Showing 120001 words to 123000 words out of 270738 words

Chapter 41 - NAMA YA DAHU ROMO DANYE COMPLETE TRUE NOVEL BY BADI'AT.doc

nina mun Farida tace ai an Waura aurena da'ita. Kinsan mutanen ?auye gani suke yi wani kuWi nayi. Ni kuma a cikin kuWin da nazo dashi da ?yar na ?u?uta harda bashi na sai Wan ?aramin gida mai Wakuna uku rak. Amarya ta tare a Waya, Wayan nazo wajen Hajiya na karSi yarana suka tare a ciki, Wayan kuma na kulle mata a matsayin Wakinta. Shine fa ta?i fahimtata ca take wai ita in saketa kawai. Yanzu taya zan saki uwar ?a?ana uhm Alaja Iyabo ki duba zancena sabida Allah kiyi mun adalci"
Jikina yayi murus hankalina sai naji ya tashi. Lallai in har haka ta faru da Uwani. Ni kam ina cikin goma sha biyu. Uwani duk sabida rufin asirinsu ta tafi wannan ?asa, amman jibi abinda ya biyo baya kafin dawowarta. Ina kuma gani da ko kalmar so Yaya Hamma bai furtamun ba?" Da ?yar na yakice tunani na sauke ajjiyar zuchiya nace.
Shikenan Hafizu zata dawo Wakinta amman dole sai dare. Sai dai da yamma ni da Ummi zamu zo mu yi mata jere" Baki ya washe yana dariya ya mi?e. Har fa ya kai bakin ?ofa ya dawo.
"Alaja Iyabo ni kuwa kayan naku masu isowa har dila nawa ne?" Hararar da Uwani ta zabga mishi ce yasa yayi firgigit ya fice yana dariya"
"Kikace zan koma Iyabo? Ni wallahi da naso in ha?ura da Hafizu. Duk wannan tatsuniyace fa ya baki Wan iska marar mutunci"
A'a Uwani ki koma kan ?a?anki, ki ri?e sana'arki ki kula da kanki da ?a?anki. Ki godema Allah ba mazinaci Hafizu ya zama ba, kuma ki gode Allah baki mallaka mishi dukiyar da kika sha ba?ar azaba wajen tarata ba. Yanzu dai ki taso muje mu sai kayan Waki na gani a faWe."
Harara ta gallamun. Nayi dariya nace.
Zaki bari matarshi ta rainaki ne, ke da kike Hajiya? Uwani kiyi ha?uri dan Allah karma ki nuna ma kishiyarki wai kinji zafin abinda suka aikata miki."
"To Shikenan Iyabo. Na Wauki shawararki. Amman sisina bazan iya kashewa akan Hafizu ko matarshi ba wallahi in tsirara zasu yi yawo sun dade basui ba. Muje ni dalla"
Fitowa mu kayi, daidai Iyaa itama ta fito.
"Ina zakuje kuma?"
Zan raka Uwani ta siyo kayan Wakine da daddare zata koma gidanta" Hajiya ta taSe bakinta tace.
"Sun gama tata Surzar kenan? Ai ha?uri dama dole za,a yi daga ?arshe, kindai ga halin mazan dai. Wannan ya isheki hankali sai ki tattala dukiyarki kiyi abinda zai fissheku. In da ke kaWai kike da Hafizu to yanzu ku biyu ne. In da ?a?anki ne kaWai ?a?a yanzu suna da ?an uba harda wani cikin" Ni dai jikina sake mutuwa murus yayi. Zuchiyata saita shiga cikin taraddadin abinda ni kaina zanje in tarar a ?auye. Ni dai har muka isa shagon saida kayan katako da Uwani da ?annenta mata biyu da suketa mana biyayya mu ga hajiyoyi. Kado da sib da mudubi kawai muka siya, sai labule da makeken kafet mai taushi. Kayan kitchen kuwa Wan tsakura tayi sabida nanda wata Waya kayanmu zasu iso. Ni da ?annenta ne muka wuce gidan, ita kuma ta wuce kasuwar kurmi Wan siyayyar kayanmu na mata.
Gidan wani irin gantalallen gidane ginin laka, ko filasta babu a tsakar gidan, datti da shara takota ina. Hafizun yana zaune a ?ofar Wakin da ya kasance na Uwani. Amarya kuma sai wanki take yi ga ciki a jikinta ga yaro a ?ofar barandar Wakinta a kwance."
