Showing 15001 words to 18000 words out of 270738 words

Chapter 6 - NAMA YA DAHU ROMO DANYE COMPLETE TRUE NOVEL BY BADI'AT.doc

taje. Babu makawa Gwadabe sai ya aureta. A daddafe na mi?e na shiga gyaran Waki, sai da na kintsa komai, na fitar mana da wankin kayayyakinmu na soma wankewa inayi ina rera wa?ar yarbawa, amman wani shashe na zuchiyata a cike yake da tsoro da fargabar zamana tare da Laila. Kafin takwas na safe na gama komai har shara da wanka duk mun yi. Abinci na WunWuma mana, kamar jiya na sake zuba ma Laila nata dai na dire mata. Ina gama karyawa na fito cikin shiri, na yi kaye_kayen kayana masu amfani na kulle uwar Wakina. Laila na falo tana cin abincin dana ajjiye mata na yi ficewata ina jaye da hannun Toye, har zuwa bayan layinmu gidan da nake yin aikin shara, wanke_wanke, da goge _goge, sai wanki amman injinne yake wankewa, ya Wauraye, ya busar gogewa ne dai nawa, sai in jera a sib, sai kuma girki amman shi ba ko da taushe bane. Babu wanda yasan ina yin wannan aiki, domin yana daga cikin sirrinmu ni da Gwadabe. Matan gida dai suna gutsiri tsomarsu akan fitar da nake yi tun safe, bani zan dawo ba sai azahar, har Gwadabe Yaya Hambali ya tara da zancan dan a tunaninsu gantali nake zuwa kawai. Yaya Haula kuwa cewa tayi bin gidajen ma?ota nake yi yawon tsogumi, dan babu wanda ya kai yarbawa gulma da munafurci a cewarta. Da sallama na shiga madaidaicin gidan. Matar gidan tana ciki, dan na hango ?ofar falon a wangale. Bayan sallama kai tsaye na shiga falon. Tana zaune tana duba wasu kayayyaki da take ta warewa na maza da mata.
"Yauwa Iyabo ashe kin dawo. Kar ki so kiga yanda wanki ya taru mana, kinsan yara da Sata kaya" Dariya nayi cikin girmamawa da Wan risinama wanda kake mutuntawa wanda ya zama Wabi'a mai kyau ga ?abilar yarbawa nace.
Ina kwana Alaja ya yaran?"
"Lafiya lau, an yi biki lafiya dai ko? Yau da Toye akazo bai je makaranta bane?"
Wallahi kuwa bai je ba sai dai zuwa ?arshen wata. Wannan kayan har da su a wankin Alaja?" Na tambaya ina kiciniyar kwashesu tace.
"A'a kayane muka fitar na kwalima, za'a tura ?auye a buhu zaki zura mun su. In akwai wanda kike so sai ki Wiba" Baki na washe nace.
Ahhh
irin na yarbawa"
Alaja nima inaso, bari in tsakura tunda mabu?atan muna da yawa. Amman duk sanda akayi a dinga cira mun. Alaja tace.
"To ki kwashe duka wannan na matan ki bar na mazan, ai ban gama kwaso kayan ba ma" Ba shiri na tsugunna ina ta faWin.
Ahh_Ahhh_Ahh
Alaja na mazan ma inaso in da hali, zan bama mai gidana shima yana da ?arancin suturu' Shiru tayi tana kallona, mamaki na bata ko tausayina taji sai Allah, sai da ta sauke ajjiyar zuchiya tace.
"To ki haWa duka ki kwashe, zan fito da wanda na ware a Wakina sai ki zuba mun a buhu. Akwai takalman maza ?afa biyu a dokin ?ofa ki haWa dasu in zai ma me gidan naki, ni zam shiga ciki."
Ahhh Olorun bukun fun o ebi re ( Allah ya albarkaceki, ya albarkaci iyalinki) Na faWa da yaren yoruba. Na fassara mata da hausa dana tuna bata jin yaren. Da "Ameen_Ameen" ta amsa ta yi shigewarta ciki. Bayan na tattare kayan na shiga aikin share_share ka'in da na'in. Ina yi ina wanki a injin. Bayan na ?al?ale ko ina kuma sai na shiga Wakin yaranta, sai da na goge kayayyakin dana wanke tas kafin na mi?e lokacin anata kiraye_kirayen sallar azahar. Na jera na yaran a sib Winsu, na Alaja kuma na kai mata Wakinta na saka mata a sib. Na gyare mata Wakin tas. Kafin nayi salla kuma. In idar da sallah sai na tsinci kaina da rashin aha'awar komawa gida. Sai na tsiri gugar kayan da Hajiya ta bamu, tunda a wanke suke, sai ?amshin turare mai daWi suke yi. Dana gama wajajen biyu da rabi dai dole na fito daga Wakin yaran ina ri?e da buhun kaya da Toye. Robar da take zuba mun abinci ta mi?o mun, da wata farar roba babba mai murfi tace.
"Miyar ganye ce a cikin robar nan, ta Wan jima a firji ne bazan iya amfani da'ita ba bansan ko kina so ba?" KarSar ledar nayi nace.
Inaso Alaja. Aidupe ( Nagode) Nayi mata sallama muka kama hanyar komawa gida. Ga buhu a kaina, ga leda a hannun hagu, ga Toye ina ri?e dashi, ga uban ciki mai tsini a gaba, ina tafe da ?yar duk jikina ciwo yake yi mun. Da sallama na shiga gidan, tsakar gidan tsit kamar ba gidan hayaniya da shewa ba. Turus na tsaya a daidai tagar Wakina bakina a sake, furucin Laila na ?arshe a waya ne ya daki kunnena.
"Ai in sha Allah na shigo kenan sai dai ta fita ta bar mun Wakin, Gwadabe nawane halak malak" Sai ta saki Dariya. Murya a da?ile nace.
Salamu Alaikum.
Nasa ?afa na shiga, tayi saurin kashe wayar da take yi. Na ?are mata kallo da kyau.
MRS BUKHARI B4B GIDAN ?AMSHI

