Showing 39001 words to 42000 words out of 270738 words

Chapter 14 - NAMA YA DAHU ROMO DANYE COMPLETE TRUE NOVEL BY BADI'AT.doc

Sai dab magriba Burodami Debisi ya shigo hannunshi ri?e da ba?ar leda sha?e da yankakkun kayan marmari ya mi?o mun. Harara matarshi ta watsa mana ta dubemu daga sama har kasa ta buga tsaki. Hannu nasa na amshi ledar nayi godiya ciki_ciki, dan wallahi ko magana akayi mun sai in ji kamar in sa hannu a ka inta kwarmata ihu. Ga mita da Iyaa take ta faman yi da kutuntumama Gwadabe da Babala ashariya. Dan da ?yar Alfa Kulle ya hanata wai ita sai taje ta Webo yara ta dawo dasu. Ni kuma wallahi a wannan lokacin har yaran bana son gani, da duk abinda ya danganci Gwadabe.
Iyaa ce ta shigo tai ta ma Yemisi faWa ita da Burodami ashe saSani suka samu har ta kai da duk ha?urinshi da kau da kanshi sai da ya Waga hannu ya mareta. Ita kuma tana ta?amar soja ce ita shine ta rama, rikicin daya tilasta mata baro gida a daren jiya. Nasiha tayi musu sosai, ya Wauki matarshi suka koma gida.
Fitarsu ke da wuya sai ga uwani da Hajiyarta sun yi sallama idar da sallana kenan ban tashi akan sallayar ba ma, ina jan carbi na amsa sallamarsu.
"Hajiya kune da magriba haka a tafe, lamarin Iyabo ya tasoki ko?"
Cewar iyaa dake gyara zamanta. Hajiya ta kalleni cikin tausayi tace.
"Yanzu sai da aka sako yarinyarnan Toyosi duk irin faWi tashin da tasha, amman dangin mijinnan nata sai da suka Wauketa akan yaranta?, jiya Tabalbalin take faWamun samuwar lafiyar mijin fa."
Baki Iyaa ta taSe tace.
"Ai tsuntsun da yaja ruwa shi ruwa kan duka. Ni Hajiya ina murna da mutuwar aurennan, domin in banda wahala babu abunda take sha a wannan gida. Sai da ta game mishi jinya ta sai da komai nata Wakinta daga robobi sai tukwane fa, shine zai sako mana ita. Ko da yake kiyi ha?uri Hajiya ku Hausawa baku fiye ri?e aure ba"
Gaggaisawa mu ka yi, Uwani ta matso inda nake, su Iyaa ma suna hirarsu ta manya.
"Yanzu a wanne hali shi Gwadaben yake sai Allah. Nayi imani duk inda yake cike yake da tashin hankali babu mamaki in akace yana gadon asibiti ma. Amman Iyabo me yasa kika baro su Toye? Kinsan fa wuya zasu sha ?ila ma a mayar dasu ?auye kinga shikenan an kashe musu rayuwa"
Inata ?o?arin ganin ?walla ta zubo a idanuna amman ina, abu yaci tura, idona ya soye. Sai da na sauke ajjiyar zuchiya nace.
Gara su yi zamansu a dangin mahaifinsu zai fi. Wuya bata kisa Uwani da wuya na kisa mu yaran yarbawa da tun muna ?anana zamu dinga mutuwa, ke kinsan irin gwale_gwalen da muka sha. Gobe asubar fari garin zan bari, kinga in na tafi bazan sake waiwayo garin Kano ba, na barta har abada. Kinga zanyi irin tafiyarnan ai bai dace in tafi da yaran mutane ba. In Gwadabe ya ga yaran a kusa dashi a ?alla zai ji sanyi"
Na ?arashe maganar a raunace. ?irji Uwani ta dafe tace.
"Ni Uwani Tabalbalin ina zaki koma to iyabo?"
Can Adamawa wajen mahaifiyata nake son in je in rayu cikin ?annena, domin in samu kafaWar da zan jingina in yi kuka. Ita kanta Dada akwai wata boyayyar damuwa wacce take cin ruhinta ainun, tun tasowata da wannan ?uncin nake ganinta. Baki ga yanda take ta ramewa ba Uwani" Uwani dai bata so ba, amman babu yanda ta'iya dole haka mu kai sallama.