Hafizu masu motar kaya suna waje ka taimaka musu. Amarya barka da gida" Na faWa a tare. Babu yabo babu fallasa ta gaishemu kana taci gaba da wankinta. Niko ?are mata kallo na shiga yi tsab, in banda abun Wa namiji ni dai banga ta inda za'a haWa Uwani da kishiya irin wannan ba. Ko da yake ita mace duk lalacewarta da ?auyancinta tana da tata baiwar da Allah ya huwace mata. Dan a hakam saita zama zarah a zuchiyar Hafizu. Shigowar su Hafizu da sib me murfi huWu ce tasa na dawo hayyacina.
Amarya a ara mana tsintsiya dan Allah " ?an murmushin ya?e tayi tace.
"Wallahi gidan bani da tsintsiya. Nima da tsumma nake sharar Wakina" Ai sai na rike baki tsintsiyar laushi ta nera goma ace ta gagari yarinyar mace.
KuWi na ciro na ba Ummi nace.
A siya tsintsiyar laushi data zabori, sai abun kwashe shara, da kwandon shara. Ki siyo kwandon sharar babba da ?arami, a siyo omo."
Nan da nan ummi taje ta siyo dake layin cike yake da shaguna. Tas muka wanke Wakin muka koro ruwan tsakar gida. Amarya ta bamu tsumma muka goge Wakin. Muka shirya Wakin Amarya tas da taimakon Hafizu sai Sare_Sare yake yi har ciwo yaji garin shigar da madubi. Amaryarshi sai harara take doka mishi. Ummi nasa ta share tsakar gidan ya dawo saiti, nasa suka wanke ?azamin banWakinsu mai zarni da warin masai. Bamu muka bar gidan ba sai biyar na yamma. Zuwa bayan Isha na raka uwani gidanta. Muna shiga Wakin ta kalli Wakin ta sharce hawayenta tace.
"Iyabo ni kam zan sai gida madaidaici kamar wannan ni da yarana saimu koma. A Wakinnan ta ina zan soma kasuwanci, banga inda zan ajjiye dilolina in sun ?araso ba. Nifa Iyabo ha?urin da zanyi a gidannan na kafin a samamun gidane in siya" Dafata nayi.
Uwani babu laifi dan kinyi hakanma. Nima kuma na goyi da bayan ki sai gidan naki ki ware kan ki. Ni zan tafi ?auye gobe sassafe, in dilarmu ta iso nasan zaki karSo mana ki ajjiye mun tawa a wajenki. Ni kaina jikina yana bani zanje in tarar Yaya Hamma ya cika gidanshi da Mata, uwani gashi Allah ya jarabceni da tsantsar sonshi.
Tsaki tayi tace.
"Ni bawai Hamma bai cancanci ki soshi bane. Ni gani nake kashe rayuwarki kawai zakiyi in dai Hamma kike son ki aura. A wannan ?ungurmin ?auyen kike sha'awar rayuwa alhalin na ?auye suke fitowa birni Iyabo. Kiyi nazari, ki kuma auna Hamma da Salim, sannan ki yi nazari mai zurfi kafin ki je ki faWa abinda zai zame miki matsala. Rayuwarki ce kece zaki zauna" Da wannan mu kai sallama na koma gida.
Nima da wannan nake cewa daku sai gobe in Allah ya ara mana rayuwar.

MRS BUKHARI


09153081057
Ga masu san magana dani kai tsaye ta whatApp ga number na
Masoyana sunata mun ?orafin babu number na a jikin littafi kuma suna son muyi zumunci, ?orafi ya ?are.



*Ina kuke mata ?an ?walisa irin Shanono? Ku firfito ga Uom Taufiq veils bead work and Abaya stone work gliter veils lafaya. Ta zo muku da haWaWWun aikin beat na hannu domin kwalliyarku da fito daku ku yi tsab.*
*Aikinta babu ha'inci ni na tabbatar. Nima Badiat Ibrahim zan bata aikin lafayata ta zuba mun aikin beat work kuzo muje tare ta gwangwajemu*
07082649563 whats app number kira 07036028230
NAMA YA DAHU...
ROMO ?ANYE
GAWURTATTU UKU
BADI'AT IBRAHIM MRS BUKHARI B4B GIDAN ?AMSHI

17
Ina daf da shiga gidan wan mahaifina Alfa Kulle dan in mishi sallamar gobe zan koma ?auyenmu. Sai naji muryar Burodami Debisi.
"Iyabo tun magriba nake jiranki a tsakankanin gidajannan biyu. Dan nasan gobe zaki tafi wajen Hamma. Nayi imani da ace yasan kin dawo da yanzu yana nani?e dake" Cikin kishi da jin zafi yake maganar. Ni dariya ma ya bani sosai. Sai da na dara tukunna kana nace.