https://chat.whatsapp.com/Dqaioj0tydVHQGo5zoG0lm


NAMA YA DAHU..
ROMO ?ANYE
BADI'AT IBRAHIM MRS BUKHARI B4B GIDAN ?AMSHI.



Lamba ta biyar (5)





Saye take cikin shuWiyar atampa, ta ci kwalliya da jan baki da hoda, fararen idandunanta rambaWe da kwallin daya sake fito da hasken fatarta. Sai wani ?amshi take yi ita da falon. Ha?i?a na tsorata da Laila da muguwar nifa?ar dake tafe da'ita. Amman in ta san wata ai bata san wata ba. Wanda ya ri?e Allah shi ke da gagarumar riba, nasara tana biye dashi. Dan duk nisan jifa dole ya dawo ?asa. Kallon dana cikata dashi shi ya jefata cikin taraddadin daya kasa Soyuwa a fuskarta. Murmushin dole na sakar mata na yi shigewata Waki, na zauna daSas a kan gado ina sauke numfashi kawai. Tagumi na zuba ina tunani. Na jiyo murya a falo kamar ta Burodami Debisi. Da hanzari na le?o ai kuwa shi Winne a tafe da abubbuwan arziki. A guje Toye yaje ya Wafeshi, shi kuma yayi maza ya rungumeshi tsam a jikinshi. ?agowa yayi ya ?uramun idanunshi, nima shi nake kallo.
Burodami barka da zuwa"
Na faWa tare da ?o?arin kawar da kallon da yake yi mun. Hijabi na zura , ban fito ba sai da na zuba mishi abincin dana dawo dashi daga aiki. Jallof Win taliyace ta ji bushasshen kifi, na zuba ruwa a kofin roba, na Waura a tiran roba, sai na fito. A gabanshi na dire tiran, na sake komawa na zubo ma Laila da Toye abincin bai yi ragowa ba, ga raina ya biya ina fatan Burodami Debisi ya ci ya rage in samu in lasa. Mi?oma Laila abincinta nayi, Toye ma na zaunar dashi a leda ya soma cin nashi.
Ekabo Burodami ( sannu da zuwa Yaya) Ya gida, wa ni Iyawo re bawo ni ebi re? ( Ya Iyaninka) Murmushi yayi mun yace.
Awon ti wani ol atanran. Bawo ni o se wa ( suna lafiya, ya kike?)
Ohh mowa daa_daa ( lafiya ?alau) Ga abinci kaci karya huce. Abincin ya kalla nima ya kalleni, saurin kawar da kaina na yi gefe guda. Murmushi yayi tare da girgiza kanshi.
"Ba zama nazo yi ba. Kuma in naci abinci anan, in na koma gida Emisi ba zata ji daWi ba in nace mata na ?oshi, dan na barota tana ta faman dakan sakwara" Wani yawu ne na jarabar kwaWayin masu juna biyu ya tsinko mun jin an ambaci sakwara, mu?ut na haWiyeshi kawai, dan bani da yanda na'iya.
"Ga TV da dvd, da kafet na kawo miki, na sauya ma Emisi kayan Wakine shine na raba muku tsofaffin. Yanzu haka daga gidan Simbin Maman Kokodeen nake na kai mata labulaye da kujeru" Har ?asa na tsugunna ina ragargazo mishi godiya, dan nayi farin ciki sosai, a cikin gidan ni kaWaice bani da kayan kallo. Wataran matan gidan suna haWuwa a Wakin mutum Waya su harhaWa kuWi a yo renting Win kaset sai dai in jiyo sauti, muna dai da rediyo da muke sauraren labarai, harma wataran in saka kasetin wa?ar yarena, dan Allah yayi ma yarbawa baiwar iya wa?a da son rerata, dan ko karatu zamu yi da wa?e muke yinshi, gamu da son sha'ani a taru taci asha ayi ashobi. Dubu biyu ya zaro ya ajjiyemun mu kai sallama ya fice. Kinkimar komai nayi na shigar Waki, na dawo na Wauki abincin nayi shigewata, Laila na zaune bakan a zaune tayi tsit da halama sa?a take yi da mugun zare a ranta. Da daddare Gwadabe ya kirani mu ka Wan taSa hira ba mai yawa ba dai haka, yai mun albishirin ?ila jibi ko gata ya dawo da izinin Allah. Fatan alkhairi nayi mishi, tare da samun alkhairai.
Washe gari ma kamar jiya ina gama komai na tafi wajen aiki abina. Ina dawowa tun daga bakin zaure na fahimci masu waje sun dawo mai tabarma dole ya naWe, dan muryoyinsu har waje nake jiyosu ana mayar da yanda akayi da yanda za'ayi. Da sallama na shigo amman babu wanda yaji balle su lura da shigowar tawa. Karab a kunnena na jiyo Laila tana faWin.
"Ai ku baku ga irin kallon soyayyar da take ma farkan nata ba. Wai ni zasu ninke baibai. Ya kawo TV da dvd harma da kafet ?ato, ga kuWi fa. Bai tashi zuwa ba sai da ta ga ba idanun Gwadabe" Yaya Haula tace.
"In banda abinki Laila yarbawa ai sun saba iskanci wannan ba wani abu bane. Su da suke zaman wa jo ko, yarinya tana gaban iyayenta saita koma Wakin saurayi, wai da sunan gwajin mahaifa, sai ya Wirka mata ciki zata dawo gidan iyayenta. Kiga anata murna abu yayi kyau zata auru. In kuwa juyace shikenan an shata musulla. To su da suke haka har dan tsohon kwarton Iyabo ya biyota Wakin aurenta wani abunne?" ?irjina take naji yana fat_fat_fat take numfashina na soma jin yana karkatsewa. Ban yi aune ba na jiyo muryar Gude tana cewa.
"A can gidansu ma fa Wakinsu Waya akace, tare suke gwamutsuwa su yi baccinsu, kinsan yarbawa dai sai a hankali basu cika hankali ba. Ni dai na rasa uban abunda Gwadabe ya gani a jikin beyerabiya wacce ?ar uwarshi Bahaushiya bata dashi. Ita ba kyauba, sai gandar baki da kayan Wuwaiwaka Saka_Saka iyakar abinda matansu ke dashi kenan fa" Dariya suka saka dukkansu. Da Suwaiba muka haWa idanu ina tsaye kasa?e ina jin irin sharrikan da ake bina dashi.