"Iyabo ni ko duk randa na dawo daga Canada, zan zo Iyaa ta bani adireshinki ko a bangon duniya kike zan ziyarceki. Sannan dan Allah ki kwantar da hankalinki ki rungumi ?addararki da zaran kin samu mane mi kiyi aurenki kema ko Allah zai sa ki samu nitsuwa."
Nagode sosai Allah ya ?addara saduwarmu. Kya dinga le?a yaran in kin samu lokaci."
Na sake magana a raunace.
Basu suka tafi ba sai wajen taran dare su kai mana sallama bayan sunci Amala. Inayin sallar isha na naWe a gado bana son ma Iyaa ta cakaleni da faWa ko hargaginta, fruit Win da Burodami ya kaqo mun shi naci. Wajajen goman dare Alfa Kulle ya kawo mun adireshin rugar da mahaifiyata take da inkiyar shi mijin nata da take aure Mahaifin su BaWWo.
"Tashi ki zauna Iyabo mu tattauna kinga gobe asubar fari ya kamata ki kama hanya dan tafiyarki mai nisan gaske ce. Kece baki sani ba, sanda muka je ?auyannan kina yarinya ?arama"
Mi?ewa nayi daga kwance na zauna kamar yadda ta uwarceni.
"To tunda kin nace sai kin koma hannun mahaifiyarki ai shikenan, bazan hana ki ba. Amman fa...."
Sai tayi shiru akwai abunda take son sanar dani, amman kuma kamar bata son faWe ko nauyi yake yi mata ne ni dai ban sani ba. Sai kawai ta Sige da yi mun nasiha tare da cewa.
"Mijin Uwarki ance jarababbene sosai, dan haka sai ki kula kar ki je ki haWata rigima dashi a wannan gidan yawa, ga kishiyoyi"
Ni dai da Toh" kawai nake amsata harta gama na koma na kwanta. Tsawon wannan dare tunanuka ne barkatai sukaita kai komo a ?wa?walwata da tunanin irin rayuwar da zan fuskanta a rugar da mahaifiyata take, da irin karSar da shi kanshi mijin nata zeyi mini. Gefe Waya kuma tunanin Gwadabe da yaran duk ya addabeni, wayata a can gidan na baro mishi abarshi dan bana son damuwa. Washe gari sassafe na kintsa tsab, Iyaa ta Wan harhaWa mun tsarabar Kano, da ?an canjina. Iyaa Kokodeen kuma ta kawo kuWin mota nera dubu biyar ta ce in ji Burodami kokodeen yace a bani na mota. Matan gida mai ishirin mai hamsin sai aka gagganWa mun, nayi musu sallama. Ina fita sai ga Burodami Debisi a mashin bespa, hawa nayi ya kaini tashar mota inda na samu motar Adamawa, na ci sa'a ma motar zata shiga har ?aramar hukumar GIRAI, daga girai in na sauka sai in kuma hawa motar wata rugar kuma, kafin na sake hawa motar asalin rugar da Dada take Tafiya ce bata wasa ba a gabanmu. Dubu biyar Debisi ya bani tare da mi?o mun wata jakar leda.
Nagode sosai Allah ya bar zumunci. Allah ya ?addara saduwarmu" Idanu ya lumshe yace.