To mu shiga inma Alfa sallama in mun fito sai muyi magana. Shi kuma Alfa muna shiga bayan na karanto mishi inaso zan koma ?auyanmu kamar jirana yake sai yace.
"Ba zamu saka miki idanu ba, sai kuma ki kawo maganar aure a gabanki hakanan. Na baki wata biyu ki fito da miji, in baki fitar ba zamu fitar miki. Dan da ace Toye yana da ranshi ma ko Saudiyya da kika je ba zai bari kije ba. Tun kafin jama'a su soma miki wani irin kallo gara ki fitar da mijin aure" Kaina a sauke nace.
In sha Allah kafin lokacin yayi zan fitar Baami." A gidan muka ci abinci a cikin Wakin Iyaa Ramata."
"Kin tuna da wancan gadon da in kun mun lefi ke da Bose kuke shigewa?" Cewar Debisi daya samu saken daga ni sai shi a Wakin. Dariya kawai nayi inacin amala.
"Yaya batun aurena dake ya kwana Iyabo? Tunda Allah ya dawo dake ya kamata muyi magana tsayayya" Rai na haWe nace.
Har abada ni da kai ba zamu zama mata da mijiba, muna nan a matsayin Yaya da ?anwarnan. Na riga na faWama tun kafin in tafi. Ina ni ina haWa miji da Soja?" Murmushi yayi mun har yana gyaWa kai.
"Lallai yarinyarnan bakin ki ya buWe. Nifa wallahi da gaske nake yi, da kinsan irin yadda sonki yake nu?ur?usar zuchiyata nayi imani da tuni kin ceci ran Wan uwanki" Kallon dana watso mishi bansan na iyaba, a mafarki banyi zaton zan iya mishi makamancin wannan kallon ba. Amman sai gashi nayi. Hannuna na tsame tsam a abinci na ficewara na bar gidanma baki Waya. Koda na shiga Yemisi na zaune tana zaman jiran mijinta su koma gida. Ban jima da shigowa ba sai gashi, ko shigowa baiba cikin ?ailula yace ta fito su tafi, gaga_gaga yai ma Iyaa sallama.
"Iyabo wai menene tsakaninki da Hamma? Dan naga damuwar da yayi akan lamarinki abun yayi yawa, yafi ?arfin ace ?an uwantakane kawai. Duk sanda Daso zata zo bayan tafiyarki dashi ake zuwa. Shine nake son jin ina fatan ba tallar nono zaki koma yi ba, ki dawo mai sharar kashin shanu da dafa madara. Ai in abune mai daWi da ba haka ba. Rayuwar matan fulanin daji cike take da bauta, matan da yawa da wannan tallar nonon suke ciyar da gida, su kuma mazan suna bin jeji_jeji suna kiwon shanunsu. Ke irin rayuwar da mahaifiyarki take yi irinta zaki jefa kanki aciki? Kwanaki can da Debisi yaje ya tarar da Daso ba lafiya ga ?aninki Amaduyal ya dawo daga inda suke fita kula da shanu ga kuWi a jikinshi a kaita asibiti ubansu ya hana. Sai Debisi ne ya dinga jigilar sai mata magani shima a Soye ana bata. Irin rayuwar da kike sha'awa kenan ko?" Illahirin jikina sai naji yana rawa da ?yar nai kokuwa da harshena wajen sarrafashi.
Iyaa ni bazan yi tallar Nono ba. Kuma Hamma shi yana fita aiki a birni masinja ne a ma'aikata bai dogara da iya kiwon shanu ba, mijin BaWWo yafi fita da shanun.Sannan....
"Otito ( ya'isa haka) ki dai yi tunani ki kalli uwarki a matsayin mudubi zaki gane mai nake nufi. Rayuwar ?auye sai ?an ?auye madamar suma sun fito ko ziyara dan dole suke zuwa" Ta dinga mun kwatance iri da kala. Da waWannan tunanin gari ya waye damu. Gaga_ gaga bayan nayi wanka nayi Sallah, saina saSi akwatina. Nayi sallama da mutan gidanmu sai tasha. Motar Adamawa saura Mutum uku ta cika, nayi zamana ina ta aikin tunanin yadda rayuwa zata kasance inna auri Yaya Hamma. Sai wani shashe na zuchiyata ya tunasar dani cewar "Ai masoyi masoyine imma a birni imma a ?auye. Zaman aure nutsuwa ake nema, soyayya babu ruwanta da Wan birni babu ruwanta da Wan ?auye. Ban rufekuba na faWa muku ni Allahn da yayini in inason abu idanuna rufewa yakeyi bana ji ko gani akanshi. ( Ina ma?iyan Hamma kuna dai jin tsuntsun soyayya abinda take faWe) Wannan tunanin saiya saisaitani, yayinda motarmu ta saitu a hanya ita kuma, mukaita ratata gudu. Bayan gushewar sakanni, mintuna, awanni sai gani a Jere Banyo cikin yardar Ubangiji sai dai galabaita da nayi. Hanyar shigowan tananan inda na barta babu abinda ya canja. Gidan Yafendona na nufa kai tsaye da sallama na shiga. Harira kaWai matar Jatau ce a gidan itama da halama dawowarta kenan.