"Ahh kin dawo ne Iyaa Toye shine ba ko sallama?" Ta kula ni ne domin ta ankarar da abokan gulmar tata tai musu isharar wanzuwata. Ai kuwa sai su kai kamar ruwa ya cinyesu kawai.
Hmmm e nadawo, ai nayi sallamar hira ce tayi daWi shiyasa baku ji ni ba. Sannunku da hanya." Ina kaiwa nan na yi wucewata zuwa Wakina. A saman kujera na zauna ?irjina na soya mun. Da ?yar na iya sa abinci a bakina, salla ma a daddafe nayi, kawai sai na ji na zama marar lafiya gaske. Sai tubka da warwara nake yi a zuchiyata hakanne ya hana ni sukuni da numfashi me kyau.
Tun dawowar su Yaya Haula daga Takai, al'amuran gidan suka sake jagwalgwale mun. Sabon gulma da tsigudidi aka buWe sabo. Laila kuwa irin ado da kwalliyar da take yi yana firgitani sosai. A tsakar gida suke wuni gulma da shewa, a gabana suke yi ma Laila adda'ar samun damar warce zuchiyar Gwadabe, tana amsa musu da Ameen.
Ranar da Gwadabe ya faWamun zasu shigo Kano da safe ina zaune ina wanki a ?ofar Wakuna, ina Wan wa?e_wa?enmu na yarbawa. Baban Nazifi ya fito daga banWaki, dake banWakin gidan a kusa da Wakinmu lungun yake. Har ya wuce sai ya dawo da buta ri?e a hannunshi.
"Wadannan randunan naki, da gayyar tarkacen robobinki, da wannan kwantenar da kike girki a ciki sun tsushe hanyar wucewa ban Waki. Sabida haka ki tattare komai a wajen ki sam inda zaki ajjiye, irin wannan tarkace suke lalata gida. Yana gama faWar hakan ya wuce yana mita. Sukairaju wanda fitowarshi daga Waki kenan yace.
"Yaya Hambali magana kake yi ne?" Ya tambayeshi. Cikin Waga murya dan in ji yace.
"Da wannan masu kwalo_kwalon nake yi, kasan yarbawa da ?azanta gasu ta tarin shirgi, ca nayi ta kwashe randunanta sun tare hanya." Harisu dake Waki sai ya amsa da cewa.
"Yaya Hambali ai nima fa na jima ina son ince tarkacen lungun su Gwadabe yayi yawa, in zaka je banWaki sai ka ta ture bokatai kafin ka wuce" Kaina na sauke ?asa kawai. Gabaki Waya akan wannan maganar sai da kowa ya tofa albarkacin bakinshi. Ni dai da zafin zuchiya na gama wankina na nufi bakin rijiya zan Webi ruwa. Laraba ?anwar Nazifi ?ar Yaya Haula kenan, tana bakin rijiyar tana Wiban ruwa.
Laraba Wan zuba mun ruwa guga biyu nayi Wauraya bayana ya ri?e" Ai ina rufe Baki Suwaiba ta iso inda muke da bokatanta da bahunanta itama zata Webi ruwa. Da safe duk matan gidan muke ciccika kayayyakin aikinmu, da randunanmu da ruwa. BuWar bakinta tace.
"Harda su kaza acin dan?o. Akanme yarinya uwarta ta sata aiki, zaki dakatar mata da aikin da aka sata kice ta zuba miki? Laraba in kin gama bani gugar" Ina tsaye Laraba ta gama jan ruwanta ta tsab sai ta mi?o ma Suwaiba guga. Ni ko nasa hannu na warce gugar a hannun Laraba. Na zura a rijiya. Suwaiba ta nemi kamani da kokawa a bakin rijiya, ai kuwa na dubeta nace.
In ki kai wasa zan miki hajijiya in jefaki cikin rijiyarnan Allah, ki shiga taitayinki ba fa tsoro nake ji ba, ina dai son mu zauna lafiya ne. Da sauri Suwaiba ta matsa dan ni Win ?atuwace tubarkalla masha Allah, kun dai san matan yarenmu akwai ?iba babu laifi, gani da mazaunai a sama Saka_Saka masha Allah. Nan matan gida su kai mun ca a kaina, kowa na tofa albarkacin bakinshi, Gude har tana zunguremun kaina. Mazajen gidan a lokacin sun fita nema. Ni dai har na gama kab aikina na tsakar gidan, basu dena kwashena iyayena da dangina albarka ba. Ina shinfiWa kafet ina hawaye harna gama shinfiWawa, na saka tv da dvdn a inda ya dace, Wakin sai ya sake sosai. Randunana na kwasosu na saka Waya a bayan ?ofar falo, Wayar a uwar Waki, bokatan na Waurasu akan randar falo, bahunan kuma na Waura a saman randar uwar Waki, na fita na share wajen tas na shigo ciki. Duk fa wannan aikin ina jin ciwon mara da nake kyautata zaton haihuwace. Ina ninkin kaya na ji ciwon na ?aruwa mun, ina jiyo Suruntun Laila a falo. Waya na Waga na kira Uwani Tabalbalin ,da Bose na sanar musu ina na?uda, Bose kuma ta kira gida ta sanar, a cikin ?asa da awa guda sai gasu dukkansu afujajan. Gashi ko reza bamu ajjiye da sunan haihuwarba, ta abinda zamu sa a bakin salati muke yi.
Zaman dirshan nayi a ?asan leda, sai zufa nake yi, ina Wan nishi sama_sama su nai mun sannu. Ana cikin haka sai ga Yaya Mulka matar Burodami kokodeen, babban Wa a gidanmu ta iso.
"Yaya jikin nata Bose? "
"Gashi nan dai tana ta fama, ko dai zamu kaita asibiti ne? ?an biyu ne fa a cikin ina tsoro" Ni da naketsakanin rayuwa ko mutuwa na shiga Waga musu hannu, ina musu nuni da su barni bazan je asibiti ba. Amman da ciwon yai tsanani gashi harna soma galabaita, babu shiri suka Waukeni, Burodami kokodeen ya zo da mota ?ofar gida. Matan gidanmu sai gani su kai an rirru?oni mun fita. Sai faWi suke
"Au na?udarce mu da muke cikin gida bamu sani ba, sai danginki kika kira? Yarbawa munafurci a jininku yake. Wannan ai iskanci da rashin daraja dangin mijine"
Bansan wacece ta yi maganar ba, amman babu wacce ta tanka mata.
Uwani maza je ki rufo mun uwar Wakina. Na ?arashe faWe ina nishi.

