a miki amanar rayuwata nasa kikai mun al?awarin babu wani Wa namiji da zaki bashi damar shiga rayuwarki. Kaico ashe ke soyayya kiketa ta yi. Ni kin barni da dakon sanki, kewarki duk ta hanani sukuni, hatta bacci me kyau ina samune duk ranar da nayi mafarkin na aureki jibi yadda na fita hayyacina Matata da abokaina kullum a cikin surutun lalacewata suke. Amman ke ashe mu biyu kika ajjiye a gurbin zuchiyarki, kin ban mamaki sosai Jabu.
Meye matsayin Saleem a wajenki, kuma me yazo yi wajenki, Allah yasa ba kukan sonshi kika yi ba?"
Shiru nayi kamar ruwa ya cinyeni tunda ya soma maganarshi harya dure. Akwai taushi da zafi cakuWe da muryar tashi.
Yaya Hamma ka yarda dani kai Waya tal ne a zuchiyata ban haWa soyayyarka data kowa ba. Ko uban ?a?ana ban soshi irin son da nake yi maka ba. Gaskiya dai Waya ce Saleem ya taimakemu a zamanmu na saudiyya. Dan shi yai mana hanya muka dawo Najeriya. Bamu yi soyayya ba, amman ya soni sosai. Dalilin zuwanshi kuma neman aurena yazo yi, kuma na faWa mishi gaskiyar lamari. Batun kuka kuma ka gafarceni tausayi ya bani ne"
?ur idanunshi a kaina yana kallona irin kallo mai fassarar ban yarda dake ba. Idanu na lumshe na buWe a kanshi.
Yaya Hamma"
Yayi saurin Waga mun hannunshi. Yayi magana da wata murya a ciki.
"Ya'isa haka dan Allah. Kar kiyi sanadiyyata inje in rataya a wuyanki. Ki koma ciki (>?#?>?#?) Uwani na jiranki saida safe"
Nayi yin?urin fahimtar dashi tare da rarrashinshi. Amman bai bani wannan damar ba sam. Haka na mi?e jiki da zuchiya babu kuzari na shiga na samu Uwani tana waya.
Jagwab na zauna a gefenta ina ambaton Allah.
"Lafiya na ganki haka Jabu, an samu tsabanin fahimta da Hamma kenan ko?"
Ke dai bari ya?i fahimtata akan zuwan Saleem Uwani. Amman zan bashi lokaci inya huce zai fahimceni. Ni wallahi komai ya fice mun arai, Hama lamarinta ya kashe mun jiki. Tsorona Allah tsorona hulWa da mai mu'amala da bokaye Uwani. Wannan wanne irin zama zamuyi kenan, da wanne irin bita da ?ullin zata bini in mijin ya zama namu mu mu biyu?" Uwani ta muskuta kana tace.
"Adda'a takobin mumuni, bacci da barin bakinki shiru ba naki bane. Ni a tunanina da ai miki kisan mummu?e aita gabza miki asirinma baki sani ba. Ai gara kin sani zaki san irin zaman da zaki yi da'ita. Ke dai ki zama me lura sosai. Kar ki sake kici duk abinda zai fito daga hannunta shine kawai tunda kin nace. Abinne Allah cuta Allah magani, tunda ko kai akazo aka tarar bakasan irin wacce za'a kwaso maka ba. In kinga irin yadda amaryar Hafizu take tata Wiban albarka irin nasu na ?an ?auye Iyabo zaki ri?e baki. Kinsan akace shege na ?auye."
Dariyar dole Uwani ta bani, duk da labarin da take bani mai ciwone a gareta itama saida ta dara.
Bani labarin yadda ta kaya a tsakaninki da Hafizu ranar da kika koma"
"Hahahahhh baki da kyau Iyabo.
A daren ranar ni ban barshi ya shigo mun Waki ba. Kafin ya dawo na gar?ame Wakina. Bugun duniya banbi ta kanshi ba, sai matarshi ce tazo ta jayeshi tana cewa wai ya barni ?ila bacci nake yi.
Sai da safe dana buWe Wakina ya shigo muka gaisa sama_sama, ni dai na?i sakin fuskata sai jana da hira yake yi nayi biris dashi. Ke saiga wani dumamen tuwo da wani ?azamin ruwan kokko harda dogon gashi a ciki matarshi ta shigo ta dure mun.
Ke dai kinsan banda daWi Iyabo, a ta?aice dai na sai gida a can saman layin ta titi, Wakuna ukune sai banWaki da kitchen harda shago a ?ofar gidan, nayi komawata. So nake inna nutsu a gyare mun shagon in soma kasuwanci a ciki, in Allah ya dafa mun shikenan fa Iyabo. In Hafizu yazo miji, in baizo ba shi da banza basu da maraba. Bazan kashe kaina ba wallahi sabida rijalu. Ko yanzu ya tafa mun takaddar sakina cafewa zanyi in cashi zawarci"
Kai na jinjina ina dariyar furucinta na kusa da ?arshe da tace in yazo miji, in baizo ba shi da banza duk Waya.
Uwani ta balbalin duniya. A irin zafinki kam zama gida Waya da kishiya ba naki bane, raba gidan yafi. Koni da ace Hamma zai amince mun da saina sai waje na gina inyi zamana a gidana da saina fi samun nutsuwa. Amman kinsan ?an ?auye su gidan gandunnan shi suke yi, kowa dai da Sarayinshi."
"Amman dai zaki gyare Sangaren naki yadda zaki ji daWin zaman wajen ko? Ina tausayinki Iyabo baki san sharrin rijalu bane hmm" Murmushi nayi nace.
Sai dai in gyara cikin Wakin nawa, wallahi Uwani bana son inyi wani abun da zai haskoma Hamma kamar na raina arzikinshi. To iyakar gyara zan yishine a cikin Wakina"
Harara ta watso mun taja dogon tsaki ta jiya baya ta kwanta.
Uwani meye haka?" Cikin masifa tace.
"Da Allah Iyabo mu bar zancannan ni bacci nake ji naga kamar kin zama majuniniyane akan Hamma"
Dole haka zancan ya tsaya. Ni kuwa na jima cikin tubka da warwara da ?yar bacci ya Waukeni cike da mafarkai marasa daWi masu tada hankali. Gabaki Waya saina wayi garin cikin damuwa da fargabar data haifarmun da zazzaSi.
Da sassafe saiga Yafendo KaSoji, da Baffa Musa sunzo.
Dada tace mu basu waje, me suka tauna oho basu jima ba suka kama hanyarsu. Muna komawa ciki saiga takaddar sallama da ragowar kuWaWen da ake binmu. Gashi yau tun sassafe Yaya Hamma ya bar asibitin. Uwani ta zauna da Dada ni kuma naje na biya kuWin da ake binmu. Ina dawowa na tarar da Amaduyal shi da Kari matarshi. Kari ce ta tayani tattare kayayyakinmu tsab, Amaduyal kuma nace ya fita ya nemo mana ?aramar mota zuwa Girai.
Ai kuwa hakan akayi motarnan ta saukemu a Girai muka hau akori kura zuwa Banyo, daga Banyo muka ?arasa jaSSi. A sabon gidan Dada muka sauka. Ta kalli gidan ta kalleni saita saki kukan farin ciki ta dubeni tace.
", Jabu Allah yayi miki albarka. In sha Allah Kamar yadda


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login