"Ki gaishe mun da Dada sosai. Sai na zo in sha Allah " Sallama mu ka yi ya figi besparshi ya fice. Hanyar da yabi na bi da kallo ni kaina bansan tunanin da nake yi ba. Mu biyu ne rak a motar ni da wata bafulatana mai yara biyu, kuma a seat Win tsakiyar Bus muke, Bus Win babbace sosai mai layi huWu ce zata ci mutum goma sha huWu harda direba. Ga motar ragwargwajajjiya ce soai. Mu dai muna zaune jigum. Ita bafulatana ta kusa dani sai wasa take da yaranta suna yara yaren fullanci. Sai lokacin hawaye ya Salle mun dana tuno da nawa yaran. Shikenan su da hawa jikina kuma ya ?are, haka suma zasu taso ba a hannuna ba, kamarr yadda nima na taso ba'a hannun mahaifiyata ba. Suma haka zan haifo musu ?an uba ko? Kamar yadda Dada ta haifo su BaWWo. Kukane sosai ya ciyoni, dole na saka fuskata tsakankanin cinyoyina na yi mai isata ba tare da Bafulatanar kusa dani ta san halin da nake ciki ba. Shigowar wasu fasinjojinne yasa na share hawayena na Wago. Suma fulaninne amman maza, harda sar?ar fulani mai duwatsu kala kala a wuya da hannunsu, ga gashi sun tara sosai a kawunansu, ga sandunansu da takalmin roba, sai ?osai da biredi suke ci suna korawa da lemun limca na kwalba. Murmushi ne ya suSuce mini kawai. Da Waya da Waya aketa taruwa a cikin motar, kujerar da nake zaune naci sa'a duk mata ne mu huWu a kujerar, dukkansu da gani fulanin usil ne, gasu da yara a hannu ga goyo raSe_raSe, tun kafin motar mu ta tashi suke ta aikin ciye_ciye. Kasancewar sammako duk muka bugo a tashar duk suke takaryawa masu abincin tasha sai ciniki suke zabgawa. Ni ko ko ruwa bana sha'awar sha balle inci abinci, yinwarma da kanta ta hutasshe da tumbina. Sai da rana ta fito ?al kafin motarmu ta cika tab, nan aka shiga binmu muna biyan kuWin mota. Dubu WaWWaya da Wari biyar kuWin motar haka muka bayar, waWanda suke zaune a injin Wari biyar. Motarmu ta fita daga cikin tasha ta hau lafiyayyen titi. In banda haya?i da jijjiga babu abunda motarnan take yi. Ji kake tututu_tuturtu, gashi bata da gudu sam. Kaina na bakin taga ina kallon mutanen dake tafe a ?asa WaiWaiku. Wasu kasuwannin ?auye da gani zasu je ciyo kasuwa, yayinda wasu kuma suka fito neman kuWi, wasu tallace a kansu maza da mata, yara da manya. Tun ina ganin mutane har na soma ganin bishiyoyi. Jama'ar motarmu kuwa sai hirar nishaWi da jin daWi suke yi, yayin da wasu suke gyangyaWi, a yayin wasu suke ciye_ciyensu, wasu kuma suna kame kamar ni haka. Tafiyace mi?a??iya mu kai ta ta faman yinta. Da azahar tayi muka tsaya a wani gidan mai mu kai sallah a masallacin gidan man. Aka firfito kowa na sayen abunda zaici, dan direba yace ba zai sake tsaiwa ba sai mun isa inda zamu sauka. Masu fitsari nayi, masu ba haya nayi. Gurasa da ?uli na siya na ashirin, na sha ruwa a randar masallaci, nayi komawata cikin mota. Kai mun Sata lokaci sosai a wannan gidan mai kafin mu ka kama hanya. Mune har bayan la'asar bamu isa ba, sai yamma sakaliya sai gamu a ?aramar hukumar girei Allah ya iso damu. ?auyan abun sha'awa, fulani makiyaya sunata wucewa da garkunan shanayensu zasu koma gida, shanayen manya lafiyayyu gwanin sha'awa, masu tallar nono mata suma sai wucewa suke da ?oransu a WoWWore a kawunansu. Sakkowa mu ka yi kowa ?afafuwa a kumbure. Matar da muka zauna waje guda na tambaya.
Baiwar Allah a ina zan samu motar Jere Banyo?" Cikin kwaSaSSiyar hausa tace.
"Nima can zani, mu je daga can gaba zamu samu mota sai mu tafi" Ajjiyar zuchiya na sauke, na bi bayanta tiryan_tiryan har zuwa wajen akori kurar dana ga ta cika ta batse da mata da mazan funani. Duk masu tallar nononnan da sukaita wucewa ashe duk can zasu je. Iko sai Allah tafiya mabuWin ilimi kenan. Haka na haye akori kura na biya nera Wari, a cakuWe muke da maza, motar an cika mutane har bana iya sha?ar numfashin kirki, baka jin komai sai warin hammata da ?arnin nono. Ga hanyar babu kyau, haka mu kaita cuccurewa waje guda da mazan da matan. Na sha Wan karen wuya ainun kafin mu isa Jere Banyo. A mugun galabaice na fito, ina mayar da numfashina.
Masu acaSa ne naji suna ta ihun faWin.
"JaSSi lamba zaki je, kuzo mu je" A galabaice na isa gaban acaSar nace.
JaSSi lamba zani, nawa ne?"