Tabalbalin:.
A guje ta shiga gidan, tana shiga Wakin Iyabo taga matan gidan a Wakin cirko_cirko. Turus tayi da ta gansu, suma kansu sun dibibice da ganin Uwani. A zatonsu babu mai dawowa, sun shigo gulmar ganin gyara. Tsaki Uwani tayi ta shige ciki tare da cewa.
"Aikin banza wallahi duk matar dana fito na sameta uwarta zanci danni ba Iyabo bace."
Karo taci da Laila a cikin uwarWakin gaban sib ta Wauko sabuwar atampa tana hannunta.
"Sata ce ta shigo dake Wakin kenan? Iko sai Allah wai na kwance ya faWi. Amman dai su Kulu anyi asara, an yi faWuwar ba?ar tasa, ko kuma ince ?arkon kifi daga ruwa izuwa wuta, ayi dai mu gani in tusa zata hura wuta." Laila kuwa ba bakin magana ai da kunya ??????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????an kama uwar miji na sata a Wakin suruka. Fisge Atampar Uwani tayi. Sum_sum ta fice, Uwani kuma ta rufo ?ofar ta fito ba kowa a falo, tsakar gidanma data fito duk sun yashe. Abundai ba haka akaso ba, wai an yi gulmar uwar miji ta ji. Tana shiga motar suka ja sai asibitin nasarawa."

