Showing 27001 words to 30000 words out of 270738 words

Chapter 10 - NAMA YA DAHU ROMO DANYE COMPLETE TRUE NOVEL BY BADI'AT.doc

A wajen wata beyerabiya mai kayan miya da ni?a na sai tumatiri da albasa da attaruhu, rabi na gyara a wajen na wanke ta ni?a mun, dama mun fito da robar fenti, rabi na ?unso abina na sayi Wanyan kifi shawa da su maggi a wajenta, Uwani ma na sai mata haWin kayan miya na Wari da hamshin, maggin hamsin, man hamshin, sai kifi Wanye na hamsin, sai murna da godiya take yi mun. Muna dawowa gida na shiga aikin abinci, ni ina jajjage Uwani na yi mun tsintar shinkafa. Matan gida sai shewa suke yi, ko wacce tana girkinta a ?ofar Wakinta, Yaya Haula kuwa kajine cikin tukunya take ta aikin musu jar suya gidan ya karaWe da ?amshi, Suwaiba kuma kifi take soyawa sukumbiya Sula_bula, ga jajjage kayan miya tana yi, ga alayyawo ta baje akan tabarma. Kullum su kam a cikin cin daWi suke kullum baren ma Yaya Haula tunda mijinta kusan shine mai kuWin familyn baki Waya ma. Tukunya na Waura na zuba mai na jefa Sararriyar tafarnuwa guda, man yana yin zafi na zuba jajjagena, na wanke kifina tas na tsaane a kwando, ai sai matan gidan baki Waya kallo ya dawo gareni kawai dan hakan sabon abune a tukunyarmu gaskiya, barmu dai da yin fara da mai, ko tu?a amala da miyar ewodu ko mai babu. Yaya Haula tace.
"Lallai bana abun arziki muma ya biyo ta layin gidanmu har mun samu, ayi dai mu gani in tusa zata hura wuta" Sai suka saki shewa dukkansu, ni kuwa ko in kula na gama tsayar da sanwar girkina nasa ma uwani hannu muka ci gaba da tsinta. Sai bayan azahar girkina ya sauka na juye tumaturina a tukunya na mayar kan gawayi. Waya na Wauka na kira Burodami Debisi nace inason nama na dubu biyu dan Allah ya turo yaro dashi. Bayan mun gama cin abinci sai ko ga yaro da nama cikin ?aramar ba?ar leda dam harda kayan miya cikin leda mai zane, yace kuma in bar kuWin naman. Allah sarki Wan uwa mai daWi kiranshi nayi na dinga yi mishi godiya, ina ajjiye wayar sai ga kiran Gwadabe ashe sun dawo Yana Wakin Umman Nazifi. Abinci na tafi musu dashi, na gaishe da Babala da jiki, na Wan jima a Wakin kafin na fito."
MRS BUKHARI


3064127935
Buhari Ibrahim Ladan
First bank

Sanya nera 500 Winki kuWin karatu anan. Wannan asusun gudauniyarmu kenan.
Ki sani in kika siya wannan littafin tamkar kin taimaki iyayen marayune, dama su kansu marayun
Kuzo mu yi tarayya cikin aikin lada. ?ar?ashin Amila Foundation gidauniyar da muka buWe ni da megidana domun iyayen marayu, ko tainakon marasa lafiya.

WaWanda suke cikin group dina mai suna (NAMA YA DAHU ROMO ?ANYE)
300 kacal zasu iya kuWin karatu
NAMA YA DAHU...
