Showing 18001 words to 21000 words out of 270738 words

Chapter 7 - NAMA YA DAHU ROMO DANYE COMPLETE TRUE NOVEL BY BADI'AT.doc

buga cinya, tana Waga murya tamkar faWa, bil ha??i ita ba faWa take yi ba maganarta ce haka, ko kuma ince mafi akasarin yarenmu suna da ?arfin murya, da ihu a cikin magana. Ni dai bani da bakin cewa, dan nasan Gwadabe na ?o?ari sosai, banso zuwa asibitin ba sabida gujema tashin hankali da tarzoma irin wacce ta afku lokacin haihuwar Toye, an yi Wauki babu daWi sosai. Dan ranar suna anci dambe an gode Allah. Burodami kokodeen ne ya katse Iyaa Debisi ta hanyar cewa.
"Yarinyar nan Iyaa Debisi ya kamata a barta haka, ko dan rabon dake tsakani, ni ina ganin dukan yayi mata yawa" Mi?ewa tayi tsaye, ta tafa hannu tace.
"Ahhhh Ahhhh kokodeen Oya were ( baka da hankali)" Nan fa ta sake shiga wani babin, ta inda ta shiga ba tanan take fita ba. Shigo da yaran da ma'aikatan kiwon lafiya suka yi ne yasa ta yi shiru. ?akin kuwa Hausawa sai kallonmu suke yi. Iyaa Debisi take ta soma rera wa?a tana rawa na murnar zuwan jikokinta. Suma su Burodami kokodeen nan suka soma rawa suna mata tafi. Tana rera wa?ar yarenmu ta musamman da akema ?an biyu.
Gabaki Waya Wakin hankalinsu yana kanmu. Murmushi kawai nayi musu, Uwani kuwa sai zolayar Iyaa Debisi take yi dama sun saba. Taiwo Iyaa Debisi ta ri?e, Burodami kokodeen kuma ya karSi Kahinde. Sai murna suke yi, domun a ?abilarmu babban abune haihuwar ?an biyu, mun Waukesu a matsayin wata babbar baiwa da Allah ya bamu. Kuma yarenmu su kansa ya?inin rayuwar ?an biyunnan mai albarka ce. Ni dai a haka baccin gajiya ya kwasheni, bani na farka ba sai jefin la'asar. ?an uwana sun cika asibiti dan?am sai tayani murna suke yi. Ga abinci iri_iri an kakkawomun. Burodami Debisi ya zubo mun amala da miyar ewodu, da miyar wake, da jar miya dukka, ga ganda haka_haka.
"Ga abinci kici ko zaki samu ?warin jikin naki, gida zamu tafi" KarSa nayi na mishi godiya. ?an uwa kuma aka shiga yi mun ya jiki, tare da murnar zuwan Taiwo da Kahinde duniya. ( Hassana da Usaini ) Amalata naci nayi ?at na kora da kunun akamu me zafi, take naji na yi gyatsa mai ?arfi, bana jin komai garau nake jina tamkar ba ni bace na haifi ?an biyu ba. Wajajen shidan yamma aka sallamemu muka fito asibiti mota biyu. Duk tare muka Wunguma mazanmu da matanmu zuwa gida. A tsakar gidan muka tarar da matan gidan kamar dai kullum ana zaman gulma da kace_nace.
"Ahh ?an biyu aka samu kenan? Kai masha Allah barka da arziki Iyabo." Cewar Yaya Haula.
Yauwa sannunku" Iyakar abinda nace kenan. A ?an uwana kuwa babu wacce ta kulasu, suma basu kula kowa ba, mu kai shigewarmu ciki. Mazan a falo suka zauna, mu kuma muka shige cikin uwar Wakin. Anty Mulka tace.
"Abun girkin ki na ganshi a falo. Anan zan dafa miki ruwan wankan ne, ko zan iya fita ?addararren tsakar gidan naku?" Sai da na ja numfashi nace.
Zaki iya fita dashi ki sa ta gefen Wakina, kafin Gwadabe ya zo ya kawo itace" Sai lokacin Bose tace.
"To wai shi gogan bai san kin haihu bane?" Kafin in yi magana Uwani tace.
"Na kirashi na sanar dashi. Yana hanyar dawowa daga legos ne, da ?yar ma na samu wayar tashi ba sabis. Amman yace abokinshi Bara'u zai tawo daga ?auye, duk abinda ake bu?ata zai yi kafin shi ya iso, dan yace mun zasu iya kaiwa ma Wayan dare basu shigoba, wata ?ila sai Asuba ma zasu shigo kanon." Tsaki Iyaa Debisi tayi tace.