Asibitin Nasarawa.
Da taimakon Allah, na haifi yarana biyu, mace da namiji da kaina, sai ?ari da akaimun kaWan. Tubarkalla yaran manya kamar ba ?an biyu ba. Sai dai fa ina sauka ma'aikatan kiwon lafiya suka soma tambayar dangina kayan da za'a saka ma jarirai, da abubbuwan da ake bu?ata. Ko allura bamu da'ita. Burodami kokodeen ne ya ba matarshi Antimi Mulka kuWin dukkan abinda ake bu?ata aka kawo babu Sata lokaci. Cikin ?asa da awa guda yarana an kintsasu tsab a cikin seti me ruwan toka, sun yi kyau sosai. ?akin hutu aka dawo dani. Da iyaa Debisi na soma haWa idanu, tayi kicin_kicin da ranta, da gani kasan ta cika ta batse ?iris take jira. Ko ma dama can haka take, kullum a cikin faWa da kumfar baki take.
"O ye koju ti e ( Kinji kunya) Ki duba kin haihu a wula?ance, babu mijinki, babu dangin mijinki, babu kayan jarirai, ba kuWin asibiti, jibi ramarki. Da ace kinji abinda aketa faWa miki daba haka ba, da Wan uwanki kike aure yarenku da kin fi haka daraja, kuma babu mai ?yamatarki, ballema ya tsangwameki." Duk wannan maganar da yare take yi mun. Tana yi tana


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login