Showing 75001 words to 78000 words out of 270738 words

Chapter 26 - NAMA YA DAHU ROMO DANYE COMPLETE TRUE NOVEL BY BADI'AT.doc

nauyin Fhatsima suka kama malam. Cikin dibibicewar data mugun ?ular da Amaryar Malam yace.
"Uwar gida sarautar mata, farar mace alkyabbar mata, zo ki zauna Fatsima" ?an siririn Soyayyen tsakin da a iya kunnen Baba Fhatsima ya sauka Amaryar Malam tayi. Kujerar gabaki Waya ta sauka ta barma malam da Baba Fhatsima, ta koma kujera mai cin mutum guda ta kumbura tai suntum. Murmushin takaici Baba Fhatsima tayi, a zuchiyarta tace.
"In banda maza da faWuwar girma ni Fatsima da yaushe zan haWa gado da yarinya ?ar cikina? Amman su maza basa ko jin kunya, da nauyin manyan yaransu. Wacce iriyar taSarace Malam bai yi ba lokacin da ludayin Amaryarshi ke kan dawo? Murmushi ta kuma yi mai cike da fassarori da dama.
"amarya ina ganin sai kin tashi kin kirawo mun Asshi, da Suwaiba Lokaci yana ?urewa ya kamata ace sun hallara" Ba dan ranta yaso ba ta fita ta bar Malam daga shi sai Baba Fhatsima ba. Tana fita Malam ya dubeta yace.
"Fatsima bakya tsufa ke dai. Wazai ga Tasi'u yace ke kika haifeshi?"
"Hmm Malam Baka rabo da daWin baki, koma kince borin kunya" Da Malam da ita da tai maganar suka kwashe da Dariya. Shi yana dariyar yanda akayi ta Wagoshi. Ita tana mai dariyar kaji kunya. A haka matan Malam suka shigo suka iskesu.
"Au aini naga kamar Amaryar Malam itace da girki ko? In ba Satan lissafi nayi ba. Ta faWa tana kallon Amaryar Malam data cika tana shirin fashewa. Suwaiba ta taSe bakinta tace.
"Girkinta ne, kin mance ita ta wuni tana hidimar yara?" Malam ne ya dakatar dasu ta hanyar cewa.
"Yanzu zaku zauna kuji dalilin kiranne ko kuwa zaku tsaya bin ?ididdigar waye me kwana waye marar kwana ne. Wai shin me yasa ke Asshi baki da aikin daya shige na ta da tarzoma ko da yaushe?" Zama ko wacce tayi a kujera. Amaryar Malam ta je ta zauna a kusa daf da Malam. Bai dai ce da'ita uffan ba. Takaddu dunkulallu ya ciro daga aljihun rigarshi ya zube a ?asa.
"Ko wacce ta Wauki Waya ta ri?e a hannunta kafin in gama bayani sai ku buWe. Sai da kowacce cikinsu ta Wauka sannan Baba Fhatsima ta Wauka a ?arshe. Malam yace.
"To wannan ?uri'ace nayi muku kamar dai yadda nake yi a ko wacce tafiya in ta taso mun. Kuma tunda nake yin wannan ?uri'ar duk wacce ta Wauki tafiya bana sakewa da'ita nake tafiya. To a wannan karonma wata tafiyace ta taso babba a gabana ta banbanta da duk tafiye_tafiyen dana saba yi a baya. Naba ko wacce dama ta buWe takaddarta duk wacce ta Wauki tafiya to Allah ya ciyar da'ita. Sannan ku sani babu zalunci ko son kai a cikin wannan lamarin Allah shine shaidata. Bismillah ko wacce ta buWe.
Nan da nan ko wacce ta shiga kiciniyar buWe takaddarta tare da zabarin ganin ta Wauki tafiya
Domin tafiya da malam ana samu alkhairi sosai, kuma macce tana samun lokacin kanta dana mijin nata, soyayya ake darza tsantsa. Cikin sa'a Baba Fhatsima ta samu tafiya. Har cikin ?asan ranta tayi farin ciki sosai, dan ta jima sosai rabon da ta samu damar tafiya tare da Malam. Kuma a halin yanzu tana cikin yarda dashi. Baba Asshi tafiyar da yayi na ?arshe wacce ba'ayi wata ba sai yanzu, tare da'ita akaje. Amaryar Malam kuwa sai da ta samu takaddar tafiya sau huWu a jere ras, Suwaiba ta samu sau biyu a tare. Wannan karon kuma Allah ya ciyar da Baba Fhatsima.
"Malam nice na samu tafiya" Bai san sanda murmushi ya subce mishi, farin ciki ya bayyana s fuskarshi ba. Malam har tsaiwar dare yayi kan Allah ya dafa mishi Baba Fhatsima ta samu wannan takadda ta aminci. Kawar da kai Baba Asshi tayi gefe, tare da taSe bakinta. Malam kuwa yace.
"Masha Allah dama kina da paspo ta kwana gidan sau?i sabida haka ki soma shirin keta hazo" murmushi Baba Fhatsima tayi mai cike da dan?ararriyar soyayyar Malam da take ta farfaWowa.
"Allah ya nuna mana lokacin malam. In ka bani dama sai in koma Sarayina" Kai ya gyaWa.
"Ki isa cikin aminci Fatsima uwar gida ran gida" Ai fitar Baba Fhatsima sai tarzoma ta tashi, daga ?arshe dai fatattakarsu Malam yayi. Amaryar Malam dake da kwana itama ta bisu tana kuka wai ta yafe kwanan ma baki Waya.
A wannan daren zukata da yawa a cikin tunani suka kwana, ko wanne da abunda yake tubkewa da warwarewa haka garin ya waye kamar yadda aka saba.