" Isokuso asan. ( Banza marar amfani)"
Ha?i?a naji zafi ainun, kuma maganar ta dokeni, ai ko banza Gwadabe uban ?a?anane." Anty Mulka ta fita bakinta a taSe. Bose ta fita da zanin jini da muka dawo dashi daga asibiti, Uwani kuma ta ci gaba da mun gyaran Waki, sauran ?an uwa kuma suka fita falo wajen su Burodami.
Zuga su Yaya Haula su ka yi, suka shigo da sallamarsu, Iyaa Debisi ce ta basu izinin shigowa. Suna shigowa ta mi?e ta koma falo"
"Iko sai Allah, Iyabo dama kunsan ?an biyu ne a cikin naki, ko kuwa sai da kika haihu tukunna?" Cewar Gude uwar son jin ?a?a aka haifi mutum.
A'a dama tun cikin ma yana wata huWu da akayi mun sikainin akace ?an biyu ne. Kun gansu mace da namiji. Taiwo da Kahinde kenan" Yaya Haula tace.
"Au suma sunan yarbawan za'a li?a musu, babu ko karar a saka sunan Mahaifin shi Gwadaben, ita kuma macen asa sunan Babala, sai wani Taiwo da Kahinde?" Uwani ce ta juyo tace.
"Ba tana nufin sunan yarbawa za'a saka musu ba. Taiwo da kahinden yana nufin Hassana da Usaini kamar yadda muke cewa a Yaren Hausa. Tunda ai kunsan ba ko waWanne ?an biyu bane ake sake musu suna ba, ko a cikin hausawa "
"To wannan ko dole a sake musu wallahi. Kun mayar da Gwadabe sai kace sususu kawai" Cewar Yaya Haula wacce da gani ta fusata. Uwani ba kanwar lasa bace na santa sarai shi yasa na katse zancan dan gudun kar su kira mun ruwa, dan ?yas su Bose suka ji wata hayaniya zasu shigo ayi Satacciya, dan kowa cike yake da haushin kowa, sai kace ba Allah Waya muke bautama ba.
Ya'isa haka Uwani dan Allah. Yaya Haula Gwadabe na da ikon ya zaSama jininshi duk sunan da yake da bu?ata. Ni bani da ikon sashi yayi abinda baya so. Ko Toye ma shi ya zaSi ya saka domin yai na mahaifina Allah ya ji?an rai takwara"
"Tunda ya kasa yi ma nashi Allah ya ji ?an ran takwaraba. Ai baki zo kin ganshi da mahaifinshi a raye ba. Dama yarbawa akuyarku ai tayi kuka wajen juya miji da jarabar bin baba lawo" Ta sake faWa da karfi . Na riga da nasan tarzoma take son tayarmun, ayi rikici su sake kafa hujja akan jarabar yarbawa, da ?in zaman lafiya. Haka dai suka fice a Wakin bayan sun yi mun barka. Ni dai ban basu yaranba, dan a al'adarmu bama ba da yaro jariri ga mutane aita jagwalgwalashi. Suma sun sani tun a haihuwar Toye, kuma sun yi rantsuwar ko yara Wari zan haifa ba wacce zata sake yin?urin Waukar jaririn. Cikin ikon Allah a ?an uwana babu wanda yaji kace_nace Win data faru, bayan fitarsu Uwani tace.
"Iyabo sai fa kin yi da gaske dangin Gwadabe zasu iya barinki kici gaba da rayuwa a gidannan, wannan ?iyayyar ta yi yawa. Wallahi ko ahalul kitabi ce ke ya kamata su sarara miki haka. Duk da su kansu Iyaa Debisi sun?i su zubar da makaman ya?insu. Amman Wazu fa kinsan ina dawowa rufe miki ?ofa da kikace. Su Haula suna falonki suna kallon Wakin. Ita kuwa ba?ar kadararcan a Uwar Wakin ki muka ci karo tana miki bincike a sib, har ta Wakko wata atampa mai ruwan malmo, kai gaskiya kina cikin wani yanayi." Shigowar Sakina ne ya katse mana hirar.
Ah Sakina kune a tafe da yamma sakaliya haka? Maraba" Na faWa ina dariya. Uwani tace.
"Kaga uwar gida, kuma Amarya a gidan Bara'u, Sakina lale." Cewar Uwani.