"Jabu use kece a garin naraba da ba?in larabawa" Da kwaSaSSiyar Hausarta tayi magana
Nice Hari, Yafendo bata dawo tallan nono bane?" Sai naga fuskarta ta sauya daga murnar ganina izuwa alhini.
"Hmmm Yafendonki tana gidanku wajen Baba Daso jikinta yayi tsanani sosai yau dan ance batasan wanda yake kanta ba ma" Daga tsayen na saki akwatina iyakar jakar hannuna da kuWaWena suke ciki na sake mata kyakkyawan ri?o. Sauri_ sauri gudu_gudu na dinga haWawa dashi zuchiyata tana fat_fat harna iso ?ofar gidan. Dawowar Baffan su BoWWo daga kiwo kenan. Yana tsaye yana kora shanu ciki. Ni kuma na rakuSe a gefe ina jiran garken shanun su gama shiga, mu gaisa in kuma ro?eshi inason ganin Dada. ko kallon inda nake baiyi ba har sai da shanun suka gama shigewa ya kalleni.
"Kar ma kice gidannan zaki shiga. Na haramta miki shiga cikin gidannan Silgel (Yarinya) Dan haka kiyi maza ki bar wajennan.
A guje wani saurayi ya fito yana faWin
"Baffa Dada zata mutu jijjiga take yi"
Jin haka yasa na kutsa kai da gudu cikin gidan, da kuma ?arfina dan idanuna ya rufe sai ganina nayi a Wakin Dada a tsaye. Baffan yayi yin?urin hanani shiga gidan, da ?arfin tsiya na bangajeshi nayi shigewata
Tozali nayi da sanyin idanuna yana tallafo kan Dada daga kwancen da take duk ya kiWime. Wata ajjiyar zuchiya ya sauke.
"Adda Jabu ashe kin dawo, gashi inzo kin samu Dada a wani irin mawuyacin hali rai a hannun Allah"
Cewar BaWWo data ?arashe maganarta da kuka. Hannunta na ri?e nima ina kuka ?annena suka tawo gareni suna neman kafaWar da zasu Waura kansu suyi kukansu. Mijin BaWWone yace.
"Amaduyal dole fa akai Dada asibiti" Inajin haka nace.
Anemo mota maza zamu kaita asibiti yanzu" Da sauri na ?arasa kusa da'ita da ?yar take jan numfashinta Yaya Hamma yana goge mata fuska da ji?a??e tsumma dan zazzaSin jikinta yayi tsanani ainun.
Sannu Dada"
Carab tana jin muryata Allah cikin ikonshi saita ri?e mayafina carab kamar wacce zata gudu. Kukanmu kawai ke tashi a Wakin har su Amaduyal suka shigo da sauri Yafendo Mahaifiyar Yaya Hamma tace.
"An samu motarne?"
"Ansamu malam iro zai kaita a motarshi. Ina fita shi kuma ya kawo kaya yana saukewa," Kintsa Dada akayi bayan mazan sun fita daga Wakin. Dani da BoWWo ne muka tarairayota jikinmu su Yafendo na taimakawa har muka fito. Kishiyoyin Dada su kai ca a kanmu.
"Ke BoWWo ba Baffanku yace kar a kuskura a fitar da'ita gidan ko wanne me magani ba?" Yafendo tana sharce hawaye tace.
"A wannan gaSar da Yaya Daso take bu?atar taimako, bama bu?atar sahakewar mai nagge. Mujenku Jabu"
Har munje bakin ?ofar fita muka jiyo Baffa a bayanmu yana cewa
"Indai kuka nuna kun fini iko da Daso, to in kuka fitar da'ita a gidannan to na saketa saki Waya. Ku kuma Cubu ku wuce cikin gida ?an gatan uwa."
Wani ba?in cikine ya dirarmun a ?ahon zuchiyata babu shiri na runtse idanuna, yayinda hawaye masu zafi sukaita shatatomun. Amaduyal da Hamma ne suka amshi Dada suka fice da'ita. Yafendona tana kuka tace.