ROMO ?ANYE
GAWURTATTU UKU
BADIAT IBRAHIM MRS BUKHARI B4B GIDAN ?AMSHI

8
A kwana a tashi A haka rayuwarmu tai ta garawa, yau fari gobe tsumma, babu laifi Alhamdulillah yanzu kam munfi ?arfin abinda zamu saka a bakin salati. Koda yaushe Gwadabe a cikin tafiye_tafiye yake, duk garin da ya je yakan siyo mana tsarabar garin, su bushasshen kifi, manja, doya, wake, gawayi duk yana siyowa ya kawo. Babala ta jima sosai a gidan sai data warke tsab, ana gobe zanyi arba'in ita kuma ta tattara ta koma ?auye. Irin ?o?arin da taga Gwadabe nayi a kanmu sai ya sake dagula komai. A tsakar gida Babala bata da aikin daya wuce faWin an ma Wanta asiri sai wahala nake bashi, ya shiga tarkon yarbawa jikokin oduduwa. In hakan baiyi mata ba sai ta sameni har Waki ta ?aremun tanadi tsab, ni dai zaman gidan gabaki Waya ya gundureni, haka naita ha?uri har Allah yasa ta koma Takai. Gwadabe ma haka yasha ha?uri da Babala, damuwa duk ta haWu tayi mishi yawa, ga matsala da yake samu a wajen ?an lodi akwai wani bawan Allah da yasa Gwadabe sosai a gaba, domin yawan tashi da motar Gwadabe take yi wajen sufurin kaya, ada yafi kowa ?wazo a matukan tirelolin har ana mishi kirari da giya dubu, akwaishi da sharara gudu a hanya dandanan sai ya isa ikko, yana isa zai sauke lodi ya sake nauso hanya. To samuwar mota a hannu Gwadabe sai ya doke giya dubu wajen ?wazo da kazar_kazar bil ha??i Gwadabe yake komai. Wata rana ana ma Gwadabe lodi giya dubu shi kuma shigowarshi ?an lodin kenan, da ya kalli Gwadabe sai yace.
"Wata rana ma ba zaka samu ?afafun da zaka taka mota ba, balle hannayen murza sitoyari in dai muna tasharnan gasa da ni ba daWi."
To daga ni har Gwadabe sai muka shiga damuwa daya dawo yake sanar dani, mu kaita adda'ar neman tsari harda sadaka, ga wannan damuwar ga damuwar Babala abubbuwa suka cakuWe goma da ashirin. Washe garin ranar da Babala ta tafi muka cika kwanaki arba'in. ?an biyu sun yi kuSul kuSul dasu gwanin sha'awa. Tun sassafe naketa kaye_kaye dan yau kam a gidanmu zanje in wuni yawon arba'in. Kafin sha biyu na gama duk abinda ya dace, Toye na dawowa daga makaranta, na kwaSe mishi inifom na watsa mishi ruwa, na shiryashi tsab, naima matan gida sallama. Atampa mai haske nasaka da sabon takalmi da mayafi, ina fita tun kafin in sauka daga kan tudun gidan na soma jiyo hayaniyar muryoyinsu suna gulmar da suka saba. Muna zuwa titi na tari Bus sai ?ofar Nasarawa inda anan gidanmu yake. Cikin layinmu na shiga tun daga titi nake gaggaisawa da mutane, wasu dole ma in tsaya su ga ?an biyu a haka harna isa ?ofar gidanmu. Gidane mai Wauke da karamar ?ofa gefe da gefen ?ofar shagunane biyu. ?aya na Iyaa Debisi daya na Iyaa Kokodeen. Iyaa Debisi soson danga dasu lagwani, ashana, sitati, gyalu, bula, kayan robibi. Su take siyarwa tana da injin ni?a har biyu dana wuta dana ruwa. A shagonnan mu kai rayuwarmu, akwai ?ofa a cikin shagunan wanda zaka Sulla babban tsakar gidan namu. Iyaa Kokodeen kuma albo, garin Amala, daddawar kalwa, da bushasshen rogo, garin rogo su take siyarwa harda ma kamun jar dawa. Wannan sana'ar tasu da ita muma mu ka yi wayo muka gansu akai, gashi har yanzu ana takusawa. A bencin dake ?ofar shagon Iyaa Debisi na zauna dan na gaji sosai. Toye kuma yayi cikin gida da gudu. Iyaa Debisi tana zaune a cikin shago taci leshi Winkin buba Waurin Wankwalinnan a cukurkuWe sai gyangyaWi take ta yi abunta, dama kullum aikinta kenan wannan gyangyaWi ba'a rabata dashi, kuma a zaune ake yinshi.
Iyaa Iyaa!! Na kirayi sunanta tare da Wan buga benci kaWan sai ta buWe idanunta muka haWa idanu.