"Lale Uwani, ashe Iyabo uwar biyu an samu kai. Sannu fa mai jego. Bara'u yana falo yace a kawo mishi yarin zai musu huWuba." Mi?ewa nayi na saka mayafi, Sakina ta ri?e Taiwo ni kuma ina ri?e da Kahinde muka fito falon. Bara'u yana kujera shi kaWai, babu kowa a falon, duk yanda akayi su Burodami kokodeen sun tafi gida ne, ko sun je su dawo. Sakina ta mi?a ma Bara'u Taiwo.
Ina wuni Bara'u. Da wannan yammar Gwadabe ya taso ku?"
"Haba dai ai Gwadabe ya wuci haka a wajena. Kuma dama muna shirin shigowa cikin garin jikin Babala ya?i yanzu haka tana asibitin Murtala. Yaya Hambali da Sukairaju suna wajenta, amman ?ila ba gado za'a bata ba dai."
Allah sarki, ai ban sani ba. Zan shirya in je zuwa bayan magriba in dai basu dawo ba." Sai Sakina tace.
"Ke da kike fama da kan ki kuma?" Bara'u daya fita sanin dawar garin yace.
"A'a in dai akayi magriba sai ki rakata ta je ta dubo jikin ai dai ba za'ace bata nuna kulawarta ba ko ba gaskiya ba" HuWuba yayi ma yaran da suna Hassana da usaini kamar yadda yace Gwadabe ya bashi umarni.
"To yara na yi musu huWuba da asalin sunayen da ?an biyu suke zuwa dashi, wato Hassana da Usaini. Taiwo da Kahinde a yarenku kenan. Sabida haka a Sangarenmu Hassana da Usaini suke. A naku Sangaren kuma Taiwo da Kahinde Allah ya raya su da imani" Mi?o mun yaran yayi na amshi Waya Sakina ta amshi Waya muka shiga ciki.
"Me za'a Waura na dare ne Iyabo magriba ta kawo kai ma?" Cewar Uwani kafin in bata amsa Iyaa Debisi ta shigo da ruwa a bawo na wankan yara ta dasa kujera.
"Fun mi ni omo ( Bani yaron) Ta furta ranta a mugun haWe. A sanyaye na mi?a mata ina fatan kar a kuma samun matsala makamanciyar ta haihuwar Toye.
Uwani ai inaga ba sai an yi girki ba, ga Amala a kuka da faten wake, ai ya ishemu, gobe a Waura girkin."
Nabata amsarta. Anty Mulka ce ta le?o tace dani in je in yi wanka ta kai mun ruwan. Wanka nayi na gargasa jikina sosai na ji daWi. Ina fitowa Su Anty Mulka suna shirin tafiya gida Burodami kokodeen yazo zai kaisu gida. Godiya nayi musu sosai, mu kai sallama suka fita ni kuma na koma ciki. Anan naga kayan abincin da su Sakina suka kawo mana, garin tuwon masara, kuka daddawa, busassun kayan miya, albasa, shinkafar hausa, da gyaWar miya harma da man ?uli jarka guda, da bushasshen kifi" Godiya nayi sosai gami da yaba ?wazon Bara'u, ya kuma yi dace da macen da bata hanashi yin aikhairin sai ma taimakonshi da ?ara ?arfafashi da take yi."

MRS BUKHARI
https://chat.whatsapp.com/Dqaioj0tydVHQGo5zoG0lm




NAMA YA DAHU...
ROMO ?ANYE.
GAWURTATTU UKU

BADI'AT IBRAHIM MRS BUKHARI B4B GIDAN ?AMSHI

Lamba ta shida


Shiryawa nayi cikin doguwar rigar Atampa, Waya daga cikin kayan da Alaja ta bani, atampar mai kyauce kuma tana da tsada da gani. Hijabi mai roba_roba na saka kalar atamfar sak. Na Wauki Taiwo na goya, Kahinde kuma Sakina ta goya shi.
Uwani zamu je asibitin Murtala Babala tana can bata da lafiya gara in je kar in yi wani babban laifin.
"To sai kun dawo, nima ?o?ari nake in gama gyare miki uwar Wakin yadda ya kamata. Gobe za'a zazzo da yawa. A nan ma ni zan kwana gobe na koma gida Hafizu baya nan ya tafi Lahadin makoli mahaifinshi bashi da lafiya. Yaran kuma suna gidanmu " nace da'ita.
To Shikenan ma, sai mun dawo to. Sakina muje." Shigarmu ward Win mata ke da wuya na hangi su Yaya Haula dukkansu a zazzaune a tabarma da mazajen nasu. Kallona suka shiga yi da suka hangoni.