"Nera hamsin ne, hau mu je"
Hawa nayi ya ja muka nitsa. Ya Allah birni ma rahamane, kwazazzabo muka dinga shiga, acaSarnan tana sama tana ?asa damu tamkar zamu kifa. ?arafan acaSar na ri?e dam, na runtse idandunana inata karanto adda'a,. Ga ?urar jar bushasshiyar rairayi data cika mun idona da hancina dam. Wallahi na Wauka kafin in sauka daga acaSarnan zamu rikito mu afka wani ?aton ramin, babu kwalta ko guntu. Bani na buWe idona ba har sai da mai acaSa yace.
"Mun iso madakata fa" kana na buWe idanuna a hankali na ganni a tashar ?an acaba. A mugun gajiye na sakko daga acaSar tare da sallamarshi. Jarabawar dana samu duk yaro ko yarinyar da na tambayeta inane gidan Modibbo Yuguda mai nagge. Sai dai su bini dana mujiya basu iya yaren hausa ba, ni kuma ban iya fullanci ba. Ga duhu ya soma doso kai. Wata baiwar Allah ce ta ja hannuna zuwa gidan wani dattijo. Bayan sun yara yaren fullanci mai daWi da garWin saurare sai ya fuskanceni cikin gurSatacciyar hausa yace.
"Gidan Modibbo Yuguda mai nagge kike nema ko yarinya? Dan ?ingel tace iyakar abunda ta gane a bayaninku kenan"
E gidanshi na zo Baba. Ni ?ar wajen matarshi Daso ce, yayar su ?odWo ce daga birnin Kano " Baki ya rike tare da girgiza kanshi, ya dubeni da mamaki maWaukaki yace.
"Kika ce ke ?ar Daso ce kuma daga birnin Kano, to Daso dama tana da wata ?a?" Take naga ya sauya kala daga fara'a zuwa kicin_kicin. Wata dattijuwar fara sol Win bafulatana mai yala yalan gashi ya kirawo ta shiga dani cikin asalin gidan. Bayan yace mun zai tura yanzu a tawo da Dadan. Cikin wata bukka aka shiga dani, sai da na sunkuya sosai kafin na iya shiga cikin bukkar, irin gidajen da suke dashi kenan a rugar . Ban taSa ganin Wakin gargajiya a zahirance ba sai yau, Wakin ya burgeni ya ?ayatar dani. Jeren ?orene kyawawa masu zanen tsuntsaye da masu zanen ?adangare gasu nan iri iri an mammanna su a jikin bangon bukkar. Daga kusurwa biyu kuma wasu ?waryane hawan hawa a jejjere ko wanne anyi mishi murfo da faifal mai kala_kala. ?ayar kusurwar kuma jeren kwallane masu hoton tsuntsaye da korayen ciyayi, ga wasu tukwanen ?asa a kikkife a gefe. Abun al'ajabi baya ?arewa sai gani ga gadon ?asa da katifar yayi. ?asan cikin bukkar kuma buhune aka Winka aka shinfiWa a matsayin ledar tsakar Waki. A gefe na zauna ?uri ga duhu_ duhu a cikin Wakin. Wannan dattijuwar ce ta shigo hannunta rike da fitilar aci bal_bal, akwai wani Wan gini da akayi a saman Wakin kamar anyi gininne musamman domin ajjiye wannan aci bal_bal Win. Bayan ta ajiye sai tace dani.
"Use Silgel ( sannu yarinya)" Sai naga ta fita. Inaso ince zan yi alwala in yi sallah amman bansan me zance ba, dole haka nayi gum. Can bayan duhu ya mamaye sararin samaniya duniya tayi ba?i ?irin sai na jiyo muryar Dada. Murya mai za?i da siranta, muryar dake raunata zuchiyata take kara mun so da tausayin uwata. Cikin bukkar ta shigo da sallama. Tana saye da wata iriyar jemammiyar atampar dana taSa sai mata a shekarun baya. Sai Wan wani yalolon tattararren mayafi mai ruwan ?wai. ?afafuwanta kuwa duk ?ura. Idanu ta ?ura mun ?ur, sai naga guraben idanunta tab da ruwan ?walla.
"Jabu kece a JaSSi lamba a darennan? Kinsan fa kin tambayeni zaki kawo mana ziyara nace miki a'a. To me yasa zaki yi gaban kanki ki zo, ita kuma uwar taki ta barki bacin tasan...."
Sai ta ja bakinta ta tsu?e tare da sauke gwauron numfashi.
"Tawo mu tafi to, kawo jakar in ri?e miki"
Ta kai hannunta zata Wauki jakata nayi wuf na Wauka.