"Ahhh Iyabo kece da tsakar ranar nan da yara, ku yaran zamani baku da hankali ai mace mai goyo ko ciki bata fitowa sa'ilin da rana ta take. Maza shiga ciki gani nan zuwa. Mahaifiyarki ma yanzu isowarta ko awa Waya ba'ayi ba tana ciki" Mi?ewa nayi ina fara'a dan na jima banga Mamana ba. Shagon Iyaa Kokodeen na shiga na dur?usa a gabanta na gaisheta , itama tace maza in shiga ciki rana ta take. Ko da na shiga samarin gidan basa nan kowa na wajen aiki, babu ?an mata a gidan tuni sun jima da aure, Bose ce da aka bari itama gashi tana gidan mijinta. Sai matan ?annen su Iyaa su su uku Iyaa Beji, da Iyaa Lekan, sai Iyaa Amope. A Wakinmu na ya da zango mahaifiyata tana tsaye tana sallah goduwa farar bafulata siririya, gata da alkunya da sanyin hali bata iya sakewa tayi hira dani, iyakarta dani gaisuwa da tambayar ya nake ni da mai gidan nawa. Iyakar hirata da'ita kenan saita tsuke bakinta tayi shiru kanta a sunkuye." Tana idarwa ta juyo tace.
"Jabu kune a tafe? ( Jabu sunan da dangin mahaifiyata suke kirana dashi kenan, dangin mahaifina kuma iyabo)" Data juyo sai naga ta rame sosai idanunta sun zurma da yawa"
Dada kinzo lafiya ina wuni?"
Bata amsaba sai mi?o mun hannu da tayi na tashi na sunto yaran na saka mata a cinyarta. Tayi ?uri tana kallonsu tana musu adda'a. Take Naji hawaye na kwarara a idanuna, Allah ya Waura mun tausayinta sosai a zuchiyata. Inna dubeta sai inga kamar tana cikin ?unci da matsi a gidan aurenta.
Dada baki da lafiya ne naga kin rame?"
Cikin gurSatacciyar hausarta ta fulanin daji tace
" E jinya nayi kusan wata shida sai dai a kwantar sai dai a tayar, shine dalilin da yasa ban Sulloku ba."
Sai kuma taci gaba da magana dani da yarbanci, dan Hausa mugun wahala take bata, dama da yarbancin muke magana."
"Ashe kin samu ?aruwa Allah ya raya. Ina Wayan jikan nawa?"
Ajjiyar zuchiya na sauke nace.
Yana Wakin Iyaa Beji can na baro shi, ya wajen BaWWo da mai gidanta? ( BoWWo ?anwatace a gidan da Dada take aure yanzu, sau Waya na taSa ganinta tal a rayuwata)
"?oWWo ta haihu tana goyon Daso an yi mun takwara" Sai naji ina kewar ?annena da dangin mahaifiyata ma, sai naji inason kasancewa dasu.
Dada inaso in zaki koma zan tambayi izinin mai gidana zan biki in gano rugarku, inaso lokaci zuwa lokaci in dinga zuwa ziyartarki ke da danginki nima ya kamata yarana su san dangina na wajen uwa su saba"
Da sauri ta Wago ta dubeni tace.
"Kar ki soma, kiyi zamanki na yafe miki. Ni zan dinga zuwa ina dubaki kamar yadda na shafe sama da shekaru ashirin ina zuwa ganinki."
?ur nayi mata da idanu ina karantar yanayinta, duk sai naga ta ruWe, tashi tayi ta bani su Taiwo ta haye ?aramin gadon Iyaa ta kwanta ta juya mun baya. Na rasa me ake Soye mun ne da Dada bata ?aunar in ziyarceta, bata son danginta su sanni, to meke faruwa ne tabbas tana ?asa tana dabo. Iyaa ce ta shigo tana faWa sosai kamar zata ari baki, tana yi tana dukan cinyarta tanata faman yare. Ashe da Debisi take yi shigowarshi cikin gidan kenan. Da yare yace da'ita.
"Kiyi ha?uri Iyaa nifa ba cewa nayi yemisi ta ajjiye aikinta ba, gani nayi ta fifita aikinta fiye da zaman auren da muke yine. Kuma tama ga damar zuwa ta haWa mun jarfa ne" Ya ?arashe a sanyaye. Iyaa Kokodeen ce ta shigo Wakinnan tace.
"Haba Iyaa Debisi wannan yaron fa yana da gaskiya kuma ma ai yayi ?o?ari sosai Ya kamata itama yemisi ta dena zuwa tana yawon kawo ?ararshi wajenki ko wajen mahaifiyarta. Ai ga irinta nan abunda ake hango muku daban abinda kuke hango ma kawunanku daban, ku kun Wauke mu ba wayayyuba. Dama duk namijin da zai auri soja ai dole sai dai ayi zaman ha?uri." Wannan maganar tamkar ingiza iyaa Debisi Iyaa Kokodeen tayi dama har gobe da mikin ?in aurena da Burodami Debisi yayi a zuchiyarta. Dan da ?yar ma aka shawo kanta bayan aurena ta zubar da makaman ya?inta, macace mai kafiya da binbinni, gata da mita.