Sannunku Yaya Haula ya mai jikin?" Sai da ta taSe bakinta tace.
"Jiki da sau?i" Gaishe da su Sukairaju nayi tare da yi musu ya mai jikin. Yaya Harisu cikin murtukewa yace.
"Da'u ka kai su wajen Babala su gaisheta" Da'u yayi gaba muka bi bayanshi har bakin gadon Babala, tana zaune ta jingina bayanta da matashin filo. Yaya Halima kuma tana tsaye tana haWa mata tea. Muna isowa Babala ta kawar da kanta gefe.
Sannu da jiki Babala, ya ?arfin jikin? Na furta muryata har tana rawa.
"Da sau?i"
Ta bani amsa ciki_ciki. Yaya Halima kuwa nunawa tayi bata ma san Allah yayi ruwan tsaron mu ba. Gaisheta nayi tare da yi mata ya mai jiki. Babu yabo babu fallasa dai ta amsa mun. Da Sakina ne dai su kai fara'a. Sunto Taiwo nayi na mi?a ma Babala ita, tasa hannu ta amsheta, Sakina ta ?ara matsa da Kahinde.
"Ba shakka gashi nan yara sun Webo ?o?on asali. Kamanninsu sak da dangin uwarsu dai kamar yadda Toye yabi sunanshi." Iyakar abinda tace kenan ta mi?o yaran. Raina ya sosu ainun ko Allah ya rayasu bata ce ba, balle ta yi musu adda'a a matsayinta na kakarsu. Yaya Halima kuwa ko kallo yaran basu isheta ba. Bayan na gama goyo ne ta kalleni sak tace.
"Na ji sa?onki na gode da har kike tunanin mahaifinki ya fi mahaifin Gwadabe daraja a wajenshi. Burinki ya cika yaranki uku babu wanda Gwadabe yayi ma takwara a danginshi. Har ni da na Wau jimirin renon cikinshi na wata goma ya kasa saka sunana ma ?arshi. Taiwo da Kahinde Win dai da kika sanar, shima shi ya jaddada a matsayin sunan yaranshi. Ko da yake dama tuni kun gama tsarin komai tun ma yaran suna ciki." Baki na buWe inason in ba Babala ha?uri amman sai Waga mun hannu tayi.
"Kije kawai, bana son ganinki, bana kuma ?aunar zamanki da Gwadabe, zuchiyata ba zata taSa samun salama ba madamar kina amsa sunan matar Gwadabe abadan" Cikin razani da tashin hankali mai girma na shiga. Lokaci guda Gwadabe da aurenshi ya fice mun a raina kwata_kwata. Na yi alkawarin inayon arba'in zan tursasama Gwadabe sakina ko dan ya ga haske a rayuwarshi, domin na fahimci har abada Babala ba zata taSa ?aunata ni da abinda na haifa ba, wannan shi ake kira NAMA YA DAHU ROMO ?ANYE. Ko Gwadabe bai sake ni ba, ni kuma zan fice a rayuwarshi.Wata wawuyar ajjiyar zuchiya na sauke a hankali na soma tafiya dan barin Wakin. In sha Allah ?arshen aurena da Gwadabe yazo, ko da kuwa soyayyarshi ita zata zam silar numfashina. Fitowa daga Wakin ke da wuya, na jiyo Harisu yana zagina tare da ?orafi kan sunayen yara da aka saka. Sai ji nayi na muzanta ko fita ma bazan iyaba. A tsaye Sakina ta iskeni.
"Ki ?ara ha?uri dai Iyabo damo sarkin ha?uri. Mu je kinji" Da taimakon Sakina na iya fitowa, amman har muka isa guda ban iya furta ko kalmar A ba, sai ajjiyar zuchiya kawai nake saukewa. In sa abinci a cikina wallahi na kasa sabida tsabar damuwa. Sakina da Uwani sai aukin rarrashina suke yi, amman na kasa ce musu komai. Ni tunanina ya na ga samarwa Gwadabe sau?i dan fishin iyaye masifa ne, nayi imani fishin da Babala take kwana ta tashi dashi akan Gwadabe shi ya hana shi yin arziki. Kullum cikin faWi tashi yake, ta hana kowa ya taimaka mishi. Yaya Hambali shago gareshi babba a kasuwa da yake siyar da dabino da gyaWa, buhu_buhu yake siyarwa yana da yaran shago sosai. Amman Babala ta hana shi ya Wauki Gwadabe ko da a matsayin yaron shago. Yaya Harisu shi kuma mota yake ja zuwa ?auyuka a haka ya sai wasu motocin guda biyu ya bayar anayi mishi hayarsu. Sukairaju kifi bushasshe yake saidawa a kasuwa, shine zuwa argungi, shine zuwa maiduguri, da Yawuri saro katan katan na kifi, kuWi yake samu sosai da sosai ?an fodiyo kuma Kafinta ne kuma ogan kanshi ne. Da'u shi kuma Yaya Hambali ne ya buWe mishi shagon sai da kayan masarufi dangin shinkafar hausa, gyadar miya, masara, wake. Duk wannan matakan sun haushine da taimakon Allah da taimako da jajircewar Yaya Hambali, domin Yaya Hambali guda ne harda Sari ga ?an uwanshi, yana musu tsananin so.