A'a Dada zan Wauka. Kuma kiyi ha?uri dole ce tasa na zo gareki, dole ce tasa Iyaa ta barni nazo, ba a san ranta na tawo ba" Duk fa maganganunnan da yarbanci muke yinshi. Babu dai abinda tace dani sai naga ta sunkuya ta fice. Bayanta nabi muka fita, muna tafe a jere da juna abinda bamu taSa yi ba kenan. Tiryan_tiryan mu kaiya tafiya, muna wuce samari da ?an mata. A yadda na lura kab garin gidajensu iri Waya ne, gidajen bukka zagaye da jinka, basu da dangar gini ko da na laka ne. Wani gida muka shiga ?atoton gaske, mata da yaran gidan nono_nono kowa ya ja zugar abokan hirarshi. Ga aci bal_bal kashi kashi, sai fullanci akeyi ana dariya. Mijin Dada yana zaune akan tabarmar keso da rediyo a gabanshi yana ji, ga abinci da kofi a gabanshi. Sallamar Dada yasa wani yaro namiji da ?ar budurwa suka nufota da sauri suna faWin.
"Use Dada" ( Sannu Dada)
Mijinta ya juyo ya dube ni, ya dubi Dada dana fuskanci tun shigowarmu jikinta yake rawa.
"Je ki gaishe da Babanku gashi can" Ta dubi wannan ?ar berar da tazo ta tareta sai tai mata yare. Shi kuma namijin sai ya amshi jakar hannuna, ita ?ar budurwar kuma tai mun jagora zuwa wajen mijin Dada, gashi ni ban iya Fullanci ba. Haka dai na dur?usa a gabanshi gaisuwar dai ta kurame mu ka yi, sannan muka zo mu ka tarar da Dada tsaye inda muka barta ta nausa a cikin tunani mai?????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????? nauyi, har sai da ?ar rakiyata ta jijjiga hannayenta.
"Dada am"
Tace kafin Dada ta dawo cikin nutsuwarta, bayan ta ja fasali sai ta dubeni tace.
"Mu je in kai ki ki gaisa da abokan zamana" Binta nayi a baya ta nuna musu ni, nai musu gaisuwar kurame biyu a cikinsu suna Wan jin Hausa sai muka gaisa da kyau. Daga cikin ?an mata da yaran gidan ma suna jin Hausa hakan yasa na Wan ji sanyi. Amman bansan me Dada tace dasu a kaina ba ni dai. Zungul_zungul na bi bayanta har cikin bukkar da nake da tabbacin nata Wakun kenan. Babu komai a Wakin sai tarkace kawai, sai gadon ?asa da katifar yayi taji zanin gado. A bakin gadon tace in zauna. Bayan na zauna Dada sai ta fita. Wannan budurwar kuma tana wajen tulu tana Webo mun ruwa a ?o?o, bayan ta bani na sha, sai nace.
"Inason zan shiga bayan gida, banyi sallar la'asarba ?ila isha tayi ma ko?"
"E muma mun yi sallar Isha. Muje in kai ki"
Cikin gurSatacciyar hausar da ba ko wacce nake ganewa ba tayi maganar. Muna fitowa tsakar gidan sai muka tarar da Dada da abokan zamanta a tabarmar da mijinsu yake zaune. Sai faWa yake zubowa yana ambaton Daso_Daso. Jikina tuni ya bani a kaina ake tattauna maganganu, da jin ?arfin muryar kuwa ba magana bace ta daWi. Na sake gasgata hakanne da na ji muryar Dada na rawa, da kuma irin yanda kab yaran gidan su kai ciko_cirko kuma suka ?ura mun idanu kamar maye yaga jariri.
MRS BUKHARI
NAMA YA DAHU....
ROMO ?ANYE
BADI'AT IBRAHIM MRS BUKHARI B4B GIDAN ?AMSHI

Lamba ta sha biyu (12)







Da jan ?afa na bi wannan ?ar budurwar da nake kyautata zaton kanwata ce uwarmu Waya. Wani waje ne aka Wan keSeshi aka zagaye da kara, nuni taimun da hannunta halamar nanne ban Wakin. Ruwa ta zuba mun a buta ta mi?o mun nasa hannu na karSa, tare da shiga ban Wakin. ?asace a ban Wakin , sai Wan gefe guda da akayi daSe inaga a wajen suke wanka, sai ramin shadda a


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login