"Basshi ai duk abinda na guje mishi kenan, shi yasa naso ya auri ?ar uwarshi Iyabo. Musamman dana fahimci ita iyabon tana sonshi. A gida ma ita ke kula da komanshi ina ga ya aurata. Yaronnan ya buWa mana ?asa a idanu, dana matsa ya je ya haWoni da dangin ubanshi akazo aka danneni. To yanzu me yake so ayi mishi? Ai haka zaka je kaita kwashe takaici da ba?in cikin zama da Soja, kuma ban yarda ka sake takurama Yemisi akan batun aikinta ba." Daga ni har Burodami Debisi muka yi tsamo_ tsamo tamkar kazar data faWa ruwa, ya Wago mu haWa idanu ya kasa sabida kunya tare da nadamar abinda ya aikata. Lokacin na shiga tunanowa a zuchiyata, a lokacin da Burodami Debisi ya murtsuke idanunshi yace shi Allah ya kashe shi bazai aureni ba. Ji nayi tamkar al?iyamatace ta tsaya. Abun bai zo mun da daWi ba, domin jaririyar zuchiyata da so da tsantsan kaunarshi ta ginu, ban taSa tunanin zuchiyata zata iya son wani mahaluki bayan Burodami Debisi ba. Ni ban iya sa abu a zuchiyaba, ban iya son abuba. Da wasa da wasa Gwadabe ya maye gurbin dana adana Burodami Debisi a ciki, harya samu matsayin da shi kanshi Burodami Debisi bashi da irinshi. Yanzu kuwa da Gwadabe ya riga ya lasamun giyar sonshi na shiga mayen ?aunarshi jinshi nake tamkar numfashina, ko kuma bugun zuchiyata, ina ma mijina irin son da har abada bazai iya samun macen da zata so shi kwatan son da nake yi mishi ba. Muryar mahaifiyata ne ya katsemun tunani, cikin ?warewa a yaren yarbanci ta soma magana kamar ba bafulatana ba.
"Ai aikin gama tuni ya gama. Abinda zai faru ya faru. Jabu tayi aure harda albakar aure. Shima Debisi yayi aure harda ?aruwar haihuwa. Ni ina ganin Toyosi ki yi haquri ki kawar da wannan batun. Kai kuma Debisi aure ai cike yake da ?aWdarori iri daban _daban. Ita kanta Jabu kana ji da ganin irin matsalolin da take fuskanta da dangin mijinta, auren ba daWinshi take ji ba ana dai zaune zaman yara ko ba haka ba Alima?" Ta kai dubanta kan Iyaa Kokodeen wacce ainihin sunanta Halima, to a harshen yarbanci kuma sukan maiyar da harafin H a matsayin a misali Alima a madadin Halima auwa a madadin Hauwa, Abu a madadin Habu. To itama Iyaa Kokodeen manya da Alima suke kiranta. Ta dubi Dada tace.
"Gaskiya ne sosai, mu kanmu wanne ha?urinne ba mu yi ba, namu ha?urinma na mutan da ba irin na yaran zamani ba. " Ranar Burodami yasa mita, sai an kawar da maganar sai can ta dawo da zancan baya. Har Burodami Debisi ya gaji ya bar gidan amman bata sauya zani ba. Haka dai wunina ya kasance bamu muka tashi shirin tafiya gida ba sai da magriba ta kawo kai. Akamu Iyaa Kokodeen ta bani da garin albo dana amala, bata taSa gajiyawa muddin zanzo sai ta bani. Dada kuma ta mi?o mun ?unshin bakon da tayo mun tsarabata.
Dada yaushe zaki koma, amman zaki zo gidana ko Dada?" Kawar da kai tayi tace.
"Me zai kaini gidanki Jabu, ai babu. Jibi zan koma ni kam in sha Allah "
To Dada gobe zan dawo akwai sa?o da nake son baki ki ba su BaWWo."