Gwadabe:.
Tun asuba yake kiran wayar Shafa amman wayar har zuwa lokacin a rufe take. Gashi yana son zuwa ganin Hadiza yaga ya ta kwana. Duk da Auwala ya kwantar mishi da hankali a daren jiya.
Tashi yayi jiki a saSule ya nufi cikin gidan. Yau matan Malam babu wanda ya amsa gaisuwar su Auwala ma balle kuma Gwadabe wanda yazo dandalar arziki. Sai Baba Fhatsima ce dake zaune a dokin ?ofa tana siyan lalle da gishirin lalle akan wata yarinya tace.
"Gwadabe yau makara kayi ne sai yanzu ka samu shigowa?" Da biyayya ya zube ya gaisheta, ta amsa cike da fara'a.
"Ka shiga Hadiza na ciki, da zazzaSi ta kwana, likita ma Matar wanku zata kaita" Kai ya kuma saukewa harda sosa kanshi.
"Subhanallaah Allah ya bata lafiya, bari in dubata" Ya faWa da kunya. Shiga yayi ya samu Hadiza a zaune tana shan kunu. ?urama juna idanu su kayi na da?i?u. Ita ta rigashi sauke ido.
"Ina kwana Yaya Gwadabe?" Bai samu damar amsawa ba, waje ya samu ya zauna a ?asa ?ur idanshi a kanta.
"Ina ro?on Allah yasa ba maganata ta jiya bace sanadiyyar ciwonnan naki ba Hadiza?" Bai jira ta amsa shi ba dan bai tambayeta yana nufin saita amsaba ya Waura da faWin.
"Wallahi ba dan Baba magaji ya tozartaki ko ya ?as?antar da darajarki bane yasa yai miki zaSin Gwadabe ba. Nima ba dan tayin da yaimun bane yasa na amsheki ba face kin yi mun kuma naji zan iya rayuwar aure dake. Yanayinki da zubinki yana mun kama da na matata Iyabo sosai. Ki fahimceni auren zumunci cike yake da tarin hikimomi.
Itama fa bawai ina nufin bana sonta bane A'a itama inai mata kalar nata son daban. Hatta tsohuwar matata gurbinta shine a ?asan zuchiyata. Ki kwantar da hankalinki kinji?" Tunda ya soma magana zuchiyarta ke lugude. Musamman da taji matsayin da Iyabo ta wawashe a rayuwar Gwadabe.


Sai Allah ya sadamu ranar Monday da izinin Allah danjin yadda zata kaya.
Ki faWi abinda kika Wauka na darasi a wannan labarin duk da bamu yi nisa ba.
https://chat.whatsapp.com/Dqaioj0tydVHQGo5zoG0lm






NAMA YA DAHU..
ROMO ?ANYE
BOOK 2

5


*Ina kuke mata ?an ?walisa irin Shanono? Ku firfito ga Uom Taufiq veils bead work and Abaya stone work gliter veils lafaya. Ta zo muku da haWaWWun aikin beat na hannu domin kwalliyarku da fito daku ku yi tsab.*
*Aikinta babu ha'inci ni na tabbatar. Nima Badiat Ibrahim zan bata aikin lafayata ta zuba mun aikin beat work kuzo muje tare ta gwangwajemu*


_Assalamu Alaikum barkanmu da juma'a. Iyabo tana godiya a bisa karSar labarinta da kukayi hannu bibbiyu_