Ina lokaci yayi da zan fita fit a cikin wannan ahalin, nima in je in yi rayuwa mai kyau. In ba haka ba bala'o'e iri_iri zasu iya saukar mana a sakamakon fishin da Babala take yi da Gwadabe. Abubbuwa nawa Gwadabe ya kama suka lalace, yayi sana'o'e a ?alla iri huWu karen mota shine na biyar. Amma tafiyar bata wani nisa sai abun ya lalace, ko mai gidanshi ya koreshi, ko a yi mai wani ?azafi, ko na sata ko na ?ashin tsiya."
"Iyabo ga tea ki daure ki sha, wala Allah ruwan nono yazo miki. Kinga Taiwo da Kahinde kuka suke yi baki ma sani ba. Kar ki kuskura waccan munafukar ta falo ta fahimci kina cikin matsala, yanzu ta shigo. Surukar taki ma an sallamota tana Wakin umman Nazifi." Hannu nasa na amshi tean hannun Uwani na sha, dan jikina har rawa yake yi tsabaragen yinwar da nake ji. Sakina ta mi?o mun Taiwo da take ta canyara ihu kamar wacce ake zare ma rai.
Ga man zaitun da audiga Sakina bani in goge kan mamana in gwada musu ko zasu jawo ruwan yazo" Mi?omun Sakina tayi, na bi kan mamana na goge da man zaitun tas na ba yaran suka soma ja. Cikin ?udurar Allah sai ruwan nono ya soma zuwa. Nan kuka ya?are aka shiga tsotseni. A wannan daren bana ce na yi bacci mai kyau ba. Misalin ukun dare sai ga Gwadabe, a lokacin duk su Uwani suna kan gado sun yi bacci ya shigo. Ganinsu ne yasa ya koma falo, ni kuma na Webo jariran na biyo bayanshi, yana zaune a kan kujera. Laila kuma tana kwance tana bacci ta yi baje_baje cinyoyinta duk a waje. Mi?a mishi yaranshi nayi yasa hannu ya amshesu yana fara'a.
"Maman biyu barka da sauka, ina fatan babu inda yake miki ciwo ko?"
Babu, sannu da dawowa" Iyakar abunda na faWa kenan shima ciki_ciki. Idanunshi yana kan yaranshi yace.
"Ya dai akwai wani abu dake damunki ne, ko an yi wani abunne? Iyabo a yanzu ya kamata ace kin saba da komai. Ki toshe kunnuwanki dan abubbuwa da yawa zasu faru kafin ayi suna kema kuma kin sani. Yanzu haka nafi awa Waya da shigowa Babala naketa ba ha?uri tayi fishi wai ban mata takwaraba ita da mahaifinmu. Nace mata zan sake yin sabuwar huWuba in hakan zai bata farin ciki. Amman ta?i fur tace mun in na sake ma yaran suna bata yafe ba, wallahi kar kiji......." ?an yatsana nasa a kan laSSana nayi mishi halama da yayi shiru, nuni nayi mishi da Laila dake kwance. Ai ba shiri ya haWeye maganarshi. Mu ka Wan taSa hirarmu kaWan, ya mi?o mun ledoji manya biyu, mu kai sallama dashi zai kwana a Wakin zaure, Wakin su Nazifi, Bara'u ma yana Wakin. Da tunane_tunane na ?arashe daren nawa, sai jefin asuba bacci mai nauyi sosai ya Webeni bani na farka ba sai taran safe lokacin ?an uwana sun ?araso, har an yima ?an biyu wanka sun fito ras dasu, dan Gwadabe ya kawo kayan jariri kala biyar biyar, sai nawa na


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login