"Me nagge kanka ka cutar ba Daso ba. Kuma ka sani sai Allah ya tsayar daku ya fitarma da Daso hakkin zaluntarta da kayi a rayuwa. Ga gidanka nan, ?a?anma gaka gasu ?ila sune zasu zama jarabawarka. Sannan ka shirya tsab tunda bakwa aure dole ka dawo mata da garken shanunta." Da gaggawa muka fita a cikin gidan, Yaya Hamma ni yake kallo idanunshi sun zama jawur kamar garwashin wuta. Namadi ne yace.
"Yafendo ku shigo mu tafi numfashinta tuni ya Wauke fa" Bayan akori kurarnan muka shiga dukkanmu. BoWWo tana goye da wata fara kyakkyawar yarinya mai gashin fulani a kayinta. Sai dai ita uwar duk kazanta da rashin zama a waje Waya ya komaWar da'ita. Kaina na sauke ?asa ina ma Dada adda'ar Allah ya bata tsawon rayuwar da zata ji daWi taci ribar ?a?a.
Cikin gaggawa muka wuce babban asibitin gwammati dake cikin garin Adamawa, sun so mu tsaya a asibitin Girei, ni kuma nace mu tafi babban asibiti kawai, ai kuwa muna shiga na shiga cikin asibitin da hanzari dan neman agajin ma'aikatan jinya. Yaya Hamma da Amaduyal kuma suka kinkimo Dada zuwa wani dogon falo. Ma'aikatan jinyarnan da suka ga mu fulanin Daji ne sai suka banzatar da lamarinmu ga Dada ko numfashi bata yi, sai da muka yanki kati muka biya kuWin gado kana suka sauraremu. Ward Win mata aka kwantar da Dada, sai dai bata samu gado ba, a katifa aka kwantar da'ita. Kasancewar Wakin cike yake dam da marasa lafiya, rabi da kwatan majinyatan Wakin fulanine. Wani dattijon likitane yazo kan Dada, dubanmu yayi yace.
"Ku duka yaran majinyaciyarne?" Yafendona tace.
"Duk yaranta ne, mu kuma ?annenta ne" Kai ya girgiza yace.
"Allah sarki, to ku Wan dakata daga waje zan dubata, inna gama sai ku dawo ko? Amman zaku iya komawa gida ku Webo kayan jinya dan naga jikin mahaifiyar taku da tsanani ri?eku zamu yi. Ku tawo da bargo babba na rufa, dan zata iya jin sanyi cikin dare, wannan na asibiti bashi da kauri" Ni dai da ?yar nake Waga ?afata sabida yanda naga halin da Dada take ciki, da irin ?anjamewar da tayi duk saina sare.
Zama muka yi a bencin da aka tanada domin zama. Babu me cewa da kowa komai. Ni dai duk Wagowar da zanyi saimun haWa idanu da Yaya Hamma. Hankalinshi gabaki Waya yana kaina ko ?ibtawa bayayi. A tsaye yake yayi tsaiwa irinta fulani, irin tsaiwar da suke yi da ?afa Waya, Wayar ?afar sai su Waurata akan Wayar. Fararen kaifafan idanunshi sai yawo suke yi a jikina.."
"Jabu yaushe kika dawo, ya kika baro jama'ar makka?" Cewar mahaifiyar Yaya Hamma.
Shekaran jiya jirginmu ya sauka a Legos, jiya muka shiga Kano Yafendo.
"Allah sarki sai kika dawo kika tarar da Adda Daso cikin jinya. Shekararta guda munata fama. Hamma shi yaita jigilar nemo mata magunguna ?auye_?auye bai taSa gajiyawa ba. Babu abinda zamu ce dashi sai dai muce Allah ya bar zumunci. Cewar Yafendona. Sai naji zuchiyata ta sake nitsewa a so da ?aunar Yaya Hamma. Wanda zaima mahaifiyarka wannan hidimar ai dole kaji ka soshi. Murmushi nayi nace.
Allah sarki. Yaya Hamma Allah ya saka maka da Alkhairi. Allah ya bar mana zumuncinmu. BoWWo kema ciwon kika yi ne naga duk kin fice a haiyacinki?" Na tambayeta cikin kulawa.
"A'a Adda yanayin canjin rayuwane kawai, da kuma ciwon Dada,. Yaya Amaduyal wannan itace yarmu Adda Jabu" Tana faWar haka Amaduyal ya rusuna kanshi a ?asa yai mun sannu da zuwa, sai murnar ganina yake yi. Nima naji daWi sosai


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login