Lokaci Waya taji kishin Iyabo ya soki murfin zuchiyarta fiye da kishin wacce za a haWasu zaman kishin na gasken_gasken.
Bata sami zarafin furta mishi kalma ba Auwala da Anty Badi'a suka shigo a tare.
"Hadiza in kin shirya muje Yayanku ya rage mana hanya ko?."
" to"
Ta furta tana kallon Gwadabe, wani irin kallo daya kasa fahimtar fassararshi.
A kunyace ya gaishe da Anty Badi'a, ta amsa cike da kulawa.
"Gwadabe maza muje Mammada na jiranmu kasan fa yau muna da aiki." Cewar Auwala kenan. Kafin ma ya mi?e Malam Magaji ya iso dokin kofar yana faWin.
"Yarannan har yanzu basu wuce aikin ba, Auwala me kuke yi a ?unshe a ?urya haka?" Da sauri suka fito, sumi_sumi sukai ma iyayen sallama suka fice a gidan. Cikin sa'a Gwadabe ya gwada sake kiran layin Shafa ya samu a buWe. Sai dai harta gama kuka ta tsinke ba a Waga ba. Yana sauke wayar a kunnenshi sai ga kiran Tamu ya shigo.
"Abokina yau kaine da kira sassafe haka, ya kwanan iyalin kuma?' Cewar Gwadabe daya tari numfashin abokin nashi ta hanyar rigashi magana. Ajjiyar zuchiya ya sauke yace.
"Tun jiya Ayashe ta sanar dani Shafa nata faman kuka ta kulle kanta a Waki. Ko da aka wayi safiyar yau ta?i cin abinci, ta?i zuwa wajen aiki. Shine nasa ita Ayashe tai kiranta dan inji menene. To ta dai ?i yin magana ma, bansan ko kana da masaniya akan kukan ba, kasan yarannan fa da zafafawa akan soyayya, dan naga ta Wauki lamarinka da girma. Kasan mata da surutu ina jin labaranka sosai ta bakin Ayashe" Jim Gwadabe yayi kawai yana mamakin halin da Shafa da Hadiza suka shiga a kanshi, ya Wan shafo Wan siririn hancinshi tare da shiga zancan zuchi.
"Ohh ni Gwadabe ni ba kyau mai suna kyau ba, ni ba tsayi ba, ga tumbi, ga ?aton kai. Amman akaina waWannan matan suke shiga damuwa haka? Dama_dama Iyabo na cancanci ta soni, duba da yanda tasha naci a wajena, da irin yanda na jajirce kan soyayyarta. Amman waWannan haWani dasu dukka akayi, bawai ni nace ina sonsu ba."
"Kana jina kayi banza dani Gwadabe ko network ne, ko ko dai wani rashin kunya Shafa tayi maka?" Tamu ya tsinke mishi zaren zantuttukam zuchin shi. Da sauri yace.
"Kai kasan komai Tamu akan Hadiza da Baba Magaji ya bani bayan na baro najeriyane. To ita Hadiza bata san da zaman Shafa ba, kamar yadda Shafa bata san da zaman Hadiza ba." Nan dai ya kwashe labarin duk yadda ta kasance musu a jiyan. Tsaki Tamu yayi kawai tare da cewar.
"Shirmen banza harma ka tunzurani ?ila saina zaneta ma. Yanzu akan wannan maganar ne duk ta takure kanta?"
"Kul wallahi kar ka soma dukan mun mata ni dai na faWa maka dan ubanka" Dariya suka yi Tamu yace.
"Wannan siriki kwai fitsararren maras kunya" Dariya suka sake sawa, kafin Tamu yace.
"Yaushe zaka shigo mana najeriyar ne Gwadabe, ka gujemu. Ko dai har yanzu damuwar rashin Iyabo ne ya hanaka zuwa? Mu kuma cike muke da kewarka, ko babu komai ya kamata kazo kaga yara" Gwadabe yaji wata kewa ta kamashi, take yaji yana sha'awa da son ganin abokan nashi da ma yaranshi.
"Tamu zan zo zuwa ?arshen wannan watan da muke ciki, kaga yau wata yayi goma biyar, yana kaiwa ?arshe zan zo in duba ku. Ya yaran?"