Kai kawai ta gyaWa mun. Iyaa kuma ta dire tace ban isa in dawo ba, in Lekan yananan in je Wakin zaure in kirawoshi in yaso sai ya bini ya amso sa?on" Ba dan naso ba akayi hakan. Da Lekan muka dawo gida. ?annena su su huWu ne, biyu mata biyu maza. Matan na cira musu atampopi guda WaWWaya sababbi dal. Na cire ma Dada lashi da Atampa coddibuwa, Baffa kuma na cire mishi shadda guda Waya ce rak. Na cirama ?annena mazan kaya kala WaWWaya a cikin kayan da Hajiya ta bani in ba Gwadabe. Dada na ?ara mata da mayafai da hijabi, da sabon takalmi dan naga takalmin da tazo dashi a ?afarta takalmin robane duk ya sha li?i gashi har Sulewa yayi. Nera dubu goma na zara na mi?a ma Lekan. Yasa hannu kenan zai karSa Laila ta shigo babu ko sallama. Banji daWin shigowar tataba sam, bin Lekan da kayan da na soma cusa mishi a bako tayi da kallo.
Lekam muje nayi ma bayani a ?ofar gida" Biyoni yayi a tsakar gidanma da idanu yuuu su Yaya Haula suka bini. Baban Nazifi ya daka mun wata tsawa fitowarshi daga ban Waki kenan.
"Waye wannan sannan wannan kayan da Za'a fita dashi menene a ciki?" Ya jufo mun tambayar bayan ya iso gabanmu. ?an fodiyo dake zaune a tabarma suna ?irga kuWi shi da Da'u ai sai ya taso yasa hannu ya fisge ledar hannuna ya zazzageta a ?asa komai suka zubo ?asa. Ganin matan gidan a gaban kayan Yaya Haula harda salati yasa na fashe da kukan ba?in ciki. Jin amon muryar Yaya Harisu ne yasa na sassauta.
"Ina za'a kai kayan. Shi wannan gona_gonan ?aton da kika shiga Wakin mijinki dashi alhalin kinsan Gwadaben bayanan fa, ko gwalen naku na yarbawan zaki shigo mana dashi?" Lekan sarkin zuchiya har zai yi magana na dakatar dashi da yarbanci cewar kar ya sake yace komai. Na mayar da hankalina kan Da'u da Baban Nazifi ya bashi umarnin wauwara kayan. Kayan maza da suka gani yasa Baban Nazifi Wago rigar yace.
"Wannan ba rigar Gwadabe bace Iyabo. Wato sace kaya kike yi ?annenki suna zuwa da daddare suna fitarwa ko? Kenan doguwar rigar Haula data Sata muna tunanin ruwan sama ne ya gudu da'ita ta rariya ashe kece kika sata? Asirin??????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????ki ya gama tonuwa a gidannan ?ila harda ?arshen zamanki " In kada baki in yi magana na kasa. Lekanne yace.
"Wannan kayan data samu a sunan Taiwo da Kahinde ne, sauran kuma nata ne na gida, sai kayan mijinta guda biyu. Mahaifiyarta ce tazo daga ?auye shine ta bayar a kaima ?annenta, kuna da matsala da hakanne to? Batun sata kuma Antimi Iyabo ba Sarauniya bace ba'a mana wannan tarbiyyar ba." Salati Gude ta saka tace.
"Au ita Iyabon dama tana da ?anne mu bamu sani ba? Sannan iyakar saninmu uwarta ma ita kanta ba tace ga inda take ba, yasar da'ita tayi tun tana ?arama ai." Yaya Harisu yace.
"To munji babu kayan da zai fita a gidannan. Kai kuma fice mana a gida" Kamar kuwa jira Lekan yake yi ya fita fuu yana sababi da yare. Da manuniya Yaya Haula ta nuna ni tace.
"Wabillahillazi huwarrahmanu sai kin biyani doguwar rigata, nera dubu takwas na siyeta , tunda na kama Sarauniyar rigar." Nan su Gude suka soma tafi tare da yi mun kururuwar naji kunya. Tsugunnawa nayi jikina na rawa na kwashe kayana zan shiga Waki dasu, Baban Nazifi ya warce buhun yace.
"Har sai kin biya kuWin rigar da kika sata zaki samu kayanki, Allah wadaran halinki." TiSi_tiSi da kayan mazaunai na tafi Waki da gudu na faWa akan gado na sau rikitaccen kuka irin wanda ban taSa yin irinshi ba a duniya. A wannan halin Gwadabe ya dawo tafiya ya tarar dani, dan wallahi ko sallamarshi ma banji ba, sai jin hannunshi nayi a jikina, ina Wagowa da naga shine na kife na sake rugujewa da kuka. A ?agauce yace.
"Wani abunne ya faru da kika je wunin gida ko? Iyabo kiyi ha?uri ki dena kuka akan matsalolinmu dan Allah."

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login