"Yara kowa lafiya lau sunata karatunsu hankali kwance. Toye ma dana shiga ?auye naga yayi noman masara shi da yaron Bara'u baka ga yanda masarar tai kyau ba. Na lura yaron yana da mai da kai akan abinda yake gabanshi, shi kanshi Bara'u ya yaba" Sun jima suna hirarsu ta abokai kafin daga bisani su kai sallama. Ko da yaje wajen aiki daya fito cikin ramin ha?ar zinariyar dan hutu sai ya kira lambar Shafa, bata shiga ma baki Waya. Da ?yar ya samu dai ta shiga, kuma yaci sa'a aka Wauka. Daga nan zancan fishi ya ?are, bayan ?an bayanai daya yi mata, da kuma kalamin kwantar da rai, sai suka balle da hirar soyayya, wanda rabi da kwatan hirar Shafa ke yinta, shi dai yana dai ?arfafa mata guiwa ne. Bayan sun yi sallama ya kira Hadiza ma yaji yaya jikin nata tare da Wan taSa hirar da rabinta da kwatanta labarin zafin da taji a zuchiyarta ne, shi dai aka barshi da aikin rarrashi.
Jigum ya zauna yayi tagumi bayan gama wayarshi da Hadiza. Kanshi ya Wauki caji ainun. Harga Allah shi dai bazai iya gane yana son su Hadiza ne, ko kuma yana kallon darajar waWanda sukai mishi tayinsu ne ba. Domin mace Waya tilo Iyabo itace a zuchiyarshi abadan. Yasan abune mai wuya dawowar Iyabo cikin rayuwarshi. Yana fatan inya shiga Najeriya Allah ya haWa fuskokinsu ko da a hanya ne. Yana kuma da burin son ?a?anshi su yi rayuwa a gefenshi damin ya Wauke musu raWaWin maraicin uwa a rayuwarsu. Mammada ne ya dafa kafaWarshi, yana zaune a gefenshi shi bai ko ji tawowar tashi bama. Abinci ya mi?a mishi, garau_garau irinta leburori irinsu, yasa hannu ya amsa.
"Menene Gwadabe, kaddai batun Hadiza ne duk yabi ya dameka?"
"A'a wallahi Mammada tunanin rayuwa kawai nake yi da rashin daWin aikinnan, tare da tunanin yarana da basa kusa dani anan" ?an murmusawa yayi, sai da ya ciko garsu_garau a cokali ya danna a bakinshi dam kafin yace.
"Wannan ai mai sau?ine Gwadabe, kai da kake jarumi me auren mata biyu, ai zasu ri?e maka yaranka wannan bama wata matsala bace" Abincinshi yaci gaba da dannawa a baki bashi da damuwar komai. Sai Gwadabe yaji dama ace shine Mammada da yaji daWi. Wunin wannan rana da tunanin Iyabo da yaransu Gwadabe ya wuni. Yayi ?o?arin samun layin Bara'u ma dan ya sanar mishi da batun zuwanshi, amman dai basu sami damar jin juna ba. Kamar dai yadda aka saba bayan isha Gwadabe ya aiki yara su kai mishi kiran Hadiza. Yana zaune a saman dakali tazo ta sameshi, bayan sun gaisa yayi mata ya jiki, sai shiru ya biyo baya. Dukkansu a cikin tarawa da Wabewa suke. Sai dai tunaninsu ya sha banban dana juna.
"Menene ya dameka wanda harya kasa Soyuwa akan fuskar taka, ko baka samu damar jin muryar Shafa bane?" ?agowa yayi suka haWa idanu. ?an gaj??????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????eren murmushi yayi mata tare da cewa.
"Babu mamaki dan naji sunan Shafa raWau a bakin ki, tunda Malam yasan sunan. Yaya jikin naki da sau?i, kuma kinsha magungunan da suka baki? Ya jero mata tambayoyin da yake tunanin zasu jaye hankalinta daga barin batun Shafa. Amman sai ta jefo mishi wata tambayar da cewa.
"Ni ko zan so ganin tsohuwar matarka ko da a hotone domin inga da abinda tafi sauran mata" Ta ?arashe maganar da taSe bakinta. Anan ne taga ya gintse fuskarshi dukkan annurunshi ya dakata.
"Kar ki kuma kawo maganar Iyabo anan wajen. Ki tsaya dai iyakar matsayinki da kike dashi a zuchiyata. Batun ita kanta Shafa ki shafe shi a kan ki, ni dake mu tattauna akan iyakar abinda yake gabanmu. Kuma ko ita Shafa in tayi mun magana a kan ki, ko Iyabo, dakatar mata zanyi domin babu abinda zaku ji daga gareni. Dukkanninku kuna da matsayi na musamman a zuchiyata" Ajjiyar zuchiya ta sauke. Ranta yayi matu?ar Saci ainun, idanunta kuma sun rufe da kishi. Amman a zuchiyarta tasan ita ke da laifi da bata cakalo zancan ba da ba'ayi ba ma balle har ya tsayar mata.
"Karshen watannan inaso zan le?a Najeriya in dubo su Babala da yaran wajena in Allah ya nuna mana da rai da Lafiya." Cikin dakiya tace.
"Allah ya nuna mana lokacin" Ya amsa mata da "Ameen" Shiru ya sake wanzuwa a tsakaninsu na kusan minti biyar cur, Gwadabe ne ya daure yace.
"Kishi yau ya hanaki yin magana ko Hadiza? Bansan me yasa kike damun zuchiyarki har haka ba wallahi. Mata ku dinga sassautama rayukanku akan kishi ko a zauna lafiya " Kallonshi tayi ido a cikin ido tace.
"Ashe kishin abinda kake so yana iya zama illa ni ban sani ba? Ai na Wauka wanda yake da girman daraja ake kishi ba wanda bai isa ba" Kai ya dafe tare da lumshe idanunshi.
"Yi ha?uri Hadiza kinji. Bance laifi bane dan kin nuna kishinki a gareni ba. Amman tunda lamarinnan ya faru baki bar zuchiyata ta zauna lafiya ba. Kinga na dawo a mugun gajiye yau. Hira dake yana warware dukkan gajiyar dana kwaso. Amman yau ke da kan ki kike shirin labto mun wata gajiyar ta daban ma" Yayi maganar da irin sigar daWin bakin maza mai zurma matan da basu gane kan rijalu ba ( Ummu nabeeha ana magana) Jin ya faWi haka ne yasa ta Wan sassauto har suka taSa hirar dai ba wani armashi.
Haka kwanaki sukaita tafiya dare ya shigo, haske ya maye gurbinshi. Gwadabe sai Wan siyan tsaraba yake yi yana adanawa kafin zuwan lokacin tafiyarshi. Baba Fhatsima itama sai shirin tafiya take ta tayi. Matan gidan kuwa sai tashin hankali ya ?aru a garesu. Cikin kwana goma suka shirya tsab da yamma Tasi'u ya Waukesu izuwa Airport. Al'amarin daya mugun tada tarzoma mai girma a gidan bayan tafiyarsu Malam. Dan Baba Asshi tana kuka a tsakar gida ta dinga kiran iyayen Baba Fhatsima tana kunduma musu ashariya. Hakanne ya tunzura Hadiza da su Auwala da shigowarsu kenan. Al'amarin dai baiyi daWi ba sam, Yaya Tasi'u ne ya dakatar da faWan ta hanyar yin hargagi ga ?annen nashi akan kowa ya kama gabanshi. Dan samarin Wakin Baba Asshi ma sun shiga rikicin.
"Ku yi ha?uri Baba. A dai dinga kai zuchiya nesa. Ya kamata ace yanzu ma?ota sun dena jiyo sautin faWa da ashariya daga gidan Malam. Wannan al'amarin tun muna yara aketa faman yinshi har yanzu tsugunne bata ?areba. Ya kamata ace mun haWe kawunanmu tun kafin wankin hula ya kaimu ga dare"
Cewar Yaya Tasi'u kenan cikin takaici da ba?in cikin irin rarrabuwar kawunan dake cikin gidansu. Inama zasu yadda a haWe a zama abu guda. Amman kash an bar kari tun ran tubani. Malam shi ke da sa sannu a faruwar komai, kuma yafi kowa da kowa son ganin ya haWe kan ahalinshi sun dawo abun sha'awa a yanzu da yake ganin kamar wankin hula na shirin kaishi dare fa"

BABA FHATSIMA
A hotel Win dake bayan harami aka sauke Malaman da aka zaSe aka biya ma aikin umara su da iyalinsu. A baya malam ya samu ire_iren kyautuka irin wannan, kujerar aikin Hajj ma da suka yi da Baba Fhatsima na farko wani Wan siyasa ne Babba ya bashi, a sakamakon adda'a da malam yake taimaka mishi dashi, kuma yana ganin buWin haka. Sun je umara da dama, gashi a wannan karon ma Allah ya nufa da'itan za'a sake komawa.
Zaune take akan kujerar dake Wakin hotel Win. Tana jiyo zubar ruwan wankan malam a ?asa. Zuchiyarta sai take jinta fes Kamar babu wata damuwa dake ?unshe a cikinta tsawon shekaru. Tunani ta faWa mai zurfi. Tana tuno lokacin da suka sauka a wannan hotel da suke ciki a shekarun baya. A lokacin Malam yana ji da'ita yana girmamata fiye da tunanin me tunani. Bata mance wasu kalamai da malam ya faWa mata a ranar da suka shigo makkah da

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login